Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*ƘASAITA BOOK 2*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 1


Ƙwana na yi ina juyi gudun kada ya je ya sanar a gidanmu, saboda na ga alama ba shi da kunyar kai ƙara, tun da ya kai ƙara ta ga Aunty.

Ganin an wayi gari lafiya, shi ne na yi wanka na saka kayana doguwar riga ce mai ruɓi biyu, ƴar Saudiyya za mu iya kiranta ko Dubai. Na fito daga gidan ko ɗankwali babu kaina na nufi bakin dutsen da nake hutawa na yi tsaye.

Lokacin kuwa ya nuna ƙarfe taƙwas na safe kawai wanda na ce na yafewa su Mansura rakiyata,ko kalaci ban tsaya yi ba. Ina tsaye nan ina ta saƙa abubuwan da na san ba zan samu ba,wato Yarima ya ji haushin maganar jiya ya ce ya sauwaƙe mini inje in auri Anwar, na ɗaga kaina jikin barandar ɗakinsa, sai na hango shi zaune a kujera ya ɗora ƙafafunsa a saman tebir ɗin gabansa.

Na juya abina, sai ma na tattaka na haye dutsen, tsayin minti sha biyar na yi sai na ji ina sha'awar shiga ƙoramar nan,ta hanyar tattaka duwatsun da aka jera layi da su, waɗanda suka yi cikin ɗan dajin inda ruwa nan ke nufa,su kuwa duwatsun babu ruwanka da taɓa ruwa idan dai har ka sa ƙafarka a kansu.

Nan take na saɓule takalman da ke ƙafata, na sulala cikin ruwan inda na dinga taka duwatsun a hankali, na yi tsaye a wurin ina ta waiwaigawa sai na hango barandar Faysal,ai kuwa juyawar da zan yi ina tsaki, sai na ga wani ƙaton miciji ya nufo inda nake tsaye, ta cikin ruwan nan kanshi a buɗe yana ta huci ban san lokacin da na yi baya da sauri ba ina ƙwalla ihu. Cikin ƙanƙanin lokaci ya tari gabana babu zancan iya motsi a yanda na ga yana hucin.

Runtse idanuwana na yi na dinga ƙara,tun ina ƙarar har ya kaini ga kiran Yarima. Saman ƙafata ya kai wa sara, sai dai naji gab,na yi wata irin ƙara, na buɗe idanuwana, sai kuwa na hango Yarima Faysal a guje shi da wasu a bayansa.

Sai na dinga cewa, "Maciji! Maciji!! Bai wani tsaya tattaka duwatsun nan ba sai dai kawai na ganshi da gudu a cikin ruwan, wanda ganin da nake masa dishi-dishi ne, daga nan kuwa sai dai na dinga jin maganganun mutane sama-sama, sai kuwa ji na yi ana jijjiga ni da kiran sunana da nake jin ana yi.

Ina jin ƙasa na juyawa da ni, sannan ina ji sama-sama Yarima na daka masu tsawa zan iya cewa ɗaukata ya yi cak ya koma gudu, amma daga nan ban ƙara sanin komai ba.

A hankali na dinga motsa idanuwana,alamar ina son buɗe su, ina cikin haka na ji Yarima na kiran sunana. "Yasmin! Yasmin!!" Sai na ji yana dafa goshina.

"Ta motsa?" Na ji an tambaya.

"Eh,tana motsa idanuwanta."

Na samu tsayin minti biyar a haka, amma na kasa buɗe idanuwana, amma ina jin abin da ake faɗa. Jin abu mai sanyi a goshina, shi ya ƙara taimaka mini na ji hular idanuwana ta saki daga nauyin da ta yi mini, idanuwana Faysal suka fara gani zaune gefen gado,yana ɗora mini abin nan mai sanyi da nake ji, sai na ga ya yi saurin jefar da shi ya ɗago kaina ya rungume a ƙirjinsa, ya yi wata irin ajiyar zuciya. Sannan na ji ya ce, "Ta tashi." Ya mayar da ni ya ƙara gyara mini ƙwanciya,sannan ya sumbaci goshina, bayan nan kuwa mutane suka dinga leƙowa suna yi mini sannu, idanuwansu kuwa jajir kamar suna ciwon idon Afolo.

Da ɗaiɗaya duk na fara gane fuskokinsu, amma matan,mazan ban san kowa ba,gwara ma ƴan na kusa da shi da ba su fi Biyar ba, ƴaƴan ɗakina kuwa har wannan lokacin kuka sukeyi.

Bayan kamar minti sha biyar duk suka fita,a inda Yarima ya miƙe shi ma ya ɗauki wayar hannu, ya fara daddannawa.

"Barka da yamma,eh, yanzun za ta yi minti ashirin, Eh, tana gane mutane, a'a ban duba ba, to yanzun zan duba. To sai kun zo,Mama da wuri don Allah yanzun ko, to zataji." Ya juyo ya yi mini murmushi.

Sannan na ga ya cigaba, "Barka da yamma, eh, Yarima ne. Eh,Mamee, yanzu ta yi minti ashirin da ɗaya,a cewa Daddy ya zo yanzun ta gan shi. To Mamee ai kamawa ta yi,to, to zataji, to sai kun iso, to a huta lafiya, eh tana ƙasa, eh, na san yanzun zata hayo,kin san ƙwana biyu bacci ina jin bacci ne ya ɗauke ta,a ɗakin ƙasa, to za'a taso ta, mungode."

Ya dawo ya zauna gefena ya matso kusa da ni sosai, sannan yasa hannunsa ya shafa gashin kaina, ya ƙara gyara mini gashina zuwa gefe, "Sannu." Ya ga dai ban amsa ba, sai na ga ya juyo sosai.

"Yasmin,kina jina? Yasmin?" Sai na ɗaga masa kai, sai na ga ya ɗan mayar da numfashi tare da lumshe idanuwa, ya yi saurin kai min sumbata a kumatuna.

Ya tashi a hankali sai na ga ya buɗe bargon da yake lulluɓe da ƙafa ta, sai a lokacin na tuna da cewa fa Maciji ya sare ni, nayi ƙoƙarin motsa ƙafar, na ji ta kamar dutse, ina kallo ya ɗaga ƙafar tawa a hankali, yasa hannu ya ɗan shafe ta.

"Ƙafar ta mutu ko Yarima?" Na faɗa da muryata irin ta marasa lafiya.

Ya rufe ya zagayo ya kama hannuna tare da zaunawa a gefena, wanda ƙafarshi ɗaya ya ɗago ta duka ya lanƙwashe ta har sai da gwiwarsa ma ta ɗan hau saman cikina.

"Bata mutu ba,za ki warke sosai ma." Ya sumbaci hannun nawa,a take sai na ji tausayinsa ya kama ni.

"A kawo miki abinci za ki iya ci?" Na girgiza kai.

"A'a,zaki ɗan ci ko yaya ne,ko abu mai ruwa ne." Ya miƙe.

"Bari inyi miki burush(Brush)."

Da saurinsa ya fito daga banɗaki da burushi na a hannunsa wanda saman shi ke cike da makilin, da ruwa a ƙaton kofi da wata silba a hannunsa, ya ajiye su gefen gado, sannan ya hayo gadon gaba ɗayansa, ya ɗaga ni ya jera filallika guda uku a bayana, na ɗago sosai, ya janye bargon jikina ya mayar da shi iya ƙuguna, ya gyara shi sosai, sannan ya sauka ya ɗauko kayan ya ɗora silbar a cinyata.

Ya kanga mini kofin a bakina, "Kuskure bakin tukunna." Na kurɓa, ya yi saurin ajiye ruwan a durowar gefen gadon, sannan ya ɗago silbar.

"Zuba a nan." Na zuba sai na ga jajawur yawun bakina, ga ɗoyi yana yi, kunya ta kamani, amma na ga shi bai nuna alamar ƙyanƙyamina ba, ya ƙara bani ruwan na kurɓa, na ƙara kuskurewa ya ɗago na juye.

Ya ɗauko burushin na ɗago hannuna na riƙe, "Zan iya."

"A'a, kada ki wahala fa."

Bazan wahala ba."

Ya ƙura mini idanuwa,sai ya lumshe su tare da yin murmushinsa, ya buɗe idanuwan tare da girgiza kai.

"No Yasmin, jikinki ba ƙarfi, ki yi haƙuri in kula da ke har ki warke,kina ga ya dace in bar yaran can su dinga kula da ke, alhalin ƙasa suke da ni, amma su ga wani ɓangare na sirrin matata? No,no,is not possible."

"Wallahi zan iya."

Ya miƙo mini burushin.

"Na amince da ke."

A hankali na dinga gogawa, saboda jikina babu ƙarfi sosai, amma duk da haka sai da naji na gaji sai da na ɗan tsaya hutawa, ya yi murmushi ya karɓa ya ƙarasa mini.

"Ya sunan ɗaya daga cikin yaran gidanki?"

"Mansura ko Muslum."

Ya miƙe da hanzari ya ajiye kayan a ƙasa ya leƙa barandar cikin falo, ya kira Mansura, da gudu ta hayo,a inda shi kuma ya dawo ya zauna.

Ya umarce ta da ta ɗauko masa mango juice a firji,ta tafi cikin saurinta, shi kuma ya shiga banɗaki da kayan ƙazantar wanke bakina a hannunsa.

Ko fitowa bai yi ba, sai ga Aunty ta ce, "Lah! Ina Yarima, bari in gaya masa kin tashi."

Sai ga shi ya fito. "Ta tashi?"

"Ta ɗan jima, abin da yasa ban ce a taso ki ba,ganin kin samu bacci shi yasa."

Ta iso ta zauna gefen gado.

"Ya jiki Yasmin?"

"Da sauƙi."

Nan suka ci gaba da zama ita da Yarima, har sai da ya ga nasha mango juice ɗin nan sannan Aunty ta matsanta masa da ya je ya yi koda wanka ne, da ƙyar ya amince.

Bai fi mintuna goma da tafiya ba, sai ga Mama ta iso, cewa take, "Barkanmu, barkanmu Yasmin,tare da Sarki muke yana ƙasa,kin san abun mata, shi ne na hayo in ga yanda ku ke tukunna." Ta juya ta yi baya, sai ga su sun shigo tare da Sarki tun da ya shigo na ga fuskarsa cike da walwala.

Sarki ne har gefen gadona,yana ta jinjina abin da ya faru, Mama ta ɗaga bargon da suka lulluɓe ƙafata, suka kalli ƙafar.

"She will be alright." Sai ga yarima da saurinsa. Doguwar riga ce a jikinsa har ƙasa ta ƴan Saudiyya, wacce ta sha aiki tun daga samanta har ƙasa da wandonta da hula kalar ruwan madara da takalman ƙafarshi kalar hular.

Yana shigowa ya zauna har ƙasa ya gaishe da Sarki, da mahaifiyarsa,yana sunkuyar da kai irin na girmamawa, amma sai na ga Sarki ya ɗan ɗaure fuska,Yarima na ɗagowa, sai na ga ya yi mini ƙyau,wanda ban taɓa gani ba a fuskarshi, na ƙara kallonsa, sai na ga fuskarshi tana ƙara sheƙi. Na juyar da fuskata gefe, saboda tunanin ko shaiɗan ne ya ƙara ƙayata mini fuskarsa.

Ranar kam naga jama'a, sai yiwa Yarima barka ake yi, madadin a yi mini. Su Mamee ma da aka zo,ai ta Yarima ake yi bata ni ba,ni kuwa madadin inji yana ba ni haushi kamar baya, sai na ji ina jin daɗi yadda yake nuna ai ya shiga tashin hankali, a inda yake baiwa masu zuwa labarin ƙwanana biyu kenan da suma haka ban farfaɗo ba sai yau.

Anan na samu labarin ashe har ƙwanaki na yi a ƙwance,lallai dole bakina ya yi ɗoyi. Ƙwanana huɗu a ƙwancan nan, amma duk wata kulawa da ake nema, tabbas Yarima na ba ni ita, har ma wacce ta fita,a inda tunda ƙwana biyu ya ce Aunty ta tafi gidanta ta ƙwana ta ji da yaranta.

Tun ban ɗaukar abin da Yarima ke mini da sunan so, har zuciyata ta amince lallai ya kamu da ciwon sona, ciwon da na lura ya riga ya yi masa katanga a zuciya,ni dai bana cewa ina son Yarima, amma tsanar da nake nuna masa a baya, yanzun bana iya yi masa ita.

Da la'asar wacce ta cika ƙwana huɗun sai ga Mama, bayan gaisawarmu ne, na ga sun fita falon sama da yake labulan shara-shara ne tsakanin ƙofata da falon, shi ya bani damar ganin abin da ke faruwa a tsakanin Yarima da Mama.

Shi ne na ga ya durƙusa ƙasa yana yi mata magana, amma bana jin maganar, sun ɗan ɗauki mintuna sha biyar sannan ya shigo.

"Yasmin can gida zan tafi da ke domin yi miki magani sosai,kin ga can an fi samun magani,a yanzun haka ma Sarki ya tura a ɗauko wani mai magani a ƙauyen Bukuru."

Na washe baki alamar na ji daɗin maganar da ta faɗa, amma sai na ji jikina kamar bai amince ba, sai dai kuma ba zancen gardama a tsakaninmu,ɗaga kaina da nayi na hango Yarima jingine a jikin bangon shigowa ɗakina, shi yasa na ji tausayinsa ya kama ni. Ya iso wajen Mama jiki a sanyaye, ya durƙusa ƙasa ya kama hannuwanta.

"Mama, wallahi ina kulawa da ita,ki tambaye ta ki ji, Yasmin ba ina kulawa da ke ba? Mama a nan fa nake ƙwana a wajenta, Mama ki bar ta wallahi zan kula da ita sosai, zan fi dama."

"Wai kai meye na damun kanka ne a kanta, kai ka ce mini baka son...."

"Mama kada ki faɗa, wannan a da ne,shin ba cewa na yi ƙwata-ƙwata ba."

"Ka ga an gama magana, sai dai ka yi haƙuri."

Ta juya ta kalleni.

"Zan tafi da ke yanzun,su wa za'a kira su shirya miki kayanki?"

"Mansura." Na bata amsa.

Ta kalleshi, "Kirawo Mansura a falo babba." Ya ce to, ya miƙe ya tafi.

Saman kujera doguwa yake zaune a babban falo, ya ƙwanta jikinta sosai, da gani ka san cikin damuwa yake, ya ɗago ya kalleni a daidai lokacin da ake saukowa da ni sai na ga ya yi murmushi.

"Ina nan zuwa anjima." Haka kawai ya faɗa,mu kuwa muka wuce.


**** **** ***"

Lallai kam na ga gata, na tabbatar da cewa iyayen mijina na ƙaunar ɗan su, shi yasa ƙaunar ta shafe ni,a nan na ƙara yarda da cewa sarauta abin ƙauna ce, ga wanda bai shige ta ba ne yake ganin tamkar aikin bauta ake a cikinta.

Yanzun kam ni da kaina zuciyata da sauran jikina suna ƙaunar sarauta, saboda ganin yanda take tafiya cikin tsari da nunawa jama'a ƙauna ta gaske. A wannan zaman ne ma na san wa ye Yarima da iyayensa.

**** **** ****

Yarima fari ne,ƙyakƙyawan gaske wanda dirin jikinsa na cikakken namijin da ya amsa sunansa, wanda gashin bakin fuskarsa ya ƙara ƙawata fuskar tasa, amma shi farin shi ja ne, tamkar na Turawa, idanuwansa kuwa sun ɗan yi girma kaɗan, tamkar na Salman Khan ɗan ƙasar Indiya.

Sai dai shi zamu iya kiran ƙirar jikinsa irin ta Turawa, da ganinsa dai ka ga (Handsome). Tabbas ya cancanci sunansa, wato FAYSAL.

Su biyar ne kaɗai ƴaƴan Sarki. Yarima shi ne babba, sai ƙannansa huɗu, amma mace ke bi masa Salimat, ita ce matar ɗan Sarkin Wasai, wato ƙaramar hukuma ce a Jos,sunan mai bi mata Idris,saurayi ne yana karatu a London, sai Sauda wacce take aure a Mina,sai autansu Ahmad. Yarima za a iya kiransa ɗan shekara talatin da biyar, ya yi karatunsa ne a Greece tun yana ɗan Sakandire aka kai shi ya karanci hulɗa da jama'a Public Relations.

Ba wai domin ya yi aiki ba, a'a don dai ya iya zama da jama'a da riƙe gari, idan ya zamana ya hau mulki.

Matan Sarki biyu ne, amma mahaifiyarsu Yarima Hajiya Mariya, ita ta haifesu su uku, shi da ƙannansa, da Idris da Salimat, amma Sauda ƴar ɗakin Hajiya Khilishi ce ita da Ahmad wanda yanzu yake makarantar gaba da Primary.

*ƘASAITA BOOK 2*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 2


Ko a ido ka ga yanda ake wa Yarima,ka san ana ji da shi, sannan kuma sam ba ka gane cewa ba ɗakinsu ɗaya da ragowar ƙannansa ba,ni kaina sai da na zauna gidan sannan na gane da kaina.

Amma Mama ta ce mini, Yarima ba shi ne ɗan Sarki na farko ba,yana da yayyansa biyu mace ce babbar gidan ƙwata-ƙwata Hajiya Asabe, sai ƙannanta Abdul Rahman, amma tun kafin sarki ya hau sarauta ya auri uwarsu Hajiya Hadiza, sun rabu tun shekaru da dama.

Yanda ta ba ni labari ba ta san abin da ya haɗa su ba, amma Sarki baya son ko sunan yaran a ambata, ba ma uwarsu ba, wannan dalili ne ma yasa jama'a da dama sun yi zaton Yarima ne babban ɗan Sarki Jafar.

Uwarsu Abdul Rahman tafiya ta yi da su hannunta tun suna ƙanana, sai dai in sun ga dama suna zuwa gaishe shi, shi ma sai a yi shekaru basu zo ba, yanda ta bani labarin, yanzun haka Hajiya Asabe tana Ibadan tana auran wani mai kuɗi Alhaji Alabi.

Shi kuwa Abdul Rahman yana Scotland zaune da matarsa baturiya (Vivian), yanda Mama take nuna mini kamar Sarki ya yafe su ƙwata-ƙwata, kenan ya barwa uwarsu su, sai dai ta ce ya kan aika masu da kuɗin makaranta da na abinci da suna yara, yanzun kuwa ko maganarsu ma baya son a tayar.

Asalinsu Mama kuma iyayenta ƴan barikin Ladi ta nan Jahar Plateau,tun da daɗewa a garin Jos,ƴan ƙauyukan garin ke zuwa karatu, wato Makarantar ƙwana ta gaba da Primary,anan suka haɗe da Sarki a lokacin bai ma hau gadon sarauta ba, daga baya ne ma da ya hau mulki ya ƙara auran Hajiya Kilishi.

Yanzun haka iyayen Mama suna nan da ransu a garin Aboko, da sauran danginta. Yarima kuwa shi ne ɗan ta na farko, sai Salimat, sannan Idris, daga su kuwa ba ta ƙara ba. Hajiya Kilishi kuwa anan Jos ya aure ta,ɗiyar hakimin Bukuro ce ta nan ƙaramar hukumar Plateau.

Saboda rashin ganin hanya a ranar da muka zo gaishe da iyayen Yarima, shi yasa ban gane cikin gari suke zaune ba,a unguwar Dogon Agogo,wai wannan rukunin da nake gani har wajen baƙwai a gidan Yarima,wai na farko fada ce in Sarki ya zo kenan dai gidansa ne na hutawa,ko kawo baƙi na musamman.

Sai masallaci a liƙe da shi, ragowar rukunin kuwa kamar namu ne,gidana da na Yarima, sai na su Idris da Ahmad,wai in sun yi aure, amma kowanne da kalar yanda aka tsara nasa ginin, amma tsananin kowanne gida zuwa wani gida, sai an shiga mota,in ba motsa jini za'a yi ba, saboda ko da Asuba ko ragowar sallolin nan an kai Yarima a mota.

*** **** ****

Tsugunne muke gaban Sarki ni da Yarima a ƙaton falonsa, na cikin gida,kawunanmu kuwa a sunkuye suke da gani ka san gaban manya muke.

"Yau ne matarka za ta koma gidanta wacce ta samu tsayin ƙwanaki arba'in da biyu a hannunmu, dalilin da sakacin da ka yi da ita har ta faɗa haɗarin saran maciji.

Bayani ya same ni na irin zaman da ka yi da ita a baya, zaman ko in kula da banzatar da ita. Wannan dalili ne ma ya janyo mata faɗawa rayuwa ƙuntatacciya, na gode,ka yi mini daidai ashe ni ina taƙama da ina da ɗa mai biyayya, ashe ban sani ba,ƙarya zuciyata ke gaya mini.

Ka bani mamaki,a ce ita mace na je na nemo auranta ga iyayenta, suka amince suka ba ka ita, alhalin ba ta san ka ba, kuma suna da wanda ke jiransu su aura masa ƴarsu, ita ma tana da wanda zuciyarta ke so, amma ta haƙura ta yi biyayya ga iyayenta, kai kuwa ban isa ba."

"Baba...." Yarima ya faɗa cikin sanyin murya.

"Kada ka ce mini komai, kai ne da bakin ka ka gaya mini da ka amince in zaɓa maka wacce na ga ta dace da kai, tun daga ranar na baza mutane a kan su gano mini matar da ta dace da ɗana wanda nake mugun ƙauna a zuciyata, Allah ya ba ni ya kuma ba da sa'ar aka samu ƴar gidan manyan mutane masu mutunci.

Ka tuna,bakina da naka muka yi wannan maganar ba fa aike na yi maka ba,ka tuna,kiranka na yi ka faɗa mini wacce yarinya ka gani ta ƙwanta maka a yi maganar auranku,ka tuna, kai da bakinka ka ce mini babu.

Yanzun na yanke hukunci zan raba auranku, amma na baka tsayin ƙwanaki biyar ka zo mini da rubutacciyar takardar sakinta...."

"Baba...."

"Bana son jin komai daga gare ka,ka bani haushi,ka ɓata mini raina matuƙa."

Ya miƙe tsaye, "Ɗiyata ina ƙaunarki da ɗana, amma ki je kiyi haƙuri, sannan ki yafe ni da na sa aka raba ki da wanda ke son ki,saboda son kai irin nawa. Zan aiko a yi kiranki." Ya juya ya tafi.

Yana ƙulewa a inda har ya ƙule, Yarima na Baba,Baba cikin girmamawa, amma bai ko juyo ba,ni kuwa na waigo a sanyaye na kalli Yarima inda ya koma ya ƙarasa zama a ƙasa.

"Tashi mu tafi." Na faɗa cikin muryar da zata ƙara karyar da zuciya.

"Kin ji abin da Sarki ya ce fa Yasmin."

Na ɗan yi murmushin da ƙago shi kawai na yi.

"Kana da magani?" Ya girgiza kai. Na miƙe na bar shi a wajen zaune,gudun kada ya karyar mini da zuciyata.

Ina jiyo su daga falo,suna cikin ɗakin Mama yana gaya mata, amsar da ta bashi ce nima ta ɗan firgita ni.

"Gara haka,ai ni har naji daɗi, tun da baka son ƴar mutane a dinga ajiyarta a gidanka,ƙwanaki nawa kuka ɗauka da ita ba ka ji kana son ta ba,sai yanzu....?"

"Mama zan iya yi miki rantsuwa da Alƙur'ani akan ina son ta, Mama duk laifinta ne...."

"Laifintan wa? Kusan kullum sai mun yi waya in har baka zo ba,in dinga ƙwatanta maka cewa don tana mace,kai ya kamata ka dinga shishshige mata,yau da gobe za ta saki jiki da kai."

"Wallahi Mama, ina yi mata, ita da wanda take so,wai shi ANWAR."

"Shi kenan ka ga yanzu ka yi wa kanka, ita kuwa tana da wani."

"Mama yanzu ya zan yi? Wallahi ina son Yasmin,ni dama can ina son ta."

"Ƙarya ka ke yi, da kana son ta da baka tsaya yi mata mulki da kuma ƘASAITA ba, haka ka ga muna zaune da mahaifinka?

Mulkinsa da ƙasaitarsa a waje suke, sai kuwa idan ya shigo gida ya ga barorinsa, wannan dole ya yi,kana kallo wata rana da kansa zai leƙo ya kira wacce yake son yin magana da ita a cikinmu.

Ko an ce maka jakadiyar da aka sa a tsakaninku, Addini ne ya shinfiɗa ta?"

"Mama matsalar, Mama, Yasmin ba ta sona ƙwata-ƙwata,ni kawai ke sonta."

"A yanzu ko kai ma?"

"Mama ki tuna ranar da na fara ganinta daga can sai nan fa nazo na gaya miki na ga yarinyar da nake so,amma ban san ko ƴar waye ba, har ki ka ce sai in je in ta nema, wallahi Mama ita ce nake gaya miki, don dai haɗuwarmu ta zo ne da saɓani shi ya sanya...."

"Saɓani ko dai ka nuna mata kai ka isa, dole ne ta

Please Login or Register in order to submit comment