Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

💠💠💠💠💠
*©®2020.*


*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥



Bʏ.
*HAWWA MUH'D USMAN.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*Wattpad link*: https://my.w.tt/29u2S26SG2
^^^^^^^^^^^
*#Iᴛꜱ ᴀʟʟ ᴀʙᴏᴜᴛ:#ʙʟᴀᴍᴇ,#ʜᴇᴀʀᴛʙʀᴏᴋᴇɴ,#ʜᴀᴛᴇᴅ,#ᴍᴀᴅɴᴇꜱꜱ,#ʟᴏɴᴇʟɪɴᴇꜱꜱ,#sᴏʀʀᴏᴡ,#ʀᴜᴛʜ,#ʀᴇɢʀᴇᴛ,#ʜᴇʟᴘᴇᴅ#ʀᴏᴍᴀɴᴄᴇ ᴀɴᴅ #ғᴏʀɢɪᴠᴇɴᴇꜱꜱ.*

*D丨丂匚ㄥ卂丨爪乇尺:* ᴛʜɪs ɴᴏᴠᴇʟ ɪs ᴀ ᴡᴏʀᴋ ᴏғ ғɪᴄᴛɪᴏɴ..ᴀʟʟ ᴄʜᴀʀᴀᴄᴛᴇʀs,ɪɴᴄɪᴅᴇɴᴛs ᴘᴏʀᴛʀᴀʏᴇᴅ ᴀɴᴅ ᴛʜᴇ ɴᴀᴍᴇs ᴜsᴇ ɪɴ ᴛʜɪs ɴᴏᴠᴇʟ ᴀʀᴇ ғɪᴄᴛɪᴛɪᴏᴜs... ᴀɴʏ ʀᴇsᴇᴍʙʟᴀɴᴄᴇ ᴛᴏ ᴀᴄᴛᴜᴀʟ ᴘᴇʀsᴏɴ ʟɪᴠɪɴɢ/ᴅᴇᴀᴅ,ᴏʀ ᴇᴠᴇɴ ʀᴇᴀʟɪᴛʏ ɪs ᴘᴜʀᴇʟʏ ᴄᴏɪɴᴄɪᴅᴇɴᴛᴀʟ.

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

Alhamdulillah.! Am back again my pepz...🙋

Pᴀɢᴇ 1.
#Dʀᴇᴀᴍʟᴀɴᴅ

Tunda ta zauna a gurin ta yi wani irin shiru mai shiga zuciya,bata sake k'ok'arin motsawa ba bare ayi tunanin tana raye.? Ta suma.? Ko kuwa mutuwa tayi.? Duka dai ga tanan ne sunkuye da kanta dake kife a tsakanin cinyoyinta,,yanayin yadda tayi she looks so restless and disturbed,wanda da kyakykyawan kallon tsanaki guda zai yi saurin sawa mutum ya fahimci yanayinta yafi kama da na mutumin dake cikin tsanani,kamar yadda both hannaye da k'afafunta dake d'aure cikin sasarin k'arfen suka yi indication,,and kuma yanayi da tsarin gurin da take ko kad'an bai yi kama da torture room ba,bare a kira shi da prison ko guardrooms.
Tsarin gurin ya kasance babu wani hayaniya,d'aki ne guda yalwatacce da bai had'a ko wane irin tarkace ba,,ita kad'ai ce zaune cikin d'akin da girmansa ak'alla zai tasamma kaiwa 30 square meters,daya kasance yana d'auke da wani irin tsohon traditional iron bed wanda hausawa kewa lak'abi da mahadi ka ture (wato dai irin hausar nan da ake nufin kafin aga bayan abu za'a d'auki tsayin zamani),then midi wooden table da kujera da suke gefe and long cutains masu sauk'in haske da suka zagaye duka windows da entrance na d'akin,,,ta d'auki tsayin lokaci a sunkuyen ba tare data d'ago ba,sannan kuma bata koma ta kwanta ba,gashin kanta daya baje ya sauka jikinta ya sake taimakawa wajen rufe ilahirin halittar fuskarta,da duk iya nacin mai naci da son bin kwakwaf akanta,zai yi wahala ya iya gano wace irin halitta ce farat d'aya,yarinya.?,Budurwa.?,Tsohuwa.?,Matar aure.? Ko kuma bazawara..?

***
Tafe yake cikin wani irin taku mai tattare da nutsuwa,tun da ya shigo cikin gidan fuskarsa ke sunkuye tana kallon k'asa,,sai dai a yanayin tsarin yadda yake tafiyar zai yi saurin sawa a kirashi da kamilalle,bcos yadda yake yi d'in tuni ya fallasa asalin nutsuwarsa da zata sa ayi saurin kiransa nutsatstse da yake bin komai na rayuwarsa a sannu,,a zahiri shekarunsa duka baza su haura 24 ba,sai dai da yake ya kasance ma'abocin ginannen jiki da duk wani siffar k'arfi na kasantuwarsa d'a namiji mai ji da shekarun yarintarsa suka bayyana kansu ta cikin fasion summer with hooded sleeveless d'in da yake sanye da ita,ta sake fallasa asirin girman jikin nasa da ka iya sawa a kirashi da mutumin da ya tasamma shekaru talatin a duniya,,tun daya shigo bai yi k'ok'arin d'agowa ba,hasalima sai sake janyo hooded d'in dake rufe da sumar kansa yake,wisely and time2time sai ya d'an lek'o ta side yana sake monitoring hanyarsa,sannu a hankali har ya wuce harabar gidan ya iso cikin d'akin da take,,y'an kalle² yayi lokacin da ya shigo,ko da ya tabbatar babu kowa direct ya nufi inda matar take zaune ya k'araso kusa da ita,slowly ya d'ora hannunsa a saman shoulder d'inta,muryarsa na wani irin trembling bayan ya janye hood d'in yana kallonta da fuskar damuwa yace
*"LOLLY..!* Kiyi hak'uri ki fad'a min yanzun.. Please..!?"
Shiru tayi bata d'ago ba har sannan,da wani irin muryar tausayi ya sake dafata yace
"Please lolly..! U have to take a look at me,always fa am growing older,why ne ba zaki sanar da ni ba..?? Why.?"
Shiru ta sake yi bata d'ago ba still kuma bata amsa tambayar da yake mata ba,shima d'in still ya sake yi mata duk muryarsa ya koma kamar zai yi kuka saboda k'in kulawa da maganarsa da tayi,a hankali ya janye hannunsa a jikinta ya juya mata baya,yana kallon wani side d'in yace
"Lolly..! U know ko wane lokaci saina tambayeki inda Daddy na yake,waye shi? Ina zan ganshi.? But always sai dai kiyi min shiru al'halin nasan kina jina,i know kin san abunda nake nufi,kuma kin san abunda nake buk'atar ji kenan daga gare ki,why don't u informed..!? Kin fi so ko wane lokaci naci gaba da rayuwa da bak'in cikin kira na *MARA ASALI..??* Ina son sanin inda mahaifina yake,na nemo shi,na rungume shi,a karon farko,a lokaci guda naji nima na zama d'aya daga cikin y'ay'a masu asali da gata,,tabbas zanyi alfahari da hakan,a duk ranar da nasan wane ne mahaifina zan kasance mai farin ciki..!"
Dakatawa yayi kad'an yana jan numfashi,idanunsa a d'an kulle amma tsananin damuwa ke sake appearing masa a saman kyakykyawar fuskarsa mai d'auke da matsaikacin haske,madaidaitan idanu,pointed noise,dim beard nd small rounded mouth mai d'auke da wasu irin soft lips masu jan hankali,,still matar tana a yadda take ba tare da tayi ko gezau ba bare yasa ran zata amsa shi,da yaga bazata kula ba cikin fushi² da a ko wane lokaci ya tambayeta tak'i amsa masa suke k'arewa babu dad'i ya juyo yana kallonta idanunsa d'auke da wasu irin hawayen takaici yace
"It's ok Lolly! Its ok.!! Tunda har bakya so na sani,,,i promised to my self nd u too,as from today till my last breathe i won't ask u,,ever..!"
A fusace ya juya zai fita a d'akin zuciyarsa da ransa duk a mugun b'ace ya ganta tsaye tana kallonsu ta hard'e hannaye a k'irji fuskarta d'auke da damuwa,haka idanunta banda tsantsar tausayawa mai girma babu abunda suke bayyanarwa,jikinsa yayi mugun sanyi bcos yasan ta hana shi zuwa gurinta shi kad'ai da irin wad'annan tambayoyin,duk da yaji fad'uwar gaba lokacin da ya ganta tsayen,but hakan bai hana shi sunkuyar da kansa k'asa ba,slowly kamar wanda tafiya kewa wahala yaci gaba da takawa har ya k'araso gefenta yana niyyar rab'awa ya fice,,ita kanta ko da take tsayen tana kallonsu tun bayan da taga shigowarsa gidan bata iya ce da shi komai ba still tana kallonsa yana tafe yana matse idanunsa,har lokacin da yayi shirin fita ya bar musu d'akin,sannan tayi k'arfin halin rik'o hannunsa,waiwayowa yayi saurin yi yana kallonta a lokaci guda hawayensa suka samu damar fara sauka saman kyakykyawar fuskarsa,yadda yake jin zuciyarsa damuwar da yake ciki a yanzun na rashin hope ya wuce yace zai iya had'iyeta a cikinsa,dole ya bawa hawayensa damar sauka ko zai samu sassauci
*"NURAZ..!* Habibiiy.! Kada kayi kuka,kada kayi Yarona..! Idan ina ganin hawayenka suna k'ona ni,,bana iya jurewa ganinka ko wane lokaci kana kuka,,shin har tsayin wane zamani zanyi ta ganinka a haka..? Bazan iya jura ba,,ka kwantar da hankalinka yarona,in sha Allah ni kuma a yau nayi *ALK'AWARI* zan sanar da kai *ASALIN KA!* Labarin ka da mahaifiyarka tare da duk k'alubalen da muka fuskanta,na amince yau zan fad'a maka..!"
Tun kafin yayi magana suka ji ta fasa wani irin razanannen ihu da dole yasa su duka biyun juyawa suka kalleta fuskokinsu bayyane da damuwa,,Nuraz da jin ihunta da yanayinta daya sauya lokaci guda babu shiri yayi saurin matsawa bayan d'aya matar yana fad'in
"Annie..! Ki ce ta bari bana so.. Pleasee.. Am scared,,tana min irin kallon nan zan dunga jin tsoro,kuma zan daina zuwa gurinta..!"
Rik'o shi Annie tayi saurin yi zuwa jikinta,a hankali ta mayar da kanta gefen da take zaune tana kallonta rai a b'ace
"Haba *HAUWA.!* ke kuwa me yasa zaki dunga tsoratar da da shi..?? Kina son rayuwarsa ta sake shiga garari ne,bayan tarin matsalolin da yake kan fuskanta na rashin sanin goben sa..??"
A hankali hawaye suka fara gangaro mata,kafin tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa tana girgizawa ba tare da tayi magana ba
"Mene matsalar ki kike kuka.?" Annie ta tambaya tana sake kallonta,ci gaba tayi da girgiza mata kai kamar wacce dama can abunda tafi iyawa kenan still bata ce komai ba,Annie da take tsaye fuskarta da damuwa tace
"Ba kya so yasan asalinsa ko..? Kinfi so mu bar rayuwarsa a haka cikin wahala da duhu..?? Mene ne amfanin boy'ewar..? Kina tunanin hakan zaisa jama'ar dake masa gorin rashin mahaifi su daina.? Mene ne laifinsa dan ya kasance a haka..!? shi kenan dan yana amfani da sunan mahaifiya sai a tsangwami rayuwarsa..Haka kike so duniya taci gaba da kiransa *MARA ASALI,,,MARA TUSHE..?* yaci gaba da rayuwa cikin damuwa da bakin ciki all the time aka kira shi *MARA ASALI.. D'AN MACE.?"*
Shiru d'akin ya d'auka na wani lokaci,a hankali Annie ta waiwaya ta kalleshi sannan ta kuma kallonta tace
"Kamar yadda muke rayuwa tun bayan haihuwarsa a cikin k'unci da bak'in cikin wannan al'amarin,,fatana har kullum shi ne daga wannan ranar komai ya zama tarihi,,na gaji da ganin rayuwarmu cikin damuwa,ke cikin wahala mu a cikin garari,,har tsayin wane lokaci zamu d'auka a hakan..? Shi kenan!³ Idan wancan lokacin kin hana na sanar da shi,wannan kam baki isaba.! Har ga Allah na gaji,,dan haka a yau zanyi k'ok'arin fitar da zuciyoyinmu daga k'angi,,zan fad'awa *NURAZ* asalinsa,ba don komai ba sai don ya zama dole yasan wane ne mahaifinsa... Ko kina so,ko bakya so,kin amince,ko baki amince ba,ni nan zan shaida masa komai bisa ga umarnin zuciyata,na amince zan fad'a masa..!"
K'ara ta sake saki mai tsananin firgitarwa har fiye da ta farko tana wata irin girgiza da fizga kamar zata tashi,Nuraz dake gefen Annie cikin damuwa yayi saurin juyawa zai fita daga d'akin dan a yadda yaga al'amarin ya san babba ne,sai dai tun kafin ya kai kofa Annie tayi maza ta kamo shi,k'ank'ame hannun Annien yayi cikin tsoro² ya juyo yana kallonta da marairaicewa yace
"Annie.! Ki ce mata to ta bari,kin san bana son ihu.! Yana sa ni shiga damuwa.! Yana tada min hankali.."
Saurin rungume shi tayi saboda ganin yana neman d'imaucewa tace "Am so sorry Yarona.. Babu abunda zai faru in sha Allah,,kayi shiru haka nan,zanyi mata magana,za ta bari ka ji,kada ka damu..!"
Yana daga jikin Annie yake sakin ajiyar zuciya da lumshe idanu,jin shiru bayan wani lokaci ya d'ago ya lek'o ta,yana kallon fuskarta ya sake saurin ja baya dan yadda fuskar gaba d'aya ta rine da wani irin firgitaccen b'acin rai,idanunta sun soye sunyi jajir tamkar garwashin wuta,tsananta rik'on da ya yiwa Annie yayi cikin tsananin damuwa yake kiran ta
"Annie.. Kin ganta ko.. Kice mata ta bari,,bana so..!"
Itama wani irin razanannen kallo take jifansa da shi mai cike da tsantsar tsoratarwa,a karon farko tunda suke magana bata tanka ba ta fara magana da wani irin murya da yake amo
"Ka fita daga nan..! Bana son ganinka.. Kada ka sake dawowa inda nake,,ku fita bana son ku zo inda nake.. Bana son ji,,na tsaneshi,bazan tab'a yafe masa ba.. Na tsane shi.!³"
Yanayin yadda take magana da ihu har tana datse harshenta tana taunawa yasa nan da nan jini ya fara fita daga bakin kamar wanda aka sa sabuwar razor aka tsarga,tsananin zafin azaba ya ratsa kwakwalwarta ta sake kurma gigitaccen k'ara had'e da tattara k'arfinta guri guda,wani irin tak'ark'arewa take tamkar k'aton gardi maji k'arfi cikin mummunan ihunta ta shiga fincike duka hannayenta,sasarin dake mak'ale jikin hannunta yayi tsalle gefe,kafin k'iftawar ido har ta kama na k'afar ta fizge,Annie dake ta tsaye suna kallonta ganin abunda yake faruwa kafin tayi yunk'urin yin wani tunani taga har ta b'alle shi ta k'arfin tsiya,a zabure kuma ta diro daga saman gadon tana kurma ihu tana girgiza,hankalin Annie a tashe ta fara nemar masa hanyar barin d'akin dan a yadda taga lamarin yazo controlling d'inta ita kad'ai ko su biyu ba zai musu wahala,,kamar wad'anda aka dannawa pause suka k'ame guri guda a lokacin guda suna binta da kallo,yayin da ita ma take ci gaba da nufo su kamar guguwar dake shirin yin b'arna,karantar nufinta da yadda take kallonsu yasa daga Annie har shi Nuraz d'in suka fara yin baya² da inda suke tsaye,lokaci guda ta tsaya tana sake kallonsu,ganin tafi maida hankalinta akan Nuraz yasa Annie dake cikin tashin hankali da kyar ta tattara kalmomin bakinta cikin k'arfin hali tace
"Habibiiy..! Yi maza ka fita daga nan,ina nan zuwa yanzun zanyi following d'inka,,sauri ka fita ka ji.." Cike da k'arfin zuciya take maganar tana yi tana tura shi bayanta

"Annie..! Am scared..!"

Tsawa tayi masa tace "Fita nace.. Kada ka damu maza ka wuce,ni nace ai zan zo yanzun na same ka.."
Kansa dake a k'asa ya kasa kallonta tun d'azun ya d'ago ya saci kallon fuskarta,,suna yin ido hud'u ta sake karkace hanya ta nufo shi gaba d'ayan ta,kamar yadda ta nufo shi haka ya juya ya kama hanyar ficewa,sai dai ko k'ofa bai kai ga isa ba,irin mugun tsalle data doko ya ganta tsaye a gabansa,yadda tayi acting kamar a movie sai yasa shi yin still yana ta kallonta tsoro k'arara a fuskarsa,,still cike da k'arfin hali Annie tayi saurin rik'e ta tana janta baya da nufin ta mayar kan gadon,a fusace ta d'ago tana fizgewa jin an rik'eta an hanata sakat,bisa tsautsayi ko data waiwayo tana fizge jikinta ganin Annie rik'e da ita ta kasa kwacewa yasa ta hankad'ata da dukkan k'arfinta,da jikin gini ta fara buguwa kafin ta silale tayi k'asa,sautin buguwarta da k'arar da tayi a lokaci guda na azaba suka sa Nuraz da har ya fita a d'akin babu shiri ya sake dawowa a d'imauce yana kiran Annie,k'ara ya fasa lokacin daya hangota kwance cikin jini,cikin tsananin tashin hankalin da bai tab'a tsintar kansa a ciki ba ya nufi inda take yashe ya d'ago kanta ya rungume,jin bata motsi a hargitsen ya fara jijjigata yana kiranta hankalisa a mugun tashe yake fad'in
"Annie..! Ki rufamin asiri ki tashi,,dan Allah kada kiyi min haka..! Idan kika tafi kika barni yaya kike so nayi..?? Ki tashi Annie kada ki tafi..!"
A wannan lokaci ko da nuraz yake kan sambatun kiranta,Annie kam bata san yana yi ba,bcos tuni tayi nisan kiwo,,juyawa ya shiga yi da tashin hankali yana dube²,haka nan duk sai yaji ya rasa mene ne yake nema,kuma ya rasa abunda ya kamata ya fara yi wanda zai dawo masa da Anniensa cikin lafiyarta,gashi shi kad'ai ne a gurin ya san da wahala ya iya d'aukarta,saboda yadda take rusheshiya tafi k'arfin ya d'auke ta shi kad'ai,,yana zaune rungume da kanta da jini yake ci gaba da zuba yana jijjigata yana kuka,ta zagayo ta bayansa without ya sani,ji yayi kawai an shak'e shi ta baya,da hannayenta biyu ta shiga hajijiya da shi cikin k'arajin maganarta da ba komai ake ganewa ba take maimaita fad'in
"I told u bana so,,bana so².. Me yasa..?? Sai nayi ajalinku.. Ni ce ajalin ku.. Kuma nima sai nayi nawa ajalin.. Sai na kashe ku,na kashe kaina,,dukanmu baza mu rayu ba.. Sai mun mutu dukan mu.. Sai mun mutu,,mutuwa za muyi.!!"

***
A matuk'ar firgice ya bud'e idanunsa dake rufe sakamakon mummunan mafarkin da yayi,cikin abunda bai wuce mintuna goma da komawarsa bacci ba,gumi duk ya wanke shi daga shi har white sleeveless singlet dake jikinsa,water bottle dake saman couch ya fara bud'ewa ya tsiyayawa a cup dake gefen bed d'in kad'an ya sha,a hankali ya shiga sauke ajiyar zuciya tamkar wanda ya sha tsere yana sake jan wahalallen numfashi da ajiyewa kafin ya fara motsa bakinsa slowly
"A'uzhubikalimatillahit'tamaat min sharri maa khalak'.. Laa ilaha illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz'zalumiiyn.. Laa ilaaha illallaahul'azheemul'haleem,laa ilaaha illallaahu rabbul'arshil-azheem,laa ilaaha illallaahu rabbus-samaawaati,wa-rabbul-ardhi,wa-rabbul-arshil-kareem kareem."
Ya d'auki tsayin lokaci yana maimaitawa kafin a hankali ya lumshe idanunsa ya bud'e yana juya su,bayan d'an lokaci ya rik'e gefen lip d'insa da hak'oransa cikin salon zurfafa tunani akan abubuwan da suke faruwa da shi a cikin bacci,,kimanin lokaci mai tsayi ya d'auka cikin halin jimami then kamar wanda aka tursasa yayi k'ok'arin janye bedspread da k'afafunsa ke ciki ya ajiye su cikin adjustable velcro slides slippers mai d'auke da tambarin Puma kalar fari,,yadda jikinsa yayi sanyi da abunda ya gani yana tashi tsaye yaji kamar ya rasa komai,hatta da kuzarin jikinsa duk sai ji yake yana kokarin gazawa,gefen bed d'in ya dafa da duka hannayensa slowly ya koma ya sake zama yana lumshe kyawawan idanunsa na tsayin lokaci,,muryar Annie ya jiyo dake ta tsaye tun d'azun akansa da sauri ya bud'e idanunsa
"NURAZ..! Habibiiy.!! Har yanzun baka tashi ba ne.!?"
Ta tambaya lokacin da take sake matsowa inda yake,a hankali ya d'ago yana kallon fuskar Anniensa da babu jimawa cikin mafarkinsa ya ganta cikin mugun yanayi,haka nan ya k'ura mata idanu,har ta k'araso bai sani ba sai data tab'a shi
"HABIBIIY..! Me ya same ka haka jikinka a jik'e.? Wasan ruwa kayi ne ko me..??"
Tana tambaya tana tattab'a jikinsa,shiru yayi baiyi magana ba,a hankali Annie ta rik'o shi tana kallonsa,tana shirin sake yin magana taji temperature d'in jikinsa ya sauya zuwa fitar da hucin zafi,da sauri ta sauke idanunta tana watsa masa kallon tuhuma
"Mene ne ya faru habibiiy.?? Wani guri na maka ciwo ne.? Ka sanar dani abunda yake faruwa.!"
Still yayi yana kallon ta ba tare da yayi magana ba,kome ya tuna da sauri ya mik'e ya kama hanyar barin gurin a niyyarsa ya shige bathroom,but sai Annie tayi saurin rik'o hannunsa
"Zo Habibiiy ka sanar min damuwarka.. Me ya same ka jikinka yayi zafi haka..!?"
Girgiza mata kai kawai yayi,a hankali ya zame hannunsa ya shige bathroom without yace da ita wani abu game da tambayar da tayi masa.....


*#HAPPY NEW YEAR.*🎉


#Comment first
#Vote &
#Share pls.
#Real Smasher.
#Jan/1st.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*      

                  *'DAN MACE..*
             (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

  
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*    
https://my.w.tt/29u2S26SG2

*YABON GWANI...*

Hassan Atk
Hussain Atk
Itz B.Y Ebraheem
Hayat Baba Zubair
Ku d'in ku ne gwanaye na,kuma abun alfahari na,idan har ina da mutanen daya kamata ace na ambata,a wannan dan tak'aitaccen rubutun nawa,tabbas ku ne farko,,bisa d'awainiya da kuke da litattafaina a social media,bani da bakin da zanyi muku godiya,sai dai har kullum ina yi muku fatan rabb ya saka muku da mafificin alkhairinsa ameen.

Pᴀɢᴇ 2.
#Eɴᴛʀᴇᴀᴛʏ

      Tun daya shige bathroom d'in yake tsaye k'ark'ashin shower,hannayensa dafe a jikin wall guda na katafaren toilet d'in da yaji kayan more rayuwa ya sake zurfafa tunani akan abunda mafarkin nasa yake nufi,a iya shekarunsa tabbas yasan bai kai matakin da za'a ce ya iya d'aukar irin wad'annan damuwar bane,to amma yaya ne zaiyi tunda k'addararsa tun farko a haka tazo.? Shi dai ya sani kuma har zuciyarsa ya tabbatar bawai yana damuwa da halin da yake ciki bane,abunda kawai yake damunsa a yanzun shi ne yana tsananin buk'atar son ya gane ma'anar yawan mugayen mafarkan da yake,,bakinsa ya bud'e kad'an yaja numfashi ya fesar,a fili ya tambayi kansa
    "Shin mene ne hakan yake nufi..??"
   Ya sake sunkuyar da kansa k'asa deeply thinking about his dreamt,ya b'ata lokacin da bai san adadi ba a k'asan shower ruwa yana ci gaba da sauka a saman kyakykyawan sumar kansa daya sha wani masifaffen undercut with long side swept,duk da yake yanzun ne yake kan tasowa amma sosai gyaran kan yayi masa kyau,but zuciyarsa tana cikin zullumi da damuwa wannan dalilin ya sake taimakawa wajen boy'ewar sirrintaccen kyaun da Allah yayi masa.
   "Tsayin wane lokaci zaka d'auka kana irin wannan mafarkan..?? Ya kamata ka bibiyi asalinkan idan har hakan zaisa ka samu nutsuwa,,lokaci yayi daya kamata ace ka gogewa mutane shakkunsu akan kasancewarka *MARA ASALI..!"*
    Zuciyarsa ke yi masa khud'ba da bashi shawara,a hankali ya d'an dakata da tunani,can daga wani gefen na zuciyarsa yake jin tana sake sanar masa
    "Ya kamata kayi wani abu wajen gano asalinka,idan ba haka ba..!"
    Sai yaji shiru kamar d'aukewar ruwan sama,,tambayar kansa yayi yace "If not.. What..!?"
     Kamar mai jira yayi tambayar zuciyarsa ta bashi amsa da "Har duniya ta tashi zaka tabbata ne a matsayin *MARA ASALI.!* Tare da ci gaba da amsa sunan *'DAN MACE..!"*
   Saitin zuciyarsa yayi saurin dannewa da hannunsa d'aya yana girgiza kai cikin wani matsanancin tashin hankali daya tsinci kansa sakamakon tunane² da yake fama da su ya furta
   "No..!! Bazai tab'a yiwuwa ba..! Sai na tambaye ki,,kuma bazan fasa tambaya ba,duk tsayin *ZAMANI* zan jira na sani,,sai na sani..! Wollahi sai na bibiyi asalina,sai na san *WANE NE ASALIN MAHAIFI NA.!"*
    Ya k'arashe
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment