Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har kin isa ki gasa mun magana?"


Mamu ce ta yi saurin faɗin "Jabir kana da hankali kuwa? ko rashin auren Najmeer ɗin ne ya haukata ka? ka fice mun daga gida tun kafin na tara maka jama'a, bayan kun raba ni da Jikanyata shine za ka biyo bayan fage kana surutan banza, to duk inda ku ka kai mun ita sai kun nemota yawwa"

"Rufe mun baki munafukar tsohuwa ai duk munafurcin da ku ke haɗawa ya dawo kunnena, na ji labarin Najmeer ta dawo gidannan kuma an faɗa mun cewar an ga lokacin da ku ka fita tare, dan haka ki aje duk wani makirci ki fito mun da matata"


"Kai Jabir ne sunanka ko waye? zan ci Ubanka anan gun na fika akuyanci, Mamu ka ke faɗawa wannan maganar?" Cewar Meera tana ɗaukar wani icce da ke gurin cikin masifa, ganin da gaske zata iya dukansa ne ya sa ya matsa da baya yana faɗin "Ku jirani zan dawo wallahi sai na ɗauki mataki a kanku, musamman ƴar tashar yarinyar nan marar kunya sai nayi maganinki" Ficewa daga gidan ya yi yana surutai kamar zararre.

Meera kam ɗaki ta nufa da Mamu ba tare da ta koma bi ta kansa ba, har Meera ta yunƙura zata fita Mamu ta kama hannunta tana mai share ƙwallan da ya zubo mata "Ina zuwa ƴarnan Allah ya sa kema ba tafiya za ki yi ki barni ba" Mamu ta faɗa tana mai fashewa da kukan da take riƙewa.

Da sauri Meera ta zauna tana faɗin "Aa ba tafiya zan yi ba Mamu, idan na tafi waye zai kula mana da ke? kuma ni bana da kowa a yanzu daga ke sai Najmeer iyayena sun rasu, zan iya cewa ku ne dangina, dan Allah ki daina kuka kar ki saka ni nima" Cikin sauke ajiyar zuciya Mamu ta ce "Allah ya jiƙan waɗan da suka riga mu gidan gaskiya, kuma Allah ya bayyana mana Najmeer a duk inda take cikin ƙoshin lafiya" Da ameen Meera ta amsa kafin suka cigaba da fira sama-sama kasancewar kowa da abin da yake tunani a ransa.





Sai da aka kira sallar magrib kafin suka yi sallah Meera ta ɗora musu girgi, ba laifi jikin Mamu ya yi dama dan tana iya miƙewa amma babu ƙarfin jiki, wayar Najmeer kuwa sai kira ake amma ba bu me ɗagawa daga ƙarshe Meera ta kashe wayar.


Wajen tara na dare ne suna zaune da Mamu a tsakar gidan sun yi jugum-jugum jiran ganin Najmeer amma shuru ka ke ji.

Mamu ce ta ce "Nikam na fara tsorata sosai kan lamarinnan? anya kuwa ba Jamilu ne ya sace Yarinyar nan ba" Jin abin da Mamu ta ce ne ya sa Meera ɗagowa a firgice ta ce "Na san wanda ya sace ta" Itama Mamu a kiɗime ta ce "Waye ya sace mun Jikanya dan Allah faɗa mun"

"Sultan Chief ne yaron hamshaƙin me kuɗinnan da ke GRA"


"Chief..., wanda na sani me taimakon talakawannan?"

"Ƙwarai kuwa shine, saboda shi muka baro gidan da mike har can ya zo da niyar kama Najmeer, na tabbata cewa shine ya sace ta"


"Subhanallahi, me Najmeer ɗin ta yi masa yake son illata min ita?" Cewar Mamu a tsorace.

Duk abin da ya faru Meera ta kwashe ta sanarwa Mamu har zuwansu nan gidan, sosai hankalin Mamu ya ƙara tashi dan ta san Chief me kuɗin gaske ne, duk abin da aka yiwa Najmeer baza ta iya ɗaukaka ƙara ba.


Har Mamu ta buɗe baki da niyar magana suka ji ana buga ƙofar gidan da ƙarfi, cikin sauri ba tare da zargin komi ba suka miƙe tare da nufar ƙofar har suna rige-rigen isa.


Meera ce ta buɗe ƙofa ai kuwa ta ji an doka mata abu a kai, nan take ta zube a sume,Mamu kuwa ture ta ƙasa aka yi kafin ta miƙe an rarumi Meera da ke kwance tare da shigewa adaidaita cikin sauri me adaidaitan ya bar unguwar.

Ihu da kuka Mamu ta shiga yi amma ba wanda ya kawo mata ɗauki, sosai ta rinƙa kiran sunan Meera da Najmeer cikin mugun tashin hankali.



Sai da aka yi tafiya me nisa da Meera kafin suka tsaya wani gida me ɗauke da ɗaki ɗaya, Jabir da ke bayan adaidaitar riƙe da Meera ne ya tallafota yana dariyar mugunta "Ni za ki nunawa barikanci? yau zan koya miki hankali kuwa".

A ɗakin ya shige da ita sannan ya cewa me adaidaita ya tafiyarsa.


Sai da ya duba ko'ina ba bu me ganinsa kafin ya faɗa ɗakin tare da rufo ƙofar.


A lakacin Meera ta farka sai dafe kai take dan zafin da yake mata.


Kallonta ta mayar kan Jabir da ke tsaye yana lashe baki, a firgice ta miƙe tsaye 'Kai Jabir me na yi maka ka kawo ni nan gurin?"


"Auuuuu tambaya ki ke? yanzu kuwa zan ba ki amsa ƴammata"


Ya faɗa yana fara cire kayan jikinsa, Meera na ganin haka ta fara ja baya tana faɗin "Kar ka ƙaraso ni wallahi zan tara maka jama'a"


"Ai ko duniyar nan za ki tara mun sai na aikata abin da nake so da ke sannan na kora ki waje tsirara"

Cewar Jabir yana faɗawa kan Meera cikin rashin imani.




........................
A ɓangaren su Sultan kuwa ba ƙaramar azaba ya ke gallawa Najmeer ba, rana ɗaya ta canja kamanni ta fita a hayyacinta, duk bayan awa ɗaya sai ya shiga ya yi mata dukan tsiya.


Yawan shige da ficen da yake ne ya sa Junaid ya zuba masa ido dan ya kasa gane abin da ke faruwa da ƙanin nasa.


Yanzu haka zaune suke kowa na tunanin da ke ransa, Mom na gefe tana kallon program ɗinta, sai Sultan da ya sha'afa da kallon wayarsa da alama ba alkhairi yake kallo ba dan sai matse ƙafa yake har Junaid ya lura da shi, ganin yanda Junaid ya ƙura masa ido ne ya sa shi miƙewa tare da nufar ɗakinsa a lokacin ƙarfe tara na dare ta kusa bugawa, room ɗinsa ya nufa yana mai danna key, ya jima a ciki kafin ya fito sanye cikin wasu kafuran kayan bacci masu ɗaukar ido, a steps ya ci karo da Junaid na ƙoƙarin zuwa nasa ɗakin, ko kallonsa Sultan be yi ba ya sauko abinsa.



Sai da Junaid ya ƙare masa kallo kafin ya ce a ransa, tabbas gurin Sumayya zai tafi kuma ba zan bari hakan ta faru ba.


A parlour Sultan ya sami Mom na shirin shigewa, cikin shagwaɓa ya ƙaraso yana mai faɗin "Mom har kin gama kallon ne?"

Itama murmushin ta yi tana mai shafa fuskarsa "Yes bacci nake ji kaima ya kamata ka kwanta ko za ka samu zuwa aiki gobe"

"Yes Mom but......"


"But....what Son?"


"Zan kwana a ɗakin waccan yarinyar"

Ɗan zaro ido Mom ta yi "Meyesa za ka kwana a ɗakinta? kana son asirinmu ya tonu ne?"

Junaid da ke laɓe ne ya dafe saitin zuciyarsa, wai me ke faruwa a gidannan ne.

Ya tambayi kansa, ganin ba bu me amsa masa tambayar ne ya sa shi cigaba da saurarensu.


Sultan kuwa kama hannun Mom ɗin nasa ya yi "Ba bu wanda zai gane Mom, kawai na rana ɗaya ne ina son na keta mata haddi dan wallahi ba zan raga mata ba, na sha wahala kafin na sameta dan haka sai ta ɗanɗani azabar da na tanada mata"


Ya ƙarasa maganar yana mai nufar upstears.

Mom kam bata yi yunƙurin hana sa ba, dan bata ƙaunar ɓacin ransa ko kaɗan.


Junaid na ganin Sultan ya nufo sama ne ya yi saurin lafewa inda ba zai gansa ba, cikin sanɗa ya rinƙa bin bayansa har hawa na huɗu, da mamaki Junaid ya ƙara zaro ido har Sultan ya shige ɗakin, da ƙarfin tsiya Junaid ya faɗa ciki dan ganin abin da ake ɓoyewa.


Cikin firgici Sultan ya kunna hasken ɗakin tare da sauke idanunsa kan yayan nasa, Junaid kuwa yarinyar da ke kwance cikin mawuyacin hali yake kallo, duk gashin kanta a baje ya rufe mata fuska shiyasa be bashi damar ganin fuskar tata ba.


Wani irin girgiza ɗakin ya yi wanda ya sa Sultan da Junaid zubewa ƙasa kamar waɗan da aka jefar, sosai ɗakin ke girgiza komi na ɗakin ya tashi saman iska tare da fitar da wata ƙara me rikitarwa, cikin mugun firgici Sultan ke kallon Najmeer da ke saman iska tana mai fitar da wata irin dariya me tada hankali, shi kansa Junaid ya tsorata matuƙa.


Cikin mintunan da basu wuce biyu ba Najmeer ta rikiɗe zuwa wata irin jibgegiyar Mage fara tasssss, duk jikinta tabon duka ne, idanuwanta blue masu ban tsoro.


Faratanta kuwa zara-zara kamar reza, bakinta na fitar da wani irin kuka me mugun rikita me saurare.

Cikin mugun gudu Magen ta daka tsalle sama tana mai dira gaban Sultan.









*SHALELEN ALHAZAWA*

*Writing and story*

*By*


*Asmeetar Hydar*

(Asma'u Ayuba)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*





P. 6





Kafin ta yi wani yunƙuri Sultan ya rikiɗe zuwa wata jibgegiyar Kada me ban tsoro, girman Kadar da tsayinta kuwa ya gauraye gurin.

Junaid da ke gefe tuni ya sume ganin ƙanin nasa ya sauya halitta zuwa mummunar Kada me jajayen idanu, cikin fusata Magen da Kada su ka nufi juna tare da fara kaiwa junansu yanka da faratan hannayensu, sosai su ke faɗan tamkar baza su daina ba, tsalle ɗaya Magen ta yi tana mai hawa bayan Kadan cikin zafin nama ta yanki Kadan a wuya da mugun ƙarfi, zafin yankan ne ya sa Kadan ɗaga jelarsa ya doki Magen a kafaɗa, ji ka ke timmmm Magen ta faɗo ƙasa cikin mawuyacin hali, kafin Kadan ya ɗago tuni Magen ta ɓace ba bu ita ba bu alamunta.

Kadan kuwa ya rikiɗe ya koma Sultan da wuyansa ke fitar da jini jiri na ɗibarsa.

Da ƙyar ya ƙarasa gurin da yayan nasa ke kwance, da hannu ɗaya ya saɓa shi kan kafaɗarsa suna mai barin ɗakin.


Be diresa a ko'ina ba sai room ɗinsa, kan bed ya kwantar da shi yana mai gyara masa kwanciya, jinin da ke fita a kafaɗarsa ne ya sa shi zamewa ƙasa a sume, kasancewar ba ƙaramin yanka Magen ta masa ba, a gafen gurin kana iya ganin dafin Magen blue.



Junaid be farka ba sai gurin ƙarfe ɗaya na dare, a firgice ya tashi bakinsa ɗauke da addu'ar da duk ta zo masa, a ransa yana godiya ga Allah da ya sa mafarki ne ba gaskiya ba, kansa da ke juya masa ya dafe yana mai kallon inda Sultan ke kwance cikin jini, cike da dauriya gami da taurin rai ya ƙaraso tare da tallafosa kan cinyarsa, daidai lokacin da Sultan ya saki nannauyar ajiyar zuciya, "Bro......" Ya faɗa yana lumshe ido, bakin Junaid na rawa ya ce "Sultan....? dama abin da na gani ba mafarki ba ne?"

"Bro wani abun ya faru ne?"

Cewar Sultan yana tashi zaune.

"Kana nufin wannan jinin da ke fita a gefen wuyanka ruwa ne ba jini ba?" Junaid ya faɗa a suface.

Saurin shafa gurin Sultan ya yi, sai ga jini kan hannunsa har ya fara daskarewa.

Miƙewa ya yi tare da ƙarasawa gurin mirrow, daga gefen wuyansa har ta bayan duk yanka ne ga niji na ɗiga kaɗan-kaɗan.

Matsawa ya kuma yi gun Junaid yana mai jijjiga shi da ƙarfi "Waye ya mun wannan yankan? me ya sameni kuma ya aka yi na shigo ɗakinka?" Duk a lokaci ɗaya Sultan ya jefowa Junaid waɗannan tambayoyin, a harzuƙe Junaid ya shige toilet ba tare da ya amsa masa ba, ganin haka ya sa Sultan barin ɗakin ransa a mugun ɓace, gaba ɗaya ya kasa tuna abin da ya faru da shi.

Junaid kuwa ruwa ya sakarwa kansa yana mai tunano lokacin da Sultan ke rikiɗewa zuwa Kada, sosai hankalinsa ya ƙara tashi idaunwansa sun ƙanƙance, shin me yake shirin faruwa ne, ya tambayi kansa a zuciya.

Ya jima a haka kafin ya yi wanka tare da ɗauro alwala.



.....................
A ɓangarensu Meera kuwa tana ganin da gaske Jabir zai iya aikata abin da ya faɗa ne ya sa maganganun da Najmeer ta faɗa mata a ranar ya faɗo mata rai, cikin ƙarfin hali ta chakumo Jabir gami da buga kansa kan ginar ɗakin, azabar da Jabir ya ji ne ya sa shi sakin mugun ƙara yana mai dafe kansa.


"Wayyyyo Allah ta kasheni".

Meera na ganin ya faɗi ta buɗe ƙofar da gudu ta fice.


Gudu take sosai ta rasa inda zata tafi, yanzu haka baza ta gane wacce unguwar ce ta su Najmeer ba, dan haka ta nufi kan titi cikin layi da neman mafita.

Sai da ta yi tafiya me nisa kafin ta hau kan titin unguwar, me adaidaita ɗaya ta samu a hanya dan haka ta shige tare da faɗa masa unguwar da zai kai ta, Meera ta san cewa bata da wata mafita a halin yanzu face komawa gurin Maleek, a ƙofar gidan me adaidaita ya sauketa, har ta juya da niyar shigewa gidan ta ji ya ce "Malama kuɗin fa?"

Zare ido Meera ta fara alamun rashin gaskiya "Amm....am.... am so sorry wallahi bana da ko sisi"

"Kutumar uba, ai kuwa baza ta saɓu ba, har kin isa na kawo ki a kyauta dan Uwarki"

Fitowa ya yi tare da kama rigarta yana zuba ashar kamar ba musulmi ba, Meera kuwa sai haƙuri take basa amma tamkar ƙara zuga shi take, kamar daga sama ya ji an ce "Ga kuɗinka ka sake mata riga......"

Wata irin murya suka ji me ban tsoro da firgita me saurare, ba shiri me adaidaita ya saki rigar Meera yana kalle-kalle, sai kuma ya kalli hannunsa da kuɗi ke ciki ba tare da ganin wanda ya ɗora masa kuɗin ba, da mugun gudu ya shige adaidaitar yana barin arean.

Meera da bata san abin da ke faruwa ba ne ta ji ana jan hannunta zuwa cikin gida sai dai bata ga kowa ba, ihu ta fara tana janye hannunta gami da sakin numfashi da ƙarfi dan ta tsorata matuƙa, har cikin gidan aka shige da ita wanda ihun da take ne ya farkar da Maleek, ba shiri ya fito yana mitsike ido alamun bacci kwance kan fuskarsa.

Ganin yanda Meera ke ihu da maganganu ne ya sa shi ja baya a tsorace, daga nesa ya ce "Ke Meera uban me ki kewa ihu haka?"

Meera da duk hankalinta baya kanta ne ta kalli Maleek cikin firgici "Na shiga uku Maleek ka taimaka mun, za su cire mun hannu wallahi ba ni ke tafiya ba, bansan waye ke ja mun hannu ba".


Jin abin da Meera ta ce ne ya sa Maleek runtumawa ɗaki da gudu yana banko ƙofa.

Part ɗin da Najmeer ta kama aka nufa da Meera, a lokacin har ta fara ɗauke numfashi.

Cikin mintin da be fi ɗaya ba Najmeer ta bayyana riƙe da hannun Meera da ke ƙoƙarin sumewa, Meera na arba da Najmeer ta ƙara sakin ƙara me rikitarwa wadda ta sa Maleek ƙara shigewa ƙasan gado domin ceton kansa.

Najmeer kuwa ta zube ƙasa tana sakin numfashin wahala, jikin Meera na rawa take nuna Najmeer da hannu "Najmeer.........., Aljana.....?"

Meera ta faɗa bakinta na karkarwa.

Sai da Najmeer ta kai kusan mintuna biyar a hakan kafin ta ɗago da ƙyar tana kallon Meera, sai kuma ta sakar mata murmushi tana faɗin "Lafiya ki ke kallona haka?" Meera da duk hankalinta baya kanta ne ta ce "Lafiya ƙalau....."

"Amma ya naga jikinki sai rawa yake? ko ba ki da lafiya ne"

"No lafiyata ƙalau, ke ce dai marar lafiya" Meera ta faɗa a tsorace.

"Ni kuma? sai dai Mamu ko, itama ai jikinta ya yi sauƙi tun da har ta samu bacci" Najmeer ta faɗa tana nuna bed ɗin da ke ɗakin, cikin sauri Meera ta maida kallonta kan gadon ai kuwa ta yi arba da Mamu kwance tana sharar bacci, har Meera zata saki ihu sai ta ji bakinta ya kasa motsawa tamkar an ɗinke shi.


Murmushi Najmeer ta sakar mata a karo na biyu tana mai miƙewa tsaye "Shhhhhhhh, lokacin bacci ya yi ni zan shiga wanka, gobe zamu bar gidannan". Ba tare da jiran abin da Meera zata kuma cewa ba Najmeer ta nufi toilet dan watsa ruwa.


Firgici, tashin hankali, ruɗani, duk sun mamaye Meera tare da tarin tambayoyin da ta kasa bawa kanta amsa, sai yanzu take tuna kalmar nan da Najmeer ta taɓa faɗa mata ranar da suka fara haɗuwa, kar ki damu a sannu za ki san ko wacece ni.

Tana zaune har Najmeer ta fito ɗaure da haɗaɗɗen tawul, daga kafaɗarta kuwa shayun duka ne sai wasu wurare a jikinta da duk tabon belt ne, hannu ta ɗaga sama cikin wata irin murya me rikitarwa ta fara faɗin wasu kalamai, Meera kam wannan karon motsin kirki ma kasawa ta yi, sai da Najmeer ta jima a haka kafin ta shafa hannunta gurin da duk wani tabon ciyo ke kwance, lokaci ɗaya ciyon ya ɓace tamkar ba abin da ya sameta, hatta dukan da Sultan ya rinƙa yi mata sai da tabon ya ɓace.

A natse ta shirya cikin kayan bacci milk masu kyau da sheƙi, sai da ta feshe jikinta da turarukka masu ƙamshin daɗi kafin ta saka ƙaton hijab ɗinta sannan ta rama sallar da ake binta, duk abin da take Meera na zaune tana kallon ikon Allah har ta kammala, addu'a ta yi sosai kafin ta koma kan ɗayan bed ɗin ta kwanta.


Sai a lokacin Meera ta iya miƙewa kamar wadda ƙwai ya fashewa, bakin ƙofa ta nufa da niyar fita ta tsinkayo muryar Najmeer na faɗin "Ina zuwa Meera?"

Bakin Meera na rawa ta ce "Gurin Maleek?"

Bushewa da dariya Najmeer ta yi har da riƙe ciki "Maleek kuma? Malama ki zo ki kwanta idan kina son zaman lafiya"

Jin abin da ta ce ya sa Meera komawa ta kwanta nesa da inda Najmeer ke kwance, tana mai karanto duk addu'ar da ta zo bakinta.




Washe garin ranar tun asuba har ƙarfe tara ake tashin hankali tsakanin Mamu da Najmeer, sosai Mamu ke faɗa da tambayar waye ya kawota gidannan, Najmeer kam sai dai ta yi dariya dan rasa amsar da zata bawa Mamu ta yi.


Ganin Najmeer ta shareta ne ya sa dole Mamu yin shuru ba dan tana so ba.


Sai da suka gama tattara komi na gidan wanda mallakinsu ne kafin Najmeer ta nemo masu kwashe kaya.

A harabar gidan suka ci karo da Maleek na ƙoƙarin fita, wani mugun kallo ya watsawa Najmeer "Ke kam daga ganinki ke mayya ce, tun da ki ka shigo rayuwarmu na daina jin daɗin duniyar"

Har Meera ta buɗe baki da niyar magana Mamu ta yi saurin katseta da faɗin "Barshi kar ki ce masa komi, kai kuma ka bi duniya a sannu, ko ba bu komi a tare da ita muke be dace ka jefeta da munanan kalamai irin haka ba"


"Mtsssss ke kuma fa? kun ga wata munafukar tsohuwa, ko kema karuwa ce?"

Cewar Maleek yana dariya.

A fusace Najmeer ta ɗago rikitattun idanuwanta da suka koma blue, da sauri Mamu ta riƙe mata hannu tare da janta zuwa wajen gidan.

Maleek kuwa ya shiga zage-zage kamar ɗan tujara "Ai sai ki barta na ga abin da zata mun, shegu haihuwar wayyo Allah, yooo ni akwai wanda nake tsoro ne a yanzu? idan ta isa ta zo mu gwada ƙarfi, wallahi da rabon na kakkarya banza"



Najmeer na jin duk abin da yake faɗa, amma Mamu ta ƙi sake mata hannu har suka shige motar kwasar kayan.


Tun da suka fara tafiya Najmeer ke musu kwatancen unguwar da za su tafi har suka isa.


Daga Mamu har Meera mamaki ne ya kama su ganin haɗaɗɗen gida me masifar kyau da ɗaukar ido, fitowa motar ta yi sannan ta buɗe gate ɗin gami da bada umarnin a shigo da kayan, haka kuwa aka yi cikin ƙanƙanin lokaci komi ya yi need, kuɗi ta biya masu motar suka kama gabansu.



Cikin gidan Najmeer ta ja su tana mai nuna musu ko'ina da kuma yanda tsarin yake, kasancewar Meera wayayya ce ya sa kayan aikin gidan be bata wahala ba, kan kujerun ɗakin masu masifar kyau suka baje, kallon Najmeer Mamu ta yi ciki alamun tambaya "Najmeer gidan waye wannan? ko sayar da mu ki ka zo yi?"

Dariyar da ke ƙara mata kyau ta yi, "Haba Mamu wannan fa gidana ne, halak malak aka mallakamun shi, idan ba ki yarda ba sai na nuna miki takaddun gidan"

"Gidanki....?" Meera da Mamu suka haɗa baki.


"Yes gidana, kuma har abada zai zauna a matsayinsa na gidana"

Mamu ce ta ce "Yanzu da kuɗin haram ki ka saye wannan danƙareren gidan Najmeer? subhanallahi na shiga uku ni Mamu"

Saurin katseta Najmeer ta yi da faɗin
"Kin ga please kar ki fara dan Allah, wannan gidan ba da kuɗin haram na saya ba, asalima kyautarsa aka bani, ina buƙatar kowannenku ya je nasa ɗakin ya huta zuwa anjima zan yi baƙo, but bana buƙatar ki fito waje Mamu, duk abin da ki ke buƙata zan kawo miki kafin na samo mana ƴar aiki"

Najmeer ta ƙarasa maganar tana hawa sama.


Da kallo suka bita har ta shallewa ganinsu.


Jiki a sanyaye Meera ta matsa gun Mamu tana faɗin "Wai nikam Najmeer mutum ce kuwa?"


A rikice Mamu ta rufewa Meera baki tana mai girgiza mata kai alamun ta yi shuru, hakan ya sa Meera barin zancen ba dan tana so ba.


Sai wajen ƙarfe biyar na yamma ta fito cikin wata arniyar riga daidai cinyarta, kayan sun masifar yi mata kyau musamman yanda shape ɗinta ya bayyana, gashinta ta ɗaure shi yana rito a baya, kunnenta ɗauke da waya da alama magana take, Meera na bayanta ɗauke da basket na kayan motsa baki.


A babban parlour suka shirya kayan cikin tsari da ɗaukar ido, ba jimawa Alhajin ya iso harabar gidan, cike da makirci Najmeer ta fito tana ɗaga masa hannu, ko kunyar Meera da ke wajen be yi ba ya rungumota yana mai manna mata kiss a kumatu "Shalelena wallahi na yi kewarki sosai, yanzu ne na ƙara tabbatar da cewar ke ta musamman ce" Fari da ido Najmeer ta yi sannan ta shafo gefen fuskarsa "Godiya nake my Alhaj, nima kewar ce ta sa na baro Dubai dan kawai na haɗu da kai"

Sosai kalamanta ya yi masa daɗi, sai a lokacin ya lura da Meera da ke kallon ikon Allah, cike da mamaki suka gaisa kafin Najmeer ta masa iso zuwa parlourn.


Meera na gefe tana kallon yanda Najmeer ke zuba makirci da kalaman soyayya kamar daga gareta aka fara sarrafosu.

Sun jima a hakan suna fira, kayan marmarin da drinks ɗin ma kaɗan ya sha.

Wata ƴar bag da ya shigo da ita ya miƙawa Najmeer yana murmushi "Shalelena ga wannan ko? i know you will like it" Itama murmushin ta sakar masa tana buɗe bag ɗin, waya ce ƙirar iphone 15promax sai ɗayar 13promax, ɗayar ledar kuwa agogo ne na gold me masifar tsada irin na ƴaƴan manya.

Cikin farinciki Najmeer ta ƙara ƙanƙame shi, "Thank you so much, kamar ka san ina buƙatar agogo, but wannan be mun ba anjima zamu tafi na zaɓi wanda nake ra'ayi, and ga friend ɗina itama ya kamata a saya mata"

"Ba ki da matsala as you wish, ai ke ɗin kin wuce hakan"


Jin saukowar mutum ne ya sa dukkaninsu kallon gurin, Mamu ce sanye cikin kayan da Najmeer ta bata, atamfa ce me kyau da tsada sai mayafi kalar atamfar, sosai kayan suka yi mata kyau, zaro ido Meera da Najmeer suka yi, dan sai da Najmeer ta hana mata fitowa dan kar ta basu kunya.

Ƙarasowa Mamu ta yi tana washe baki ganin kayan marmari zube kan tire, da sauri Alhajin ya rusuna yana gaisheta, ba tare da Mamu ta amsa masa ba ta ɗauki lemu ɗaya tana zama kusa da Najmeer "Lafiya ƙalau ɗannan ya gidan?"

Alhajin na sunkuyar da kai ya amsa da "Alhamdllh"

Ganin yanda Mamu ke wulla ido gashi tana neman yarfasu ne ya sa Najmeer miƙewa a fusace ta damƙo hannun Mamu tana faɗin "Keeeee rashin kunyar taki ta ƴan aiki har ta kai haka? waye ya ba ki izinin shigowa har parlourna gaban baƙona, kuma ki ka saka mana ƙazamin hannunki cikin abincinsa"


Meera ce ta karɓe zancen da faɗin "Hmmm gaskiya wannan tsohuwar akwai rigima, shiyasa na ce miki ki kawo matashiya wadda zata iya aiki cikin natsuwa amma kin kwaso mana me taɓin hankali"

Daga Alhajin har Mamu kallon su Najmeer suke, musamman Mamu da duk tsoron Allah ya kamata, har ta buɗe baki da niyar magana sai ta ji tamkar an saka mata makulli, duk iya ƙoƙarinta na ganin ta yi magana amma ina, Meera ce ta kama hannunta ta nufi sama da

Please Login or Register in order to submit comment