Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ya sake watso min tambaya.


Amsa mishi nayi da cewa "Ina ganin almost 2 month kenan".


"Ina zuwa" Dr ya fad’a a tak’aice.


Tashi yayi ya je ya d’akko kayan gwaje-gwajen shi ya dawo ya zauna ya fara auna ni.


Bayan ya gama gwajin shi ya ajiye kayan aiki a gefe.


Jin bai ce min komai ba game da gwajin da ya min yasa na ce "Dr na ga ka gwada ni ba ka min bayanin abin da yake damu na ba".


"A gwajin da na miki ban ga komai ba, amma zuwa gobe zan tafi da jinin ki da fitsarin ki sai a je dashi lab a ga me yake damun ki".


"Allah ya kaimu goben" na fad’a.


"Amin" ya amsa min a tak’aice.


Washegari kuwa Dr ya tafi da jini na da fitsari asibiti dan a min gwaji.


Tun a jiya da Dr da ya min gwaji ya gano ina da ciki, sai dai ba yaso zargin shi ya tabbata dan har yanzu bai shirya ma haihuwa ba, gani yake har yanzu suna da sauran lokaci kafin su haihu.


San da yaje asibiti yasa an mishi gwaji a lab, sakamakon ya fito da cewa ina da cikin sati goma.


Abin da yasa ya daina d’aura ni akan tsarin family planning saboda yadda nake mishi k’orafin rashin samun ciki na da kuma dad’ewar da nayi ban samu ciki ba sannan yana da tabbacin tsarin da ya d’aura ni akai zai yi wuya in samu ciki da wuri haka, sai gashi Allah yayi ikon shi ya bani ciki a lokacin da bai yi tsammani ba.


Shawarar da ya yanke shine ba zai fad’a min ba dan shi bai shirya ma haihuwa ba, yasan in na sani ba k’aramin farin ciki zan nuna da jin labarin ba dan yadda a yanzu nake buk’atar samun ciki.


Lokacin da zai tafi gida ne ya tawo da wasu pills da zai bani.


Ko da ya dawo na mishi tarba ta musaman kana na kawo mishi abinci ya ci.


Ganin bai ce min komai ba akan gwajin da yace in ya je asibiti za a min yasa na ce "Dr an yi gwajin kuwa, me yake damu na".


"Oh kin ga na sha’afa in fad’a miki result d’in gwajin, daman nayi zaton Typhoid ke damun ki san da jiya na miki gwaji, yau d’in ma da aka yi gwajin a lab haka ya nuna hakan, ga magani na zo miki dashi, ki je ki d’ebo ruwa ki sha a gaba na dan nasan za ki iya mantawa ba ki sha ba tun da ke ba son shan magani kike yi ba" cewar Dr.


Tashi nayi na je na d’ebo ruwa a cup na dawo na zauna a kusa dashi.


Bani maganin yayi na sha da ruwa ina zuba mishi shagwa’ba shi kuma yana biye min.


Ban fi mintuna 30 ba da shan maganin na ji marata ta fara min ciwo.


Yatsina fuska na fara yi saboda yadda maran take neman takura min.


Dr ne ya kalle ni ya ce "Ya akayi ne Zarah".


"Mara ta ce naji ta fara min ciwo" na amsa mishi.


Cikin kulawa ya fara min sannu.


Tashi nayi da niyyar tafiya dan in je in kwanta ko zan samu relief akan ciwon da mara ta take min.


"Ina zaki ne Zarah" Dr ya tambaye ni.


Amsa mishi nayi da cewa "Zan je in kwanta ne, na ji marar tana so ta matsa min".


Dr ne ya ce "Ayya, sannu Zaarah, jeki ki kwanta, za ki ji sauk’i in kika samu bacci".


D’akina na wuce naje na kwanta.


Abu kama wasa, tun ina jin ciwon marar a hankali har ciwon ya fara fin k’arfin tunani na.


Tunanin abin da yasa min ciwon marar na fara yi, gashi ba period d’ina ba ne zai zo ba re in ce shi ne ya haddasa min ciwon marar tunanin.


Tun ina iya daurewa har ta kai ga ba zan iya jure wa ba.


Yanda nake jin ciwon ne yasa hawaye ya fara zubo min a idanu na.


Rik’e mara ta nayi ina juye-juye a gado, a lokaci d’aya ina sai jero addu’o’i nake yi a raina ko zan samu sauk’in ciwon da nake ji.


Gani nayi jini ya fara gangarowa ta k’afa na, har wani guda-guda ne ke biyo bayan jinin.


Hankali na ne ya tashi ganin jini na gangaro wa.


A iya tunani na wannan ba jinin mensturation ba ne saboda yadda yake zuba.


Dr ne ya shigo d’akin ya same ni a halin da nake ciki.


Da sauri ya k’araso ya d’ago ni.


Jiki na ne ya saki saboda wahalar da na sha.


Cikin rud’u Dr ya ce "Zarah me ya same ki haka ba ki kira ni ba".


"Ciki na da Mara ta ciwo suke min Dr" na fad’a cikin galabaita.


"Sannu Zarah, insha Allah za ki samu sauk’i kin ji" Dr ya fad’a cikin tausayawa.


D’auka ta yayi ya shigar dani Ban d’aki.


Sai da ya gyara ni kana ya kai ni side d’in shi ya bani taimakon da ya dace a matsayin shi na likita.


Magunguna ya bani nasha kana ya min da allurar bacci.


Cikin d’an lokaci k’ank’ani bacci yayi awon gaba dani.


Sai da na kwashe sama da awa biyu sannan na farka daga baccin da nake yi.


Dr na gani zaune a kusa dani, alamu na nuna yana jiran farka wa ta ne.


Dr cikin tausayawa ya kalle ni ya ce "Sannu Zarah kin tashi, ina ne yake miki ciwo yanzu".


Cikin sanyin murya na ce "Mara ta ce har yanzu take min ciwo".


"Zai daina ne a hankali, bari in had’o miki tea ki sha" ya fad’a yana mik’ewa.


Bayan fitar Dr ne na fara tunanin jinin da ya zuba a jiki na, sai dai abin da yake bani mamaki shine tun da na sha maganin da Dr ya bani na fara ciwon marar na da ciwon ciki, tambayar da na yi ma kaina shine me ya had’a maganin typhoid da zubar jini wanda ya haddasa min tsananin ciwon mara da ciwon ciki.


Kau da wannan tunanin nayi a raina na barshi akan cewa may be maganin da Dr ya bani ya min k’arfi ne, shi ya haddasa min ciwon.


Dr ne ya dawo ya zauna rik’e da cup d’in da had’o shayi a ciki wanda ya sha madara a ciki.


A baki ya dinga bani, sai da yaga na sha ai yawa sannan ya k’yale ni.


Haka Dr ya wuni ya na bani kulawa ta musamman.


Waya yayi da Farida akan ta yi mi farfesun kayan ciki da girki ta kawo bani da lafiya.


Wajen magrib sai ga Farida ta kawo farfesun da tayi da fried rice da ji hanta a ciki.


Haka Dr ya matsa min na ci abinci duk da ban jin dad’in baki na.


A kwana biyu na samu sauk’i, sai k’arfin jiki na ne bai dawo dai-dai ba
Har a lokacin ban san ‘bari nayi ba.


""""""""""""""""""""""""""""""


Yau yaya Khalil ne yake zaune a falo d’auke da Amatur-Rahman a hannun shi.


Anisa ce tazo ta zauna kusa dashi tana sakar mishi tattausan murmushi.


Shima murmushin ya maida mata.
"yaya Khalil sannu da hutawa, na barka kai kad’ai".


"Kar ki damu k’anwa ta, nasan uzuri ne yasa kika barni ke kad’ai dan kin je ki mana delicious food d’in nan naki da yake sa ni santi".


Fuskar tace ta yalwatu da annuri jin yadda yaya Khalil ke yaba mata.


Mik’a mata Amatur-Rahman yayi wacce ta fara kuka.


Amsar ta tayi ta fara jijjiga ta.


Kallon ta yayi cikin tsokana ya ce "babyn nan wai rigimar wa tayi ne, ni dai nasan ban da rigima".


Dariya tayi ta ce " Nima dai ban da rigima, ina jin rigimar Antyn ta tayi".


Shima dariyar yayi ya ce "Wace Antyn ta d’in".


Anisa ce ta ce "Kai wa kake tunanin nake nufi in ba Fatima ba".


Yaya Khalil ne ya ce "Sai yanzu nima nasan in da tayo rigimar, amma a ‘bangaren kuka ke tayo dan ki fi Fatima saurin kuka, tsiwa ce dai Fatima ta fi ki".


Murmushi Anisa tayi kana ta ce "Ina missing d’in Fatima, yaushe za ka kai ni gurin ta in wunin mata".


"Ki bari ran weekend sai in kai ki" yaya Khalil ya fad’a.


"Allah ya kaimu, amma yaya Khalil rashin haihuwar Fatima yana damu na, nasan haihuwa lokaci ne, sai in ga itama tana son haihuwa yanda take ma Amatur-Rahman in muka had’u, in na mata maganar sai ta nuna min ba ta damu ba, a yadda na fahimta ba taso a san ta damu ne, rashin haihuwar na damun ta" Anisa ta fad’a cikin nuna damuwar ta.


Yaya Khalil ne ya ce "Allah ne bai kawo mata haihuwar ba, in lokaci yayi sai ki ga ta haihu, ki ci gaba da taya ta da addu’a, Allah ya kawo mata masu albarka".


"Amin yaya Khalil, Allah ya amsa addu’ar mu" cewar Anisa.


"Amin Anisa" yaya Khalil ya amsa mata.


Da haka suka ci gaba da hirar su cikin so da kulawa.



Bayan four month na sake jin canji a jiki na, wannan karan ban da zazza’bin da nake fama dashi da amai da nake yi, ga yawan bacci sannan ga kwad’ayi da yawan cin abinci da nake yi.


Ni da kaina na fara zargin ko ciki ne dani saboda na ga wasu alamomi na masu ciki a guri na.


Bayan Dr ya dawo ne na kai mishi ruwa yayi wanka kana ya fito ya shirya ya zo ya zauna akan dinning table naje nayi serving d’in shi dan ni na riga na ci nawa.


Lokacin da ya gama cin abincin ne muka dawo falo ya zauna a kujera yana kallon tauraron d’an adam.


Jikin shi nazo na kanta ya fara wasa da gashin kaina da na mishi gyara na musamman tare da turarurruka masu k’amshi na kai.


Ban wani jima a jikin shi ba bacci ya fara d’auka na.


Cikin kulawa Dr ya ce "Kwana biyu na ga alamar ba kya jin dad’i, ban san me yasa ki ke ‘boye min rashin lafiyar ki, ko kin manta mijin ki Dr ne".


"Ni kaina Dr ba zan ce ga in da yake min ciwo ba, ina dai jin jiki na so weak da fever, ni abin da yafi matsa min Dr shine yawan baccin da nake yi da kuma cin abinci da nake ci akai-akai ga kwad’ayi" na fad’a cikin shagwa’ba.


Tak’aitaccenn murmushi yayi kana ya ce "Kar ki damu, na zo miki da magani, bari in je in d’akko sai in baki ki sha".


Side d’in shi ya je ya d’akko maganin ya dawo d’auke da ruwa a hannun shi.


Maganin ya bani na sha, sai da ya bari maganin ya bi jiki na kana ya kwantar dani a jikin sa.


Bacci ne ya d’auke ni saboda daman baccin nake ji.


Cikin bacci naji ciwon mara ya ziyarce ni a lokaci guda.


Ba shiri na farka daga nannauyan baccin da ya d’auke ni a jikin Dr.


Tashi nayi na zauna ina rik’e mara ta tare da fad’in "Wash Allah! Mara ta".


Kallo na Dr yayi kana ya ce "Ya kike jin ciwon maran".


Kuka na fara yi saboda yadda nake ji na ce "Dr ba zan iya fasalta maka yadda nake jin ciwon marar ba, sai dai ina jin ciwon kamar na lokacin baya da nayi san da ka bani magani na sha, Dr ka taimake ni".


Rik’o ni yayi ya fara lallashi na ganin yadda na rik’e mara ta da nake ji kamar za ta fashe saboda ciwo.


D’auka ta Dr yayi da niyar kaini d’aki, jini ne ya fara gangarowa kamar wancan karan.


Da sauri Dr ya k’arasa dani band’aki ya gyara ni, ko da muka fito daga band’aki jinin bai daina zuba ba.


Duk wani taimako da Dr zai bani yayi iyakar k’okarin shi amma jinin bai tsaya ba, hakan yasa ya d’akko min hijab d’ina ya sa min.


D’auka ta yayi ya sani a motar shi muka nufi kangiwa hospital inda yake aiki.


Taimako na gaggawa aka bani tare da taimakon Dr, a k’arshe dai sai da aka min wankin ciki.


Nan na tabbatar da cewa ‘bari nayi.

Wajejen yamma Dr ya d’akko ni muka dawo gida.


Ni kad’ai nasan yadda naji san da na tabbatar da cewa ‘bari nayi, na sa rai da wannan cikin da na samu dan a yanzu baabin da nake fata da ya wuce in haihu, sai gashi Allah yayi ikon shi a kaina.


Tun da muka dawo gida nake faman kuka, duk lallashin da Dr ya min bai san a daina kukan ba, a yadda na fahimta shi Dr bai nuna damuwar shi akan ‘barin da nayi ba.


Kallo na yayi ya ce "Wai Zarah kukan me kike yi ne haka, duk lallashin da na miki bai ishe ki ba, ko akwai inda yake miki ciwo ne" ya k’arasa maganar da tambaya ta.


D’ago kaina nayi na kalle shi na ce "Dr yanzu laifi na kake gani dan nayi kuka, cikin da na dad’e ina burin in samu Allah ya bani a lokacin da ban yi tsammani ba, sai gashi Allah ya amshi kyautar da ya min amma ka ce ba zan yi kuka ba" na k’arasa maganar da k’ara sautin kuka na.


Jawo ni jikin shi yayi ya ce "for God sake miye amfanin kukan nan da kike yi, ni ban ga abin d’aga hankali ba dan kin yi ‘bari ba, at any time Allah zai iya baki wani, ba na so ki dinga d’aga hankalin ki akan k’aramun abu".


Janye jiki na nayi daga jikin shi na kalle shi cikin ‘bacin rai na ce "Dr miscarriage d’in ne k’aramin abu? In a gurin ka k’aramun abu ne, ni a babba na d’auke shi, daman na ga ba ka nuna damuwar ka akan ‘barin da nayi ba".


"ya kamata ki fahimce ni Zarah, you have to take patient tun da haka ya faru, har wani dad’ewa muka yi da aure da za ki sa kan ki a damuwa dan kin yi miscarriage, mu d’auki k’addara tun da Allah yayi babyn mu ba zai rayu a womb d’in ki ba" Dr ya fad’a.


Kasa ce mishi komai nayi saboda takiacin da maganar shi ta sa ni, nasan ci gaba da zama na a gurin ‘bacin rai da haushin abin da Dr yake fad’a min zai k’ara min matuk’ar Dr ba zai taya ni jimamin abin da ya same mu ba na miscarriage d’in da na samu ba.


Tashi nayi na bar mishi gurin na wuce d’aki na.


Ranar ma a d’akina nayi kwanciya ta dan har yanzu ban daina jin haushin rashin caring d’in da bai nuna min ba akan miscarriage d’in da nayi, ban san me yasa Dr bai son in haihu da wuri ba, ya d’auki halin turawa ya sa ma kanshi, dole ba zai nuna damuwar shi akan rashin haihuwa na ba.


Ganin ban zo d’akin shi ba yasa ya biyo ni muka kwanta a d’aki na.


Haka ya dinga fad’a min sweet words masu kwantar da hankali akan in cire damuwar da nayi akan miscarriage d’in da nayi.


Duk wannan maganganun da ya fad’a min jin shi kawai nake yi, da na gaji da sauraren maganar da yake fad’a min na lumshe ido na kamar mai bacci, hakan yasa yayi shiru shi ma.


Da haka bacci ya d’auke ni.


Washe gari Dr ne ya ya turo Farida akan ta taya ni aiki kasancewar jiki na ba k’arfi.


Momin Dr ce ta kira ni ta min ya jiki kasancewar Dr ya fad’a mata abin da ya same ni, ta ce in ta dawo daga aiki za ta zo ta gaishe ni, da haka muka yi sallama da ita.


Na kira Ummu na fad’a mata nayi ‘bari, ta nuna jajantawar ta gare ni saboda ita ma a yadda na lura ta damu da rashin haihuwa ta, ba tason yi min magana ne dan kar ta d’aga min hankali.


Da daddare Momi tazo da Hanan sun duba ni tare da jajanta min, ta kira Dadin Dr ta ba ni muka gaisa dashi shima ya min ya jiki kasancewar ba ya gari.


Anisa ma da Anty Jiddah sun kira ni a waya sun min ya jiki.


Cikin kwana biyu na samu sauk’in jiki na, hakan yasa na tashi na fara aikace-aikace na, na gyara d’aki na.


Bayan na gama ne na tafi side d’in Dr na je fara mishi gyara.


Ina cikin gyaran ne na tafi ‘bangaren wardrope d’in shi na fara jera mishi gogaggun kayan shi, a nan na ga wasu pills a cikin kwalin maganin ya ajiye su a cikin wardrope d’in.


D’aukar maganin nayi na karanta amma ban gane ko na menenen, sai dai maganin yayi kala d’aya da wanda Dr ya bani.


Maida wa nayi cikin wardrope d’in na ci gaba da aiki na.
Zuciya ta ce take ta sa min tunani akan maganin nan, zuciya ta sai bani shawara take yi akan in yi bincike akan maganin saboda yadda sau biyu ya saukar min da ciwo da ciwon mara had’e da zubar jini wanda har ya kai ni ga zuwa asibiti.


Iya tunani na, maganin da Dr ya bani ya min k’arfi a jiki na ne shi yasa na ke samu wannan matsalar.


Ina gama aikin nayi hanyar fita, maganin ne ya k’ara fad’o min a rai na, hakan yasa na koma na bud’e wardrope na d’akko maganin.


Zama nayi a bakin gado na bud’e data na sa sunan maganin a google.


Bayani ne akan maganin da yawa suka nuno min a site d’in, hakan yasa na bud’e d’aya daga ciki.


Bayanin da na gani akan maganin shi yayi barazanar d’auke numfashi na, sai da na d’auki tsawon mintuna biyar ban san a wani hali nake ciki ba.


Da k’yar na jawo jarumta na ara ma kaina na dawo cikin natsuwa ta.


Dan kar in gasgata zuciya ta yasa na k’ara shiga wani site d’in amma duk bayani d’aya yake zuwa min dashi.


Abin da bayanin ke sanar dani cewa wannan maganin zubar da ciki ne da na gani a wardrope d'in Dr wanda yake bani a matayin maganin typhoid.


Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo min daga idanu na.


Abu d’aya ne yazo min a raina shine maganin da Dr ya bani ba typhoid ba ne kamar yadda ya ce min, maganin abortion Dr ya d’auka ya bani da hannun shi na amsa na sha da kaina saboda yardar da nayi mishi da soyayyar da ke tsakanin mu.


"Me yasa Dr zai yaudare ni ta wannan hanyar, me yasa Dr zai raba ni da gudan jini na da nake son gani, me yasa Dr zai min sakayya ta irin wannan hanyar bayan yasan yadda nake so in samu ciki?" Na tambayi kaina.


Zuciya ta ce ta bani amsa da cewa yayi hakan ne dan bai shirya ma haihuwa ba kamar yadda yake fad’a.


Tunano lokutan da ya bani magani har sau biyu nayi, yanayin da na tsinci kaina a farkon maganin da Dr ya bani na zubar jini da ciwon mara kenan hakan na nufin miscarriage nayi kenan, hakan bai ishe shi ba sai da ya k’ara bani maganii a karo na biyu ya k’ara ‘barar min da ciki.


"Ashe daman so na iya zuwa da cutarwa?" Tambayar da nayi ma kaina kenan.


Tambayar da ya kamata a ce da kaina na gano amsar ta amma ban da halin yin haka saboda halin da nake ciki.


Kenan shi yasa bai nuna damuwar shi akan halin da na shiga ba lokacin da nayi ‘bari.


Wani irin ‘bacin rai ne na ji ya ziyarce ni a lokacin.


"Inna lillahi wa inna ilaihir raji’iun" na dinga ambata a raina daboda in samu sauk’in halin da na ke ciki.


Ba abin da a yanzu nake buk’ata da ya wuce dawowar Dr.


A yadda nake jin zuciya ta zan iya fito na fito dashi dan ba zan bari ya nakasa min rayuwa ta ina kallon shi ba saboda tunanin shi ina son shi.
[8/29, 21:10] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💝💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*



*BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽


ww.maryamahmadpaki.blogspot.com


Facebook: Kainuwa writers Association




*Na Baku wannan shafin kyauta*

_Hauwa_

_Safiya_

_Fateema_

_Maman Umar_

_Fadeela_

_Fatima M lawal_


_Ina godiya da yadda ku ke nuna ma wannan novel d’in one love_.

_Y’ar mutan Paki na mik’a gaisuwar ta gare ku_.





85-86


Ban san lokacin da na d’auka a zaune ba a halin da nake ciki.


Shigowar Dr d’akin ne yasa na d’aga kaina na watsa mishi wani kallo mai tattare da ‘bacin rai.


Sallama ya yi ya k’araso cikin d’akin yana kallon irin kallon da nake watsa mishi.


In ban da sanin darajar amsa sallama da nayi da ba zan amsa mishi sallamar ba.


Ciki-ciki na amsa mishi sallamar da ya min.


K’arasowa yayi ya zauna kusa dani ya sakar min mayaudarin murmushin shi ya ce "my Zarah jiki yayi normal kenan, tun da na shigo gidan na ga ya canza min, nasan aikin my Zarah ne, na je side d’in ki ban gan ki ba, ashe kina nan".


Shiru na mishi kamar ba dani yake magana ba.


Kallo na yayi ya ce "Zarah wai lafiya na ga mood d’in ki ya canza, ko har yanzu jikin ne".



A karo na biyu na k’ara mishi shiru saboda ni kad’ai nasan ‘bacin ran da nake ciki.


Matsowa yayi da niyyar hugging d’ina ya fara magana cikin wasa ya ce " Yau sarauta kike ji kenan, bari in ji wa ya ta’ba min Zarah ta".


Ganin zai yi hugging d’ina yasa na mik’e cikin ‘bacin rai na ce "Dr kar ka ta’ba ni".


Kallon mamaki ya min kana ya ce "Wai Zarah me yake faruwa ne?".



"Abin da yake faruwa kake so ka sani Dr, yanzu ko zan fad’a amma abin da yake faruwar" na fad’a cikin fushi.


D’akko maganin nayi na nuna mishi na ce "Menene wannan Dr, ina so ka yi min bayanin wannan maganin, menene shi kake bani a matsayin maganin typhoid".



Mamakin ganin maganin yayi da har ya kasa magana, sai bi na da ido da yake yi.


Ganin ba zai yi min bayanin maganin ba yasa na ce "Dr nasan daman ba za ka min bayanin maganin menene ba dan kasan ba ka da gaskiya, wannan maganin da ka ke hidden d’in shi a wardrope d’in ka na ganshi wanda kake bani a matsayin na typhoid, na gano maganin da kake ba ni maganin zubar da ciki ne, in kuma na fad’i akasin haka ka fad’a min".


K’arfin hali Dr yayi ya ce "Ke Zarah wa ya fad’a miki wannan maganin abortion ne da kike d’aga ma kan ki hankali akai, dan ki yi miscarriage sai ki d’auki laifin ki d’aura a kaina".


Cikin fad’a na fara da cewa "Ba wanda ya fad’a min cewa maganin abortion ka bani, jiki na ne ya bani hakan da kuma binciken da nayi na gano hakan, Dr in a tunanin ka ni ba likita ba ce, amma kasan akwai hanyoyi da zan iya bincike akan maganin kamar yadda na bincika a waya ta".


D’akko waya ta nayi na bud’e site d’in da nayi browsing na mik’a ma Dr wayar na ce " In kana tunanin ni zan maka k’arya akan abin da na fad’a akan maganin da ka bani, na tabbata za ka yarda da bayanin internet dan na ga daman da turawa kake koyi shi ya sa har ka bani maganin da zai zubar min da cikin da na ke rok’on Allah ya bani…".


Cikin tsawa Dr ya katse ni da cewa "Ya ishe ki Zarah! Enough! Na ga ina bin ki in a polite way ba ki sani ba, abin da kike zargi haka ne, maganin da na baki na abortion ne, nasan kina sane da cewa cikin da na zubar nawa ne ba na wani ba ko? ba ki da wani mataki da zaki d’auka akan hakan, haihuwa ce na ce ba yanzu nake so ki haihu ba, rayuwa ta ina mata planning ne da kike gani na, in lokacin da nake so ki haihu yayi zan bari ki haihu, dole ne ki bi instruction d’in magana ta tun da ni ne mijin ki".


Ban san d’abi’ar Dr yayi nisa haka ba akan koyi da yahudu da har zai ce yana ma rayuwar shi planning bayan Allah shi yake tsara wa bawa rayuwar shi.


" Dr ba zan ta’ba bin ka ba in dai akan wannan maganar nan ce, Dr babu da’a a gurin yi ma wani biyayya a gurin sa’ba wa mahalicci, dan haka ba zan maka biyayya ba wajen zubar da cikin da kake min, idan har ba ka son kyautar da Allah yayi maka ni ina so, a shirye nake na amshe shi hannu bibbiyu, wasu ma da kud’i suke neman Allah ya basu kyautar bai ba su ba sai mu da Allah ya ba mu ce ba za mu amsa hannu bibbiyu ba, da kake maganar kana ma kan ka planning, ina jin ka manta Allah shi yake tsara wa bawan shi rayuwar shi, A ce Allah yayi wa mutum kyauta
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment