Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kirzufa
kuma mun san inda suke to mu tashi mutum daya masanin
kissa da tuggu mu turashi izuwa wannan Kauye da su
Muraisu suka sauka a matsayin Hamshakin dan kasuwa
domin ya yi mana leken asiri ya gano mana inda Muraisu
da mabaifiyarsa suka kwana.
Da zarar mun gano haka sai mu tashi zakwakuran
mayaka wadanda suka kware a aikin kisa suje cikin dare
kuma a cikin 6ad-da-kama su kashe Muraisu da
mabaifiyarsa, sai dai kawaia wayi gari aga gawarsu ba tare
da an san wanda ya kashesu ba.
Ka ga faruwar bakan ma za ta haddasa rashin
fahimtar juna a tsakanin jarumi Imran da su jaruma Suzaila
wadanda yake kokarin janyo ra'ayinsu su karbi addininsa.
Ka sani cewa idan suka karbi addinin Musulunci
mulkinmu ya karye."
Koda Sarki Imras yazo nan a zancensa sai Sarki
Huraisu ya bushe da dariyar farin ciki ya cc, "Ya kai
abokina hakika yanzu na dada gamsuwa cewar karfin
damtse da karfin sibiri basu kadai bane abubuwan da suke
kai mutum izuwa nasara ba.
Tunani, hange da basira sune akan gaba.
Tabbas zamu gaggauta amfani da wannan shawara
ka amma dola nc na za6o gawurtaccen jarumi wanda zan
d ya yi wannan aiki saboda koda asirinsa ya tonu ya
ZAmana cewa zai iya kare kansa".
Haka dai Sarki Imras da Sarki Huraisu suka ci gaba
da tattaunawa bisa wannan matsala har izuwa lokaci mai
tsawo sannan suka yi sallama aka kai Sarki Huraisu izuwa
masaukin sa.
a can suka
tattaunawa a tsakaninsu sai
aka rabu akan cewa gobe da safe za'a dugunzuma a tafi
izuwa can bakin kogi da ke karshen gari domin a yaki
wannan katuwar masifaffiyar Kada wacce ta hana mutunen
Kauyen gabatar da sana'ar kamun kifi.
Nan take aka
masaukinsu.
Kauyen kuwa bayan su
jarumi Imran Sun gama
aka kai Muraisu da mahaifiyarsa
Jaruma Suzaila da tawagarta ma sai aka basu nasu
masaukin dabam, shi kuwa jarumi Imran shi kadai aka
bashi masauki a wani gida da ke makwabtaka da shugaban
Kauyen.
Lokacin da jarumi Muraisu da mahaifiyarsa Husnaila
suka shiga cikin nasu masaukin suka kwanta domin suyi
barci sai barcin ya gagara domin domin kowannen su
Zuciyarsa a cike take da tunani gami da wasi- wasin anya
burinsu na ganin abokan gabarsu zai cika?".
Koda Husnaila ta fahimci cewar duk su biyun suna
cikin damuwa ne iri daya sai ta dubcshi ta ce, "Ya kai dana
na san duk abin da yake damunka, kana tunani ne akan
yadda za mu sami nasarar ganin bayan abokan gabnmu.
Shin kamanta da duk shirin da mukayi a baya?" Na
gaya maka cewa abu na farko da zamu yi shi ne mu tura a
Sato mana wannan kwalbar sihiri wacce wannan gashi ke
ciki a wajcn Sarki Huraisu tun da indai muka mallaki
gashin ni na san hanyar da zamu bi mu dawo da sihirin da
ke jikin kahon BUSA A MUTU, dana dajin Kirzufa."
Koda jin wannan batu sai Muraisu ya dubi Husnaila
cikin alamun tsananin damuwa ya ce, "Ya ke Ummina
yanzu ta ya ya Zamu iya zuwa mu sato wannan gashin sihiri
albalin gashi muna tare da jarumi Imran kuma kin san cewa
ba zai taba yarda ba dayanmu ya tafi wani wajen ba?".
Da jin wannan tambaya sai Husnaila ta yi murmushi
ta ce, "Ya dana kayi sani cewa babu abinda kudi ba zai siya ba.
AA Misau ke Magana
A can
Birnin Lairuf akwai wani
mutum dana sani wanda
ake kira da suna Zaitar
ibini Mazwan wanda ya kasance shahararen barawo wanda
yake yin sata ta ban al'ajabi.
ba.
Duk satar da zai yi in dai ba zai samu kudi sama da
Dinare dubu dari ba, ba ya yin ta.
Kuma a tarihin sana'arsa bai taba samun bacin rana
A can gidan sarautar Birnin Lairuf na san wurare uku
inda Sarki ya ke ajiyar dukiyarsa kuma ni kadaice na san
Sirrin yadda za'a iya bude inda kudin suke a đebo minsu.
Zan tura a kirawo Zaitar Ibn Mazwan na bashi
kwangilar sato mini wan can gashin sihiri a gidan sarautar
Sarki Muraisu bisa sharadin biyansa lada guda biyu
Lada na farko kafin ya yI aiknsa zan sanar dashi dala
misan tsafin da zai karanta ya bude ma'adanar farko va
debo dukiya wacce adadinta ya kai Dinare dubu dari uku.
Bayan yaje ya kawo mana kwalbar dake dauke da
gashin sihiri zan gaya masa dalamisan isafin da zai karanta
ya bude ma'adana ta biyu wacce ke dauke da Dinare dubu
dari shida. "
Koda jin wannan batu sai Muraisu ya cika da tsananin
mamaki da farin ciki ya ce, "Hakika kin zo mana da
shawara mai kyau to amma yanzU Wa za ki tasa ki aike shi
izuwa Birnin Lairuf don ya kirawo miki Sarkin barayi
Zaltar Ibn Mazwar kuma shin kina da ladan da za ki iyar
biyan manzon da zai je ya isar miki da sakonki ga shi
Zaitar din?".
Da jin wadannan tambayoyi guda biyu sai Husnaila ta
yi murmushi ta ce, "Kada ka damu ya kai dana ai
shckaruna a duniya ba za su tashi a banza ba, kuna
amfanin ilimi da hankali aiki da su.
Yanzun nan za ka ga aiki da cikawa don masu iya
magana sun ce, "Da zafi - zafi akan bugi karfe'"
Koda gama fadin hakan sai Husnaila take ta bude
wata tsohuwar Akwatunta ta karfe waccec tun kan Muraisu
ya girma take ajiye da ita a cikin dajin Kirzufa ta dauko
kudi kimanin Dinare ashirin, ragowar Dinaren da ke cikn
Akwatin kuwa ya kai dubu uku.
Nan take ta daure wannan Dinare asbirin a cikin
tsumma sannan kuma sai ta dauko alkalami, Tawada da
takarda ta rubuta wasika.
Bayan ta gama rubuta wasikar ta nannadeta sai ta
mike tsaye ta dubi Muraisu ta ce, "Ka jirani zan je gidan
shugaban Mutanan Kauyen nan na dawo.
Ko kala Muraisu bai ce da ita ya bita da kallo kawai.
Lokacin da Husnaila ta isa gidan shugaban Kauyen ta
sami ganawa da shi, sai ta ce da shi tana bukatar manzo
wanda zai kai ma ta wasika izuwa Birnin Lairuf cikin abin
da bai wuce kwana uku ba,"
Da jin haka sai shugaban ya yi ajiyar numfashi ya ce,
"Tabbas ina da wani zakwakurin bawa wanda zai iya yi
miki wannan aiki, amma dole ne ki biyashi ladan kudi a
kalla Dinare goma sha biyar."
Koda jin haka sai Husnaila ta yi murmushi ta ce, "Zan
iya bashi Dinare ashirin ma amma ina son ka tabbatar mini
da gaskiyarsa da amanarsa".
Shugaban ya ce, "Ai tun kafin ma addinin Musulunci
ya zo mana wannan bawa nawa ya sami shaidar gaskiya
akan aikinsa a wajan gaba dayan mutanen garin nan.
Sama da shekaru arba'in yana wannan sana'a ta kai
sakonni izuwa birane da kauyuka ba'a taba samunsa da
ha'inci ba".
Da jin haka sai hankalin Husnaila ya kwanta, nan take
ta fiddo wannan Dinare guda ashirin gami da wannan
wasika ta mikawa shugaban Kauycn tà ce, "Gashi ka
Kirawo wannan bawa naka ka bashi wannan sak0 amma
akwai bukatar na gana da wannan manzO".
Shugaban ya ce, "Ai wannan mai sauki ne".
Nan take shugaban ya kwalawa wani bawansa kira ya
shigo cikin harabar gidan ya dubeshi ya ce, "Ma za ka je ka
kirawo mini Ashtar manzon sako.
AA Misau ke Magana
Bawan ya risina ya ce, "An gana ya shupabana"
Nan take bawan ya fita da gudu ya tafi cika umarni
Jim kadan kuwa sai ga Ashtar manzon sako ya iso
Da zuwansa sai ya yi sallama.
Shugaban ya amsa masa sallamar sannan ya shigo
cikin harabar gidan ya iske Husnaila tare da shugaba a
Zaune.
Cikin ladabi manzo Ashtar ya isina ya kwashi
gaisuwa sannan ya zauna a gefe guda.
Nan take shugaba ya dubi Ashtar ya ce, "Wannan ita
ce Husnaila matar marigayi Sarki Muraisu na Birnin
Lairuf
Yanzu za ta ba ka sako izuwa Birnin Lairuf kuma
zata biyaka ladan aiki".
Koda gama fadin hakan sai shugaban ya mike tsaye
ya basu wuri.
Nan take Husnaila ta mikawa Ashtar kudi da wasika
ta dubeshi ta ce, "Ga ladan aikinka Dinare goma, wannan
wasika kuma idan ka isa Birnin Lairuf sai ka nemi Zaltar
ibini Mazwan ka bashi".
Sa'adda Ashtar yaji wannan batu sai ya yi dan jimn
yana tunani cikin alamun 'yar damuwa.
Ilusnaila ta dubeshi ta ce, "Lafiya, tunanin me ka ke
yi haka? Ko kana gantn cewa ba za ka iya wannan aiki
bane?"
Ashtar ya yi murIushi ya cc, "Ai gabatar da wannan
aiki mai sauki ne a gareni tamkar Cire silin gashi ne daga
cikin tandun mai.
Kawai inda matsalar take shi nc, wannan mutum da
kika aikeni wajensa barawo ne shahararre kuma gagararre.
A matsayina na ma'aboci addinin Musulunci a yanzu
laifi ne na taimaki mai laifi ya sami nasarar cutar da wani."
Koda jin wannan batu sai Ilusnaila ta yi murmushi ta
ce, "Kada ka damu ai ba dukiya na umarceshi da satowa ba,
rantse da darajar iyaycna abinda zai samo min ko dinare
daya ba za a iya siyansa ba domin wani silin gashi ne guda
dava na kan bil'adama, kuma ni da dana kadai gashin zai
yiwa amfani".
Koda jin wannan batu sai hankalin manzo Ashtar ya
kwanta.
Nan take ya karoi sakon Ilusnaila sannan ya yi ma ta
alkawarin cewar lallai a cikin abinda bai wuce kwana uku
ba zai dawo.
Ba tare da bata wani lokaci ba Ashtar ya yiwa
Husnaila sallama ya tafi, itama sai ta yiwa shugaban
Kauyen sallama ta nufi masaukinta.
Lokacin da Husnaila ta iso masaukin na ta sai ta iske
jarumi Imran tsaye a kofar gidan da aka saukcsu fuskarsaa
murtuke babu alamar annuri.
Nan take taji zuciyarta ta buga da karfi, tsoro ya
dabaibayeta saboda kwarjininsa.
Cikin alamun ashin gaskiya lHusnaila ta karaso kusa
da jaruni Imran ta tsaya tana mai sunkui da kanta kas.
Shi kuma sai ya dubeta cikin biyayya da girmamawa
ya ce, "Ya ke Ummul Muraisu kin sani cewa rayuwarku a
cikin hadarí take ke da danki saboda me kuma za ki dinga
fitowa daga cikin masaukinku kina yawo a cikin garin nan?
Hakkina ne na kula da lafiyarku da rayuwarku a
yanzu tunda ni ne na baroku da inda babu wanda ya isa
yaje har can ya cutar da ku.
Ki sani cewa tun dazu ina biye da ke na ga saadda
kika fito daga cikin wannan gida da aka saukeku har kika
isa gidan mai garin nan.
Bani da sha'awar sanin abinda ya kaiki can, amma
hakkina ne na san duk inda za ku je ke da danki a ko
yaushe, don haka in dai kuna bukatar za ku je wani wuri to
ku fara sanar da ni".
Lokacin da jarumi Imran ya zo nan a jawabinsa sai
lHusnaila ta dubcshi cikin alamun nadama bisa abinda ta
aikata ta ce, "Ka gafarceni ya kai wannan jarumi mai ban
al'ajabi, ka yi sani cewa daga yanzu duk inda zamu je ni da
dana sai mun sanar da kai".
Koda jin haka sai jarumi Imran ya yi ma ta guntun
murmushi ya ce, "Shi kenan, kOmai ya wuce sai da safe",
Yana gama fadin hakan sai ya yi tafiyarsa ya nufi
nasa masaukin, amma yana waige-waige da kalle-kalle don
tabbatar da tsaro.
Dama kuma tun kafin akai kowa masaukinsa sai da ya
sa shugaban Kauyen ya samo dakaru aka baza su suka
kewaye gidajen da aka saukesu don tabbatar da tsaro don
kada mekiyan su Muraisu su kawo harin sumame ba a sani
ba.
Kai hatta gidan da aka ajiye Muraisu da mahaifiyarsa
a ciki sai da jarumi Imran ya karanta addu'o'in tsari a
cikinsa ya tofa a gabas da yamma, kudu da arewa.
Wannun shi ne abinda ya faru a can Kauyen
jarumi lmran suka sauka.
AA Misau ke
A can Birnin Hutaira kuwa, kashe gari da
sassafe Sarki Imras ya sa aka yi masa
iso a wajen Sarki Huraisu.
Bayan sun gaisa sai Sarki Imras ya dubeshi ya ce,
"Ina labarin Bafataken da za mu tura izuwa Kauyen da su
Muraisu suka sauka, shin ka samo wanda ya dace ya yi
wannan aiki?"
Koda jin wannan tambaya sai Sarki Huraisu ya yi
murmushi ya ce, "Ai tun a darcn jiya na gama shirya
komai. Yanzu haka ina tare da wanda zai yi mana wannarn
aiki."
Yana gama fadin hakan sai ya tafa hannayensa sau
uku, kawai sai Sarki Imras ya ga wani dogon mutum
ma'abocin kwarjini ya fito daga cikin wani daki.
Kallo daya mutunn zai yi masa ya gane cewa Attajiri
ne kuma sadauki ne saboda yanayin tufafin da yake sanye
da su da kuma yanayin siflar jikinsa ta sadaukai.
Mutumin ya risina ya gaishe da Sarki Imras ya kame
kamar gunki.
Shekarun mutumin ba ra su yi kasa da arba'in ba.
Sarki huraisu ya gabatar dt mutumin ga Sarki Imras
ya co, "Wannan shi ne attajiri AMLAS IBINI BALMARU
Kwararre ne shi a iya kasuwanci. Gwani ne shi a iya
batar da kama kuma kasurgumi ne akan yaudara da cin
amana. Tabbas Amlas ne kadai zai iya aiwatar da wannan
aiki da muke bukata komai irin tsaron da za a sa a wannan
Kauye sai ya san hanuyar da yabi ya gano a
inda Muraisu da mahaifiyarsa Husnaila suke kwana.
Nan take Sarki IHuraisu ya kawo dinare dubu arba'in
va baiwa Attajiri Amlas a matsayin guzurinsa na wannan
tafiya da zai yi sannan aka yi masa alkawarin ninki uku na
abinda aka bashi idan ya cika aikin nasa bida yadda aka
umarceshi cikin nasara."
Cikin tsananin murna Amlas ya karbi wannan
dirhami dubu arba'in yana ta godiya sannan ya yiwa Sarki
Huraisu sallama ya tafi.
Fitarsa ke da wuya daga cikin turakar sai Sarki Imras
yai ajiyar numfashi cikin murna ya ce, "Sai yanzu
hankalina ya kwanta.
Amma tsawon wane lokaci kake ganin cewa attajiri
Amlas zai iya kammala wannan aiki domin mu tura
Dakarun da za su kashe abokan gabar tamu akan lokaci?"
Sarki I luraisu ya ce, "Zai isa can Kauycn a cikin
kwana hudu kuma ya yi alkawarin kammala aikin a cikin
kwana goma sha hudu, wato mako biyu kacal. Ka ga ke
nan a cikin kwanaki goma sha takwas kacal zai gama".
Da jin wannan batu sai Sarki Imras ya bushe da
dariyar farin ciki har yana faduwa kasa daga kan kujerar da
yake zaune saboda murna.
Shima Sarki Huraisu sai ya tayashi yin dariyar har sai
da dariyar ta gundurcsu sannan suka daina. Lokaci guda
kunna sai Sarki Imras ya fashe da kukan bakin ciki har da
hawaye
Al'amarin da yai matukar girgiza Sarki Huraisu ke
nan ya cika da tsananin mamaki ya dubeshi ya ce, "Ya kai
abokina ina dalilin zubar wannan hawaye na ka?"
Surki Imras ya cc, "Ya kai abokina ka yi sani cewa ba
wani abu bane ya saņi wannan kuka ba face tsananin
takaici bisa yadda har yanzu bamu sami nutsuwa ba ta jin
dadin Daular Mulkin da muke kai bayan bakar wahalar da
muka sha ta neman duniya tunda bamu da kwanciyar
hankali sakamakon fargabar abokan gaba.
Yanzu dai ka ga ni sai da na shafe sama da shekara
goma a cikin daji tare da DAKARUN TAWAYE muna
shirya yadda zamu yiwa dan uwana Sarki Muraisu juyin
mulki amma abu ya gagara har sai da na hada kaj da kai.
Ina ji ina gani muka kashe dan uwan nawa wanda
muka kasance jini daya ni da shi kuma shí kadai ya rage
mini a duniya don dai kawai na sami wannan duniya.
Ga shi na sami duniyar amma ina ji ina gani zama
akan karagar mulkin ya gagareni.
To wai shin yaushe ne zan sami wannan kwanciyar
hankali har dukkan tsoro da fargaba su kau duga cikin
zuciyata?"
Koda Sarki huraisu yaz0 nan a zancensa sai shima
Sarki Imras idanunsa suka ciko da kwallah ya ce, "Ai duk
irin ciwonmu daya.
Ka tuna cewa fa nima akan na sami wannan duniya
Ne na hana 'yar uwata yin aure alhalin babu wata mace mai
kyanta a gaba daya wannan Nahiya, amman kuma har gobe ana farautar rayuw:rta duk da cewar ita ce kadai sauran
dangina jinina a doron kasa.
Hakika yanzu ne na tabbatar da cewa dukiya da
mulki su ne babbar masifa ga bil'adama, domin a kansu
babu abinda mutum ba zai iya aikatawa ba.
Ni kaina AA Misau Akan neman Dukiya ne Yasa zan dakata anan naje nemansu
Mai Magana Ko Kuma Nace Naku Akullum
Admin AA Misau ke Magana
WhatsApp group
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q
Facebook page
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063661782295BUSA A MUTU 💕
Littafi Na Bakwai (7)🩸
Part C💎
Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴
Typing by AA Misau ke Magana
✍️⭐⭐⭐
( kuciGaba dayi mana likes and comments domin Samun cigabansu akan lokaci)
MULKI SU NE BABBAR MASIFA GA BIL'ADAMA, DOMIN A KANSU
BABU ABINDA MUTUM BA ZAI IYA AIKATAWA BA.
Ai kuwa yadda zuciyoyin nan namu suka kekashe
ban ga abinda zai sa mu ja da baya ba ko mu ji tsoro bisa
ida nufinmu".
Sarki huraisu ya ce, "Kwarai kuwa! Koda kuwa sama
da kasa za su hade sai mun cimma burinmu.
lokacin
da manzo Ashtar ya iso
Birnin Lairuf bai zame ko ina
ba sai kasuwa.
Dama a wannan lokaci ya jagoranci wata tawaga ne ta
Fatake wadanda adadinsu ya kai mutum dubu biyu suna
janye da rakuma sama da guda dubu uku tare da dakarunsu
masu bada tsaro.
Bayan wannan tawaga ta sauka a kasuwa kowa ya
ncmi hanyar gidan da zai kwana, sai manz0 Ashtar ya kira
mai kula da gidan da ya sauka ya dubeshi ya ce, "Samari
ina da tambaya. Shin, ko ka san gidan Zaitar ibini
Mazwar?"
Koda jin wannan tambaya sai saurayin ya guntse
bakinsa da hannayensa biyu ya dubi Ashtar cikin álarmun
Tsoro ya ce"Ya shugabana akan wane dalili kake neman
mutumin da ya zama tamkar dodo a garin nan?
Ka sani cewa Zaltar ibini Mazwar baya harka da
kowa face manyan Sarakai da manyan Attajirai wadanda
suka mallaki dukiya ta gaban kwatance.
Ina mai tabbatar maka da cewa baka da abinda Sarkin
barayi Zaltar zai saurarcka".
Koda jin wannan batu sai manzo Ashtar ya yi
murmushi ya ce, "Na san cewa ni bani da kudin da zan iya
hulda da Zaltar, amma idan har na yi arba da shi na mịka
sakon da aka bani a hannunsa dole ne ya karbeni hannu
biyu kuma ya yi hulda da ni.
Ni kawai abinda nake da bukata shi ne ka rakani
gidan Zaltar domin na gana da shi".
Koda jin wannan batu sai mai kula da gidan ya kama
noke-noke yana kokarin ya yi tafiyarsa.
Nan take Ashtar ya zura hannu a cikin aljihunsa ya
dauko dinare biyu ya mika masa ya ce, "Ka rakani inda
nake bukata yanzu".
Jikin mai kula da gidan na rawa ya karbi wannan
kudi ya ce, "Mu je zuwa Mahaukaci ya hau Kura".
Nan take Ashtar ya fice mike tsaye ya bi yaron gidan suka
Suna fita suka kulle kofar gidan sannan suka kama
hanya suka yi ta tafiya har suka iso cikin gari.
A sannan ne Ashtar ya ga sun fara wata sabuwar
tafiyar.
Su kutsa nan su fita can, sai da suka shafe kusan rabin
saa suna tafiya kamar ba za su je inda suka dosa ba, sannan
suka iso Karshen gari inda suka yi kicibus da wani
dankareren gida wanda in banda gidan sarautar garin ba
wani gida wanda ya fi shi kyau da kawatuwa.
Daga nesa kadan da gidan dan rakiyar ya coge ya
Dubi Asbtar ya ce, "To ni fa nan ne iyakata, don haka kai
sai ka karasa.
Lan jira ka anan idan ka dawo a raye sai mu koma
cikin gari tare."
AA Misau ke Magana
Lokacin da Ashtar yaji wannan batu, sai nan ta ke
shima tsoro ya baibayeshi, zuciyarsa ta buga da karfi.
musamman da yaji dan rakiyar tasa ya ce sai ya dawo a
raye sannan za su koma tare.
Amma da ya tuna tafiyar da ya shafe a baya mai
hadari ya iso nan Birnin Lairuf sai ya ga ai duk irin hadarin
da zai fuskanta yanzu mai sauki ne tunda dai ga shi ya iso
inda zai bayar da sakon.
Nan take Ashtar ya yi kundumbala ya durfafi wannan
kerarren gida wanda sama da Dakaru dubu ke kewaye da
shi suke gadi.
Tun kafin Ashtar ya karasa daf da kofar gidan,
Dakaru kimanin mutum đari uku suka rugo da gudu izuwa
gareshi suka yi masa kawanya suna masu zare makamai.
Kawai sai daya daga cikin Dakarun ya dubi Ashtar ya
ce, "Wane ne kai kuma mene ne ya kawoka nan gidan mai
girma Zal tar?"
Maimakon Ashtar ya budi baki ya bayar da amsar
tambayoyin da aka yi masa sai kawai ya zaro wannan
wasika wacce Husnaila ta bashi, ya mikawa wanda ya yi
masa tambayoyin ya ce, "Ka kaiwa maigidanku wannan
wasika zai gane ko ni waye, kuma zai san daga inda na
fito,"
Mai tambayar ya karbi wasikar ba tare da wata
gardama ba sannan ya juya ya nufi wannan gida ya bar
ragowar yan uwansa zagaye da Ashtar din suna muzurai,
kawai jira suke su ga Ashtar ya yi wani yunkuri na rashin
gaskiya su afka masa su hallakashi.
Bayan kamar shudewar dakiku dari uku da tamanin
da tafiyar wannan badakare sai gashi ya
dawo fuskarsa cike da annuri ya dubi Ashtar ya ce
"Maigidana yana yi maka barka da zuwa, kuma ya ce na yi
maka jagora 1zuwa gareshi".
Nan take dakarun da suka yiwa Ashtar kawanya suka
Ja da baya suka bude masa hanya ya bi wanann Badakare a bayaa suka durfafi wannan kerarren gida.
Koda suka iso kofar gidan aka bude musu suka shiga
sai Ashtar ya zamo cikakken dan Kauye ya kama kalle-
kalle saboda a iya yawon duniyar da ya yi a rayuwarsa bai
taba ganin gidan da aka kawatashi ba kamar wannan.
Duk inda suka gifta baya ganin komai face kyawawan
kuyangi, furanni da kayan ado iri-iri, wadansu sun isa su
yayewa mutum duk irin bakin cikin da yake ciki a rayuwa.
Sai da suka wuce manyan fadoji guda shida sannan
suka iso fadar Karshe ta bakwai wacce Sarkin 6arayi Zaltar
yake zaunc bisa wata kujerar mulki ta alfarma.
Hadimai maza da mata sun kewayeshi tamkar wani
Serki.
Koda shigowar Ashtar cikin wannan fada sai Zaltar
ya mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune cikin
matukar farin ciki ya taryeshi yana mai rike hannayensa
Karmar wanda ya sadu da dan uwansa wanda suka dade
bass hadu ba.
Zatar ya ja Ashtar har izuwa kan kujerarsa suka
tare
yana yi masa lale marhaban
Zamansu ke da wuya aka kawo muSu abinci da abin sha
suka ci suka yí hani'an, kai ka ce dama sun dade da sanin
Juna.
Bayan sun kanmala cin abincin sun nutsu sai Zaltar
Ya dubi Ashtar ya ce, "Ya kai wannan bakon
alheri ka yi sani cewa ban taba yin farin ciki ba irin na yau
saboda muhimmnancin wannan sako da ka kawo mini
domin kuwa sako ne wanda na dade ina jiransa tsawon
shekara da shekaru.
Yanzu zan sa a kaika masaukinka ka kwanta ka huce
gajiyar taliya in ya so gobe da safe sai na sallameka ka
koma izuwa Kauyen da ka baro mai girma Husnaila."
Nan take Zaltar ya sa aka tafi da Ashtar izuwa
masaukinsa inda aka shigar da shi cikin wani kasaitaccen
daki mai dauke da luntsumcmen gado.
Akan gadon a kwakkwance wadansu kyawawan
kuyangi ne su shida sun ci ado suna ta faman kamshi.
Koda Ashtar ya yi arba da wadannan kyawawan
kuyangi sai ya daka tsalle ya fada tsakiyarsu ya yi
kwanciyarsa, su kuwa suka shiga yi masa tausa kai ka ce
shi ne maigidan.
Kashe gari kuwa da safe Sarkin barayi Zaltar ya kawo
amsar wasika ya bai wa Ashtar sannan ya bashi tukuici na
dinare dubu goma kuma ya hadashi da Dakaru hamsin ya
ce su yi masa rakiya har izuwa Birnin Lairuf don tabbatar
da cewa ya isa gida lafiya saboda kasancewar babu fatake
abokan tafiya da za su koma tare da shi tunda ba su
kammala harkokin kasuwancin su ba.
Farin ciki a wajen Ashtar a wannan rana ba zai
misaltu ba domin a iya rayuwarsa ta duniya bai taba
mallakar dinare dubu daya ba ma nasa na kansa, amma yau
gashi shi ne da dinarc dubu goma nasa na kansa.
Wannan shỉ ne abinda ya faru a Birmin Lairuf bayan
manzo Ashtar ya sadu da Sarkin barayi Zaltar ibini
Mazwar.
A can Kauyen da su jarumi Imran
suke kuwa, lokacin da gari
ya waye sai kofar gidan
maigari ta cika makil da jama'a saboda murna da đokin
gagarumin aikin da za a fita a yau na zuwa bakin kogi
domin a kawar da wannan katuwar Kada wacce ta hana yin
sana'ar su a garin.
A wannan lokaci ne jarumi Imran, Suzaila, Muraisu
da Husnaila tare da Dakarun Gimbiya Suzaila suka fito a
cikin gagarumar shigar yaki kowannensu na rike da
makamai.
Kawai sai jarumi Imran ya dubi shugaban Kauyen
wato maigari ya ce, "To mu zamu tafi izuwa can bayan gari
inda kogi yake domin kawar muku da wannan muguwar
Kada wacce ta hanaku yin su.
Abinda nake bukata da ku shi ne, ku tayamu addu'a
Allah ya bamu sa'a akan wannan Kada".
Koda jin haka sai gaba dayan mutanen Kauyen suka
yi kabbara da karfi, Imran da Lushaira ma sai suka yi
Koda hasnalu da Muraisu suka ji Lushaira ma tayi
kabbara sai suka cika da tsananin mamaki suka kura ma ta
Idanu domin su dai a saninsu basu san lokacin da ta
musulunta ba don haka akan wane dalili za ta yi wannan
kabbara?"
AA Misau ke Magana
Koda Lushaira ta fabimci cewar tayi subud-da-baka
ta tonawa kanta asiri sai ta sunkui da kanta kas tana
basarwa.
Ba tare da 6ata wani lokaci ba jarumi Imnran ya dubi
Maigari ya ce, "Kada wanda ya ce zai biyomu a baya don
ya ga irin gumurzun da zamu yi da wannan Kada. Mu
kanmu bamu da tabbacin zamu sami nasarar hallaka
wannan Kada sai abin da Allah Ya zaryar, don haka idan
kunne yaji to gangar jiki ta tsira.
Yanzu zamu tafi da zarar kun jiyo bushin kaho daga
can bakin kogi to mun sami nasarar, idan kuwa kuka ji
shiru mun hallaka."
Koda gama fadin hakan sai jarumi Imran ya juya ya
wuce kan gaba izuwa hanyar da ta nufi kogi, suma sauran
jaruman da abokan tafiyarsa sai suka bishi duu! a baya aka
bar gaba dayan mutanen Kauyen a tsaitsaye tare da maigari
a kofar gidansa suna masu binsu da kallo.
Da yake Lushaira na biye da jarumi Imran daf da daf
sai ya faki idanun kowa ya rada ma ta addu'ar da za ta
dinga karantawa a ranta don kariya ba tare da kowa ya ji
ba.
Sai da suka shafe kusan sa'a daya da rabi suna tafiya
sannan suka iso bakin wannan kogi sannan suka tsaya suka
yi cirko-cirko suna kallon kogin kawai a

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

1 Comments On BUSA A MUTU Book 7
avatar
walid

9 months ago

Reply

Is so sweet

Please Login or Register in order to submit comment