Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

MAKASHIN MAZA
Rubuta Labari
Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Ɗaukar Nauyi
Mansur Usman Sufi
08137237071




Bayan shekaru dari takwas, zamani mai tsawo ya shude, an yi wani mashahurin sarki mai suna Lamisu a cikin birnin Ban nur. Wannan sarki ya kasance mai tarin dukiya, kuma ma'abocin son jin dadın duniya ne. A bisa wannan dalili yasa aka tara masa dukkanin magina na kasar, yace dasa yana so a gina masa kasaitacciyar fada wadda babu kamarta a duniya.


Ko da jin wannan batu sai sarkin magina ya mike yace "Ya sarkin duniya hakika ka zo mana da babban al'amari, don haka muna bukatar ka ba mu kwana bakwai mu je mu yi tunani"


Sarki Larmisu yayi murmushi yace "Na amince, kuma ina tabbatar muku da cewa komai yawan dukiyar da za'a kashe a kan wannan gini zan bayar"


Daga nan ya sallame su suka tafi.


Bayan kwana bakwai sarkin magina ya dawo yace da sarki sun gama shiri, nan take sarki ya bayar da duk abubuwan da ake bukata aka fara aiki.


Ana cikin yin haka sai aka tono wani irin ruwa a cikin karkashin kasa, wanda yai matukar tsorata wadannan magina. Shi dai ruwan mai kauri ne, kuma wani abu na motsi a cikinsa. Maginan suka yi iya kokarinsu akan su kwashe wannan ruwa amma sai abu
ya gagara, saboda tsananin santsinsa. Cikin tsananin razana maginan suka ruga izuwa fada suka sanar da sarki halin da ake ciki. Ko da jin haka, sai sarki Larmisu tare da bokansa Arjalu suka rugo izuwa wannan wuri. Da zuwa suka iske wannan ruwa, Boka Arjalu ya fiddo wata battar tsafi yayi wani tsafi, take wannan battar ta zude wannan ruwan gaba dayansa.


Arjalu ya dubi sarki Larmisu yace "Ya sarkin duniya, hakika akwai bayani mai hadari dangane da wannan ruwan, akwai bukatar bincike, zai fi kyau ka bini zuwa dakin tsafina"


Ba tare da wata gardama ba sarki Larmisu ya amince da shawarar boka Arjalu, suka tafi izuwa dakin tsafin su biyu kawai.


Daki ne wanda aka gina shi da duwatsun wuta, babu komai a ciki face tarkacen kayan tsafe-tsafe kamar kahunhuna, gashin dabbobi iri-iri, da kwalabe masu dauke da ruwa mai launuka da yawa. Da shigarsu cikin dakin sai boka Arjalu yai nuni ga wata kujerar karfe ga sarki Larmisu yace ya zauna.


Larmisu ya zauna, shi kuma sai ya fiddo battar nan wadda ya zuke ruwannan a ciki, wato ruwan da aka hako a wajen gini. Take boka Arjalu ya dora battar bisa wani farin gilashi ya fara surutai na tsafi tare da rufe ido. Jim kadan da faruwar haka, zufa ta lullube Arjalu, jikinsa ya kama karkarwa, al'amarin ya da ya firgita


sarki Larmisu, daga can kuma sai ya ga wani farin hayaki ya bulbulo ta cikin kunnuwan boka Arjalu.


Boka Arjalu ya kwalla ihu mai karfi tare da mikewa tsaye zumbur, sai da yayi dogon ajiyar numfashi gami da atishawa, sannan ya dubi sarki Larmisu yace "Ya sarkin duniya, hakika wannan ruwan ba ruwa ba ne mutum ne"


Cikin tsananin mamaki sarki Larmisu ya mike tsaye yace "Ban gane ba, me kake nufi?"


"Wannan ruwa, ruwa ne na masifa, ruwa ne na bala'i, hakika maginanka sun tono babbar jaraba ga dukkanin mutanen duniya. Wannan wani tsohon azzulumin matsafin sarki ne wanda ya gallabi mutanen duniya a zamaninsa, sunansa Marganu dan Jandanu jikan Gundukurki, ina tabbatar maka da cewa idan ya tashi kowa ya shiga uku. Ba zan iya ci gaba da tsare shi ba a cikin battar nan fiye da kwana arba'in, ka sani idan ya tashi karagarka tafi karfinka, ba kai ba ma gaba daya sarakan duniya da matsafan duniya mun shiga cikin mummunan bala'i"


Ko da jin wannan batu sai hankalin sarki Larmisu ya kara dugunzuma, ya fara kai komo a cikin dakin tsafin, ya kasa tsaye ko zaune, sai ya kai gwauro ya kai mari. Daga can ya tsaya ya dubi boka Arjalu suka fuskanci juna sosai yace "Kai boka Arjalu! Ka tuna kai matsafi ne dan matsafa kuma jikan matsafa, maza ka






shiga aikinka! Ka bincika ko akwai hanyar da za mu bi mu samawa kanmu sauki, mu ceto rayuwarmu da ta sauran jama'ar duniya"


Yayın da boka Arjalu ya ji haka sai ya tuntsure da mahaukaciyar dariya har sau uku, sannan ya shafi gemunsa yace "Ya sarkin duniya, hakika ka zuga ni kuma na ji dadi, saboda haka zan yi aikina, na rantse da darajar tsafi sai na samo mana mafita, amma ina so ka ba ni tsawon kwana biyu"


Yayin da sarki Larmisu ya ji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya, sannan yace "To shikenan na amince zan kasance mai sauraronka"


Daga nan suka yi sallama sarki ya tafi.


Sarki Larmisu shi ne sarki na dari hudu da ashirin a jerin sarakan da suka mulki kasar Ban nur, tun daga zamanin sarki Hafis mahaifin Badiya, macen da ta daukaka a duniya akan baiwar fassara mafarki, kuma ita ce wadda ta bar babban abin tarihi a masarautar Ban nur wanda har yau yana nan a rubuce cikin kundin tarihin sarautar garin, a cikin wani daki na musamman a gidan sarautar.


A halin yanzu sarki Larmisu na da mata goma sha bakwai, kuma yana da 'ya'ya kimanin arba'in a da doriya. Shi dai wannan sarki ya mallaki dukiya mar tsananin yawan da shi kansa bai san iya adadinta be. Larmisu mutum ne shagalalle, babu abin da yake tsore


face mutuwa ko rabuwa da mulki, wannan dalili yasa hankalınsa yayi matukar tashi da ya ji cewa Marganu dan Jandanu zai dawo ya raba shi da karagarsa. Lokacin da Sarki Larmisu ya baro wajen boka Arjalu, sai ya dawo gida cikin matukar damuwa. Ko da yai arba da amaryarsa gimbiya Lamsiya, sai ta fuskanci hakika yana cikin damuwa.


Lamsiya ta tarye shi da sauri inda ta rungume shi, sannan ta zaunar da shi bisa wata kujera ta alfarma suka fuskanci juna sosai tace "Ya sarkin sarakai, me ne ne ya tayar maka da hankali na ganka a cikin damuwa?"


Larmisu yai gyaran murya yace "Ya ke sarauniyar taurari, kin sani cewa duk irin bacin ran da na shiga da zarar na yi ido biyu da kyakkyawar fuskar nan ta ki sai na ji zuciyata tai sanyi, amma kin ga yau an sami sabanin haka, tabbas ina cikin mummunan tashin hankali"


Nan take va kwashe labarin abin da ya faru tsakaninsa da boka Arjału ya zayyana mata. Ko da jin wannan batu sai Lamsiya ta tuntsure da dariya, cikin matukar mamaki sarki Larmisu ya janye jikinsa daga nata yace "Me ne ne ya baki dariya?"


Lamsiya ta mike tsaye ta yi 'yar tafiya taku uku, sannan ta waigo ta dube shi tana mai murmushi tace "Yanzu kai akan wannan ne ka tayar da hankalinka? To tsaya ka ji, ni bana tsoron abin da zai zo muddin na san


da zuwansa, wanda ban san da zuwansa ba shi ke ba ni tsoro. Ka je ka saurari bokanka nan da kwana biyun idan har baka sami nutsuwa da mafita ba ka zo gare ni. ni zan baka mafita."


Ko da sarki Larmisu ya ji wannan batu sai yai shiru ya kura mata ido ya kasa cewa komai, ba dan komai ba sai don ya san cewa tana da babban abin dogaro. Mahaifin Lamsiya wani kasurgumin matsafi ne wanda ya shahara a duniya, domin a wannan zamanin ana kyautata zaton babu matsafi kamarsa a duk duniya. Shi ne matsafin da ya mayar da mutanen wani babban gari birai gaba dayansu, yau shekara ashirin kenan da faruwar al'amarin, har yau mutanen na nan a matsayin birurruka an rasa wanda zai warkar da su, har ma sun hakura sun rungumi kaddarar karasa rayuwarsu ta duniya haka, sunan wannan gari na birai Maduwal, shi kuma matsafin da ya mai da su biran wato mahaifin Lamsiya sunansa boka Zafaratu, a yanzu haka idan mutum ya je birnin Maduwal zai iske su a cikin rayuwa irinta bil'adama babu abin da ya sauya na daga al'adu da harkokin yau da kullum, matsala daya kawai basa magana kamar yadda sauran bil'adama ke yi, idan fatake suka shiga garin sai dai su yi harkar kasuwanci cikin bebanci.


***


aderbege


*shirya


Bayan kwana biyu sun cika sai sarki Larmisu ya koma gidan boka Arjalu yace da shi "Ya kai boka Arjalu, ka sani cewa yau ne ranar cikar alkawarinmu, dan haka na zo na ji daga gareka, me ne ne mafita a bisa wannan masifa da ta tunkaro mu?"


"Wannan zance haka yake, ya sarkin sarakai kamar yadda na gaya maka cewa zan yi bincike, to na yi kuma an dace, sai dai al'amarin ya zo da wani babban al'amari mai wuyar gaske. Inda zaka yi bincike a cikin littafin tarihin sarautar kasarka zaka ga yadda wadansu jarumai su biyu Sham'unal gazi da dan'uwansa Uzaifa suka narkar da Marganu dan Jandanu, ya zagwanye ya zama wannan ruwa da maginanka suka tono. Ka sani cewa su wadannan 'yan'uwa ma'abota addinin Musulunci ne, to kasa ni a duk fadin duniyarnan babu wanda ya isa ya kawar da Marganu idan har ya tashi, face tsantsan ziri'ar su Sham'unal gazi. Yau shekara dari takwas kenan da zamaninsu, babu sauran ziri'arsu a duniya face wani saurayi guda daya kacal da mahaifinsa, wadanda suke zaune a can birnin Kashmir da ke kasar Hindu, ana kiran yaron Bilal. Shekarun Bilal ba za su wuce ashirin da biyu ba, kuma shi jika ne na dari da arba'in ga Sham'unal gazi dan Safwan. Daga nan zuwa birnin Kashmir tafiyar kwana sittin ce ga matashin aljaai mai matukar jarumta, amma akwai wani aljani mai suna


Daskin wanda zai iva zuwa čikin kwana goma sha bıyar Idan ka amince zan ıya hadaka da Daskin va kai ka ka je ka zo da Bilal kafin kwana arba'in, wato kafin Marganu dan Jandanu ya tashi"


Yayın da sarki Larmisu ya ji wannan batu, sai bankalinsa ya dada dugunzuma fiye da kowanne lokaci, maimakon ya sami nutsuwa da abin da boka Arjalu ya sanar da shi.


Boka Arjalu ya dubi sarki cikin mamaki yace "Yaya kuma na ga hankalinka ya kara tashi Larmisu yai ajiyar numfashi yace "Shin ka taba ganin ruwa da wuta sun hadu an zauna lafiya?b Boka Arjalu yace "A'a"


"Karka manta mu ba mu da wani addini a kasarnan face tsafi, shi kuma Bilal dinnan da kake magana musulmi ne, baka tsoron idan na zo da shi yai mana maganin Marganu, jama'a za su yi imani da addininsa?"


Ko da Arjalu ya ji wannan batu sai yayi shiru yana mai tunani, daga can yace "Hakika ka zo da magana mai karfi, hakika sam ban yi tunanin wannan al'amari ba, to amma ka da wannan ta tayar maka da hankali, kafin ya zo sai mu sihiree zuciyoyin jama'arka"


Sarki Larmisu yace "Kai al'amarinnan yana da wuya, abinda za a yi nima ka bani kwana biyu na je na yi nawa tunanin, in ya so sai na zo mu yanke shawara"


Boka Arjalu yayi murmushi yace "Ya sarkin duniya, kada ka wahalar da kanka, na rantse da girman tsafi babu abin da za'a yi a sami nasara fiye da wanda nace ayi"


Nan dai sarki Larmisu yai sallama da boka Arjalu ya dawo gida cikin damuwa, da zuwa ya sanar da Lamsiya duk abin da ya faru tsakaninsa da boka Arjalu.


Da jin haka Lamsiya ta bushe da dariya tace "Ai na gaya maka cewa kada ka damu zan kaika wajen babana boka Zafaratu, shi kadai ne a doron kasa zai iya yi mana maganin masifar nan."


Larmisu yace "Hakika na amince, abin da za'a yi yanzu ki tashi mu yi shiri yanzun nan sai nasa a shirya mana 'yan rakiya"


Lamsiya tace "Haba ranka ya dade saurin me ka ke yi?"


"Dole na yi sauri don ba ni da isasshen lokaci, yau fa saura kwana takatin da takwas Marganu ya tashi, kuma kin sani cewa daga nan zuwa garinku tafiyar kwana guda da yini ce."


Lamsiya tace "Hakika ka yi gaskiya, don a bari ya huce shi ke kawo rabon wani"


"Kwarai kuwa, kuma Zama a waje daya tsautsayi ne ba"


Nan take sarki yasa aka shirya dawakai da guzurin tafiya tare da barade hamsin, suka dau hanya izuwa


burnin Hazaras inda mashahurin matsafın yake wato boka Zafaratu mahaifin gimbiya Lamsiya amaryar sarki Larmisu na garin Ban nur.


***


Sannu-sannu sarki Larmisu da amaryarsa Lamsiya uka iso birnin Hazaras. Birnin Hazaras karamin gari ne mai dauke da jama'a kadan da daidaikun gidaje. Gaba daya mutanen garin sun yi imani da sarkinsu wanda shi ke sanar da su komai na dangane da rayuwarsu, a karshen kowacce shekara sukan taru a kofar gidansa ya sanar da su abubuwan da za su faru a sabuwar shekara Ya kan sanar da su mutuwa, fari, yabanya da sauran al'amuran rayuwa.


Tun kafin su sarki Larmisu su karaso kofar gar suka yi kicibus da 'yan tarya, wasu kartin saman mutum hudu sanye cikin jajayen fatu, wadannan su kasance barorin gidan su Lamsiya ne. Ko da ganinsu bisa dawakai sai Lamsiya ta kira sunayensu, suka amsa take suka sauko daga kan dawakansu suka zube kasa su kai gaisuwa a gareta da kuma sarki Larmisu.


Lamsiya ta dube su tace "Ina zaku je ne?"


Daya daga cikinsu wanda ya fi sauran kwarjin yace "Ranki ya dade ai dama ku muka zo tarya, ai tur jiya sarki ya sanar da mu zuwanku"


Duk da sarki Larmisu ya san al'amarin boka Zafararu, sai da yayi alajabin yadda akai ya san da Puwansu. Nan dai yan tarya suka juya suka wuce gaba su sarki Larmisu suka bisu a baya, tafiya kadan suka iso gidan boka Zafaratu, aka shigar da su har cikin fadarsa.


Boka Zafaratu yai musu marhaban aka gaisa. sannan ya dubi sarki Larmisu yace "Na san kana cikin zumudin ganawa da ni, amma ina so ka yi hakuri ku huta tukunna ku ci abinci, in ya so sai mu gana da daddare."


Sarki Larmisu yace "Godiya na ke, ya sarki bokayen duniya"


Ba tare da bata lokaci ba aka kawo masa ababan ci da sha na alfarma, ya ci ya sha, sannan ya kwanta ya huta, ita kuwa Lamsiya tuni dama ta wuce cikin gida wajen mahaifiyarta. Sai da aka sami sa'a biyu da faruwar wadannan abubuwa, sannan boka Zafaratu ya aika aka kirawo sarki Larmisu da Lamsiya suka gabata gareshi.


Boka Zafaratu wani dattijo ne wanda shekarunsa sun haura dari da arba'in, duk da wannan tsufa na sa babu alamar gajiyawa a jikinsa ko kadan. Yana da farin dogon gemu mai tsananin haske da shekl, gashin girar sa ma fari ne, yana da kwala-kwalan idanu masu girma kamar na mujiya, hancinsa mai tsini ne, kuma yana da


karamin baki, dogo ne matuka kuma kakkaura, kai da ganinsa ka san da can an yi kasurgumin jarumi.


Lokacin da sarki Larmisu da Lamsiya suka shigo cikin dakin boka Zafaratu, sai suka iske shi zaune bisa wani buzu mai kyawun gaske. Cikin biyayya Larmisu da Lamsiya suka zauna a gefe guda aka sake gaisuwa, sannan shiru ya biyo baya, har tsawon dakika goma.


Sarki Larmisu yai gyaran murya sannan ya bude baki zai Magana, sai boka Zafaratu ya tari numfashinsa yace "Kada ka wahalar da bakinka duk abin da ke tafe da ku na san da shi fiye da shekaru sittin baya, boka Arjalu ya sanar da kai cewa Marganu dan Jandanu zai tashi nan da kwana talatin da takwas, kuma idan ya tashin kowa zai shiga tashin hankali a duniya, kwarai kuwa abin da ya gaya maka gaskiya ne. Kuma ka nemi ya sanar maka da mafita, inda yayi binciken kwana biyu sannan ya sanar da kai cewa sai ka je birnin Kashmir ka dauko Bilal, wannar ma haka ne, amma idan kai hakan har abada ka rabu da mulkinka kenan da dukiyarka, wannan yaro Bilal shi zai maye gurbinka"


Ko da jin wannan batu sai sarki Larmisu yace "Ya sarkin bokayen duniya, kai mini rai, ka ceto matsayina da kimata, ka dubi darajar 'yarka guda daya cal a duniya ka taimake ni"


Boka Zafaratu ya tuntsire da dariya, sannan ya hade fuska yace "Hakika Marganu dan Jandanu


cikakken hatsabibi ne, ina da labarinsa tun ina da shekara takwas a duniya, duk irin tsafe-tsafen da yayi ya sami daukaka a duniya na yi bincike akansu na gano yadda yayi su, ina tabbatar muku da cewa ni ma zan iya yin duk abin da yayi, sai dai kash! ni ba ni da wannan burin a zuciyata, saboda yanzu tsufa ya riske ni kuma gani na sami nisan kwana a duniya. Ya kai wannan sarki ina sanar da kai cewa ya zama dole mai laya ya kiyayi mai zamani, Marganu ya ci zamaninsa tuni. yanzu ni nake cin nawa, bai isa ya dawo ba ya fi karfina. Tun ina da shekara takwas na san da cewa akwai ranar da Marganu zai dawo duniya, kuma tun a sannan na fara kokarin neman abin da zan hallaka shi. a cikin bincikena na gano cewa idan ina so na hallaka Marganu yadda har abada ya tafi kenan, sai na samo wadansu abubuwa guda uku, abu na farko shi ne gashin jelar Ifiritu na kwalba, wato takadarin aljanin nan wanda aka kulle shi a cikin kwalba aka jefa cikin teku ya bace a karkashin ruwa, har yau ba'a sake ganinsa ba. Abu na biyu shi ne ainihin sandar sarki na farko wanda ya fara sarautar aljanu a doron kasa, wadda a halin yanzu tana nan ajiye, kuma a tsare cikin gidan sarautar sarkin aljanu na birnin Sin. Abu na uku wanda gaba daya yafi wadannan wahala, shi ne kitsen kifin da yafi kowanne kifi girma a duniya. Tuntuni na gano cewa ni da aljanuna masu yi mini hidima baza mu iya samo


wadannan abubuwa ba, face da taimakon aljani guda daya, ba wani ba ne face aljani Daskin. Ka sani duk duniya babu wanda ya isa ya saka Daskin aiki face boka Arjalu, don haka ka koma gare shi ka gaya masa bukatarka zai amince, amma zai shimfida maka wadansu sharuddai guda uku, sai ka duba ka gani idan ka ga zaka iya sai ka yi. Ni kam ina tabbatar maka in dai ya amince va ba mu aron Daskin, to babu shakka a cikin kwana bakwai za mu samu wadannan abubuwa guda uku. Da zarar abubuwan sun zo hannuna shekinan mun gama da Marganu, zaka ci gaba da mulkinka duniya ba tare da wani ya zo ya rabaka da addininka ko karagarka ba"


Ko da boka Zafaratu ya gama wannan jawabi, sai gumi ya karyowa sarki Larmisu, ya sake shiga sabon tunani. Take ya ji duniyar gaba daya tai masa zafi, sai da ya sami kusan rabin sa'a sannan ya dago kai ya dubi boka Zafaratu yace "Ya sarkin bokaye, hakika na ji duk bayaninka kuma na yi tunani na tabbatar da cewa bani. da wata mafita face na bi shawararka, saboda hak na amince zan koma gida na sake neman taimakon Doña Arjalu, kuma zan amince da dukkanin sharuddan da ya shimfida mini."


Da jin haka murna ta kama boka Zafaratu yace "Hakika ka yi tunani mai kyau, kuma idan har ka yi


hakan ka tsare mutuncinka da namu daga sharrin abokan gabarmu mabiya addinin Musulunci"


A cikin wannan dare sarki Larmisu da matarsa Lamsiya tare da 'yan rakiyarsu suka kimtsa suka koma garin Ban nur. Da zuwa kai tsaye suka wuce izuwa gidan boka Arjalu, sarkı Larmisu ya gabatar da bukatarsa.


Yayın da Arjalu ya ji bukatar sarki, sai yai shiru ya sunkuyar da kansa kasa, jim kadan ya dago yace "Ya sarkin sarakai, ka sani cewa kamar shekaru hudu da suka gabata na taba zuwa gareka na nemi wata alfarma amma ka ki amincewa, wannan alfarma ba komai ba ce face ka bani auren kuyangarka Samali, idan har kana so na baka aljani Daskin sai ka bani abu uku, abu na farko shi ne ina so ka daura aurena da kuyanga Samali, abu na biyu ina so ka raba dukiyarka gaba daya kasu biyu ka bani kaso guda, abu na uku ka raba kasarka biyu ka bani rabi na mulka, in dai kai haka zan baka aron aljani Daskin ya je yai maka wannan aiki." -


Sa'adda sarki Larmisu ya ji wadannan sharadai sai bakin ciki ya mamaye zuciyarsa, bai san sa'adda kwalla ta zo masa ba, duk tashin hankalin da ya shiga a baya _sai ya ji kamar ruwan sanyi ne akan wanda zai shiga nan gaba idan ya rabu da wadannan abubuwa guda uku, wadanda boka Arjalu ya bukata daga gareshi. Abu na farko dai ita kuyanga Samali tun tana shekara shida


sarki Larmisu ya kwato ta daga hannun wani sarki da Karfin tsiya, ma'ana sai da ya yake shi. Samali kyakkyawar yarinya ce wadda bokayen duniya na wannan lokaci suka tabbatar da cewa duk sarkin daya aureta ba shi ba talauci har bada, kuma ba za'a taßа cinsa da yaki ba. Bokayen sunce ba za'a auri Samali ba sai ta kai shekara ashirin a duniya, a halin yanzu shekararta goma sha takwas kenan yana kowonta, a yanzu kyawun Samali ya bayyana sosai karara a fili yadda duk namijin daya dubeta sai ya kamu da sha'awarta. Bakin cikin sarki Larmisu shi ne yanzu saura shekara biyu lokacin daurin aurensu da Samali yayi gashi boka Arjalu zai raba shi da ita. Abu na biyu wanda ya sosa ran sarki Larmisu shi ne ya tabbatar da cewa idan ya raba dukiyarsa da kasarsa biyu ya baiwa Arjalu rabi, ai tamkar sun zama daya ne. Idan suka zama daidai kuwa babu mamaki wata ran Arjalu ya neme korarsa daga Bar nur ya mamaye garin gaba daya. wannan shi ne abin da yai ta kai komo a cikin zuciyar sarki Larmisu.


"Ya sarkin sarakai lafiya na ji ka yi shiru?" Boka Arjalu ya tambaye shi


Larmisu ya dago kai ya dube shi sannan ya dubi Lamsiya yai shiru, jam kadan kuma ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

2 Comments On MAKASHIN MAZA Book 1
avatar
hauwau-tijjani-bako

28 days ago

Reply

Meyasa bayayin download?

avatar
taskar

28 days ago

Reply

Replying to hauwau-tijjani-bako

sai kin yi subscription zaki iya downloading, akasin hakan kuma sai dai ki karanta kawai

Please Login or Register in order to submit comment