Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

An fara ďaukar sahun wasu daga cikin christoci ta hanyar kai Manzon ALLAH matakin da bai kai ba don wasu har ta kai ga suna jinginawa shehunan su matsayin Annabi SAW ko ma sama da haka. Wasu ma saboda tsabar 'kin gaskiya sai su dinga isgilanci wa ALLAH don duk wanda aka mai nasiha akan wata bid'ah har takai ga yace idan ita ita zata shigar dashi wuta to idan ya shiga zai cigaba. Ai kaga wannan ba mu yake wa isgili ba ALLAH yake don ai wuta ta ALLAH ne kuma duk wanda yake ganin abunda aka 'kirki bayan Manzon ALLAH SAW da sahabbansa da tabi'ai daidai ne, lallai alama ce ta ta6ewa. ALLAH yasa mu gane
BILAL BIN RABAH
(Mawadacin Jarumta)
Duk lokacin da Umar (ALLAH ya 'kara masa yarda) zai ambaci Abubakar (ALLAH ya 'kara masa yarda) yana cewa: Shugabanmu wanda ya fanshi shugabanmu wato Bilal. Fansar Bilal da Abubakar yayi yana ďaya daga cikin falalolin sayyadina Abubakar a musulunci don Bilal ba 'karamar gudunmawa ya bayar a duniyar musulumci ba. Bari mu shiga daga cikin tarihin wannan gwarzon..
'Kaddarar Bilal tasa ya kasance daga cikin bayin wasu mutane daga ka'bilar "Juma" dake Makkah wanda mahaifiyarsa ta kasance baiwar waďannan mutanen. Bilal ďan Rabah Ba'ki ne wanda yake aikin bauta na kiwo da sauransu kafin rana tsaka ALLAH ya aiko Manzon ALLAH SAW wanda daga bisani ya kar6i musulunci bayan ya ďauki lokaci yana samun labarin addinin wanda musulunci ya zamo abun surutu da hiran ýan gari sanadiyyar da yasa iyayen gidansa suka fara azabtar dashi da nau'ika iri-iri na azaba a matsayinsa na bawa mara gata kuma a matsayin addinin musulunci na addinin da mutanen Makkah (Qurayshawa) suke tsananin 'ki a daidai wannan lokacin. 'Kabilar juma sun kasance daga cikin ka'bilu mafi Alfahari a garin makkah saboda haka suke ganin ai zubar musu da mutunci ne ace bawansu shi ya bi addinin Muhammad a cewar su. Suka fara ďanďana masa azaba da niyyar lallai sai ya bar addinin musulunci ya koma addininsu na kakannin wanda Bilal duk azabar da suke gana mishi sai dai yace: 'Daya! 'Dayya (ALLAH! ALLAH!!) har takai ga sun fara tausaya mishi sai suka fara cewa: Kaga muma mun gaji da azabtar da kai, kace Lata da Uzza kawai sai mu sake ka. A lokacin magana ma bata fitowa amma duk da haka sai yayi yun'kuri yace: "ALLAH! ALLAH!!" Dalilin da yasa ba zasu iya kashe shi ba shine bawa kusan yafi komai daraja a gurin su a matsayin su na ýan kasuwa masu kasuwanci wanda bawa abu ne mai daraja tunda da kuďi suka siye shi. Ana haka wata rana Abubakar yazo wucewa inda ya ga Bilal ana ta gana mishi azaba a cikin rana inda yace: Kuna azabtar da mutum don yace ALLAH ďaya ne? Sai Ummayah bin khalaf (Uban gidan Bilal) ya mishi iho yace: To ka kawo kuďinsa mana. Bayan Abubakar ya biya sai Umayyah bin ka'ab yace: Gashi! Na rantse da lata da uzza!! Idan da ka'ki siyan shi a farashi mai kyau, ko dirhami ďaya zan siyar maka dashi. Da kamar Abubakar ba zai ce komai ba amma sai yayi tunanin idan yayi shiru, kamar an ci mutuncin ďan Uwan sa na musulunci ne a gabansa amma ya kasa komai. Sai Abubakar yace: Na rantse da ALLAH idan da ka'ki siyar mini dashi sai a dirhami dubu, zan siye shi. Abubakar ya ýanta shi nan take ya zama cikakken mutum mai ýanci kamar sauran mutane wanda ya bashi damar kasancewa daga cikin na gaba-gaba daga cikin sahabban Manzon ALLAH SAW. Bilal ďan Rabah ya samu matsayin da sauran manyan sahabbai suka nema basu samu ba na Ladanci wanda yana da falaloli na musamman a musulunci. Daga cikin falalar Bilal a matsayinsa na Ladan shine Manzon ALLAH SAW yace: Bilal me kake yi ne? Naji takun ka a Aljanna. Sai Bilal yace: Na kasance duk lokacin da na kira sallah, ina yin raka'a biyu. A ya'kin Badr Bilal ya kashe Umayyah bin khalaf wanda da ya janye kansa daga zuwa ya'kin inda wani abokinsa yaje ya same shi a bakin Kaba ya zuga shi suka tafi. Bayan Ummayya bin Khalaf ya ga ya'ki ya canza, sai yaso yayi amfani da wata dama don ya ku6uta daga kisa ta hanyar cewa shi ya zama ya zama fursunan Zubair ďan Awwam amma haka yaci tura.
Bayan Manzon ALLAH SAW ya koma ga ALLAH, Bilal baya iya kiran sallah kamar da duk da ya kasance mafi murya daga cikin sahabbai. 'Karshen kiran sallar da yayi shine a lokacin khalifancin Umar lokacin da ya kai ziyara syria wato inda Bilal ya koma sai mutane suka nemi da ya saka Bilal ya kira sallah, a lokacin Abubakar kuwa da ya matsa masa akan sai ya cigaba da kiran sallah cewa yayi: Idan a da ka ýanta ni don kanka, zanyi abunda kake so. Idan kuma ka ýanta ni don ALLAH ne, ka barni kawai (don bazan iya cigaba da kiran sallah ba). Sai yace to me zakayi? Sai Bilal yace: Naji Manzon ALLAH SAW yana cewa: Mafi kyawun aikin mumini shine jihadi a hanyar ALLAH. Sai Abubakar yace: To me kake so? Sai yace: Zanyi jihadin jaddada addinin ALLAH har sai na mutu. Malaman tarihi sun rabu anan inda wasu suka ce ya tafi ya yita jihadi har 'karshen rayuwar shi inda wasu suka ce ya amsa ro'kon Abubakar inda ya zauna har lokacin khalifancin Umar inda ya ro'ka aka bashi damar tafiya syria.
ALLAH yasa mu dace
Domin gyara, 'karin bayani ko jan hakali:
(08067396502) WhatsApp
©Aliyyu Abdullahi 'Dan Malam

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment