Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakan
na nufin zanmutu ne, zan canja halina
zanbar duk abinda nakeyi, saboda taraiya
dakai yafi komi muhimmanci agareni,
yakalleni yajuya yatafi, tun daga ranar ni
Ambar na nutsu, nadaina xuwa duk wani
party, hatta shigana na canja, naje kasuwa
nasiyo yadin hijabai nadinka nafara sawa,
nadaina kula kowa, saidai har lokacin fuad
yaki bani fuska, narame ina shirin fita
hayyacina domin soyayya, ibada na dawoyi
sosai ina rokon gafaran Allah sannan ina
neman hankalin fuad, nazauna a barhaq ina
cin abinci watarana, wani yazo yanata
murmushi ambar, na kalleshi na kauda kai,
yayi yayi naki kulashi. Kaina a sunkuye, can
naji mutum yazauna kusa dani yakira mai
bada abinci yayi ordern abinda nayi order,
inajinshi anma tunanina baya gun, hankalina
bai nutsu ba, can yace ambar, gabana yayi
mummunan fadi, muryan fahad dayadda
yake kiran sunana na dago naga shine for
the first time naga yanamun murmushi. Sai
yace kishirya karfe 5 zanxo anjima yaci
abincinss harya gama bance komiba, kodan
murna ne,? Ina xuwa hostel nayi wanka nayi
sallah dama hafsat taje abuja gun wani
saurayinta, nashirya tsaf cikin abaya karfe
biyar yazo yakiran nafita muka zauna a
motarsa yace nalura kin canja sosai ambar,
hakan dakikayi shine mutunci kinga kinjawa
kanki mutunci, ko ina kikaje, anma macen
dabata da kamun kai ba mace bace, nan
yace ambar tun randa nafara sonki naji ina
sonki saidai da aka gayamun halinki naji na
tsaneki, nayi niyyan bazantaba alaka dake
ba anma ganin kincanja saboda ni yasa
nabaki chance, ambar i love u, kuka nayi
sosai, bance komaiba, har muka rabu,
tundaga ranan nida fuad kaman tom nd jerry,
soyyanmu tayi karfi soyayya mai tsabta,
hannuna fuad baitaba rikewa ba, duk
shaawata haka nake dannewa yazo yakawo
nafara azumi hakan ya mugun taimakona,
dlfuad ya taimakamin ina kara ilmin addini,
duk wanda yasanni yasan fuad har gun
momy nakaishi taji dadi saboda tayaba da
hankalinshi, nanfa ma hassada akasamu
abunyi yau akai wa fuad wannan gulman jibi
akai masa, most abunda ya fi burgeni shine
baitaba sauraransu ba, saidai yayi ignoring ,
tuni nasawa raina nasamu mijin aure, a
satin hafsat tadawo nan namata bayani fuad
atake nace oya bani dubu dari na. Tace zata
samun, hankalina a kwance, bansaniba ashe
hafsat ma son fuad take tadade tana
harinnsa bata sameshiba gashi tashi daya
nasameshi abinda ya bata mata rai kenan,
haka muka gama wannan semestern nida
fuad kullum tare cin abinci tare. Karatu tare
komi tare, munason junanmu sosai, saidai
duk lokacin da fuad yaga hafsat baya
sakewa yasha cemun narabu da ita ba kawa
bace karnazo ina dana sani, nakancemasa
itakadai natashi da ita anma zanyi kokari
naga ta. Canja
10anma duk dahaka fuad bayaso, ahaka
muka shiga aji biyu alokacin fuad yagama
yafita da second class upper munyi murna
sosai, nan yafara shirin tafiya service,
mukuma munshiga aji biyu watarana ina
assighnment naga kiranshi nadauka tareda
cewa my dear, yace fito inason ganinki
yadda yayi maganan muryanshi narawa nace
toh, inafita kofan hostel nace dear na meya
faru, yace karki kuskura ki yaudaren,
macuciya azzaluma, marar imani ashe haka
kike nayi danasanin saninki, nayi danasanin
haduwa dake. Hankalina yatashi sosai nace
fuad menayi yaja tsaki yace ashe
soyayyanmu akan bet kikeyi? Akan dubu dari
ambar kika karbi soyayyata? Allah ya isa
tsakanina dake, nace fuad bahaka bane wlh
tlh fuad bahaka bane, yace ki amsamin yes
or no, na sunkuyar da kai sannan nace yes,
ya buga motan dakarfi how could u ambar?
Y? Ya shiga cikin motansa sannan yace kisa
aranki baki taba sanin waye fuad ba,
tsakanina dake yakare, yaja motansa yatafi
kuka nafarayi nadauki wayata nakira hafsat
tace tana daki dasauri naje raina abace nace
akanme zaki fada wa fuad? Tace luk hafsat
rayuwace, kowacce mace da basirarta,
kinmanta kema duk macen dakika ga
saurayinta kwacewa kikeyi? Yes naga fuad i
love him, kuma naga yanasonki so i have to
separate the two of u before na iya shiga
ransa, na rikota nahadata da bango hafsat i
hate u, nayi regretn saninki , saninki
baijawomin komi ba sai bakin ciki, nan fa
muka fara fada dakyar aka rabamu na
tattara kayana nadawo gyda, nan momy
hankalinta yatashi dana gayamata meya faru
momy shiru tayi tace kiyi hkr, kicireshi kema,
nace mony fuad nacikin bacin raine anma
inya huce zanbashi hkr tace tohm, anma
me???, sati daya nagagara cin abinci fuad
baya picking calls dina z nima nadaina zuwa
lectures koyaushe ina nemanshi ranan muka
hadu akofan barhaq ina bashi hkr haka fuad
yakallen gashi akwai mutane haka nasauke
girman kai, yadauki ruwan gora ya watsamin
tareda cewa ambar in mafarki kikeyi kifarka
nace bansanki ba i hate u, ko ke mayyace?
Nayi kuka sosai har cikin raina, bantashi
shiga tashin hankali ba saidanaga hafsat da
fuad a mota suna dariya cikin kwanciyan
hankali, innalilahi wainna ilaihi rajiun sanda
ne agefena na karfe nadauka ina xuwa jikin
motan nabude najawo hafsat na kwala mata
ko ta ina ajikinta fuad dakarfi ya fizgeni for
the first time arayuwata da fuad yarikeni, ya
wankamin mari tareda cewa ambar bana
sonki bana sonki bana kaunar ganinki kifita
acikin rayuwata dolene? Kuka nakeyi sosai
ga mutane suncikaa ina kuka sosai, har suka
tafi, yakai hafsat clinic, nayi ciwon SO, maza
mayaudara ne, maci amana, basuda
alkawari, duk sacrifice dazaki musu idan
halinsu ya motsa saisunyi abunda ransu
yabasu, idan zaki bawa namiji hakorinki na
karshe anma namiji zaiyi using wannan
hakorin yayi dariya wa wata, zaki iya
mutuwa akan namiji anma namiji zai je
dawata janaizarki, tuni nafita hayyacina,
nafara sumbatu domin kuwa son fuad yamin
kololuwan illa, of all girls inrasa
meyaudarata sai hafsat? Sumbatu nake,
bana hayyacina, tuni nakoma ruuwa
tsundum, wannan karon harda shaye shaye
nafara
rayuwata ta kara shiga garari, randa
naga bazan iyaba kawai na wuce club
daredare anan nahadu dawani banma san
sunanshi ba don alokacin nafara ganinshi
yalura ina cikin damuwa tuni yabani kwalban
giya yace nasha kadan, aikuwa dana kafa
kai saida nasha yafi rabi, yayi dariya yace
daga yanzu bazaki kara jin damuwa ba, tuni
na fita hayyacina nan nafara surutai ba buge
buge. Yadaukeni yakaini hotel, dama sanadin
fuad nashiryu nadena kula maza donhaka
atake nazubar da randan shaawan dake
damuna, mun mori juna duk abuge,
washegari dasafe ganina nayi nikadai a hotel
tuni nasa kayata nadauki wayata nayi gida,
momy hankalinta yatashi anan na mata
karyan ai na kwana a makaranta saboda
wani assighnmemt nan tamin fadan aidana
fada mata sannan duk lokacin da zankwana
nagayamata, nan nacigaba da xuwa party na
aboye, ina shaye shaye na, idan nayi high
sai dai na tsinceni a hotel, gaba daya
kwanyata ta toshe nadena karatu hatta
exams banyi cikakke ba, muna hutu wata
rana natashi da amai, sosai hakan yasamin
zazzabi nanfa hsnkalin momy yatashi tace
ko malaria ne, anan mukaje asibiti test din
farko likitan yace inada ciki, tunda momy ta
haifen bantaba shiga tashin hankali irin
wannan ba, momy atake tazubar da wayoyin
hannunta, tace likita zamu dawo , tasani
agaba mukaje gyda, momy tana kuka amina
na kuka, momy nacewa yanzu ambar
tarbiyan dana baki kenan? Haba ambar!
Yaza ki samin zargin cewa ban baki tarbiya
mai kyau ba, innalilah. Tadauki waya takira
daddy tace kayi kazo gyda duk garin dakake,
tarufeni adaki nikuwa sai kuka, danasani fal
a fuskata, nan na fara tunanin wacce irin
rayuwa nadauka ma kaina, washegari daddy
yadawo har lokacin bawanda yaci abinci
acikinmu, tamishi bayani a harzuke daddy
yacire belt yashigo dakina yarinka naushina,
duka kam nasha har takeni daddy yayi
tsantsan duka, yanacewa shiba irin tarbiyan
dayabanba kenan, infita inbarmoshi gida
karna spoiling masa image a matsayinsa na
babban mutum sannan dan siyasa, nan
momy takafe cewa laifin dady ne inba kana
zaune agyda ba tayaya zaka dauramin
tarbiyan yara mata ahannuna nikadai,
inbanda aikinka baka da lokacin kowa, gashi
yarka ta kwaso maka rabonka, nanfa fada
yakoma kan momy, daddy yace ya
gwammaci ace masa na mutu akan acemasa
na yi ciki, habawa sai duka yarufeni yace
kasheni zaiyi, tabbas nasan zai iya daddy
nada mummunan zuciya donhaka tuni naroki
momy ta taimakamin tadauko atm da purse
kudine aciki tace gashi ambar kibar garinnan
ki tafi gombe akwai kudi aciki kiyi settling
zanzo nasameki , tabudemin kofa ina kuka
nafice motan gombe nashiga tunani nakeyi
sosai don Allah yagani nayi dana sanin
abunda na aikata
Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 15
3 days ago
Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 14
6 days ago
Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 13
1 week ago
Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 15
3 days ago
Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 14
6 days ago
Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 13
1 week ago
Share this on WhatsApp
Share this on WhatsApp
muna isa gombe bansaniba saida ta
gefena ta tabani sannan ta sanar mun ,
nafito jiki a kasale, na hau kekenapep nace
malam kataimaka kakaini inda zansamu
hotel, aikuwa yakaini wata hotel yar daidai
nakama daki na sati nashiga ciki da falo,
kwantawa adakin nayi nafara kuka sosai,
nayi nadama sosai, tunanin momy da daddy
nake, bayan gydan nashiga domin na yi
wanka, nashiga bathtub din fad na sulale
nafadi, na bugu sosai sannan namuke nafito
jini ke zuba ajikina nan nakira hostel service
din tuni suka kaini asibiti bansan adadin
kwana nawa nayiba nidai nabude naga
momy agefena, zanyi magana tahanani, nan
take cemun ai cikin ya zube, a hotel din
sunrasa wazasu nema nawa, saisuka dauki
wayata suka kirata, tace alhmdlh da cikin
yafita yanzu kinga daddynki zai hakura
kizauna, Allah yagani haushin dadyna nakeji
duk shiyajawomin bayada lokacinmu, harda
laifina nabin kawayen banza dasunan
wayewa akarshe wa wa gari ya waya?
Nagama asara , ba budurci ga ciki ga shaye
shaye ga hulda da maza. Subhannalah, kuka
nayi sosai koda aka sallamen nadawo gyda
dakyar daddy yabarni nazauna, nanfa naciga
da rayuwa a takure, anan nakejin lbrn ai
hafsat sunrabu da fuad,anma bawanda
yasan dalili, gashi anma result gp na ya
balain saukowa har 1point ga courses
danake carryn, naji haushi tuni nasiya sabon
littafin canja rayuwa, nadawo mumina, ba
ruwana azubi mon nd thurs, ga hijabi da
liqab, ga zuwa islamiya rayuwata nadawo
ina takurata ahaka nasamu nacigaba da
karatuna, wasa wasa bana da saurati
tsayayye guda daya na arziki wanda zanfitar
a matsayin miji, duk samarin danake ganin
sunmin over yanzu lokaci yakai da bana
ganinsu , magidantan ma insunxo jikina
sukeso daga baya nadawo nukadai kaman
mayya dox moments are the worst moment
of life, momy tace i should learn a simple
lesson from dat duk wacce batayi usn
ooppotunitynta ba tym will come da
zaiwucemiki nd u shall regret it, aikuwa
nagani don wasa wasa gashu har nayi grads
babu mijin aure. Gashi inason auren, anma
me,??
samarin duk sun gudu, bana ganin
kewar kowa, tunda na kama kaina, harnake
cewa tph kowani namiji dan iska ne, wasa
wasa harnagama atbu nayi 6yrs dakyar
nafita da second class lower, nan nazo
inajiran inyi service duk dahaka shiru,
watarana nafito daga sallooon zanyi gyda
kawai abun mamaki naga taslim a
makwabta yaje hira, na kare masa kallo
tabbas yakara girma gashi yayi kyau , ga
kwarjini yayi fresh na kalleshi saina tunafa
ashe shine yafaramin illa a rayuwata, gashi
yazauna da wata a mota hankalinsa kwance
sai hirarsa yake nazo na wucesu, anma
ranan ban iya bacci ba, taslim is my first
love dole sonshi tadawo min danye araina,
nanfa nalura yarinyan dayake xuwa gunta
fauxa ss2 take lalle namiji dan iska ne,
yagama lalata yanmata anma sai kuga
yanabin kananun yara dasunan aure, aikuwa
tuni haukata ta motsa nace idan ban
aureshiba toh kuwa bawacce zata aureshi,
nasa aka nemomin nukbansa nakirasa yayi
mamaki kwarai tareda cewa yazata nayi
aure nace masa aina zanyi aure munyi
alkawari dakai, yayi murmushi yace bakida
mantuwa ambar ai lokacin yarinta ne, dakin
yi aurenki dont bother abt me, nace but i do,
so is beta kasan nayi don naga kwana biyu
inda kake xuwa yu bets change plans or yull
c a big problem, yayi shiru can yakashe ina
zaune naga txt dinshi gashi akofar gydanmu
nafita nasameshi yakalleni yace ambar nazo
mu fahimci juna, ambar u r my age mate,
aurenmu bazaiyi yiwuba kuma ni tuni na
manta dake. Nayi darriya nace dole kamanta
dani tunda ka kwanta ka ketamin budurcina,
yaja tsaki toh ai kinga matsalar ku kenan na
hausawa mace don kayi havn sex da ita
saitace aurenka zatayi, ke kintsba ganin anyi
haka,? Na kwanta dake na aureki? No i need
a fresh blood, kinmun tsufa, kuma am quite
sure badani kadai kikayi ba, beta find away,
before nazama ciwon kai, yaja motarsa
yatafi nayi kuka sosai nayi dana sani, duk
dadin bakinsa ina yake? Namiji zaimiki dadin
bakine idan yanada bukata duk lokacin
dakika kuskura kika bayar toh daga ranan
dake da slippers darajanku daya, zaki iya
zama da namiji yana binki akan kibashi
kanki for years kiyi tunanin sonkine, anma
inaaa duk randa kika kuskura toh wlh zai
rabu dake, idan bai rabu dake alokacinba toh
kinzama masa sex machine don zai bukaceki
ko yaushe sannan maganan aure na tasowa
shikenan zakiga ya ware, toh waini meya
kaini tun farko? Na farko bin kawar banza,
na biyu rashin rikon addini, don nasan ko
salloli nake tsayarwa da kyau bazai barni na
aikata zinaba, duk mai zunubi mai aikatawa
ya binciki addininsa, ga dai tarbiyan iyaye
alhmdulilah sunyi kokari, kuka nake sosai
bantashi fuskantan tashin hankali ba sai da
aka cemin aminanmu zatayi aure, wayyoni
kanwata ta kama kanta gashi miji yazo mata
tun tana ss2 yafi mata, nifa ? Yatawa
rayuwar take?
nanfa mukayi bikin amina muka gama
tasha gata kam, nanfa nafara jin surutai
danginmu anfara maganan meyasa bazanyi
aureba, nanfa momy hankalinta yatashi dady
kuwa cewa yayi yaban sati biyu idan ban fito
da miji ba toh zai badani, ban damuba
gwara ma yayi hakan saboda ayanzu da
banda tsayayyen nab gwara hakan, aikuwa
daddy yabadani wa dan abokinsa aliyu
haidar, ali baitaba aureba anma shekaransa
34 nanfa ba shiri aka fara hidiman biki ko
bari baayi munsaba ba, shimadai ba yabo ba
fallasa, tun randa daddy yace nafito da miji
ko yasamamin nafara dilka da gyran jiki,
akalla na kashe sama da dubu dari duk dan
na suke kar ali yagane, idan muna waya
yakance ina burgesa yaga nagama jamia
anma ba ruwana kaina akame, shiru nakeyi
don dayasan past dina daba haka ba, nayi
gyran jiki sosai na kimtsu, atunanina duk
bazai ganeba tunda na suke, abinda
bansaniba ko ince mata dayawa basu saniba
shine wannan gyran da akeyi its not natural,
cusa wancan kimtsa wancan no matter how
pure it is, mace tana zuwa da niimanta tun
haihuwa, donhaka idan tabari yatafi
samunsa bamai wahala bane anma kowa
yafison original, nadauka budurci baida wani
muhimminci tunda nayi gyran jiki, anma
budurci fata ce ajikin mace, idan yafita babu
mahaulakin dazai iya sama miki wani, don
haka magani ko gyran jiki bazai kwace ya
mace ba, saidai yarufe hanya!, ahaka mukayi
biki banda wasu kawaye sosai saboda duk
sunyi aure nanfa daddy yazubamin kaya na
tare agydan mijina aliyu, darenne yakamata
ace tazama tafarkona toh anma bahakanba,
washegari ali yadda yake ba yabo ba fallasa
donhaka saina fara tunanin ko bai ganeba
harda adduoina, muna zaune lfy da ali ina
service dina yana aiki, saidai abunda ban
gane ba shine duk lokacin da ali yakiran yajii
inagun service sai yace na bawa kawata
daya mugaysa , baidamenba tunda idan suka
karbama cewa yske su lura dani, sannan duk
lokacin danace zanfita idan kasuwa nace
zanje zaikaini yajirani nagama mudawo hatta
wani hidiman dangi yana makale nikuma
sainaga rashin dacewar hakan, donhaka
naxaunar dashi nace karya damu zanna
zuwa ko ina, yanuna rashin amincewarsa
anma na dage sai yabarni, watarana muna
office dinmu yakamata ace naga officerna
don yamin sighning wasu papers, anma
mutumin baizoba akace sai bayar na
yamma, don haka naxauna muka jirashi
haryazo alokacin na nemi abun hawa narasa,
sai nadauko wayata don nakira ali anma
naga ba caji, hankalina yatashi sosai ga
magrib tayi, wasu yan batch dinmune zasuyi
gyda kasancewar suna girmamani a
matsayita ta matar aure sukace bari su
saukeni nayi niyyan naki amincewa saidai
ganin dare zaimin a gun gashi bakowa yasa
nashiga yana ajiyeni a kofar gyda nabude
gydan nashiga ali nazaune rike da cup din
coke batare da na lura da yanayinsa ba nace
dear yau na wahala da kyar nasamu mai
kawoni bansamu abun hawa ba, yaja tsaki
wacce ta sa najuyo idonsa jajur cikin tashin
hankali nace meya faru dear? Ransa abace
yace kimin shiru munafuka, azzaluma
mayaudariya, iskancin dakikayi awaje bai
isheki ba yanzu kin yi aure bazaki dainaba?
Aini naji mamaki ashe cutana zaayi aka
daukeki akabani, wacce tagama saida
mutuncinta wa samari awaje, yanzu wani
yakawoki a mota anma zakicemin wai aiki,
yanzunnan nadawo agun meyasa ban
samekiba, wlh nayi nadaman aurenki , meye
amfanin auren karuwa???
idona cike take da hawaye, nace bahaka
bane sir, kirifamin baki jahilar banza, kuka
nake sosai anma bai kulani ba, tunda ga
ranan zaman dadi ta karemin agydan ali,
bayacin abincina, baya dawowa gyda sai
tsakar dare sannan idan yafara zagina har
kakkanina saiyazaga, na zauna zaman
hakuri harna gaji daganan na yanke
shawaran nanemi takardata, saidai nace
barin kira momy naji, ina kuka nake mata
bayani tace nanemi izini nazo , dana
tambayeshima cewa yayi adawo daga
karuwanci lfy, nadai kimtsa da kyar nafita
ina xuwa gyda na tarar amina ma tazo, tayi
bul abunta ga ciki ajikinta sainaji hawaye
nazubomin nace amina hankalinki a kwance
ko? Tace adda ambar kinyi kuskure tun
farko dakika dau wannan rayuwar, ganinan
dai duk kawayena suna cemin ban wayeba,
anma meye rashin wayewan dasuke nufi?
Rashin harka da maza, zuwa party
dasauransu na yadda, saboda a tunanina
shine asalin jahilci. Meye wayewa kina harka
da maza? Kowani namiji yarainaki? Yasan
hawanki yasan saukanki? Ina wayewa aciki
kowani namiji yasan bangare najikinki? Ina
wayewa aciki namiji yataba jikinki wanima
gobe yaxo yataba? Wannan shine jahilci. , ki
kama kanki kizama mace on ur own, be d
boss of ur own life, karki kuskura wani
namiji yaga saukanki, neva b a victim, do not
cry for a guy, it would be used against you,
karki bari namiji yaga downfall dinki,
donkinason namiji bashine zaiza yayi dake
kaman akuya ba, yayi ruling dinki kaman
bakida yanci. Balle harki biye mishi waidon
kiyi ladabi da biyayya,
inata kuka amina na bayaninta nayi
nadama sosai inata kuka momy ma kuka
take, tacemun kiyi hakuri bakomi, yanzu ki
koma da ubangijinki kawai anma maganan
ali yasakeki adda baitasoba, kizauna kiyi
hakuri laifin da kika shuka kike girbawa, ba
kedai ba, kowacce mace me irin halinki dole
ta fuskanci tashin hankali a rayuwanta,
baaayiwa Allah wayo, nayi kuka sosai,
momy da amina suka bani shawaran
nazauna a gydan ali duk hakurin aure ake,
kowani aure dakika gani hakuri akeyi, momy
nafada tana kuka tace daddynku duk da
baku taba ganin tashin hankalinmuba
bakusan me nake cikiba, anma nayi hkr
nazauna shiyasa kuka tsinceni haryau,
dadynku baya zama siyasansa yafi masa mu,
momy na kuka tana bamu tarihinta da daddy
yadda tasha wahala sosai, gashi dan siyasa
yanmata suka tsaya mata agaba, dasunan
partners, nanma amina tadaura dacewa ko
hafsat dakike fada kinji lbrnta? Nace a a,
tace toh hafsat haryau batayi aureba, last a
makwabta nakejin labari tabi mijin
makwabciyata kuma kanjamau take dashi,
hauka ne yafara damunta domin kuwa shaye
shaye yamata yawa, ambar ki gode Allah kin
nutsy rayuwanki tacanja so use ur time kiyi
hakuri kizauna har Allah yadawo miki da
hankalinshi, haka na hakura nakoma
nacigaba da zaman gydan ali, abu sai gaba
yake har nazo nafara lura ali neman aure
yake, tunda nake bantaba shiga tashin
hankali da tsanan kaina ba da nadama sosai
akan abubuwan danayi abaya sosai,
haka inaji ina gani abdul ko fadan
kishiya bai kawomin ba, momy ce tazauna
tahadamin kaya akwati set hudu, sannan
tacanjamin kayan daki, ranan mungama gyra
daki nida amina nace amina nifa tunda muka
fara rikicinnan baya saurarona gashi zai kara
aure nasan gatana takare, amina tsyi dariya
tace bai kareba yaruwa auren shine kadai
hanya kisa musu ido karki tanka musu.
Sannan ki gyra jikinki sosai idan momy zasu
tafi london kice tasiyo miki kananun english
wears, sannan ga littafin girki na kawomiki.
Adda mikewa tsaye zakiyi ba boka ba
malam, mijinki nasonki donhaka ki kokarta
duk abinda zai jawo zargi a tsakaninku ki
kawar, nace amina toh mufara da gyran jikin
naji wata a gydan biki kwanaki tana cewa
akwai hadin dawo da budurci, amina tayi
dariya tace adda babu, duk duniya babu
mahaulakin dazaice miki maganan gyran
mata zai dawo miki da budurci karyane ko
shi wayene, sannan idan mai siyarwa ne toh
sunfadane don kawai kisiya kayansu,
maganin gyra saidai ya tsukeki, don budurci
kam karyane don budurci fata ne ajikinki,
saidai maganin gyra yamiki maintainin
jikinki, toh idan yana dawowa da budurci
nawa kika kashe da amarcinki? Almost
200,000 anma meyasa budurcin baidawo ba
har ali yagane? Sannan bakowani maganin
gyra zaki dauka ki cusa ajikinki ba, ki
tabbatar da asalinsa, donhaka dakanki ma
zaki iya gyra jikinki, kisiya miski, gabaruwa,
ganyen magarya da lalle, saiki dage da shan
fruits musamman kankana, wadannan kadai
inkin rike ba ruwanki da asaran kudin gyran
jiki, domin specified ne daga matan zamanin
annabi, ga girki karki kuskura ki maimaita
abinci a sati. Kaya kuwa sai inda karfinki
yakare, habawa nan fa muka dukufa, amina
ta tafasa ruwan ganyen magarya da
gabaruwa tasa nashiga ciki na zauna tace
nayi na sati, ga shafa miski idan nafito,
saikuma shan kankana, sai inyi blendn dinshi
da dabino da mazar kwaila insa madara
insha, tamin hadin mayukan jiki tuni nayi bul,
nayi shirin amarya, ga dinkuna na agun tela,
satin biki sukayi abinsu nima ba yabo ba
fallasa, nadan sake, anma abun cin fuskan
shine nida ali watanmu sha daya anma
harya kara aure, aka kawo amarya tana site
dinta, daredare ali yakiran yazaunar damu
dukka biyu yayi waazi sannan suka wuce
daki, ranan kasa bacci nayi, kwana nayi ina
sallah saidai asuba ne bacci yadan
kwasheni, karfe bakwai naci kwaliyya taf
shaar dani nafito nashirya kumalo, na ajiye
musu nakoma daki ali da amaryarshi basu
fito ba sai karfe goma, anan suka karya
nafito na gaysheshi ya amsa sai wale baki
yake, itakuwa saiwani fici fici take da ido,
nan nakare mata kallo tas, shikuwa kaman
munafiki, ina zuwa daki nazauna lallecin
fuska yarasa wacce zai dauko min sai riri?
Wacce mukayi secondry da ita? Wannan yar
iskan yarinyan? Toh ai angudu baa tsira ba,
munafuka jiya tana ganina ashe shiyasa
dayake waazi tarufe fuska cikin gyale
maima zaiyi da ita? Kyau dai da komi
ba abunda banfitaba, naja tsaki na cigaba da
goge daki, haka har sukayi sati, ninake girki
bai damenba, randa zan karba ba kunya tayi
sallama tazo dakina bayan mungaysa wai
ambar nazo rokan alfarma ne, don Allah
kitaimaka ki sayar min da kwananki, nayi
dariya nace kiyi hkr, nima ina bukatar mijina,
haka tamike tafice, dayadawo ma yana
kwance a falo ina daki, hakadai harya fita
dama kwana bibbiyune, , ganin haka yasa
nazauna nayi tunani barikinta takeyi a gyda
yadda taga dama, idan suka fara wasu
surutai tashi nake nabar musu gu donhaka
na yanke shawaran nima zasu ga nawa
fannin lokacin momy tadawo tasiyomin wasu
arnan english wears. Na jerasu a wardrope,
nan nayi shirin aiki, da sassafe sainayi
wanka naci kananun kaya, wataran mini
skirt da top, wataran wando gajere wataran
bomshot inci kwaliyya inyi paking gashina
infeshe jikina da turaruka, munacin abinci ina
daddana wayana ina ci cikin kissa ina
lumshe idona, takasan ido ina hankalce dashi
sai hadiyan yawu yake, ya kallen yajuya,
dazatan nagama innatashi tafiya nanfa
zanzage na juya jikina sosai, ga kananun
kayannan sunzauna, inje kicin ingama abuna,
inje falo, ko yazo yazauna sai insa ear piece
a kunneta ina jin radio, anma duk ina
hankalce dashi, riri kuwa haushi takeji sosai
saboda bayadda ta iya dani jikinta nanan
kaman na maza kotasa kayan bazatayi
kyauba sannan batada gashin yin yanda
nake, kwata kwata bata da kyau da
charisman dazata hada kai dani donhaka
nayita rayuwata ina sane dasu anma daga
ita harshi sasu nake a kwandon shara,
musamman shi naga yanzu yafara sake
fuska, inyaggani wataran da wani adon sake
baki yake , gashi riri ta rasa aina nake siyo
kaya haka takarbi kudi agunshi tasiyo
enfmglish wears ina kallonta tafara sawa
dariya ma taban. Nanfa nacigaba dabasu
assighnment, tuni ali yadawo saiti yafara
gwadamin maitarsa anma inaaaa ambar
jaaa ajikinki, abinda zuciyata kefadamin
kenan yadda ya wulakantani gwara nadan
jamasa rai duk da cewa nasan m payn for
my misteks, kuma inason kasancewa ds
mijina anma dole nayi hakuri
kullum kwaliyan daban nake, nakoyi
kuskurena, nayi nadama kuma kullum ina
kara nadama, fatana Allah ya gafarceni
abinda na aikata, na lura da son da ali
yakemin,hmnn danma ban kaimishi
budurcina ba, da ace nakai mutuncina da
kimana zaifi haka yawa, bazai taba zargi
naba, kullum acikin koyan sabon salon girki
nakeyi, zanbashi yaci yakoshi, idan kwanana
ne na gyra mishi daki na feshe da turare
sannan na wanke mishi toilet bana bari mai
aiki tayimin wannan, sai akwanan riri ne mai
aiki ke masa hidima, donhaka sainayi usn
wannan advantage din, nadawo da tunanin
mijina kaina, ran jumaa itace ranar da nayi
niyyan mushirya mu daidaita, aikuwa godiya
kan godiya da alkawuruka kala kala, nasan
adduoi danakeyi ne yasa Allahna yaji
tausayina, ahaka nadaidaita da ali komi
normal, ina tarairayan kayana kaman jariri,
ahaka nasamu ciki riri ma haka , nan muka
cigaba da rainon yaran cikinmu duk wani
bita da kulli da riri ke hadamun bana kulata,
hakan yasa fada baya hadamu, cacar baki
ma sai naga dama nake kulata, ahaka
wataran naje biki makwabciyata ammata
kishiya, nayi mamaki sarai danaga hafsat
agun bikin itace kawar amaryar, ta lalace
duk jikinta yasake, gashi tana abu kamar
marar saiti, ba cikaken hankali kuma
haryanzu ba mijin aure ga makarantan
tagama anma miji shiru, yanzu ko
samarinma zaurawan tadena gani, rokona
tayi tayi gafara acewarta ita tayi sanadin
rabani da fuad, anma fuad nasona, nayi
dariya nace dama can ba mijina bane, kinga
mijina muna zaman lfy, taban hkr nan
nabata shawara nace tayi nadama ta gyra
rayuwanta ko Allah zaijikanta inyaso ko da
magidanci ne tasamu, tacemin akwai wani
matansa biyu yana sonta anma ita tana
tsoron wulakancinsa
nayi dariya sosai sannan nace ai
rayuwar dakika dauko dolene namiji ya
wulakantaki shanyewa zakiyi kiyi hakuri
kijure, tace bakomi, bayan natafi satin na
haihu nasamu na mace, nasa mata suna
amina, riri ma ta haihu na mace, tasa mata
bilki,nan muka samu dakyar muke dan hada
kai, duk da mukan samu sabani wani lokacin
anma ba wannan bane damuwata, babban
damuwana shine mijina yasoni kuma ya kula
dani, alhamdulilah bayan gyran kuskure na
danayi, nasamu hankalin maigida na, fuad
ina ganin sanarwan bikinsa wata ustaziyan
mace yanemo ance tana da hankali banyi
mamaki ba tunda dama shidin haka yake,
wanda yafiban mamaki shine taslim yar
sarkin malamai ya aura ance yarinyan akwai
zubyn hadda, naji mamaki kwarai, namiji ba
abun yadda ba, su zasu zauna su bata miki
rayuwa anma insungama suje sunemo
ustaziya, ya ishi mata ishara duk wacce
namiji ke binki don jikinki ya ke yaruwa
kisani yana samun abunsa zaiyi gaba bazai
aureki ba, zainemo yar mutunci da kamala,
shawara ta rage name shiga rijiya, anan
nakawo karshen labarin budurcina yancina,
(don Allah wannan labarin hadawa ko ince
kirkira nayi it has nothing to do da rayuwan
wani, but if plx yazo mistakenly daya da
rayuwar wata, am sorry, don anfara bina
privately ana min wasu illegal tambayoyi,and
please masu copy and paste, idan zaku tura
kuna cire numbana don Allah, ana yawan
adyn dina tahaka) muhadu a labarina na
gaba wato A SANADIN HAKURI

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment