Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yake.


Nafeesa ta........


Urs Xayyeesherth
[3/16, 2:24 PM] Xayyeesherthul-humaerth: https://chat.whatsapp.com/GeuRcMbmDGuHPBZu4928K8

_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_



*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH


https://www.facebook.com/106494781436168/

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_

PAGE-23

_*JASMINE,RANO ON TOP,MAMAN SHUKRA,MR MUBARAK,AISHATUL-HUMAERAH,MAMAN KHRT,MAMAN IHSAN,NAFEESAT,DAMA SAURAN DANA MANTA🚶‍♀️🤸‍♂️DUK KAN KU YAYA JAMILU (NAFSEEN NA GAIDAKU KYAUTA😂AMMAN FA YACE BAN DA NAFEESA😓ABUN TAUSAYI*_


BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM




Tsorata, abun ya bata mamaki kawai jikintane yafara rawa, Maryam ido ya yi zuru-zuru ga dalibai an fito kowa idonshi Kansu.


Wata irin kara Nafeesa tai nan take aka ajiye Mutansir gefe, tausayinsane ya kamata nan take,ta karasa gareshi duk jikinsa ya kurkuje.


Ganin Nafeesa gabansa maimakon yaji tsoro ko yaji da radadin jikinsa,murmushi ya fara sakewa yana kallonta.

Ita kuwa cikin dimuwa take fsdin, "Sannu kaji, nikam dai ban ma komai ba,ka gani ko? Sannu ban San waya Tabaka ba."


Kasa magana yayi ban da murmushi ba abun da yake saki.


Maryam ce ta karaso tare da rikye hannun Nafeesa tana, "Habibbty mu tafi kinji."


Nafeesa ta fara kuka, "Habibbty kin gani fa,ina ni ban masa komai ba."


Maryam ta ce , "Eh tashi muje."

Dakyar Maryam ta janye Nafeesa daga gun Mutansir ba su ma tsaya lectures din Yamman ba,Maryam ta lura da yanayin Nafeesa hakan yasa kawai suka nufi gida.



Mutansir kuwa sai da aka kai shi asibiti.



Fatima takaici kamar tayi yaya, kara duban kanta tai,shin wai da me figiggiyar yarnan tafita ne, da har mutansir zaiki ta,tsaki taja azuciyarta tana , "Sai shegen karyar iskanci ga dukkan alamu yarinyarnan matsafiyace, Dan haka nima yanzu aka fara daga ita har Mutansir din sai na basu mamaki wallahi."

****Suna fara tafiya Nafeesa ta mance da abun da ma ya faru gabadaya ta dawo hayyacinta tamkar ba ita ba, dukkansu sunyi shiru sai kallon hanya suke kawai,tsayuwar da mai nafensu yayi ne ya ankarar da su.

Kabeer ne ya tsayar da mai nafe din.

Maryam na ganinsa taji wani Abu ya tokareta akirji tsaki tayi azahiri sannan ta kawar da kai.



Nafeesa ta kalle shi cike da fara'ah , "Ah Yah Kabeer kai ne?"

"Eh Wallahi Nafeesa na ga yau kun kammala da wuri gashi nima gida zani mai zai hana in rage maku hanya?" Cewar Kabeer

Nafeesa ta ce, "Ayyah Yah Kabeer Karka damu wallahi ai mun kusa gidanma."

Kabeer yace, "Eh ai ba Matsala ko Mallam? Nawane kudin in ba da?"


Mai nafe yaga alamun za Adan samu cikin Sauri ya ba da amsa, "Eh yallabai."


Cikin Fada Maryam ke magana,"kinga Habibbty nifa bazan Iya ba,kai me nafe in zaka kai mu ka kai mu haba, wannan ai wulakancine in baxaka ba mu sauka ai ga wasu nan ma hau.".

Maganar take tana kokarin fita a nafen.


Nafeesa ta rikota, "Miye haka Habibbty? Ni dai ban sanki da irin wannan halinba,kuma sai mun hau motar Kabeer ko kinki ko kinso in kuma ba za ki hau ba ki ta tafi ni ya kai ni."



Ko da wasa Maryam bazata Iya barin ta ba domin tana gudun bacin ran Nafeesa fiye Da nata.

Ba yadda ta Iya haka ta shiga,da zata shiga baya Nafeesa ta ce aa, bata da zabi da yafi na Nafeesa hakan yasata shiga Amman fuskarnan amurtuke.



Kabeer ya ba mai nafe dubu daya kan ya dawo suka fara tafiya, murmushi ya yi yana kallon Maryam ya ce , "Niko Nafeesa kun San cewa in kuka bata rai ba karamin kyau kuke karawa bane?"



Dariya Nafeesa tai, "Lallai Yah Kabeer,yo kaga mukai kyau ma in mun bata ran bare mun sakesa, ina tabbatar maka cewa Habibbtyna ta mussamance, yanzu ma da zatayi murmushi sai ka kusan suma."


Saura kiris Dariya ta subucema Maryam Amman ta basar domin ban da kara jin tssnar Kabeer ba abun da take.




********Nafseen ne yafito daga cikin daki cike Da murmushi afuskarsa, wata yar matashiyar Mata ta biyo bayansa tana, "Umm Husband ban fesama turaren ba fa."



Kwaikwayon yadda ta shagwabe yayi shima, "Umm Wife kina gani lokaci na kuremun kuma inna biye ki wallahi sai in makara yau fa zamu fara daukan sabon film dinnan So akwai bukatar na isa Kano kan lokaci, kuma na fesa turaren nan fa wai bai isa bane nikam."



Murguda masa baki tayi, "ni dai ka daina kwaikwayona,kuma ai naka ka fesa ni baka fesa nawa ba,Allah ba zan Yarda ba." Ta karasa maganar cikin sigar shagwaba.

Dawowa yayi kusa da ita, yana magana ahankali, "Fesamun Amman indai yayi yawa kika janyo yau na miki kanwa shikenan ba ruwana."



Dariya tayi kan ta ce , "Kanwa! Allah kawota ai a kujera zata zauna ba kaina ba,kowa ya Iya allonsa ya wanke,in yasoma ya sha ruwan."



Hade rai yayi, "Wato ma ko irin kishinnan nawa bakya yi ko?"


Fara fesa masa turaren tayi tana sakin murmushi, "Ina kishin Mijina fiye da kowa, kishi Mara misaltuwa Amman ban isa in sauya kaddarata ko ince zan musa ikon Allah ba,Ina Sonka Mijina,fiye da numfashina, fatan nasara,Allah Sa afita asa'a adawo lafiya, Zan yi kewarka."


Hannunta ya riko suka fito tare, ji yake tamkar kada ya barta domin kuwa yafi kowa Sanin cewa yayi dace da mace ta gari, mai hakuri,hankali da tunani.


Kallonta yayi,yana, "Maddala da matar kirki,Amin Amin Na gode, Allah ya miki albarka,byrrbyee."



Kamar za ta yi kuka ta ce, "baka fadamun ba."


Cikin tsokana ya ce, "Me zan Fada?"


Hawayene ke kokarin fito mata, da sauri yadawo tare da rada mata wata magana akunne,murmushi tayi kawai.

Ya kara da, "I Love You Wify."


"Love you more husband,byeebyee."



Hanyar kano suka kama,da yake tafiyar ranane har dare basu isa ba.

Kwatsam wata babbar mota tayo kansu,ba damar kaucewa haka ta danne motarsu

Innallillahi-wa'inna-ilaihir-raji'un



🤭🤭KUNA SO NAFSEEN YA MUTU???🤸‍♂️🤸‍♂️A TSARE KOMAI YAKE AMMAN YAU ZAN GA MASOYAN YAYANA.



Urs Xayyeesherth_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_



*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/106494781436168/

NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH



✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_

PAGE-24

_*SADAUKARWA GA SAI NA AURI MARUBUCIYA FANS GRP😘ARADU SAI NA AURI MARUBUCI FANS GRP2 ZAN YI SHARA🥺KAF XAN CIREKU TUNDA BA SHARHI*_


Banda salati ba abin da ke tashi a motarsu Nafseen duk wani Wanda ke wannan wajen saida hankalinsa ya tashi domin duk Wanda yake cikin motan ba Wanda ake sa rai da zai Rayu.



wanine akasamu yayi hankalin kiran yan road safety suka zo da gaggwa aka fara kokarin daga motan da kyar aka samu aka daga motan aka fara fitowa dasu Amma duk basa hankalinsu sannan kuma driver din baya da rai.
cikin gaggawa aka wuce dasu asibiti domin ceto rayuwarsu.





Muta sir kuwa tunda ya koma gida wani irin ciwon kai da zazzabi ya rufe shi sosai son Nafesa na Neman halaka shi, zuciyar shi tana mashi zafi sosai ko ruwa ya kasa sha bare abinci duk jikin sa rawa yake, ko ido ya rufe ita kadai yake hange, yanzu kuma kaman ita yake kallo tana masa murmushi shima murmushi ya fara hadda kokarin fita a blanket dinsa ya nufi wajenta yana zuwa ya durkusa a gaban ta "Nafesa kema kin fahimci Irin son da nake miki ko? na san za kiji tausayi na dama, plz give me a chance ."


Momy ce ta ce, "waye ita?"

saiko mutansir ya dago "Momy dama ba Nafesa bane momy plz ki tausaya min zan mutu idan ban same ta ba, wallahi ina sonta." Ya karasa maganar jikin kuka.


yau ce rana ta farko da Momy taga mutansir yana kuka da girman sa dago shi tayi taji duk jikinsa ya dauki zafi sosai.

ta ce, " son yanzu akan mace Kake wannan abin? Daman na San za arina ai,akwa ranar kin dillanci."


"Momy nidai Dan Allah ki taimaka min bakiji yadda xuciyata ke min ba Momy, ji nake tamkar zan Iya rasa raina."


Momy ma duk jikin ta ya mutu ban da hawaye ba abin da take, domin ban da dai fita ta Mutansir da ke Sa basa shiri amman tana matukar son 'dannata.


Kallonsa tai cikeda tausayi ta ce, " Idan Dady yadawo zamuyi magana,kar ka damu kaji, ka san Dadynka zai iyama abun da yafi wannan ma,bare wannan da nake Sa ran shi zai kara shiryaka."



Mutansir ya ce, " Momy plzz kice dady yazo yanzu Dan Allah momy, ni ko yanzu ma a auramun Nafeesa Dan Allah. "



Shafa kansa tayi kan ta ce, "yanzu dai kayi wanka kasha magani kayi sallah kaga sakka kara yin addua ko ? Kan Dady ya dawo ai yama kusa."


da to ya amsa,sanan ya nufi bangarensa, Momy da kanta ta hada masa ruwa sai da ta tabbata yayi wanka yayi sallah sannan ta bashi abinci duk da ya kasa ci Amma yadanci magani ta bashi tace ya kwanta kafin Daddy ya dawo ba musu ya kwanta shi kadai yasan me yake ji rupe ido yayi Kawai ba Dan yanajin bacci ba Momy data ga ya rufe itama ta fito tana mai jin tausayin Dan nata sosai,tabbas So ba karamun Abu bane kuma zai Iya yin illa ga zuciyar kowa..


****
Sai Dare Nafeesa ta bar gidansu Maryam tunda kabeer ya saukesu tare.

Karfi tara bayan tayi karatunta na QUR'ANI ta zauna tare da nufin zata bude data take ko zataga Uncle ya Mata magana.

Messegese nata shigowa Amma na shi shiru duk jikinta yayi sanyi ko lafiya kuwa uncle baya online ko dai zan tambaya a group ne can kuma tace hmmm danke kadai ne me baki ko ? to ko na kira shine?

Ta ba kanta amsa ehh Bari na kira number dinsa ta duba harzata danna call sai ta ji duk jikin ta na rawa Gaban ta na faduwa numfashinta na fita da karfi wayan ta jeda kan gado itama ta kwanta tafi mintuna ashirin a haka nan da nan ta fara kuka tana cewa "uncle meya sameka kasan inason ka Dan Allah karka min nisa jikina yabani wani Abu ya sameka,Kayi hakuri please." kukanta ne yayi yawa sai da Mamma ta shigo dakin cikin,hanzari ta ce, "meke faruwa ne? Nafeesa kina lafiya kuwa?"



Cikin shidewa take fadin "Mamma wani Abu ya same shi wallahi, ba zan Iya....... Kawai sai ta jita shiru ,ta leka ko harta tafi baccin data saba addu a ta mata ta fito, tana gaskiya lamarin Nafeesa ya fara yawa da bukatar fadada Neman magani...




A bangaren Nafseen kuwa asibiti aka wuce dasu cikin ikon Allah duk sun dawo hankalinsu sai dai sunji ciwo sosai.

doctor ne yazo yana dubasu ana tambayan su daga inda suke sai lokacin ya tunada wayarsa da bai san ina zai ganta ba.

tambaya yayi sukace su dae basu samu waya a motan ba. rike Kansa yayi" ohhhh my God." kadda8 ace masa wayan shi ya bata kuma sai wata zuciyar tace masa ka gode ma Allah da abin ya tsaya akan waya azahiri ya ce, "Alhamdu Lillah Allah nagode maka."

baa dauki lokaci ba yace a bashi Aron waya Dr din ya bashi ,
****

Rukayya na zaune ita kadai ban da kuka ba abun da take Kanta har ya fara ciwo ta rasa meke faruwa tunda ya tafi bai kirata ba kuma ita ta Kira shi Amma bata samunsa switch of.


wayanta taji ya fara kara da gudu tayi daki a tunanin ta zataga sunan sa Amma sai ta ga number wani haushi ne yakamata har kiran ya katsewani ya kuma shigowa sai da yakusa katsewa ta daga muryansa daya daki kunnenta ne yasata Kara sa wani kuka .


yace" haba my rukky meye na kukan kidaina plzz ."


Ajiyar zuciyata tana ,"ina kashiga meya faru da kai ka fada min plzz."

Murmushi ne ya bayyana afuskarsa kan yace, " ki yi shiru zan dawo gida ina lafiya banson kukanki kema kin sani ko?"


tace, " har yanzu hankalina be kwanta ba,ni wallahi."

da kyar yasa ta hakura akan zai dawo ta ganshi .

" to e
Ina wayanka ?" Cewar Rukayya .

Nafseen ya ce, " ba caji ne shiyasa na karbo na abokina Dan hankalinki ya kwanta to yi murmushi mana babyna."


murmushin tayi tareda Masa sallaama akan yana hanya.








Maryam ce zaune itada Ummi suna cin abinci wayan ta ya fara kara number din Kabir ne danta gane number din nan da nan yanayinta ya sanja tayi rejecting kiran Ummi ta ce , "waye yake kira?"


" hmm ummi wata course mate dinane kuma shirme zata min shiyasa bazan amsa ba."



Ummi murmushi Kawai tayi Wai Maryam ni zata nuna ma wayo kaman banina haifeta ba Allah dai ya shirya min ke Maryam.



kiranne ya kuma shigowa take ta kara rejecting wayan tana ta fishi karshe ma abincin dabata Ciba kenan tace bacci take ji dakinta wuce, tana shiga kuwa kiranne ya kara shigowa, cikin fushi ta amsa tare da karawa akunnenta.......


Urs Xayyeesherth
https://chat.whatsapp.com/GeuRcMbmDGuHPBZu4928K8

_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_



*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/106494781436168/

NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH



✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_

PAGE-25


_*TUKWICI GAREKU YAN team DIN YAYANA🥺DUK DA DAI INA KISHI KUNFI SONSA AKAINA,JASMINE, MRS MUBARAK,RANO ON TOP,AMATULLAH,FATIMA ZAHRA,BELAR MAXARE,XEE XEEN BABA,FATIMA SULAIMAN,UMMU NIHEEL, DA MA SAURAN ,I HEART U OLL🥰*_


🤔🤔 _*WATO ANGA NA DAGE DA TYPING SHINE ZA AFARAMUN ISKARAN BARANCI🥺TO DAGA WANNAN FEJIN SAI BAYAN SALLAH TUNDA HAKA KUKESO🚶‍♀️*_




*****


Sallama Kabeer ya yi cikin sayayyar murya.


Amsawa tai tamkar mai ciwon baki.


"Ba zan gaji ba,domin ina Sa ran cewa wataran wannan kiyayyar zata koma so, Ina Miki so tsakanina da Allah Maryam, Ina son nai rayuwa dake rayuwa ta farinciki irin ta masoya,kowa na miki kallo acewa ke Maryam ce kadai Amman anawa bangaren ke tamkar taurarice da ke haskaka sararin samaniyi,aduk lokacin da nai kewarki kallon sama Kadai kan sani nishadi bare kuma ace ke din da kan ki na gani,Dan Allah ki amshi muradin raina ko da sai dayane,tare da sakarmin murmushi komin kankantarsa,duk da kasancewar bama tare Amman hakan ba zai hanani siffata kyakkyawan murmushi da zai bayyana afuskar gimbiyata ba."



Maimakon bayyanar murmushi afuskar Maryam wani irin hamshakin takaicine ya turnike mata azuciya, ji take tamkar zaginta yake, kamar yadda ta tssni Kalmar so haka ta tsani kalaman so.

Ba ta San lokacin da ta sake wani kasurgumin tsaki ba,Wanda sai da ya ratsa cikin wayar tamkar agaban kabeer tai.



Yaji tsakin Amman so da kauna ya hanashi jin haushi ko ganin laifinta illa murmushi da ya sake,domin kuwa yaune rana ta farko da har ta Iya amsa kiransa.

Maryam ta ce, "Ka gama?"


Jiki asanyaye ya ce, "Ba zan taba gamawaba,Amman ganin cewa baki cika son yin maganar ba yasani dakatawa."



Wani tsakin dai ta kara sakewa kan ta ce, "OK Na gode." Batare da ta jira amsar shi ba ta datse wayar.

Masalin karfe goma na safiya aka sauke Nafseen Kofar gidansa.

Rukayya zaune tai tagumi ban da tunanin Mijinta ba abun da take.


Da sallamarsa ya shigo ta karasa gareshi da gudu ,yanayin ta ganshi ne yasa jikinta yin sanyi.

Duk jikinsa plaster koba,a fada mata ba ta San wannan hatsarine yayi.


wani kuka ta fashe dashi tare da rungumarshi tana da kyar ya lallamata tayi shiru .

falo suka shiga ta tayashi ya zauna tana hawaye tace Bari na hada maka ruwan wanka ji take kaman ciwon yadawo kanta.





Taimaka masa tayi ya yi wanka,tare da gasa masa jiki,kwanciya yayi ita kuma ta fito cikin hanzari ta hada masa abinci kawo masa tai ta ce, " bari na baka kar kaji zafi ."


Murmushi kawai yayi aransa yana kara jin tsantsar so da kaunar matar ta shi,tana bashi tana hawaye kaman ciwon a jikin ta yake.

"Yanzu dama abinda yasa meka Kenan kako fada min?"cewar Rukayya

Nafseen ya ce, "kiyi hakuri banso hankalinki yatashine, kuma kinga ma ai abun yazo da sauki mussaman yanzu da nai wankannan naji dadi sosai, Mah Yar Lukata." Ya karasa maganar cikin zolaya.

Hannu ta kai zata dakeshi, sai kuma ta tsaya tare da murgada baki , "Yasin ni ba yar lukutace ba,kuma zan rama yau Dan baka da lafiyane."

Murmushine kawai ya bayyana afuskarsa batare da yace komai ba.



Rukayya ta kara da , "yanzu wayarkan fa?

Nan ya ce, " Ban gani ba fa tun adaren jiyan, Allah kadai ne yasan meyake nufi da hakan, zanyi amfani da dayar wayar kawai,kinga yanzu ba,a welcome back kan lokaci ga sabgogi sunmin yawa wancan sim card ba kowa yasanni dashi ba zan dai rasa wasa daga contacts Dina."



Rukayya ta ce, "Allah Sa hakanne mafi alkairi."


Ya amsa da "Ameen."




GIDAN SU MUTANSIR

Daddy ne yadawo Momy take sanar masa halin da Mutansir ke ciki nan da nan tashin hankali ya bayyana a fuskarsa.

Batare da ya ce komai ba,bangaren Mutansir din yayi tare da nufan dakinsa.


Ban da rawa ba abun da jikinsa ke yi duk ya fita a hayyacinsa.

hankalin Dady ya tashi,matukar gaske.

" Son Wai akan Mace ne nake shirin rasa ka? ka fada min ko yar waye bazan bar komai yasameka ba, na maka alkawarin haka son, Dan Allah kacire damuwar komai ka tuna cewa kai waye kuma waye mahaifinka,inka cutar da kanka ba zan yafe ma ba."

Kokarin Mikewa Mutansir yake kaman ba abinda ke damunsa, Dady ya yi kokarin tallefa, ya rungumer dadyn ya yi yana "Dady da gaske Dan Allah? Wallahi ina son Nafeesa, na San zaka auramin ita."


" In Sha Allah Son, yanzu ka taso mu ci abinci."

Haka Dady ya rike shi suka wuce dining Momy ta zaunaddashi,Sannan suka fara cin abinci,Dady kuwa ya kasa ci tunanin yadda zai bullowa lamarin kawai yake.




***Mammah ta gama shirya kayan break tasan tunda taga Nafeesa bata fito ba,to tabbas bata farko awannan barcin nata ba, dakin ta shiga domin dubata.

Tana nan dai kamar yadda ta barta, addu'a ta shafa mata cikin yanayin damuwa kan ta fice daga dakin.


Haka RANAR Mammah ta zauna agida bataje asibiti tana jiran ko Allah yasa Nafeesa ta farka Amman shiru har Yamma, Maryam ma taje skul gsshi har sun tashi Amman ba Nafeesa, kuma ta kira wayarta akashe hakan yasa ana tashi ta nufi gidan.


Isarta kuwa Mammah ta samu zaune tai tagumi afalo.

Ta sanar da ita halin da ake ciki,cikin damuwa Maryam ta shige dakin,kuka take tana mai yiwa kawar tata addu'ah,Mammah ce ta kara gyara mata kwanciya tare da kokarin cire mata glass din kar ya dameta,abun Mamaki glass din ko motsawa bai yi yaki fita, ba yadda Mammah ta Iya haka ta bar mata.


Maryam ta ce, "Mammah wai me ya farune ma har ya janyo barcinnan nasan dole sai an mata wani Abu."





Mammah ta ce, "Hmm nima dai ji nai tana kuka ina zuwa ta ce mun wani Abu ya sameshi daga nan bata kara magana ba."

Maryam ta ce, "To shi wa?" Sai kuma ta tuna.

Kukan ta kara fashewa da shi.



Sallama akayi agidan
Maryam ta fito wa zata gani......??



Urs Xayyeesherth[4/7, 9:51 AM] Xayyeesherthul-Sweery: _*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_



*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/106494781436168/

NA
XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH



✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_


PAGE-26


_*SADAUKARWA GA SAI NA AURI MARUBUCI FANS GROUP 1ND 2😘INA YINKU HAR CIKIN KAUNYEN RUHINA*_
_*FATIMA SULAIMAN MUHAMMAD FATAN ZAKIYI MURMUSHI? TARE DA NMCY NA AMATULLAH😘*_
*********
Mutansir ne tare da mahaifinsa.


Maryam na ganin Mutansir sai da gabanta yayi mummunar faduwa,Shi ko Mutansir ban da murmushi ba abunda ke bayyana afuskarsa.


Jiki A sanyaye Maryam ta ce, "Ina kwana?"


Cike da farinciki Dady ya amsa da "lafiya, ince wannance surukar tawa?"


Karaf Mutansir ya ce, "Aa fa wannan kawartace Maryam ita kuma sunanta Nafeesa."



Murmushi dadi ya yi, "Ah to Amana sallama da mutan gidan ko?"



Maryam ta ce, "To." Sannan ta shiga ciki domin sanar da Mammah sun yi baki,batare da tai bayanin suwaye ba.


Cike da Mamaki Mammah ta Sa hijabi sannan ta fito.


Rusunawa tai ta gaida Dady,haka ma Mutansir ya gaidata.

Mammah ta ce, "Ga shi Mai gidan baya gari,Allah Sa dai lafiya?"


Dady ya ce, "Ayyah! Aiko banji dadin hakan ba Sam, zan bukaci number wayarsa domin mu fara tattaunawa kan lamarin nan,zumunci zamu hada, Wanda nake fatan duk zamu karu da juna."


Mammah dai bata fahimci mai yake nufi ba,number kawai ta bashi tare da yi masa sallama.

Mutansir kuwa ya dage sai lek'e yake ko Allah zai sa ya hangi Nafeesa Amman ina ba alamarta bare ita.


Har Mammah zata shige gida, Dady ya mikawa Mutansir wasu makuden kudi, da gudu ya karasa gabanta tare da mika mata.

Mammah taki karba fir, Dady ya ce, "Indai ko kika ki karba tamkar kin rainamun arxikine,sannan kuma kin maida hanun kyauta baya."


A haka dai da kyar har Mammah ta karba Amman ba da son ranta ba,domin har cikin ranta batajin son mutanen ko kadan yanayinsu bai birgeta ba.

Tana shiga ciki kuwa Maryam ta ce , "Mammah Allah Sa dai lafiya? Wannan fa Dan skul din nan namune wanda da yasa Habibbty agaba,ya dawo kuma yanzu yana sonta."



Mammah ta numfasa kan ta ce, "Oh Sai Yanzu na fahimta atakaice dai Sunzo siyan Nafeesane ba ma Neman aurenta ba,tunda kiga kudin da suka ban ya fima na sadakin." Ta karasa maganar tana juya kudin da ke hannunta.



Maryam ta ce, "Hmm Wallahi Alhajin Mutansir zai Iya abun da ya fi hakama Dan farincikin Dan Sa."



Ta shi Mammah ta yi tana, "Koma miye dai ai sai da amincewar Nafeesa za ayi,ayadda take dinnan da ace zataso shi inda gaske yake da nafi kowa jin dadi, Amman indai bata son shi akace za amata dole tabbas zamu Iya rasa Nafeesa,ke kan ki shedace Maryam,ni narasa banbance waye nafseen dinnan SHIN NAFSEEN MUTUM NE KO ALJAN?"


Maryam ta ce, "Mammah nima wallahi narasa ganewa kan lamarin Habibbty ga shi dai muna ganin littafai da films din da ya rubuta,Amman ganinshi ya zama wani babban Abu,duk da kasancewar Kwanaki ta fadamun cewa ta fara chatting da shi."




Mammah ta ce, "Allah ya kyauta,bara in ajiye wannan kudin mutafi gun mai magani domin ga dukkan alamu wannan barcin na da banbanci da Wanda ta saba."




Maryam ta ce, "Hakane kan bara na Kira mana mai Nafe sai muje kawai."


Haka kuwa akayi daukan Nafeesa Mammah da Maryam sukai suka sata a nafe har akaje gun mai magani, in kaga fuskar Nafeesa za ka sha mamakin yadda take sheke domin barcinta take bilhakki da gaskiya, ba motsi Amman numfashinta na fita kamar kowa.



Mallam Ado,Duk da kasancewar shine mai maganinta,tun tana karama Amman har yau bai daina mamaki ga irin yanayi na kaddarar Nafeesa ba,acewarshi kamar yadda take fada akullum Sirrine Wanda Allah kadai ya San wannan sirrin da kuma ranar bayyanarsa.


Adu'o'i ya mata ya shafa mata,sannan ya basu hayaki akarshe ya sanar da Mammah , "In sha Allah zata farka Amman ba kamar sauran ba,wannan barcin ya banbanta kamar yadda kuka gani, zata Iya yin watama ko fi cikinsa,babban abun dai bai huce adage da addu'ah ba Amman nafeesa na cikin lafiya da kwanciyar hankali, ban San miye ba dai Amman sanda abun da takewa barcinnan ya kau zata farka da yardar Allah,domin barcinta ayanzu shine mafita inda ko batai barcinnan ba baxaku taba gane kan ta ba."


Mammah ta numfasa kan ta ce, "To Mallam glass dinnan fa tun agida nayi-nayi na kasa cire mata ba zai mata wata illa ba?"


Murmushi Yayi , "Hajiya kenan,kin yi kuskuren tabawama da baki taba mata ba domin inda da bukatar hakan da tuni kin tsince shi gefe ko ince ki rasa shi ma, tamkar kariya yake gareta karki damu da hakan ko kadan, ayadda Nafeesa take banjin cewa akwai wani Abu da za a Iya mata na illatawa,abubuwan da ke faruwannanma kisa aranki kawai kaddarane,kuma komai yayi farko zai yi karshe acigaba da addu'ah dai muma muna kan yi."


Godiya Mammah ta yi sosai kan suka nufi hanyar dawowa gida.


*****bangaren Mutansir da Daddy kuwa suna komawa gida Mutansir ya Sa shi agaba kan cewa sai an kira Abhi.

Ringing biyu ya daga kasancewar ya tsaya shan mai amota...






08103080717
✍️ Xayyeesherthul-humaerath
[4/7, 9:51 AM] Xayyeesherthul-Sweery: _*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_
_(Nafseen)_



*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Gidan karamci, rubutu don ci

Please Login or Register in order to submit comment