Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga tsakanin Al'ameen da Fadeelah, har ya zamana cewa babu ranar banza da zasu shafe awa biyar basu ji lafiyar junansu ba ta hanyar waya ko chatting d'in da hannunsu ke mak'ale akai.

Wani abu ne da ita kanta Fadeelan bata san sanda ta jefa kanta a ciki ba, ko kuma ace ta bari Al'ameen din ya jata don a sati uku kad'ai yasa tana jin kamar ta sanshi ne tsawon shekaru uku ne, tana jinsa kamar wani aboki ko d'anuwanta namiji data rasa a baya.

Hatta Mami ta lura sosai da canjawar Fadeelah amma tunaninta bai tab'a kawo mata cewa wani abu ne tsakaninta da Al'ameen ba duk kuwa da yawan zuwa gidan da yake yi a cikin kwanakin bayan, tarin zirga-zirga da d'awainiyar dake kansa.

A gefe guda kuma karatunta da Adam yana cigaba da gudana ta hanyar bi da dukkan abubuwan data lissafa masa daki-daki. Wani abun ma sai taga kamar wasa ne ko shirme, sai ana cikin yi idan ta fara gane lissafin, sannan ta fahimci yayi ma'ana.

Ranar da suka zo kan inda ta rubuta
hobby d'inta na sauraren alqur'ani, shiru kawai tayi tana kallon yadda ya saita MP3 d'in da ya siyo kafin ya ware sassanyar volume d'im k'irar sheikh Mahir a cikin library d'in, sannan suka fara topic na goma sha uku a lissafinsu, kuma har suka kai k'arshe karatun bai fasa rangad'owa ba.

Abinda ya d'aure mata kai game dashi kenan, idan har zai iya sauraren alqur'ani na tsawon awa d'aya, me yasa a baya zai shiga cikin masu yad'a b'atanci akan addinin alqur'anin?

Bayan haka kuma, zuciyarta ta gano wani b'angare daga cikin halinsa a kwanaki biyar na kowanne sati da take shafe awa guda tare dashi, ta fahimci cewar yana da sauk'in hali ba kamar yadda take hangensa a baya ba, saboda duk irin maganganun da take gaya masa basa tab'a b'ata ransa sannan duk abinda tace in dai ya duba yaga hakan ne, to ba musu zaiyi... sai dai in har ba daidai bane to bama zai saurare ta ba zai bi hanyarsa ne, wanda sai yayin kuma zata ga cewa nasan ne daidai.

"Zan iya tambayarka wani abu?"

Ta tambaye shi a wata rana bayan sun gama karatun, A lokacin saura topics uku kwata-kwata su gama guda ashirin da biyun da zasu yi, don yadda kwakwalwarta ke ganewa a yanzu yasa suke yin sauri sosai, dama ya fad'a mata a baya...

... sauran karatun abu mai sauki ne da zamu iya gama shi in har ba matsalar.

Maimakon ya amsa sai ya juyo kawai ya kalle ta da lumsassun idanunsa, sannan ya kalli gefe kad'an, ba tun yau ba ta fahimci cewa bai fiye son kallon idanunta ba akan dalilin da bata san shi ba. Yanayin nasa ya nuna alamun yana saurarenta ne, don haka tace.

"Tambayar bata danganci karatun nan ba."

Yatsanta d'aya ya nuna paper da suka gama kacaccalata da lissafi.

"Kar ki damu ina jinki."

Ta d'aga kanta game da had'iye yawu kad'an sannan tace.

"Meye tunaninka game da addinina?"

Sakan d'aya, biyu, uku, hud'u... kamar bai ji abinda tace ba, kafin ya motsa kad'an sannan ya dawo da idonsa kanta.

"Me yasa kika tambaya?"

A yanzu ta riga ta zaba da lazy muryarsa don haka kai tsaye tace.

"Saboda tun da ka shigo makarantar nan, kana d'aya daga cikin masu yad'a b'atanci game dashi, har zanga-zanga kuka had'a kan a hana mu zuwa da hijaab makaranta, dalilin da yasa na..."

Sai kuma tayi shiru hannunta da take alama wajen bayanin ya mak'ale a iska.

Adam ya sake lumshe idonsa a hankali yana kallon nata idanunta da a kullum yake jin kamar suna zuk'e k'arfin jikinsa ne duk sanda yake tare da ita, ko bata k'arasa ba, ya riga ya san me zata fad'a kuma itama ta san ya sani, ya gyara zamansa kad'an sannan yace.

"Abinda nake yi a makarantar nan wani abu ne da ya zama dole na ba wai don ra'ayi ba ko saboda ina da ak'idar hakan, kuma daga lokacin da zan k'arasa aikin dana keyi, zan barshi ne har abada.

Saboda haka addininki bai tab'a damuna ba leelah, don na yarda cewa a duniyar nan kowa yana da damar da zai bautawa ubangijinsa ta irin sigar da yaga dama, abu muhimmi shine mu duk d'in bayinsa ne kuma akwai ranar da zamu koma gare shi da adadin tawakkalin dake zuciyoyinmu."

Ta fahimci k'arshen zancen amma bata fahimci farkon ba wanda da alama personal problem d'insa ne, saboda haka tace.

"Abinda ka fad'a kusan haka ne, mu duk bayin Allah ne kuma zamu koma gare shi watarana da adadin Imanin dake zuciyarmu, sai dai ba ta kowace hanya ya kamata mu bauta masa ba. In ma kalli wannan Maths d'in da muke yi ka san ba ta kowacce hanya muke binsa ba, akwai tsararriyar hanyar da dole sai ka bita sannan zaka yi daidai, ni ada ai wata hanyar nake bi daban inyi lissafina kuma ya tafi ba daidai ba, sai da na had'u da kai sannan kake d'ora ni kan hanyar da take daidai.

Kamar haka bauta ga Allah ma yake, akwai tsararriyar hanyar da ubangiji ya turo manzanninsa su nuna mana don mu bauta masa a daidai, ba sai ranar da zamu koma gare shi sannan muga cewar mun b'ace hanya ne kamar yadda nake yi a lissafina na da ba, sanda zan d'auko hanya daidai, sai daga baya in kauce in tafi wani shirmen daban.

Saboda haka yadda Mr. Hawkins ya aiko ka don ka nuna min yadda ake lissafin nan daidai, kamar haka ne Allah yake aiko manzanninsa don su nuna mana hanyar bauta masa daidai, don idan muka ce zamu bi kowacce hanya zamu b'ata ne."

"Me yasa to kuke ganin musulunci ya zama shine hanyar daidai a cikin kowanne?"

"Saboda tarin dalilai da yawa, a cikin alqur'anin da muka gama ji yanzu da kuma sauran litattafan, har da Bible d'in da kuke..."

"Ni ba christian bane." ya katse ta tun kafin ta k'arasa, sai ta d'ago sosai ta kalle shi, idanunta cike da mamaki.

"Bani da addini." ya fad'a mata amsar da bata tambaya ba.

Sai ta gyad'a kanta a hankali kafin tace.

"Idan har baka da addini kuma kana da irin wannan tunanin akan musulunci, na yarda cewa kai ba kafiri bane gabad'aya, kana wani mataki ne da k'okorinka zai iya tsallako da kai hanyar gaskiya."

Da alama maganar ta bud'e wani b'angare na kwakwalwarsa kuma ta saka shi tunani, irin tunanin da baya son yi a gabanta, saboda da sauri ya kawar da kansa sannan ya bud'e jakarsa ya zaro wayarsa.

"Lokacin mu ya cika leelah, sai gobe kenan?"

Ta d'aga kanta a hankali sannan ta tattara kayanta ta cusa a jaka ta mik'e tsaye, shima ya mik'e.

"Sai gobe?" ya sake tambaya a hankali, itama ta sake d'aga kai kawai sannan ta nemi hanyar k'ofa.

Kafin ta isa gate d'in makarantar, motarsa ta tsaya a gefenta, ya sauke glass d'in sannan ya sunkuyo da kansa kad'an.

"Zan iya kai ki gida?"

Ta matse hannun jakar a jikinta sannan tace.

"Ka barshi kawai ina samun mota duk sanda na fita."

An dad'e da wuce lokacin da take gaya masa duk maganar data fito bakinta don ba amfanin yin hakan ga wanda ta fara gani kyautatawarsa a yanzu. A hankali ya maida glass d'insa ya rufe sannan yaja motar ya wuce ta.

Amma daga wannan ranar sai ya zama kamar tayin yana d'aya daga cikin karatunsu ne, a kowacce rana baya sun fito zai tambaya in zai iya kaita gida ita kuma ta tankwab'e hakan.

Sannan a kowacce wucewar rana da fitowar wata, zuciyarta na k'ara bude wasu kofofin ne da take fahimtar halayensa masu kyau, hirar addini ma sai ta sami gurbi a lokacinsu, sau da yawa shi zai fara tambayarta wani abun da zata yi ta bashi iya amsar data sani tana kuma kawo masa banbanci musulunci da sauran addinan, har ta kai in ya koma gida zai duba wani abun a yanar gizo yazo ya nuna mata.

Har ta kai hira tsakaninsu ta zama ba wani abu sabo ba, har ta kai shashashar zuciyarta ta fara rage yawan duhun tsanarsa a cikin zuciyar tata, har ta kai su Melissa ma sun sauko daga tunanin da suke akansa... sannan har ta kai zuciyarta na tuna shi bayan sun rabu har tayi hirarsa a wani waje, hirar yadda ta tsane shi kamar annoba a baya da yadda kirkinsa yazo ya canja tunaninta, sannan hirar data zama sanadin bud'e wani sabon shafi a rayuwarta!

"Wai me yasa kike yawan zancen Adam d'in nan ne Fadeelah?"

Al'ameen ya tambaya ta cikin wayar da suke yi a wani dare. Earpiece ne a kunnenta saboda haka ta danne giyar motar da take driving a cikin game d'in da take yi sannan tace.

"Na gaya maka yana da kirki sosai, ban tab'a tunanin haka halinsa yake a baya ba, sannan baka ga tarin topics d'in dana iya ba saboda shi, kuma yana da son musulunci don ya rage abubuwa da yawa da yake yi a makaranta, yanzu kuma jikina yana bani kamar ta hanya ta zai iya musulunta."

"Ta hanyarki?" ya tambaya a hankali kamar iya abinda yaji kenan kawai.

"Kince kun kusa gama lesson d'in, me zai hada ku kuma bayan nan?"

"Babu." Ta amsa kai tsaye.

"... amma a makarantar yake ai, duk da ma Mami na ta shirye-shiryen komawarmu Nigeria..."

"Please..." ya katse ta a hankali.

"...Fadeela bana son zancen nan duka biyun."

Ta koma ta kwanta akan gadon da take zaune.

"Saboda me? na san baka son zancen tafiya Nigeria, amma meye da zancen Adam?"

"Ban sani ba..." ya sake fad'a cikin speaker a hankali.

"Ban sani ba ko kishinsa nake yi."

Cak! tunanin cikin kanta ya tsaya a lokaci d'aya.

"Ban san me yake faruwa dani ba but I think I'm falling in love with you, kullum ina gayawa zuciyata cewa ni dake kawai abokai ne amma abin ya kasa yiwuwa Fadeelah, ban taba jin yadda nake ji akanki game da kowa ba, shi yasa bana jin zan iya cigaba da pretending ban fad'a miki abinda yake zuciyata ba... Da gaske nake ina sonki!"

A daidai wannan lokacin motar cikin game d'in ta daki wani gini, ta tarwatse sannan ta kama da wuta.

***

Kamar yadda ake zarewa mutum laka ya zama bashi da wani katab'us, haka Fadeelah ke jin jikinta a safiyar data wayi gari bayan Al'ameen ya bud'e mata dukkanin sirin zuciyarsa game da ita.

Ta rasa kuzarinta da walwala dama komai, tunani ya hargitse fal a cikin kanta harda kuwa irin tunanin da take yi duk sanda ciwonta ke kokarin tashi, irin tunanin dake son tuna mata wani sabon abu a rayuwarta ta baya. Hakan yasa ta rubuta a jotarta cewa makamancin hakan ya tab'a faruwa da ita a rayuwarta ta baya kenan, Wani ya tab'a cewa yana son ita d'in da bata san ko wacece a baya ba.

Tun bayan sallar asuba har kusan azahar tana kwance a d'aki bata fito ba, ba irin tambayar da Mami bata yi mata ba akan me ya same ta amma ta kasa lalubo wani dalili ko ma k'arya guda d'aya ta fad'a mata, harshenta yayi nauyi, bakinta ya k'ulle gani take data bud'e zata fad'o dukkan kalaman da Al'ameen ya gaya mata jiya ne ta fallasawa Mami.

Ganin bata da niyyar magana yasa Mamin tace da kowa ya kyaleta watakila hutu take buk'ata kamar yadda ta lura a yanzu duk sanda ciwonta ya tashi in ta huta yana yin sauki ne.

Wanda kuma zuwa wajen la'asar d'in ta fara jin d'an dama-dama, sai dai ba'aje koina ba Iman ta shigo ta b'arar da hakan sannan ta d'auki duniyarta ta juya gaba a baya.

"Aunty deelah, kinga trophies d'ina? Mami tace yanzu su Haneefa zasu zo zan nuna mata ne?"

"Wace Haneefan?" Bakinta ya furta a hankali amma cike da rud'ani, kamar akwai wata Haneefan da suka sani ne bayan k'anwar Al'ameen a garin.

"Haneefan Aunty Miryaamah, yanzu zasu zo gabad'ayansu."

Kalmar 'gabad'ayansu' ta ruguzo da wani k'aton gini a zuciyarta. Tun daga ranar da suka je gidansu ita da Mami ana kwana d'aya da dawowarsu bata k'ara taka k'afarta a gidan ba, duk sanda Mami ko su Zahra zasu je zata nemi wani uzirin da zai sa ta zauna a gida, kuma yawancin lokacin zuwan Aunty Miryamah gidan tana makaranta ne, saboda haka tsawon wata guda bata sanya matar a idonta ba... wani babban dalilin daya k'ara gina alak'arta da Al'ameen, don in suna tare zuciyarta bata taba tuna mata cewa ya dangance ta.

Sai a yau da yazo da wani sabon labarin daya canja rayuwarta shine zai tattaro uwar tasa su zo? idonta ya kai kan wayarta dake gefe, ta tabbata ya kira ta yafi k'irgen mai tunani Saboda tun jiyan bata kunna ta ba, don haka babu makawa ta san ma shi zai kawo su ba driver ba.

Mintuna goma bayan haka, hayaniya daga falo ta tabbatar mata cewa sun iso, gabanta yayi wata mummunar fad'uwa sanda taji Aunty Miryamah na fadin.

Al'ameen baka rufe k'ofar motar ba."

Ta kad'e har ganyenta, in har wannan matar ta san yadda ta saba da d'anta a cikin watan daya wuce, balle kuma ta san maganganun daya fad'a mata jiya? ta tabbata babu abinda zai hana ta kashe ta har lahira.

Sai ta lalubo wata shud'iyar hular sanyi mai k'atuwar toluwa ta auduga ta d'ora akanta, hakan bai hana bargajajjen gashinta fitowa ta kowanne gefe ba, ta bud'e window d'akin daya tafi ta bayan gidan ta tsallaka ta fita, anan taga tarin kayan wankin da Mami ke shanyawa kasancewar dryer su ta lalace, sai ta sunkuya kawai ta d'ebo wasu ta shiga shanyawa don tana buk'atar wani abu da zai d'auke zuciyarta daga hayaniyar falon da take jiyowa.

"Fadeelah..."

Muryarsa ta amsa a cikin kanta sanda take kokarin shanya wata rigar Mami, wannan muryar tasa mai taushi da kullum ke saka ta farin ciki da nishadi, amma a yanzu sai wad'annan abubuwan suka juye zuwa hargitsi da rud'ani, taji k'afafunta sun k'ame a wajen ta kasa juyowa ta fuskance shi.

A hankali take jin k'arar nasa takun har ya zagayo ya tsaya a gabanta, amma sai rigar data shanya ta zama wani hijabi tsakanin fuskokinsu. Bata iya wani motsi ba har yasa hannunsa d'aya ya zuge rigar ta koma gefe.

Ya salam! yayi kyau cikin wasu hadaddun kaya k'irar pakistan, kalar bak'i wadda ta k'ara fito da hasken fata da kuma kyansa, yayin da ita take sanye cikin bulamar rigar baccinta kalar yellow da kuma shud'iyar hular sanyi, ga gashinta duk a barbaje ya hargitse cikin rashin gyara, duk da ya d'an had'e rai amma fuskarsa na haskawa da wani annuri yayin da tata ke a kumbure saboda rashin wanka da kuma kwanciyar data dinga yi tun safe.

Sai taji ta zama wata 'yar mitsitsiya a gabansa, tunaninta ya shiga kwancewa d'aya bayan d'aya, kuma ta rasa wanne zata fara tattarowa don amsa tarin tambayoyin dake take hango kyallinsu a cikin idanunsa.

Daga can jikin tagar falo, Aunty Miryaamah ta damk'e labulen data yaye tana hangen d'anta a gaban wannan mahaukaciyar yarinyar!
●﹏●

BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

11

(☆_☆)

Ya k'ank'ance idonsa a hankali yana kallon ta, yaluwar doguwar riga, shudi'yar hula, ga fuskarta a kumbure sannan gashinta ta kowanne gefe ya fito, sai ta k'ara yi mishi wani irin kyau a take... yaga ta koma kamar wata 'yar Bebi ta wasan yara da ko babba zai so ya d'auke ya b'oye don ta kasance tare dashi kullum.

Sai dai kuma a kowanne lungu da sak'o na fuskar tata, alamun damuwa ne fal da kuma wani abun da bai sanshi ba, wani abu da yayi masa kama da yanayin da mutum ke shiga lokacin da zuciya ta karye, ka rasa wani abu da ka saka rai akansa (Heartbreak).

Allah ya sani zuciyarsa ta fara sonta tun daga ranar daya fara ganinta, sai dai ra'ayin mahaifiyarsa akanta yasa yayi tunani ko tana da wani aibun ne, shi yasa yayi ta bibiyarta a hankali har ya fahimci halayyarta wadda a kullum ke k'ara adadin sonta a zuciyarsa. Shi kansa bai so sanar da ita hakan ta waya ba a jiya, ya san a yanayin ciwonta hakan zai iya damunta ta wani b'angaren, amma ba yadda ya iya... zancen wani Adam da take masa a kullum ya sanya bakinsa ya sub'uce ya fad'i abinda bai tanadi fada mata a yanzu ba.

Har ya bud'e baki da niyyar magana gefen idonsa ya hango masa d'agewar labule daga can jikin windon falo, bai lura da wanda ke tsaye a wajen ba amma jikinsa ya bashi ko waye bai cancanci ganinsu a haka ba, saboda haka ya zare hannunsa daga kan igiyar a hankali sannan yace.

"Ki kunna wayarki dan Allah."

Da haka yayi gaba ya wuceta, fuskarsa ba alamun ita yayi wa magana.

***

"Al'ameen kayi hakuri, ni da kai bamu dace ba, mun bari zuciya tafi karfinmu ne har aka zo wannan matakin, watakila kuma ni na ja ka, na biye maka muka fara alak'ar da har kake tunanin zata kaimu wani matakin, ina da tarin abubuwan da nake kokarin saita kwakwalwata akansu yanzu, ba zan iya k'ara mata wani sabon al'amarin irin wannan ba, na d'auke ka ne kawai a matsayin d'anuwa na ko wani aboki da nake samun tallafi a wajensa.

Sannan ga al'amarin mahaifiyarka, ni da kai mun sani abu ne da ba zata tab'a bari ya faru ba, na yarda nayi kuskure tun farko da na bari sabo ya shiga tsakaninmu ba tare da hangen nesa ba, don in har aka cigaba a haka dole ne sab'ani ya shiga cikin zumuncinku... kayi hak'uri Al'ameen amma kasancewata da kai ba alkhairi bane."

Ta fad'i hakan ne duka a tsaye gaban dogon mudubin d'akinsu da take kallon kanta ta cikin dim hasken fitila guda d'aya dake ci a d'akin, ta riga ta tsara wad'annan kalaman kuma ta yanke hukuncin yanke alak'arta dashi tun komai yana tsakaninsu a yanzu, kafin ma na ukunsu yaji.

A hankali ta jawo wayarta dake kan bedside drawer, ta danne power button d'in ta kunna ta, ba tare da wani b'ata lokaci ba messages suka shiga tururuwar shigowa wanda mafi yawancinsu daga number Al'ameen ne, number da ada hannunta har rawa yake wajen bud'e sak'onsa, amma a yanzu bata ko bi ta kansu ba, ta shiga cikin wajen sabon rubuta sak'o, ta rubuta abinda ya gajarta zancenta...

Kayi hak'uri Al'ameen, abinda kake tunani ba zai tab'a faruwa ba, kuma ina ganin ya kamata mu tsaya da koma meye hakan, tun kafin abubuwa su fara tab'uwa!

Sak'on na nuna mata cewar ya isa, ta lalubi makunnin ta sake kashe wayar, ta d'auki zuwan wannan sak'on a matsayin almakashin daya datse alak'arsu, tayi wa kanta alkawarin daga yanzu tsakaninta da Al'ameen gaisuwa ce kawai, gwara tayi wa kanta katanga dashi tun kafin al'amarin ya had'o da mahaifiyarsa.

Su Zahra sun dad'e da kwanciya a lokacin saboda haka ta lalubi gadonta ta kwanta a hankali itama, idonta na kallon wayar sannan kwakwalwarta na gaya mata cewa ta hak'ura da ita kenan har abada, abada wadda Al'ameen zai gaji ya daina nemanta.

Kwanaki biyu bayan nan, yazo gidan sau d'aya amma bata bari ya ganta ba, ta shige toilet har lokacin da ya gaji yayi tafiyarsa, don ta yarda babu wata sauran alak'a tsakaninsu yanzu bayan text d'in data tura masa, haka take yini a kullum da jiki mai nauyi babu walwala ko kad'an, ta riga ta saba dashi, ta saba da hirarsa mai shiga rai, shi yasa take jin kamar rayuwarta bata da wata sauran ma'ana ne a yanzu da ta yakice shi daga ranta.

We should'nt have talked, watak'ila kyawunka ne ya rud'e ni har nayi nisa da tunani na amma insha Allahu komai ya k'are yanzu.

Da zata iya maida hannun agogo baya, zuwa ranar data fara ganinsa a tsakiyar kitchen d'insu, da ta daure zuciyarta akansa, da bata sake fad'awa tarkon sa ba!

A tunaninta, Al'ameen ya zama tarihi kenan cikin rayuwarta, sai dai ashe wata k'addarar bata ma fara ba!

***

Kamal matashi ne amma kuma babban lauya dake b'angaren Corporate law (lauyan kamfani) a wata sananniyar k'ungiya dake garin, asalinsa iyayensa mutanen k'asar Somali ne, amma a garin washington aka haife shi har yayi girma da karatunsa anan, lokacin da Al'ameen yake shekara ta hud'u a karatunsa ne k'ungiyar su Kamal suka kai ziyara makarantarsu akan wayar da kan d'aliban dake karatun law kan harkar shariah, anan suka had'u da Al'ameen kuma abota mai k'arfi ta shiga tsakaninsu.

Hakan yana d'aya daga cikin dalilan da yasa Al'ameen yayi farin cikin dawowarsu washington bayan gama karatunsa, don shi ya sama masa gurbi a ma'aikatarsu kasancewar shima abinda ya karanta a birnin london kenan, shekara shida yana practising CORPORATE LAW.

Saboda haka a d'an lokacin nan na samun aikin Al'ameen a ma'aikatarsu sai ya zama kusan komai tare suke yi duk da banbancin matsayinsu, tun dama Kamal ya dad'e yana maraicin d'anuwa musulmi a ma'aikatar.

Lokacin da ya shiga office d'insa a safiyar laraba, Kamal ya d'ago ya kalle shi yace.

"Yanzu nake nemanka, Philiph yana buk'atar wannan file din da kayi assessing patnership da kamfanin beauty products d'in nan."

Bai ko saurareshi ba ya zube files d'in da ya shigo dasu sannan ya nemi kujera ya zauna ya dafe kansa.

"Meye yake damunka? ba dai aikin ne ya sami matsala ba?"

"Forget about the damn case Kamal, rayuwata ce ke neman birkicewa."

Sai ya ajiye biron hannunsa da yake rubutu dashi ya gyara zama yana kallonsa sosai.

"Me ya faru?" ya tambaya cikin nutsuwa.

Al'ameen ya d'ago da kansa ya d'ora yatsu biyu kan lebbensa sannan ya huro iska ta tsakaninsu, wani abu ne mai kama da guguwa a cikin kansa duk sanda idanunsa suka hasko masa text din da Fadeelah ta turo masa, kwata-kwata kwakwalwarsa ta kasa karb'ar kalaman balle ma ya yarda dasu, gashi ta kashe wayarta kuma yaje gidan yafi sau a k'irga amma ta hana shi damar da zasu yi magana, in har zai ganta to zata gaishe shi ne kawai a tsakiyar su Mami daga nan kuma ta b'acewa ganinsa, sau da yawa ma haka zai je ya dawo bai ganta d'in ba.

Tunaninsa a yanzu gabad'aya ya tafi wajen lissafawa da neman hanyar da zai iya samunta ne suyi magana, tunda da alama ta yanke shawarar daina amfani da waya a rayuwarta.

"Na tab'a gaya maka zancen wata yarinya dana gani a gidan Mami kwanaki ko?" Ya fad'a kai tsaye.

"Yes, wadda ta sami matsalar memory loss."

"Right, to ni da ita a kwanakin bayan da suka wuce kusan mun saba sosai har ta kai ina yawan zuwa gidan Mami bayan na tashi daga aiki saboda ita."

"Na fahimta."

"Ban san me ya kaini ba, amma ba tare da na tsara komai ba bakina ya gaya mata cewa ina sonta, tun daga lokacin kuma sai komai ya rikice ta daina d'aukan kirana ta kashe wayarta ma gabad'aya, daga baya ta turo min da sak'on cewa inyi hak'uri ba zai yiwu ba saboda wasu shirmen dalilai da take tunani, naje gidan yafi cikin k'irga amma bata bari na ganta ko ta bani damar yi mata magana kamar da, idan na tambayi Mami ita sai tace min wai bata da lafiya ne, bayan na san ba hakan bane.

Da har na yanke shawarar fadawa Mami abinda ke tsakannmu, amma tsorona d'aya ne Kamal, kar in gayawa Mami kuma ita tazo ta k'aryatani tunda har bata riga ta amince dani ba, kuma na san in har na fad'a Mami sai ta tambayeta tukunna."

Kamaal ya gyara zamansa a hankali alamun ya fahimci dukkan zancensa.

"What's the point yanzu? me kake so?"

"So nake in ganta, in tabbatar mata wad'annan shirmen dalilan da take tunani basu da tasiri don wallahi da gaske nake ina sonta, sannan kuma inji irin tunanin da take akai na, amma na rasa ta yaya hakan zai yiwu."

"To ka same ta a wani waje mana, me yasa dole sai a gida?"

"Ban san wajajen da take son zuwa ba, kuma idan har na cika bibiyarta Mami zata zarge ni, ya zamo har Mommy (yana nufin Aunty Miryamah) ma tazo ta sani tun kafin in san matsayina a zuciyarta."

"Ajiye zancen su Mami a gefe, kana nufin ita yarinyar kullum tana gida bata fita koina?"

Ya d'anyi shiru bai amsa ba.

"Bata fita makaranta?"

"Tana zuwa." Bakinsa ya furta a hankali.

"To ka same ta a can, na tabbata zata saurareka in har taga cewa ka bita har wani wajen."

Ya gyad'a kansa a hankali sanda tunanin hakan ya gifta cikin kansa, da wani d'an guntun murmushi ya shiga d'agawa Kamal babban yatsansa guda d'aya, kwakwalwarsa na gaya masa cewa babu abinda zai hana shi ganin Fadeelah a gobe, ko da kuwa mitar Auny

Please Login or Register in order to submit comment