Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

danyen
gold mai matukar tsari ,
Alhaji ya jinjina kai
"To shikenan sai mun hadu"
Mutumin ya mike
"To sai na ganka"
Suka yi sallama yatafi alhaji yaba ma jamilu akwatin
"Ungo wannan kaimin motata, ka bude aljihy(glove
compartment) ka sanya min aciki"
Ya karba yatafi ba'a jima ba ya maido wa alhaji makullin
"Nakai"
Aka cigaba da harkoki anahaka har loakcin sallar la'asar
yayi , nida Alhaji muka fara tafiya masallaci da muka
dawo sai jamilu da ibrahim suka tafi,
Ana haka ne akayo wa alhaji waya ya dauka suka fara
tattaunawa,
Wani mutunne yakeso abashi cikakken addreshin wani
kamfani a ingila
Alhaji ya dubeni loakcin daya ke mikomin makulli
"Don Allah kaduba kan seat din baya akwai wani karamin
littafi kadauko minshi kayo sauri"
Na karba na tafi aguje ba'adadeba na dawo da littafin
.Alhaji yabashi adreshin sannan yabani na mayar ,
akacigaba da sabga .har lokacin tashi yayi akabani kudin
mota kamar yanda aka saba nakama hanyar gida.
********** ********** *********
Nayi mamakin irin wannan sammako da alhaji ya bugo a
yau mu dukkaninmu ya rigamu zuwa.
Hatta ibrahim wanda shi yake tafiya da makullai.........
YAU KUMA WATA KALUBALECE
KE KALUBALAN TAN UMAR
Don't trouble troubles
Till troubles trouble you
Shuraih 99%
Zan cigaba


TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 12
Nayi mamakin irin wannan sammako da alhaji ya bugo a
yau mu dukkaninmu ya rigamu zuwa.
Hatta ibrahim wanda shi yake tafiya da makullai.........
Naga saukar ibrahim daga mota kafin mu karaso to
menene ya fito dashi?
Kodai irin abinnane domin yakama mai kin fitowa da
wuri.
Na durkusa na gaidashi jamilu ne kawai bai iso ba.
Ba 'afi minti biyar ba shima ya'iso akafara hada hada
"Kuzo inji alhaji"
Ibrahim yafada yana raba mana idanu
Muka nufi wajensa cikin rashin sanin abin da kiran ya
kunsa.
"Ku zauna "
Yace damu lokacin daya ke nuna mana benci.muka zauna
daura da juna
"Bawani abune yasa na kirakuba illa wani abu daya afku
wanda banji dadin saba.ya nunani nida jamilu jiya ku na
aika cikin motata , to amma dana isa gida sai natarar da
abin da baiyimin dadi ba, wanda banga amfanin abar min
kes ba alhali an dauke agogon.
Wand yin hakan babbar rainin hankaline da bazan juraba
.
Abin dana keso nasani shin jamilu kaine ka zare agogon
ka kai kedin kawai ko kuma umar kaine ka dauki agogon.
Kuna iya bani amsa anan izan bahaka ba kuwa kuna iya
shaida ma yansan da"
Uka kalli juna nida jamilu akuma lokaci guda muka fara
rantsuwa ,wallahi mu bamu dauka ba.
Alhaji yayi murmushi
"To shikenan kuzauna anan "
Yazare sailula bisa ga dukkan alamu yana ma yansanda
wayane. Bada jimawaba sai gasu sun iso su hudu
"Gasunan ku tafi dasu gida jensu ku bincikomin agogona
"
Aka tasamu agaba .
Nidai babban abin daya dameni aga nazo da yansanda
gida a matsayin ana zargina da sata.to amma badan
hakaba to da ina iyayin komai ma
Musamman tunda nasan bandauki agogoba.
"Ku hau nan"
Yansandan sukace damu lokacin da muka iso gindin
motarsu.
Bayan mun zauna kan bencinne aka fara tambayar inda
za'a nufa .
"Ana iya zuwa ko'ina ma "
Nabada amsa cikin halin yarda da kaina .
"Wanene umar"
Daya daga cikin yansandan ya tambaya.
Na dora yatsana a kirji lokacin da nake nuna kaina
"Gidan ku za'anufa"
Dansandan yacigaba da fada.
"Dama kana da kyasa kyasan sata harbiyu abaya"
Nazare idanu sakamakon jin kazafin da bazai yiwu na
musa shi ba.aka sanar da direban inda za shi.
Bai gushe yana tuki ba saida muka iso kofar gida.
Bakom al'amarin ya sanya tulin yara taruwa, cikin
kyarma nasa kuba na bude dakin , tare da yansanda
muka shiga.
Suka shiga laluben kowanne lyngu da kowanne kusurwa.
Badon bakin cikin daya ke cina ba da babu abinda zai
hanani dariya.
Sakamakon dagewar da yansandan sukayi neman agogo.
Wanda hakan tamkar leka tundin kulline domin gano
rakuminka daya bata.
Tuni sun gama birkita ko'ina amma haryanzu ba'a ga
agogo ba.
"Muje a duba cikin gida"
Daya daga yansandan yafada.
"Dakata tukunna"
Inji wani dayake kokarin daga katifata.kyalkyalin daya
bayyana a karkashin katifar shi yasanar dani akwai wata
ajiyar da bansan da'ita ba,
Ba komai bane illa kyakkyawan agogo yana walkiya,
daukewar numfashina yazo daidai da lokacin dawani
radadi ya ratsa kuncina.
Sakamakon wani bahagon mari da daya daga cikin
yansandan ya kwadamin.
"Kace bakai kasata ba"
Nan danan bakina yafara fadin abin dani kaina nasan
baza a yarda da shi ba.
"Wallahi yallabai sharri akayimin"
"Barawon banza barawon wofi dama tun sa'arda kazo
kake yimana sace sace kaboye kudin alhaji, kaci sailula ,
yau luma gashi ka saci agogo"
Jamilu kenan ya hauni da bambami sa'arda muka fito
waje!
"Barawo! Barawo!! Mai kasata? Agogo ya sunan ka? Umar"
Wata kwarya kwaryan waka kenan da yara suka kirkirota
bayan da'aka watsani mota akafara tafiya.
Aguje sukabi motan suna raira waka , basu rabu da muba
saida muka hau titi.
Nasha zagi kala kala da kuma mari dabam dabam kafin
mu karasa.
Ahaka muka iso har kasuwar kwari daya da ga yansandan
na cumuimiye da kuquna . Ya kwadamin mari sa'arda
yake kokarin dankwafar dani agaban alhaji
"Alhaji yaron tsinannen barawone daya kamata a
ladabtar dashi"
Yamika ma alhaji agogon kafin kace meye tuni mutani
sun cika wajen.
Kama daga kwastomomi zuwa masu kanti.
"Allah wadaranka"
"Allah tsinema"
"Allah watsa ka"
Sune mabambantan lafuzzan dake fita daga bakin
mutane.
Wadansu har basa samun daman ganina sabida
cunkosan mutane.
Zazzafan radadi yarinka bin jikina, ba radadine na zafin
duka ba 'a'A radadine na mamakin sharrin da'aka yimin
da babu daman na musa shi, babban abinda yafi damuna
shine sunana daya riga yabaci akasuwa da
unguwarmu,toni yanzu da wacce fuskar zan ringa kallon
mutane.
"Wayyo Allah umar kacuceni kaci mutuncina"
Muryar yayanace lokacin daya iso yana kuka, ya nufo
kaina da gudu yansanda suka rirrikeshi.
"Ku kyaleni na kasheshi tunda bashi da sauran amfani"
Da kyar yansanda suka janyeshi baya
"To shikenan daga yau umar na sallameka kar ka kara
fitowa indai akwai mutumin da bama shiri dashi bai wuce
barawo ba"
Alhaji kenan loakci na farko dayayi magana tun bayan
isowar mu.
Ya sallami yansanda, da sunso abarsu su tafi dani alhaji
ya hana 'aka barni anan .
Har saida jama'a suka watse sannan na. Tashi, aranar
unguwarmu sai da daddare nashiga........
AYYA JIKI MAGAYI
DAMA DUK WANDA YACE ZAI TARI ARADU DAKA TO
LALLAI SHIMA YASAN SAKAMAKON
(Maudu'I)
Izan da kaine umar zaka cigaba da soyayya da farida ko
ko zakayi hankali
Waitin for sharhi
Zanci gaba
Its shuraih 99%


TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 13
aranar unguwarmu sai da daddare nashiga........
********* ************ ********
Ahalin yanzu nida tsuntsun da'ake kiwonsa akeji duk daya
muke ,
Domin kuwa bana fita ko'ina daga shago sai shago,
Sai idan angama abinci a miko min ta kofa mai shiga cikin
gida ,izan kaga na fita to da daddarene ko da asubah idan
zamuje sallah nida yayana.
Shi kansa rashin jituwa mai karfi ta shiga tsakaninmu.
Abisa abunda yakira cimasa mutunci.
Nayi masa rantsuwa da Allah akan duk abubuwanbani da
hannu aciki yaki yarda.
Sai yanzu na fuskanci ashe irin wasan da mutuminnan
yake nufi kenan.
Hakikanin gaskiya wasan nasa bantaba ganin wanda
yakaishi muni ba, sai dai duk wannan bana zaton zan bar
farida,domin kuwa kaunarta ta rigaya tabi jikina.
Yau iatace rana ta farko dana shirya zanje wajenta tun
bayan da'aka yimin sharri.
Bakomaine yasa na daga kafa illa tsabar bakin cikin dake
damuna.
Ahalin yanzu kuka awajena babu wuya domin kuwa da
zarar na tuna bana control na kaina abinci ma kadan
nake ci.
Na isa goron dutse da kimanin karfe tara na dare .
Badon komai ysa nayi dare hakaba sai don gudun kada
wani wanda yake kasuwar kwari yaganni ya tona min
asiri.
Tuni su farida rufe gida, nasani abune mai wuya ace wai
bacci take kasancewarta mai matukar kwazo, na
kwankwasa kofa.
Bada jimawaba naji takun kafa
"Waye"
Aka tambaya muryar farida ce
"Umar ne"
Na bada amsa tuni ta gama shaida muryata nan da nan ta
zare sakata takuma bude kofa kawai naga ta fashe da
kuka.
Nayi mamakin abinda yasa haka , kodai dun na dade
banzo bane?
Muka dunguma cikin gida kukantane yafoto da hajiya yau
maimakon gaisuwa kuramin ido kawai tayi,ta kuma rike
baki
"Ashe zaka sake dawowa gidanmu umar, na dauka bazaka
kara takowa ba"
"Me zai hanani zuwa mummy?"
Itama sai naga tafara kwalla
"Kai kuma umar hanyar da za'abi da kai kenen"
Sai nagane ashe labarin abin dayafaru tuni ya iso
garesu.banyi mamaki ba domin kuwa goron dutse
unguwace data kushi yan kwari da dama.
Nida farida muka zarce daki alokacin datake ta faman cin
kuka.
"Umar nafadamaka muddin kana tare dani bazaka sami
kwanciyar hankali ba amma ka ke keshe kasa kaki yarda
to yanzu daka gani da idonka ai ka hakura"
Tacigaba da kuka
"Dakata farida"
Nace da ita
"Shin wai kin daina kaunatane ko yaya"
Ta tsuguna agabana
"Umar bazan daina kaunar kaba har abada"
Nayi murmushi
"To indai hakane farida banga wani abin dazai sani in
janye ba,kisani na dora tubalin soyayyarmune akan gini
biyu,imma dai nasami cikar burina imma a kirgani a
mutum na hudu daya rasa ransa, kisani ahalin yanzu
cigaba da kaunarki ya fiyemin sauki,domin kuwa mutuwa
afagen dagar neman aurenki yafiyemin mutuwa
asakamakon hauhawar jini"
Na sunkuyo gareta
"Farida izan narasaki bazankai labaraiba"
Kuramin ido kawai tayi tana kallona , unkai tsawon minti
daya mun zurawa juna idanu, daga bisani fuskarta ta
yaye izuwa murmushi.
"Oh! Umar Allah yabar mu tare har abada"
Na mayar da murmushinta sa'arda bakina yake motsawa
a kokari na lalubo kalmar amin .
Tamike tsaye akuma loakci guda da tazauna akan hannun
kujerata ta dubeni fuska da fuska
"Da ka gujeni umar da mutuwa zanyi, bazan iya rayuwa
babu kai ba "
Na girgiza kai
"Bazan gujekiba farida har abada koda kuwa za'rika
yankan naman jikina
(Kaji soyayyar gaskiay kenan
Its shuraih 99%)
******* *********** ********Tarar Aradu
Littafi na daya 1
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 14
.
.
Toh jama'a sakamakon rashin sauran fallayen littafin hakan yasa, dole da kaina zan karasa maku wannan labari sai ayi hakuri da kura kuran da za'ai arangama da su
.
Ahalin yanzu nida tsuntsun da'ake kiwonsa akeji duk
daya
muke ,
Domin kuwa bana fita ko'ina daga shago sai shago,
Sai idan angama abinci a miko min ta kofa mai shiga
cikin
gida ,izan kaga na fita to da daddarene ko da asubah
idan
zamuje sallah nida yayana
.
Wata rana da asubah na fita sallar asubah nida yayana toh dama ni idan na fita salla nida yayana bama dawowa gida sai safiya domin kuwa tsayawa muke a masallacin muita karatu har sai gari ya waye, kaman kullum yau hakan ta faru,
Mun fito muka nufi gida ina zuwa kofan gidan gabana ya buga sakamakon ganin kfan dakina danayi a bude,alhalin kafin na tafi masallaci sai dana sanya dan makulli na kulle dakin gaba daya
.
Na dai daure na doshi dakin ina bude dakin na saki wani salati sakamakon abunda nagani acikin dakin,
Wata mata daga ita sai shimi iya cibiya da wani dingilallen wando iya cinya tana kwance kan katifar barcina,
Ina bude dakin matar ta tashi tayi mika, sannan tadan mummustsuka idanuwanta ta dubeni tace yauwa malam kai nake jira dama tun dazu nake son na tafi,
.
Na dubeta baki bude cikin mamaki nace mata wacece ke sannan meya kawoki cikin dakina,
Tayi tsaki tace kaji rainin hankali kadauko ni kuma kana tambayata ko waye ni lallaima, malam ka bani kudina yanzu ina son zan tafi
.
Ke dan ubanki wani kudin zan baki, yi maza ki fice daga cikin daki yar iskan karya, na fada cikin fusata,
Ai nan matannan tai tsalle ta cakumemin gaban riga muka fito daga waje tana cewa wallahi sai ka biyani kudin kwana na, tayaya za'a yi ka dauko ni ka kwana dani sannan kace baza kaa biya ba ai wallahi sai ka biya,
.
Ba'a bata wani lokaci ba har matannan ta tara min jama'a nan raina ya baci na tsinka mata mari ai ba shiri ta sakeni, na cigaba da jibgarta da kyar mutanen angwa suka kwaceta a hannuna amma duk da haka matannan sai ihu take ita sai na biyata kudinta, a haka yayana yazo ya samemu
.
Yayi bakinciki sosai kuka ne kawai baiyi ba ya tambayeta nawane kudin bakunya bare tsoron Allah matannan tace dari uku ne, cikin kunan rai yayana ya ciro kudin ya bata, matar ta wuce dakina ta kwashe kayanta tazo wucewa ta dubeni tace Assha, ai wallahi daga yau baka dauko ni dakinka, sai de mu ringayi acan yadda muka saba,tunda kai kace tsiyane aranka,, ko kallonta banyiba donni abun har mamamki nake ni daban taba ganinta ba,
.
Na dafa yayana nace wallahi yaya....ya katseni ta hanyar daga mani hannu yace umar da na zata abun naka zai tsaya kan sace sace ne toh tunda takai ga sai ka bata bin suna ka kawo karuwa cikin gidana toh ka kwashe naka ya naka ka kara gaba kasan inda dare ya maka daga yau kabar gidannan kenan
.
Iya tashin hankali yau na gani, kuka ne kawai banyi ba,
Cikin kankanin lokaci na shiga shagona na dauki wata tsohuwar jakar kayana, na dauki hanya wacce bansan ina na nufa ba
Tafiya kawai nake zuciyata sai radadi take yimin A lokacin da hotunan abubuwan da suka faru dani suke yawo a kwalkwata tamkar a majigi,
Duk da ya kasance wunin ranan bansa ka komai a cikina ba, amma hakan bai sa naji yunwa ba
Na isa wata angwa na samu gindin wani waje na zauna na kifa kaina a cikin guiwowina, ayayin da tunani iri iri keta zarya a kwakkwana, ji nake tamkar na kashe kaina na huta
.
******
Na tashi na nufi wani masallaci domin yin sallar Isha'I domin kuwa yanzu na tabbata mutane ko sun gani ba zasu shaidani ba, bayan na gama sallar ne sai kwanta a masallacin da nufin na kwana a masallacin in yaso gobe da safe sai in wuce kauyenmu wajen iyayena,
Mutane daddaiku ne sukayi saura a cikin masallacin har barci ya fara dibana sai naji ana tashi na na dago da kai domin naga waye wannan
"Malam tashi koh zamu rufe masallacin ne "
Su biyune suna sanye da manyan kaya
Kallo daya nai masu na ayyana araina kodai limaman masallacin ko kuma wasu malamai na daban
na tashi cikin rashin jindadi na fita daga masallacin na samu wani dan kewaye a jikin masallacin na kwanta,
Bayan sun kulle masallacin ne zasu tafi sai naji dayan yace "malam ladan kaga wannan yaro ya koma can ya kwanta kuma, da alama matafiyine don ga shi dauke da Jaka"
Wanda aka kira da ladan yace"malam liman kenan ai wannan yaro daka ke gani kasurgumin barawo ne, sau uku ana kamashi a kasuwar kwari, yanzuma daka ganshi anan inaga koh ya lababo ne ya sace mana mita,ko kuma mic"
Liman najin haka sai ya rike baki yace "assha "
Sai ya daga murya da alama wasu yakewa magana yace "kai samari kuzo ku jibgi wannan mara kunyar barawon, tun kafin ya kassaramu"
.
Ina jin haka ban san lokacin dana zabura a guje ba na tsallake, dan karamin katangar daya katange gewayin dana ke kwance na ranta ana kare, inajin ihu da kururwan mutane suna cewa atare barawone atare haka na ringa cin uban gudu har na fice daga angwar gaba daya, ina shawarar na tsaya kenan sai naji wani Abu mai nauyi ya bugi kaina daga nan kuma sai ji nayi na kife akan wani ruwa ruwa mai wari, daga jin wannan wari na gane warin giyane ko na aman giya,
Idanuna dishi dishi suke gani, wani katon mutum nagani ya tsaya akaina yana rike da wata katako 2 by 2, mutumin ya sunkuyo da kansa daidai kunne na yace
"Umar dan wasa daga yau wasanka ya kare , dun kuwa yanzu zan aika ka kiyama, dama sakamakon irinku kenan masu taurin kan tsiya"
Ya daga wannan katakon sama da nufin ya buga mini aka.........
.
Masu karatu anan muka kawo karshen littafin TARAR ARADU na daya 1
Kaman yadda kamin mufara wannan littafi na fada maku cewa 1 and 3 kadai nake da su bani da 2, dun haka gobe zan fara post na TARAR ARADU littafi na uku 3 Allah ya kaimu da rai da lafiya
$
TARAR ARADU
(m) Umar Lawan Abdul
Littafi na daya 1
Typing Shuraih Usman
.
.
Domin download na wannan littafi dama wasu sauran littatafan sai ku shiga shafinmu anan kuyi like
Like:- www.facebook.com/hausaebooks
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment