Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

SARAUTAR MUTUWA
Haƙƙin mallaka
SUFI
Shekarar bugu
2023
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071




Babi na ɗaya

A ƙarni na biyu bayan yaƙin duniya na ɗaya, a yankin arewacin larabawa anyi wani kasaitaccen birni da ake yi wa laƙabi da zawatul-ifdar.
Birnin zawatul-ifdar ya bunƙasa a harkokin kasuwanci,noma,kiwo da ƙarfin tattalin arziki.
Sarkin da ke mulkin birnin yakasance gawurtaccen matsafi kuma mashahurin attajiri ana yi mashi laƙabi da Lazwar ibn kaulat.
A gaba ɗaya nahiyar larabawa babu mashahurin sarki tamkar shi bisa wannan dalili ne ya sanya ya zamto GAGARABADAU a tsakanin sarakunan nahiyar.
Duk waɗannan abubuwan da sarki Lazwar ya tara da ya danganci ƙarfin sihiri da tarin dukiya gami da ƙarfin masarauta ya tashi a banza, domin a daren kowa ce rana sai na kulle ƙanshi a turakarshi ya yi ta kukan takaici da baƙin ciki, har sai kuyangin shi sun shayar da shi barasa sannan yake samun barci.
Ba komai ne yake sanya sarki lazwar wannan kuka ba face wani dalili guda ɗaya jal!
Dalilin kuwa shi ne bisa binciken da ya gudanar bisa halarar tsafin shi ya gano cewa har abada ba zai samun haihuwa da kowa ce ya mace ba face ya karya wani sihirin tsafi da a bokin gabarshi sarki darwazu ya yi mashi.
Matsawar kuwa ya yi ganganci ya sadu da wata ya mace koda da kuwa kuyangarshi ce take dukkanin sirrikan tsafinshi da duk abin da ya mallaka zai ƙare zai dawo talaka fakiri.
Tsawon shekaru biyar sarki Lazwar yana cikin wannan baƙin ciki dare da rana.
Kwatsam! Wata rana sai kawai aka ji ya ƙwalla ƙara sannan ya bushe da dariya, sautin dariyar tashi ya amsa kuwwa izuwa gidan sarautar baki ɗaya.
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa kowa mamaki kenan, domin yau tsawon shekaru biyar ba'a taɓa jin shi ya yi hakan ba.
Abin da mutane ba su sani ba shi ne bakomai ba ne ya sanya sarki lazwar wannan dariya ba,
sai domin yau ne ya gano hanyar da zai lalata sihirin da abokin gabarshi sarki darwazu ya yi mashi.
Abu na farko da zai mallaka shi ne hawayen wani gawurtaccen dodo dake zaune a dajin Darul-shatir dodo murgazu yakasance hatsabibi wanda ya addabi fatake da biranen da maƙwabtaka da dajin Darul-shatir.
Abu na biyu shine tsumin tsafin bokanya lazira,
bokanya lazira ta shafe tsawon shekaru dubu biyu tana tsuma tsumin tsafin domin ta cika burin ta na tashin kakanta sarkin bokaye daga cikin kushewarshi domin ya sanar da ita waɗansu sirrikan tsafi da zata mulki duniya da su.
Abu na uku shine ruwan tekun Bahar-dawa'u, tekun Bahar-dawa'u na yamma maso arewacin duniya, yana ɗauke da waɗansu irin musifaffun kifaye da macizai da adadin su ya kai dubu biyar, tsananin ƙarfin damtsen ɗaya daga cikin kifayen yafi na bil'adama hamsin.
Abu na huɗu shine alkyabbar sarkin bokayen duniya na ɗaya boka Murkatul-azab, a halin yanzu alkyabbar na ajiye a fadarsho dake ƙarƙashin tekun Bahar-maliya, matsafa,bokaye da masu hasashe sun tabbatar da cewa a halin yanzu a duniya babu wani waje mai tattare da musibu tamkar fadar sarkin bokayen duniya.
Abu na ƙarshe shi ne wata jaruma da ake yiwa laƙabi da Sharifa bintu Usman.
A halin yanzu Sharifa na bauta ne a ƙarƙashin masarautar birnin Istanbul a matsayin baiwa, mahaifanta sun rasu ne a bisa KANGIN BAUTA a masarautar.
Baiwa Sharifa ce kaɗai zata iya taimaka mashi ya samu nasarar mallakar waɗancan abubuwa.
Sa'adda darki Lazwar ya ga wannan al'amari sai ya cika da matuƙar farin ciki, sai dai wani abu daya dugunzuma hankalin shi, shine halarar tsafinshi ta bayyana mashi cewa ba zai taɓa samun nasarar saduwa da baiwa Sharifa ba har ya bayyana mata buƙatar shi na son ta taimaka mashi ya samu nasarar mallakar waɗancan abubuwan da zai karya sihirin ba, face shi ma ya mayar da kanshi bawa ya yi bauta a ƙarƙashin masarautar na tsawon shekaru.
Sannan ma inda gizo ke saƙar shi ne, ba lallai ne Sharifa ta iya amincewa da buƙatar shi ba, tunda a halin yanzu ta rasa dukkan wani farin cikin rayuwar ta.
Kasancewar masu iya magana na cewa biyan buƙata yafi dogon buri, kuma inda rai da rabo.
Sai sarki Lazwar ya tsayar da ranar da zai fita farautar baiwa Sharifa.


Babi na biyu

Kashe gari tun da duku-dukun safiya sarki Lazwar ya fara shirye shiryen tafiya izuwa birnin Istanbul , a dai-dai lokacin da rana ta fara haske ne ya kammala shirin tsaf!
Tun daga kuyangi masu hidima, dakaru, gami da bayi.
A can fada kuwa jama'a sun cika maƙil babu masaka tsinke. Duk inda mutum ya kalla kawunan bil'adama ne rututu babu saka tsinke tamkar dandazon kiyasai.
Kowa ya zuba idanu ana jiran fitowar sarki domin ganin wane zai baiwa riƙon sarautar shi.
Tsawon daƙiƙa latalin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne aka jiyo bushin algaita haɗe da bugun tambura.
Daga can sai ga sarki Lazwar tafe tare da tawagarshi yana sanye cikin surutu na alfarma da sukayi matukar yi mashi kyawu, kai tsaye ya huce izuwa kan karagarshi ta mulki ya tsaya sannan ya fuskanci jama'a ya yi gyaran murya ya ce "ya ku mutanen wannan fada tawa mai albarka ku yi sani cewa a yau ne zan yi gagarumar tafiya izuwa nemo abubuwan da za su warkar da ni daga sihirin da abokin gaba ta sarki Darwazu ya yi mini.
A bisa al'adar wannan masarauta sarki da kanshi yake zaɓar wanda zai bawa riƙon sarautar shi.
Bisa ga nazari da kuma hasashe da nayi babu wanda zai riƙe sarautar wannan birni da amana face magajin gari Yasiran".
Sa'adda sarki Lazwar yazo nan a zancen shi sai jama'a suka ruɗe da shewa da jinjina domin suna ganin shike nan sun huta da mulkin zaluncin sarki lazwar.
Kaico! Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce rashin sani yafi dare duhu, inda a ce jama'a sun san wane ne magajin gari Yasiran da sun gwammace gwara sarki lazwar sau ɗari.
Bayan an ɗora Yasiran a bisa karagar mulki sai kawai sarki Lazwar ya buɗe bakinshu ya ƙwala wa wani hadimin aljanin shi kira sau uku, yana gama rufe bakinshi sai kaga wata halitta shirgegiya na ketowa daga cikin gajimare tana sauka daga sararin samaniya. Nan fa suka ɗimauce suka fara guje-guje da ifice-ifice tamkar sun hango mutuwarsu, wasu ma saboda razani har sakin fitsari suke a wando basu sani ba.
Aljanin ya sauka a turba yana mai shimfiɗe fuka-fukanshi a ƙasa, shi dai aljanin ya kasance shirgege tamkar tsauni yana da rafkeken kai mai ɗauke da kwala-kwalan idanu jajur tamkar garwashin wuta, hancinshu ƙato ne kofofinshi tamkar bututun shaƙar iska, bakinshi yana da girma tamkar bakin rijiya, maƙale a kwiɓin hamatarshi yana ɗauke da manyan fuka-fukai guda huɗu.
Haƙiƙa wannan aljani yakasance mummuna kuma abin tsoro ga duk wata halitta mai numfashi.
Aljanin ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa ga sarki Lazwar.
Sannan ya ɗago da kanshi ya dubi sarki Lazwar cikin ladabi ya ce cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce "ya mai duniya gani na amsa kiran ka me kake da buƙata ya shugabana?
Wani alfahari ya shiga kwanyar sarki lazwar jin aljanin ya ambace shu da mai duniya,
cikin BAƘAR IZZA Lazwar ya ce " ya kai Za'aratun-layal ka yi sani cewa bakomai ya sanya na kira ka nan ba sai domin ka ɗauke ni da tawaga ta domin gudanar da wata gagarumar tafiya mai matuƙar haɗari.
Sai dai ina so ka yi sani cewa wannan shine aikin ka na ƙarshe da zan 'yan ta ka ' daga ƘANGIN BAUTA a gare ni".
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai aljani Za'aratun-layal ya bushe da dariyar farin ciki, dariyar tashi ta haddasa wata gagarumar girgizar ƙasa mutane suka fara halaka, sai da sarki Lazwar ya daka mashi tsawa, sannan ya tsuke bakinshi, a sannanne komai ya samu dai-dai ta.
Ba tare da ɓata lokaci ba sarki Lazwar da tawagarshi su ka hau bisa kan Za'aratun-layal da ya haɗar da sarkin yaƙin birnin da waɗansu zaratan bayi gami da kuyangi masu hidima suka zauna aka ɗora abin guzuri akai.
Sannan aljani Za'aratun-layal ya yunƙura ya tashi sama yana mai kaɗa fuka-fukanshi tare luluƙawa cikin gajimare yana mai tsala azababban gudu, tun jama'a na daga masu hannu har suka dai na hango su.
Sai da aka shafe tsawon sa'a bakwai ana tafiya a sararin samaniya ana keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya.
Lokacin da sa'a ɗaya ta shuɗe ne aljani Za'aratun-layal ya saki fuka-fukanshi ya sauka a turba,inda ya saukar yakasance wani daji ma'abocin kwarjini daban tsoro tun da aka shiga dajin kowa yasha jinin jikinshi, domin dole ne a samu wani abu mai cutarwa a cikin shi.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka ga waɗansu irin masifaffun kibiyoyi suna sauka a dajin, duk da irin ƙwarewa ta dakarun sarki Lazwar kafin su yi wani yunƙuri sai da kibiyoyin suka hallaka fiye da mutum ɗari.
Al'amarin da ya fusata sarki Lazwar kenan ya karanta waɗansu ɗalasiman tsafi amma bisa mamaki sai kawai ya ga ya zama hayaƙi.
Al'amarin da ya yi matuƙar bashi mamaki kenan kuma ya ɗaure mashi kai kawai sai ya zare takobinshi ya kama kalle-kalle da dube-dube a dajin cikin matuƙar fushi.
Kwatsam! sai aka jiyo motsawar ganyayyakin bishiyun daga wani ɓangaren dajin, daga can sai a kayi arba da wata kyakkyawar yarinya mai kimanin shekaru goma sha biyu, zaune a bisa kan shirgegiyar damisa jikin ta sanye da kayan fata riga da wando da takalmi, a gadon bayanta tana rataye da wata zabgegiyar takobi, a hannunta na riƙe da wata irin kwari da baka, nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su sarki Lazwar da yarinyar.
Lokacin da aka shafe tsawon daƙiƙa latalin ana kallon-kallo tsakanin wannan kyakkyawar yarinya da su sarki Lazwar. sai Lazwar ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar duban yarinyar cikin matuƙar fushi yana mai nuna ta da tsinin takobinshi cikin kakkausar murya ya ce "ya ke wannan 'yar ƙaramar ƙwaruwa shin wane irin rashin hankali ne ya sanya ki aikata wannan laifi a gare ni? Ina so ki bani amsar wannan tambaya kafin na zare miki ruhinki daga gangar jikinki kiyi mutuwar wulakanci.
Ko da jin wannan tambaya sai kawai kyakkyawar yarinyar ta bushe da dariyar mugunta.
Al'amarin da ya bawa kowa mamaki kenan kuma ya fusata su ainun, bisa ganin cewa yarinya ƙarama da bata huce ayi mata kwab ɗaya ba amma ta yi GABA DA GABA da dandazon mayaƙa amma bata razana ba.
A Lokaci guda yarinyar ta murtuke fuska sannan ta dubi sarki Lazwar cikin wata irin zazzaƙar murya mai ɗan karan daɗi tamkar sarewa ta ce
"Ya kai sarki Lazwar ibn kaulat na birnin zawatul-ifdar ka yi sani cewa fiye da shekaru biyar baya na san da labarin ka kuma zaka yaɗa zango a wannan daji domin ka gudanar da tafiyar ka ta nemo abubuwan da za su warkar da kai daga sihirin da abokin gabar ka sarki Durwazu ya yi maka.
Ko da jin wannan batu daga bakin kyakkyawar yarinyar sai sarki Lazwar ya cika da matuƙar mamaki ya dubi yarinyar ya ce "shin ya aka yi kika san ko ni wane ne kuma mene ne buƙatar ki agare ni.
Yarinyar ta ce "mahaifina mafarauci Murrasu kafin rasuwar shi ya sanar da ni labarin ka kuma ya bayyana mini cewa kai ne zaka iya taimaka mini na samu nasarar saduwa da mahaifiya ta dake ƘANGIN BAUTA a can birnin Istanbul bayan na taimaka maka ka sadu da Baiwa sharifa wacce za ka je farautar ta a cikin birnin Istanbul.
Ko da jin wannan batu daga bakin kyakkyawar yarinyar sai sarki Lazwar ya sake cika da matuƙar mamaki,
kuma ya taka da ƙafafuwanshi ya durfafi inda take ya yin da ya rage saura taku goma a tsakanin su sai ya ja ya tsaya.
Cike da matuƙar mamaki ainun ya sake duban ta ya ce "ya ke wannan yarinya mai abin al'ajabi shin mene ne labarin ki? Kuma mene ne ya kai mahaifiyarki bauta a birnin Istanbul?
Da jin waɗannan tambayoyi sai hawaye suka kwaranyo daga idanun yarinyar.
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa sarki lazwar mamaki kenan ya ce a ran shi, shin ina dalilin wannan hawayena yarinyar?
Yarinyar ta share hawayen ta cikin alamun matuƙar damuwa ta ce "da farko dai suna na Shuraiba bintu Murrasu, ya kai Lazwar ka yi sani cewa mahaifina mafarauci Murrasu lokacin yana raye yakasance babban hadimi ga sarkin birnin Istanbul, shi ne mai kula da abin da ya shafi tufafin da sarki ke sanyawa da ma sauran iyalan gidan sarautar birnin baki ɗaya.
Wata rana mahaifina ya fita farauta daji domin farauto wata dabba da sarki ya ce ke bukatar a yi mashi alƙyabba da ita.
Tun safe ya tafi amma har la'asar ta shuɗe bai dawo ba nan fa ni da mahaifiyata mu ka shiga cikin matuƙar damuwa, muna cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai mu ka jiyo haniniyar dawakai a can ƙofar gida
Kafin mu yi wani yunƙuri sai muka ga dakarun sarki sun shigo gidan, ina ji ina gani su ka kama mahaifiyata ta ƙarfin tsiya suka tafi da ita.
Ina ta rusa kuka tamakar raina zai fita a daren wannan rana ne mahaifina ya dawo daga farauta hankalin shi a tashe idanunshi sharkab da hawaye kuma jikinshi duk jini.
Ko da mahaifina ya ganni a cikin wannan hali sai ya janyo ni a jikinshi ya rungume a lokaci guda mu duka biyun mu ka fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya daban tausayi.
Sai da muka ɗauki tsawon lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani mahaifina ya janye jikinshi daga nawa.
Bata re da ya ce mini ƙala ba ya ɗauki wata jakar fata sai KWARI DA BAKAN shi da ke rataye a gadon bayanshi kawai sai ya kama hannuna muka fice daga cikin gidan muka nufi Kofar gari, har muka fice daga birnin muka nausa izuwa cikin daji, a kowacce rana sai nayi kuka wiwi ina mai tambayar mahaifina ina ummana ta ke. Amma sai ya lallashe ni ya kwantar min da hankali cewa ba wani abu ne ya same ta bazata dawo gare mu cikin ƙoshin lafiya.
Bakomai ya sanya mahaifina yaƙi sanar da ni labarin mahaifiyata ba, sai domin ganin cewa ni yarinya ce ƙarama bansan komai a rayuwa ba.
Sai bayan na girma ne mahaifina ya bani labarin irin zaluncin da sarki ya yi masa na mayar da ummina baiwarshi da yake saɗaka da ita, saboda al'adar sarki duk macen da ya ƙyallara idanu ya gan ta in dai har ta yi mashi to ko matar wane ne sai ya kwace ta ya aure ta ta ƙarfin tsiya.
Baƙin cikin rashin mahaifiyata shine abin da ya yi sanadin mahaifina cutar ajali ta kama shi.
A daren ranar da zai rasu ne ya mallaka mani KWARI DA BAKAN shu da dukkanin kayan farautar shi bayan ya sanar da ni dukkan sirrikan birnin Istanbul da shi kanshi sarki Ladiyas kuma ya ba ni dukkanin labarin ka ya kai Lazwar.
Tun bayan rasuwar mahaifina ne na sha alwashin ceto rayuwar mahaifiya ta daga hannun sarki Ladiyas, dare da rana ina rayuwa a cikin ƙunci da baƙin ciki, babu abin da ke ɗebe mini kewa face wannan damisa da na gada daga wajen mahaifina.
Sa'adda kyakkyawar yarinyar tazo nan a labarin ta sai ta fashe da kuka mai matuƙar tsuma zuciya da ban tausayi ga duk wanda ya ji shi.
Bisa mamaki sai sarki Lazwar ya ga wannan damisa da yarinyar ke zaune akan ta ita ma ƙwalla na zubowa daga idanuwanta.
Al'amarin da ya sanya Sarki lazwar da sauran tawagarshi suka ji sun kamu da matuƙar tausayin yarinya Shuraiba kenan shi kanshi aljani Za'aratun-layal da ya kasance aljani sai da ƙwalla ta zubo mashi saboda tausayi.
Sai daga can sarki Lazwar ya dubi yarinya Shuraiba ya ce " ya ke wannan yarinya mai abin al'ajabi haƙiƙa labarin ki cike ya ke da ban tausayi matuƙa, kuma tabbatas sarki Ladiyas ya cika baƙin AZZALUMI, ina mai ɗaukar miki alƙawarin cewa zan taimaka miki har sai na ga kin cika burin ki na saduwa da mahaifiyarki da kuma ɗaukar fansa a kan sarki Ladiyas".
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai yarinya Shuraiba ta cika da matuƙar farin ciki maral musaltuwa.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba aka kafa sansani,nan fa kuyangi suka shiga aikin dafa abin kalaci, bayan an kammala ne kowa ya kimtsa cikinshi aka huta sai aka sake ɗunguma wa aka hau bisa kan aljani Za'aratun-layal aka cigaba da tafiya tare da yarinya Shuraiba tare da damisar ta.
Ana cikin wannan tafiya ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai sai a ka ga waɗansu zaratan dakarun aljanu ɗauke da waɗansu miyagun makamai da idanu basu taɓa ganin irin su ba, gaba ɗayan su suna shirye cikin wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro, adadin su ya kai dubu ɗaya da ɗoriya.
Nan fa tawagar sarki Lazwar suka firgice, wasu daga cikin su har suna sakin fitsari a wando saboda firgici, sarki Lazwar ne kaɗai bai razana ba shi ma a matuƙar firgice ya ke, kawai dai ƙarfin hali ne da ƙi faɗi irin ta hamshaƙan sarakai.
Shi kan shi Za'aratun-layal duk da kasancewar aljani sai da ya ɗimauce, domin iya tsawon rayuwarshi ko a labari bai taɓa ganin aljanu masu kwarjini da ban tsoro tamkar su ba.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su na tsawon daƙiƙa latalin, sai daga can wani mummuna daga cikin aljanun wanda da alama shi ne shugaban su ya buɗi baki cikin wata irin kakkausar murya mai ban tsoro yace "ya ku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa ban zo gare ku tare da rundunar mayaƙa na ba domin na yaƙe ku ba sai don ku ba ni yarinya Shuraiba, mu kai ta ga sarkin mu mai girma Zammar, domin ya yanka ta ya sana'anta jininta don ya yi wa matayen mu maganin cutar da ke damun su ta makanta fiye da shekaru hamsin.
Ya ku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa matsawar ku ka yi taurin kai wajen damƙa Shuraiba a gare mu, ina mai tabbatar maku da cewa ɗayan ku ba zai ƙetare daƙiƙa goma a raye ba.
Ko da jin wannan batu daga bakin shugaban dakarun aljanun sai sarki Lazwar ya yi ƙarfin hali ya tari numfashin shi yana mai daka mashi tsawa ya dube shi ya ce " ya ke wannan ƙaramin ƙwaro tabbas ƙaryar ka ta sha ƙarya, kuma ka yi ɓatan basira da ka ke tunanin cewa za ka iya raba mu da Shuraiba.
Ina mai umartar ka da ka janye waɗannan rafkanannun mayaƙan na ka ka koma izuwa ga matsoracin sarkin ku ga faɗa mashi cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne".
Kafin sarki Lazwar ya gama rufe bakinshi jikin aljanun ya kama tsuma yana kyarma tamkar za su ci babu.
Kawai sai su ka yi wani irin ihu da kururuwa mai firgitarwa suka ɗauki kan su.
Ko da ganin hakan sai su sarki suka zare makaman su, ana haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi mai matuƙar muni ban tsoro da tashin hankali.
Kaico! haƙiƙa tashin hankali ba'a sa ma sa rana, kuma duk wanda ya taɓa fita filin yaƙi shi ne ya gama ganin tashin hankali.
Nan fa karafniyar ƙarafa gami da ihu da kururuwar dakarun aljanu da bil'adama ta cika dodon kunne, duk sa'adda makaman yaƙin ɓangarorin biyu suka haɗu sai ka ga walƙiya gami da tsawa tamkar za a ke ce da ruwan sama.
Ana fara wannan arbu ne sai wani abin mamaki ya faru domin kuwa yarinya shuraiba ta zame wa dakarun aljanun alaƙaƙai kuma ƙadangaren bakin tulu, ya zamana cewa duk wajen da ta sanya a gaba sai ka ga aljanun na zubewa ƙasa matattu.
Duk wannan artabu da ake yi tsakanin su sarki Lazwar da dakarun aljanun sarki Zammar ya gani a cikin madubin tsafin shi, a lokacin da yake zaune a fadar koda yaga cewa an kashe gaba ɗaya tawagar shi sai ya cika da matuƙar baƙin cikin maral musaltuwa kuma ya takarkare ya kurma ihu.
A ɓangaren su sarki Lazwar kuwa bayan sun samu nasarar hallaka dakarun aljanun sarki Zammar, sai kowa ya shiga sanya magani a raunukan shi, amma aƙalla anyi asarar dakarun yaƙi mutum ɗari biyu da ashirin.
Bayan komai ya samu dai-daituwa ne ba tare da wani ɓata lokaci ba sai
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment