Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

��ࡱ�>�� �����������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~�Root Entry�������� �F� WordDocument����<0Table���������Data
�������������������� P�ʲKSKS�<eV�������tt������� ���ddddddddf$��{*t��dd����d����d�d��dd�� GARKUWAR MUSULMI


SHIMFI�A: Akwai muhimman sirrika masu mabambantan fa'idodi a cikin ayoyi da hadisan Manzon ALLAH (SAW) waWanda idan musulmi mai imani yayi ri�o dasu, tabbas ya gama cin riba da nasara a rayuwar shi ta duniya da lahira. A wannan littafin na kawo kaWan daga cikin fa'idodi da sirrikan da suke cikin Qur'ani da hadisan Manzon ALLAH (tsira da amincin ALLAH su �ara tabbata a gare shi) kuma zan cigaba da kawowa a cigaban wannan littafin in shaa ALLAHU don ina da niyyar rubuta guda Wari saboda haka wannan littafin mai Wauke da guda sha biyun na farko ne daga cikin jerin littattafan da zasu zo masu taken GARKUWAR MUSULMI.

� ANSARULLAH
WhatsApp no. +2348067396502
Email: abdullahialiyu3214@gmail.com







(1)
Qur'ani garkuwa ne ga mumini ta yadda akwai ayoyi a cikin sa waWanda suke zama garkuwa ga wanda yayi ri�o dasu da imani. Daga cikin ayoyin Qur'ani akwai wasu da Manzon ALLAH (SAW) ya koyar da amfani dasu a waWansu lokuta domin amfanin masu imani saboda shi Qur'ani waraka ne daga dukkan cututtuka kuma akwai garkuwa a tare da ayoyin cikin sa. Akwai wasu ayoyi guda biyu waWanda ko �an fashi ne ko wasu mugaye masu cutarwa ne suka bi ka zasu cutar da kai idan ka karanta su tabbas zasu zamanto maka garkuwa sai dai idan baka da imani. Ayoyin su ne: Aya ta 9 ta cikin suratul Yasin (sura ta 36), ta biyu kuma itace aya ta 45 ta cikin suratul Isra'i (sura ta 17). Duk waWannan ayoyin Annabi yayi amfani dasu kuma ya ga aikin su haka ma magabata sun gwada kuma sun ga tasirin su.

(02)
Musulunci bai bar komai ba sai da ya kawo kuma musulmi mai imani komai nashi ibadah ne idan har zai aiwatar bisa turbar koyarwar shari'a. Komai zaka yi akwai Addu'ar da Manzon ALLAH (SAW) ya koyar. Akwai addu'ar yin barci, tashi daga barci, shiga bayan gida, fitowa daga bayan gida, yin alwala da sauran abubuwan rayuwa na yau da kullum.
Akwai lokuta na musamman waWanda ake amsa addu'a kuma akwai waWansu mutane waWanda ba'a mayar da addu'ar su. Dangane da lokutan da ake saurin amsa addu'a a cikin su Manzon ALLAH (SAW) yace: Mahaliccin mu mai tsarki da buwaya yana zuwa a ko wane dare kusa da kusa a thuluthin �arshe na dare (kashi Waya cikin uku na dare na �arshe) sai Yace: Akwai wanda zai ro�e Ni don In amsa mai? Akwai wanda zai tambaye Ni don In bashi abinda ya tambaya? Akwai wanda zai nemi gafara Ta don In gafarta Mishi? (a wannan lokacin ALLAH Yake buWe �ofar da addu'a take saurin karSuwa domin a lokacin gwanjon rahamar Sa Yake yi ga masu rabon kasancewa a farke don amfani da wannan damar a wannan lokacin). Akwai wani ladabi na yin addu'a a ko wane lokaci. Ladabin shine ka yiwa Wan uwan ka addu'a ba tare da ya sani ba. Manzon ALLAH (SAW) yace: Duk wanda yayi wa Wan uwan sa addu'a, Mala'iku suna nan zasu cewa Amin kai ma haka (ALLAH Ya baka abinda ka ro�awa Wan uwan ka). Idan Mala'iku suka ce Amin kai ma ALLAH Ya baka irin abinda ka ro�awa Wan uwan ka, addu'ar karSaSSiya ce a gurin ALLAH. A aya ta 85 ta cikin sura ta 4 (suratun Nisa'i) ALLAH Ya tabbatar da hakan kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba na 1432 da Muslim mai lamba na 2627 suka tabbatar da fassarar ayar. Sau da yawa taimakawa Wan'uwan ka ta hanyar addu'a yafi taimaka mishi da kuWi amma mutane sun Wauka kawai sai ka basu kuWi kawai shine ka taimaka musu bayan bawa mutum kuWi shine kusan nau'in taimako na �arshe a �an uwantaka tunda yana biyo bayan shawara, nasiha da sauran su. Akwai kuma wani lokaci wanda Manzon ALLAH (SAW) yace lokacin ta�aitacce ne a ranar juma'a wanda Annabi yace duk wanda ya dace da wannan lokacin yana sallar, duk addu'ar da yayi za'a amsa mishi. Mafi ingancin zance shine gab da faWuwar rana wanda ba'a sallah a wannan lokacin amma Manzon ALLAH (SAW) ya tabbatar da cewa duk wanda ya zauna a masallaci yana jiran sallah, to kamar yana cikin sallah ne. Akwai kuma lokacin sujuda wanda Manzon ALLAH (SAW) yace a yawaita addu'a a wannan lokacin saboda idan mutum yana halin sujuda, ya fi ko wane lokaci kusanci ga ALLAH. Lokutan amsa addu'a ya haWa da lokacin saukar ruwan sama da bayan kiran sallah da bayan an yi sadaka ko wani aikin alkhairi da ikhlasi duk �ankantar shi za'a iya tawassali dashi a ro�i ALLAH.
Game da waWanda hadisi ya nuna ana saurin amsar addu'ar su akwai matafiyi (idan kana halin tafiya wacce ta halatta kayi amfani da wannan damar ka ro�i ALLAH don Yana saurin amsa addu'ar da aka yi a wannan yanayin), addu'ar wanda aka zalunta (Annabi yace bata da shamaki gurin isa ga ALLAH saboda haka yana saurin karban ta da zarar an yi), addu'ar iyaye ga �a�an su da addu'ar shugaba adali (duka waWannan addu'oin ALLAH Yana saurin amsar su).

(03)
Manzon ALLAH (SAW) yace: Idan mutum yayi addu'a; ko dai a amsa masa nan take, ko kuma a jinkirta masa ko kuma a tanadar mai sakamakon ta zuwa ranar Qiyama wanda sai ya gama cire rai da tsammani daga samun aljanna sakamakon �arancin ayyukan sa sai a kawo wani lada mai nauyi da girma a Waura a mizanin ayyukan shi na alkhairi wanda nauyin shi zai sa ayyukan alkhairin shi su rinjayi na sharrin da yake dasu. A lokacin zai yi buri yace ina ma da ba'a taSa amsa addu'ar sa a duniya ba (ina ma duk addu'o'in da yake yi ajiye mai ake don wannan ranar).
Daga cikin amfanin addu'a akwai tare bala'i wato idan wani bala'i ya tunkaro ka a halin da kake yawan yin addu'a, addu'ar zata fuskanci bala'in kuma suyi karo da ita wanda yafi wani �arfi ya rinjayi Wayan. Idan kaga bala'i ya same ka da sau�i, amfanin addu'ar da kake yi ne. Manzon ALLAH (SAW) yace: Babu abinda yake mayar da �addara (ba abinda yake da �arfin tunkuWe mummunar �addara) sai addu'a.
Musulmi mai imani baya cewa ya gaji da yin addu'a saboda ba'a amsa ba. Idan har kana da imani to tabbas sai kaga amfanin addu'a a rayuwar ka sai dai idan kana yin munanan ayyukan da suke hana addu'ar karSuwa.

(04)
Abu Huraira (ALLAH ya �ara yarda dashi) yace: Naje gurin Kabal-Ahbar a ur (dutsen sinin) inda muka zauna dashi muna hira (ta ilimi) ya karanta min Attaura nima kuma na karanto masa hadisan Manzon ALLAH (SAW). Daga cikin hadisan da na kawo mishi akwai wanda Manzon ALLAH SAW yace "Mafi falalar rana daga cikin ranakun da rana take Wagawa a cikin su itace ranar Juma'a. Itace ranar da aka halicci Annabi Adam (AS) kuma a cikin ta aka saka shi a Aljanna, a cikin ta ALLAH ya yafe masa kuma a cikin ta ya koma ga ALLAH (ya mutu). A cikin ta (Ranar juma'a) akwai wata sa'a (lokaci) wacce duk wata dabba tana sauraron zuwan ta tun wayewar gari har faduwar rana cike da fargaba banda mutum da aljani. Lokaci ne wanda ALLAH yake bawa bawan sa musulmi duk abinda bawan ya ro�a idan ya dace da lokacin yana sallah. Ka'ab yace: Wannan sau aya ne a shekara? Abu Huraira yace: A'a duk ranar juma'a ne. Sai Ka'ab ya karanta Attaura yace: Lallai Manzon ALLAH (SAW) ya gayi gaskiya. Abu Huraira yace: A hanya ta na hau da Basra an Abu Basra Al Giffari ya tambaye ni yace: Daga ina kake? Sai nace mishi daga �ur sai yace: Idan da na ga tafiyar ka ba zaka je ba don naji Manzon ALLAH (SAW) yace: Kuyi tafiya kawai zuwa masallacin Makkah, masallacin Madina da Baitul Ma�dis. Abu Huraira yace: Sai na haWu da Abdullahi bin Salam kuma na bashi labarin zuwa gurin Kabal Ahbar da nayi da kuma hirar da muka yi dashi sai Abdullahi bin Salam yace: Ni ko nasan wannan lokacin. Sai Abu Huraira yace: Ka sanar dani (kar ka Soye min). Sai Abdullahi bin Salam yace: �arshen ranar juma'a ne (lokacin fauwar rana). Sai Abu Huraira yace: Ya za'ayi ya zama wannan lokacin bayan Manzon ALLAH (SAW) yace: Lokacin da mutum yake sallah ne kuma Manzon ALLAH SAW ya hana sallah a wannan lokacin? Sai Abdullahi bin Salam yace: Baka ji Manzon ALLAH (SAW) yace: Duk wanda ya zauna a masallaci yana jiran sallah to yana cikin sallah har lokacin sallar ba? Sai Abu Huraira yace: Eh haka ne. Sai Abdullahi bin Salam yace: To lokacin ne.

(05)
Lokaci irin wannan wato lokacin sanyi/hunturu yana da matu'kar mahimmanci ga masu ibadah kamar yadda dare ya fi rana tsawo a irin wannan lokacin. Ko baka sallar dare ya kamata ka fara don kar kayi asarar irin wannan lokacin da masu wayo suke son zuwan shi don cin riba a cikin shi. Masu wayo ko basa yawan yin azumin nafila suna yawaita yi a irin wannan lokacin saboda sau�in da yake tare dashi. Ko karatu da bincike kake yi irin wannan lokacin zai zamanto maka wata dama ta musamman tunda zaka iya amfani da tsawon dare wajen yin abinda ba zaka samu damar yin sa a wuni ba saboda gajarcin wunin.

(06)
A cikin aya ta 21 ta cikin suratul Ahzab (sura ta 33) ALLAH yace: "Ha�i�a koyi mai kyau daga halayen Annabi (SAW) ya kasance gare ku; ga wanda yake fatan samun yardar ALLAH da sakamako mai kyau a lahira kuma yana ambaton ALLAH da yawa". Wani ya tambayi Waya daga cikin uwayen muminai wato Ummu Salma (Waya daga cikin matan Manzon ALLAH SAW) Wabi'un Manzon ALLAH (SAW) sai tace mai: Baka karanta Qur'ani? Sai yace: Yana karantawa. Tace to Qur'ani shine Wabi'un sa. Duk mumini yana bu�atar Wabi'antuwa da Wabi'un Manzon ALLAH (SAW). Manzon ALLAH (SAW) yace: Ba'a aiko ni ba sai don in cika kyawawan Wabi'u. Kyawawan Wab'iun Manzon ALLAH (SAW) sun taimaka masa matu�a hatta wajen isar da sa�on Manzonci wanda ALLAH ya aiko sa dashi wanda hakan yasa da yawa daga cikin ma�iyan musulunci sun shiga musulunci ta sanadiyyar kyakkyawar mu'amalar Manzon ALLAH (SAW). A matsayin ka na musulmi me ikirarin son Manzon ALLAH (SAW) ya kamata a ga tsantsar soyayyar da kake mishi a aikace ta hanyar koyi da halayen sa da yin abubuwan da yayi da waWanda yace ayi da barin abubuwan da yace a bari. A matsayin ka na mahaddacin Qur'ani ko masanin hadisai da tarihin Manzon ALLAH (SAW) ya kamata a ga abu da ka sani a aikace a tare da kai don idan ba kayi rayuwar ka ta hanyar aiki da ilimin ba babu amfanin sanin tarihin rayuwar Manzon ALLAH (SAW) da kayi. A aya ta 29 ta cikin suratul Fath (sura ta 48) ALLAH ya kawo siffofin sahabban Manzon ALLAH (SAW) waWanda su ne sukayi koyi dashi da gaske don mu ma muyi koyi dasu. ALLAH yace: "Annabi Muhammad Manzon ALLAH ne kuma waWanda suke tare dashi masu tsanani ne ga kafirai (ba zaka gane wannan ba sai kasan yanda suka yi a fagen daga) amma masu rahama ne a tsakanin su...." Tambaya anan itace: shin mu a yau masu rahama ne a tsakanin mu? ALLAH yasa mu gane amma dole ne muyi koyi da karantarwar musulunci a aikace ta hanyar yin ri�o da Wabi'u da halayen Manzon ALLAH (SAW) da sahabban sa da sauran magabatan da suka bi sahun su kafin mu cika sharaWin zama muminai domin muminai kamar gini suke wanda idan matsala ta samu wani Sangare, kamar ta shafi duka ginin ne saboda haka zasu haWa �arfi da �arfe wajen magance matsalar da ta samu wani daga cikin su kuma ta hakan ne zasu ci nasara a duniya da lahira.

(07)
Sura ta farko a jerin sifofin Qur'ani wato suratul Fatiha wacce ake kira Ummul Kitab (uwar Qur'ani) garkuwa ce kuma akwai maganin cututtuka a cikin ta. Wata rana wasu sahabban Manzon ALLAH (SAW) suna halin tafiya sai suka wuce ta �auyen wasu mutane na wata �abila daga cikin larabawa sai suka nemi yada zango a �auyen (saboda dare yayi) amma sai mutanen �auyen suka �i basu masauki (saboda haka sai suka kwanta a waje). Kunama ta harbi shugaban mutanen �auyen kuma sun yi duk maganin da suke dashi amma shugaban nasu ya kasa samun sau�i sai wasu daga cikin mutanen garin suka ce tunda ba maganin da yayi me zai hana su tuntuSi waWancan ba�in (sahabban Annabi) domin mai yiwuwa suna da wani maganin da zasu mishi. Ba ko kunya suka je gurin da sahabban suke (duk da sun �i karSan ba�untar su) suka ce musu sarkin su ne kunama ta harbe shi (ko maciji) kuma sun yi duk magungunan da suke dasu amma duk a banza. Suka cewa sahabban ko suna da maganin da zasu iya mishi. �aya daga cikin sahabban yace eh yana da maganin da zai mai amma sai sun biya shi tunda sun �i karSan ba�untar su. Suka yi ciniki suka amince zasu biya shi garken awaki idan ya yiwa shugaban nasu magani kuma ya warke. Da suka tafi suka kai shi har inda shugaban nasu yake sai ya karanta masa fatiha (a inda kunamar ta harbe shi). Yana gama karanta mai sai shugaban mutanen yaji ya samu sau�i kamar an kunce shi daga Waurin sar�a. Sai aka bawa wannan sahabin garken awakin da aka yi sharaWi. Wasu daga cikin sahabban suka ce a raba awakin amma shi wanda ya bada wannan maganin yace a bari sai an koma an gayawa Annabi yadda aka yi don a ji me zai ce (shi wanda ya karantawa shugaban �auyen Fatiha har ya warke yace haka ne saboda yana jin tsoron kar su raba awakin da suka samu kuma ya zama sun yi ci da addini shi yasa yace kar a raba a bari sai an tambayi Annabi matsayin awakin da aka samu ta wannan hanyar tukun). Da suka koma suka bawa Annabi (SAW) labari sai yace: Ya aka yi ka san Fatiha ru�iya ce? Sai (Annabi) ya cigaba da cewa: Kayi daidai kuma nima a raba har dani. Fatiha ru�iya ce ru�iya ce (magani ce) musamman idan aka tofa a ruwan zamzam.

(08)
Manzon ALLAH (SAW) yace: �oluluwar daraja (daga cikin surorin) Qur'ani itace suratul Ba�ara kuma a cikin ta akwai ayar da tafi ko wacce a Qur'ani (wato) Ayatul Kursiyyu. Ayatul Kursiyyu tana da falala da sirrika masu yawan gaske musamman ma ta 6angaren tsari. Akwai wata �issa ta wani bawan ALLAH wanda yana kan tafiya mai nisa sai dare ya cin masa kuma ya yada zango a daji. Da yazo zai kwanta sai ya karanta Ayatul Kursiyyu sannan ya kwanta. Cikin dare sai ya dinga jin 'karar wani abu yana tahowa sai yaci karo da wani abu wanda sautin yafi kama da na katanga. Haka ya dinga jiyowa amma kuma da yake ya yarda da abin da ya karanta yayin kwanciya a gurin, sai ya cigaba da barcin sa ba tare da tsoron komai ba. Da safe bayan yayi sallar Asubah yayi Azkar kamar yadda ya saba sai ya kama hanya don cigaba da tafiya. Yana fara tafiya sai yaga wani tsoho a zaune a gefe sai tsohon ya tambaye shi yace: "Me ka karanta da zaka kwanta a gurin can"? Bayan ya gaya mishi sai shi tsohon yace: "Ni Aljani ne kuma wannan gurin da ka kwanta gida na ne; na dawo nazo shiga shine na dinga cin karo da wata katanga". Tasirin Ayatul kursiyyu ta kai idan ka karanta ta ba iya gidan ka ba hatta ma�wabtan ka sai ALLAH Ya kare su da kariyar Sa albarkacin karanta ta da kayi. Ayatul Kursiyyu babbar makami ce ta ya�ar shaiWanu musamman na cikin Aljanu. Idan ka karanta ta a dare tabbas ALLAH zai tsare ka har wayewar gari sai dai idan baka da imani don ba iya shaiWanun Aljanu ba hatta shaianu daga cikin mutane waanda suka haa da 'yan fashi duk tana maganin su.



(09)
Aya ta 22 ta cikin Suratun Nur (sura ta 24) an saukar da ita ne ta sanadiyyar Abokin Manzon ALLAH (SAW) wato sayyidina Abubakar (ALLAH Ya �ara yarda dashi). Abinda ya faru shine: Bayan an yiwa �ar sa uwar muminai Aisha (Matar Manzon ALLAH SAW) �azafin zina, mahaifin ta Abubakar ya gano cewa daga cikin waWanda suka bada gudunmawa wajen yayata �azafin akwai �an uwan sa waWanda suka zo suna zaune a gurin sa shine cin su shine shan su wato ma'ana dai basu da komai don sun yi hijra ne. Saboda butulcin da suka mai sai Abubakar Win yayi rantsuwa yace: Ba zai �ara musu komai ba (don ba�in cikin abinda suka aikata na yiwa Nana Aisha �azafi). Sai ALLAH Yace: "Kar ma'abota falala da dukiya su yi rantsuwa akan ba zasu taimakawa �an uwan su (na jini) da talakawa da waWanda suka yi hijra akan hanyar ALLAH; kuyi yafiya kuma ku manta. Shin ku bakwa so ALLAH ya yafe muku ne? ALLAH mai yawan gafara ne". Da Abubakar Win yaji ayar sai Yace: Eh muna so! (Ma'ana mu ma muna so ALLAH Ya yafe mana). Wannan yana nuna mana komai zamu yi muyi da kyakkyawar niyya wato don ALLAH. Idan muka yarda don ALLAH muke yin aikin alkhairi, lallai zamu tsayu a kai kuma haushin mai jin haushi da hassadar mai hassada da barazanar mai barazana da �in mai �i ba zasu sa muyi ko gizau ba daga tsayuwa a hanyar ALLAH kuma zamu dogara da ALLAH ta yadda ALLAH Zai taimake mu kuma Ya cika mana al�awarin da Ya mana na cika mana ladan aikin da muka yi domin Sa tunda baya rage ladan masu kyautatawa.
�alubane ne gare mu; mu dinga yiwa mutane alkhairi kawai don ALLAH domin Shi ALLAH baya karSan aikin da ba'a yi don Shi kaWai ba. Idan ka yiwa mutum alkhairi don ya ramawa kura aniyar ta, idan ya rama maka iya ribar ka kenan baka da lada a gurin ALLAH. Idan kuma ka yiwa mutum alkhairi don kai ma ya maka amma sai bai rama maka abinda ka mishi don shi ma ya maka ba asara biyu kenan.


(10)
Manzon ALLAH (SAW) yace: "Duk wanda yake so ALLAH ya �ara mai yawan arziki kuma ya �ara mai tsawon rayuwa to ya sadar da zumunci". Wannan bai ci karo da hadisan da suke tabbatar da cewa ana rubuta komai na mutum tun yana cikin mahaifiyar sa ba. Malaman da suke cewa abinda hadisin yake nufi shine idan mutum yana sada zumunci ba za'a �ara mishi tsawon rayuwa da yawan arziki bane, suna cewa abinda aka rubutawa mutum na arziki da ajalin sa ba zai wuce su ba. Suna cewa abinda hadisin yake nufi shine za'a �ara yawan albarkar rayuwar mai sada zumunci da albarkar arzikin sa. Ba haka hadisin yake nufi ba kuma dangane da ayoyin da suke kafa hujja dasu kan cewa ba'a jinkirtawa wata rai idan ajalin ta yazo, idan kuma bai zo ba fa? A ta�aice dai aya ta 39 ta cikin suratul Raad (sura ta 13) ta rama gardama don ta tabbatar da cewa ALLAH Yana da ikon goge abin da ya rubuta a uwar littafi (Lauhul Mahful) kuma Yana da cikakken ikon mayar da abinda Yaga dama gurbin abinda Ya goge. WaWanda suke wancan fassarar ta cewa ALLAH ba zai �arawa mai sada zumunci tsawon rayuwa ba suna raunana ikon ALLAH ne. Ko mutum ne yayi rubutu yana iya gogewa ya mayar da wani abu a gurbin balle ALLAH. Kamar yadda addu'a take kawar da mummunar �addara, haka ma sadar da zumunci yana �ara tsawon kwana da yawan arziki a kan wanda aka rubutawa mutum tun yana cikin mahaifiyar sa idan yana sada zumunci. Akwai riba mai yawa a cikin sadar da zumunci musamman ga waWanda basa sadar maka dashi kuma kayi don ALLAH ba irin zumuncin yanzu ba wanda sai kana da abun duniya shine za'a sadar maka a'a irin wannan ba lada kuma babu riba don ba don ALLAH aka yi ba. Manzon ALLAH (SAW) ya tabbatar da cewa: Mai yanke zumunci ba zai shiga Aljanna ba. Ka sadar ko za'a wula�anta ka a zage ka kuma kar kace sai kayi kuWi kafin kayi don baka da tabbas a rayuwar ka kuma ko kayi kuWin da wuya ka iya yi idan baka iya yi tun yanzu. Ba sai da kuWi ake zumunci ba kuma ba don kuWi ake yi ba balle ma ka ji sakamakon da ake sakantawa masu sadar dashi tun a duniya kamar yadda Manzon ALLAH (SAW) ya faa. ALLAH ya bamu ikon sadar da zumunci don mu ma ALLAH Ya sadar damu da rahamar Sa.

(11)
An tambayi Manzon ALLAH (SAW) cewa: "Wane aiki ne yafi kyau a musulunci?" Sai yace: "Ciyar da abinci da yaa sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba".
* Ciyar da Abinci babi ne mai zaman kan sa wanda yana da fadi sosai. Ciyar da abinci ga mabu�ata da sauran mutane masu tsoron ALLAH garkuwa ne mai saurin sadar da bawa ga rahamar ALLAH. Ya tabbata Manzon ALLAH (SAW) yace: Salihai daga cikin bayin ALLAH masu gudun duniya zasu yi ceto irin nasu bayan ALLAH Ya basu dama. Bayan an musu hisabi kuma ALLAH Ya tabbatar da sakamakon SHI na ni'imar SHI a kan su, ALLAH Zai ce: "Ku zagaya (a filin Qiyama kenan) duk wanda kuka gani wanda ya taSa shayar daku wani abun sha ko ya ciyar daku ko da loma Waya ne (a duniya), ku kamo hannun shi ko hannun ta zuwa Aljanna (waWanda hakan zai faru akan su wato waWanda za'a ceta su ne waWanda ayyukan su suka hana su shiga aljanna; ayyukan su sun yi kaWan saboda haka suna bukatar �arin lada don mizanin ayyukan alkhairin su yayi nauyi su shiga Aljanna). Manzon ALLAH (SAW) yace: "Kar wani ya ci abincin ka sai mai tsoron ALLAH". Tabbas ta hanyar ciyarwa ALLAH yana tausayawa mutane saboda al�awarin ALLAH ne cewa duk wanda ya tausayawa Wan'uwan sa musulmi ALLAH Zai tausaya masa, duk wanda ya ciyar da musulmi ALLAH zai ciyar dashi, duk wanda ya tufatar da Wan'uwan shi musulmi ALLAH zai mishi sitira duniya da lahira. Akwai wani mutum da aka bani labarin sa wanda ya mutu. Kafin mutuwar tasa ya kasance yana yin azumin Litinin da Alhamis kuma yana yin azumin wata rana ma har rana ta faWi bashi da abinda zai yi buWe baki dashi kuma bai daina ba, a wannan halin ya koma ga ALLAH don an ce a washegarin ranar da ya mutu (ya mutu ranar juma'a) to ranar Alhamis yayi azumi amma sai ya rasa abinda zai yi bue baki dashi. Ba sai kana da kui ne shine ma�wabtan ka suke da hakki a kan ka ba balle ma kaWan Win da kake rainawa shine mai yawan da wasu suke gani. Mu tanadi abinda zamu gayawa ALLAH yayin haWuwar mu da ALLAH idan muna barin ma�wabtan mu da yunwa a yayin da muke ci mu �oshi a cikin gidajen mu har ma wani lokaci a zubar a shara. Wannan da na kawo labarin sa iri-irin su suna nan a cikin mu kuma idan bamu taimaka musu ba to lallai bamu sauke nauyin da ALLAH Ya Wauka mana ba. Wani idan ka bashi Wari biyar a irin wannan lokacin, kamar ka bashi dubu goma zai ji duk da rashin daraja da albarkar kuWin da aka fuskanta don shi kuWi ne mai yawa a gurin shi don ta yiwu bashi da komai ka bashi wannan Wari biyar Win. Idan kana zaune a anguwar da akwai talakawa a cikin ta, ka tambayi matar ka don ta san duk irin waWannan mutanen a cikin anguwar a ma�wantan ku. Manzon ALLAH (SAW) yace: "Kuyi rahama (ku sau�a�a, ku tausayawa) waWanda suke �asa sai Wanda yake sama (ALLAH) Ya tausaya muku kuma kuma Ya sau�a�a muku. Al�awarin ALLAH da maganar Manzon ALLAH (SAW) tabbatattu ne.

(12)
A cikin hadisul Qudsi Manzon ALLAH (SAW) yace: ALLAH Ma'abocin girma da Waukaka yace "Farkon abinda za'a fara yiwa Wan Adam hisabi dashi ranar Qiyama shine sallah. Idan aka samu sallar shi ta cika, ya ci nasara kuma ya rabauta (saboda sauran abubuwan ma ana sa ran zasu zo da sau�i). Idan kuma bata cika ba, zai taSe kuma asara zata tabbata a kan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment