Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za'a aura mini,ban san ko waye ba a cikin ƴaƴan nasa, shi ma Dad wai ya amsa shi zan aura,ni kuma bana son shi, koma waye a cikin su, duk azzalumai ne fa."

Na saka kuka na miƙe na cakume shi.ina ji ya saukar da ajiyar zuciya, ya ɗago kaina.

"Haba Yasmin ƴar ƙanwata,ki yi tunanin irin son da Dad yake nuna miki yanzun haka in za ki buɗe zuciyar Dad shima baya so, Amma,zan je in tabbatar da me yake faruwa."

"Kada ka gaya masa cewa na ce bana so."

"Ba zan faɗa ba,kin ji ƙanwata."

Ya goge mini hawayen fuskata,sannan ya juya ya fita.

Bayan mintuna hamsin ne Yaya ya shigo, ya yin da ya nuna mini sai dai in ta addu'a kawai, saboda aurena ba fashi, yanda yake gaya mini ma har sun tsayar da ranar ɗaurin aure, da sarki Jafar,nan da wata biyu shi ma domin mu samu shaƙuwa da juna.

Iya bayanin da Yaya ya yi mini kenan, ya fita shi ma jikinsa a sanyaye, ban taɓa shiga tashin hankali ba tun da nayi wayo sai a cikin ƙwanakin nan tara, ban taɓa tunanin za'a samu abin da zai girgiza min zuciya ba, amma yanzu ga shi na samu wanda Yake neman kawar mini da tunanina.

Yau ƙwana goma sha bakwai da zuwan sarki Jafar kenan ya rage saura ƙwanaki arba'in da uku yinin bikina, sai yau ne aka ce ai ga Faysal wanda zai zama angona, duk da sanyin da ake yi, amma sai da na ji tamkar an watsa mini ruwan zafi.

Mamee ta shigo ta umarce ni da in shirya in isa falon Daddy na yi baƙo, lallashi, nasihohi,Mamee ta dinga yi mini na kada in nuna masa halayyar sakarcina. Ni kuwa ba ta san gani nake ma ba ta ƙaunata.

Dogon siket da riga ne,ƙirar ƙasar Japan nasa a jikina, dogayen hannu gare su har idon hannuwana,buɗaɗɗan wuya gare su tamkar irin ɗinkunan da ake ya yi yanzu a Najeriyarmu, sai dai tare yake da ɗan ziririn mayafinsu wanda za mu iya cewa iya wuya kawai ya tsaya.

Mamee ta lulluɓa mini shi, ta sako leɓe ɗaya a gaban ƙirjina,ɗayan kuwa ya nufi bayana, gashin kaina kuwa yana can baya aka tattara shi, sai ƴan ƙwayoyi da ta ɗan gyara mini su ta sako su gefen fuskata, wanda ya bi ƙirjina ya ƙwanta.

Na sha turare da gyaran fuska, abin ka da kalar ruwan ƙasa mai cizawa ne,siket ɗin sai ya yi mini ƙyau,rigar kuwa baƙa ce mai ƙyalƙali a gabanta, ɗan mayafin kuwa kalar siket ɗin ne,baƙaƙen takalma na saka a ƙafata, waɗanda suka yi daidai da rigar, na ɗauki baƙar wayar hannu na riƙe a hannuna.

Kafin in yi sallama in shiga, sai da na leƙa ta kafar labule,jiri ne yasa na koma baya da ƙarfina, na sulale ƙasa na zauna, wanda na samu da ƙyar na isa ga bango na jingina,gumi ne ke ta tsatstsafowa daga jikina,a take na ji yunƙurin amai a lokacin da cikina ya juya.

Cikin zafin nama na yi gudu zuwa ɗakin Dad ɗina,na shige banɗakinsa,amai kam tamkar in zazzago kayan dake cikina, na samu da ƙyar na ƙwaye shantalin matsatstsan siket ɗin jikina na gabatar da fitsari mai yawan gaske, daidai lokacin da aman ya ɗan tsagaita mini.

A saman tudun da ake tsugunnin lalurar bahaya anan na zauna, tsayin mintuna goma, sannan na samu da ƙyar na ɗauraye jikina na miƙe, isa na yi ga madubin da ke manne a jikin (Wardrobe) ɗin Dad na kalli jikina yanda na faɗa a lokaci ƙanƙani, sannan na zauna saman wata ƴar kujera mai ɗan tebir a gefenta na kunna ƴar ƙaramar fankar da take a samanta, wacce zan iya cewa daidai fuskata kawai da wuyana take baiwa iska.

Shi ma domin in samu gumin da ke fitowa a jikina ya tsaya, ɗan wanda ya fito kuma ya tsotse. A take kuma dabara ta faɗo mini na in dinga karanta "Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un!"

Cikin ƙanƙanin lokaci na ji na samu nutsuwa, na isa ga gefen gadon Dad,na ɗauki farar butar da Mamee ke ajiyewa, domin gyarawa Dad fuska, na ƙara gyara tawa fuskar na fice, sai falon Daddy,inda baƙo ke jirana wanda ganin shi ya tayar mini da hankali,wai shi Yarima Faisal.

Na yi sallama na shiga,a lokacin da wasu mutum biyu ke zaune a ƙasa a kowanne gefensa, biyu kuma na tsaye saman kan shi gefe-gefe, biyu na bakin ƙofa a tsaye, sun saka ƙofar a tsakiya ɗaya ne ke tsaye tsakiyar kanshi ta baya yana firfita shi da wannan ƙaton maficin nasu.

Da ƙyar ya ɗago ido ɗaya ta gilashi ya kalleni, maimakon in ga ya nuna razana da mamaki,sai dai na ga ya ɗan yatsina fuska, ya ƙara gyara ƙwanciya a kusurwar kujera ya kishingiɗa, sannan na ga ya ɗan ɗaga hannu kaɗan.

Sai na ji sun ɗauki magana gaba ɗayansu na tsaye duk sun yi saurin zubewa suna cewa.

"Takawarki lafiya,ƴar manya, Gimbiya taka a hankali ƴar ƘASAITA,matar ƘASAITA,Yarima na gaishe ki,yana yi miki sannu da isowa."

Ɗaya daga cikinsu ya yi saurin isa kujerar da zan zauna yasa wani abu mai kyau kamar abin sallah ya shinfiɗa mini, ɗaya kuwa ya yi saurin isowa bayana da ƙaton maficin nasu ya fara yi mini fifitar tun Ina tsaye.

A take nima na fara nuna irin tamu isar ta mata, na zauna tsakiyar kujera na mayar da ƙafa ɗaya a kan ɗaya na ɗora, ina ɗan juya jikina a hankali. Yarima Faisal mutumin da muke takun saƙar ƙiyayya da shi,mutumin da ya kaɗe ni da mota, kamar ya banke akuya, shi ne yau ya zo wajena a matsayin mijin da zan aura mu yi zaman aure mai tsayi, na gani.

An ɗauki mintuna goma, gaba ɗayan falon shiru yake, sai masu gadin ke cewa ana gaishe ni, can sai ɗaya daga cikin waɗanda ke ƙasa zaune ya fara magana.

"Allah ya taimaki Sayyada, Gimbiya, ɗan Sarkin Sarakuna,Yarima na gaishe ki, kuma mun zo nan ne domin amsa gayyatar da ki ka yi mana ta alheri, wannan da ki ke gani dai shi ne Sadukul ummati."

"Eh,Yarima kenan wanda yake jiran gado,yau ko gobe ko anjima ma."

"Haka yake, gaskiyarka ne, Sarkin dogarawan zamani."

"To shi ne muka zo a kan...."

Na ɗago masa hannu, ya yi saurin cewa,"Dole ne in bi umarni,shiru ma hankali ne, godiya nake."


*ƘASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 7


Sai da na yi yatsina nima na ɗaga baki da ƙyar na yi masu magana.

"Ku fita gaba ɗayanku ina son yin magana da shugabanku."

"Godiya muke, Allah ya daɗa girma, umarninki ne abin bi."

Suka sunkuya gaba ɗayansu gabanshi.

"Mun barka lafiya."

"Eh, Gimbiya ce ta bayar da umarni."

Ya ɗaga kai yana ɗan jingina shi,wato ya amsa kenan,wai! ƘASAITA. Ya amsa,eh, ya ce ya amsa godiya muke. Suka bi layi suka fice ƙofar waje.

"Yau fa ake yin ta!" Na faɗa a zuciyata, saboda na ga yanda za'a yi a yi magana tsakanin ni da shi. Mun ɗauki minti goma sha biyu kenan, ba wanda ya yi cikakken motsi a cikinmu, na ga ina ɓatawa kaina rai da lokaci, sai na miƙe na isa ga ɗan ma'ajin takardun Dad na ɗauko biro da takarda.

"Me ya kawo ka ne?"

Shi kawai na rubuta na miƙe na isa na miƙa masa, sai da ya ɗauki mintuna biyu, sannan ya miƙo hannu ya karɓa.

"Cewa aka yi in zo in gani in kinyi mini." Na karanta,a lokacin da ya taso shi ma ya miƙo mini.

"Ka koma ka gayawa wanda ya turo ka na ganka, cewa ba ka yi mini ba,ni Yasmin a ƙara gaba." Na miƙa masa.

Sai a lokacin ya ɗago kai ya kalleni, sai na ga ya yi murmushi, irin na isa ya mayar da kan shi.

"Dole ma in yi miki, tunda mu ba ma saɓa maganar iyayenmu,ki sani, ba ki tsarin cikin matan da zan iya aure, darajar Sarki kawai za ki ci." Ya miƙo mini.

"Ka tuna,ni ce wacce zan zame maka masifa, idan kuma ka kuskura ka tsallake ɗaya daga cikin dokokin da zan dinga gindaya maka, zan bayyanar da boyayyen sirrinka a gaban Sarki!"

"Na gama da ke, tun da zan zamo mijinki."

"Ba ni da lokacinka, ina kuma gargaɗinka." Na miƙa masa, na koma cikin gida.

Ina laɓe ta labule na ga ya rubuta wani abu ya ajiye, sannan ya yi gyaran murya, sai ga su sun shigo a guje, ina kallo ya yi wa ɗaya daga ciki magana, amma ko shi wanda ake wa maganar sai da ya sunkuyo kusa da shi sosai, sannan ya ji abin da ake cewa, to balle ni da ke laɓe a bayan labule.

Cikin rawar jiki na ga ya sa hannu a aljihu ya fito da wasu dogayen takardu da biro ya miƙa masa da sauri ya sunkuya bayanshi, sai na ga ya ɗora a kai yana rubutu, ya ajiye.


Sorry,kin ji." Na ɗaga kaina.

"Thank you."

"Je ki ciki kiyi hidimar ki zan zo miki da labari mai daɗi, nima dama ba san auran nake ba,ke tashi ma mu tafi tare,in ajiye ki gidan Salwa da dare na aiko a ɗauke ki kin ji?" Na ce to.

Na miƙe na shiga gida na ɗauko ɗan guntun mayafi na rufe kaina da shi, wanda riga da siket ne na atamfar Super Holland ce a jikina wacce ake kira da suna A daidaita Sahu, inji mutanen Kano,mu kuwa muke ce mata Open Neck.

Da kuka na shiga gidan Aunty Salwa.

Aunty Salwa ta Zauna ta dinga lallashina ina gaya mata abin da ke damuna, da ƙyar na ƙwashe labari na gaya mata, tun farkon haɗuwata da shi da irin fansar da ya ɗauka a kaina,Ni kuma da ramuwar da nayi na ba ta takardar zancen da muka yi da shi yau da ƙarfe uku.

Ta yi shiru na tsaya kusan mintuna taƙwas, sannan na ga ta juyo da hankalinta gare ni.

"Haba Yasmin,kada ki bayar da kanki fa, kada ki zubar da ajinki,ki tuna ke ce macen da ya kamata a ce kin tsunduma kanki gidan sarauta, saboda ƙyawun da Allah ya yi miki.

Ki kalleni ki gani,ƙyawuna fa ya sani auran ɗan manyan mutane,ki sani dama fa ajinmu ya wuce na ƙananan yara, balle ƴaƴan talakawa."

"Gaskiya Aunty ni dai ina son Anwar,ko da kuwa zai dinga yin dako yana ba ni abinci ni shi nake so, balle fa da aikinsa."

"To yanzu Yasmin ya ki ke so ayi miki? Mu haɗa kai mu kunyata mahaifinmu,ko kuwa? What do you want?"

Ta matso ta ƙara dafa ni.

*Haba ƙanwata me yasa ba zaki haƙura ki bi umurnin iyayenmu ba, alhalin su suna yi mana abin da duk muke so,in na tambaye ki zaki iya ba ni amsa tsakaninki da Allah?"

Na ɗaga mata kai, saboda kuka ya hana ni magana.

"Ba shi da ƙyau ne?"

Nan take na karanto fuskarshi a idanuwana, tabbas ƙyakyƙyawa ne, wanda ba zan iya misalto ƙyansa ba, na tuno ƙwayar idaniyarsa da ta kalleni fara ƙal, kamar kullum a ruwa take ajiye,ƙwata miliyan ɗin gashin bakinsa kuwa daidai fuskarshi.

Na ɗan nutsu ina tunano mai irin gashin bakin a take na tunano (Craig David), shahararren mawaƙin turanci, sai dai na san Faisal ya fi shi ƙyau nesa ma ba kusa ba, sannan shi Faisal fari ne, irin farin da za mu iya cewa yalo-yalo.

"To me ye baƙya so ne a tare da shi, wanda har yasa ki ka tsane shi?"

Maganar Aunty ta dawo da ni daga karanto fuskar Yarima da nake yi,ni taƙamar shi ce take ba ni haushi, kamar fa shi ne Sarkin fa, yanda mutane ke yi masa, Aunty ga shi azzalumi ne,kin ga gidan yarin da ya kai ni kuwa, wallahi sai kin yiwa mutanen ciki kuka,in kuwa kina da saurin jin tsoro,ke da bacci sai an dage da yi miki addu'a."

"To shi kenan ma,kin ga yanzu aikin samun lada ma ya zo gare ki, sai ki yi haƙuri,ki aure shi ko don taimakawa waɗanda ke gidan yarin a sannu kuma duk ki san yadda za ki yi ki raba shi da halayyar da ba ƙya so,miji fa Yasmin dole ne fa ki juya shi. Yasmin kin ma bani dariya ko da yake dole ne,ki ruɗe tunda har yanzu yarinya ki ke,ko me sanin ki da namiji miji ya fi shi.

Tunda shi namijin waje zance ne kawai da kalaman so, amma fa kuma ki sani duk inda sarauta take, aƙwai ƘASAITA, ta musamman a wajen, ba kuma za ki iya raba jinin sarauta da ita ba ke duk sarautar da ba ƘASAITA,ai zaki ga ma ba ta da ƙarfi, saboda haka, kema fa sai kin koya."

Hankalina ne naji ya ƙara tashi, kenan ni ba ni da mai goya mini baya? A nan take na yi tunanin ko in gudu zuwa Adamawa su ma in gaya masu,wataƙilan na samu a raba ni da wannan auran. A take na yi tunanin ban ƙyauta ba, tunda ban cewa Dad ba na so ba,bai kuma sani ba, balle in ce ya tilasta mini.

Ba ni da wata hanyar fita, maigadin gidan Aunty ne ya shigo da rawar jiki wai an yi baƙi, Aunty ta tambaye shi maza ne ko mata? Ya bata amsar maza ne. Ta miƙe ta shiga ɗakin mijinta Uncle Abdulƙadir ta gaya masa, doguwar riga ce ta shan iskar maza ce a jikinsa ya fita.

Cikin mintuna baƙwai sai ga shi ya shigo a nan ne yake gaya mana,Yarima ne yake nema na, saboda haka mu bayar da falon zai shigo. Takaici zan ce ko baƙin ciki,ko haushi,ni dai zan iya haɗa su gaba ɗaya in ce su ne a zuciyata, amma sai na ga Aunty har da turaren Humra ɗan Maiduguri shafa mini, ban da wanda ta fesa mini ta ja ni da tsiya sai na yi ƙwalliya kada ya fahimci na yi kuka.

Amma na ƙiya, na ce gara ya san ba na son shi tun yanzu kada ma ya yi tunanin son shi nake yi. Bayan ƴan mintuna ne na fita falon a inda yake da gayyar jama'ar nan tasa da ke bin shi ko'ina, haushi ya ƙara kama ni.

Kafin in Zauna ma na yi masu alama da hannu su fita da rawar jiki da kirarin nan nasu suka yi waje, sannan na zauna fuska a ɗaure, cikin sakan uku ma na jini ba na ma son ganin shi, na mayar da kaina na kifa a cinyata.

Ban ɗago kaina ba, amma daga ƙwancen da kaina yake na karkato na kalle shi, bayan mintuna kamar goma da zamanmu falon wanda ya yi tsit, shi ma maganar da naji ya yi ita ta bani mamaki wacce ya yi cikin sanyin murya.

"Sorry about what happened last time Sarki ne ya yi mini faɗa sosai, ya ce inzo in ba ki haƙuri."

Ina kallonshi daga ƙwanciyar cinyar nan da na yi,yasa hannu ya cire gilas ɗin fuskarshi ya ajiye shi gefe ɗaya, sannan ya miƙe tsaye ya iso inda nake zaune, ban ko motsa ba, ya miƙo mini ambulan ƙatuwa mai ruwan (pink) na sa hannu na karɓa,bai ce komai baya ya juya ya tafi. Ina kallo ya mayar da gilashin fuskarshi ya juya ya ƙara kallona, sannan ya yi gaba.

Na miƙe na shiga ɗakin Aunty,tana ƙwance a gadonta, na miƙa mata ambulan ɗin. Aunty ta buɗa, sai ga katin ban haƙuri ƙato,dana nuna ana son ka,I love You, Greeting Card,sai takarda inda muka buɗe muka karanta.

"Ni ma ba da son zuciyata zan aure ki ba, saboda ba zan iya yi wa mahaifina gardama ba, na san abin da ke damun ki, shi ne baƙya sona, kamar yanda nima zuciyata take ƙuna in na tuna ba ni ne na zaɓi matar da zan aura ba.

A matsayinki na mace kuwa, na san ke taki zuciyar tafi tawa ciwo da ƙuna, da tsana ta, amma ki yi haƙuri, rayuwar da muka tsinci kanmu kenan."

Husband

Na ƙara narkewa da kuka.

"Aunty bana son shi, Aunty guduwa zan yi."

"Ai kuwa da kin yi wayon banza,a ce kin wulaƙanta naki uban a idon duniya, namiji ma ya yi haƙuri ya bi doka da umarnin iyayensa, sai ke mace. Haba My sister don't be a silly girl mana."

Ta taso ta iso inda nake ƙwance, ta ɗago ni ta rungume.

"Ki tuna Yasmin mu uku kaɗai mahaifinmu ya haifa,ki tuna gaba ɗayan duniyar nan mu ya sawa ido, ya ga mun zama ƴaƴa nagari,ki tuna cikinmu ba wacce yafi so da ƙauna sai ke,mu ƴan uwanki mun sani, duk wanda yake tare da Dad ya san ke yafi ƙauna. Ki tuna ba shi da iyaye sai mu kawai gare shi.

Amma a ce kece za ki ci mutumcinsa a idon duniya. Haba Sister, kada ki yi mana haka mana,haƙuri shi ne naki,kin san halin sarauta, yanzu haka an gama aikawa duniya da katikan gayyatar bikinku,ko kin manta,ki duba ki gani fa yanzu, duk iya sarautar Sarki, amma Dad ya je ya tunkare shi da maganar da ki ka gaya masa ta game da ɗansa,kina kallo ko awa ɗaya ba, sai da ɗanshi ya dangane da inda ki ke ya ƙasƙantar da kansa ya ba ki haƙuri.

Haba Yasmin ya ki keso Daddy ya yi, ya goya ki ko kuwa ya saki Mamee ya aure ki? Iya kacin so kenan. Ke ma Yasmin kin san Dad ya nuna miki shi a fili,ni dai shawara ta a nan shi ne, ki yi haƙuri a yi auranki lafiya,ki nuna murna da farin cikinki a fili duniya ta gani, amma da an gama biki,ki ja matsayinki na mace.

Wato ki zauna matsugunin ɗakinki har nan da lokacin da ya kawo kan shi gare ki, ya ajiye duk wata taƙama da ƘASAITA gefe ɗaya, ya zo ya roƙi arziƙin kanki da kanki, amma da me? Kin san gidan sarauta da akwai girma, balle na Sarki Jafar, saboda haka sai kin ajiye komai kin dinga fita shan iska, cikin ƙwalliya mai jan hankali da sauran hidimomin da za su iya janyo miki shi.

Ki tuna Yasmin,ke mace ce fa, wacce ko tsoho ya hango ki sai ya yarda sandar hannunsa dan ƙyau,dirin jiki, gashi Yasmin ba inda Allah rage ki, balle ki ce,ni nasan dole ne ma ya so ki. Ki tuna ke mace ce,son ɗa namiji baya wuyar shiga zuciyarki,ki tuna mu mata haka Allah ya halicce mu, balle ma kin ce shi ma ƙyakƙyawa ne."

Aunty ta samu wajen awa ɗaya tana ta lallashina, har muka koma falo,mun buɗe talabijin, gidan talabijin na kasa N.T.A ya ƙyallo sanarwar auranmu da harshen Turanci.

_His Highness, the Emir of Plateau, wishe to invite the general public, to the wedding ceremony of his son,Prince Faysal,on 27th June, 2005, at Emir's place at Jos._

Hankalina ya ƙara tashi, na miƙe na canja tasha na mayar gidan talabijin ɗin jaha na dawo na rabka tagumi. Aunty dai ba ta ce komai.

Ƙarfe taƙwas da rabi na dare su Aunty suka mayar da ni gida ita da mijinta Uncle Abdulƙadir. Na samu Dad shi ma da Mamee a falonmu na gida suna ta hirarsu.

Mamee kuwa ƴan bautar aure ana ta yiwa Dad susa a kai, har ma sai na ji kunyarsu ta kama ni, abin da ban taɓa ji ba ko don an ce za'a yi mini aure ne? Oho. Ya zaunar da ni ya ƙara yi mini nasihohi da ban haƙuri da sa mini albarka.

Kalaman da ya yi amfani da su,su suka ƙara ƙwantar mini da zuciya na ji na haƙura. Haka ma Mamee kullum sai ta yi mini huɗubar da zata ƙara ba ni ƙwarin gwiwa.


*ƘASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 8


Yau ne ranar juma'a, wanda ya kama ashirin da bakwai ga watan Yuni, wacce ta zo daidai da ranar ɗaurin aurena da Yarima Faysal mutumin da sai a wajen harkar biki muka haɗu da shi, tun a ranar da ya je gidan Aunty rabona da shi. Gaskiya ni kaina na san na gaji da hidima kala-kala, wanda tun saura ƙwana goma ɗaurin aure ake ta yin ta.

Garin Jos kuwa,ba masaka tsinke, wanda a wajen hidimomin nan na dinga ganin manyan mutanen da sai a talabijin nake ganinsu. Tsayawa ambatan fatikan da hidimomin da makaɗan da suka halarci wannan hidimar aure namu,ɓata lokaci ne saboda Allah ya yi yawa da su.

Abu ɗaya ne ba zan manta ba, shi ne ƴan wa'azin da suka kai mana ziyara,a matsayin gudummawar su, wanda suka yi a babban masallaci na Jos washegari da aka kai ni gidan Yarima kenan, ranar Lahadi a kan biyayyar aure suka yi shi. Tabbas a ranar jikina ya yi laushi, amma ragowar hidimar sai dai in ce Alhamdulillahi.

Riƙe nake da Daddy gam,ina ihu zan ce ba kuka ba,a lokacin da ya gama yi mini nasihohi wanda zan iya cewa uba ke yi kafin a kai ƴarsa gidan miji, wanda suka haɗu da ragowar ƴan'uwansa aka yi mini,fita da ni daga falon Dad ita ce ta zamo tashin hankali.

Da ƙyar mata suka ɓanbare ni daga jikinsa. Ganin yanda nake yi ne yasa Daddy ya ce su tafi, zai kai ni da kanshi daga baya. Hakan yasa sai dai aka lulluɓa wata abokiyar wasata aka fita da ita a matsayin amarya.

Ni kuwa har goma da rabi na dare,Daddy nata lallashina da ƙyar na amince, shi ma sai da ya yi mini alƙawarin gobe tun da safe zai je gidan,in ya ga ban haƙura ba zai dawo da ni, kai ni kaina na san dai wayo kawai ya yi mini.

Duk da na san dai shi kanshi dole ta sa zai rabu da ni,kari da ganin hankalin Dad ya yi mugun tashi har yana zubar da hawaye ganin yanda nake kuka, har da neman shiɗewa.

Da lallashi da ban magana,Daddy ya kaini har gidan Faysal, shi da kanshi ya rakani har cikin ɗakin da yake nawa bayan nan ma sai da ya ɗan zauna ya ƙara yi mini ƴan maganganun da za su ƙwantar mini da hankali, wanda sai da jama'a suka ɗan ba mu fili, saboda yawa, amma duk da haka da zai tafi sai da na ji hankalina ya yi mugun tashi.

Abu ɗaya ya hana in bi shi, ƴan'uwa da ƙawayena da sauran waɗanda suka isa a kaina, kamar ƙannan Dad da na Mamee,da suka riƙe ni suna lallashi, dole dai ta sa na haƙura. A wannan rana sai da aka bar mini mutane daga gidanmu suka ƙwana, har da ƙawayena,ganin Aunty Salwa ta ƙwana,shi ma ya ƙara taimaka mini.

Sabuwar hidima ce ta ɓalle da gari ya waye,taro a cikin ariyar (area) gidan Sarki tamkar yau aka fara bikin, tun daga get kuwa har izuwa cikin gidana, wani sabon biki ma ni zan ce ake yi. Yamma na yi kuwa, sai hawan Daba ya tashi ranar Litinin kenan.

A al'adarsu,wai amarya da ango ke fitowa saman gidan Sarki, Sarki da tawagarsa a gefe ɗaya, ango da amarya a gefe ɗaya a sama. To sai a dinga kawo gaisuwa, dole ta sa na shirya, saboda Aunty na nan, ban da sauran dangin iyayena,ƴan Syria,kuwa suna can wajen Mamee suna taya ta zama.

Sai da muka kai gaisuwa wajen Sarki, sannan muka wuce ni da Yarima muka zauna, baya ga ƴan bi baya da muka samu, tun daga fitowata, kafin ma in iso inda Yarima ke jira na,a nan zaune har sai da aka yi kiran Magriba, tsakani da Allah na ga girmamawa da ƙauna a wajen jama'a. Wannan tasa ma na saki jikina.

Ranar Talata kuma amarya da ango ke zuwa gidan Sarki na cikin gari, amma iyakacinmu fadarshi aka gabatar da mu ga manya-manyan hakiman Sarki.

Daga nan kuma sai zuwa gaishe da iyayensa, shi Sarkin wanda dangin amarya ne ke raka ta, kuɗi,ƙyaututtuka kuwa,wai na sha su,ni kaina na sake da irin ƙaunar da ake nunawa Faysal, na san kuwa iyayenshi suka fara nuna masa ita.

Ranar Laraba,a ranar ango ke yin tashi walimar da abokanansa, saboda gabatar da amaryarsa a gare su, ita ma ta san su, sannan da ƴan ƙawayenta ko su goma ne,a wani babban wajen taro na manya. Iyakaci na da Faysal wajen hidimar auranmu, da mun iso gida, kowa hanyarshi yake nufa,dama kuma ba mota ɗaya muke shiga ba,ni da motocina, shi ma da nasa.

Ranar Alhamis ita ce ranar da na ga kowa na tafiya, wasu da safe, wasu

2 Comments On KASAITA 1
avatar
khadijat-6-8

5 months ago

Reply

Thanks

avatar
khadijat-6-8

5 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment