Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

binta ta fada haka ne


To yanxu zo kiji binta ta rada ma ummie shewa sukayi sannan suka tafa


To kinga mu fara gwada wannan shawaran sai muga me zamuyi bayan sa

Suka tashi cikin karfin gwaiwa


Shi kuwa namijin gaske dakin sa ya nufa ya kwanta ruf da ciki yana tunani yanxu ne ya kamata ae yaja suhailat a jiki dan ya kamata ya nuna mata kulawar sa


Khalisat ganin shiru be biyo ta ba kuma parlon shiru ta biyo shi dakin sa a bakin gadon ta zauna ta fara shafa kansa baby yana ganka cikin wannan hali

Kana dani me zai bata maka rai janyo ta jikin sa yayi kaina ne Ke min ciwo kin san bamu sami isashen bacci ba nan suka fara soyayyar tasu kamar wasu mayu kullum suna tarea makale da juna😏


haka su ummie da binta sukai ta shirin kulla ma suhailat mugunta

Sai da suka tabbatar suhailat lokacin fitowar yayi suka zuba Shampoo akan tayels gashi kuwa yasha mopping kowaccen su ta koma daki ta labe suna jiran tsammani


Suhailat kuwa tana daki yunwa ta ishe ta sai murkususu take abinka da me ciki bata jure yunwa ciki rashi karfin jiki ta daddafo ta fito


Santsin tayel gami da na shampoo suka kwashi suhailat Ayya jikakai tim ta kifa da ciki


Wata azabarbiyar kara ta saki ta da sauri namijin gaske ya tashi jin kara kamar ta suhailat kamr karar nake Ji khalisat ta fada eh nima dai haka


Da sauri ya fito har yana kokarin faduwa khalisat na biye da shi da gudu ya karasa wajen ganin suhailat a kwance jini yana xuba jijjagata ya fara sam ba alamar rai a jikin ta kara ya saki ya rungumota


Sai a lokacin su binta suka fito suna fadin lapiya me yafaru ina suhailat sam bata san inda kanta yake ba

Daukko min keys da gudu khalisat tai dakin sa shi kuwa daukar suhailat yai sai mota ko takan bodyguards nasa bebi ba suka shiga mota shida khalisat


Shewa su ummie suka yi ahayye nanaye yau maga takamar da ake mana da shegen cikin yau sai dai a rariya sukai dariya suka tafa
Farin ciki kamar su xuba ruwa a kasa su sha

A million ya figi motar Allah ne kawai ya kai su lapiya sabida irin gudun da yake shararawa


Suna isa aka karbeta akai A&E (accident and emergency) likitoci suka rufu akan ta

A bakin kofar dakin yai ta safa da marwa sai da suka dibi Kusan 3hours sannan wani likata ya fito yana share gumi da sauri suka isa wajen sa

Ya jikin nata ka biyo ni office ya fada yai gaba su kuma suka dafa masa baya

Ki koma wajenta ko da zasu fito da ita to khalisat ta fada ta koma inda suke ta zauna


Shi kuwa suna shiga doctor ya fara fada kamar be san namijin gaske ba ya zai a bari tai irin wannan fadawa haka gashin nan da kyar muka iya shawo kan lamarin da tuni cikin ya zube


To yanxu me yafaru ya fada hankali tashe ka kwantar da hankalin ka an samu an mata kullin baki mahaifa sai dai a kula amma wanna ba karamin hatsari bane dan ita kanta za'a iya rasa ranta


Aka fito da ita aka kaita dakin Hutu khalisat ce a wajen ta har ya dawo Kije gida ki hado mata kayan bukata ni zan zauna


Tana fita yazauna a gefe gado ya rike hannun gam yana tausaya mata amma wannan yasan makircin bazai wuce nasu binta ba

Shafa cikin ta yai da tuni amsa asarar sa hmmmm shi kadai yasan irin hukuncin da su binta zasu fusakan ta





By marsal💞*👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣1⃣
*by 2besties*

_salma Ali wadah_

_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter

*wannan shafin na sadaukarwa da khadijah kankarofi,ina tayaki adu,a ubangiji Allah yasa ki dace kuma Allah ya cika miki burinki*





→★ adams yashiga zurfin tunani,kawai yaga an banko kofa anshigo khalisace kamar zata haukace tsabar kishi


Adams yace my only meye faru,fadawa tayi jikinsa ta fashe da kuka tace ina bukatarka my only zan iya mutuwa akanka taso muje hotel dan Allah



Adams ji yake kamar ya kwarara ihu khalisat tanaso ta kasheta ita kullum bata gajiya ba damar ya musa mata,ya tashi yana karewa suhailat ido suka fice.
Bude ido suhailat tayi ta fashe da kuka mao tsuma zuciya,tanaaon shan shayi amma ba maitaimaka mata.



Wata nurse ce tashigo tace aunty mekike bukata?


Suhailat tace shayi nake bukata kuma banga an kawo kayan shayiba


Nurse tace karki damu aunty ainan asibitinku,bari inje office din doctor in tambaya


Kafin tarufe bakinta mominta tashigo da kanwarta cikin murna suhailat tace momy dama zan sake ganinki


Kuka momy tasaki tace anya wannan suhailat dinace waya zamarmin dake haka?

Kuka suhailat tasa yayinda momy matakara fashewa da kuka tace suhailat ina shi adam din yake?munje gidan abokan zamqnki sukace kinyi bari kina asibiti inashi adam din ai yakamata ya zauna ko kina bukatar wanu abu



Suhailat tayi murmushin takaici bazata iya boyewa momy ba tace yadauki amaryarsa sun tafi hotel


Momy tace what?bazaiyuba wallahi bazan lamuntaba bari inkira mahaifinsa yazo yajawa dansa kunne yasakarmin diyata donni ba,a rainamin hankali



Ruko hannunta suhailat tayi tace no mom ki barshi kawai


Momy tace rufemin baki sokuwa maiduguri zaki koma,danna waya,ringin biyu dadyn adams ya dauka yace ranki ya dade


Momy tace inafa wani ranki ya dade his excellency kazo asibitin a&e danka yanason kashemin yata wallahi bazata sabuba


Dadyn yace what?ganinan zuwa,ba,afi mintunaba karar injiniya yacika asibitin,dady da momin adams aka bude musu mota suka fito sai kwasar gaisuwa ake

A fusace dady yashigo yana ina adams din


Momin suhy tace kalli yanda yabar yata suka tafi soyewa da amaryarsa,gaskiya nibazan yarda ba don lokacin da aka kawomai yata fresh take abar sha,awa amma kalli yanda tayi baki tarame



Dady ya dafa kan suhailat yace yata kiji tsoran Allah ki gayamin abinda ya wakana tun lokacin aurenku.

Momyn adams tace eh ki gaya mana musan matakin dazamu dauka



Suhailat tace tunda na auri namijin gaske bai taba dukanaba yana bala,in sona ina wulakantasa,basu labari tayi komai amma bata basu labarin abinda binta suke mataba.




Salati dad ya dauka yace zaizo yasameni wallahi saina dau mataki shiwai dan soyayya ko bari ya dawo






By
Marsal[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣2⃣
*by 2besties*
_salma Ali wadah_

_maryam yarmama_

®online hausa writter



¤namijin gaskene ya danno kai harabar asibitin,yasha jinin jikinsa daya hango motocin *his excellency*


Khalisat saikara mannemai take fitowa sukayi daga motar khalisat na rike d take away



Jiki asanyaye yashigo dakin


Momynsa ta kallesa tace to romeo and julliet iyayen soyayya kun dawo,to bata mutuba,ka kyauta son nace ka kyauta wannan ya tabbatarmin dakai lailai namijin gaskene kwarai,kunbar yarinyar mutane to kabani takardarta kokuma ka samesu akotu.



Adams yace mom bafaka bane kafin yakarasa dadynsa ya wankesa da wawan mari har guda biyu yace kai kasan wacece suhailat awuri da wurin mom dinka to inbaka saniba kasani yau suhailat yar kanwar mom dinkace,mahaifinta shi yasha fama har yau na haye matakan danake,tun banida komai yabani kudi najuya nazama hamshakin maikudi kuma da taimakon Allah ta dalilinsa nazama shugaban kasa,kaci amana kaci amana kabani takarsarta kafin in tsinema Albarka kabi duniya



Adams jikinsa yayi sanyi yaje ya durkusa agadon suhailat ya rukko hannun suhailat yace suhailat ki gaya musu kina sona ,karki gujeni suhailat wallahi ina matukar kaunarki suhailat


Momynsa tace munafuki tashi suhailat karki yarda da kallamansa mayaudari tashi kabada takardarta ko nima in tsinema


Kuka adams ya saki,ya ce suhailat zansakekine badan banasonkiba zan sakekine domin bin umarnin iyayenmu suhailat nasakeki saki daya




Adams yafita aguje yakuka maicin rai,shiga motarsa yayi yanata kuka,khalisat ce tashigo tace haba dear,meye abin kuka bayan gani

Adams yace suhaikat bazaki ganeba bazaki ganeba inajin kaunar suhailat ajinin jikina tayaya kike,itace macen dana faroso arayuwata ki tukani bazan iya ttuki ba


Haushi khalisat yabata ta tukasu zuwa gida,dakyar namijin gaske ya fito daga mota,bintane zaune sunyi jigum jigum



Sunaganin khalisat tashigo suka mata inkiya da ido,mayar musu tayi alamun ansamu nassara


Namijin gaske ya wuce dakinsa kota kansu baibiba ya haye saman gado,yakira bodyguard dinsa yace yazo


Ba,afi mintunaba sai gashi yashigo,namijin gaske yabashi miliyoyin kudi yace inason kasiyomin barasa ,amma karku bari kowayagani ta kofar baya zaku shigomin dashi gwanda insha inmanta da suhailat


Abin yabawa bodyguard din mamaki yace yallabai amma kasamn haramun ne kuma akwai illlah acikinsa kuma bantaba gani kashaba.



Dakamai tsawa adams yayi yace nabaka minti biyu kaje kasiyo


Ba,afi minti ukuba saiga bosyguard din yana sshigowa dakaton din giyoyi kala kala yana tausayawa rayuwar adam


Adams yadauki giya daya yabude yq dinga kwankwada,yasha kwalba biyu,surutan banza yafara


Khalisat tana shigowa,taci karo da warin giya cikin mamaki tace adams giya akan wata banza



Adams yaga khalisat tana mai gizon suhailat,dagudu yanufi wajen yana suhailat meyasa kika zabi ki gujeni


Khalisat taga yafasa kwalbar yana. Suhailat taho inji duminki,ina da gudu tafita yana biye da ita khalisat ta taddasu binta azaune afalo cikin nishi tsce wallahi kowa yagudu namijin gaske zaiyi kisa ya haukace


Da gudu binta ta nufi shashinta ta kulle,ummi da khalisat suka fada shashin suhaikat suka kulle




By
Marsal
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣3⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_

_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter








🖤 kixo dan Allah Karki guje ni kice kina sona Karki bari su rabamu haka yai ta buga kofa amma basu bude ba


Ke wai me ya faru ne ummie ta tambayi khalisat nima wllh ban sani ba dg na shiga ya taso yana kiran waccen banzar suhailat din dariya sukai su tafa dan yanxu sun hade kan su da ita wallahi kadan ma suka gani


Haka ya gaji ya koma sama ya kuma kwankwadar giyar sa

Kullum yana daki duk yabi yayi baki ya rame, ita kuwa suhailat tana gidan su ba irin kular da ba'a bata amma tunanin Adams ya hana ta sakewa gashi cikin ta ya tsufa ya shiga watan haihuwa


Tunani Adams yake yanxu da ta haihu tagama iddar ta wata karamar akwati ya daukko ya zuba dollars a ciki sannan ya rubuta wasika yasa a ciki


Wani daga cikin bodyguards din sa ya akai gidan su suhailat dan Aiken ne ya isa gidan su suhailat suna zaune tayi jugum kamar kullum haba daughter kin sa damuwa aranki kuma kinsan bake kadai ce ba hb dan Allah kicere komai dg ranki

Mome Adams fa Ke ki kyale shi kin ji kuka ta saka ana haka dan ake ya shigo hajiya wai gashi inji oga ya mikawa suhailat a sanyaye ta karba ko har ya tafi tana juyawa takasa katabus


Daki ta tashi ta shiga ta bude wani akwati ne me kyau budewa tayi kudi ne 1million dollars ne sai takarda


Budewa Tai ta fara karantawa

_Assalamu alaikum ya kike dafatan kina lapiya Ke da abinda yake cikin ki suhailat na janye sakin da nai miki tun ranar kiyi haquri wallahi ba laifina bane ga wannan kudin ba yawa me kaunar ki har abada Adams namijin gaske_

Wasu hawayen farin ciki ne ya zubo mata ko nauyin cikn jikin ta bata Ji ba ta fito parlo da gudu mome kinga ta nuna mata tsaki tayi Ke ni kyale ni ba inda zaki koma haba mome ni fa...Ke rufe min baki wadda bata san ciwon kanta ba



Sam namijin gaske ya daina walwala ya daina shiga harkar su

Suna parlo suna hira nifa gaskiya nagaji da ganin Adams a haka khalisat ta fada uhmm kyale shi zaiyi zai gama ne ummie ta fada ae wallahi zamu yi maganin su ne gaba daya Bari naja ta dawo daga tafiyar da tayi zamuje wajen boka me kankat aci uban su


Cikin dare ciwo ya turnike suhailat tun tana daurewa har ta fara kuka momee ce ta jiyo kukan ta da sauri ta fito tayi dakin tana isa taga nakuda ce aka dauke ta sai asibiti


Haka sukai ta kai kawo har Allah ya sauke ta lafiya ta haifo santalelen yaron ta me kyau namiji kato mome ce ta fara bugawa tana fadawa yan uwa da abokan arziki ko kan kace me asibiti ya cika damkan da yan uwa ita kuwa tana ta sharar baccin ta hankalin kwance


Momeen Adams ce tazo tun da dauki dan take kallo ikon Allah kamar su daya da Adams haka kowa yai ta daukan dan cike da so

Har aka sallami suhaily namijin gaske be san ta haihu ba momen sa ce ta kira sai da ta kira Sau biyu be dauka ba sai ana uku yana dubawa yaga mome cikin sauri ya dauka

Eh sai yanxu na tabbatar da baka da mutunci ya Kwana uku da haihuwar matar amma.ko waya baka kira kaji lapiyar ta ba mome me ta Haifa namij in ka ga dama kaje ka gani

Tuni wani farin ciki ya lullube shi yafara shirin zuwa ganin dan sa

Haka yasa akai masa.odar kayan jarirai ma masu tsadar gaske

Ya shirya tsaf fuskar sa cike da annuri khalisat ta shigo shirin me kake haka ga wani farin ciki da kake suhailat ce ta haihu namiji kamar saukar aradu taji zance har ya fita bata sani ba


Da gudu ta fito tana kirin su binta ku kuna ina ne ku fito kar bakin ciki ya kashe ni ni kadai me ya faru suhailat ta haihu wani uban ashar ummie ta saki me ta Haifa namiji ta basu amsa.kamar zata kurma ihu......


By marsal💞
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣4⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_

_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter








🔵mene abinyi yanxu ta tambaya dan tun da yaji haihuwar yake wani farin ciki wallahi har na tsani dan da zan ganshi zan iya kashe shi


Shi kuwa yana isa gidan su suhailat yana ta wani washe baki yana yake karbar yaron yayi yana kallon sa cike da so ba kunya ya wani rungume shi yayi yana shafa yaron shi kansa yaga kamar sa suke yi dashi

Duk da tana kewar sa amma ko kallon sa batai ba satar kallon ta ya dinga yi tayi masa kyau sosai sabida kulawar da take samu ko wannan kumburin na jego bata yi ba

Suhailat wai baki ganni ba ne murmushi kawai tayi masa ta tashi ta bar gun duk da bata kula shi ba amma yaji dadin murmushi da tai masa.

Nan yai ma dan sa huduba da sunan mahifin sa mome ga shi nan ya mika mata shi yana fadar sunan da yasa masa

Ko da yaje gidan su fada momeen sa ta dinga yi masa kamar zata dake shi kuma gashi ta haihu ta gama idda mome ae ni na meda ta tun a ranar kuma ko ita ki tambaye ta kiji

Ga kayan baby sai akai mata
Wane kaya kuma Alhaji ma ya sa an hada anjima za'a tafi kaiwa to mome sai a hada da su nan ta gaji da fada ta koma nasiha

Haka akaita shiga da kayan baby dana suhailat kamar ba gobe kaya ne masu kyau da tsada


Ran suna suhailat tayi kyau sosai kamar wata amarya haka akai taro akai lapiya kowa ya koma gida yana san barka da inda suke kiran yaro da sultan


Kullum.sai Adams yaje gidan su yaima Momeen sa magiyar a dawo masa da suhailat da kyar da yarda zata je gidan su koda taje mahaifiyar suhailar fir taki sai da dadyn sa yai magana sannan ta yarda zata koma


Haka akai ta shiri ran da za'a dawo da suhailat ba irin kukan da batai ba duk da yanxu ta tabbatar da irin son da Adams yake mata

Haka aka kawo ta gidan ta ita da sultan ya kuma girma yayi kyau sosai gwanin sha'awa kiri kiri su binta suka nuna bakin cikin su a fili

Wata kulawa admas Ke bawa suhailat da sultan hakan ba karamin ciwo yake ma su khalisat ba

Sam suhailat bata shiga sabgar su tana ta taka tsam tsam da dan data

Naja ce kawar binta taje musu gidan boka me kankat boka ne ya daka mata tsawae kika zo yi afuwan Kasan banda wani wanda yake biyan bukata sai kai nan ta fara yi masa kirari wata dariya ya dinga shekawa

Mene bukatar ki akan maganr wannan kishirya kawata muna so ka yi aikin da zata haukace tsawa yayi mata har sai da bukkar ta girgiza bazai yihuba har yanxu aljani *dakkariyari* be gama jinya ba

To boka ka sa tsana a tsakanin su sannan shima yaron kasa ya tsane shi nan yai wata dariya ajiye masa kudi tai ta fita da rarrafe kamar yarda dokar sa yake


Taje ta labarta masu har wani party suka hada ganin Adams baya nan

Dauki Adams yake ya dawo yaga dan sa jirgi yana sauka driver ya daukko shi inda binta,ummie,khalisat sai kuma suhailat da sultan suna gefe ana jiran dawowar namijn gaske

Motocine suka fara shigowa kansa ne yai wata irin sarawa jariri na dibarsa dade kansa yai ya zauna har sai da ya lafa sannan ya fito

Da gudu khalisat taje ta rungume shi haka su binta akaje ana kwarkwasa ita kuwa suhailat ganin ko kallon ta be ba yasa jikin ga yai sanyi sai da yazo daf da ita tsinkar muryar ta yai tana masa sannu da zuwa wata irin tsanar ta yaji a ransa kallon banza ya watsa mata sannan ya shige


Juyawa suke gaba dayan su suna mata gwalo

To wannan me yake nufi Kila ko gajiya ce ta shige daki sai da yai wanka sanan suka hallara a dinning ita ma fitowa tai ta zauna wata tsawa ya daka mata Ke tashi ko bani waje kallon sa yai shike da mamaki bazaki tashi ba. Ko sai nayi ball dake da gudu ta shi tai dakin ta dan Ji yai gaba daya baya son ganin ta da ita da sultan




By marsal💞
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣5⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_

_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter










⬛wata irin shakara da yanga kwarkwasa suka fara yi masa shi kuwa yana wangale musu baki yana farin ciki ganin sun hade kan su


Murna kuwa sunyi ta kamar wanda akai musu albishir an basu jirgin sama ✈

Haka rayuwa ta cude ma suhailat ko fitowa tai sun dunga hantarar ta kyara da zagi ba irin wanda Basa yi mata

Suhailat ce tazo gifatawa khalisat tai magana

Darling wai mene amfanin wannan a gidan nan ne ta nuna ta hmmm ni dan kar momee tai min fada wallahi da tuni na korata gidan su

To ba sai ta dinga ayukan gidan nan ba a sallami en aiki binta ta fada gaskiya ne tunda baza a dinga ciyar da ita a banza ba ummie ta fada batare da yayi dogon tunani ba yace a kirata

Jikin ummie har rawa yake ta tafi kiran ta da sauri tazo karta kuma wani laifi tana goye da sultan ta durgusa kanta akasa gani Ke ko bude kunnen ki kiji daga yau Ke zaki dinga aikin gidan gaba dayan su tundaga wanke wanke goge goge har girki kuma in kika yi ba dai dai ba ranki sai ya baci tashi Kije

Ah Ke zo nan binta ta fada to ae baka ce ta dinga bawa flowers ruwa ba sabida gaba daya za'a sallami en aiki to kinji abinda tace ko

Kuma aikin ki daga yau zai fara

Maza tashi ban son ganin ki tana kuka ta tafi cike da bakin ciki wannan wace irin rayuwa ce Allah ka kawo min sauki

Tundaga wannan lokaci rayuwa tai mata zafi aiki safe da rana tarame tayi baki tana kitchen tana girki ta kwantar da sultan a parlo yana bacci

Ummie ce ta fito wane shegen ne ya ajiye wannan a nan sa hannu tai ta tunkudo shi daga kan kujerar tai saurin komawa daki

Tana kitchen ta jiyo kukan sa da gudu ta fito da gudu ya fadi kasa bakin sa ya fashe sabida azabar kukan da yake har shidewa yai ya kasa kuka

Ita ma kukan tasa ta dauke shi tai daki dashi ta gama jijjagi yana bacci ta ma manta da girkin da take

Binta ce a parlo tana kwala mata kira da sauri ta fito Ke wacce irin jaka ce sabida baki san darajar abu ba kin bar abu ya kone

Kiyi haquri sultan ne ya fadi shine nake rarrashin sa mari ta kwada mata to daga yau kika kuma wllh sai kin gane kuren ki banza

Wallahi da hauka kika dace kuma ki maza ki gama mijin mu ya kusa dawowa

Tana goye da sultan dan yanxu bata bari suyi nisa sabida azabar da su binta Ke masa a farfajiyar gidan tana bawa flowers ruwa


Hajiya hussaina ta shigo sam bata gane ta ba sai da tai gaba juyowar da zatayi wazan ganewa idanuna suhailat ce ko me kama da ita nice Hajiya mamaki ya hana ta magana matsowa tai kusa da ita tana kallon ta kuka ta saki suhailat haka sukai mai dake

Yi shiru hajiya kar su Ji kamo ta gaban ta yana dukan tara tara haka tai palon tai sa'a bakowa a parlon suka shige daki tana kuka tana fada mata

Kiyi haquri in Allah ya yarda zan taimaka miki in na koma zan turo miki addu'o'in da zaki dinga yi bari na tafi kar naja miki wani laifin

Suna fitowa sukai karo da khalisat wai mugun kallo ta watsa mata lallai kan mage ya waye Hajiya hussaina na ma kallon banza tai ma da sannu Allah zai kawo karshen ku

Ta fita ta bar ta su binta ummie ku fito kuga ikon Allah da sauri suka karaso

Dai dai da zuwan namijn gaske lapiya wata kawar ta me zugata ce tazo nan ta shirya mata karya nan take ya hau ya zauna

Kan Kace me ya fara dukan ta ta ko ina tun tana.kuka har ta daina sai da suka ga ta galabaita sannan suka ja shi dakin sa aka barta a kwance

Bayan 30munites binta ta fito a kwance ta ganta freg ta bude ta daukko ruwa me shegen sanyi ta kwara mata a zabure ta tashi da halla tashi ki bawa mutane waje kan ma kara miki wani baza ta iya tashi ba haka.ta rarrafa tana shiga ta tarar fuskar sultan duk busashen hawaye yayi kuka har ya gaji





By marsal💞
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣6⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_

_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter







♥rungume sultan tai ciki da tausayin sa wannan wace irin rayuwa ce kuka ne ya kubce mata tayi me Isar ta idon ta ya kumbura sosai muryar ta kuwa ko fitowa bata yi


Kira taji ana kwala mata da gudu ta fito dan ta san kiran wadan nan ba alkhaeri bane gani Ke a gidan ubanki haka kika gani in an kira ya tsaya a tsaye


Tan kokarin durkusawa taji an warto kafarta take ta zube bakin ta ya bugu da tayels nan take ya fashe


Daga yau sai yau duk lokacin da daya daga cikin mu ya kuma kiran ki kika tsaya a tsaye wallahi sai mun miki wanda ya fi wannan khalisat ta fada


Maza jeki kitchen ki hado min water melon shake da chefs kuma sauran ki kawo beyi sanyi ba


Ta tashi zata tafi khalisat tace wai saurin me kike ne eheee dawowa tai ta durkusawa indomae zaki dafan da scrambling egg Saura kiyi min shirme ki raina wayon ki

Ke ta dago kai ummie ce ta yi mata wani mugun kallo sannan tace ki dafo min checking peper Saura ki kiyi da sauri ki tsaya wannan shashancin naki ko kuma ki zabgan yaji


Kitchen ta nufa

Please Login or Register in order to submit comment