Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*🌹RASHIN SANI🌹*

*by oum yasmeen*

inkinsan bazaki comment ba dan Allah ƙar ki shiga iya mata zallah sanna sai kin tora group ukku kafin kishiga kina torawa zai buɗe

https://chat.whatsapp.com/Hz9SPZ73qsq4oWXLw0V5SY

marubuciyar

AFIF

YA ƊIN MAGE

Bismillaahir Rahmaa-nir Raheem

*Page 1-2*

"tun daga ne sa in ka kalli building din makarantar kasan makaranta ce ta ya'yan manya ce iya tsaruwa ta tsaru tamkar ba a ƙasar nan kake ba gaskiya mai makarantar nan ba ƙaramin attajirine
S.D.giwa midwifery and nursing da ke kano da sauri ko wanne dalibi yake fitowa daga hostel saboda ƙarfe 7:30 kowa ya shiga aji cikin hostel ɗin na shiga aikuwa naga duniya domin tundaga reception ɗin nasan cewa an kashe dukiya wasu irin kujerune na gabion akajere su a waje ga wasu irin bishiyu masu kyau da yake lokacin sanyine iska sai kaɗawa su take shiga cikin reception ɗin nayi wasu ma aikatane suna zaune sai danne danne suke a computer ga wata web camera sai aiki take gawata ƙatuwar tv sai nuna abin da ake awajan da shige da fican dalibai kusan hawa biyar ne awajan duk hostel ne hostel A,B,C har D duk wanda yaje d ya kusan fita daga makarantar na maza daban na mata daban hawa na ɗaya nayi inda na shiga room three wata yarinya nagani tana kwance ta lulluɓa da wani blanket mai uban taushe sai duk ta rufe jikin ta da sauri wata budurwa bazata huce shekara goma sha taraba tana sanyi da farin hijab iya kirjin ta hakama rigar ta fara wandon ta blue kayanta sunci guga ga school bag pink color kusa da gadon ta tsaya ta fara tashin wacce take kwance fanna fanna fanna 7:30 fa kinsan muna da lecture kinsan da huri muke shiga aji amma kin sami gu kin kwanta

"da sauri ta tashi tana sanye da kayan sanyi masu kauri gashin ta duk ya har gitsai har gadon maba fara ce tas yawa ka taɓaa jini ya fito ta na da madedecin baki lips ɗin mai dan tudu kadan bakin ta dan ƙarami gwanin ban sha'awa ga wasu manyan idanuwa dara dara girar ta har haɗewa take sabuda gashin ta baƙi siɗik hancin ta yana da tsayi daidai misali wanda ya ƙawara duguwar fusƙar ta kyau bazata huce shekara goma sha takwas ba duk wanda ya kalle a ba zai so ya ɗauke idon sa ba akan ta domin ta dauko kyahun barebari na usul baggara dafe kirji tayi tace da hausar ta da bata fita tace

"na shiga uku kar sir yusif birnin kudu ya shiga ƙinsa aƙwai baƙin hali duk da abokin sa ya fisa ,

kinga fanna ki sauri kiyi wanka ki shirya mu tafi bana son surutu

"kinga inkin ga zan ta kura ki ki tafi ai daman dan garun kune dole kiyi kishin sa kinga na taɓa dr giwa kin fara kunfar baki ga ƙanin abba ko sa ta shiga banɗaki?"

"lalle yarinyarnan kinji hausa ni kike faɗawa haka kinci sa'a ammy da abbie a hannu na suka ɗamƙaki da yau na tafi na barki kujerar dake gefe ta jawo ta zauna ta fito da wayar ta iphone 14 tana dannawa daure da towel ta fito da sauri ta dauki hair dryer domin busar da gashin ta

au yanzu sai kin tsaya busar da gashi fanna we me isa kikeso idanuwan dr giwa ya fara kaiwa kanmu kinsan fa wallahi ba yason makara yana tsaye akan mu da malaman da suke koyar damu

Laila yanzu so kike in tafi gashina na zubda ruwa haba laila a dinga yin na Allah mana

"fanna yanzu da abunnan na hanci zaki fita kinsan fa an hanamu sa abun ado,

wayyo lailah giwa yanzu ɓulal hancin da tun da aka haifan akai min sai kice sai na cire barima ta tab wallahi yayi abin da ya gadama yawa ba prevent school ba fi'ilin sa yayi yawa we dan Allah in tambaye ki ?"

da hallacan ki sauri

Hmm tace mata da sauri ta sa irin kayan da ke jilin laila sai de ita jakarta sky blue ce ta sayan ya madedecin glass mai kyau da alama medical ne sai ya ƙawata fusƙar ta wayar ta ta ciro dake chaji tace

"muje lailah giwa ta shi tayi ta zura wayar ta a jaka ta rataya ta ta saki ɗaya hannu jaƙar wata ash color mota ce ta tawo aguje da alama mai motar sauri yake yayin da ya tada ƙura har ta sauka akan fararan kayan fanna wanne shegenne ya baɗamin ƙurah ai bata ƙarasa ba taga wanda ya fito zaro dara daran idanun ta tayi yayin da futsari ya kusan zubuwa lailah domin ta tabbata ya jita ……………✍🏼



*🌹RASHIN SANI🌹*



*🫧story*
*and writing🫧*

*🎀Oum yasmeen🎀*

*IN FA BANA GA NIN RUWAN COMMENT ZAN MAI DA SHI PAYMENT DOMIN BA ZAI YIHU BA ANA WASA BABU DARIYA BA*
💃💃💃💃💃

https://chat.whatsapp.com/Hz9SPZ73qsq4oWXLw0V5SY
*wannan group ɗina ne a kwai lokacin da zan dena posting a kowanne group sai a nawa in kuka shiga inga ruwan comment ko in mai dashi payment*

💞💞💞 💞💞
💞💞💞 💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

3-4

"""""na shiga ukku fannan shikkenan baƙin ki yau ya jamana kin san waye acikin motar nan kuwa ?"

cikin tsiwa ta murguda baki tace

ko ma waye ba ya ganin gaban sa ya baɗa mini kura jibi fa kayana yarda sukayi nasan wannan alhuda hudar ne mai baƙar zuciya

Dafe girji lailah tayi domin ta rasa wacce irin tsana fanna buƙar gana tayiwa dr giwa ko ba komai ai dr giwa yayanta ne domin da baban shi da baban ta uwa daya uba daya fannan tana girmama kowa na dangin giwa ban da dr giwa
abu ɗaya tasani fanna bata son makarantar kwana sai gashi an kawota in tayi mata fada sai tace da be buɗe makarantar shi ba da ba a kawo ta da ƙyar ta i ya buɗe baki tace

"dan girman Allah fanna kiyi shiru kinga fa yana ƙoƙarin fitowa ai kuwa bata rufe baki ba sai gashi ya fito kallo daya nayi mai ban so in dauke ido akansa ba chocolate color ne irin black american ko kuma ka ce ethopian color shi ba fari ba ba koma ka kirashi bakiba wane irin farine da shi idanuwanshi suna sanye da baƙin glass ga wata iriyar ƙasumba ta sha gyarah sai sheƙitake yana sanye da suit baƙa inda ya samata fa'ar shirt yana sanye da wando baki yayi kyau yawa ƙar kadena kallosa a kuma tunsa na dama yana da wata tawadar allah wacce ta ƙarawa fusƙarsa kyau hannunsa ruƙe da lab coat da wasu files ahannusa yayi da sir yusif birnin kudu ya roƙemai jaka da alama magana suke mai mahimmanci jan


Laila tace

"Fanna zu mubar gunnnan ,

naƙi wallahi ko ba yau ba sai na rahama dan rainin hankali mai ido yawa na mujiya

hmmm fanna ai kida shi baku da maraba yana da ido kina dashi wallahi wani zubin ganin ki nake kina kama da family ɗin giwa

Allah ya kiyaye inyi kama da shi jibe shifa tsoho dashi yo ba dole yayi baƙar zuciya ba antsufa ba aure dole abubuwa su dame shi

rufe mata baki tayi karaf a idon sir birnin kudu yace lailah giwa ku zo lafiya kike janta yawa wasu yara

wata uwar harara fanna ta yiwa lailah kamar idonta zai waɗo ƙasa sum sum sum ta tafi duk da ji take ka mar ta koma hostel ta canzo kaya gawata yunwa da take ji daman bata karyaba suka fito sai anjima sai sudawo suyi girki su koma makaranta haka lailah ta take mata baya tsugunawa sukai da ƙƴar suka haɗa baki wajan cewa

Good morning sir daga haka su kai shiru sukayi yayin da dr giwa ko arzukin kallo basu samu ba yan mata da yawa na makarantar sun mutu akan son sa

sir birnin kudune ya amsa yace

"lailah lafiya kuke faɗa kida aminiyar ki ?"

Cikin tashin hankali har tana rarrabe magana alamun ba gaskiya tace

Sir ba-komai ke fannan tashi mutane fi aji

aa ai ban sallame kuba in ke yar barno ya akai ake janki kike turjewa da alama de jinin secondry yana jikin ku ya kafe ta da idanuwa

Wani baƙin cikine ya tokare zuciyar fanna ga wani rainin hankali shiru tayi tana wasa da yan yatsunta zara zara

cikin deep husky voice ɗinsa ako yaushe yace

"ke ciro abin da ke hancin ki ,

Da sauri ta dago ta kalleshi wato shide wannan tsohon duk inda aka haɗa hanya da shi matsalane yanzu duk irin dukiyar da yake da ita sai ya karɓi gold ɗin da befi na dubu dari biyar ba yanzu inta koma gida ta cewa ammi me inta tambaye ta yana ina domin da za atawo da ita sai da ta ƙarba ta ajiye a gunta saboda sun karanta roles ɗin makarantar sunga ba ado ba sa abin hannu balle sarka ba yin kunshi to sai tayi da bara ta je ta dauko abarta cikin sassanyar muryar ta kamar sarewa cikin shagwaɓa tace

"sorry dr ,

Tsawa ya daga kamata aikuwa tuni hawaye ya fara zarya afusƙarta da sauri ta tashi ta rumgumai lailah ta fara kuka

Lailah ciro min abin da ke fusƙarta

"TO, to yaya giwa da sauri ta dago fusƙar ta ta fara cirewa kash barimar irin me ƙawanyar nan ce kunsan da huya sata da cire ta abin ka da farar fata tuni hancinta yayi ja ana cirewa ta ja da baya ta kifa ƙanta amotar sa ta saki kuka mai cin rai

ungo

okay ya sa hannu ya amsa motar sa ya shiga ya ajiye ta sannan ya dubi sir birnin kudu yace

ni zan shiga office nan da anjima zani giwa hospital dayake bani sa da makarantar taci kima ana iya shiga

"okay afito lafiya,

tafiya ya fara tamƙar mai tasauyayin ƙasa da nutsuwa tambas kamiline kuma muskili mai kafiyar zuciya ba macan da zata same shi amatsayin miji ta kusheshi

yanzu yar barno kihi haƙuri zan yimai magana insha Allah zai baki kinji

cikin kuka tace

ɗazu ya baɗamin kura yanzu kuma ya kwacemin abuna

dokar makaranta ce haka yar barno ba mukula ba muna saurine kihi haƙuri

tashi tayi daga kifa kan datayi idanunta sunyi ja saboda kuka tace laila zo mutafi

cikin tsokana yace lailah kama hannun babyn ki naga alama yar rigima ce daga magana sai kuka

dan Allah fanna kihi haƙuri insha Allah dr giwa zai baki

kinga lailah bara in je hostel inshirya kinga naɓaci da gudu ta bar gun tanufi hostel yayin da laila tabita

wannan kenan

yana shiga office ɗinsa ya tararda aiki da yawa zama yayi ya fara duba abin da ke gaban sa cikin rashin sani ya kai hannusa dede hanci sa wani dogun tsaki ya ja we wannan rigimammiyar yarinyar tun ɗazu yake zuwa toilet yana wanke hannunsa amma oud ɗin datayi amfani dashi yaƙi barin hannun sa shifa yanzu yafara tunanin anya kuwa mutumce wannan wanne irin turarene yayi tsaki yafi cikin kwando

lafiya dr naga kana tunanin ?"

Firgigit ya dawo hayyacin sa ya maze dayake yana da zurfin ciki da huya kagano meke damunsa yace

lafiya qalau yanzu so nake inji giwa inga ya aikin nasu yake tafiya tashi yayi yafara neman mukullinsa da wayar sa

hmmm dr giwa dan Allah ina nemarwa fanna afuwa kaga sabowace bata san yarda

da katar dashi yayi yace

pls birnin kudu bana son jin maganar nan ai duk wata doka ta makarantar nan sai da na faɗa

me isa baka daukan abu da zafi amma ayannzu ka zafafa dan wannan kuskuran da fanna tayi

ban za yayi mai ya fita ya bugumai kofa mota ya shiga zuciyarsa na ɗaci yarasa dalili shima besan da lilin dayasa yayi haka ba tunda yana yiwa sababbi afuwa
……………✍🏼


*RASHIN SANI*

*🫧story and writing🫧*

*🎀Oum yasmeen🎀*

*IN FA BANA GA NIN RUWAN COMMENT ZAN MAI DA SHI PAYMENT DOMIN BA ZAI YIHU BA ANA WASA BABU DARIYA BA*
💃💃💃💃💃

*dan girman Allah inkinsa ba zaki comment ba karki shiga*

https://chat.whatsapp.com/Fu2P8PebrYYAXRI3z0vvXh
*wannan group ɗina ne a kwai lokacin da zan dena posting a kowanne group sai a nawa in kuka shiga inga ruwan comment ko in mai dashi payment*

💞💞💞 💞💞
💞💞💞 💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞
*page 5-6*

"""amma me isa ita naƙi in mata uzuri toni wata zuciyar ta ce mai saboda ta nuna maka sangarta ta ya'yan gata shiya,

tsaki yaja ganinn tunani zai zautar da shi ya damu kansa gani yake kamar be kyauta mata ba tsaki yaja gaban wani tamfatsaitsan asibiti ya tsa inda yayi horn gate man ya najin horn ya taso ya buɗe mai cikin girmamawa yace

Barka da zuwa oga

Yauwa yace ya ja motar sa yayi gaba parking space ya nufa inda ya faka motar sa ya fito kai tsaye yanufa office ɗinsa ya nufa aikuwa ya tarar da mutane da yawa yau yasan ba zai bar Asibitin nan ba sai dare saboda ya tara aiki da yawa

da sauri wata budurwa ta sha gaban sa tana sanye da fitted gown ta matsaita sosai inda ta rataye mayafi chantili a kafadar ta sai taunar chin gum take ta ci make up bakin nan ya sha jan janbaki takalmine mai tsaye a kafarta cikin salon jan hankali tace

" your well come my dr tayi wani far da ido ita ala dole saita burgeshi,

banza yayi mata ya sa wani kati aikuwa nan da nan kofar ta buɗe ya shiga iya haduwa office ya hadu ga kayan more rayuwa biyoshi tayi har tana tuntuɓe kamar zata waɗi saboda saurin da take kuma rigar ta matsaita sai uwar tsaga har cinya cikin muryar kuka da yake cin ta tace

"haba dr tun safe nake jiran ka amma kaxo kayi banza dani honey kasan irin son da nake maka kuwa wallahi ba zan iya rayuwa bakai ba ka tausayamin ka aure ni wallahi in kaina kakeso in baka zan baka ?"

pls dan girman Allah rumaisa ki fita ina da patient da yawa kuma na san kin gani kin san asati sau biyu nake zuwa asibitin nan ko ki tafi gida zan neme ki

Wallahi ba inda zani sau nawa kake cemin in tafi bacin faɗi kake baka nemana dan girman Allah ka temaka min wallahi sonka zai hallaka ni daya daga cikin kujerun da aka tanadar domin zaman marasa lafiya ta ja ta zauna ta kifa kanta tana kuka mai ban tausayi

Zuba mata idanuwanshi yayi sunyi ja tamkar garwashi domin ya cire glass ɗin sa ransa inyayi dubu ya ɓaci mai isa rumaisa ba xata gane ba tana ɓata wa kanta lokaci mai isa takasa fahimtar bata ɗaya daga cikin jerun matar da zai aura numfashi ya fesar mai huci yace

Pls rumaisa ki fita ina da aiki da yawa tun da nace miki zanne meki ki yarda

dagowa tayi duk make up ɗin da tayi ta ɓaci ta saki ajiyar zuciya tace

" rely?"

yes i promise to you

farin ciki ne ya mamaye fuskarta da zuciyar sa ta saki dariyar jin daɗi ta ɗauki jaƙarta ta tsaya tana kallon sa da tana da iko zata iya mai da dr giwa zuciyar ta ba macan da ta isa ta kalle shi tana mai wani irin so ita kanta batasan iya kacin saba a hankali ta sunkuya har yana iya jiyu numfashin sa tace

My honey ina sonka ina jinka ajinin jiki na pls ka tausayawa rayuwata karayu dani har abadah ƙar ka bar wata ƙofar da wata macan da zata zo cikin rayuwar mu wallahi ba dan dukiyar ka nake son ka ba ina yi maka true love wacce ba sirkin cuta a cikin ta kai min alkawari zaka rayu dani har abada

Rumtsai idonsa yayi ya nuna mata hanya da hannun sa

"Okay bakomai na gode da ka tsaya ka saurareni ta juya zata fita ta murɗa handle ɗin kofa ,

yace

kice wanda yake kan lahi ya shigo

"To, my dr ,

wannan kenan

aguje ta waɗa kan gadon ta tasaki kuka domin yau dr ya ɓata mata rai taci alwashi kala kala akansa domin sai ta rama

Haba fanna yanzu ki canza kaya kizo mutafi kin tsaya wani kuka

yanzu a gaban ki dan uwanki ya cimin mutunci baki dakatar da shi ba shine kike cewa inzo mutafi ba zani ba

Hmmm fanna kinja wowa kan ki tun farko sai da nace miki ki cire kika ƙi kiyi haƙuri kawe shine mafita yanzu

wallahi sai na rama dan rainin hankali tsoho kawe

uhm uhmm fanna ba asan inda rana zata faɗiba

Allah ya kiyaye ko zata waɗi saide awani gun mai zanyi da tsoho

hmmm kina ban mamaki inkin ce da dr giwa tsoho shekarar sa arba'in fa matashi ne fa

Wallahi an cucu matashi ni nayi mamaki ma dabe fara furfura ba

hmmm wallahi fanna kinyi nisa

tashi tayi ta canza kaya suka fito kai tsaye aji suka nufa har sir birnin kudu ya shiga sosai suka maida hankali kan karatunsu

Wannan kenan

Da gudu ta faɗa jikin mahaifiyar ta cikin muryar kuka tace

"wallahi hajja in ban sami ya sa'eed ba zan iya mutuwa ku temaki rayuwata ku aura min shi kowa na giwa yasan ina son shi amma kun zuba ido da ace shine da tuni anne mamai mafita ,

wani tsaki hajja ta saki tace

"We ke Amal mai isa ba kƴa jini ba nace ki bar min komai a hannu na ba ,

Hajja sai yau she asirin da kike mai zai cishi kin daɗe kina ɓatar da kuɗin ki nide kawe ki samo min hanyar da zan sace zuciyar sa

ai tuni ta buge mata baki tace

"wato amal kin ƙagu da abin da nakeyi ko komai inayi danke domin wallahi dole in kastantar da ahalin fatima tunda har ta haifi dan da akafi son sa fiye da kowa a dangin giwa ba zan gaji ba wataran zanyi nasara na tsani fatima da duk wanda ya rabe ta tafini komai na rayuwa ga danta ya tara dukiya dole ki aure shi sannan in kashe shi da hannu na mu sami dukiya wannan hanyar ce kaɗe zan iya kuntatawa fatima har zuciyarta ta buga shi daman wancan tsohon yana kan hanyar gangara ………✍🏼

kuyi haƙuri da wannan na gama typing ɗina aka yimin banned ɗin whatsapp

*RASHIN SANI*




*🫧story and writing🫧*

*🎀Oum yasmeen🎀*

_DAN GIRMAN ALLAH IN KINSA BAZAKI COMMENT BA KAR KI SHIGAR MIN GROUP_


https://chat.whatsapp.com/Fu2P8PebrYYAXRI3z0vvXh

*IN FA BANA GA NIN RUWAN COMMENT ZAN MAI DA SHI PAYMENT DOMIN BA ZAI YIHU BA ANA WASA BABU DARIYA BA*
💃💃💃💃💃

*wannan group ɗina ne a kwai lokacin da zan dena posting a kowanne group sai a nawa in kuka shiga inga ruwan comment ko in mai dashi payment*


💞💞💞 💞💞
💞💞💞 💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞
```page 7-8```

"""A'a hajja agaskiya nide nagaji kawe ki nemo hanyar da zai kalleni kullum ai ta abu ɗaya ,

hanka ɗeta tayi ta tashi domin abun na amal ya huce hankali anya ba wani asiri akaiwa yar tata ba anya zata bata haɗin kai su gudanar da aikin su lalle akwai aiki agaba ta faɗi aranta

Kuka

Please Login or Register in order to submit comment