Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*

🔥BAJININA BACE🔥
2021
NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI


MAMAN ISLAM






Bismillah Rahmanir Rahim Allah kayi dad in tsira da aminci ga shugabanmu jagaba fiyayye annabi muhammadu S A W tareda dukan ahalin gidan sa da sa habbansa baki d'aya




Wannan shafin naku ne JININA ABDU WAHAB ABDULAZIZ
TARE DA
ADAMU ABDULAZIZ
Ina matuk'ar farin cikin tayaku murnan k'aruwan yara maza da kukayi Ahmad Adam da muhamma Sani Abdul WAHAB Allah ya albarkaci rayuwar su yasa cikon addinin musluncine Amin


Page 1

"Ke Maryam naji wata ’yar matashiyar budurwa tana kira cikin muryar rad'a" da sauri naga yarinyar da aka kira da Maryam ta waigo fatabarakallahu asanulkalik'in shine abinda na fad'a lokacin da idanuna suka arba da zankad'ed'iyar kuma matashiyar budurwar aka kira da MARYAM wani shegen murmushi tasaki tace "ba saikin fad'aba Halima nasan abinda yasa kike wannan kiran sai kace makauniya' a d'an dame Halima tace "kinsan halin wannan bros d'in nakifa baida mutunci yanzun saiya b'ata mana shiri"




Wani d'an iskan kallo Maryam ta sakarwa Halima tace "ke ya dama ni kam banga wanda ya isa hanani abinda naga damar yiba uwata da ubana basu ta kuraniba sai wani can daban, kinga malama aje acigaba da shirya wajen ayi yadda zamufita kunyar abokanmu"




kai kawai Halima ta jinjina batare da ta ce komai ba domin tasan halin Maryam da shegen taurin kai idan ta kafe akan abu babu wanda ya isa ya juyata sai YAYA MUHAMMAD daya daneta ya shanye a taurin kai gashi bala e en sojan dana k'asansa suke masifar tsoronsa gashi miskili ne shi na gaban kwantace inba ta k'ureba zai wuya kajishi yana yawan magana hatta abokansa da abokan aikinsa sun saba da halinsa sau tari da ido yake basu umarnin abinda zasuyi kuma su aikata domin sun riga sun saba da halinsa.




Ta juya kenan zata gidan su anwar wani mate d'inta ne yayansu yana d'inki to duk kayan da zata buk'ata shi tabama d'inkinsu, saiga Nasser ya k'araso da gudu yace "Adda Maryam kizo inji Ammyna" wata shegiyar harara ta galla masa tace "kaje kace tazo tajani bazan zoba inkuma zata iya tazo tajani"



Shima hararan ya maida mata dan babu ragayya a tsakaninsu ko kad'an yace "kada Allah yasa kizo d'in banza wacce batasan darajan nagaba da itaba"



Cikin b'acin rai tayi Kansa tace kai dan uwarka ni kake zagi?"
"Anzage kin ni uwata sa ar wasanki ce da zaki zauna kina aikena da wannan banzayen zantukan?"



Kansa tayi da nufin mammake shi ya d'ebi sauri tabishi tana cigaba da gaya masa bak'ak'en maganganu akan mahaifiyar sa, shi kuma koda wasa bai saurara mata ba duk zagin data masa Sai ya maida mata martani acewar sa tunda ita Allah baiyota da ruwan mutunci ba baiga dalilin da zaisa ya kyaleta ba.




Yana bud'e get ya hango bros wani shu'umin mirmushi ya saki sannan ya tak'ark'are ya zunduma wani uban ihu har Sai da bros ya to she kunnensa ya juyo afirgice dan jin wannan ihun tayi zaton kunama ne ya d'alleshi ganin shi yai yana nufoshi yana cigaba da kukansa wata uwar harara ya maka masa wadda tasa nan take ya had'iye kukan ya k'araso kusa dashi, da ido yake tambayar shi abinda akayi masa yace





"Ba Adda Maryam bane kawai dan Ammyna tace na kirata shine ta hau zaginmu nida Ammeyn danna ce badai Ammeyna ba shine ta mareni kuma ta biyoni wai zataje gaban uwar tawa ta takamin kai taga inda abinda ta isa tayi"




Kafin yace wani abu saiga maryam d'in ta shigo a fusace kuma har lokacin bata bar fad'ar bak'ak'en maganganun da take fad'awa Nassar ba, abinda ya dad'a b'ata ran bros kenan yayi mata wani mugun kallo wanda sam bata kula daahi ba Sai da tashigo tsakiyar gidan itama had'e rai tayi ta bala in d'auke kai tai kamar batasan da zaman su awajen ba.



.
"Ke zo nan" ya fad'a cikin dakakkiyar muryarshi da babu alamun wasa aciki had'e rai tayi tare da kuma galla masa harara sannan ta saki tsaki tayi cikin gidan abinda yai masifar k'ona masa rai kenan ya kama hannun Nassar suka nufeta ai tana ganin ya nufota ta taka aguje tayi ciki' mamanta da Ammey suna zaune afalon suna d'an tab'a hirar su dake babu laifi basu cika fad'a da junansu ba saboda hak'urin haj. Amina da kuma tsantsar biyayyar da take wa abokiyar zamanta haj. Lubabatu hakanne yasa ba ajin kansu indai ba Maryam aka tab'owa haj. Luba ba yanzun zakaji ruwan masifar ta da bala I.





Suna cikin hirar Maryam ta shigo da gudu ta shige bayan mama cikin shagwab'ar daya zame mata jiki tace "mama kinganshi ko zai dakeni "



"Wa kenan?" mama ta tambaya tana duban hanya ai tana ganin wanda ya shigo tai masifar had'e rai dan a duniya idan da wanda taiwa masifaffiyar tsana to Muhammad ne dan ya riga da ya hana ta sakat ya shige mata hanci da k'udundune tarasa yadda zata fyato matsiyaci ta huta.





Sosai tai masifar had'rai tace "dan ubansa idan ya isa yazo ya tab'aki tsabar masifa da jaraba abi a hana yarinya sakat to wallahi ni na gaji bari alhajin ya dawo dole yayi mana tsakani dakai dan 'yata na baiwa bace"




Kafin takai ga dire jarabar da take Muhammad ya shammace ta ya fisgo Maryam ya d'auketa da wani gigi yaccen mari wanda yasa nan take ta shid'e numfashinta ya tafi yajin aikin hucin gadi kafin tasaki wata azababiyar k'ara, karar ce ta ankarar da mama ai har mayen ya damk'eta sunan da tasaka masa kenan dan duk inda takai da bala I matuk'ar yayi niyyar mata hukunci babu wanda ya isa ya hanashi sai Baffa wato mahaifinsu




Ranta yai masifar b'aci cikin bak'in ciki tace "matukar ka kuma dukanta Allah ya isa ban yafe makaba shege mugu azzalumi ta Allah batakaba munafiki wallahi bari alhaji ya dawo sai yayi mana tsakani dakai tunda kai Allah yayi ka da zuciyar kafurai.




Duk zagi da munanan kalaman da take binsa dashi bai saurareta ba saida ya tabbatar ta turarawa Maryam jikinta sannan ya wulla mata ita jikinta ya juya ya fice yana huci yayin da mama taci gaba da zagi tana la antarsa.




Rungumo maryam tayi wacce take rusar kuka na fitar hankali domin ba k'aramin dakuwa tayiba jikinta kuwa banda azaba babu abinda yake mata abinka da farin mutum fatar nan tayi jajur tayi rud'u rud'u, suna had'a ido na Nassar tayi mata gwalo ta hayagagar ta tace



" wannan munafikar uwar taka ita kayima gwalo dan uwarka shege mai kama da d'iyan aljanu🤣🤣🤣🤣dole na dara domin duk wanda yaga Maryam yaga Abdul Nassar yaga JINI





Tana dire zagin bros yana dad'a danno kai daman a bakin k'ofa yatsaya domin ya San da cewa dama bazatayi shiru ba dole zata fad'i wani abun.






Comments and shere





Maman isi ce
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________

🔥BA JININA BACE🔥
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI


MAMAN ISLAM


Goron Taya murna
Ga
Shugaba ummy khaleel tasamu k'aruwan baby girl Allah ya rayata yasa cikon addinin musluncine amen



Ina gaidaku daukacin y'an kungiyata ta first class Allah ya k'ara daukakamu ya yabamu ikon rubuta abinda za a amfana dashi dan fiyayye Annabin rahama Amen

Page 2
Tana ganisa ta shige d'aki da gudu ta datse k'ofar da key dan tasan k'aramin aikinsa ne ya biyota har d'akin yacasa kayarsa.



Sai da taci kukanta ta gaji sannan ta mik'e ta shiga wanka fasa amsar d'inkin da tai kenan, bayan ta fito a wankan ta zauna ta d'and'asa kwalliyar ta tai matuk'ar kyau dan dama maryam mayyar kwalli yace duk da tsantsar kyawun da Allah yai mata akwaita da son kwalliya.



A can b'angaren Halima kuwa ad'ari d'ari take komai domin ba ta da tabbacin fitowar Maryam tunda wannan mayen bros d'in nasu mai fad'an tsiya ya dawo.




Sosai masu docuration d'in suka k'ayata wajen sai kace wani bikin aure ba walima ba.



Maryam kuwa duk da tsamin da jikinta yai mata saboda azabar dukan datasha bata fasa shirye shiryenta ba dan bata tsoron bros ko kad'an acewar ta ai dukane kawai guda zai daka kuma guda zai bari.




Bata samu damar karb'o kayan ba sai wajen k'arfe hud'u da sauri tazo ta shirya cikin wani d'anbanzan swess mai azabar kyau da tsada ita da kanta tasan cewa babu k'arya tayi masifar kyau ba na wasa ba.




Tana shirin fita suka kicib'us damama tana shirin shigowa galala tayi da baki tana kaonta da irin kyaun da tayi rumgume maman tayi tace "mamana na shirya, nayi kyau kuwa?"

" fad'a ma ai b'ata bakine 'yata kyawun da kikayi bazai fad'uba fatana dai ki kula da kanki kinji ko karki bari wani abin yasamar min ke in hakan yafaru bazan yafe ma kainaba?"




Wani lallausan murmushi ta sakar mata tareda manna mata kiss a goshi tace karki damu mamana insha Allahu babu abinda zai faru, yauwa ansaka min duk abubuwan da nace amitar?"




" komai ya kammala kije driver ke yake jira kar ku b'ata lokaci"
Had'e rai tayi tayi kicin kicin da fuska, take naga hankalin maman ya tashi tajawo ta jikinta tace "me kuma ya faru baby? muna maganar mu lafiya yanzun kin canja?"



Cikin shagwab'a tace "mama nafa ce miki da kaina yau zanja shine zakima driver magana gaskiya nidai ni da kaina zanje" murmushi maman ta saki tace "yanzun ke da wannan shine zaki b'atamin ranki abanza gashi" ta fad'a tana mik'a mata mukullin ta amshe tare da kuma rumgumeta ta sakar mata kiss a kumatu tace "ina k'aunar ki mamana sai na dawo" ta fad'a tare da yin waje aguje.




A d'an farfajiyar gidan ta tarar da Ammey tana kiranta amma ko kallon banza bata isheta ba balantana na arzik'i, tun kafin ta tada motar ta saki wani d'an banza hom ai baba mai gadi yanajin haka yataso aguje ya bud'e mata k'ofa dan yasan order ta ya fita daban dana kowa acikin gidan.




Ammey na tsaye har tafice sannan ta girgiza kai aranta tana mata addu ar sauka lafiya.




Ba d'an k'aramin gudu maryam take ba domin acewar ta wai ta b'ata lokaci abokanta na cen suna jiranta ga wani uban kid'a data k'ure wanda zai sa Sam bazata fuskanci ko gane abinda zai fad'a mata ba, wannan tabi ar tace sam maryam bata da mutunci ko kad'an bata sami tarbiyar kwarai daga maman tata ba ta nuna mata kudi sune komai na rayuwa dan haka tayi komai babu komai kud'ad'en mahaifinta zasuyi mata maganin duk wata damuwa.





Cikin k'ank'anin lokaci ta isa wajen, tasami gu tayi parking saida ta fara manna arnan glass d'in daya dace da kwalliyar tata kafin ta zuro kyakyawar farar k'afar ta waje ahankali take takawa, yayin zuciyar ta ya falfala da gudu cikin wajen saboda kid'an data ke jiyowa awajen da maryam gwana ce wajen rawa gata mayyar rawar ce biki ko batasan maishiba taje sai ta taka.




Tunda ga sanda ta faka motar yakafe wajen da ido har zuwa lokacin data fito cikin yauk'inta datakun ta mai tafiyar da hankalin 'yan maza kai har ma da matan bak'aramin mummunar fad'uwa gabansa yaiba ganita gashi babu damar shiga wajen domin lokacin shiga meeting d'in da zasuyi yayi dole ya wuce amma aransa yana fatan har sugama bata bar wajen ba tunda yaga wajen data shiga yasan cewa wani bikinne tazo.





Ita ko maryam tana ganin ta shiga wajen har ta fara wata irin rawa da juyi karab idanunta suka sauka akansa, take ta aro wata irin nutsuwa ta arawa kanta dan tana masifar gudun abinda zai b'arar da ajinta wajen masoyin nata kuma abin k'aunarta Muhseen.




Abokanta na hangota suka saki shewa da ihun murnan ganin ta da sauri suka k'araso wajen wasu na d'aukar ta pic yayin da wasu ke suka take mata baya har suka k'arasa cikin wajen.




Kujerar da aka tanada mata wacce ta kasance kusa da Muhseen ta zauna kamar wasu amarya da ango tunda shigo wajen akan idanunsa har rawa data soma amma sam bai nuna ya gantaba domin maryam ba k'aramar 'yar disgi bace shi yasa yake masifar kame kansa agabanta.





Ba tare da b'ata lokaci ba aka fara gudanar da abinda ya Tara su awajen sukaci suka sha sannan ta rarraba kyautukan data tanada domin abokanta duk Halima ce ta kula da wannan yayin da maryam ta masifar kame kanta agaban Muhseen sai da za ayanka cak ne ma ta d'an dubeshi k'asa k'asa ta gaida shi murmushi ya sakar mata ba tare da ya amsaba ya tashi suka k'ara wajen, wa ashe na murnan zagayowar haihuwar muhseen abin ya k'ayatar dashi yadda ya kamata yadda maryam take 'yar bidiri to shi har ya dameta ya shanye bayan gama yanka cak ne aka bud'e musu filin rawa suka shiga suna wani irin taku mai ban shi' awa da burgewa, juyowar da zatayi kawai idanunta suka sauka hakansa yana tsaye sanye cikin kakinsa dayake masifar yi masa kyau ya hard'e hannayensa a k'irjinsa ya kafeta da fitinannen kallonsa, take gabanta yai masifar fad'uwa hankalin ta yai mugun tashi ba dan komai ba sai dan gudun kar ya disga ta agaban saurayinta da abokanta musamman da ta kalli idanunsa taga sunyi wani irin rinewa sabo da b'acin rai, amma dan k'arfin hali irin nata kawai sai ta basar taci gaba da rawarta, abinda yai masifar k'ona masa rai yafara takawa cikin tafiyar sa na ingarman namiji batasan ya isota ba sai dayayi mata wani mugun damk'a kamar zai karyata saida ta saki k'arar wahala Muhseen kuwa yana ganin haka ya cika wandon da iska dan yasan sojoji ba imanine dasu ba yanzun sai suyi masa walmakalifatu.





K'ok'arin kwacewa ta soma ai kuwa yana juyowa ya d'auketa da wani azababben mari wanda a take hancinta ya balle da jinitayi luuuu zata fad'i saboda tsabar gigita ya fisgota ta fad'o jikinsa ya dad'a d'auketa da wani marin har guda biyu tsabar wahala da azaba bai barta ta gane inda take ba ya fincike ta daga jikinsa ya hau janta har jikin motar sa ya wullata ciki har Sai da ta gwaru da murfin motar saura kad'an ya had'e da hannunta wajen rufewar mukullinta ya jefawa driver da ya kira shi kuma ya tada tasa yabar wajen da masifaffen gudu yayin da yabar k'awayen ta da abokanta da jimami da tausayinta Allah ya had'ata da jarababben d'an uwa mara mutunci d'an hana ruwa gudu.





Daga yanayin order dayake ma mai gadi yasan cewa babu lafiya wannan jarababbiyar yarinyar ta tab'oshi, da sauri ya bud'e masa get yai saurin matsa gefe dan yasan cewa ba shigowar dad'in rai zaiyi ba ilai kuwa saida yayi wani irin masifaffen cin taya sannan ya danna hancin motar ciki, Nassar da dawowar sa kenan daga masallaci ya kwasa da gudu yai cikin gida domin yasan indai yayan nasa yana cikin zafi to kan mai uwa da wabi yake duk wanda yasamu bi yake ta kansa.






Maryam kuwa zuwa lokacin ta gama shiga wani hali tsabar wahalan dukan data sha haka ya kuma fincikota yajata ciki keeee ya gwara da kujera yana huci sai kace mayunwacin zaki a idanun haj. Luba ya watsar mata da 'ya kamar kayan wanki nan kuwa ta hau jaraba tana tsine masa ko kallon ta baiyi ba yayin da sai da ya kuma lallasata sannan ya d'ago yana huci ya kalli Ammey dake karatu cikin wayar ta bata ko kalli inda suke ba yace.







" Ammey yakama ta ace kinsa ido akan yarinyar nan domin kuwa kema 'yar mijinki ce dan haka kina da hakki akanta bai kamata ace kinsa ido ana watsa tarbiyyar yarinya ba idan ba haka ba idan Baffa ya dawo zan fad'a nasa irin rashin d'ar da yake faruwa agidan kamilin mutum kamar sa"





"Uaban Kane ya koya mana bad'alar nace uban kane bad'alalle d'anb iska mara mutunci kai dan ubanka tarbiyyab'ace da kai kai dazaka zauna kana gayan magana d'an iska mara zuciya dakana da zuciya da tuna ka fita harkana da 'yata amma dake kai zuc..................take ta had'iye sauran maganar saboda wani matsiyacin kallo daya watsa mata duk bala inta tana tsiron Muhammad domin ba shi da mutunci idan ransa ya b'aci MD kenan kamar yadda abokansa suke masa lak'abi.





Sai data yi jinyar jikin ta na kwanaki biyu kafin ta samu ta warware har ta iya shiryawa ta fice gidan su Ammey ta nufa wajen malam Babba mahaifin Ammey hakanan Allah ya nufeta da son tsohon saboda shi mutum ne dayasan kansa ya iya zama da mutane abinda ya kamata ace uwa zatayiwa d'anta shine malam Babba yake ma maryam cikin hikima da dabarun su irin na tsofaffi domin ya kula Luba banzar Uwa ce irin iyayyen nannan da basu son b'acin ran 'ya'yan su dan haka komai yaro zai basa tsawatar wa.




Tun daga nesa ya ta hango wani kamar bros a kusa da malam d'in take kuwa tai bala in had'e rai da k'yar ta iya yin sallama ta k'arasa kusa da MALAM d'in ta durk'usa har k'asa ta gaida malam sai wani ciccin magani take murmushi malam yasaki yace.




Idan naga zan iya zan dinga yin posting safe da dare idan na Gama daukiin Kuma sai abinda Allah yayi 😂😂😂😂😂😂😂😂

Maman Islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM




Page 3



"Maryamu kenan maryamu sarauniyar mata me ya faru ne naga maryam d'in tawa tana wani ciccin magani?"
Murmushi ta d'an saki batare da ta shirya wa hakan ba yadda yai maganar ne dole abin yabaka dariya cikin shagwab'a yace "har ga Allah bazan yafe abinda ake minba malam kawai dan anga ubana baya gari shine ake neman kasheni ko akassaramin rayuwa nidai nabar mututm da Allah gaskiya"

Ta k,are maganar tare da zubowar hawaye.



"Subhanallahi wake neman kassara min rayuwar uwa ina raye a duniya da lafiyana?"


Had"e rai ta k'arayi tana hararan MD k'asa k'asa sarai ya ganta ya basar yayin da malam ya d'an kalleshi yace "kodai kaine muhammadi kake takurawa uwata?"



Murmushi kawai yayi yana shafa kansa yayin da malam yace "ashe kuwa kaine gaskiya muhammadu karka k'ara dukar min uwata shifa duka baya shirya mutum sai daima ya dad'a kangara shi dan haka naaiha itace kawai zatasa mutum ya rusuna ba wai dukana kaji ko muhammadu"






"Shikenan malam yafad'a cikin sanyin sa" yayin da maryam ta tsagal tace "tab waye zaimin nasihar ai wallahi sai dai yaiwa kansa mutanen da suke zama cikin bariki suna k'arewa matan abokan aikinsu kallo har su kyasa ne zaimin wata nasiha" ta k'arasa tana manna masa wata shegiyar harara dan har ga Allah ta tsanesa saboda gana mata azabar da yake.



Murmushi malam yayi yace "haba uwata shid'infa yayanki ne bai kamata ace kina masa raahin kunyaba"




"Tab' ai wallahi sai dai ya nemi k'anwar sa ni babu abinda na had'a dashi'


Malam yace "gidanku nace gidanku ai ko ke kika had'a hanya da shi kuma alak'arku ba mai yankewa bace har k'arshen rayuwar ku"




"Ai kuwa ni zan Malku wannan bak'ar alak'ar kuma zakace na fad'a maka malam babu ni babu shi wallahi yadda baya sona baya k'auna ta nima haka"


Ta k'arasa maganar yayin da idonta yake nuna gaskiyar abinda yake kenan har k'asan ranta, malam yace "uwata idan zakiyi so kiyi so dan Allah haka idan zakiyi k'i kiyi domin Allah domin bakisan me gobe zai haifarba dan haka nake so ki cire duk abinda kika sanya aranki game da d'an uwanki"



"Malam alkhairi goben zai haifar ta fad'a idanunta yana cikowa da kwalla taci gaba da cewa malam dukanfa dayaimin ne yasa kayi kwanaki baka ganni ba ina can ina jinyar jikina, ni bama dukan ne ya fi b'atamin rai ba irin yadda ya disgani a gaban saurayina da k'awaye na dan haka wallahi ni babu ruwana da shi"



Malam yace "saurayi kuma maryamu shi Baffan naki bai sanar dake yayi miki miji bane?"




Da mamaki Maryam tace miji kuma malam? Ni bai fad'amin ba yadai ce na kasance mai kula da kaine kuma bai amince na saurari kowa ba har sai ya bani izini iya abinda na sani kenan"





"Yanzun bai isaba kenan shiyasa har kika fara kula wani batare da izinin saba"malam ya tambaya babu alamar wasa atare dashi, tace" bafa haka bane malam shid'in fa yayan k'awata ne wallahi yana da nutsuwa"





"Ke zaki fad'a mana hakan ko kuma mu zamu gano da kanmu?"
"Kune malam ta fad'a asanyaye ganin babu alamar wasa atare daahi.




Ranan dai hiran da malam batayi armashi ba ta sallame shi ta wuce, tana barin wajen malam ya dubi MD yace "akwai matsalafa muhammadu MD ya kafe malam da manyan idanunsa batareda ya furta komai ba, gane me yake nufi ne yasa malam cigaba da cewa kamata yaifa ace kaja maryam ajiki ba wai kadasa mata tsanarka a zuciyar taba kasanfa meke faruwa tsakanin ku dan haka nake neman alfarmar ka rik'a janta a jiki ba wai ka rik'a tsan gwamar taba hakan zai iya haifar da Marsala"






"Insha Allahu zanyi yadda kace malam cewar MD cikin sanyin jiki dana murya sannan ya d'ora da cewa " yarinyar
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment