Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

batare da ya yi musu magana ba,bin bayanshi major Marry ta yi, dukkansu biyu daga ita har shi LGT.Taj suna cikin shiga na farin kaya babu wanda ze gansu ya yi tunanin sojoji ne.


Haka suka kwana basu saka komai a cikinsu ba,Anty Teema ta musu tambaya har ta gaji amma sunki faɗa mata abinda ke faruwa.

Tana toilet tana wanka soso ya rike abin hannunta, ta yi iya yinta amma ya ki fita ajikin soson hakan yasa ta cire shi a hannunta.se sannan ne ta samu ya fita ajikin soson ajiyeshi ta yi a gefe ta gama wankan ta,bayan ta kammala ta daukeshi ta fito miƙawa Asmita ta yi ta ce "rike mini bari in sa kaya" karba Asmita ta yi tasa shi a hannunta.

Bayan ta gama sa kayan kuma ta manta bata karba ba.

Gari na wayewa suka farka duk da hakan ba ɗabi'ar su ɓace, amma yau haka kawai suka tashi da wuri,baranda suka fito suka zauna suna kallon masu wucewa suna hira sama_sama har Anty Teema ta fito ta samesu a wajan,komawa cikin dakinta ta yi ta dauko musu kankana ta basu karba sukayi suna gaisheta.

Hira sukayi sosai duk da firgicin abinda ya faru jiya be fita a ransu ba har yanzu suna kallon yanda wa'yannan azzaluman suka kashe Barrister Lameer yanda suka jefashi kan titi mota ya takeshi.
Har kusan karfe sha ɗaya duk suna zaune awajen anan sukayi karin safiyar su. Taheer ne ya kira Asmita a waya,ya faɗa mata yana baƙin gate din gidan,kallon Sabriyah ta yi ta ce "my Jerry muji waje Taheer yazo."
Barin Anty Teema sukayi a wajan suka ce mata bari su je wajen Taheer.

Fitowa sukayi suka sameshi a bakin gate a cikin motar shi tun kafin su iso ya keyi wa Asmita murmushi shiga cikin motar su kayi suna hira se jan su da zolaya yakeyi,be fi minti talatin ba ya ce musu ze tafi Saboda yanxu haka ma airport zeje Ya ce bari yazo ya ga Asmita.

bankwana sukayi dashi yaja motar ya tafi tsayawa sukayi suna bin bayan motarsa da kallo. wata ƙatuwar bak'ar jeep ya tsaya agabansu,kafin suyi wata_wata wani namiji ya fito ya sa hannu ya janyo hannun Asmita dake riƙe dana Sabriyah cikin motar,raba hannun nasu ya yi ya rufe kofar motar ya ja suka tafi. Sabriyah dake tsaye a wajan kamar gunki,daura hannu akai ta yi tasa ihu me matuƙar ƙaran gaske Wanda yayi sanadiyar jawo hankalin al'umman Wajan kanta da gudu tabi bayan motar amma ina sunyi mata nisan gaske zubewa ta yi akasa lokacin da ta dena hango su tasa Marayan kuka kamar ranta ze fita,ji ta yi ansa hannu an ɗago ta sama kallon wanda ya ɗagonta ta yi taga mutumin jiya da suka haɗu a kasuwane har ya wurgata kasa ne.bude baki ta yi zata yi magana yasa hannu a aljihun jacket din shi ya fito da hanky ya shaƙa mata a hanci nan take ta sume ta faɗo jikinshi.
Hannu ɗaya LTG.Taj ya saka ya dauketa kamar yar tsana ya nufi mota da ita da sauri major Marry ta bude mishi motar ya shiga driver yaja suka tafi.

Tafiya me nisa sukayi kafin suka tsaya a wani katafaren filin da babu gida ko daya a wajen se private jet din LTG.Taj ne kaɗai a wajen fitowa ya yi,ya shige cikin jirgin, major Marry ce ta dauko Sabriyah a kafadarta suka shiga jirjin,nan take ya tashi a cikin sararin samaniya.



MAIDUGURI STATE


Karfe biyu na dare su ka shigo Maiduguri saboda sun tsaya a headquarter Damaturu,kowa ya yi bacci a gidan Masu tsaron gidan ne da kuma sojojin da suka zo daga gari mabanbanta domin kulawa da lafiyar LTG.Taj, ne kaɗai idon su biyu packing motar driver ya yi acikin gidan,fitowa ya yi yana me karewa gidan kallo, saboda ganin gidan ya keyi kamar sabon waje a wajensa domin an sabunta komai a cikin gidan,shekaru goma ya diba be waiwayi wannan gidan ba.

Daukar ta ya yi ya nufi cikin Mansion din da ita yana isa ya jefata akan 3 seater na main part din gidan ya haura upstairs din da ze sada shi da part din shi,kallon Sabriyah major Marry ta yi se taji,be kamata abarta ta kwana a wajen ba amma babu yanda ta iya haka ta haura upstairs din itama ta bi bayan shi,be juyo ya kalleta ba ,da hannu ya nuna mata wani bedroom da yake upstairs alamar anan ne zata sauka shiga ciki ta yi taga komai akwai acikin bedroom din nan take ta shiga ta yi wanka saboda sun kwaso gajiya.

A bangaren LTG. Taj ma haka wanka ya yi,sannan ya yi wasu bincike kafin nan ya tada sallar nafila.



Asuba na gari, mazan gidan kowa ya tashi saboda zuwa Masallaci duk babu wanda yasan da zuwan Tajuddeen, sede kawai sojojin sa da suka gani acikin gidan,da mamaki suka je sukayi sallah suka dawo kowa ya koma domin ci gaba da bacci.


8:30am


A hankali tafara bude manyan idanunta da suke a kumbure saboda kuka da kuma baccin da ta yi tun jiya,ji ta yi sun yi mana nauyi sosai, mikewa ta yi ta zauna tana riƙe da kanta,da shima ya mata nauyi,se a sannan ne idonta ya samu damar budewa gaba daya,da mamaki taƙe ƙarewa falon da take ciki kallo,da hanzari ta mike tsaye tana kallon ko ina na cikin falon.nan take ta tuna abinda ya faru jiya.aranta ta ce "wato ji mini ciwon da ya yi ne be isheshi ba shine ya sato ni,to Wallahi ni be isa ya sato ni ba"

Dawuwa tsakiyar falon ta yi ta rike kugunta cikin daga murya ta ce"uban wayeeeeeee. Ne ya kawo ni gidan nan!?in ka isa ka fito ka mayar dani in da ka sato ni!".

Da iya karfinta take magana,tana jiran ya fito,ganin babu wanda ya fito yasa ta ci gaba da magana da karfi wanda hakan ya yi sanadiyar tashin mutanen gidan daga bacci duk suka fito falon maza da mata,amma banda anty amarya,suna kallon Sabriyah acikin falon suka fara tambayar junansu ita kuma wannan wacece?.

Saghar ne ya ce"ke kuma daga ina zakizo kina yi wa mutane ihun hauka!?,wait! in the first place uban waye yabaki izinin shigowa cikin gidan nan!?"

Kowa dake cikin falon se kallon Sabriyah sukeyi suna mamakin me take yi a cikin gidan.

Watsawa Saghar harara ta yi,cikin tsiwa da daga murya ta ce "na fiku rashin mutunci ni za'a gwada wa duniya da bariki nida na fito daga cikinta,a sato ni sannan a zo ana tambayata me nake yi anan.ka da ka kuskura ka zageni yauwa."

Tashin hankali su Zoya kam da ido kawai suke bin Sabriyah suna jinjina rashin Kunyar ta ganin yanda ko tsoron Saghar bataji ba,ta tsaya tana gaya mishi maganar da ranta ya so.

Sahil ne da yaga in sukace ta haka zasu biyo mata tofa bazasu ji abinda suke son ji a wajanta ba,hakan yasa cikin ruwan sanyi ya ce"baiwar Allah daga ina me kike bukata?"

Juyawa ta yi taga me maganar ta ce"ai ku zan tambaya,meye dalilin ku na sato ni?".
Kallon juna suka fara yi.

Ammi ce ta matso kusa da ita ta ce"yan mata ki nutsu ki faɗa mana menene ya kawo ki". calmly Ammi ta ke mata magana wanda hakan yasa taji Ammi ta yi mata matukar gwarjinin da bazata iya bata wani amsar da bashi bane.

"Wanine ya sace ni,shine yanzu ina farkawa na gan ni a nan".jinjina kai Ammi ta yi ta ce "daga wani gari kenan!?",amsa Sabriyah ta bata" daga Lagos afafa " dukkanin su zaro ido waje sukayi se sannan ne ma suka sa'ke kare mata kallo sukaga irin shigar dake jikinta.


Tsaki Ammuh ta yi ta ce "to wani shegen ne ya kawo mana karuwa kuma cikin gidanmu,na halak!?"


Muryansa da basu yi tsammani ba suka ji ya ce.

"Ni na kawo ta"

Gaba dayan su a tare suka maida kallonsu da kuma hankalinsu upstairs,cike da al'ajabi suke kallonsa babu ko kyaftawa.

Cikin isa da takama yake saukowa daga stairs din kamar bayaso,yana sanye da gajeren wando da kuma rigar t-shirt gaba daya farfadar kirjinsa a bude saboda botile din rigar biyu kawai yasa, damtsen hannunsa duk yana waje rigar me guntuwar hannu ne.

Karasa saukowa ya yi falon idonshi akan Ammi da take sakar mishi murmushi.




Se mun haɗu Monday in me duka yakaimu da rai da lafiya.


Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.


Comment,like and share 🖋️🖋️

*🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹*


Page 17


*_Story & written_*


By

*MRS🌹ISHAM🌹*
( Yar lelen Jarumai)




*THE WRITER OF 🖋️*
*NIDA PATIENT DINA*


~And now~
*🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*



📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️


Page 17


Karasowa cikin falon ya yi da mamaki suke kallonsa,suna al'ajabi yaushe ya zo,cike da kissa Ammuh ta zo ta rungumesa ga murmushi a fuskarta tana"oyoyo!oyoyo! oyoyo!ɗana sannu da zuwa, gaskiya na yi kewarka sosai"hugging dinta back shima ya yi,duk da bayason yawan magana amma hakan be hanashi cewa Ammuh "missed you too Ammuh dina"saketa ya yi,ya je wajan Ammi ya rungumeta yana me sauke ajiyar zuciya,hakan da ya yi bakaramin bata ran Ammuh ya yi ba,nan take taji ranta be so hakan ba,aranta kuwa se kulle_kulle takeyi tana son ta sake taso da tsohuwar ƙiyayyar da Tajuddeen yakeyiwa kowa.

A tare samarin gidan suma suka rungume shi suna mishi sannu da zuwa,su Zoya kam kwakkwaran motsi sun gagara yi ɓalle su mishi sannu da zuwa, Parsa dake dauke da wannan ƙayata zaciyar murmushin nata ne tazo ta rungume shi tana.

"Welcome back ya Taj we have missed you alot".

Shafa bayanta ya yi be ce komai ba,kaff gidan kowa yana son yarinyar saboda ko kadan bata da damuwa, she's very unique,kusan ma za'a iya cewa ita ce logon su,weak point din su,ji sukeyi da ita kamar yanda ake ji da kwai.wannan dalilin yasa kowa na gidan yake son ta hatta shi kanshi LTG yana ji da ita.

Kowa dake falon seda suka mishi sannu da zuwa duk da bawani amsawa ya keyi ba.
A bangaren Sabriyah kuwa tunda LTG ya sauka take kallonsa musamman damtsen hannunsa da kuma farfadar kirjinsa, tunda take bata taɓa ganin mutum me irin zubin halittar jikinsa ba,hakan yasa ya koma tv awajanta.can kuma ta tuna da sace ta da ya yi, ga kuma mutanen gidan sun wani tsaya se wani sannu da zuwa suke mishi sun manta da sabgarta hakan ne yasa,ta matso kusa da shi.

Ta ce "wato raunin da ka ji mini a kasuwa be isheka shine ka sato ni,to baka isa ba kawai in kanason kwanciyar hankali da kai da mutanen gidan nan ka maidani gidanmu!"ta karasa maganar tana wani girgiza kai kamar dukan shi zata iya yi ,ga ta yar karama a gabanshi se ta daga kanta tukun take kallonsa duk da itama tana da tsayi dede gwargwado.

Ko kallon in da take tsaye be yi ba bare ta sa ran ze amsa mata,se ma juyawan da ya yi ze koma part din shi.da sauri ta bisa a baya tana"kazo ka mayar dani dan Allah,akwai yar uwa ta da aka sace zan nemo".


Su de su Ammi da kallo kawai suke binsu,domin kuwa sun rasa dalilin da yasa LTG ya daukota ya kawota gidan.

Haurawa ya yi ko juyowa be yi ba,ganin ya haura ne yasa ya tsuguna agun ta fashe da wani sabon kuka, babban damuwarta ita ce Asmita,bata san wani hali take ciki ba, batasan su waye suka sace ta ba.burinta kawai taga ta samo Asmita,gaba daya abubuwa sun haɗe mata kai ta rasa da wanne zata fara guda daya.


Ganin ta tsuguna tana kuka ne a matattakalar benen yasa Ammi ta haura ta ɗaukota suka dawo kasa,zaunar da ita ta yi, akan kujera.hajiya babba ce ta matso ta zauna kusa da Sabriyah ta ce "yarinya ya sunanki!?",se da ta goge hawayen fuskarta tukun ta iya cewa" sunana Sabriyah".

"Meyasa kike kuka kuma meye ya haɗa ki da Tajuddeen!?", Hajiya babba ta sake je fo mata tambayar,tsaki Ammuh ta yi ta ce "gaskiya mutanen gidan nan akwai ku da son yin gwaninta!,karuwar ce ku ka tsaya kuna wani lallabata!?"ta faɗa tana harare_harare kafin ta sa'ke jan wani tsakin ta wuce part dinta,ummah part dinta itama ta wuce dama ita tunda ta fito batace komai ba.sude su Sudais da su Zoya duk suna tsaye a falon sun zubawa Sabriyah ido,gani sukayi tana kusan yanayi dasu,ga kuma kyawunta me jan hankali kukan da takeyi ma ƙara mata kyau ya yi, girgiza kai Hajiya babba ta yi kawai sannan ta ce "kar abinda ta faɗa ya dameki faɗa mini inajinki",kwashe gashinta da ya zuba ta gefen wuyanta tayi ta maida shi baya kafin ta ce"ah ah maganar ta be ɓata mini rai ba,kuma ai gaskiya ta faɗa!,na haɗu da wannan mugun ne a kasuwa ban taba ganinsa ba amma ranar da muka haɗu dan kawai munci karo da juna shine ya yi wurgi da ni,na faɗi se da naji ciwo a hannuna,ranar da wasu wa'yanda bamu san ko su waye ba suka sace mini yar uwa ta,aranar shima ya sace ni ya kawo ni nan."jinjina kai sukayi bayan sun gama jin abinda ta faɗi su de har yanzu basu ga wani dalilin da har ze sa, LTG ya sace yar mutane ba,abin ya daure musu kai,duk shuru sukayi basu ce komai ba, kowa da abinda yake saƙawa a ransa,ɗago kai Sabriyah ta yi ta kalli Ammi ta ce"ki yiwa wannan mugun magana ya mayar dani inda ya dauko ni,in je in nemo yar uwa ta".murmushi Ammi ta yi jin yanda Sabriyah ta ke kiran LTG da mugu duk da har ranta bataji dadin kalmar ba amma yanda Sabriyah ta yi mata magana cikin shagwaba ya bata dariya hakan yasa ta ce"shikenan ki kwantar da hankalinki zanyi mishi magana kuma ze mayar dake nice mahaifiyar sa,in Allah ya yarda za ki koma garin ku."gyada kai Sabriyah ta yi,kallon su Umaisha Ammi ta yi ta ce Umaisha zo ki dauketa kuje part dinku ku zauna tare.

"Okay Ammi"umaisha ta faɗa tana yiwa Sabriyah murmushi,yatsina fuska Zoya ta yi,cikin mamaki ta ce"like serious Ammi!?, gaskiya wannan karuwar bazata je mana part din mu ba,najasa ce f......"wani irin tsawa Sudais ya daka mata wanda ya hanata karasa maganar da zata faɗa."will you be quiet,you idiot!in na sa'ke jin muryarki se na ci ubanki a gidan nan mahaukaci kawai."nan take ta nutsu ta sun kuyar da kanta dan tasan karamin aikin Sudais ne yanzu yamata ɗan banzan duka.

Hajiya babba ta ce "Zoya wannan banzar halin naki ki gaggauta barinsa nade gaya miki yarinya kenan se bakin hali"haka Hajiya babba ta dinga surfa mata masifa.duk cikinsu babu wanda ya ji dadin maganar da Zoya ta faɗa,saboda duk yanda mutum yake baze ji dadi ba in aka kirasa da wannan abun.


Rike hannun Sabriyah Umaisha ta yi ta ce "sis ta shi muje part din mu"fisge hannunta Sabriyah ta yi,ta ce "babu inda zani fa,bazan taɓa motsa wa anan ba se wancan mugun ya fito ya maida ni"ikon Allah yau ake yin ta,yau Allah ya hadasu da me taurin kai da naci,ga ta daga ido de ba za'ayi tunanin za ta yi taurin kai ba, se de duk wanda ya mata kallo ɗaya yasan za ta yi masifa da tsiwa da kuma rashin kunya amma alamar taurin kai be nuna a tattare da ita ba.
Kallon Zoya Sabriyah ta yi ta galla mata harara ta ce "ke kuma dakikiyar banza da kike cewa karuwa bazata shiga muku waje ba ,to ni me ma ze kaini ko an gaya miki ina son in ƙara ko da second daya a gidan nan ne!?,ki shiga taitayinki nafiki hauka tam.karki ga ke yar masu kuɗi ce, ki ce zakimin tijara.sauya miki kamanni zanyi babu abinda yashamin kai".yanda Sabriyah take magana da masifa_masifa kamar zata je ta da ki Zoya ne ya bawa Sahil,Salim,Jawan dariya ganin sun samu wata comedian a gida.

"Yi hakuri Sabriyah,tashi ki bi umaisha kuje ku ciki, lokacin breakfast ma ya wuce kuyi sauri, Umaisha ki nuna mata komai tayi wanka,ki bata kaya tasa"Hajiya babba ta yi magana tana kallon umaisha sannan ta kalli kayan dake jikin Sabriyah ta girgiza kai aranta tana tambayar kanta ko yarinyar nan musulma ce.domin kuwa shigar jikinta kwata_kwata beyi tsari ba.

Rike hannun Sabriyah Umaisha ta sakeyi a karo na biyu,bin bayanta Sabriyah ta yi badan taso ba,bataso ta tsaya musu da su Hajiya babba da Ammi ne. saboda duk fitsaranta bazata iya musu ba.har sun haura upstairs Ammi ta kira sunan Umaisha juyawa ta yi,Ammi ta ce "Umaisha give a decent dress please" "okay" sannan sukaci gaba da tafiya,Zoya de tunda Sabriyah ta zazzage mata salon nata rashin kunyar da tsiwa ta yi shuru bakinta ya mutu murus,part din Ummah ta yi fuuuu,kamar zata fire sama.bin bayanta sukayi da kallo,Jawan cikin daga murya da tsokana ya ce"gaba ma da gabanta aljani ya taka wuta,kin haɗu da wacce ta fiki rashin ji ai"ko waigowa Zoya bata yi ba se ma kara saurin da ta yi,dariya duk sukayi, Parsa ta ce "Rameesa, Sabriyah kyakkyawa ce ta burgeni sosai "dariya Rameesa da iklas sukayi.iklas ta ce "honestly she's very gorgeous" "to yanzu de kuzo muje muyi wanka se mu fito a yi breakfast"cewar Rameesa da ta fara tafiya bin bayanta sukayi su dema.

Zama Saghar da Jawan sukayi kasa_kasa da murya Saghar ya ce "amma Jawan kai a naka tunanin me zesa LTG guda ya sato mace!?",shima Jawan kasa da murya ya yi,ya ce"that's what am still wondering!me ze sa ya Taj ya sato wannan zankaɗeɗiyar budurwan batare da dalili ba!?".haka suka dinga magana kamar wasu munafukai,babban abinda basu sani ba shine su Sudais Sahil, Salim, Ammi,Hajiya babba duk sunji abinda suka faɗa.tafa hannu Hajiya babba ta yi "la'ilahaillahu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallama,yanzu dama maganar da ake faɗa a gari cewa gulma ya tashi daga kan mata ya koma kan maza ashe da gaske ne!ikon Allah wato Saghar da Jawan kude bazaku dena wannan iya shegen naku ba.tabb dijam ahhh lallai lamarin ku ya girmama,ku de bari Tajuddeen ya ji ku". tunda Hajiya babba ta fara magana suke dariya har su masu gulman saboda su kwata_kwata basu yi tunanin ana jinsu ba.tsagaitawa da dariyar Salim ya yi ya ce"ai Hajiya babba kaff gidan nan babu irin Saghar da Jawan a wajen fannin sa ido da gulma ne"tabe baki Hajiya babba ta yi sannan ta ce"yooo ai naga alama,bari ma in shige ciki."haurawa part dinta ta yi tana tafiya tana tafa hannu irin abin ya bata mamaki.(hhhhhhh, Hajiya babba kema akwai abin dariya ba laifi,to ai gulma ya daɗe da koma kan maza mutanen mu).
Ammi de se murmushi take musu maida hankali ta yi kan Sudais ta ce "rabu da wa'yannan naga yau su basu da niyar yin breakfast din ɓalle suje wajen aiki".kallonta sukayi atare su biyun suka haɗa baki wajan faɗar "Ammi abin kuma wariyar launin fata ne!?"Saghar da Jawan suka faɗa,marairace fuska twins Sahil, Salim sukayi sukace"ayyah Ammi muma fa yan gaban goshin ki ne,shine za ki cewa Sudais shi kadai ya ke da niyar zuwa gun aiki!", kwaikwayon yanda sukayi maganar Sudais ya yi yana"yen!yen!yen!ƙatti da ku agaban ƙannenku kuna wani shiririta shame on you guys" Ammi de ce musu ta yi"ku de ba'a iya muku,se anjumanku mu haɗu a dinning kawai".ta faɗa tana barin falon.
Duk watsewa suka yi a falon kowa yaje dan ya shirya .


Part din su suka shiga,cike da walwala Umaisha ta ce "muje ki sauka a dakin mu !"burki Sabriyah taja ta haɗa fuska ta ce "ke banason iyayi fa, na ce bazan sauka a wajanku ba dole ne!".zaro ido waje Umaisha ta yi tana mamakin hali irin na Sabriyah aranta ta ce "wai nikan wannan ba'a mata gwaninta ne?ohhh wato kowa da irin halinsa"karewa part din nasu kallo Umaisha ta yi,idonta ne ya sauka akan wani daki madaidaici wanda ya kasance extra room din dake part dinsu,bayan daki guda biyun dake cikin part dinsu din akwai daki madaidaici.

Gaba Umaisha ta yi ta ce "to muje dakin nan,ke kadai anan din,tunda kin fison zama ke daya,ai kadaici kadai ma se ya isheki.nifa inni ce wallahi bana iya zama Ni daya kamar mayya,ko yaushe nafison injini cikin mutane ai yafi dad'i, mutane rahama ne!,ke nifa bama wannan ba,abinda yasa bana zama ni kadai ina da matukar tsoro,se in ga kamar dodo ze kamani.yanzu ke haka kika zabawa kanki zama ke daya!?,haba Sabriyah ke haka za ki zauna Kamar wata mayya!?,"bin bayanta Sabriyah ta yi tana mamakin surutu irin na Umaisha tafiya takeyi amma se zuba takeyi kamar kurna, bata ko haɗiye yawu,jera magana takeyi ko gajiya batayi ba.sabriyah takasa dena kallonta,ita de tana fama da abinda yake damunta na sace Asmita ga kuma kawota nan da LTG ya yi ga kuma Umaisha da tasata a gaba da magana kamar wata yar jarida.

Dakin suka shiga, ya hadu komai akwai aciki.
Nuna mata yanda zata yi amfani da toilet din da kuma sauran abubuwan ta yi,kafin ta ce"kiyi wanka bari in kawo miki kayan sawa".ba tace mata komai ba toilet ta shiga,ita kuma Umaisha ta fita a dakin da hanzari,wanka Sabriyah ta yi ta ta wanke gashinta, daura towel din da ta gani ta yi. fito gashinta na diga da ruwa,tsane jikinta tayi ta goge dogon baƙin gashinta,tana zaune a gaban mirror ta shafa mai din da ta ganim ta taje gashinta ga handryer a kan mirror amma bata san meye amfanin shi ba kuma bata san ya akeyi dashi,ta cikin madubi ta hango kayan da Umaisha ta kawo mata,mikewa ta isa gaban gadon ta dauki kayan,warwaresa ta yi,abaya ce dark brown color har ƙasa yasha stones ta ko ina se kuma wando jeans black color wanda za'a sa ta ciki,tsaki ta yi a yayinda take wurgi da rigar akan gado ta ce "Tabb dijam waye ze saka wannan ƙatuwar rigar lallai kam ai dole in nemi wata rigar da zansa da wandon nan,ita kadai take magana ta nufi hanyar barin dakin daga ita se towel a daure a kirjinta ga rabin fararen tula_tulanta awaje,dakin da ta gani kusa da inda ta sauka ta shiga ta tsaya daga bakin kofa,ta ce "abani riga t-shirt!"Parsa da ita kadai ne tayi saura a dakin ne,ta ɗago kai ta kalleta ta yi murmushi ta ce"okay bari in kawo miki"da sauri ta mike ta nufi dressing room din su ta dauko mata sabuwar riga acikin ledarta ta fito ta bata,karba Sabriyah ta yi a wajen ta saka ta dawo da towel din kugunta sannan ta bar bakin kofar ta koma nata masaukin.

Shiryawa ta yi tsab cikin riga da wandon ta zauna a dakin tana tunani ina zata samo Asmita,wani hanya ya kamata tabi ta samo Asmita, Rameesa ta shigo ta ce "hi yan mata!ance ki zo muci abinci." "nakoshi"cewar Sabriyah,barin dakin Rameesa ta yi bata sa'ke magana ba.


Kowa ya hallara a dinning table hatta LTG da major Marry duk suna zaune kowa ya fara cin abinci Rameesa ta dawo ta ce "Ammi wai ta ce ta koshi"gyada kai Ammi ta yi ta kalli fatime ta ce "ki shiryawa bakuwarmu abincinta,ki kai mata". "to Ammi" shiryawa Sabriyah abinci fatime ta yi,ta nufi upstairs.

Kallon Ammi anty amarya ta yi ta ce "Ammi yaushe akayi bakuwa!?, wacece haka!?"ta jerowa Ammi tambayoyi tana son jin amsarta,kafin Ammi ta yi magana Ammuh ta rigata cewa"wata karuwa ce Taj ya kawo"da mamaki anty amarya ta ce "karuwa kuma!?, kamarya karuwa!?"LTG de abincinsa kawai yake ci kamar be ji me suke faɗi ba.major Marry kuwa se kallon bakinsu takeyi yana magana amma bata iya gane ko da kalma daya da suke faɗa tunda ba Hausar take ji ba.

"Tajuddeen ne ya kawo ta duk da be faɗa mana dalilin da yasa ya kawo ta ba".
Ammi ta gayawa anty amarya jinjina kai ta yi taci gaba da cin abincinta.
Uncle Hameed ya ce"LTG meyasa ka daukota, kuma naji Ammuh dinku na cewa wai karuwa ce?".

Sipping din black tea din dake hannunsa ya yi ba tare da ya ɗago ba ya ce"bincike ne ya biyo ta kanta"daga haka
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment