Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ci saitin kujeru uku iri daban-daban saboda girman sa. Ya kawatu da kayan alatu da air condition ta tsaitsaye a kowacce kusurwa, komai na jin dadin rayuwa yaji a wannan falo mai kama da palace, din wani gwamnan kai ka ce babu ranar mutuwa a zuciyar mamallakin sa.
Amani ta shiga tako matattakala tana saukowa daga saman benen ta tana tafiyar nan tata tamkar bata so.
Kallo daya Mukhtar da ke zaune gefen Alhaji ya iya yi mata a lokacin tana saukowa daga stairs din, cikin takun nan nata tamkar na macen Dawisu mai ji da kasaita, ya yi maza ya sunkuyar da kai cikin jin faduwar gaba don bai taba yi mata kyakkyawan kallo ba, yau din ma kamar kullum, a sace ya kalle ta, amma ya ga surar jikin ta sosai a cikin kayan barcin, sai ya samu kan sa cikin jin takaicin wadannan sharasharan kuma bingilallun kayan dake jikin ta a matsayin ta na mace kuma Musulma a cikin mutane, domin kamar kanwar sa ya ke kallon ta.
Har ga Allah Amani bata san da shi a falon ba ta riga ta saba gaida mahaifin ta da kayan barci in har tana son su gaisa kafin ya fita, kasancewar sa maabocin sammako. Tana cigaba da saukowar bugun zuciyar Mukhtar na dada karuwa, ba tun yau ba hakan ce take kasancewa da shi a duk a lokacin da ya hangi Amani ko daga nesa ne. Duk da dai wata kalmar fatar baki bata taba hada su ba. Amma Tafisun tun dawowar ta daga ATBU take yi masa kwarjini sosai.

Tafisu na dauka tuntuni kin shirya jiran isowar Mukhy kike ya zo ku wuce ki duba Boutique din naki?

Amani ta yi kicin-kicin da fuska cikin sakalci irin nata tace Daddy ai ba sai mun tafi tare ba, yayi gaba, tunda yana da mota a hannun sa, ni inna kintsa na gama breakfast na yi wanka sai in zo mu hadu a can.
A zuciyar ta kuwa fadi take Allah ya tsare ni da shiga motar sa, Allah tsare ni hada hanya da shi.
Don dai ita Amani fisabilillah bata yarda hakanan Mukhtar ya bar baban ta ba, tafi yarda da cewa asirin su na Diffawa yayi masa yake son sa irin haka, kada ta je itama ya hada da ita ya dinga juyata yadda yake juya Daddyn ta.
Daddy ya ce cikin lallashi, amma kin san bana so kike tuki da kan ki ko Amani? Tunda duk kin kori direbobin saboda masifar ki sai ki shiryo Mukhy yana jiran ki ku tafi tare, ban yarda ki kara tuki daga yau ba, kada ki manta sau uku kenan kina yin accident din da sai na biya diyya ga wadanda kike bugawa mota ta baya, tunda tukin bai karbe ki ba, to a hakura da shi babu dole. Duk inda kike son zuwa ki kira Mukhy a waya ya zo ya kai ki.
Amani ta hau tumami da kafa cikin shagwaba tana fadin "Ni gaskiya bazan daina tuki ba, da koyo akan iya Daddy. Kuma da haka ne zan kware da tukin".
Hon. Yace "duk ba na ki ba, ina nufin for the mean time zuwa kafin ki koya din nake magana, daga yanzu duk inda zaki Mukhy na yarda ya kai ki.
Shi kin ga bayan iya tuki na hankali, harda nutsuwa da sanin ciwon kai a tare da shi.
Maza shiryo ki zo ku tafi kin ji Tafisu na? Bana son musu. TA FI SU KIN FI SAURAN MATA!.
Ya fadi kirarin da ya san da shi yake lallashin ta, duk da tana cewa bata son kirarin amma sosai mahaifin nata yake ciyo kan ta da shi ta yi masa abu idan ta yi gardama, kamar wata karamar yarinya.
Fuskar nan ta Amani kamar hadarin da ya nausa yayi gabas ya juya yayi yamma. Wato Daddy na nufin ita bata san ciwon kan ta ba kenan kuma bata da nutsuwa sai Mukhy din sa. A fusace ta juya zuwa hanyar data fito, bayan ta zabgawa Mukhtar wata hadaddiyar harara tamkar manyan idanun nata zasu fado kasa.
Mukhtar wanda kansa ke sunkuye yana danna wayar hannun sa bai san tana yi ba, ya yi sallama da Daddy yana fadin zan jira ta a mota Daddy ya ce ka dai tabbatar da lafiyar motar da za ku hau din ko Mukhy? Kuma Amani zata so hawan wadda ka zabo din? Bata so tana tafiya a hanya mota ta samu matsala, kuma bata son dindimemiyar mota. Mukhtar ya dan cije lebe cikin jin takaici, ya ce Alhaji kai ka ce min farar Brabus ta fi son hawa, kuma ita na dauko, lafiyayyar mota ce.
Yayi kyau, to sai kun dawo, kada ka manta ka yi tuki a hankali bata son gudu, ku dauko Hajiya a filin jirgi in zaku dawo, yau zata dawo daga Umrah da zarar kun gama da boutique din sai ku je ku dauko ta, na san kafin nan jirgin nasu ya yi landing don sai bayan azahar zasu sauka.
Ba tare da ya ce komai ba yasa kai ya fita daga falon. Takaicin yadda Alhaji ke sakalta yarinyar sa ya fi komai bata masa rai. Amma shi ya isa yace wani abu? Shi yasa take ma mutane kallon hadarin kaji kallon kowa banza ne saboda ta san Alhaji ya daure mata gindin sakarci.
Mukhtar Yafi karfin mintuna sittin zaune cikin motar yana jiran saukowar yar mulki Amani, har aka rufa awa guda da rabi babu Amani ko inuwar ta, tun yana duba rantsatstsen agogon hannun sa swatch' dama na motar as well, har ya gaji ya kishingida a kujerar direba, ya ware sautin radiyon motar yana sauraren waqar mutumin sa mai debe masa kewa a duk lokacin da yake tuki, wato fasihin mawakin nan Ba-sudane Mahmoud AbdoulAzeez. A rayuwar sa ba abinda ya tsana irin jira, to amma ya zai yi? Umarnin Alhaji ne, kuma in an bi salsala Amani itace kamar second Boss din sa bayan Alhaji. Dole yayi zaman jiran ta a mota, ta shanya shi iya yadda ta ga dama.
Tun lokaci na farko da suka fara haduwa da Amani da ya fahimci dabiun ta na sangartattu ne kuma bata ganin kan kowa da gashi yake taka-tsan-tsan da shiga shaanin ta, yake kokarin kaucema haduwar su a yawancin lokuta, in kuma ta kure sun hadun baya yarda ya yi mata kallo na biyu, sabida yadda ta ke masa kwarjini da sanya shi faduwar gaba. Ga harara kala_kala da yake sha daga kyawawan idanun ta. Maigadin gidan Hon. Usman wanda tasu ta zo daya wato Malam Tajuddeen Bafillace, ya sha yi masa fatawar cewa,
muddin kana son zaman lafiya da Alhaji, muddin kana son tafiyar ku tayi tsaho, muddin kana son fadar ka ta fadada a wurin sa kuma tauraruwar ka ta cigaba da haskawa a idanun sa, to ka kyautatawa mara kunyar yar nan tasa mai soyayyun idanu a tsakar ka.

Shima ya yarda da hakan don idan ya zauna da Alhaji na minti biyar to hirar sa ta mintina uku cikin biyar din a kan tilon 'yar sa Amani ne da irin tanade tanaden da yake yi mata a rayuwa don baya so ko bayan ran sa ta sha wahala ko ta nemi wani abu ta rasa tunda bata samu soyayyar Uwa data dangi ba.
A irin haka watarana ya taba gaya masa cewa ya gina mata estates har guda biyu ya kuma mallaka mata su da sunan ta, karkashin idanun lauyoyin sa a cikin Birnin Katsina da babban birni, Abuja. Watau AMANI FASKARI HOUSING ESTATES. Wadanda dukkansu ya zuba tenants 'yan haya duk shekara suna biyan Amani miliyoyin da shi kan sa bai san zai same su a jikin gidajen ba. Hakan ya sa dole ya bude mata hannun jari a kasar Mexico.
Mukhtar ya kan yi mamaki a cikin ran sa, mugun mamaki don bai san ana haka ba, wai uba ne ke kaunar dan da ya haifa har haka! Wasu lokutan abun ya bashi sha'awa ko ya burge shi, don bai taso ya ga ana yin hakan a gidan su ba. Bai san dadin kaunar Iyaye ba. A nasu gidan ba'a san komai ba sai uwar riko sai 'yan ubanci, kishi tsakanin iyayen su mata, burin gado da horo mai tsanani da sunan tarbiyya, wannan itace rayuwar da ya taso ya budi ido ya ga ana yi a gidan su, wadda karfi da yaji ta koya masa zama independent.
Shi ko alfarmar gaisawa da nasa mahaifin ba ya samu a sanda yake tare da shi, yana raye ba wai ya mutu ba kuma suna cikin gida daya. Amma sai ya yi wata biyar suna gidan da shi bai saka shi a idanun sa ba. Ko fuskar sa baya samun alfarmar gani.
Wannan dan tunanin da ya mika a zaune, yasa kyakkyawar fuskar sa yin jajir, ta rikide zuwa yanayin ta na tun fil azal da aka san shi da shi wato yanayin sa na rashin walwala da kwantaccen bacin rai, irin bacin ran nan mai kwanciya a kasan idanun mutum, ya sauya ainahin kalar su zuwa brown, ya nuna zahirin rudanin da ke cikin zuciyar dan Adam. Wanda a duk lokacin da ya tuna mahaifin sa ko ahalin sa hakan ce ke faruwa da shi, ya ji yana son kara nesanta kan sa da Diffa many more miles away! If possible, har fiye da nisan da yayi da gida a yanzu, don Najeriya ba nisa da Nijar, zai fi son ya tafi can karshen duniya wato kasar China birnin Hong-Kong ya yi rayuwar sa a can.
Matsalar guda daya ce yana jin dadin zama da Alhaji Usman don soyayyar Uba yake nuna masa irin wadda bai san da ita ba, bai san irin ta na existing ba. Shi kan sa yana mamakin soyayyar Alhajin gare shi a matsayin sa na bare a gare shi. Ba don haka ba da ya kara lulukawa cikin duniya ya kafa rayuwar sa a can.
Dagowar nan da zai yi da zummar fita daga motar don zaman ya fara gundurar sa ya hangota tana takowa cikin rangajin ta na halitta, tamkar reshen bishiyar da iska ke kadawa ko kuwa Dawisun da ya baza adon halitttar sa yake tafiyar takama a doron kasa, sai kayi tsammanin beauty contest zata tafi.
Ta yi kyau ba dan kadan ba cikin wani material lace kalar ja da ratsin baki, an yi mata dinkin riga da siket wanda aka tsaga kafar sa ta baya, babu mayafin arziki a jikin ta baya ga wani rakani gantalin cantitly sai daurin kai da ta kalmasa gwanin shaawa da dankwalin kayan kai bazaka ce ta hada jinsi da hausawa ba.
In da abinda yafi bakanta masa rai a dabiun ta bai wuce rashin daukar mayafi da lullubi da muhimmanci ba, bai taba ganin ta da lullubi a kan ta ba balle a kai ga zacen hijabi ba.
Amma shi waye da ya isa ya yi mata magana a kai? Zai iya yi wa Baban ta ya yi mata, amma ya lura Baban ma bashi da katabus a kan ta, tamkar itace uban shine yar, babban abinda yasa ya tsani Amani kenan.
Duk halayen ta na sangarta, rashin ilmin zamantakewa da rashin sanin addini basa gaban sa, don ya san masu iya gyaruwa ne in ta samu uwa ko abokin rayuwa nagari, ba irin Hajiya Rabi ba uwar gantali uwar bisa titi wadda mijin ma baya gabanta irin kasuwancin ta da yadda zatayi ya bata kudi kullum, amma rashin girmama mahaifin nan nata da bata yi ko ta wajen magana yasa ya sallama mata, yana roka mata shiriya a kasan ran sa, don ya lura girman hannun namiji ce. Irin su Amani suna abu bisa kuskure ne ba tare da sun san cewa kuskure bane, saboda tun farko basu tashi ana kwabar su ko ana nuna musu girmama na gaba ba, aah, an raine su ne a bisa tafarkin duk abinda suke so dole su samu karkashin soyayyar iyaye masu duniya a tafin hannun su, irin mai samar da komai na bukatar rayuwa ga yaro ba tare da ya yi gumi ko ya fidda hawaye ba.
A haka ta iso motar ta tadda shi, ta tsaya tana jiran ya bude ya fito ya bude mata yadda direbobin ta ke yi cikin rawar jiki, don da kunnen sa ai yaji Daddy ya ce daga yau shi zai dinga tuka ta which means yana matsayin sabon direban ta kenan.
Amma Mukhtar sunkuyar da kan sa yayi, kamar bai san da tsayuwar ta a wurin ba ya dukufa danne- danne cikin tsaleliyar wayar hannun sa amma fa shi kan sa bai san me yake dannawa ba, saboda kwarjinin Amani mai bi har cikin bargon sa.
Hey! Baka ganin mutane sun iso ne? Ko makaho ne kai?
Mukhtar ya dago cikin slow motion ya zuba mata fusatattun idanun sa masu kama da an diga zaiba a cikin su. Nan da nan Amani ta daburce, bata san sanda ta bude kofar motar ta shige ba. Ta kuma rufe kofar motar da karfi. Ko gama rufe kofar motar bata yi ba ya ja motar, saura kadan ta rufe da kafafun ta.
Wata irin shakkar Mukhtar ta soma shigar Amani, domin bazata iya fassara alamuran data hango fal cikin idanun sa ba. idanun cike suke fal da abubuwan da shi kadai ya san su, ga tarin damuwa da fushi da rashin walwala, sannan tuki yake amma ko kallo bata ishe shi ba.
A rayuwa bata taba haduwa da namijin da bai yi mata kallon kwal uwar daka ba koko kallon kin yiwa sauran mata zarrah idan ta yi kwalliya sai shi wannan baabzinen. Koda take ce ma Daddy bata son sunan TA-FISU tana fada ne kawai, amma fa tana son sunan, domin yana kara mata alfahari da kyawun surar ta mai ruda yaya maza, wani lokacin har mata yan uwan ta (will not keep wishing they were like her).
Yau ga ta ga namijin da bai yi mata kallo na biyu a duniya ba, ta saci kallon kan ta kadan, to kyawunta ne bai ishe shi daga ido ya kalla bane ko kuwa kwalliyar data cancada bata kai ta kawo bane? Ko kuwa shi din ma YA FI SAURAN MAZA ne?
Kwafa tayi tace cikin yar rawar murya Malam ka rage gudu, baa gudu da ni a mota, I think Daddy ya gaya maka, drive with care. Yayi fumfurus kaman bai ji ta ba, maimakon hakan sai ma karawa motar sa wuta da yayi yana fadi cikin ran sa ai ni ba Daddyn naki bane, Mukhtar nake.
Amani tayi kyacci, kamar ta ji me yake fadi a ran sa. Daddy ya san kai makaho ne kuma kurma ne sannan baka da seti ya saka ka tuka ni a mota?
Sai lokacin Mukhy ya dan juyo a gicciye a dube ta, da idanun sa masu kalar silver, duban da sai da yasa hantar Amani da hanjin cikin ta karkadawa domin ta yi zaton kwada mata mari zai yi, don ko da bai yi magana ba ta san kallo ne na zazzafan gargadi ya yi mata, wato ta san irin maganar da zata dinga furta masa. He is not that stupid as she thinks.
Suka isa Goruba Estate wato inda boutique din Amani yake. Nan ma jira take ya fito ya bude mata kofar mota ta fito amma ya bude yayi ficewar sa ya bar ta a zaune. Masu kula da wajen sai gaishe shi suke yi don su a tunanin su shine mamallakin shagon, sabida duk wani shige da fice shi ya dinga yin sa har komai na boutique din ya kammala, tankareren shagon yana daga jerin farko-farko na shagunan da ke cikin plaza din. Mai gadi ya kawo masa mukullan hannun sa ya bude ya shiga ciki. Da Amani ta tabbatar ba zai bude mata kofa ba sai tayi kyacci ta bude ta fito ta bi bayan sa.
Ta tara shi fal a ranta har da karin gishiri da maggi na abubuwan wulakanci da zata gayawa Daddy ya yi mata, tana shiga shagon ita kanta ta girgiza da irin dukiyar da mahaifin nata ya narkar mata, takalma ne da jaka na mata na zamani na yayi da sittiru yan waje na yara da manya, shi kansa wanda ya zabo kayan ta sara masa wajen iya investing kayayyakin da zasu dauki hankalin kwastoma, a rashin sanin ta ba kowa bane dan mutanen Diffa ne amanar Alhaji Usman Faskari.
Duk kushen ta da high taste din ta ta kasa kushe tsarin da Mukhy ya yi wa shagon nan. Ko da suka gama dubawa abubuwa kadan ta iya cewa a kara. Shi din ma rubutawa ta yi aka takarda ba da fatar baki ta gaya masa ba. Yayi gabas ita kuma ta yi yamma a cikin shagon don kada ma ta hada hanya da shi. Ta rubuta iya abubuwan da take bukata a kara sannan ta fice daga shagon ba tare da ta ce masa ta gama ba, shi kuma yana can zaune bisa wata kujerar roba a cikin shagon yana jira ta gama gatsine-gatsinen ta tana kallon komai tamkar ta ga kashi, nan kuwa can a kasan ran ta yabawa take yi komai ya yi mata, ta kuma jinjinawa fasahar wanda ya tsara shagon nan. Wasu kayan ma da aka zuba duk gayun ta bata san da irin su ba farkon shigowar su Katsina kenan.
Da ta gama abinda zata yi mota ta koma ta shige ta zauna ta hau danna horn ji kake biiiiii..biiiii..kamar mai kiran kare. Yana jin ta ya yi kamar bai san tana yi ba, ya gama danne dannen sa a wayar sa ya mike ya haura zuwa upstairs na shagon yayi zaman sa. Ya rantse a kasan ran sa sai ya rama shanya shin data yi a gida cikin mota kafin ta fito. In bai manta ba ai jiran awa biyu kwakkwara yayi cikin mota yana jiran ta, to itama sai ta yi shi yanzu.
Bakin ciki da bacin rai a wurin Amani abun baa cewa komai, data gaji da zama sai ta kira Daddy a waya yana dagawa ta hau kuka da balbalin masifa tamkar mai magana da kanin ta. Daddy kuwa cewa yake me ya faru ne Tafisu? Daga ina kike magana? Tace.
Daddy daga cikin motar da wannan Dirty Human Being din ya shanya ni, tukun nama Daddy ka taba zaunar da shi ka gaya masa ko ni wace ce a wurin ka? Shi ba kurma ba shi ba makaho ba amma wallahi sun fi shi ji da gani, mutum dunkumkum sai kace dankali ba um ba um um sai bakar zuciya zaka hada hanyata da shi? Ko bude min mota fa bai yi ba, yanzu haka zaman sama da awanni biyu nake cikin mota har baya na ya fara ciwo. sai ta koma kukan shagwaba wanda Daddyn kadai take yi wa irin sa. Tace.
Daddy in baka zo ka dauke ni da kan ka ba ba zai san matsayi na a wurin ka ba, idan baka kore shi ba dauka zai yi ni yar aikin gidan ka ce, babu wanda ya taba yi min wulakancin da mutumin nan naka yayi min. Amani ta tsinke da fada kamar tsinkakken carbi duk a kan kunnen Mukhy da bata ma san yaushe ya bude motar ya shigo ya zauna ba, bayan ya duba agogo ya tabbata awa biyu ta cika, kuma ko da take ma Daddy wannan balbalin kara fusata shi abun yayi because he respects Alhaji so much, ba zai iya jurar jin ana masa wannan rainin ba. Don haka ya fizgi motar a gujen gaske saida Amani ta zunkuda ta koma ta bugu da kujerar data ke zaune.
Amani ta zuga salati tana cewa Daddy ka cece ni zai kashe ni Daddy ya ce bani Mukhtar din tace Daddy Allah ya sawwake ya taba min waya ya shafa mata bakin hali irin nasa abin nata sai ya koma baiwa Alhaji dariya, ya ce alright, bari in kira shi ya katse kiran nasu ya soma kiran Mukhtar.
Yana ganin kiran Alhaji amma kuma yana tuki don haka saida kiran ya katse. Ya gangara gefen titi ya kashe motar sannan cikin nutsuwa ya bi bayan kiran Alhajin.
A yadda ya tausasa murya ya kuma russunar da kai duk da Alhajin baya ganin sa sai kayi tsammanin da mahaifin sa ya ke magana, ya ce Alhaji muna hanyar dawowa kana son wani abu ne? Alhaji cike da damuwa ya ce No Mukhy, karar ka aka kawo min kala-kala, ka bi ta a hankali ka ji? Ka san wani lokacin haka take abu na yayan fari. Mukhtar ya saci kallon ta sai kumburi take kamar zata fashe ya ce Alhaji ai babu damuwa ina iyawa da ita, musamman da wani lokacin tana abu zayyal majnunah (kamar mahaukaciya), abinda bazan lamunta daga gare ta ba shine rashin kunyar da take maka, ka gaya mata ta dinga maka magana with respect irin yadda yaya suke yi wa iyaye, saboda kai ne gaba da ita ba ita ba. Idan ta cigaba da yi maka magana irin haka bazan kara daukan ta a mota ba.
Alhaji ya ji dadi, ya ce Mukhtar kada ka damu da shirmen Tafisu ka ji? Ka san wanda baida mahaifiya a kusa sai ana masa uzuri Mukhtar yace ni ba zan yi ma ta uzuri da wannan ba, babu uzuri a cikin biyayyar iyaye, in dai a kan daga sautin ta sama da naka ne zan iya bubbuge bakin ta Alhaji Alhaji yayi murmushi yace to shariar taku ta fi karfin waya, ku dawo gida sai mu yi ta a zaune. Kuna ina yanzu?
Yace muna hanya ko rabin isowa gida bamu yi ba. Ni gaskiya Alhaji a gate zan sauke ta, ni kadai zan je na dauko Hajiya, daga can ina da inda za ni Alhaji ya ji wani iri ya ce Mukhtar ban san ka da rashin kirki ba kada ka fara akan kanwar ka ya ce Alhaji sai ta daina yi maka fada zan yi kanwa da ita, in ba haka ba kowa ya yi rayuwar sa cikin gidan nan ba ruwan Yaya da kanwar, bani da zuciyar da zata iya daukan ana raina min kai.
Daga haka ya kashe wayar sa Alhaji na fadin ka dai shigo da ita kada ka sauke ta a gate don Allah ba don halin ta ba.
Duk abinda suke fada a kunnen Amani, mamaki da haushi ya hana ta ko kwakkwaran motsi, anya wannan mutumin bai taki komai ba? Yaya kana zaman yaron gida kake ma uban gidan ka Gadara irin haka shi kuma yana biye maka sai kace uban da ya haife ka? Amani ta saci kallon sa sai suka hada ido, ya kashe ta da harara, yana kokarin cire farin gilashin idon sa don ya sha round din da zai kai su unguwar su. Wani irin kyau ya yi a

1 Comments On AMANI
avatar
nafisa-adamu

9 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment