Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zube qasa a sume, yaya Rafeeq jingina yayi da bango dan shima yanada niyyar fad'uwa, sai dai likita ya zaunar da shi bisa kujera.




likita ya danna wata qararrawa saiga Nurse guda biyu suka kama Hanan suka d'aurata gado sannan suka nufi wani daki da ita da sauri likita yana biye da su.



Dakin da Sultan yake kwance babu wanda yayi tunanin Sultan babu rai har Mami bata gane saboda bata kawo mashi mutuwa ba ko daya.



Saida wata Nurse tashigo tana basu haquri tasa farin kyalle ta lullube gawar Sultan.














*Real Miss J*🙋😘*🎀ADALILIN KANE🎀*

[5/11, 22:04] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀ADALILIN KANE🎀*



*STORY & WRITTEN BY JAMILA SAMAILA YUSUF*


*EDIT BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*




*230-235*





Bayan sun fito, Zuhra tace "su taso suje suci abunci".


Islam kunya ta Kama ta sosae, ji take kamar tace ta k'oshi, to tasan halin 'yan kayansu, tana cewa ta k'oshi zai fara hararar ta.


Iman ko ajiki nta, ai dama so take yaji, cikin zuciyar ta take fad'in hakanan a matsa ma mutum yayi ta karatu, dan kuma ka fad'i abinda yake ranka sai aji haushinka.



Suka isa dinning area, kowa yasamu kujera yazauna, Zuhra ce tayi serving dinsu sannan ta zuba nata ta zauna kusa da mijinta.



Islam ta kasa cin abinci, ko motsin kirki ba tason yi, saboda kunya.


Iman ko babu ruwanta abincin ta take ci hankalin ta kwance.


Bayan sun gama cin abinci, suka koma parlour suka zauna suna firarsu, jefu jefi yaya Rafeeq yana d'an saka baki idan t akama dole yayi magana.



Iman dai tayi tagumi tana jiran yace su tashi ya kaisu gida dan ita ji take kamar saman k'aya take.


Tunda ta zauna babu abinda tace sai Islam da Zuhra ke firarsu dama basu wani saba da hira da yaya Rafeeq ba.


Yaya Rafeeq ya tashi yanufi part dinshi yabar su a porlour.


Yana fita Iman kamar jira take ta turo baki tace "ni fa wlhy na gaji, so nake naje gida, haka kawai an kawo mutun wuri kuma sai faman d'aure mashi fuska ake".



Islam tace "haba Iman, wai me yasa baki da haquri ne, yana fa sane da mu fa".


Zuhra tace "au ba zaku yi min weekend din ba?".


Iman ta ware ido tare da bud'a baki tace "a ina zamu yi weekend din?, ki bari duk ranar da wannan mijin naki ya tafi unguwa to ni da kaina zanzo yi maki hutu bama weekend ba".


Islam tace "ni fa kunyar shi na keji wlhy duk bana jin dadi".



Zuhra tayi murmushi tace "ai sak'o na nan zan bashi".


Islam tace "dan Allah abar sak'on nan wlhy wasa nake yi".


Iman tace "wane wasa, ni fa da gaske nake, amma dai kada a fada mashi".


Gaba dayansu sukasa dariya.



Da marece yaya Rafeeq ya kaisu gida, bayan ya gaishe da Mami da Abba sukayi fira sosae sannan ya dawo gida cike da k'aunar matarshi.



Ranar saturday Islam da Iman sukaje GRA gidan su Aunty Hanan suka d'auko Sultan, sai bayan sallar isha'i sannan driver ya maida shi gida tare da tsaraba mai tarin yawa, dan tin a school duk abinda suka gani na yara sai sunsaima Sultan, ga kuma Mami tasa driver yayima Sultan shopping aka hadashi dasu aka mai dashi gida.



Sultan yaro qarami tare da tarin masoya da farin jini, daga dang n uwa harna uba, yanzu yana da wata goma sha daya haqoranshi hudu biyu sama biyu qasa, kuma yadan fara tafiya kadan, yanayi taku daya biyu saiya zauna.



Kayan wasa wurin Sultan da kayan sawa ba'a magana, Mami ta saya, Mummy, daddy, Abba, Aunty Hanan, yaya Rafeeq da kuma Zuhra, har iyayen Zuhra idan taje gida suna ba dawa akawoma Sultan, amma Hanan bata sani ba saboda da ta sani baza ta ta6a sakama yaronta bayan Zuhra ba.



Ranar Sunday Mummy tasa driver yakai Sultan gidansu,yaya Rafeeq na kwance shida Zuhra sukaji door bell, ya saka jallabiya yafita, yana ganin Sultan dadi ya kamashi dan dama tunaninshi yake.


Shima Sultan yana ganin mahaifinshi ya bude haqoranshi guda hudu yana dariya,yaya Rafeeq ya'anshi Sultan tare da yima driver hasahi kamar yadda yasaba, driver yayi ta godiya yana wangale baki, yayi mashi sallama yatafi.



Tinda yaya Rafeeq yashiga da Sultan, Zuhra ta'anshe shi tanatajin dadi,ta nayi mashi wasa,ta saka shi cikin keken yara tana turashi, Sultan sai dariya yake.


Yaya Rafeeq ya tsaya kusa da ita tare da kwanciya bisa gadon bayanta,yace "kin mance da ni ko?".


Zuhra tayi murmushi tare da juyowa tace "kaima zoka shiga ciki in turaka".



Gaba daya sukasa dariya hada Sultan da bai san abinda aka ce ba.


Yaya Rafeeq yayi kissing din goshinta yace "saidai ki shiga in turaki".


Ya koma bisa kujera ya zauna yanata kallonsu, sai Zuhra ta bashi tausayi cikin zuciyarshi yace "ya Allah ka nunamin 'ya'yan Zuhra, Allah yashirya mani su da sauran yan uwa musulmai".


Zuhra tadauko Sultan tadawo tazauna kusa da Rafeeq tare da rugume Sultan bisa jikinta tana wasa da yatsun hannunshi.


Zuhra tayi murmushi tace "yayana komai na Sultan irin nakane fa, gaskiya kayi ma Aunty Hanan wayau".


yayi murmushi tare da kallon cikin idanuwan ta cike da qaunarta yace "kema ai wayau zanyi maki".


Zuhra takalleshi tayi murmushi cikin zuciyarta tace "ai da naji dadi wlhy".


Yaya Rafeeq yamatso kusa da ita yace "tunanin me kike kuma?".


Zuhra tace"babu komae".



Ya d'aura hannunshi bisa cikinta yace "Allah yasa ina da ajiya cikin cikin nan".


Zuhra tayi murmushi tare da boye fuskarta bayan Sultan.



yaya Rafeeq yayi murmushi yace "ni fa kullun addu'ata Allah ya nuna min yaran ki mata na Zuhra beauty".


Zuhra tace"Allah yakawo nagari toh my only".


Yace"ameeen my wife".



Yace "kinga dama ina so yau muje mu gaishe da su Mama".


Tuni fara'a ta cika fuskar Zuhra tace "kai amma naji dadi wlhy, dama abinda nakeso na tambaya kenan".


Yaya Rafeeq yace "kinga daganan sai muje ki gaishe da Mummy ko?".



Fuskarta tayi gwanin tausayi tace "wlhy yaya Rafeeq ina tsoron Aunty Hanan".


Ya kama hannunta ya hada da nashi ya rintse ya fara lallashinta cikin kulawa yace "babu abinda zata yi maki Zuhra, ki kwantar da hankalinki".


Zuhra tafara shiri, bayan taqara yima Sultan wanka ta saka mashi kaya, yayi bacci itama taje tayi wanka ta shirya cikin wani swiss boyel lace pick mai zanen flower black tayi kyau sosae.


Bayan tagama shiri tana fesa turaruka masu qamshi yaya Rafeeq yashigo cikin shirin tasa shadda galila ruwan sararin samaniya hada hula yayi kyau sosai, kamar wani balarabe.



yana ganin Zuhra dasauri ya rungumeta tabaya yace "kinyi kyau sosae,inama zama zamuyi agida inta kallon wannan kwalliyar taki".


Zuhra tayi murmushi tace "k'amshinka shine ya tababbatar min da kaine mijina na haqiqa da ban sameka ba da sai an ta yimin jaje, amma nagode ma Allah daya bani kai mijina mai qaunata tsakani da Allah, ina sonka sosae,bani fatan abinda zai rabani da kai".



ya lunshe ido biya bayanta kafin yasaketa, suna yin ido hudu, Zuhra tace "masha Allah, gaskiya har kishi ya kamani".


Yaya Rafeeq yace "nami fa?".



Zuhra tace "na matan da zasu ganka mana".


Yayi murmushi yace "ki kwantar da hankalinki, Rafeeq naki ne ke daya".


Zuhra tace "idan kan ya faru zanji dadi, amma yaya Rafeeq kasan Aunty Hanan tana sonka sosae, kuma idan nabar Sultan a haka iyayenshi na rabe ban yima kaina adalci ba.......".


Badan ta so ba dan dole tayi shiru sakamakon d'aga mata hannu da yayi, ya daure fuska yace "idan kin gama shirin ina jiranki a house premeses" yafita ba tare da yaqara cewa komai ba.




Mayafinta ta dauka tare da jaka, sannan ta sa'bi Sultan a kafad'arta ta fita, ranta babu dadi.


Koda ta'isa house premeses, zaune yake cikin mota Anaconda 2018 ruwan sararin samaniya, ta bude motar tare da sallama tashiga, sallamar kawai ya'ansa amma bai kalli inda take ba.



A haka suka yita tafiya babu wanda yayi magana, har suka tsaya wani supermarket tayi parking ya fita, yakawo abinda zai sawo masu aiki suka saka mashi akin boot sannan ya sallamesu ya shigo mota suka tafi.




Zuciyar Zuhra cike da tunanin yaya Rafeeq daga fad'in gaskiya sai fushi, ita ta rasa inda zata saka kanta.


Fuskar Sultan take kallo wanda yake ta faman baccinsa, tausayinshi ya kamata, bata san lokacin da hawaye suka zubo bisa fuskar Sultan ba daga cikin idanuwanta.


Tasan tabbas idan Aunty Hanan ta dawo, itace za tasha wahala, amma duk da haka, tana son tazo tariqe yaron ta, saboda cikin abubuwan da suke ma Zuhra tausayi, su tada mata hankali harda taga yaro baya tare da mahaifiyarsa gashi yaya Rafeeq yace da an yaye shi zai anshi abin shi.


Zuhra tasa hannu tagoge hawayen da suka qara zuboya mata,sannu hawayenta,tada Sultan daga bacci.


Yaya Rafeeq ya samu wuri yayi parking din motarshi a bakin titi.



Bayan yayi parking ya busar da wani iska mai zafi daga cikin bakinshi sannan yabige sitiyari, ya juyo yana kallon Zuhra ranshi babu dadi.


A hankali yake magana yace "amma kin san babu abinda na tsana irin zubar hawayenki ko?".


Zuhra ba taace mashi komai ba, ta fara qoqari tsaida hawayenta amma ina, dama gata sarkin kuka ga tausayi.



yace"kinga idan bakibar wannan kukanba wlhy zani juya motar inbaidake gida sannan ni intare ingaishe da su".


Tasamu hawayen suka tsaya,sannan yatada mota yatafi.



Suka isa unguwarsu Zuhra, mai gadi ya bud'e masu gate suka shiga, Alhmdllh gidansu Zuhra yyi kyau babu laifi dan in ba wanda ya sani ba, ba wanda zaice su Zuhra sun ta'ba talauci a duniya.



ya samu wuri yayi parking, sannan suka shiga, Mama ce suka tarar a porlour tana kallon tashar Africa tv 3.






Murna cike da fuskarta ta'anshi Sultan, suka zauna cikin jin dadi.


yaya Rafeeq ya zauna qasa tare da gaishe da Mama cikin girmamawa, Mama ta'ansa tare da saka masu albarka.




suka dan taba hira, Mama tace "gashi kun yi rashin sa'a Baban naku baya nan".


Rafeeq yace "ai zan dawo daukarsu zuwa anjima insha Allah".



Mama tace "Zuhra tashi kawo mashi abinci da lemu".


Rafeeq yace "Alhmdllh Mama nagode".



Zuhra tace "idan yadawo zamuci Mama".


Mama tace "toh Allah ya dawo da shi lafiya".


Bayan yayi masu sallama yafita, yayi ma mai gadi magana, ya fara shigo da kayan da ya sawo masu, kayan lashe lashe da tande tande da ruwan roba da sauransu.




Mama tai ta saka mashi albarka, tare da godia.



suka shiga firar su irinta tsakanin uwa da diyarta, nan mama ke fad'a mata duk ranar juma'a sai Rafeeq yazo gaishe da su tare da kud'i masu yawa.



Zuhra taji dadi sosae ko babu komae yaya Rafeeq ya damu da iyayenta kuma bai ta'ba fad'a mata cewa yana zuwa gaishe da su ba.


Mama tace "Zuhra, ya naga idanuwan ki kamar kinyi kuka?".



Zuhra tace "wlhy Mama yanzu da zamu taho daga nayi ma yaya Rafeeq maganar dawowar Aunty Hanan,shikenan yayi fushi".



Mama tace "banda wannan kuma fa?, akwai abinda yake yi maki?".



Zuhra tace "wlhy Mama idan nace ga abinya yaya Rafeeq yayi min marar kyau nayi qarya, wannan dai maganar ce kuma itama yaune mukayi ta da shi".



Mama ta tausasa murya tace "Zuhra tunda baya son wannan maganar, kibar yi mashi ita, ke dai ciki gaba da addu'a Allah ya tabbatar maku da alkairi, kuma idan Allah ya qaddara Hanan zata dawo to babu makawa zata dawo, idan kuma babu rabon dawowarta to ba zata dawo ba, kedai ciki gaba da addu'a".



Zuhra tace "toh Mama, insha Allah zan ci gaba da addu'a".



Mama tace "Allah yayi maku albarka, kema kuma Allah yabaki zuri'a tagari".



Zuhra tace "ameen Mama".


Zuhra ce ta dafa masu abincin dare, tuwon shinkafa da miyar agusi tare da farfesu yan ciki da kan rago, sai lemun kwakwa wanda yaji madarar gwangwani da ruwa da lemun ayaba wanda yaji youghout.




Haka su ka sha yinin su sannan sukayi wanka, ita da Sultan dama tasaka mashi kayanshi da pampers cikin jaka.



Bayan sallar magrib sai ga yaya Rafeeq ya dawo daukarsu, dama su sunci abincinsu yaya Rafeeq yaci nashi har ya gama Baba bai dawo ba.




Bayan yaya Rafeeq ya gama, saiga Baba yadawo cikin motarshi 406 baqa, suka gaishe sosae cikin jin dadi, sannan Mama ta fada ma Baba abin da kawo masu.



Baba yace "yo kai Rafeeq baka gajiya da hidima da mu?".


yaya Rafeeq yace "wlhy Baba babu komae, idan banyi maku ba wazai yi maku".



Baba yayi ta saka masu albarka sannu sukayi sallama suka tafi.





Saida suka fara zuwa gida wajen Mami, Zuhra ta gaishe da Mami cikin girmamawa Mami ta'ansa tare da jin dadin ganinta, ta d'auki Sultan.


Islam da Iman suka ja Zuhra dakinsu suka dan fara hira, Mami da Rafeeq suna porlour, Sultan ne yafara rigima, Mami ta kira Islam.


Mami tace "zoki dauki abinku".



Islam tayi dariya tace "kaji abinda matarka tafadi wai in dauki abinmu ko?"


Sultan kamar yana jinta sai yafara qoqarin zuwa wurin yaya Rafeeq, wai wajenshi zaije.



Islam tace "iyeh kaga masu uba, to tafi".


Tare da miqashi tana fadin kaqara zuwa gidan kasameni ai.


Mami tace "ai ni da mai gidana bamu rabewa har yaqi Aunty saboda ni".



Islam tayi dariya tace "Mami saboda daddy din dai".




Mami tace "gobe da safe Katsina zani je dan haka da mijina zanje".



Mami tace"yawwa kaga sai ka biyo ka tafi da su school ko, gashi Iman ta matsa abamu mota sutafi da ita".



yaya Rafeeq yace "Mami kema kin goyi bayan a basu mota?".



Mami tace "ai Abban ku yace sai anji ta bakin ka".



Yaya Rafeeq yace "wa zai ba wa'annan yaran mota, yaran da basu san ciwon kansu ba".


yaya Rafeeq yaqi ba da goyon bayan a basu mota.



Bayan sallar isha'i Abba yadawo lokacin yaya Rafeeq yadawo daga masallaci, bayan sun gaisa Abba ya dauki Sultan,sun dan dad'e a gidan sannan sukayi sallama suka tafi.




Babu inda suka tsaya sai gidansu Hanan, duk da dama Hanan tana ta zaman jiran dawowar Sultan amma ranta bai ba ta harda Zuhra za'azoba.



koda sukayi parking harabar gidan, suka shiga cikin parlour, babu kowa sai Asabe mai aiki ta dake ta fatan gyaran porlour.



Bayan ta gaishe da su, tayi ma Mummy magana.


Babu 'bata lokaci Mummy ta fito fuskarta d'auke da fara'a tare da murnar ganin Zuhra a gidansu.


Mummy ta samu kujera ta zauna tare da cewa ''ku dawo bisa kujera ku zauna mana kamar wasu baqi.


suka zauna bisa kujera sannan suka gaishe da Mummy, Mummy ta'ansa cikin jin dadi.


Bayan sun dan taba fira, Mummy ta'aika akira mata Hanan.





Bata jima sosae ba sai gata ta fito, cikin shigar riga da wando na bacci dan ita har tayi shirin kwanciya.



Sultan yana ganin Hanan yafara qoqarin kwace kanshi daga hannun Mummy yanason zuwa wajenta.


Hanan tana ganin d'anta tafara murmushi tace "babyna tun d'azu kai nake jira muyi bacci" tasa hannu ta'anshi Sultan dan ita bata lura da wasu mutane ba.



Mummy tace "Hanan baki ga yayanki ba da kuma Zuhra?".


Da sauri Hanan takalle su tace "sannunku da zuwa".



Zuhra ce ta'ansa tace "yawwa, Aunty Hanan kin wuni lfy?".



Hanan tace "lfy ya karatu?".


Zuhra tace "Alhmdllh"


Hanan ta kalli Rafeeq tace "yaya Rafeeq ina wuni".


Yace"lfy".


Yace "Mummy mu zamu koma gida".


Mummy tace "ko ruwa baku sha ba, Hanan a kawo masu ruwa mana".




Yaya Rafeeq yace "Alhmdllh Mummy daga gidansu Mami muke".


Zuhra ta fiddo turaruka guda biyar masu tsada ta bada aba Sultan.



saida Mummy tayi da gaske sannan suka sha lemu da ruwa suka tafi.


Bayan sun koma gida sunyi wanka sukayi shirin kwanciya dama sunci abinci gidan Mama, suka d'an taba fira sannan suka kwanta.



Da asuba Mummy ta kira wayar yaya Rafeeq, ta fada mashi suna asibiti Sultan babu lafiya.



Hankalinshi ya tashi sosae, dama yayi sallah, ya fadi ma Zuhra sannan ya tafi, Zuhra tayi yunqurin bin shi, amma yace tabari idan ya dawo sai su tafi idan ba'a sallamesu ba.


Zuhra harda kukanta, tausayi Sultan take ji sosae.



Yaya Rafeeq yana zuwa asibitin su Mami da Islam da Iman suna isowa.


Idanuwan Hanan sunyi luhu luhu sunyi jajir abin tausayi, Islam da Iman suna ganin Aunty Hanan suka fara kuka.



Mami ta fara yi masu fad'a, su da za suyi addu'a kuma su kwantar ma da Hanan hankali shine zasu qara saka mata damuwa.



yaya Rafeeq ya rude, hankalinshi ya tashi da yake yasan likitan dake kula da yara kuma asibitin Mami ne, ya bi bayan Mami suka shiga cikin office din likitan.



Suka tambaya zasu iya shiga su ga Sultan?.


likitan yace "eh amma banda hayaniya plz".



yayi masu jagora suka shiga dakin, likitoci biyu ne kan shi, amma ba hausawa ba, lokacin da suka shiga sun gama gwaje gwajensu,suka fito su Mami suka shiga.



TUni d'akin ya cika ciki da dangi da abokan arziqi, duk wanda yaga Sultan sai ya zubar da hawaye irin yadda cikin dare daya Sultan yakoma.




Hanan ko saida aka riK'eta saboda juwa take ta gani.


likita yace "yana son ganin iyayen Sultan".



Rafeeq da Hanan suka bishi office, likita ya dafa Rafeeq yace "Rafeeq kayi haquri sakamokon chlora da taci qarfinshi sai dai kuyi haquri Allah ya anshi abin shi".



Ai Hanan tuni ta zube qasa a sume, yaya Rafeeq jingina yayi da bango dan shima yanada niyyar fad'uwa, sai dai likita ya zaunar da shi bisa kujera.




likita ya danna wata qararrawa saiga Nurse guda biyu suka kama Hanan suka d'aurata gado sannan suka nufi wani daki da ita da sauri likita yana biye da su.



Dakin da Sultan yake kwance babu wanda yayi tunanin Sultan babu rai har Mami bata gane saboda bata kawo mashi mutuwa ba ko daya.



Saida wata Nurse tashigo tana basu haquri tasa farin kyalle ta lullube gawar Sultan.














*Real Miss J*🙋😘*🎀ADALILIN KANE🎀*
[5/11, 22:04] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀ADALILIN KANE🎀*



*STORY & WRITTEN BY JAMILA SAMAILA YUSUF*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*



*235-240*



Saida wata Nurse tashigo tana basu haquri tasa farin kyalle talullu6e gawar Sultan.


Islam ji tayi kamar saukar aradu,kamar wani mafarki,hankalinta yayi mugun tashi sosae.


Iman kuwa kuka tafasa mai bantausayi,tarasa inda zata saka kanta.


Mummy ce tarungumeta tana lallashinta tare da bada haquri duk da irin d'acin da rad'ad'in da takeji cikin zuciyarta.


Mami banda salati babu abinda takeyi takasayin komae,ga wasu zafafan hawaye da suke zubo mata.


Mummy ce tafiddo wayarta daga cikin jaka,tashiga kiran layin Daddy domin tasanar da shi rassuwar,dama kuma yayi tafiya zuwa Abuja,amma tinda Mummy takirashi da asuba tafadi masa rashin lafiyar Sultan yafara neman biza zuwa Kano.


Tinda aka fita da Hanan,yaya Rafeeq yake tsaye yakasa ko motsin kiriki.


Doctor yayita fama da shi akan yazauna saboda yaga kamar yanada niyyar fad'uwa.


Amma yaya Rafeeq yace zai'iya tafiya babu komae.


Dole Doctor yabarshi yafita.


Jikinsa babu qwari yake tafiya,kamar wanda qwai yafashe mawa ciki.



Yana isa bakin room din da Sultan yake,yakasa shiga yayi kamar 5mins agurin kafin bude qofar,yayi sallama sannan yashiga.



Yana shiga kowa yamaida attension din kansa,cike da tausayawa.


Mummy tace"Rafeeq kuyi haquri kaji,Allah yabamu haqurin rashinsa".


Mami ce takira wayar Abba tafada mashi rassuwar Sultan.


Hankalin Abba yatashi sosae,lalle rayuwar duniya abin tsoro ce.



Wayar yaya Rafeeq ne yashiga ruri,hannunshi yayi mashi nauyi hakanan yasamu yad'auki wayar.


Zuhra ce hankalinta duk yabi yatashi tinda yaya Rafeeq yafadi mata,Sultan babu lafiya take kuka har yanzu ko breakfast batayi ba.


Takira wayar Mama tafad'a mata Sultan yana asibiti,itama Mama hankalinta yatashi sosae.



Cikin disashshiyar murya take magana tace"yaya Rafeeq tin d'azu nake kiran wayarka baka daukaba,ya jikin Sultan din ne?,Dan Allah yaya Rafeeq inason inzo inganshi,ince driver yakawoni?".



Yaya Rafeeq yadan saki murya yace"Inacan wurin Doctor ne,kawai driver yakaiki gidan Mami,jikin Sultan da sauki yanzu zamu dawo amma gidan Mami zamuje kinga saimu had'u acan".



Zuhra tace"toh shikenan bari inyima driver magana,Allah sarki Sultan d'ina kace inayi mashi sannu kafin muhad'u".



Yaya Rafeeq yace"zaiji sosae"tare da kashe waya.



Mami tace"Rafeeq ina Hanan?,naga ban gantaba ne".


Yaya Rafeeq yace"anyi admitting dinsa".


Mami tace"lafiya me yafaru kuma?".



yaya Rafeeq yafadi mata duk abinda yafaru.


Saboda kawaici irin na Mummy komae bata ceba,saida Mami takama hannunta suka tafi room d'in da aka kwantar da Hanan.


Babu 6ata lokaci Zuhra tasa driver yakaita gidan Mami,amma abin mamaki tararar da gida cike da mutane,maza awaje ansaka Canopy.


Kanta yakulle hakanan take tafiya,ranta sai fama saqa mata abubuwa yake.


Hakanan tashiga cikin gidan,tana shiga porlour taci namma taga mutane anyi jigun jigun,bayan tagaishe da su tamu wuri tazauna.



Abba yazo asibitin tare da driver aka tafi da gawar Sultan tare da su Islam da Mummy.


Mami ce tazauna asibiti jinyar Hanan.


Haka su Mummy suka tarar da mutane daga qofar gida har cikin gidan.


Islam da Iman na ganin Zuhra suka qara fashewa da kuka,hankalin Zuhra yaqara tashi saboda tinda tazauna babu wanda taji yayi maganar rassuwa.


Zuhra tatashi taje kusada Iman,zuciyarta a razane tazauna.

Idanuwanta na zubar da hawaye,mata da yawa sai kallonta sukeyi,wasu na tausaya mata, wasu kuma sunajin haushinta yan uwan Hanan kenan.



Ahankali take magana tace"Iman lafiya?, dan Allah kifada mani abinda yake faruwa".


Iman tana kuka tace"Sultan yarassu Zuhra saidai muyi haquri,Sultan yatafi yabar...........".



Tin kafin ta'ida fadin abinda yake bakinta,Zuhra tafadi asome.



Iman taqara sautin kuka tana kiran sunan Zuhra,rabin matan dake zaune porlour sukayo kanta.


Haka akayima Sultan wanka aka kaishe makwancinsa(Allah yasa mucika da imani,amin).


Lokaci kad'an yaya Rafeef yafita hayyacinta,ya rame fuskarshi cike da damuwa.



Zuhra tana farkawa taganta bedroom din Mami kwance bisa gado,Islam da Iman ne kusa da ita sunyi tagumi.


Fuskarsu takunbura idanuwansu sunyi jawur da su.


Zuhra tafara qoqarin tashi zaune,da sauri Iman tazo tatemaka maka tashi zaune.


Zuhra tafara magana cikin muyar kuka tace"ya Allah kasa mafarki nake,wannan mummunan mafarki,Islam dan Allah kada kuyi fatan kuyi irin mafarkin da dani har qarshen rayuwarku,ina Sultan yake?,dan Allah kukawomin shi".


Iman tafasa sabon kuka,har saida Mummy da Mama suka shigo cikin bedroom din.


Islam tace"Zuhra ba mafarki kikayi ba,da gaske ne Sultan ya'ansa kiran mahalicci,saidai muyi haquri".


Zuhra taci gaba da kuka kamar ranta zai fita,Mummy da Mama suka shiga lallashinsu amma sunqi suyi shiru.


Ashe dama amfadima Baba rassuwar,shi kuma yasanadda Mama,amma koda sukayi waya da Zuhra basu nuna mata cewa sun sani ba.


********


Asibiti ko da Hanan tafarka saita fara surutai kamar wadda tasamu ta6in hankali.


Saida akayi mata allura tasamu bacci sannan aka samu sauqi.


Har'aka gama zaman ukku Hanan tana asibiti sauki saiga Allah,hankalin kowa yatashi sosae ga kuma tausayinta da mutane sukeji,ga rassuwar Sultan ga kuma ciwon dake damunta.


Bayan sati daya,Mummy da Daddy suka yanke shawarar afiddata abroad.


Hanan tasamu mental retarded,aka fara shirye shiryen fitarda ita waje domin aduba lafiyarta.



Sun shirya komai tsaf, tare da Mummy suka tafi duk wanda yaga Hanan saiya tausaya mata cikin halin da take.

Duk abinda Zuhra tad'auko na Sultan shikenan ranar babu zama lafiya.


Ita da yaya Rafeeq sunfita hayyacinta ,sun rame kamarba suba duk farin cikin da suke ciki ada yanzu babu.


Iyayensu sun lura da halin da suke ciki,Abba da Mami da kansu sukazo har gida sukayi masu nasiha akan suyi haquri,Allah yasan dalilin yin hakan,sannan Abba yace duk abinda sukasan na Sultan ne suje suyi sadaka da shi ko zasu samu sauki.


Bayan tafiyarsu,yaya Rafeeq yashiga parking din kayan Sultan domin yabi maganar da mahaifinsa yafada mashi.


Nanfa Zuhra tashiga kuka tana roqonshi akan yabarmata kayan bazata qara tada hankalinta bayi mashi alqawari.



Yaya Rafeeq yace"Zuhra nalura kayan nan suna qara tada maki hankali,kamar fiddasu zaifiye mana".


Zuhra tace"dan Allah yaya Rafeeq kataimaka min kada kafidda kayan nan,wlhy idan ina ganinsu suna d'ebemin kewar Sultan d'ina".


Yaya Rafeeq yace"ai banda pic dinsa zan fidda fa,kayan wasa akawai da kayan sawa".


Zuhra tace"toh shikenan,mijina yadda kace haka zakayi"


Haka aka kwashe kaya masu yawa akayi sadaka da su.



Watan Hanan biyu a asibiti qasar turai,ana kula da lafiyar Hanan,Alhmdllh dan yanzu da sauki ba kamar da ba.


Dukda ana waya da Mummy,amma saida Mami da Abba sukayi shirin zuwa ganinta,Abba yacema yaya Rafeeq yashirya atafi da shi.



Ba dan ranshi nasoba haka yashirya aka tafi da shi,kwansu ukku suka dawo,jikin Hanan yayi sauki sosae har amfara maganar sallamarsu.



Watansu ukku a London suka dawo gida Nigeria,amma har lokacin Hanan saita dauko kayan Sultan tarungume tayita kuka kamar qaramar yarinya.



Yan uwa da abokanan arziqi sukayita zuwa yimata ya jiki.



Hakama Mami da Abba da su Iman da Islam sukaje ganinta da yake lokacin anyi hutun second semester suna gida.


Zuhra kau saida tayita roqon yaya Rafeeq sannan yakaita taganota tare da yimata ya jiki.


Hanan tarame sosae,saida jikinta yayi kyau sosae taqara fari kamar ba itaba.




Mummy da Daddy sunji dadin zuwansu,sukayita saka masu albarka.




Bayan wata hudu da dawowarta asibiti jikinta yakoma normal tayi kyau saidai tari damuwa da tinani,masoya sai faman zuwa sukeyi masu sonta da aure kuma masu kudi masu ji da kansu hada dan ministan kudi amma basu dameta ba.



Mummy tayita fama da ita akan tafita sugaisa amma bata zuwa,saidai tarabu da ita,gashi dama likita yace kada abarta cikin damuwa,saboda ciwon zai iya dawowa sabo.



Kullum addu'ar Mummy itace Allah yakawo masu tafita akan wannan al'amari.




Yanzu zaman Zuhra da yaya Rafeeq yadawo normal saidai abinda ba'arasa ba.


Haqiqa Zuhra tanajin tausayin Hanan,dan wani lokacin idan tazauna tayi tinanin irin yadda Hanan keson yaya Rafeeq tin tana yarinya kafin tasan me nene so,da kuma irin yadda yake nuna rashin damuwarsa akanta ga kuma rashin yaronta da tayi ga kuma ciwon daya sameta duk adalilin yaya Rafeeq har kuka takeyi.



Tana tinanin da itace haka tafaru da ita ya zatayi,sai taji wani sabon tausayinta yakamata.



Aunty

Please Login or Register in order to submit comment