Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

.
[8:18AM, 10/23/2016] Rash Kardam:
MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
&
Khadija Candy
~
Da safe kuwa yanda naga, idon Ayshat
ya yi ja, nasan ta niku ba kad’an ba.
Khaleel ko sai tarairayata yakeyi, tamkar
kwai. tundaga wannan rana suka
shimfid’a soyayyansu, mai cike da
burgewa, komai tare sukeyi, inka gansu
gwanin ban sha’awa, Khaleel ta tattala
matarsa, itama tana gudun abunda zai
bata masa rai.
Ayshat tayi kyau ta k’ara haske. Niko
Rash “nace anya wannan ,haske haka na
kalau ba”. Sannu a hankali rayuwa ke
tafiya dad’i da ba dad’i, kayan garansu
ya kare, randa inya samo musu mai
maik’o suci. Randa in bai samu ba har
garin kwaki suke ci, ko kad’an Ayshat
bata taba nuna fushinta ba, kulum tana
cikin masa, Addu’a da fatan alkairi.
Safiyar yau ta tashi da zazzabi mai
tsanani, ga jiri da ke d’ebanta.
Hankalinsa ya tashi matuk’a, gashi ko si-
si bai kwana dashi ba. Ko dayaje
gidansu, yatarar da iyayensa, gari kwaki
suke sha, ya gaida su Mamansa
tace”Khaleel lafiya na ganka haka?.
Cikin damuwa yace”Aysha ba lafiya
kusan sati d’aya, gashi banda ki naira a
hannuna.
“Yasalama towo gashi muma haka muka
wayi gari, amma ga wancan tv kaje ka
sayar sai a samu a mata jinya. Tv ya
d’auka yaje ya sayar dubu biyar da d’ari
bakwai, sukaje asibiti a ka mata gwaji,
likita ya tabbatar da tana d’auke da juna
biyu, har na wata hud’u. Magunguna ya
rubuta musu, sauran ya sai musu kayan
abinci, rabi ya kaimusu, saura ya kai ma
su Ummansa. Ko da Ayshat ta samu
sauki, yace ta shirya, kaita gidansu ta
gaida iyayenta, daga nan suka wuce
gidansu Khaleel da murnan Umma ta
tarbeta, tarinka ina zansaka dake. Da
daddare da zasu tafi, “Umma ta mata
nasiha sosai, da takara hak’uri da yanda
mijinta ke. Ayshat”tayi godiya ma Umma
suka tafi.
Khaleel result ya fito yayi kyau sosai,
yanzu aiki ya dunkufa nema, kulum sai
ya fita amma shiru, Ayshat ko kulum
tana cikin masa addu’a da fatan alkairi.
Safiya kam harka take ba sanya, ta
maida bariki kamar rigan sakawanta, ko
shakka babu, yanzu motanta biyu, kud’i
kuma ta tarasu ba’a magana.
Samarukanta na da duk ta canza, Abuja
kuma ya dawo mata kamar gida.
Kwanki sun ja, Aysha ta shiga watar
haihuwanta, Khaleel ko kula ta
musamman yake bata, yana tattala yar
matansa. Safiyar yau ta tashi da nakuda,
hankalin Khaleel ya tashi, mai napep ya
nimo suka nufi asibiti, aka shiga da ita
labour room, “addu’a yaketayi Allah ya
sauketa lafiya.
Wayarsa kiran nokia, irin mai tocin
nan, ya kira Baban Aysha ya sanar ma,
ya kira gidandu ma ya fad’a musu.
Ayshat ta kasa haihuwa da kanta, likitoci
sukazo suka sanar masa dole sai an mata
tiyata. Ba k’arami min tashin hankali ya
shiga ba, don kud’in da ya tara 8k ne,
ana haka sai ga iyayensa, nan ya sanar
musu, Malam yace”abasa ruwa a kofi da
ruwa, murfin flaks aka miko masa,
Addu’a ya yi, dake wanda suke kanta
mudulmai ne, ba’a samu matsala ba,
sukabata cikin ikon Allah ba’ayi minti
biyar ba, ta zankad’o yaranta guda biyu,
mace da na miji. Wayyo karkuga murna
gun khaleel, bayan nurses sun gyarata,
ta huta suka dawo gida. Yan’uwa da
abokan arziki sai murna sukeyi, Khaleel
daman ya sai ragonsa yana kiwo bai
samu matsalaba, ana gobe sunane aka
kirasa ne, fidelity bank suka kirasa,
daman ya rubuta musu Application, ya
samu aiki a gurin. Cikin murna ya zo
gida ya sanar musu kowa sai murna
yake masa. Ko ni Rash nayi murna sosai,
gaskiya yan biyu sunzo da goshi.
….Na….
Rash Kardam
&
Khadija Candy
[8:18AM, 10/23/2016] Rash Kardam:
MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
&
Khadija Candy
~
Cikin ikon Allah anyi aiki lafiya lau,
acire ciki murna agun Sofy ba’a magana,
Alhaji ya had’o mata magunguna, da
kayan ci masu kyau. Kula ta musamman
yake bata, sai da ta warke sosai, tukun
suka sake komawa ruwa don bata bar
Abuja ba sai da tayi samaru biyi, kuma
duk halin d’aya ne,Ta samu kud’i ba
kad’an ba suka dawo Kaduna.
Kwanaki sun tafi, yanzu Ayshat ta
kamala jaraba wanta, biki yarage saura
sati d’aya duk dangi sun had’u sai
shirye-shirye akeyi.
Sofy kuwa waya tayi ta sanar da Alhaji,
dubai ya aika aka sayomata, wasu ready
mate d’in kaya, Kala 6 da takalama su,
wanda zatayi fitan biki kawai. Inna ta
kuwa wani mai shago ta wanka ya bata
Swiss less masu kyau, tabayar aja d’inka
mata.
Ayshat bata shirya yin wani event ba,
kasancewan mijinta bayida k’arfi,
d’aurin aurene da yini kawai. Haka
akayi ta su cin-cin, ranar jimma’a ta
zago aka d’aura aure, da daddare mota
uku sukazo d’aukan amarya, aka kaita
gidanta, washegari yini karkuso kuga
inna da d’iyarta don sunyi wanka kece
raini, wankan nuna masa’a. Ko ina a
gidan biki su ake nunawa, baran Sofy
duk kayanda tasaka abinsone. Wasu
kuma gulmasu suke a ina take samun
kud’i haka?.
Yayinda wasu dangin uban yan neman
k’ora, sun makale musu, yini kam a
gidan amarya Alhamdulilah! Biki ne na
rufin asiri bana k’arya ba.
Da dadare yan’uwan Umma, suka saka
Ayshat tayi wanka ta canza kaya, nasiha
sosai suka mata, da gwada mata irin
gidan ta suke, tarike bakinta banda
gulma, kuma duk kashin abunda mijinta
ya kawo, tamasa godiya, ta amsa da
mutunci. Kuka tayi sosai dakyar ta barsu
suka tafi. Ni ko Rash na zo gulma don
inga yanda d’akin Amarya ya tsaru.
‘Daki d’aya ne, sai gadonta da kujeru
guda biyar, sai d’an fridge karami, da tv
karami. ‘Daki dai sai son barka a
talakance yayi, abokan ango ne sukayi
sallama, bayan sun zauna, nasiha sosai
sukayi Ayshat, sannan suka musu fatan
alkairi, suka tafi abunsu.
Bayan tafiyansu ne, Khaleel ya umurceta
da tayi alwala suyi Sallaha, ba musu ta
d’auro alwala, suka gatar da sallah, yan
tambayoyi ya mata gameda addini, ta
bashi amsa. Kayan da yazo dashi ya
d’auko musu, tana yar kunya ya ringa
bata abaki, saida ya tabbatar ta qoshi
tukun shima yaci. Daga nan yasoma
janta da hira, ganin ango da amarya
suna buk’atar hutu, yasa na fito a
d’akin, don ba hurumina a gun, nidai
Rash na musu fatan alkairi, naja musu
qofa aci Amarci lafiya.
…..Na…..
Rash Kardam
&
Khadija Candy
[8:18AM, 10/23/2016] Rash Kardam:
MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
&
Khadija Candy
~
Ranan suna yara sukaci sunan,Ameena
da Kabir, ana kiransu da Amrah da
Ameer. Cikin ikon Allah Khaleel ya fara
zuwa aiki, ya kasance mai hazaka da
k’okari a gun aiki, yanzu Alhamdulilah
suna cikin rufin asiri.
Safiya duniya gidan dad’i a gunta, yau
tana shirin zuwa Abuja gun wani
saurayinta, a motarta ta tafi, tana zuwa
office d’insa direct ta tafi.tana zuwa
kanciyansa ta d’ale, “my honey nayi
missing d’inka da yawa. rungumota yayi
suka soma bad’alansu, office d’in aka
turo Alhaji Tijjanine yazo, wani kalo ya
bisu dashi, “oh! Sorry nashigo ba excuse!
Tk yace”no! Ka shigo kawai, Sofy ta mike
ta zauna a d’aya kujeran, tunda taji ya
ambaci sunan sa, ta gane abokinsa TJ
dake bata labarinsa. Yana da kud’i sosai,
TJ yace”barinje na kawo maka, files d’in
ya fita.
Yana fita Sofy ta matso kusa dashi, tare
da kashe masa ido, ganin bai kula ba ta
soma balle botilan riganta. Cikin zuciyan
TK yace”yarinya bakisan waye Tukur ba,
ganin kar TJ yazo ya gansu, ya mika
mata phone d’insa. Number ta tasaka
masa, ana haka sukaji za’a bud’e qofa,
da sauri takoma mazauninta. TJ ya basa
komai yamusu sallama ya fita.
Daga office gidansa suka nufa, suka
bud’e babi iskancin su, kwanta uku suna
tare tace”zata tafi”.
Badan TJ yaso ba, ya bata kud’i ta masu
yawa tamasa sallama, tana fita TK ta
kira ya bata address d’in ida zata
samesa. Wani gidane kayatace na gani
na fad’a, ko da tashigo da man, ya sanar
da masu gadi zuwanta. Sai da ta wuce
gate uku bayan babban gate, sai qofofi
hudu, asalin cikin gidan yana da duhu,
ko da tashigo k’irjinta, ya soma duka
uku-uku. TK da murna ya karbeta sai da
ya kaita wani d’aki, sai da suka zuba
iskancin su yayi wanka ya fita. Wani
d’aki ya shiga, waya yakira yace”
gatanan ta iso, a turo da masu aiki,
sannan ka basu sabon wukan.
Daga d’aya bangare akace”ok! In kun
cire abunda kuke so, ina son gan-gan
jiki.
“To ba matsa”. Ya kashe wayar yana
wani muna fukin dariya.
……Na…..
Rash Kardam
&
Khadija Candy
[8:18AM, 10/23/2016] Rash Kardam:
MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
&
Khadija Candy
~
“Ok! Ba matsala”. Wayar ya kashe yana
wata munafuk’in dariya, hahaha
“Yarinya ke baki da wayo, an gaya miki
mata suna gaba nane?.
“kud’i shine da muwata, war har damin
signal da ido.
‘Dakin ya dawo, ita ko cikin wasu
matsatsun kaya wanda shi da babu duk
d’aya ne, tazo ta rungumesa bakinta ta
sanya anasa, da zai tureta, amma da
yatuna karta gane target d’insa, sai ya
biye mata suka sake kalacea. Yana
kwance a gefen gado, sai maida
numfashi yake wayarsa ne tayi k’ara, da
sauri ya d’aga yace”ya kun isone? Daga
d’aya b’an garen akace”eh! Gamu a cikin
gidan.
“Ok! To ku shigo. Ya kali Safiya yayi
murmushi yace”baby taso muje”.
Cikin shagwab’a tace”ina zamuje haka?.
“Oh! Baby kitaso da sauri, wani big deal
zamuyi. Jin babban harka yasa ta mik’e
da sauri. Suka nufi wani d’aki, wasu
k’arti ne su hud’u, suka shigo, nan take
fiskan TK ya canza tamkar bai tab’a
dariya ba. Safiya da tawani kwanta a
jikinsa, tana sha-shafa shi, hankad’ata
yayi gaban wayannan k’arti, Yace”gata
ku rike min ita. Cikin azama suka
damketa, Safiya tace”TK wani irin wasa
ne haka?.
Dariya ya bushe dashi”kee angaya miki
TK sakarai ne irinki?.
“Mayyar kud’i banza, akan kud’i kin
zubar da kimanki, darajanki, kin
bargidan iyayenki, kina bin maza don
subaki kud’i.
“Safiya kin d’au ma kanki abunda zaki
wahala.
“Kisani duk abunda d’a namiji yayi ado
ne garesa, banda’ya mace.
“Yau zan koya miki hankali.
“Ku rufe mata baki. Safiya ta fara
cewa”TK dan Allah kayi hak’uri, kar ka
cutar da ni.
“Na maka alkawarin daga yau na daina
iskanci daga yau.
Dariya yayi yace”ke ta shafa, yanzukan
kijira zuwanki kiyama. Safiya ba halin
magana an rufe bakinta.
Wanu abu ya d’auko a gidansa, kamar
na shentos, yarike ya kaleta yace” na
manta ban sanar miki ba, ayanzu duk
wanda kika ga yayi kud’i kazamin kud’i
to ba duka bane na gaskiya, suna
had’awa da yankan kai da shan jini.
“Nima ina d’aya daga ciki, son kid’in ki
ya kawoki.
“Ko TJ da kike gani ba zaman office bane
ya tara mishi wannan kud’in, shima
yana yankan kai, abunda ya hana bai
yanka ki ba, sabida yana matuk’ar sonki.
Shiru yayi na d’an wani lokaci, Safiya ko
hawaye ke zuba sosai, tana sonyin
magana ba dama.
TK yacigaba da cewa”Safiya amma ke
tsaban bariki da cin AMANA, abokinsa
yazo kika nuna kuyi tarayya dashi, ni
kuma ba na sonki niman mata baya
gabana, wacce nakeso d’ayace kuma
bana had’a soyayyanta dana kowa. Yana
gama fad’an haka, yace”kurike min ita”.
Safiya naji tana gani yazo gabanta
wannan abun, yafesa mata a ido, take
taji wani azaban, da bata taba’a jin
irinsa ba, tana kuka haka suka saka
wuka cikin kwarewa, ya cire mata
idonta duka biyu.
Suna gamawa yace” ku kaimasa gan-gan
jikin na d’auki abunda nakeso.
Safiya da azaba yasa ta suma, kattin nan
suka d’auki ta suka sata a Mota suka bar
gidan. Ko da suka fito wani abun
mamaki, gidan da ke cikin gari ya koma
jeji, gudu suka soma shararawa a titi.
Nikam Rash da tsoro yacikani, kasa bin
su nayi, har sai sunyi nisa nabisu inga
mai zai wakana, don kar nima a yanken
kai.
…..Na….
Rash Kardam
&
Khadija Candy
[8:20AM, 10/23/2016] Rash Kardam:
MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
&
Khadija Candy
~
Gudu sosai sukeyi, sai da sukayi tafiya
mai nisa, d’aya daga cikin mutane
hud’un nan yace”ya Baba nifa yarinyan
nan tun d’azu na kamu da
KWA’DAYINTA, ko zamu ratse da ita ne,
in mun kwashi gara, sai mu kaimasa ita,
kuma kaga yanayin jikintan nan zamu
huta. Duka suka yarda a haka, kwana da
motarsu sukayi, suka nufi wani
k’aramin gida mai kyau, nan suka kaita,
biyu suka shuga cikin gari suka sayo
musu abinci da juice, sai da suka yayya
fa mata ruwa ta far-fad’o, suka bud’e
mata baki, d’ayan yace akwai sauran
maganinane ka bata, don oga yaso mata
mugunta ne, da ya shafa maganin nan
bazataji zafi ba. ‘Dayan ya d’auko wani
ruwan magani, suka shafa mata, take taji
idon ya rage zafi, abinci suka tura mata,
sai da taci ta koshi suka bata ruwa tasha.
‘Daki suka kaita nan suka cire kananun
kayan jikinta, suka fara cika aiki. Safiya
duk son Sex d’inta yau tashiga nadama,
yau ta yarda da karin maganan hausawa
dasuke cewa duk wanda yashiga MOTAR
KWA’DAYI zai sauka a tashan wulakanci.
Yau maza hud’u a kanta gashi bata da
ido, nan tafara addu’a Allah ya kwaceta.
Sai da suka gama biyan buk’atar su suka
tashi.
‘Dayan yace”gaskiya tunda nake d’ana
mace, ban tab’a jin mai test kamar
wannan ba, haka sukayi tayin hira, da
yamma biyu suka fiya d’aya yashiga
wanka, wanda ya yaba da ita yace”ke
zan taimake ki, zai kaiki qofar gida
kisan yanda zaki gudu, don banzo acinye
ki, kin min kyau, kai ta d’aga masa
alamar eh!.
Kama hannuta yayi yana leke ya tura ta
waje yace ta mike da gudu, yana komwa
daman a falo suke da ita, daki yashiga
ya kwanta kamar bai san komai ba.
Gudu take sosai gashi bata gani, haka
zata fad’i ta tashi duk ta gwara jikinta
sai jini yakeyi, a haka harta fito wani titi
batayi aune ba sai jin kiiiii kake mai
mota ya kad’eta, yana gani ba mutane
kusa ya juya yasa gudu, mutane da suka
gansu, suka zo da gudu suna salati, ko
dana leka me zan gani, k’afar Safiya
guda d’aya ya dagargaje tundaga cinya,
a sume akayi asibiti da ita, sai da ta far-
fad’o. Aka tambayeta ita yar inane,
tace”a Kaduna na ke” bata sake cewa
komai ba ta suma, nan take a ka
d’auketa sai asibitin Kaduna, kwanata
uku bata san ida take ba, hakan yasa aka
d’au photo ta aka saka a gidan Tv ana
cigiyar iyayenta.
Inna Safiya tana zaune tace”oh! Yau
barin kali labarai”.
Tana kunawa dai-dai lokacin da’aka
nuno fiskan Safiya. “Ihu tasaka a guje
tayi d’akin Malam tana fad’a masa da
kamar bazai tashiba amma tuna
hakkinsu yasa ya mike, take suka nufi
asibiti, suna zuwa a ka nuna musu
Safiya Malam ya jin-jina al’amarin, nan
likita sukace su kawo dubu d’ari da
hamsin a mata aiki. Malam yace”nikam
banda shi daman duk wanda bai ji
bariba yaji hoho.
“Duk wanda yashiga MOTAR KWA’DAYI
to ba makawa zai sauka tashan
wulakanci.
“Kee na yarki gashi kun gani, kisani ba
balabarinta da ban sani ba, ido na zuba
muku, harda zuwanki gun boka, amin
asiri Allah ya kareni, yanzu sai kisan
nayi, ya juya yatafi ko wai-waisu baiyi
ba.
Inna mashin tahau da ta je gida ta d’au
gwala-gwalan Safiya duka taje kasuwa,
da tambaya taje shagon masu sayan
gwala-gwalai, tasayar dubu d’ari biyu.
Asibiti taje ta basu kud’in aiki aka shiga
da Sofy, sunaji suna gani aka yanke ma
Sofy k’afa d’aya. Haka Inna tayi zaman
jinya a asibiti.
Wanamaker sun tafi cikin ikon Allah,
kafan Sofy ya warke, har tafara tafiya da
sanda. Cikin da ke jikunta ya fito
watansa shida, Inna tana cikin tashin
hankali, ga Sofy ba k’afa, gashi ta samo
cikin shege, tabbas bariki baiyiba bariki
ba gurin zama bane.
……Na….
Rash Kardam
&
Khadija Candy
[8:22AM, 10/23/2016] Rash Kardam:
MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
&
Khadija Candy
~
Inna ta fashe da kuka tabbas,
KWA’DAYINA shi ya jawo min, na cikin
yanayin aka basu sallama, ta k’arba
suka d’au hanyan gida.
Ayshat suna rayuwansu cikin jin dad’i
da rufin asiri, duk wata yana d’aukan
70k a haka har gida 3 bedroom ya sai
musu, iyayensa ya gyara musu gidansu
suma, ya sai yar motarsa k’arama, ya
shigo gida cike da fara’a, My Sweetheart,
kina ina kizo kuga abun Alkairi, da sauri
suka fito da yara, kama hannuta yayi
suka fita qofar gida, kimga amaryan mu,
Allahu Akbar tafad’a tare da hamdala,
cike da murna yace”dan haka ki d’au
himar d’inki tare zanuje gida asanya
mana albarka. Cikin gida ta koma, ta
sauya ma twins kaya, suka shiga mota
sai gidansu.
Inna sun iso gida, suka shigo Malam
yabkaleta yace”ina kuma zaki ae ki
d’auketa kukoma ida kike turata, nikam
na yafeta a cikin ‘ya’ya na, Inna ta fara
basa hak’uri, har waje ya korosu, ana
haka sai ga su Aysha da sauri tafito, ta
rike Safiya tana kuka.
Hak’uri suka ringa bama Malam tare da
nasiha, Ayshat tace”Baba ina to zasuje ai
bata da gidan da yafi wannan.
“Kuma gannuka baya rub’a kace zaka
yar.
Umma ma hak’uri ta basa, sai Khaleel
yasa baki hakan yasa Malam ya hak’ura,
yace”kekam Inna na sakeki saki uku,
kuka ta fara tana rike rigansa ya kwace
ya tafi. Yace”kuma bana son ganinki a
gidana.
Dole Inna ta d’auki Sofy suka tafi,
duniya juyi-juyi.
Haka su Ayshat sukayi gaisuwa suka tafi.
Bayan kwana biyu, Matar abokin
Khaleel bata da lafiya, suka shirya zuwa
asibiti sai da suka gaidasu, sunzo zasu
shiga mota, Aysha taji ana kiranta, ko da
tajuya wata tagani, baka ta rame tamkar
skeleton. Nan tsoro ya kamata ta rike
Khaleel, wacce ta kira sunanta tace”baki
ganeni ba ne?.
“Seema ce kawar Safiya”
Ido Ayshat ta zaro cike da mamaki
tace”kee ce haka?.
Seema tace”eh! Nice, Ayshat tayi”salati
nasiha ta fara mata.
“Ga irin abunda ake gudun muku, ke da
k’awarki duk k’arshe ku baiyi kyau ba.
Cikin kuka Seema tace”ae mugani kam
itama naga ba k’afa ba ido.
” munyi nadama tabbas na yarda da
kalman da kuke fad’a mana duk wanda
ya hau MOTAR KWA’DAYI zai sauka a
tashar wulakanci. Kuka take sosai Ayshat
ta bud’e jakanta ta bata dubu biyi, godia
tayi mata suka shiga mota, suna hanya
kenan, juyawan da zatayi taga wasu
kamar su Inna suna bara, cike da
mamaki tasa Khaleel ya dawo, ae ko
sune fitowa tayi tace”Inna kune ana
subhanallah, Inna sai kuka, sofy ma
kuka ta fara, saida Aysha ta musu nasiha
ta ciro dubu biyar ta basu, Inna tace”
yaranki kenan har sun girma, Aysha
tace”eh sun girma.
Inna ta kira Amrah ama fir taki zusa
haka suka musu sallama suka nufi gida
cike da jimami.
Ayshat tace”tabbas iskanci bayida rana,
kuma duk wanda ya hau MOTAR
KWA’DAYI zai sauka a tashan wulakanci.
Nima Rash na kali Khadija Candy
nace”My Mumcyna tabbas hausawa
sunyi gaskiya, duk wanda ya hau
MOTAR KWA’DAYI to zai sauka tashan
wulakanci.
BAN HAK’URI
Ina mai baku hak’uri, makaranta littafin
MOTAR KWA’DAYI, na tak’aita labarin
sabida k’aratuwan Azimi. I a muku fatan
Alkairi da kuma murnan zuwan wata
amai Alfarma, Ya Allah ka amshi, ibadun
mu, Ya Allah kasa muna daga cikin
wayanda za’a yanta daga wuta zuwa
Aljannah, Ya Allah ka yafe mana
laifukan mu Ameen.
KIRA GAREKU YAN’UWA
Kira ga reku yan natan zamani, kuyi
hattara da rayuwa, bariki back
matabbata bane, iskanci baida amfani,
karuwanci back komai acikinsa said
nadama da zubuni.
Kung a daily yanda k’arshe Sofy ya
koma, muji tsoron Allah, Ya Allah ka
bamu, ikon tsare mutuncin mu, da
Imanin mu Ameen.
ALHAMDULILAH
Dukkan yabo tsarki, Mulki su tabbata ga
Allah, da yabam ikon kawo k’arshen,
wannan labari maisuna MOTAR
KWA’DAYI, kura-kuren da ke ciki, Allah
ya yafe min, ya bani ikon ganewa na
gyara. Ina fatan kun wa’azantu dashi
kuma ya nisha d’an tar da ku.
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan littafin ga
masoya da yan’uwa Allah ya barmu tare,
taku a kulum RASHEEDA ABDULLAHI
KARDAM tare da KHADIJA CANDY
KUNA RANMU
Duk Marubuta Online Hausa Wtriters,
muna muku fatan alkairi.
GODIYA
Godiya mai tarin yawa ga wayan nan
group d’in
EXTREME HAUSA WRITERS
WISDOMS HAUSA WRITERS
BEST WRITERS GROUP
GALAZAY WRITERS
MODERN HAUSA WRITERS
CLEVER WRITERS
Luv u all my fanz
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
+2347039625239

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment