Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuskar macce.

116.

Makaho idan idonsa ya buxe karya sandarsa yake yi. Wani ma qona ta

zai yi da wuta. Haka xan Adam yake da saurin manta alheri da qin tuna
baya. Duk wanda za ka taimake shi yi ma sa don Allah. Idan kana jiran
godiya da sakayya daga mutane babu shakka za ka sha mamaki.

117.

Wawa ne yake faxin abin da zai aikata. Mai kuri shi yake bayyana

abin da ya aikata. Mai natsuwa aikinsa ne ke bayyana matsayinsa.

19

118.

Gishiri da Sukari kalarsu xaya ce. Banbancinsu yana bayyana ne idan

aka xanxana. Haka mutane su ke; sai an gwada akan san na qwarai.

119.

Zama da mutanen kirki yana qarar da kai ababe guda shida: Son

Allah, da bin Allah, da ambaton Allah, da gudun duniya, da son lahira da
barin girman kai.

120.

Har abada akwai zukatan da ke son ka ko da kana munana ma su.

Akwai kuma ma su qin ka duk yadda ka kyautata ma su. Kowa da kiwon da
ya karve shi.

121.

Marar gaskiya kamar mai yagaggen wando ne, duk inda zai zauna sai

ya rinqa kame-kame. Mai gaskiya a natse yake zamansa.

122.

Ana gane mumini ne a wurare guda uku: Idan ya samu ya gode ma

Allah, idan ya rasa ya koka ma Allah, idan ya shiga damuwa ya koma ma
Allah.

123.

Abubuwa uku idan suka haxu da wasu uku ba su da magani: Talauci

idan ya haxu da kasala. Qiyayya idan ta haxu da hassada. Jahilci idan ya
haxu da girman kai. Allah ka sa mu gama da duniya lafiya.

124.

Abubuwa uku ba su da tsada: Ilimi da Lafiya da Sadaki.

125.

Idan kuxi suka fara zance dole ne gaskiya ta rufe bakinta.

20

126.

Tsare gaskiya ba ya hana rayuwa jin daxi. Qarya da zalunci da cin

amana ba su kawo samu.

127.

Abu biyu idan kana da su kai Sarki ne: Lafiya da wadatar zuci.

128.

Duk abin da ya sa ka damuwa idan ka yi nazarin sa ya tava sa ka

murna. A duniya babu abin murna na din-din-din sai dai a aljanna.

129.

Qaramin yaro da Fensir yake rubutu. Idan ya girma sai ya koma ga

Biro. Dalilin haka shi ne, kuskuren yaro mai sauqin gogewa ne. Goge
kuskuren babba kam akwai wahala gare shi.

130.

Mutane iri biyu ne: Wani yana rayuwa ne don ya ci, wani kuma yana

ci ne don ya rayu. Koka gane bambanci tsakaninsu?

131.

Zunubin da ya sa ka yin da-na-sani da komawa ga Allah ya fi ibadar

da ta sa ka girman kai da xagawa!

132.

Sarakunan da suka yi mulkin duniya duk sun tafi ba su san daxin

duniya ba. Ba wutar lantarki, ba ruwan Firijin, balle kuma Fanka da AC. Ba
su hau keke ko Mashin ba, ballantana motoci da jirage. Ba su san abin da
ake kira Tarho ba ballantana wayar tafi-da-gidanka. Duk hasken gidajensu a
wancan lokaci bai wuce na Kyandur da Fitila mai amfani da kalanzir ba. A
yau kai Sarki ne amma ba ka gamsu da abin da ka samu ba. Idan kana da
mota ta maqwaucinka kake kallo. Idan kana da gida na wani ke ba ka
sha’awa. Oh! Allah Sarki. Xan adam da guri yake mutuwa.

21

133.

Idan ka kasa gane wurin da ka yi shuka kada ka samu damuwa.

Watarana ruwan sama ne zai nuna ma ka. Haka rayuwa take. Yau da gobe
babbar makaranta.
134.

Hattara da hawaye guda uku:

- Hawayen iyaye da
- Hawayen maraya da
- Hawayen wanda ka zalunta.
Kowanen su hawayensa na iya nutsar da kai a cikin tekun bala'i.
135.

Mala'iku suna da hankali ba su da sha'awa. Dabbobi suna da sha'awa

ba su da hankali. Xan adam ne Allah ya haxa ma sa guda biyun. Idan
hankalinka ya rinjayi sha'awarka ka bi sawun Mala'iku. Idan sha'awarka ta
zarce hankalinka ka shiga sahun dabbobi.

136.

Karatu akwai wuya, ilimi akwai daxi. Nema akwai wuya, arziki akwai

daxi. Zama da jahilci ba wuya, rashin ilimi akwai takaici. Haka duniya take,
yaro vata hankalin dare ka yi suna!

137.

Allah ya yi mana kunnuwa biyu da idanu biyu amma ya yi mana baki

guda xaya saboda ya fi son mu yi kallo, mu yi saurare fiye da yadda mu ke
magana.

138.

Idan na qwarai da mugu suka haxu kowa ma yana iya gane bambanci.

Amma a tsakanin na qwarai da wanda ya fi shi, da mugu da wanda ya fi,
wannan sai masu hankali ke iya rarrabewa.
22

139.

Ba a sanin matsayin saurayi sai ya yi aure. Ba a sanin halin talaka sai

ya wadata. Ba a sanin gaskiyar xan Siyasa sai ya kai ga muqami.

140.

Ba kowane wayayye ne mai ilimi ba. Ba kuma kowane mai ilimi ne

yake da wayewa ba. Idan Allah ya ba ka ilimi nemi sanin duniya da zamanin
da kake cikin sa, sai ya zama kana da haske a kan haske. Idan kuma kana da
wayewa da sanin duniya matsa kusa da malamai ka qara sani, sannan ne
wayewarka za ta amfane ka.

141.

Idan kana son ganin yadda duniya za ta kasance a bayanka, ka duba

yadda take a bayan mutuwar wani irinka. Za ka ga yadda masoya ke manta
masoyansu, rigima ta harxe tsakanin magadansu. Wanda bai manta ka kawai
shi ne Allah mahaliccinka. Manta da kowa ka nemi yardarsa.
142.

Wanda ba ya sallah an haramta ma sa jin daxin duniya. Sannan zai

gamu da wahalhalu a wurare guda huxu: A nan duniya, da ranar mutuwa, da
cikin qabari da ranar hisabi. A duniya ana xebe ma sa albarka, a cire ma sa
kwarjini daga fuska, a sa ma jama'a qyamar sa. A ranar mutuwa zai mutu da
wulaqanci da yunwa da qishirwa. A cikin qabari Allah zai quntata ma sa, a
hura ma sa wuta a cikin sa, a aika ma sa kumarci a tsakanin fatar jikinsa da
namansa. A ranar hisabi za a baqanta fuskarsa, a yi masa hisabi dalla dalla,
sannan a haxa shi da Zabaniyawa da za su wurga shi cikin wuta. Lallai,
Sallah ita ce ginshiqin addini.

143.

Idan kana jin kaxaici ka tuna Annabi Adam Alaihis Salam. Ya zauna a

duniya shi kaxai ba kowa. Idan ka sha wuya a wajen wa'azi da karantarwa ka
23

tuna Annabi Nuhu Alaihis Salam. Shekarunsa dubu ba hamsin yana wa'azi.
Idan 'yan uwanka sun cuce ka ka tuna Annabi Yusuf Alaihis Salam. A cikin
rijiya su ka jefa shi. Idan mahaifinka na tsanar ka a kan riqon addini ka tuna
Annabi ibrahim Alaihis Salam. A kan haka ne ya sha wuya a hannun
mahaifinsa. Idan ciwo ya addabe ka ka tuna Annabi Ayyub Alaihis Salam.
Har sai da ya ji qamshin mutuwa a kan cuta. Idan matsalolin rayuwa sun
dabaibaye ka, ka tuna Annabi Yunus Alaihis Salam. Kifi ne ya haxiye shi
amma ya samu kuvuta a dalilin ambaton Allah. Idan an yi maka qazafi ka
tuna iyalin shugabanmu ma'aiki Sallallahu Alaihi wa Sallam. Kwana hamsin
tana cikin sunu da takaici sai da Allah maxaukaki ya wanke ta. Matsaloli da
wahalhalun rayuwa ba su ne qarshen xan Adam ba. Manya ma sun gamu da
matsaloli kala-kala. Abin damuwa shi ne matsalarka ta zama sanadin
rabuwar ka da Allah mahaliccinka.

144.

Abu biyu neman ka suke yi: Arziki da ajali. Arzikinka ba zai wuce ka

ba, kai kuma ba zaka wuce ajalinka ba. Kada ka wahalar da kanka wajen
neman abin da ke neman ka. Kada ka ji ciwon abin da ka rasa, idan naka ne
zai dawo ma ka, idan ba naka ba ne dabararka ba ta kamo shi.

145.

Idan duniya ta aure ka sai ta kwashe alherin mutane ta yava ma ka.

Idan kuwa ta sake ka sai ta kwashe alheranka ta jefa ma wasu.

146.

Lokaci kamar walqiya ne; ba ya jira. Ko ka ci moriyar sa nan take ko

kuma ya tafi ya bar ka.

24

147.

Wanda fuskar mata take ba shi sha'awa mata daya ba ta isar sa. Amma

wanda kyakkyawan hali yake so xaya ma sai ta ishe shi.

148.

Idan kana cikin damuwa ka jira samun sauqi daga wurin Allah,

wannan jiran da kake yi ibada ne. Domin kyautata zato ne ga Allah. Wanda
ya kyautata ma Allah zato kuwa lallai ne Allah zai ishe shi.

149.

Duk lokacin da fitila ta yi sama haskenta ya fi yaxuwa. Idan Allah ya

daukaka ka, yi qoqari ka zamo fitila mai kawar da duhu da damuwa daga
mutane.

150.

Urwatu bn Zubair, ya gamu da jarrabawar ciwon Cancer a qafarsa. Da

magani ya gagara sai aka yanke shawara aka cire masa qafar ga baki xaya.
Amma a wannan dare bai fasa karanta abin da ya saba yi na Alqur'ani da
Zikirin ubangiji ba. Duba ka gani, sau nawa ne qaramar matsala ta durqushe
ka daga ibada?

151.

Kyawon hankali ya riqa tunani. Kyawon harshe ya riqa faxin gaskiya.

Kyawon Budurwa kunya. Kyawon Yaro biyayya.

25

152.

Idan ka kyautata ma mutum za ka mallake shi. Idan ka wadatu daga

mutum za ka zama tsaran sa. Idan kuwa ka buqatu zuwa ga mutum, to dole
sai ka zamo bawansa.

153.

Tuntuven harshe ya fi tuntuven qafa zafi. Na qafa saurin warkewa

yake yi, na harshe kuwa illanta mutum yake yi har qarshen rayuwarsa.

154.

Ilimi ya fi kuxi, kuma ya fi mulki. Kai, har lafiya ma ya fi ta. Kuxi da

mulki da lafiya duk suna gushewa. Amma Ilimi yana nan tare da mai shi ba
su rabuwa.

155.

Abin al'ajabi da lura: Masallatai suna cika ne bayan isowar liman,

amma filayen qwallo suna cika tun kafin zuwan ‘yan wasa.

156.

Kada lamarin duniya ya dame ka. Duk abin da ke cikin ta na Allah ne.

Kada sha'anin arziki ya dame ka. Domin daga wurin Allah yake fitowa.
Kada ka samu damuwa a kan gobe, domin a hannun Allah take. Abin da ya
kamata ya dame ka shi ne, neman ka samu yardar Allah.

26

157.

Karan dawa yakan sunkuya ne idan yana xauke da alheri. Idan yana

fanko sai ka gan shi tsaye qyam. Ba kowane mai xaga kansa ne ya cancanci
jinjina ba.

158.

Mumini yakan yi adalci ko yana a cikin fushi. Yakan yi gaskiya ko

yana a cikin matsi. Yakan daidaita ko yana a cikin damuwa.

159.

Idan ka kwatanta kanka da rayuwar mawadaci ka lura ya fi ka, to ka

duba yanayin ibadarka ko kai ka fi shi? Domin kada ya yi maka bugu biyu;
ya ci nan kana kallo, a ranar lahira kuma ya shige aljanna ya bar ka.

160.

Gurgu na gaskiya shi ne wanda ba ya zuwa masallaci, makaho na

gaskiya shi ne wanda ba ya duba Alqur'ani.

161.

Idan ka xauka cewa, ba ka yin kuskure to wannan shi ne kuskurenka

na farko. Duk mutum xan tara ne, bai cika goma ba.

162.

Kada ka bari girmanka ya faxi a kan kalma guda xaya da za ka sosa

qaiqayin bakinka da ita. Kada ka bari tuntuve guda ya zubar maka da
mutunci.

27

163.

Kada ka sa ranka cewa mutane duk za su so ka. Zukatan mutane a

kullum cikin Canji suke; abin da suka so yau, shi suke qi gobe.

164.

Qauyanci shi ne ka yi kuri da babbar riga ko fankaceciyar mota ko

danqareren gida a birni alhalin iyayenka na qauye suna cin busasshiyar
gurasa.

165.

Duk kyawon da kake taqama da shi duniya ke cinye shi. Duk kyawon

da kake bukata, a lahira an yi tanadin fiye da shi. Me ya sa muke son duniya
muna manta lahira?

166.

Aiki kaxan mai xorewa ya fi yawan surrutu mai wucewa.

167.

Mutane uku ne suke kewaye da kai:

168.
169.
shi.

Mai son ka tsakani da Allah. Wannan ka mutunta shi.
Da makusancinka amma yana qyashin ka. Wannan ka yi hattara da

170.
Sai maqiyinka wanda ba ya voye jin haushin ka. Wannan ka roqi
Allah kariya daga sharrinsa.
28

171.

Mai wa'azi ba shi yake hisabi ba, amma yana tunatar da kai cewa

akwai hisabi a gaban ka.

172.

Kada ka bayyana murnarka a gaban wanda yake cikin damuwa. Kada

ka faxi yawan dukiyarka a gaban talaka. Kula da damuwar jama'a yana cikin
alamun Imani.

173.

Idan kana cikin jira, lokaci zai yi tsawo. Idan kana jin tsoro lokaci zai

yi sauri. Idan kana ciwo lokaci zai yi nauyi. Idan kana cikin nashaxi lokaci
zai gajarta. Lokaci da yanayi a tare suke tafiya.

174.

Abu uku ba su amfani idan aka rasa abu uku:

- Rayuwa idan babu lafiya
- Da kuxi idan ba a kyauta
- Da magana idan ba aiki.

175.

Shan toka da tsare gida sukan sa a qosa da kai. Yawan raha da sakin

jiki kan jawo maka wulaqanci. Ka lizimci tsakiya a komai, shi ne alheri.

29

176.

Gaskiya ta fi tasiri idan aka sha wahala a kan ta. Sirri ya fi daxin ji

idan aka inganta voye shi.

177.

A kan pillow Sarki yake kwana. Haka shi ma talakka. Amma babu

wanda zai ji daxin bacci sai wanda yake da kwanciyar hankali.

178.

Mutakabbiri kamar mutum ne a qololuwar dutse; yana kallon mutane

qanana a qasa, suna kallon sa xan karami.

179.

Ba dole ne ka faxi duk abin da ka sani ba, amma yana da kyau ka san

duk abin da kake faxi.

180.

Tunaninka naka ne. Amma magana da zaran ka furta ta, to ta fita daga

ikonka.

181.

Duk wanda yake saurin amsa tambaya, lalle ne sai ya yi kuskuren

bada amsa.

182.

Duk wanda ya gudu daga aiki ya gudu daga hutu.

30

183.

Kana da girma a idon mutane matuqar ba ka nemi abin hannunsu ba.

Da zarar ka nema shikenan girmanka ya faxi.

184.

Kuxi ba su da amfani sai an kashe su. Idan an kashe su kuma ba za su

dawo ba, sai dai a sake nemo wasu.

185.

Mai hasada ba ya haxuwa da abu xaya, ba ya rabuwa da abu xaya:

Mai hasada ba ya rabuwa da kwaxayi. Ba kuma ya haxuwa da qoshin zucci.

186.

Aikin da Allah ya fi so duka shi ne ka faranta ran mumini, ko ka yaye

ma sa damuwa, ko ka biya ma sa bashi, ko ka raba shi da yunwa.

187.

Wanda duk ya haxiye fushinsa Allah zai rufa asirinsa. Wanda kuwa ya

biya buqatar xan uwansa Allah zai tabbatar da qafafunsa a kan siraxi.

188.

Idan farce ya yi tsawo shi muke yankewa ba yatsan ba. Haka ne idan

muka yi savani, kawar da shi ya kamata mu yi ta hanyar tattaunawa ba ta
hanyar yanke alaqar da ke tsakaninmu ba.

31

189.

Idan kana son sanin yadda ake gudun duniya ka zauna kusa da

qaramin yaro ko kuma tsoho mai hankali. Na farkon bai san duniya ba. Na
biyun kuma ya riga ya sallame ta.

190.

Kiyaye ladarka kamar yadda kake kiyaye shexarka. Watarana

shexarka za ta qare. Kuma daga nan ne ladarka za ta fara aiki.

191.

Mutane biyu ne suka ci moriyar duniya: Wanda ya rubuta abin da ya

kamata a karanta, da wanda ya aikata abin da ya kamata a rubuta.

192.

Kada ka xauka cewa, duk wanda ya yi shiru kurma ne. Wani ya yi

shiru ne yana jiran lokaci. Wani ya yi shiru ne don yana nazari. Wani kuma
kawaicinsa shi ne maganarsa.

193.

Abu uku sanin su zai amfane ka:

- Duniya ba a tabbata a cikin ta.
- Kuma babu hutu a cikin ta.
- Sannan ba a tsere ma zargin mutane.

194.

Idan za ka yi bacci kada ka manta abu uku: Alwala, da karanta Ayatul

Kursiyyu, da kwantawa a hannun dama.
32

195.

Mai hankali ba ya neman hutu a duniya. Yana tanadin ruhinsa wanda

zai je sama bayan mutuwarsa, fiye da yadda yake tanadin gangar jikinsa
wadda idan ya mutu za a rufe ta a cikin qasa.

196.

Yawan jayayya alamar girman kai ne. Yawan surrutu alamar tavuwar

hankali ne. Kawaici ado ne. Kyauta halin girma ne. Yafiya xaukaka ce.
Yabon kai jahilci.

197.

Sanin da ya fi kowane sani amfani shi ne ka san kanka. Ladabin da ya

fi kowane ladabi amfani shi ne ka tsaya matsayinka.

198.

Wanda ya wayi gari yana da abinci, ga shi kuma a cikin qoshin lafiya

da aminci, a garinsu akwai kwanciyar hankali da kawaici, wannan ya gama
haxa ni'imomin duniya.

199.

Mantuwa ga xan Adam ni'ima ce. Ba domin mantuwa ba da rayuwa ta

gurvace.

33

200.

Wanda ya kame harshensa, ya kiyaye farjinsa, ya shiga taitayinsa, ba

zai tava yin da-na-sani a duniya ba.

201.

Ikon Allah: A da mutane suna rayuwa babu mota, babu wayar tarho,

ba ruwan fanfo. A yau kuma mutane suna rayuwa babu qauna, ba mutunci,
ba zumunci.

202.

Masu hikima sun ce: Rayuwa ta tambayi mutuwa, me ya sa mutane

suke so na, amma ba su son ki? Sai mutuwa ta ce, saboda ni gaskiya ce mai
xaci. Ke kuma qarya ce mai cike da ado da xaukar hankali.

203.

Idan ka xauki Alqur’ani Shexan yakan fusata. Da zaran ka buxe shi

sai ya fashe da kuka. Kana yin Bisimilla zai faxi qasa warwas. Da ka shiga
cikin karatu sai ya suma ya fita hayyacinsa. Mu yi qoqari mu rinjayi Shexan.

204.

Mai hankali yakan gane ko wane ne kai daga maganar da kake yi a

kan mutane ba daga maganar da mutane suke yi a kan ka ba.

205.

Rayuwa gidan jarabawa ce. Da haifuwar xan Adam za a yanke masa

cibiya, zai ji zafi yana kuka. Idan an naxe shi a tsumma zai samu takura, ya
quntata yana kuka. A wurin shan nono zai gamu da wasu wahalhalu da
34

rashin jin daxi. Bayan haka zai sha wahalar fitar haqora, sannan faxuwarsu
da sake fitowarsu. Idan an cire shi daga shan nono zai samu damuwa da
baqin ciki wadanda ba su misaltuwa. Idan lokaci ya yi za ayi masa kaciya ya
sha wata wahala sabuwa. Daga nan zai fara sanin wahalar tashin safe, da
zuwa makaranta, da tsananin wasu malamai da tsarguwar wasu manyan
xalibai, da takurar wasu abokai. Bayan ya girma akwai hidimar aure da
zaven abokin zama a gaban sa. Sai rainon yara da hidimar tarbiyyarsu.
Neman abinci, da gida, da abin hawa, wata damuwa ce babba. Idan tsufa ya
zo akwai wahalar curutoci da jinya da raunin jiki. A tsakanin haka yakan
gamu da ciwon kai, da ciwon ido, da ciwon kunne, da zazzabi, da sanyin
mura, da waxansu curutoci daban daban. Idan ya zo mutuwa akwai jinya,
akwai wahalar fitar rai. Sannan kwanciyar qabari da tambayar Munkaran da
Nakiri. Bayan busa qaho akwai tsayin qiyama, da tsallakar Siraxi, da awon
ayyuka. Mazaunin xan Adam na qarshe shi ne gidan aljanna ko na wuta.
Kai, xan Adam! Ba ka da hutu sai ranar da ka yada zango gidan aljanna.
Tashi ka nemi samun tsira.

206.

Idan aka cuce ka, ka buxa baki ka ce: Allah ya isa, to fa ka xage kyas

xinka ne daga kotun qasa zuwa ta sama.

207.

Idan kana son sanin muhimmancin lafiya ka ziyarci asibiti. Don sanin

daxin 'yanci ka je gidan yari. Wanda bai gane muhimmancin rayuwa ba ya je
maqabarta.

35

208.

Agogo yana zagayawa ne a kan kowace sa'a. Haka rayuwa take

zagayawa da mu a kan yanayi daban daban. Yi haquri idan yanayinka a yau
bai yi daxi ba, wataqila gobe ne za ka yi dariya.

209.

Duniya kamar littafi ce; shafukanta yawa gare su. Wanda bai yawata

ba zai san shafi xaya ne kawai na duniya.

210.

Kibiya sai an ja ta baya sannan ake harba ta. Kai ma xan Adam wani

lokaci kana buqatar ka ja da baya don cim ma buqatarka.

211.

Idan ka qi gaskiya za ka faxa vata. Idan ba ka ji nasiha ba, za ka yi da-

na-sani. Wanda bai ji bari ba ya ji hoho!

212.

Abu huxu su ke maganin abu huxu:

- Maganin gajiya bacci.
- Maganin wahala hutu.
- Maganin musiba haquri.
- Maganin qiyayya kyauta.

36

213.

Duk wanda ka haxu da shi akwai rawar da zai iya takawa a

rayuwarka. Wani zai taimake ka, wani ya nemi taimakonka, wani ya so ka,
wani ka so shi, wani ya amfane ka, wani kuma kai ka amfane shi.

214.

Haifuwar namiji ba zavi ba ce, yin Allah ne. Amma zama Namiji

qoqari ne, sai wanda ya dage.

215.

Fahimtar sabon abu ba shi ne matsalar xan Adam ba. Babbar

matsalarsa ita ce barin abin da ya saba.

216.

Mai fushi da mai dariya, mai murna da mai kuka, duk ba za su hana

duniya tafiya ba. Hutar da rayuwarka kada ka sa damuwa ta hana rayuwarka
ci gaba.

217.

Savani a tsakanin miji da mata ko 'yan uwa ba shi ne matsala ba.

Babbar matsala ita ce mayar da savani dalilin adawa da gaba.

218.

Kukan yaro qaramin abu ne yake jawo shi. Idan ka ga babba ya koka

to lallai kam matsala ta vaci.

37

219.

Sallah abincin zuciya ce. Idan abinci bai wadaci jiki ba yakan lalace.

Haka ita ma zuciya idan ba a samu sallah mai kyau ba sai ta lalace.

220.

Komai yakan fara a qarami ne sannan ya girma. Amma ban da abu

xaya, shi ne; Musiba. Ita kam da girmanta take farawa. A hankali a hankali
sai ta fara ragewa, har ta vace gaba xaya.

221.

Duk abin da ya yi yawa zai rage qima in banda abu xaya, shi ne;

Ladabi. Shi kam duk ya qara yawa sai ya qara daraja.

222.

Duniya gonar lahira ce. Abin da ka shuka a nan shi za ka girba a can.

223.

Kurma yana son ya ji muryar jama'a. Makaho yana so ya gan su. Bebe

yana son yin magana da su. Duk Allah ya haxa maka wadannan a cikin "ji"
da "gani" da "harshe". Ka gode ma ni'imomin Allah.

224.

Ba za ka iya barin miki a jikinka yana tsiyaya ba. Haka ne bai dace ka

zauna dumu dumu a cikin zunubi ba ka tuba ba.

38

225.

Da yawan matsalolin da suke raba kanmu xayan biyu ne: Ko dai abin

da ake nufi ba mu fahimta ba, ko kuma wanda muka fahimta ba shi ake nufi
ba. Kyautata ma xan uwanka zato a kodayaushe, sannan ka nemi qarin
bayani idan ba ka gane ba.

226.

Kada ka yi dariya sai a kan dalili. Kada ka shiga cikin abin da bai

shafe ka ba. Kada ka tambayi abin da ba ka da buqatar sa. Kada ka zauna da
wanda ba ya voye asiri. Kada ka yi maganar da ba ta da amfani.

227.

Ba matsala ba ce idan kana bin Allah amma ba ka samu biyan

buqatarka ba. Tabbas watarana za ka samu. Babbar matsala ita ce kana
savon Allah amma yana ba ka duk abin da kake so. Watarana idan ya damqe
ka ina mai karvar ka?

228.

Abu biyar ana gane su daga abu biyar ne.

- Ana gane daxin bishiya ne daga 'ya'yanta.
- Ana gane haqurin macce ne idan mijinta ya shiga halin talauci.
- Ana gane mai imani idan ya gamu da jarabawa.
- Ana gane mai kyauta idan ya samu wadata.
- Ana gane gaskiyar xan siyasa idan ya ci zave

39

229.

Wanda ya samu ababe biyar sai a masa san-barka: Macce ta gari, da

xa mai ladabi, da aboki na kirki, da maqwauci na qwarai, da malami mai
faxin gaskiya.

230.

Ababe uku suna xaga darajar mutane uku:

- Ilimi yana xaukaka qasqantacce.
- Tsentseni yana xaga darajar mai ilimi.
- Kunya tana qara qimar 'ya macce.

231.

Abu uku suna vatar da wasu uku:

- Kuxi suna voye aibi.
- Gori yana rufe daxin kyauta.
- Tsoron Allah yana voye son zuciya.

232.

Ababe uku suna qarfafa wasu uku:

- Lafiya idan ta haxu da arziki.
- Bacci idan ya haxu da qoshi.
- Dare idan ya haxu da ambaton Allah.

40

233.

Idan kana cikin damuwa ka jira samun sauqi daga wurin Allah,

wannan jiran da kake yi ibada ne. Domin kyautata zato ne ga Allah. Wanda
ya kyautata ma Allah zato kuwa lallai ne Allah zai ishe shi.

234.

Babban mabuxin alheri shi ne Istigfari. Idan ka yawaita shi

matsalolinka za su kau, damuwarka za ta gushe, sauqi daga ubangiji zai zo
maka.

235.

Rayuwa ta karantar da mu cewa, duk abin da yake xorewa sai an sha

wahala wajen samun sa. Abin da duk aka same shi da sauqi kuwa ya fi
saurin kubcewa.

236.

Ya fi kyau ka haska kyandur guda xaya a kan ka la'anci duhu sau xari.

237.

Duk abu mai daraja rufe shi ake yi. Daddaxan abinci a kwano ake sa

shi. Ayaba da gwadda da kankana da abarba da Aful da Mangoro duk a
lulluve mahaliccinmu ya yi su saboda darajarsu. Haka ne 'ya mace take,
tsadarta ke sa ta yin lullubi.

41

238.

Idan ka ga mutane suna yabon ka akwai alherin da suka gani a gare

ka. Akwai kuma wani aibinka da Allah ya voye daga idanunsu. Ka gode ma
Allah a kan suturar da ya yi maka.

239.

Ladan yana Kiran sallah. Rediyo yana Kiran sallah. Kwamfuta tana

yi. Agogon hannu da na bango duk suna faxa mana lokacin sallah. Amma
duk da haka muna makara zuwa masallaci. Allah ya shirye mu.

240.

Abokai na gaskiya suna da wuyar samu, suna da wuyar bari, suna da

wuyar mantawa.

241.

Maigida bango ne, mutan gida su ne allo abin jinginawa.

242.

Halin ‘yan Adam akwai mamaki. Sai su ce Allah suke so, amma suna

sava masa. A kullum suna la'antar Shexan amma kuma suna biye masa.

243.

Zamani ya canza: A da idan ka zagi wani kowa sai ya kau da kansa. A

yau idan za ka ci naman xan uwanka har ruwan wanke baki ake ba ka.

42

244.

Mai sadaka ba kashe kuxinsa ne yake yi ba. Yana shigar da su ne a

wani asusun ajiyarsa.

245.

Abu nawa ne Allah ya ba ka baka roqe shi ba? Ka tabbata idan ya

hana ka abin da ka roqa to, akwai dalili.

246.

Da shekara Arba'in ake ce maka “Baba”. Da su kake yin furfura,

ganinka ya fara ragewa, lafiyarka ta fara ja da baya. Da su kake gano daraja
da matsayin naka iyaye. Idan ka yi Arba'in ya dace ka sake nazarin
rayuwarka, ka shirya da ubangijinka, ka nemi gafarar zunubinka, sannan ka
gyara aikinka. Allah ya bamu ikon gyara.

247.

Mafi munin hali ga xan Adam shi ne Rowa. Abin da ya fi ta muni shi

ne ka ba mutum sannan ka yi ma sa gori.

248.

Idan ka qi gaskiya don gudun xacinta, ka xanxani qarya don kwaxan

zaqinta, watarana sai ka nemi maxaci don ka wanke cikinka.

43

249.

Abu biyu ne suke sanya aure ya yi qarko:

- Idan ba ka da gaskiya ka amsa rashin gaskiyarka.
- Idan kana da gaskiya ka yi shiru.

250.

Duniya kamar inwarka ce; duk inda ka tafi za ta bi ka, amma idan ka

tafi neman ta za ta riqa gudu, kuma ba za ka tava cim ma ta ba.

Alhamdu Lillah
Mu haxu a fitowa ta biyu cikin yardar Allah

44


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya





Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment