Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tasa hade da xani da dangwali" bayan ta gama shiryawa kujera ta dauko tafito bakin kofa ta xauna hade da gwadawa Zahra kira.

"Da sauri Zahra ta fito hade da dukawa a gaban mm tace gani" Zahra tana fitowa kallon da zata wa mm kayan da Haidayr ya siye mata ne a jikin mm a take taji wani iri a xuciyarta nan da nan idanunta suka cuko da kwalla.

"Mm tace wa Zahra tashiga kici ta dibo masara ta fanfare ta rabashi da kodagon shi sae akai nika" Zahra tace to.

"Shiga tai ta dibo masaran taxo ta zauna tana fanfara tana kwalla"da haka har ta kare tana karewa ta kwashe kodagon takai ciki snn taxo ta share gun takoma daki.

"Tana shiga daki ta fashe da kuka" haka tai tayi har Haidayr yadawo, Koda yadawo ya ganta tana kuka babu irin tambayar da bemata ba amma taki fadi masa.

"Haka yagaji ya kyaleta.

"Haka dae rayuwar Zahra ya kasance a gidan Haidayr.

"Bayan wasu kwanaki Zahra ta tashi da zanxabi da amai"Duk abinda taci baya xama hakan yasa Haidayr yace ta tashi ya kaita asibiti.

"Mm tace yabari ta jika masa magani gida.

"Haidayr yace aa gara sutafi asibiti xaifi.

"Mm tace adawo lpy.

"Haidayr yace amin mm.

"Haka ya dauketa suka tafi asibiti.

"Suna zuwa yasiye kati snn sukaga likita"idanu Zahra yafara dubawa da tafin hannu yagano tana da ciki, Duk da haka sae da yasa akai mata text na fitsari snn ya tabbatar da cikin ne da'ita na wata daya da kwanaki.

"Bayan ya fitone yace nurse tai masa mgn da Haidayr"Bayan Haidayr ya shigone likita yake sanar masa Zahra nada ciki har na wata daya da kwanaki.

"Haidayr yai murna sosae.

"Snn likita yace tana bukatar abubuwa masu kara jini da vitamin" kuma kada tayi aikin karfi sbd komai zai'iya fadiwa.

"Haidayr yace babu damuwa in Allah ya yarda za'a kiyaye.

"Snn likita da ya rubuta masu magani suka koma gida" Haidayr da murnarsa ya sanarwa mm.

"Itama mm murna tai sosae.

"Itako Zahra daki ta shige sbd kunya.

"Tun daga lokacin duk dare sae Haidayr ya siyewa Zahra su akwai balangu wani lokacin kuma yace asoya mata indomie da akwai"Idan yanada isanshen kudi ya hada mata da moutina.

"Ranar da beda kudi kuma ta hakura" Da mm tagane har daki tabisu lokacin suna cin soyayyar kwai da kaza mm ta xaxxagesu daga shi har Zahra.

"Har tana cewa Aley kabani mmki ashe akwai ranar da xaka iya cin abu ka yabani Aley.

"Karfa ka mance sbd naga kasamu ingantance rayuwa kamaxa abin kwatance a garin nan yasa na tsaya tsayin dake akan ka nasiyar da duk wani kaddarata da wanda mahaifiyarka yabashi nasiya dan naga kafita da ban acikin matasan yankinga.

"Inaso ka fadimi daga kauyenga har makobtanmu waye yasamu ilimi kamar ka?" Duk baga'year uwana wanda mazajensu suka rasu bayan nake uban ba"suyi aure su barni.

"Nima ai ba wuce auren nai ba'kuma ba rasa maniman nai ba"Duk na jinginasa ne sbd naga rayuwar ka ta iganta amma shine har xaka iya cin wani abu kaida matarka kuwareni.

"Mm ta karisa mgnr ne da kuka fita tai takoma dakinta tana share hawaye.

"Hankali Haidayr yai mummunar tashi sakamakon maganganu da mm take fada a kasa.

"Mikewa yai yabita har daki dukawa yai gwiwa bibbiyu yana fadin dan Allah mm kiyi hakuri kiyafemin in Allah ya yarda hakan bazai sake faruwa ba.

"Banxa mm tai dashi bata tankasa ba.

"Kara matsowa Haidayr yai kusa da'ita hade da rike mata kafa yana fadin dan Allah mm" na tabbata idan kikai fushi dani baxanga haske a al'amurata ba kiyi hakuri kinji mm.

"Nisawa kawai tai hade da cewa Allah ya kiyaye gaba.

"Haidayr yace amin nagode.

"Itako Zahra tai kuka har ta gode Allah.

"Haidayr yana shiga daki kwanciya kawai yai.

"Tun daga lokacin Haidayr ya daena siyowa Zahra komai"Idan har yasiyo mata matsa masa tai da ko kuma idan tasa masa kuka.

"Shine yake siyo mata" Shi din ma bari yakeyi sae ya tabbata mm tayi bcc snn zai bude kofa ya siyo mata, da asuba idan xai fita sallar asuba daukar ledar yakeyi ya fita dashi idan yai nisa da gida sae ya yar.

"Bayan wata daya lokacin Haidayr yatafi aiki"ita kuma Zahra tana daki kwance mm ta kwada mata kira.
"Zahra na fitowa tace mm gani" da fara'arta tace dama gerone nakeso ki surfemi sbd yau furan hannu ne nskejin sha.

"Kafin mm ta karisa gaban Zahra yai mummunar fadi" to kawai tace.

"Amsar geron tai taje ta xuba a turmi hade da ruwa tafara daka"Tunda Zahra tafara daka cikinta ke juyawa amma besa tabar dakan ba.

"Idan yamatsa mata da juyi tsayawa takeyi har yafada snn taci gaba.

"Tana gamawa ta diba ta kaiwa mm tagani ko yayi" mm na daki kwance Zahra ta kai mata ta gani, Tace yayi saura wankewa amma kada ta tabi ruwan randa sbd shikadae ne yarage nasha kuma sauran randunar gidan babu ruwa.

"Zahra tace mm shikadaene kawai randan da akwai ruwa" mm tace eh ina sane bokiti zaki dauka kije rafi koda kai dayane kidibo sae a samu a wanke geron.

"To kawai Zahra tace tana fita daga dakin mm gefe tatsaya tana tunani xuwa rafin.

"Jin motsin fitowar mm ne yasata daukar bokiti da sauri hade da hijab tafita "tafi fita garzali ya hangota da sauri ya mike yana binta abaya batare da tasani ba.

"Tana tafe cikinta na ciwo" sae da takai bayan gari snn garzali yakira sunata hade da yimata dariya.

"Gabi haka yaasa tafara sauri hade da gudu" Shima garzali binta yakeyi gudu Zahra tasa garin gudun ne tafadi akan wani dutse taje da ciki.

"Gani garzali yayo kanta nan tabar bokitin tamike. aguje tana tafe tana tallafe da maranta sbd ji takeyi kamar xaifashe.

"Hakan yasa tasake fadi"tana fadi jini ya banle, ihu Zahra keyi hade da kiran xanmutu.

"Garzali yana xuwa duk da jini daya gani beda mesaba hannu yasa ya dauki Zahra hade da dariya
[7/17, 10:43] Washa: πŸ’ŽπŸ’¦πŸ’Ž
πŸ’



GARKUWATA
(RELIANCE)



FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.πŸ’



πŸ’ŽMMN USWANπŸ’Ž


DIDECATED TO SWEET SIS MARDIYA KA'OJE



18



"Garzali yana daukar Zahra can cikin daji ya kaita inda ba lailane wani yasan da mutum a gun ba.


"Shima kanshi sanadiyar yasan gun sbd anan ne suke zuwa shaye shayen su.

"Suna isa ya sauke Zahra ya'ije ta a kasa" Itako Zahra in ba ihu da kiran cikinta ba babu abinda takeyi.


"Garzali yana ijeta gu yasamu ya zauna kusa da'ita yana mata dariya" ihu Zahra keyi hade da cewa garzali ka taimakeni mutuwa zanyi.


"Dariya Garzali yai hade da cewa wlh Zahra inda mutuwa kikayi yafimu da ace kina raye na ganki da wani katon banxa.

"Wlh daga yau anace yabar sake ganiki kinriga kin masa nisa.


"Zahra najin haka wani sabon kuka tasake fashewa dashi hade da kokarin yunkurawa amma ina takasa"Sakamakon juyin da cikin yake mata.


"Hakalin Zahra ba karamin tashi yayi ba sbd gani jini dake xuwa daga jikinta ita kuma batasan dalili ba"Ga azabar ciwon cikin da takeji.

"Shiko garzali ko a jikinsa"Duk uban kukan da takeyi hade da juyi amma besa yaji imanita ba.

"Mmki ya kama mm gani yadda Zahra ta dade daga dibo ruwa kawai rafin da ba nisane dashi ba" A zuciyarta tana fadi kodae gidan su maryama tabiya shiyasa ta dade haka?.

"Kuma tasan Zahra bazata daga aike bazata biya ko'ina ba"Batare da iziniba.

"Kodae tabi bayan tane taduba ko lpy?"Tunda gashi har anfara kiraye kirayen sallah kuma gashi maigidanta ya kusan dawowa.

"Shiru tai tana tunani kala kala takeyi sbd jikinta yafara sanyi da al'amarin.

"Mikewa tai ta dauki buto taje tashiga bayi tsarki"Tana fitowa tai alwala taje sallah.

"Mm bata idar da sallah ba Haidayr yai gani babu kowa ya tsakar gida yasashi shigewa daki" Yanasa kafa a daki yaji gabansa yai mummunar fadi, karisawa ciki bekawo komai a zuciyarsa ba.

"Rataya yakarsa yai a kusar dake bango snn ya zauna a bakin katifa ya dauki kofin dake gefen katifa yasha"Dama dabi'ar Zahra ne tunda tasan yanada bukatar ruwa a kowani lokacin ko cikin dare ne sae ya tashi yasha.

"Shiyasa ta cire daya daga cikin kofunanta ta wanke tas snn ta'ije a gefen katifar ta kowani lokaci baya rabuwa da ruwa aciki.

"Uncle Haidayr yana sha medawa yai ya rufe shiru shiru bega Zahra ta shigoba hakan yasa yafara kwada mata kira.

"Yayi kira yakai sau uku amma beji an ansanshi ba"mikewa yai yafita zuwa dakin mm, yana shiga mm na sallame sallah.

"Betsaya ya saurari abinda mm zatace ba yace mm ita Zahra?" Nadawo nashiga daki naga bata kuma ba takalminta a bakin kofa.

"Sae da mm ta nisa snn tace wlh Aley yau nai maka laifi nine na aiketa rafi dibo ruwa...

"Karam haidar yace ruwa kuma mm?.

"Mm tace eh sae dae tuntunine bansan abinda yahanata dawowa ba"dama so nake idan na idar da sallah nabi bayanta naga ko lpy...

"Be tsaya ta karisa ba juyawa yai yafita yakami hanyar rafin.

"Haidayr yana tafene yana zancen zuci hade da tunani kala kala har yakai rafi" Ga mutani burjik amma babu Zahra a cikinsu kansa yasake daurewa, ya kuma rasa yadda zai tambayesu sbd matan aure ne.

"Har ya juya zai tafi, Sae dae yace bari ya gwada tambayar yagani komawa yai yai masu sallama" wasu daga cikinsu suka amsa snn yace dan Allah tambaya nakeyi.

"Matan da son jin kar duk suka saki wankin da sukeyi suna sauraron suji abinda zaice.

"Hardar yace dan Allah mai dakina nake tambaya ance nan taxo diba ruwa?" Kusan hada baki sukayi hade da cewa mudae bamu ganta ba kuma tun safe muke nan muna wanki inda taxo zamu damu ganta.

"Shiru Haidayr yai snn yace to nagode" har ya juya zai tafi wani yar matashinyar budurwa tace gadae wani botiki da muka gani a hanya lokacin muna zuwa.

"Banxa da'ita haidayr yai sbd ba mgnr bokitine a gabansa ba.

"Juyawar da zaiyi karab idonsa ya fada kan botikin sune da sauri ya karisa gun yace dan Allah aina kikaga wanga bokitin?.

"Yarinyar tace acan hanya nagani lokacin zanxo rafi gefensa kuma duk jini ne kamar anyanka rago.

"Cikin dimauta Haidayr yace dan Allah ta'ine gun?" Yarinyar ta kwatanta masa gun.


"Daukar bokitin yai yafara sauri hade da gudu" Yana isa gun yaga jini da yarinyar take fadi gaskiya ne.

"Babu wanda haidayr ya kawo zai iya masa haka sae garzali a guje ya nufi fadar maigari bbn garzali.

"Yana isa tsalla yai ya shako maigari hade da cewa ina d'an ka ya kaimin matata?" Cikin dimauta da mmki maigari yace wace matarka kuma?.

"Haidayr betsaya bawa maigari amsa ba ya kaimasa nushi" fadawan take zaune a fadan suma suka hau haidayr da duka.

"Suna dukansa shikuma yana dukan maigari" nan da nan gari ya dauka da cewa anan ana dukan maigari.

"Duk irin wuyar da haidayr keji besa ya dae na dukan maigari ba.

"Gani barnan zaiyi yawane yasa maigari cewa fadawarsa sudae na dukan Haidayr" sauran sun dae na amma banda daya daga cikinsu.

"Dauko icce yai zai rutsawa Haidayr" Da Haidayr ya lura da haka kukan kura yai ya fisge icce ya kwadawa mutumin daya dauko icce" daga nan yakoma kan me uwa da wabi.

"A take duk mutani dake fadar suka watsa harda maigari yarage samarin gari.

"Suna kallon duk abinda ake ciki amma basuyi kokarin taya maigari ba sbd suma ba barinsu yai ba sae ma dadi da sukaji.

"Gani Haidayr yana kokarin binsu matasan dake kallon suka rikeshi" kwance kanta yai zaibishi gani hakan yasa sukai taron dangi suka danne Haidayr.

"Gani sunci karfinsa ihu Haidayr yasa hade da fashewa da kuka jikinsa kuma har rawa yakeyi" Suna cikin haka sae ga mmn Haidayr taxo gani abinda yakeyi tace susakeshi, suna sakeshi mikewa yai zai bisu da sauri mm ta rike mata hannu.

"Da karfi ya fisge hannunsa yasake sa gudu" suma matasan suna gani haka aguje sukaje suka sha gabansa.

"Mm na xuwa gun wanka masa mari tai lafiyayyu guda uku snn Haidayr yadawo haiyacinsa kama masa hannu tai xuwa gida.

"Suna tafe mm ta masa fada da harshe fillanci" shidae Haidayr binta kawai yakeyi har suka isa gida"suna isa bakin kofar dakinsa ta xauna dashi nan ma taci gaba da yimasa fada.

"Haidayr be tanka taba sae tsareta d yai da ido" kallonta yakeyi bayako kubtawa ga kayan jikinsa duk su yage.

"Gani haka yasa mm dibo ruwa a randa taxo ta kwara masa a jiki" wani irin ajiyar zuciya yai snn yakoma kallon kayan jikinsa gani duk sun yage mikewa yai ya cire kayan yatage dagashi sae gajeran wando.

"Snn ya shiga daki" dauko wasu kayan yai yasa yasake fitowa zai fita, da sauri mm tasha gabansa tana tambayar ina xaka?"

"Shiru Haidayr yai be tanka ba" kamo masa hannu tai suka koma ciki kan kujera ta xaunar dashi itama ta xauna suna fuskantar juna snn mm tace Aliyu.

"Haidayr yace na'am mm.

"mm tace ina xaka?

"Haidayr yace komawa gun sa xanyi saeya fitomin da matata.

"Idan ba ubansa naciba ba zaiceea d'an sa ya fitomin da matata ba...

"Haidayr ya karisa mgnr ne hade da yunkurawa xai mike" da sauri mm ta dannosa yakoma ya zauna cikin lailashi take tambayarsa abinda ya faru.


"Nan Haidayr ya kwashe komai ya fadi mata.

"Salati mm tai ta sanarwa ubangiji"Snn tace kai waye ya fadi maka shine ya dauki Zahra?.

"Haidayr yace sbd in ba shiba bani da wani wanda xaimin haka" shidinema mm.

"Mm tace to shikenan tashi muje gun nagani da kai na.

"Mikewa yai da ita suka jawo kofofin dakunan suka fita.

"Hanyar rafin suka kama kai tsaye.

"Shima maigari tuni ya baza fadawarsa duk inda garzali yake su nimosa"sbd yasan in har Haidayr bega matarsa ba yasan fada be kare ba.

"Suna isa Haidayr ya nunawa mm gun da yaga jini" mm tace to abinda zamuyi shine bin hanyar da mukaga digon jini zamuyi da alama tanan yabi da'ita.

"Haidayr yace to haka suka kama tafiya Haidayr na gaba mm na baya suna bin duk inda sukaga digon jini.

"Suna cikin tafiya suka hadu da mutani da maigari ya tura su nimo masa garzali" babu wanda ya tanka wa d'an uwasan haka suka wuce juna.

Har sunyi nisa sae daya daga cikin dogaran yace sukoma su bisu" daya daga cikinsu yace yace meyasa?.

"Sae yace tunda har kunga sukami hanyar dani duk yadda akai akwai labarin da suka samune" dan Allah mubisu muga abinda zasuyi amma kada wanda yai masu mgn.

"Sukace to sbd shine shugaba a cikinsu shiyasa duk abinda yace basu musu.

"Abinka da kauye gari duk ya dauka da d'an megari yasaci sirikan talatu matan anace" masu Allah ya kyauta suna cewa masu fadin yadibowa kansa masifa suma duk suna fadi.

"Mutani suna fadin hakan ne sbd babu wanda besan mm wajan fada ba"hakan ma yasa ko makwabtanta basu shige mata.

"Mm sunyi tafiya har sun gaji ita kanta mm tafara kokwanton kodae basu garzali ne aka gani ba" shima Haidayr da yaga tafiya taki karewa kuma gashi digon jini da sukebi sun daena gani.

"Yasa jikinsa sanyi amma kuma ajikinsa yanajin akwai Zahra a gun.

"Mm tace Aley kodae xamu koma gida ne?" Haidayr yace babu inda zani banga Zahra ba, kafana kafar ta...

'"Be karisa mgnr abu ya hango acan nisa kamar zani Zahra" A guje ya karisa gun.

"Yasa isa gun ita din yagani kwance cikin jini tana faman juyi" da sauri ya karisa kanta ya dagota hade da kiran sunanta.

"Shiru Zahra tai babu mgn sae idanu kawai" Da sauri mm da yaran megari sukayo kansu.

"Mm na gani Zahra cikin jini tasa salati"Haidayr bebi ta kansu ba daukar matansa yai a guje sukabar gun.

"Ko kafin su iso cikin gari asibiti sun gari sun tashi" mm tace suwuce da'ita gida kawai.

"Haidayr yace aa mm.

"Mm tace idan baka kaita gida ba kanada yadda xakai da'ita ne?.

"Haidayr yai shiru.

"Sae mm tace to mutafi gida.

"Be tanka ba hanyar gida kawai suka nufa" suna isa mm tace yakai ta dakinta.

"Mm shinfida tabarma tai Haidayr ya shinfida ta daga rigarta mm tai ta matsa marinta taji cikin ne ya lailace amma kuma har yanxu gudan cikin yana nan.

"Haidayr yace mm ya dae?.

"Mm tace cikin da yake jikinta ya lailace..

"Rum tsa ido Haidayr yayi.

"Mikewa mm tai ta dauko wata jakar da take ije magugunarta wani bantalen icce ta dauko dade da dauko ludayin duma snn ta dibi ruwa kadan a ciki jefa icce tai acikin ludayin, be wuce minti biyur ba tacire snn tace Haidayr ya dago kanta yana dagawa mm ta juye mata magani a baki.

"Suna xuba mata ta share ko minti goma batayi da shaba wani sabon ciwon cikin yataso mata" kankanme Haidayr tai da karfi shiko Haidayr sae faman cemata yake sorry yakeyi.

"Da haka har dare yayi cikin be dae nawa Zahra ciki ba.

"Gani haka yasa Haidayr ya tsinkewa al'amarin.

"Da haka har 2AM yai da mm taga haka tacewa Haidayr ya dago mata Zahra" Haidayr yana dagota hannu mm tasa daedae maran Zahra da karfi mm ta dan na maran sae ga gudan jini yafito da karfi.

"Mm tace alhamdllh.

"Dama tanada kaya ajikinta dauko wani zani mm tai saeda ta rufe mata al'auranta snn suka cire mata wanda yakeda jini ta fitar dashi waje.
[7/17, 10:43] Washa: πŸ’ŽπŸ’¦πŸ’Ž
πŸ’



GARKUWATA
(RELIANCE)



FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.πŸ’


πŸ’ŽMMN USWANπŸ’Ž



DIDECATED TO SIS MARDIYA KA'OJE.



19



"Ashe tun daga nisa garzali ya hango su uncle Haidayr hakan yasa shi guduwa ya boye jikin wata itaciya.

"Har uncle Haidayr ya dauki matarsa suka tafi be fitoba amma yana kallansu.


"Suma dogarai suna komawa fada suka kwashi duk yadda aikai suka fadiwa maigari" mmki hade da tsoron abinda zai biyo baya sbd a tunanin dogarai fyadene garzali yaiwa Zahra.

"Shiyasa cikin dare da garzali ya dawowa gida kwanciya megari yabawa garzali kudin mota cikin dare yacewa garzali yabar gari yatafi birni idan komai ya lafa sae yadawo.

"Shima da yake a tsorace yake betsaya musuba amsar kudin kawai ya bar garin.

"Da safe megari ya tara yaran fadarsa yace koda dawasane kada yaji labarin ya yadu a wanga kauyen" idan kuma yaji to abin aikin wanda ya fadi kuma sae yabar masa garin.

"Duk sukace babu wanda zaiji xancen.

"Haule mmn garzali har gida taje ta samu kawarta Hajjo ta zaiyana mata abinda yafaru.

"Cikin isa da shewa Hajjo tace wlh kunga damata idan nine babu inda xan tura dana sbd yai ma wata banxa fyade idan banda abinku me suke dashi?" Yau koda kotu kukaje basuda kudin da zasu ja daku.

"Haule tace to Hajjo kinfi kowa sani hali kauyenga idan har nace ya zauna ko kibce da yarface ya'isheni na kasa shiga jama'a amma kinga da yabar garin idan komai ya lafa saeya dawo.

"Kuma bama haka ba kinfi kowa sani halin anace da uwarsa nacin fadane dasu tsorona dayane kada anace yaxo ya kasaramin garzali d'an guda dayan da nake gani.

"Shuewa Hajjo tace d'an shegiya ba.

"Nai dae suka ta hiransu har lokacin tafiyarta gida yai snn sukai sallama.

"Bayan tafiyar Haule ko minti goma batayi ba saega megari yashigo gun farkansa Hajjo.

"Dama tun bayan rasuwar malam Haruna ko takaba bata karewa basu holewarsu ko mata da miji sae haka.

"Dama lokacin Zahra na gida batai aureba ita ke takura masu sae kuma malam Habu amma yanxu da kowa ya kami kansa ba karami holewa sukeyi ba.


"Mm na kare wa taje ta hura wuta tasa ruwan xafi, Yanayin xafi juyewa tai ta kawo daki tsmma ta samu idan tasa a ruwan sae ta matse tana ringa goge mata jiki dashi.

"Da haka har ta kare" Bayan ta karene tace Haidayr ya dauko wasu kayan a canxa mata.

"Mikewa yai ya koma dakinsu ya dauko snn ya dawo Haidayr da kansa ya canxa mata kayan sae mm tace ta kwanta a dakinta ta huta.

"Uncle Haidayr yace aa tabari su tafi dakinsu kawai.

"Kamata yai suka koma daki" Suna shiga ta kwanta shima kwanciya yai kusa da'ita minti da minti sae yace sannu Zahra.

"Da haka har asuba yai"mikewa yai yaje yai alwala snn ya dawo daki yai sallah, Bayan ya idar ne ya hau kan katifar hade da kara bakinsa a kunninta yana kiran sunanta.

"Lokacin idonta biyu" Haidayr yana cewa Zahra.

"Tace na'am.

"Yace ya jiki?

"Tace da sauki.

"Yunkurawa tai xata tashi"Da sauri uncle Haidayr ya taimaka mata ta mike hade da jinginata a bango.

"Shima zama yai suna fuskantar juna" Kare mata kallo yai yaga tasamu sauki sosae snn yace yanxu ina yake maki ciwo?.

"Tace babu ko'ina.

"Yace da gaske?.

"Tace eh.

"Gani yadda take mgnr da alamu sauki yace uncle Haidayr yace Zahra garin yaya hakan yafaru?.

"A lokacin ne Zahra ta fashe da kuka.

"Da sauri uncle Haidayr ya jawota jikinsa hade da cewa daga tambaya Zahra.

"Fisge jikinta tai daga nasa.

"Mmki ya kama Haidayr sbd tunda yake da Zahra betaba riketa ta kwace jikinta daga nasa ba.

"Haka ya sake gwada riketa"itama tasake fisge wa, tun daga lokacin kyaleta yai yai besake rikewa taba.

"Itama da taga zai matsa mata komawa tai ta kwanta hade da jawo zani ta rufe fuskanta.

"Shiru Haidayr yai yana munanin abinda yasa Zahra take masa haka.

""Kamar daga sama ya jiyo maryan Mm tana sallama" Da sauri ya sauka daga kan katifan taje ya amsa hade da yi mata iso xuwa ciki.

"Tana shiga gefe ta samu ta tsaya gani haka uncle Haidayr yace mm ga katifa ki zauna mana.

"Banxa dashi tai hankalin ta nakan innawuro tace ya jiki.

"Banxa da'ita Zahra tai kamar bataji ba.

"Koda mm tasake mgn Zahra bata tanka ba" sae da uncle yace Zahra mm cefa ke gaida ki.

"Snn Zahra tace da sauki"Amsawar ma ba lailane kaji abinda take fadi ba.

"Gani haka yasa mm tace kyaleta Aley kilan har yanxu jikine.

"Fita tai ta barmasu dakin". Tana fita uncle Haidayr ya hau katifar hade da kiran sunata da sauri Zahra ta juya masa baya.

"Duk mgnr da uncle Haidayr yai banxa dashi tai bata tanka ba.

"Shima da yaga hakan besake tanka mata ba"Gefe ya koma ya xauna yaci gaba da lazumin sa, sallamar mm ne ta katseshi ya amsa da na'am.

"Batare da ta shigowa ba tace ga ruwan yai xafi idan xatai wanka.

"Uncle Haidayr yace to mm.

"Yana shafa addu'ar ya mike yaje ya dibi ruwan ya sirka snn ya kaimata bayi" yana ijewa komawa yai daki ya sanar da'ita.

"Haidayr yai mgn yakai baki uku snn Zahra ta mike soso kawai ta dauka snn ta fita ko kallo inda yake batayi ba.

"Tana fitane Haidayr ya kankade gado ta sake shinfida wani zani gado snn ya share daki kafin tafito daga wanka yana gamawa yafita yaje siyo kayan tea"Tana fitowa daki takoma ta samu bakin katifa ta zauna batare da tasa komai ba tagumi ta zabga tai shiru.

"Haidayr yai sallama yakai baki uku amma baji shiru"hakan yasa yasa kai yashiga yana shiga ganinta yai xauna ta xabga uban tagumi.

"Da sauri yaxo kusa da'ita ya xauna hade da dafa bayanta yana cewa lpy Zahra kodae jikin ne?.

"Ture masa hannu tai tamike" Tana mikewa jini yagani duk ya bata katifa da sauri ya dauko tsunma hade da ruwa sae da ya yayyafa ruwan agun snn yasa tsunman ya goge gun tas.

"Yana gamawa bude akwati yai ya dauko mata pan da wasu kayan hadewa yai da mai ya'ije mata a gefe sbd yasan koda mgn yai mata ba lailane ta amsashi ba.

"Yata yai yaje ya dibo ruwan xafi ya hada tea ije mata nata yai snn ya dauki nashi dana mm yanufi dakin mmnsa, a nan ya karya ita ko Zahra tana gama sa kayan ta koma ta kwanta.

"Koda Haidayr ya dawo dakin inda ya ije mata tea din haka yaxo yagani"a lokacin ne raisa ya baci anan ya hauta da fadi inda yake shiga banan yake fita ba.

"Jin fadar da yakeyi ne yasa mm xuwa hade da tambayar lpy?" Haidayr be saurari mm ba yaci gaba da fadarsa, ita ko Zahra babu abinda takeyi sae kuka gani hakane yasa mm ta kamo masa hannu yafita daga dakin.

"Mm na tambayar meyafaru Haidayr yace babu komai"Yunkurawa yai xaikoma dakin da sauri mm ta tare shi hade da cewa ina xaka kuma?" Uncle Haidayr yace mgn xanmata ta shirya mutafi asibiti.

"Sae mm tace to bari ni nafadi mata lekawa mm tai dakin tace innawuro mijinki yace kishirya kutafi asibiti.

"To kawai tace.

"Shima Haidayr din fita yai yaje gun abokinsa aro mashin kafin yadawo tashirya yana dawowa lekawa yai dakin yace da'ita kifito mutafi.

"Hijab kawai ta dauka tafito shima lekawa yai ya sallami mm snn suka fita" yana tada mashin ta hau suka tafi, koda suke tafiya babu wanda yakewa d'uwansa mgn har suka kai sae idan yashiga gargada taji xata fadi shine take rike masa riga ta baya.

"Suna isa sukai sa'a babu mutani dayawa agun haka yasa suka samu shiga gani likita" sae da uncle Haidayr yafara bayani snn likita ya tambayi Zahra itama takara masa bayani.

"Bayan likita yakari dube-duben sa snn ya rubuta masu magani sukai sallama Haidayr ya dauki matarsa suka koma gida.

"Suna isa sukai karo da maryama da fara'arta ta taresu da snn da dawowa Zahra na sauka ta

Please Login or Register in order to submit comment