Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

makarantar oho. Wajen la'asar ne bayan mun fito Sallah muka had'u da Sahiba.
Muna Alwala ne nace
"wai menene yake faruwa ne naga har Malamai ba'a barsu a baya wajen hada grp da alama kuma magana ce suke mai zafi"
Y'ar dariya ta yi "wai baki san me ya faru ba?,ko da yake taya zaki sani keda ba waya ce dake ba bare ki hau social Media"

"Sooyal me?"

"Social media"

"Sooyal medea"

Dariya Sahiba tayi "social media ake cewa mana Sahla kar ki bani kunya duk san koyan turancin naki kuma kin kasa fad'an wannan kalma da ba wani wuya ne da ita ba" baki na turo cikin jin haushi nace

"Ki gayamin ni abunda ya faru kawai"

"Kinji labarin ance Yarima yazo gida ganin Maimartaba ko?"

Kai na d'aga mata ina sauraran ta, ta cigaba da cewa

" toh in gaya miki wai yau ya fito shawagi gari cikin k'aramar mota shi kaɗai babu masu tsaro. yana tafiya kan titi wani ya yi irin overtaking d'innan nasa saboda yanda yake tafiya shi bai tafi ba bai kuma bari wasu sun wuce ba. Shi wai dan mai wani zai shiga gabansa yana tuki. Ina gaya miki tsakiyar titin ya faka mota ya fito ya tare titin. Gaba da baya ya hana kowa wucewa ya had'a uban go slow kan titi. Kuma ya haukan motar ya zauna yana shan taba kaman ba hakkin mutane ya shiga ba. Kinsan babu wanda ya tab'a ganinsa a waje mutane suka yi caa a kanshi zasu rufeshi da duka sai ga masu tsaron lafiyar sa. Anan ne cikin kowa ya d'uri ruwa duk wanda yake kan titin nan dana mota,mashing, kafa, keke sai daya yaci ubansa ya hana kowa wucewa masu sauri zuwa gurin aiki, majinyata da sauran mutane. Saida aka yi awa hud'u tsaye kowa yana tsoron gudun dan ance wasu shegon sojojine jajayen fata da shegun bindigo suka tsare titi kar mutum ya motsa su harbi shi. Labari yaje kunnen Maimartaba saida ya tako da kansa yazo ya lallabashi sannan yabar mutane suka shaki iska suka fara wucewa. Ya sha zagi kuwa da tsininuwa yau d'innan. Cikin k'ank'anin lokaci labari ya baza social media. Amma abinda yafi d'aukan hankalin yan media shi ne matsanancin kyau da aka ce yana dashi. Duk matan da ki ka ga suna hiran nan zancen kyansa kawai suke mata sun mutu a kansa"

Dogon numfashi ta sauke har ta bani dariya. Kai amma dai mutane sai a barsu. Yanzu su basu ga abunda ya yi ba sai kyansa kawai. Nina rasa gane mene ma abun burgewa game dashi . Ba ance ba musulmi bane?ai kome kyansa tunda baida hasken musulunci banga abun burgewa ba?. Kai Allah ya kyauta gaba d'aya sun k'ara samin tsanarsa duk da ban taɓa ganinsa ba sai labarinsa da nake ji. Kaf labaran nasa kuma babu wanda ya taɓa fad'an abun arziƙi a kansa sai sharri. Toh wai dama haka Mulkin yake ne?. Indai kuwa haka yake Allah wadai da irin wannan Mulki. Allah kuma ya tsaremu da rab'ar masu irin wannan Mulki.

Sai bayan mun tashi ne nafara fargabar komawa gida bansan abunda zan tarar ba. Jerewa mu kayi da Sahiba da wasu yan ajinmu. Ana tafe ana maida zance Ai KING AJ ya had'u su basu tab'a ganin Namiji mai kyan sa ba. Wace tsiya wace arziƙi. Harda masu cewa in dai zai so su koda bai musulunta ba da gudu zasu amince su sun tsallake sai dai na k'asa yasha kallo. Bansan sanda naja mugun tsaki ba saboda takaici su ko kishin k'asarsu da Addinin su basa yi.

"Sahla Ridwan "

Da sauri na juya inda naji sunan. Malam Halliru ne tsaye jikin gate na makaranta kaman mai jiran abu. Yau kuma me nayi da ya tare gate yana jirana. Da wuri dai nazo balle yace nayi makarar da na saba. Fuska babu walwala na k'arasa gabansa na durkusa ina gaishe shi. Ido kawai ya zubamin na wasu yan sakanni baice komai ba har na fara jin haushi. Ya titseni gaba yana kallo dan tsabar wulaƙancin. Da yasan ba wani abu zaice babya kirani. A dan fusace na d'ago zanyi magana sai idanmu suka had'u. Kasa furta masa maganan nayi dan wani irin kwarjini naji ya yi min yau. Da murya mai sanyi yace

"Baffan ki yana nan anjima bayan sallan magriba?"

Nayi saurin ce masa
"A'a baya nan yaje duba Kaka"
Haka kawai zaije gurin Baffa. Yace masa me? karo na farko kenan da yasani karya. Ido ya zubamin kaman bai yarda da abunda nace ba.

"Shikenan tashi kije"

Da sauri na tashi nayi wajen su Sahiba dake jirana ana ta gulma. Ina k'arasawa kuwa Barira ta yi suarin cewa

"Anya kuwa Sahla Malam Halliru ba sanki yake ba? Kinga kallan da yake miki kuwa?ko ba haka ku ka gani ba?"

Ta juya tana kallan su Sahiba. Gaba d'aya suka had'a baki "Walh muma dai haka muke tunani"

"Allah ya sauwake nayi Soyayya dashi. Kunsan wanda kuke magana a kai kuwa?,malam Halliru fa,mutumin dake buri yaga ya tab'a min lafiyar jiki sannan kuce wai yana sona?,wlh ko maza sun kare a duniya babu abunda zanyi da mugu Azzulumin mutum"

Fuu na wuce su dan sun masifar bani haushi. In banda ma rainin hankali malam Hallirun za suce yana sona?. Toh har muka k'arasa gida muna cece-kuce dasu. Su fad'a na fad'a kafin muyi sallama kowa ya kama gabansa. Kaman koda yaushe Baffa na zaune riƙe da charbi da littafin Addini baje a gabansa gefensa Musaddiq ne mak'otan mu. Saurayi ne da a kalla ya yi sha tara. Yana san karatu sosai duk lokacin da Baffa ya fito indai yana nan shima zaka ganshi kusa dashi yana karatu. Sai da na gaishe su sannan na shige gida cike da tarar radin abunda zan tarar d'azu nayi laifi nasan kuma Baba Lantana baza ta hak'ura ba. A soro na labe ina leke d'an sakar gidan namu dake fes yasha suminti sai shek'i yake. Babu kowa sai tukunyar awara dake yashe a k'asa an kwashe ta cikin buhu. Takarmina na cire da sand'a na shige kaman barauniya. Ina zuwa kofar d'akin mu nayi wuff na fad'a ciki ina sauke ajiyar zuciya Bilkisu dake kwance kan gado rik'e da waya ta kalleni taja mugun tsaki. Aikin kenan dai.

"Da kin bar wahalar da kan ki babu abinda zai hana Baba hukun taki cikin gidan nan. Yanzun ma ta fita ne wajen Sahura ta siyo kayan miya"

Haba shi yasa ko karfe nawa zan kai ina guje-guje nasan sai ta jirani. Ban kulata ba na ajiye jakata na cire uniform dina na ninke su na zuba cikin yar drawer mu dake d'akin. Ina k'ok'arin fitowa dan fara shirin fita da kaya waje sai ga sallamar ta. Da sauri na koma na labe a bayan kofa. Da masifar ta ta shigo.

" su mutane in basuyi san zuciya ba basu jindaɗi. Yanzu ina kayan d'ari biyar a nan. Komai sai an cuce ka kayi magana kuma a nuna anfika baki"

Haka dai kullum. Ni na rasa da Baba Lantana da Sahura wa yafi wani masifa cikin su. Gashi dai kullum suka had'u basu rabuwa lafiya amma a haka kawaye ne na kut da kut. Dama ance ai ba'a kawance sai hali yazo d'aya. Ajiyar zuciya na sauke da alama ta manta dani koma mene ya faru tsakanin su ya mantar da ita nawa Laifin dan haka da sauri na fito na fara kwashe kayan ina yin waje dasu ko kallo na bata yiba tana ta mita. Saida na gama fita da komai na dawo d'aukan awarar data gama yankawa harzuwa lokacin bata daina mita ba. Bilkisu ta fito a guje

"Baba kinga, kinga hoton Yarima. Wayyo Allah na ina san shi wlh Baba"

Nima da shigiyar gulma nayi kansu da sauri ina leka wayar. Ina so naga wanene wannan Yariman da duk inda ka wuce sai kaji anyi maganan sa. Tsabar yanda nake miƙe wuya kaman zai tsinke. Da sauri na matsa ina sosai kai dan wani rankwashi ta zubamin masu zafi a kai.

"Dan ubanki zaki wuce min daga nan ko kuwa. Ina sane dake ban manta ba. Awarar yau ta dubu uku da d'ari biyar ce. Bazan ce kar ki fasa ci ba kici kinji Allah ya baki sa'a "

Baki na zumbura na kwashi bokitin nayi waje dashi ina kunkuni. Da kallo Baffa ya bini.

"Zonan Uwata"

Gabansa na durkusa "akwai abunda yake damun ki ne ?,Lantana ta yi miki wani abu ne ban sani ba?"

Kai na girgiza masa ina murmushi "babu komai Baffa. Nida Bilkisu ne"
Dan jim ya yi "ni nasan akwai abubuwa da yawa da ki ke b'oyemin Uwata. Amma tunda kince babu komai tashi kije Allah ya yi miki Albarka ".

♥︎♥︎♥︎

Toh ina ajiye kayan kuwa maza sukayi caa a gurin kaman jira suke na fito. Babu bata lokaci na fara suya da sallaman mutane yau Imrana na taimaka min. Gab da magriba awarar tawa batafi ta d'ari biyu ba ta kare a lokacin Sai wata irin kururuwa da hayaniyar mutane ta fara doso layin namu. Zo kaga gudu ana yin inda hayaniyar ke fitowa kai mutane da gulma nima dake zaune sai d'aga wuya nake dan san ganin abunda ke faruwa. Wani irin mashin ne katon gaske baki wuluk dashi mai masifar kyau Ya shigo layin namu da wani irin gudu kaman iska. Shi kanshi wanda ke kan mashin d'in bakaken kaya ne a jikinsa har hular kwanon dake kansa. Abu d'aya ne ba baki ba kyallin sarka dake wuyansa da ya fito da ita waje. Mashin d'in ga shegen kara kaman zai fasa kunne. Tuni maza suka rud'e kaman had'in baki suka d'auka

AJ, AJ, AJ,

Ai tuni na manta da suyar awarata na tashi a guje na k'ara matsawa dan ganin wannan AJ. fuu ya wuce kaman guguwa wasu shegon motoci suka rufa masa baya. Duk wani dake kan titin saida ya sauke gefe ya bashi hanya. Zo kaga mata,yara da manya yanda ake tururuwan fitowa daga gida. Har Bilkisu sai gata a guje Tsulun kaman an wulluta. Yatsa na cize dan banga fuskar tasaba saboda hulan kwanan dake kansa mai Glass. Amma daga ganin yanayin suffarsa a mashin d'in kaga basamude mutum. NAMIJIN ZAKI.
[13/12, 10:25 am] Ashanty 💞🌙: 💎𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈💎

👑
By

Ashanty Love.
(M Afnan)


ASHANTY©AREWABOOKS.COM


✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯



BABY AK

TAWA WANNAN PAGE NAKI NE KAMAN YANDA NAYI ALKAWARI. KAR KI BAWA KOWA😂


P 5/6.


Sai da k'ura ta lafa ne bayan wucewar sa na tuna da awara ta da na bari da sauri na juya ina Addu'a Allah yasa ba'a samu wani d'an iskan ya kwashe ba. Addu'a ta kuwa bata karb'u ba dan an kwashe ragowar nan tas ko marmashi babu. Hannu na dora aka ina salallami. Ni bama abunda Baba Lantana za tamin bane ya dameni dama ragowar na ajiye zan soya mana nida Baffa sai gashi an samu wani matsiyacin yamin bakin ciki. Kai amma walh ko waye wannan wuta balbal ban yafe ba. Inda Baffa ke zaune na kalla har yanzu dai yana nan zaune kuma da alama ya ga duk wanda ya kwashe ragowar awarar nan amma bai hana ba. Amma anyi d'an akuya koma waye ya kwashe min awara. Yasan Baffa na kallan sa amma ya murje ido ya kwashe saboda baisan wani abu wai shi kunya ba. Ko da yake laifin AJ ne, shi dai duk inda yabi babu Alkhairi. Yanzu ta sanadiyar sa gashi na rasa abincin dare. Niba awarar ba kuma abincin ba.
Allah ya isa wlh ko uban me ma ya biyo dashi ta layin mu oho. Hayaniya dai bata k'are ba dan kaman an had'a dandazo ne na guggun mutane ana ta yi. Can na hango Bilkisu da k'awayen ta suna ta ihu kaman sunga Annabi. Tsaki naja marasa aikin yi kawai. Kayan na kwashe ina ta mita ni kaɗai. Zan shiga gida Baffa ya kirani na zauna kan tabarma ina zumbura baki.

"Me ya faru ki ke bata rai"

"Amma Baffa kana kallon wanda ya kwashe awarar da zan soya mana ka yi shiru baka hana ba"

"Shi ne abunda ya bata miki rai?"

Kai na d'aga ina ji kaman na fashe da kuka.
"Ta nawa ce ta rage?"nayi wuff nace "saura ta d'ari biyu Baffa "
Murmushi ya yi yana lalube cikin aljihun wandon sa ya fito da chanji d'ari biyar. Mik'o min ya yi

"Gashi ki cire kuɗin awarar sai ki riƙe chanjin ki siyi abunda ranki ke so" .

dad'i ya kamani yaushe rabo da na riƙe kuɗi nawa na kaina. Duk da cewa Baffa yana k'ok'arin wajen ganin ya biya mana bukatunmu na gida dana waje ban cika tambayar sa abu ba saboda halin rayuwa. Idan kaga na tambayi abu toh ta kama dole ne babu yanda zanyi. Sautari yana kirana ya tambaye ni ko akwai abunda nake so nace A'a sai bukatun makaranta kawai nake gaya masa. Shi yasa indai yana da d'an kuɗi zai bani y'ar dari biyar na cire d'ari biyu na ajiye sauran cikin banki.

Cas na lale kuɗin Baba Lantana na damka mata a hannu ita kanta tayi mamaki ai kuwa naga fara'a sosai kan fuskarta da kanta take min tayin abinci.

"Maza kije ga abinci can kici ki huta "

Ohh wato kuɗi shegen abu ne. Duk irin laifin da mutum zai maka idan da kuɗi mantawa ake Allah ya kyauta. Kwanon na jawo tuwon shinkafa ne miyar d'anyan kub'ewa. Duk da cewa babu komai a ciki amma biyar tayi dad'i sosai. Ka dai bar Baba Lantana da masifar ta da bala'in ta amma ta iya sarrafa abinci kaji kaman ka had'a da Kwanun ka cinye. Sai da naci nayi nak na shige d'aki na cire nayi banɗaki dan watsa ruwa. Bayan nayi salla nayi karatu nabi lafiyar gado na kwanta raina fari tass sai a lokacin Bilkisu ta shigo gidan ko daga ina take oho?. Ina jin fad'an Baffa da ya biyo bayan ta bayan ta shigo Baba Lantana na kare ta barci mai nauyi ya d'auke ni banji yarda suka yi ba.

♥︎♥︎♥︎

Yau tsawon sati d'aya kenan da zuwan AJ layin mu. Har yau da nake gayama maku maganan zuwansa bai mutu ba duk inda kaga group na samari to ana maida zancen kayan jikinsa, ko mashin d'in da yazo dashi na k'asar waje wai bekk(BIKE) ko kaji ana zancen motocin da suke binsa ance duk matakan tsaron sa ne kuma duk turawa ne. Ance..ance.. kai har na gaji dajin zancen wannan AJ wlh. Shinkafa nake gyarawa da yake yau asabar ne da wuri naje kasuwa na dawo zan dora abinci da wuri saboda yau karfe d'aya zan shiga Islamiya. A koda yaushe dai gimbiyar tana zaune gefe tana fama da waya. Baffa tun safe ya fita wasu daurin aure da ake yi a unguwar su ne kuma wakilai.

"Yauwa Sahla maza ki gama na aike ki gurin zubairu ki karb'o min mankuli zuryan, sai ki biya gurin Hamisu ki karbo wa Bilkisu d'inkin ta"

Kaman nace ita Bilkisun fa nadai fasa na amsa mata da toh. Takarmi na kawai masa na fito . Kasuwan na fara zuwa na siyo mai har zan karya hanya na biyo ta lungu nace kai bari kawai nabi titin abuna yafi sauri. Ina gabda k'ara sawa shagon Hamisu telar wani irin mahaukacin horn ya rudani na kwasa a guje na koma gefe duk da a gefen nake tafiya ashe nayi kusa da kwata sai jina nayi chab'al cikin ta. Wata irin motace mai shegen girma kaman jirgi bak'a wuluk da ita ta wuce a guje babu alamun duk wanda ke tukata zai tsaya ya bani haƙurin ya tsorata ni na fad'a kwata. A fusace na miƙe na rarimi dutse dake kusa dani katan gaske na saita motar da iya karfi na na jefa. Ina jin yanda gurin ya dauka da "ke, ke kul" ai ina tuni aikin gama ya gama cikin ikon Allah kuwa na samu glass d'in motar ta baya. Ji kake tasss

Wani irin mugun birki motar taci ta tsaya chak bata motsa ba kan titi. Wani dake gefe ne ya ce

"Innalilllahi kinsan abunda ki ka yi kuwa kinsan waye cikin motar nan?"

A fusace nace "koma uban waye, bashi da hankali zai dinga yiwa mutane irin wannan horn yana tsorata su?,yanzu dubi yanda yasa na fad'a cikin kwata da kuma asara da nayi"

Har yanzu motar na tsaye tsakiyar titi. Ita bata tafi ba,ita bata dawo ba. A fusace nayi motar ina masifa mutane na hanani.

"Kowane d'an iska ne ya fito. Saboda kuna cikin mota mai tsada ne ku ka fi karfi ku bada hakuri?. Kuɗin banza da wofi. In Allah ya yarda kafin kaje gida sai tayar motar ta lalace bama tayar kad'ai ba harda motar ita kanta sai inga ta isa da tunkaho".

Gaban motar na tsaya ina bugata da iya karfina da naga dai ba fitowa mai motar zaiyi ba na dawo bangaren direba na hau dukan glass d'inta da karfi kaman zan fasa motar dan raina ba k'aramin baci ya yi ba. Jikina gaba d'aya tun daga kuguna zuwa kafata kwata ce har diga nake. Duk wannan bai dameni ba akan man Baba Lantana da ya ke laye cikin kwatar. Babu irin kashedin da bata yimin ba akan kuɗin mannan dubu hud'u da dari bakwai cif ta bani na kwalba biyu.

K'ok'arin bode motar da naga ana yi naja baya kad'an ina jijjiga jikina. Da wani irin slow kofar ta buɗe sai kafa ta biyo baya sanye cikin wani farin cambas mai kyan gaske. Kafar kawai ya fito da ita ya ajiye waje wajen minti biyu kafin ya janyo jiki ya fito. Wani irin ingarman namiji ne ya fito ya tsaya gabana sanye cikin wasu kananan kaya rigar kaman ta sanyi mai hulan mai mad'auri ruwan toka sai wando na jeans light blue mai haske. Duk yanda naci burin d'ud'd'ura masa zagi sai na tsinci kaina da rawar jiki wani irin mugun tsoran sa ya shige ni amma na boye hakan a fuskata. Jingina ya yi da motar ya zubamin wasu tsumanmun idansa masu girman gaske da suke gasu nan su ba fari ba baki ba(grey eye's). Ikon Allah shi kuma har kala yake sawa a ido?. Ko da yake alamu sun nuna kaman bature ne. A zafafe nace

"kai wane irin mutum ne zaka tsorata mutane haka. A gefen titi nake tafiya ka yiwa mutane wani shegen horn ka tsorata su. Duk kan titin bai isheka tafiya ba sai ka had'a da gefen titi? Wlh sai ka biyani asarar da kasa nayi bazan hak'ura ba"

Maimakon ya bani haƙurin sai ya ciro wata irin taba daga aljihun wandon sa ya dora ta gefen bakin sa ya fito da wata lighter ya kyesta. Dago kai ya yi yana wani iran zukar ta na fara tari dan dad'in ta sam babu dad'i. Hannu nasa na toshe hanci ina karkade hayakin dake yowa inda nake.

"Malam ka biyani dubu hud'u da dari biyar d'ita dan walh baza kasaci bulus ba"

Motar ce ta bud'e wajen mai zaman banza wani hadedden saurayi ya fito sanye cikin manya kayan. Doguwar riga ta shadda fara da wando ta. Yana fitowa ya fad'a kalman data hausana min ciki

"AJ, what did she wants?"

Au Allah. Toh badai uwata ba walh. Nace a zuciyata. AJ. Ido na zare bayan sunan ya kara dawowa kunyar kai na nayi saurin maida hankali kan sa. Take na fara zikiri cikin zuciyata Wainnahu min suleimanu wainnahu bismillah rahmanun rahim, kalu Innalilllahi,hasbunnallahu wa ni'imal wakil.A tsorace na ja baya ganin shi gab dani . Kai wannan mutum badai tsayi ba. Kawai sai ji nayi ya fesamin tabarnan a fuska ta. Tari ya mugun sarke ni tuni tsoron nasa ya bace na hau masifa

"Allah ya isa wlh bazan yafe ba. Mugu Azzulumi "

"Ke baki da hankali kinsan dawa ki ke magana kuwa?"

"Koma waye shi ai ba Allah bane. D'an Adam duk inda yake dajara ce dashi shi kuma bai isa ya wulaƙantani ba na kyale"

Baki d'an uwan nasa ya hangame yana kallo na cikin matsanancin mamaki da Alama yaune rana ta farko da aka yi musu haka. Sai kuma ya kwashe dariya na kara tunzura zan kwaba masa bakar magana kawai naji hannunsa kan fuskata ya cafki lebena da iya karfinsa. Ji nayi kaman na saki fitsari saboda azaba dagewa nayi na gartsa masa mugun cizo da har saida na huda hannun nasa. Da sauri kuwa ya sakarmin baki yana yarfe hannu da wata irin kaukausar murya tamkar a shake (deep voice) ya yi magana.

"Fuck"

Tsabar bakin ciki hawaye suka biyo kuncina amma bakina bai mutu ba.

"Allah ya isa daka tab'a ni dan iska kawai ,kedarin banza,kedarin wofi. Ka d'auka kowama irin kane dan iska da zaka dinga tab'a mutane. Allah sai ya sakamin wlh "

yawu na tofa masa na juya fuu ina sharar hawayen bakin ciki. Har waye shi dazai tab'a ni cikin mutane salon yaja ace nima y'ar iskace irin sa. Duk inda na wuce sai an tambayeni me ya faru bani da bakin magana sai kuka har naje gida.

Da ace Sahla zata juya taga irin kallon da ya bita dashi to dah tabbas sai taji kaman ta ruga a guje tana fitsari. Kallo d'aya ya yiwa gungun jama'ar dake gurin suka fara tseren gudu tamkar wanda suka yi gamo. Zuka d'aya yawa tabar ya shanye ta ya jefar a k'asa ya take ta yana kallon bayanta tana tafiya kaman zata kifa tsabar sauri duk inda tayi ruwan kwata na binta kaman zuba mata ake. Harshen sa ya taune cikin bakin sa idansa ya yi wani irin ja ya kalli hannunsa dake digar jini.

"I will destroy you"

Ya juya a zuciye ya shige mota. D'an uwan nasa da suke tare ya yi saurin shiga motar shima dan yanda yake a fusacen nan tsaf zai iya tafiya ya barsa a gurin. Gaskiya yaga k'ok'arin yarinyar da alama bata tab'a jin labarin AJ ba tunda har tayi jarumtar cizon sa bata tsaya a nan ba harda tofa masa yawu? Gaskiya yaga k'ok'arin ta. Gashi ta janyowa kanta masifar da babu ranan karewar ta.


♥︎♥︎♥︎

"Uwata, subhanallahi me ya same ki haka?"

Ai ina jin muryar Baffa na k'ara rushewa da kuka nayi inda yake tsaye da wani. Saboda yanda bana cikin nutsuwa ta ban kula da Malam Halliru bane. Cikin damuwa ya k'ara jefamin wata tambayar.

"Me ya faru jikin ki duk kwata haka? "

Ina kuka na kwashe duk abunda ya faru na gaya masa amma ban fad'a masa ko waye ba dan nasan fad'a zansha idan yaji wancan tantirin yaron ne. Ajiyar zuciya ya sauke mai karfi.

"Shiga gida ki gyara jikin ki, zan shigo na samu Lantana "

Shigewa nayi ina sharar hawaye. Ai tana ganin shigowa ta ta rafka salati tana tafa hannu.

"Ni dama nasan sai anyi haka. Wlh wannan yarinyar da mugun hali ki ke. yanzu dan tsabar bakin ciki saida kika salwantar min da kuɗi. To ahir d'inki sai kin biyani wlh "

Ban kula taba tana ta banbami kaman zata dokeni nasan muryar Baffa da taji a kofar gida ya hanata.

"Da Allah ki matsa a kan mu mana haba, kinzo kin tsaya mana a ka da warin kwata wa ya sani ma ko kina sane kika jefa kan ki tunda ba kece da asara ba. Ai wlh Baba karki raga mata sai ta fito miki da kuɗin ki"

Ji nayi kaman na rufe su da duka gaba d'ayan su. Tana kwance kan cinyar ta tana yi mata susar kai. Wuce su nayi na shige banɗaki na barsu tana ta masifa. Har na fito bata daina banbami ba na shige d'aki. Ina sallah naji Baffa ya shigo yana mata bayanin abunda ya faru yasan halin Lantana da rashin hak'uri sai daya lale kuɗin nan ciff ya biya ta dan kafewa ta yi kuɗin sana'a ne kuma gaba d'aya dan jarin ta tattare ta bani na suyo mai dashi. Makarantar da banje ba kenan ranan na kwanta ko tsakar gidan ban fito ba sai da aka yi sallan la'asar na fito nayi alwala na d'auki abinci na dake cikin kwano na shige d'aki. Haka na wuni sungun -sungun da fargabar abunda zaije ya dawo.
[13/12, 10:25 am] Ashanty 💞🌙: 💎𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈💎

👑
By

Ashanty

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment