Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

           Suma su Saif na kammala break fast 'din sai suka hanzarta 'karasa shirin su suka wuce makaranta.

   Koda Alhaji Baba ya dawo bai same su agida ba da yake sai kusan 'karfe tara ya dawo gidan so a lokaci, sun da'de ma a makaranta.
         

      A harabar gida ya ha'du da Mu'een sai suka dawo ciki tare suna 'dan ta6a hira.

       Anan Alhaji Baba ke fa'din " ai da har zan tashe ka muje ta'aziyar tare amma danaga kamar baccin gajiya kake yi kawai shiyasa na barka nai tafiya ta".

Mu'een kam cikin ransa yace " ai gara hakan ma".
Afili kuwa murmushi yayiwa Alhajin sannan yace " Ai kuwa gara ma da baka tashe nin ba...mafarki nake yi ina gaban ka'abah, daka tashe ni da har sai nayi kuka".

" Lalle yau ka kai babbar ziyara".
Fa'din Alhaji Baba yana dariya.
Mu'een sai yace " wallahi kuwa, dan ma naji haushi hannu na bai 'karasa ta6awa ba na farka".

" Allah ya sa mu dace to".

" Amin Amin"
Ya amsawa Alhajin da shi.
Haka suka cigaba da 'dan hira har lokacin da Ammi ta gabatar masa da abin karin sa, batare da 6ata lokaci ba ya karya sannan yayi shirin tafiya gidan gonar sa.
Har ya kama hanya zai fita sai kuma ya juyo ga Mu'een yace da shi" ko zamu tafi tare ne, naga gidan shiru kar kuma ka gaji da zama kai ka'dai 'din babu da'di".

" ah ah Alhaji...ni kam ba yau ba sai dai gobe in Allah ya kaimu".

" to shikenan Allah ya nuna mana goben ni kam na wuce".
Fa'din Alhaji Baba tare da juyawa ya fara tafiya
" Allah ya bada sa'a " Ammi tace yayin da Mu'een yace da shi " adawo lafiya".

Ko bayan fitar Alhaji Baban ma bai bar parlourn ba zama yayi suka cigaba da hirar su da Ammi.
   Ya kanji farin ciki sosai a duk lokacin da yaga yanda rayuwar ahalin sa ya kasance a yanzun gaskiya sai dai Alhamdulillah kawai za'ace, domin bai ga alamun suna tare da damuwar komai ba...gashi Allah ya 'kara bu'da musu gidan gona sai ha66aka takeyi.

   Shima 'din ya kanji farin ciki ta 6angaren sa marar misaltuwa, domin kuwa har mantawa yake da damuwar dake cikin ransa.
  
    
Kwanan sa 'daya ne tak amma Alhamdulillah cuz bai samu lokaci ya zauna dan tunani kan abinda ke damun sa abaya ba, hakan kuwa yayi masa da'di sosai, shiyasa 'karfi da yaji yake 'ko'karin maida kansa surutacce na dole ba wai dan hakan ra'ayin sa bane, face dan kawai ya ringa 'dauke hankalin zuciyar sa daga damuwar data ke 'kunshe da shi.
     Wannan kenan.



*****
     " Ummah kinga Hudah ta'ki tayi da sauri ko?"
Cewar Nanne dake ta faman ha'de fuska tamkar zatayi kuka.

" me ya faru ne Nanne me Hudahn tayi miki?"
Ummah ta tambaye ta tana mai tattaro dukkan hankalin ta gareta.
Nanne sai tace
" Tun 'dazu fa nake ta cewa tayi sauri tayi wanka ta shirya amma ta 'ki kuma fa tun 'dazu akayi azahar har an kusa yin la'asar ma,malamin mu kuma bulala zai mana idan mukayi latti".

Kafin Ummah tayi magana sai nayi saurin le'kowa nace " Nifa Ummah yau bazani ba gaskiya, tayi tafiyar ta kawai".
Ummah 6angaren da nake ta maida idanun ta sannan tace dani " me yasa bazaki ba Hudah ba fa na san shiririta ni"
Ummah tayi maganar da 'dan masifa harda da nuno ni da yatsa.

Ni kuwa baki na na  turo gaba sannan nayi komawa ta ciki batare da na 'kara fa'din komai ba.

Daga wajen Ummah ta sassauta murya gami da fa'din " kinga uwata yi tafiyar ki, wannan ja'irar ba zuwa zatayi ba nasani tunda har ta fadi da bakinta kuma ma ai kinga bata shirya ba har yanzu...tafi abinki Allah ya bada sa'a, banda wasan banza kinj uwata?"

Ina daga cikin daki na ta6e baki na gefe da jin lalla6an da Ummah ke yiwa Nanneh da ko ni da nake auta ma bana samun hakan.
" to Ummah "
Nanne ta fa'di gami da ficewa daga gidan, Ummah ma bata 'kara bi ta kaina ba ta cigaba da abinda take yi.
Yayin da nayi kwanciya ta cikin 'daki har bacci yayi awon gaba dani, haka kawai yau na tsinci kaina da rashin son zuwa islamiyar duk kuwa da cewa ba 'karamin son makaranta ce da ni ba amma yau sai naji bana son zuwa.
         A kullum ina riga ta shirin zuwa islmiyar, na safe ne ka'dai take rigani shiryawa kasancewar ita bata yin aikin komai da safen illah tayi sallah taci abinci sai saka uniform.....shiyasa lokuta da dama ma tafiyar bata dai-dai ta kusan kullum sai ta riga ni tafiya makarantar.


〰〰〰
          Tafe take a hankali kamar yanda ta saba, tana rungume da takaddun ta a 'kirjin ta.....dai-dai kan layin gidan Alhaji Baba take a lokacin  sai dai bata riga ta iso kusa da gidan ba.

Yana tsaye a 'kofar gidan yana amsa waya, yayin da ya kwantar da hannun sa jikin 'karafunan bubler 'din dake daga wajen gidan nasu.

     Tun daga nesa  yake hango ta, kunnuwan sa na kan sauraran wayar amma idanun sa da hankalin sa gaba 'daya yana kanta,  yanayin yanda take tafiya kawai ne ya birge shi, yana matu'kar son mutum mai natsuwa a rayuwar sa musamman ma mace, bai fiya son mace mai hayaniya sosai ba.

     Koda ya gama wayar kuwa tattaro dukkan natsuwae sa yayi ya mayar kanta tashin farko kawai yaji yarinyar ta birge shi jiki da zuciyar sa, bai ta6a jin irin hakan farat 'daya game da mace ba sau 'din, yarinyace 'karama mai cike da natsuwa da haiba.... da kansa ya 'kiyasta shekarun ta a ransa, gani yayi kamar bazata wuce 14-15 yrs ba.
   Cigaba yayi da kallon ta yana sake yabawa da kyau da tsarin ta  har 'kaguwa yayi ta iso kusa da shi dan ya ganta da kyau da idanun sa.

  Baifi taku ashirin ya rage tazo ta gifta shi ba kawai wata dake can bayan ta itama sanye da kaya irin nata ta 'kwalla 'kiran sunan ta, ga dukkan alamu makaranta 'daya zasu je.

Juyawa tayi batare da ta amsa ba dan ganin mai 'kiran nata.
   'Bangaren sa kuwa hakan da tayin sai ya sake birge shi har zuciyar sa, sunan da yaji an 'kirata da shi ya cigaba da maimaitawa cikin ransa yana sake binta da idanu..ya maimaita _Nanne_ ya kai sau uku, bai san ma'anar sunan ba amma a hakan yaji sunan ya mai da'di.

" d'an jirani mu tafi dan Allah".
   Wacce ta 'kira tan ta sake fa'di tare da 'kara saurin tafiyar da takeyi dan tayi saurin cimmata.

Bata ce komai ba har 'dayar ta 'karaso kusa da ita suka fara tafiyar tare a hankali tamkar basu don yin tafiyar....'mita Nanne ta fara yi mata k'asa-'kasa da fa'din " Ke dan Allah kullum sai ki rin'ka 'kiran sunan mutun da ihu Allah..nifa bana so".
   " yi ha'kuri to na daina yanzun ma ai naga kin min nisa ne shiyasa...ina Hudah kuma yau 'din na ganki ke ka'dai?".

  Duk baiji wannan hirar da sukayi ba illah amsar da ta bayar na cewa " Hudah ta'ki zuwa cewa tayi wai bazata je ba yau 'din".
Wannan 'din ma yaji ne kasancewar daf dashi suke a lokacin.

Bayan su yabi da kallo yayin da sassanyar muryar ta ya ratsa mai dodon kunne har cikin zuciyar sa bai bari ba, idanu ya lumshe a hankali yana jin wani nisha'di na ratsashi, haka kawai sai ya tsinci kansa da binsu da idanu har suka 6acewa ganin sa.
  

                Wannan shine ya kasance rana ta farko da Deen ya ta6a tsintan zuciyar sa cikin shaukin so da 'kauna na gaskiya....wanda babu algus acikin sa...bai ta6a sanin da'din da ake ji idan an kamu da soyayya ba sai a wannan lokacin.
     
         Yana daina hangosu sai ya sau'ke ajiyar numfashi yana murmushi ya juya ya wuce cikin gida, inda bai jima a gidan ba ya fito bayan ya 'dauro alwalar sallar la'asar, masallacin da yafi kusa da gidan nasu ya nufa dan bin jam'i.

Ana idar da sallah bai zauna ba sai ya koma gida, 'dakin sa ya wuce ya mi'ke kan kujera...tun lokacin da idanun sa yayi arba da yarinyar murmushi bai bar kan fuskar sa har yanzun, kallon 'daya zakayi masa ka fahimci cewa yana tare da nisha'di marar misaltuwa.

 
      Sam Mu'een bai hana zuciyar sa tunanin yarinyar ba dan ko yace zai yi hakan ma ba iyawa zai yi ba, bai gushe ba yana tunanin ta har sai da ya tabbatar da cewa da gaske son yarinyar ne ya kamashi so kuma matsananci, he can feel his heart beat yanda ya canza gaba 'daya....bai kuma 'kalubalanci hakan ba, domin 'dari bisa 'dari zuciyar sa tayi na'am da ita, tashin farko zuciyar sa ya bata tambarin masoyiya agare shi kuma sanyin ransa,  damuwar sa kawai a yanzun shine ya san bayaga Nanne menene asalin sunan ta.

      Ko lokacin da aka tashi daga islamiyar ma dawowa yayi ya tsaya da ya saiti 'karfe biyar tayi yasan duk tsiya bazasu wuce hakan ba.

  Yana tsaye a wurin 'yan biyun Ammi suka dawo suka shige gida...ba'a 'dau lokaci ba sai ga su nan itama da 'kawayen ta sun taho, sauran nata hira amma ban da ita, dan sam ita ba gwanar hakan bace tun asali, ko ta kansa ma babu wanda yabi balle su san da tsayuwar sa a wurin abinka da 'yan yara dake ji da yarinta....Duk da 'kura mata idanun da yayi amma sam baiga alamar ta san da tsayuwar sa a wurin ba.... amma ga mamakin sa suna gifta shi sai yaga ta waigo ta kalle shi suna ha'da ido sai tayi 'kasa da kanta gami da juya ta cigaba da tafiyar ta.

       Tsabar yanda Deen yaji da'din hakan har dafe 'kirjin sa yayi...yana sau'ke sassanyar murmushi.....saman la66an sa ya furta " wannan tawa ce ni ka'dai insha Allahu ke zan aura ko dan in cikata gurbin farin cikina".



*****
      'Bangare na kuwa.....washe gari da safe da nazo gidan a 'kofar gida na samu Alhaji Baba zaune a kan farar kujerar roba yana hutawa.

   Ganin sa wurin ne ya sanya ni gaida shi sannan na shiga cikin gida.

     Yau kam parlourn babu kowa sai TV dake aiki shi ka'dai, ba gwanar zama inyi kallo ba ce ni shiyasa ma sam ko hankali na ban kai wurin TVn ba, kitchen na wuce wurin Ammi dan nasan tana can a dai-dai wannan lokacin.

  Gaida ta nayi sannan na sanar da ita cewa na ajiye a dinning kamar yanda naji suke 'kiran abin da shi.

Banko bi takan su Saif dake can 'dakunan su ba kawai nai wucewa ta waje.

Gurin Alhaji Baba na koma na zauna daga gefen sa, dama shi babu ruwan sa matu'kar na ha'du dashi to sai na tsaya surutu da yake shima biye ni yake yi.


  " Har kin fito ne?"
yace da ni yana kallo na.
Ina shirin zama kan wata kujerar nace masa " ehh na fito gidan shiru sai Ammi".
Sai yace
  " Ina jin suna can 'dakunan su basu fito ba tukunna, shiyasa ma ashe naga kin fito da wuri dan nasan idan da kin ha'du dasu Saifuddeen da ba yanzu zanga fitowar ki ba".

Dan 6ata rai nayi nace
" Ai nayi fa'da dasu ma kuma babu ruwana da Zaid "
Nayi maganar ina dama fuska tamkar yanzu ne abin ya faru.
" laifin me yayi har haka?"
Alhaji Baba ya tambaye ni yana kallona da fara'ar sa sai nace " ai shine jiya ya hana ni in taya shi zane".
Alhaji Baba murmushi yayi tare da fa'din
" Lallai Zaidu bai kyauta ba, amma ki barshi watarana ai da kansa ma zai ce miki ki taya shi idan yaga kin fishi iyawa dan nasan 'yar tawa gwana ce ko ba haka ba?"

" Hakane"
na bashi amsa ina washe ha'kora na jin dadin an yabe ni.
Shima murmushi yayi Alhaji Baban sai ya sake fa'din " to maza kije ki shirya zuwa makaranta karki makara kinji..bana son ana dukan yata kullum a makaranta"
Kai na juya na kalli hanya sannan nace masa
  " ni sai na huta zan tafi...ai na gaji da tafiyar".
A fili Alhaji Baba yayi murmushi mai sauti sannan yace " to 'yata ki huta amma ka'dan sai ki wuce ....".

Bai gama rufe bakin sa ba sai mukaji sallama daga bayan mu.
Alhaji ne ya amsa sannan muka kalle shi dukkan mu.
Sanye yake da wando 3quarter na rubber jeans da wata armless riga ja, wuyan sa rataye da headphone babba sai tsiyayar gumi yake yi.
Baki na ta6e gami da kawar da kaina gefe.
" barka da hutawa Alhaji"
Yace bayan ya iso ta gaban mu.
Fara'ar dake kan fuskar Alhaji naga ta karu fiye da na dazu wanda cikin hakan yace.
" Yauwa Muhammad gudun ya isa kenan?"
yayi mafanar yana kallon fuskar sa.

    Da murmushi kawai ya amsa Alhajin sannan batare da ya furta komai ba ya tunkari mashigar gidan nasu a hankali.

Ni kam 'kasa-'kasa nak hararar sa dan sau 'daya kawai ya kalle ni daga haka bai sake bi ta kaina ba.
Alhaji ne ya juyo ya kalle ni sai yace " Baki gaida yayan ki ba..."
Tun kafin ya dasa aya na bu'di baki na da 'dan 'karfi nace " ina kwana"
Ko kula ni.ma bai yi ba k'ilan bai ma san cewa da shi nake ba...ni kuwa ban kara ba sai ma na kawar da kaina.

Alhaji Baba murmushi yayi shi kam.
Daf da zai shige gidan Alhaji Baba ya 'kira sunan shi
" ammm Muhammad!"

Cak ya tsaya gami da waigowa cikin raina nace " ashe gaisuwar tawa ma yaji da gangan ya ki amsa min tunda gashi ya ji sunan shi da Alhaji Baba ya k'ira...ban koyi la'a kari da cewa yanayin amon muryar mu ba 'daya bane dashi.
..... Alhaji Baba ne ya ce dashi" sai kayi sauri ka shirya mu wuce da wuri ko....dan yau akwai sa'kon da nake so zan bayar".

" Yanzu zan shirya insha Allahu"
yace tare da juyawa ya shige cikin gida.

 
Kallon Alhaji Baba nayi bayan shigewar tasa a hankali nace " Alhaji Baba wannan ma 'dan ka ne?"
Cike da kulawa yace dani
" D'ana ne Hudah...baki ta6a ganin sa ba ko?"
" ah ah jiya na ganshi a parlour".

Alhaji Baba sai yayi murmushi yace " to shima yayan ki ne kinji shine babban 'dana...kina ce masa Yayah".

Tunzuro baki na nayi gaba tare da fa'din " ni dai ba Yayah na bane...shida ma har marina yayi jiya dan nayi karo dashi kuma yanzu ma ai dana gaida shi k'in amsawa yayi...kuma bazan sake gaida shi ba ma".

Da mamaki Alhaji yake kallo na yace
" Mari kuma? Deen 'din ne ya mareki?"
Kaina na daga sami gami da fa'din
" Ehh amma Ammi tace zata rama min"!
Na karasa maganar harda jin da'di na.

Murmushi yayi dan yasan Ammi ta fa'di hakane kawai dan ta lalla6ani....

Kafin ya sake yin wata magana sai na riga shi da fa'din " Alhaji Baba Deen 'din ma sunan shi ne? Naji Ammi ba haka tace jiya ba, kuma naji ka ce mishi Muhammad duka sunan na shi ne shi ka'dai?"
Ta'kaitacciyar dariya yayi tare da fa'din
" Sunan sun masa yawa ko Hudah?"
Sai na 'dage kaina sama alamar " ehh"
Alhaji ma sai yace
" Kuma ai duk sunayen shi ne, Muhammad Mu'inuddeen sunan sa....zaki iya ce masa Mu'een sannan Deen duk wanda zaki iya ki fa'di.....gaya min wanne yafi miki sau'kin fa'da ?"
Ya 'karashe da tambaya ta...a hankali na bu'di baki na na furta
" *Deen* !"

Alhaji baba sai yayi murmushi yace dani " yayi to duk 'daya....daga yau kuma shima yayan ki ne idan bakya yi masa rashin ji bazai na dukan ki ba kinji?".

"Uhmn"
Nace da Alhajin gami da mi'kewa " na tafi " na sake fa'di batare da jiran jin komai daga bakin sa ba kawai nayi gaba abina.

     Cikin gida kuwa yau ma Mu'een kunun sa ya sha son ransa harda waina ya hada yaci har guda biyu, cikin ransa yake yabawa da da'din wainar da duk zaton sa Ammin ce keyin kunu da wainar dan sam bai san cewa da safen ake kawo shi ba.  
      Kofi ya 'daya ya kur6i kunun a hankali bayan ya ha'diye sai ya kalli Ammi yace " Alhaji Baba fa bai shigo yayi break 'din ba kuma naji yana fa'din zamu fita yanzu?"

" Azumi yake yi"
Ammi ta bashi amsa a takaice.

   Sai ya jinjina kansa tare da fa'din " ai na manta ma ashe yau thursday...duk da'din kunun ki ne kuma fa ya sani mantuwar Ammi".
Ya karashe maganar yana murmushi.

" Da'din kunun masu kunu dai...."
Ammi tace da shi.
Deen bai wani sa maganar aka ba kuma balle ya fahimci me take nufi...da yake ma tana gama waccan maganar sai ta sake fa'din " ba surutu ba ka hanzar ta dai kasame shi tun da yana can yana jiran ka"
Wannan maganar ne ya 'dauke masa hankali harya gama breakfast 'din ya tashi da hamdala bayan ya goge bakin sa....bai tuna maganar Ammi ta farkon ba.





*Kuyi ha'kuri fa kun jini shiru jiya...alhini ne ya hana ni posting* *wlh.....amma yanzu Alhmdllh...zamu cigaba da iznin Allah.*

🤔AMMA READERS ME YASA BA KWA SHARING NE❓.......any ways🤷‍♀👇🏼

~A CIGABA DA GASHI....~ 🤞🏻







_Comment, Vote and share please_ 👌🏻




*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)


By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*


🅿 *27*

Da yamman ranar kuwa babu islamiya  da yake ranar Alhamis ne kuma bama zuwa, ranar ma ni da Nanne muka kai marka'den shinkafar wainar Ummahn mu...da kuma gya'da dayake yau d'in harda gya'da ta gyara shiyasa muka tafi mu biyu, dama ranar da duk za'ayi markaden gya'da ne muke tafiya mu biyu idan kuwa marka'da'd'iyar gya'dar Ummah bata kare ba ni ka'dai ke zuwa in marka'do mata shinkafa.

     A hanyar mu ta dawowa muna tafiya muna 'yar hira, wani sa'in kuma fa'da mukeyi da ita dan ni nawi ya dame ni sosai yayin da ita kuma take faman jan 'kafa tafiyar ta kamar dan dole take yin sa.

Burina tayi sauri mu wuce gida ita kuma ta'ki a hankali take tafiyar ta kamar yanda ta saba.

      Cikin shirin zuwa ball yazo ya gifta mu ban sani ba ko bai gane ni amma ni kam sau 'daya na kalle shi amma sai na gane shi.

   Sai da ya wuce ne sannan Nanne tace da ni " tab amma wannan yana da kyau gaskiya".

" Waye wai wancan ?"
Na tambaye ta gami da nuna shi da bakina cuz da duk biyun hannaye na ri'ke roban dake kaina.
Nanne sai tace " ehh mana koke baki ganshi ba "
Juyawa nayi na cigaba da tafiyata sannan nace
" Na ganshi mana... 'dan gidan Alhaji Baba ne, mugunta ce dashi ingaya miki sosai".

  Baki kawai Nanne ta ta6e bata 'kara magana ba, daga nan kuwa muka cigaba da tafiyar mu.

  Na kanyi gaba in barta dan yanayin tafiyar mu ba 'daya bane da ita sam...ban sani bama ashe Nanne kam hankalin ta duk ya koma kan Yah Deen ne, tafiya take tana waigen sa lokaci-lokaci....ni kuwa dake gaban ta bansan hakan ba sam....bazata kawai naji karan fa'duwan abu...waigowata kawai sai naga ashe marka'den dake kan Nanne ne ya kife gaba d'aya sanadin tuntu6e da tayi.....ido na zaro na kalli marka'den sannan na kalle ta...." ta6'di Nanne marka'den wainar kika zubar?"
Sai tace dani " ai tunt6e nayi ban kula ba".
" To ki 'dauko robar mutafi gida...."
Hannu ta kai ta dago robar sai muka ga ashe itama ta face yayin da marfin ta yake nan garau jefe a gefe guda.

" ko zamu 'dan kwasa ka'dan?"
Nanne ta fa'da tana kallona" Sai nace kamamin mu sau'ke to sai in tayaki".

" ka'dan muka kwasa muka bari dan gaba d'aya ya lalace a wurin ba zai 'kara amfani ba.

Koda muka je gida kuwa Ummah bata ce komai ba jin cewa Nanne ce ta zubar kawai sai ta kar6i wanda muka kwasa 'din ta ha'da da ruwa da dama ta baiwa ragunan Baban mu suka shanye abinsu.....wannan dalilin ne ya sanya washegari bata yi waina ba harma da kunun baki d'aya.....sanadin kallon Deen da Nanne keyi wanda a lkacin ita kanta ma bazata iya shaidar ya san da zaman ta a duniya ba ko a'a duk da kuwa ha'duwar su da shi ta biyu kenan inda yau.
 




*****
      Tsananin yanda Deen ya saka Nanne cikin zuciyar sa ya sanya kafin sati har ya nemi duk wasu bayanan da ya kamata ya sani game da ita, cikakken sunan ta da sunan mahaifin ta harma da gidan su duk ya sani amma bai ta6a zuwa ba.

Da yake da wayo yake yin tambayar ba a fili yake fitowa ya bayyana manufar sa ba...misali ranar da zai fara yin tambayar aranar wani friend 'din sa yazo wurin sa ne sai da ya daidaici 'karfe biyu tayi sai ya jashi suka fito wajen gida suka zauna kamar da gaske, daka yanzun 'karfi da yaji yake tilastawa kansa zaman waje kawai dan ya ganta yaji sanyi cikin ransa..wani sa'in ma idan ya fito sallar azahar baya ta6a komawa gida koda kuwa 'karfe nawa zai kai a wurin to bazai ta6a shigewa ba sai yaga giftawar ta...(ni kuwa nace...aiki ya kama gwari).

  Suna zaune a wurin muka zo muka wuce bamu ma kula da su ba....

Ashe Deen kam hankalin sa na kanmu sai ya koma ya kishingi'da ya wani lumshe idanu bazaka ta6a yin zaton yana ganin abu a hakan ba.

  Shi 'dayan abokin Deen da bai san meke faruwa bane da wucewar mu sai ya girgiza kansa yace " Allah sarki...wallahi yarinyar nan na matu'kar bani tausayi...gata haka zaka ganta kamar lafiyayya amma wallahi kar kaso kaga wurin jinyarta, hankalin kowa sai ya tashi a dangin ta, gata da masifar shiga rai".
Ya 'karashe maganar da sanyin murya.
Mu'een na jin haka sai ya gyara zaman sa da kyau da mamaki yace da shi " wace kake magana akai wai?"

Juyawa yayi ya kallomu dan shi baya ya juya mana Yah Deen ka'dai ne ke facing da hanyar da muka bi.

" Nannen Malam Mamman nake magana akai...gasu can yanzun nan suka gifta mu 'yar doguwa mai hasken....ai kai bazaka sansu ba saboda ba'a garin kake zama ba shiyasa...
Yah Deen taran shi yayi da fa'din " to wani irin suna ne kuma Nanne?"
Hannu wancan 'din ya 'dago yace kai dakata " cikakken sunan ta Amina Nannen kawai sunan gida ne".

Komawa yayi ya kishingi'da yana kallon abokin na sa kamar mai nazarin wani abu a hankali sai yace to me ke damun ta har haka da kace tana baka tausayi?"

" Ai kai de ka bari...wallahi sickler ce da ita abin tausayi yarinyar ni ai badan hakan ba wallahi sai na nemi auren ta yarinyar akwai natsuwa tun tana 'yar 'karamar ta".

Idanun sa ya miyar ya limshe su a hankali cikin ransa yace " gara hakan ai, kaga ni sai na nemi auren ta in kula da ita....."

A fili kuwa " Allah yata lafiya" kawai ya furta daga nan bai 'kara fa'din komai ba.

A ranar ne Mu'een yasan haka game da Nannen mu....to ko ranar da yaga gidan mu ma sanadin wani da suke ha'duwa a filin ball ne ya sa mu ganin gidan da yamma bayan sun tashi daga ball 'din sai hanya ta biyo da su ta wurin anan yaga Nannen mu ta fito daga ma'kwabta ta shiga gida.

Shi 'dayan bai ma kula da ita ba Yah Deen ne ka'dai ya lura da hakan.

Basarwa yayi sai da ta shige gidan kafin ya tambaye shi wai wannan gidan...gidan waye ne?"
" Gidan Malam Mamman ne...me ya faru?"
Abokin ya 'karasa da tambaya, Mu'een sai yace " bakomai".

Tafiya ka'dan suka sakeyi tare wancan 'din ya shige gida sai ya rage saura shi ka'dai...yana tafiya yana tunani....." Nannen Malam Mamman da abokinsa Ashiru ya fa'da da kuma yanzu da aka ce masa " nan gidan Malam Mamman ne, kenan nan ne gidan mahaifinta.

Cikin ransa yake ta tunani har ya isa gida....baiji 'kwarin gwiwar da zuciyar sa ke bashi ta ragu ba saboda sam bai hango wani

Please Login or Register in order to submit comment