Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai tayi ta ce"zani" ya ce" good gurl".



*SHEIKH HEESHAM*[3/5, 16:00] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4
*I Dedicated this book to yhu Aunty Sarauta my nimcyluv, much luv*


*Paid book*
*Free page 7-8*


Murmushi Ameera ta yi ta ce"yau ɗiyar Sheikh ce a gidan namu?" zama Jiddah ta yi ta ce" ina yini y gd?" "lpia lao" kalle-kalle ta yi sai kuma ta ce

"Ina junior?"

"Yana makaranta maybe suna hanya"

Okay Jiddah ta ce sannan ta yi shuru dan damaan ita ba gwanar magana bace.




Har kusan isha'i tana gidan Bilal, dan tare suka dafa abinci da Ameera tana koya mata wasu abubuwan


"Mom"

Juyowa tayi tana kallon ɗan ƙaramin kyakkyawan yaron ta ce

"Toh sarkin tambaya yanzu kuma mene ne?"


Turo baki yaron ya yi sannan ya ce
"Dad ne ya ce wai aunty Jiddah tazo zai maida ita gida"


Kallonsa Jiddah ta yi ta ce"ka ce masa gani nan"

Juyawa yaron ya yi Ameera ta ce" bazaki kwana ba?"


Girgiza kai tayi ta ce" Abba zai min faɗa"

Murmushi Ameera ta yi ta ce

"Kaga ɗiyar Sheikh"

Rufe fuskarta ta yi da hannunta sannan ta ce"na tafi"

"Tom sai anjima "


Sannan ta fito parlon ta ɗauki school bag ɗinta sannan tayi waje.


Har suka isa gida ba tace dashi ƙala ba saboda kwata-kwata ta matsu taga Abbanta ji take kamar tayi shekara bata gansa ba



Tsaye ta tarar dasu a parlon kowa ya yi shuru, da mamaki take kallonsu dan ta ɗauka wani abunne ya faru


"Daughter me yasa kika bi Bilal baki sanarwa kowa ba?"


Rarraba idanu ta yi sai kuma ta ce" ai na ɗauka ya faɗa muku shiyasa Daddy kuma..



Wata kyakkyawar tsawa da Sheikh ya daka mata yasa ta yi shuru jikinta nata ɓari, lokaci ɗaya kuma ta fashe da kuka



"Idan baki yimin shuru ba i'll deal with you"


Tsit ta haɗiye kukan nata tana sauke ajiyar zuciya, ya juya yana tafiya dan dauriya kawai yake a haka har ya haura benen



Girgiza kai Daddy ya yi dan yasan halin Heesham kawai ya juya ta tafi, Shareefat ce ta ƙaraso gabanta ta dafata


"Kiyi haƙuri kinji Jiddah ki tashi ki tafi ɗaki gobe sai ki bashi haƙuri"


Ɗagowa tayi tana kallon Shareefat da idanuwanta da suka kumbara ta ce

"Wlh bansan bai faɗawa Abba ba da bazan bisa ba"


Gogo mata hawayen ta yi ta kama hannunta suka shiga ɗakinta



Saida ta tabbatar ta daina kukan sannan ta fito daga ɗakin lokacin ta shiga banɗaki



Juyi kawai take akan gadon amma kwata-kwata ta kasa bacci ko meyasa?????



Da wuri ta tashi kamar kullum ta gama shirin makarantar ta sannan ta fito, kallon ƙofar ɗakin kawai take tanajin kamar ta shiga kamar kuma karta shiga. Jiki asanyaye ta buɗe ƙofar bakinta da sallama ta shiga, zaune ta hangeshi kan carpet ya tankwashe ƙafafunsa ya yi shuru dan bazakace ga abinda yake ba.



Zama ta yi gefensa kanta ƙasa ta ce

"Abbana ina kwana?"

Shuru ya yi mata hakan yasa taji ta ƙara tsinkewa da lamarinsa hawaye suka fara rige-rigen zuba daga idanunta, kuma har sannan bai ɗago ya kalleta ba kusan 5mins hakan yasa kawai ta miƙe jiki babu kwari tayi waje


"Heeshama"

Sunan da taji ya furta kenan sanda take shirin fita daga ɗakin, batasan wace yake kira da wannan sunan ba amma kawai ta juya ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da nata idanun, da hannu ya yi mata alama da tazo aikuwa da saurinta ta tafi kamar zata waɗi. Tana zuwa ta tsuguna gabansa

"Heeshama!"

Ɗago idanunta tayi dan tana son tabbatar da wacce yake kira da wannan sunan, numfasawa ya yi sannan a nutse ya ɗora hannunta ɗaya saitin zuciyarsa. Sosai zuciyarsa take wane irin bugawa da ƙarfi ta runtse idanunta

"Naji zafi Sosai, akiyaye"

Fashewa ta yi da kuka ta ce"kayi haƙuri Abbana wallahi bansan Dad ɗin Junior bai sanar dakai ba dan Allah ka yafemin Sheikh"

"Na yafe miki duniya da lahira Heeshama"

Sai asannan ta saki fuskarta ta kama gemunsa tana murɗawa ta ce

"Abbana ni ce Heeshama?"

Gyaɗa mata kawai ya yi ta yi murmushi har saida beauty point ɗinta ya loma ta ce

"Abbana sunan da daɗi sosai ina sonshi, Heeshama"


Shuru sukayi duka na rashin abin faɗa kusan minti 5 sannan ya ce

"Tashi ki tafi dare nayi"

Kwaɓe fuska ta yi ta ce" Abbana ka barni anan "

Girgiza kai ya yi dan yasan rigima takeji da, gyara mata zamanta ya yi kan cinyarshi ta ɗora kanta kan ƙirjinsa idanunta a lumshe, ajiyar zuciya ya sauke wadda shima baisan ya yi hakan ba saukar numfashinta da yaji yasa ya tabbatar da tayi bacci. Anutse ya miƙe da'ita yafara tafiya. Babu kowa a parlon banda tv dake aiki har ya kaita ɗakin amma haka kawai ya ji bazai iya barinta ita kaɗai ba a ƙasa alhalin kowa ya sama. Kallonsa take har ya kwantar da'ita gefen gadon sannan ya ce

"Daga yau tare zaku dinga kwana understood?"

Gyaɗa masa kai tayi ya juya ya fita. Kallon Jiddah ta yi wacce take barcinta hankali kwance, haka kawai taji tausayinta ya shigeta girgiza kai ta yi sannan ta kwanta itama.




Dariya kawai tayi ya ce" wlh ina baki labari wife kinganki kuwa ranar?" murmushi ɗauke a fuskarta ta ɗago kanta dake kirjinsa ta ce"Allah Doctor banaso, bayanma ka fini yin kyau ranar"


Riƙe bakinsa ya yi ya ce" kin taɓa jin inda ango yafi amarya kyau?" gyaɗa masa kai tayi tana murmushi ya ce

"To ban yarda ba"

"Wlh da gaske nake maka Doctor wata friend ɗita da mukayi bikinta kwata-kwata batayi kyau ba angon kuwa handsome guy dashi"


Dariya kawai ya yi sannan ya ce" shikenan kiyi bacci kinsan gobe zan fita da wuri"

"Ayya doctorna zan raka ka"

Waro idanunsa ya yi ya ce" so kike wani ya ganki haka kawai yaji kin masa, kinsanfa inada kishi sosai"

Rungumeshi ta yi ta ce"I Love you so much doctor"

Shafa kanta ya yi ya ce" nima haka Nabeela, Allah ya nuna min randa zaki haifamin Twins, can't wait"

Da sauri ta kalleshi ta ce" nikam bazan iya ba Doctor" murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce" zamu gani".



Da mamaki take kallon inda ta ganta, murmushi Shareefat ta yi mata ta ce" Abba ne ya kawo ki jiya" ba tace komai ba ta tashi a hankali ta nufi kofa ta fita. Tana gama shiryawa ta fito lokacin Dad ne Mami zaune suna ɗan taɓa hira

"Ina kwana?"
ta faɗa a sanyaye, "lpy ƙlao Hauwa'u kin tashi lpy?" Dad ya tambayeta

Da murmushi a fuskarta ta ce"lpy klao Dad" "Masha Allah" kallon Mami tayi wacce ta ɗauke kai dan bama zaka ce tana wajen ba lokaci ɗaya jikin Jiddah ya yi sanyi, tsugunawa ya yi cikin girmamawa ya ce" Mami ina kwana?" murmushi ɗauke a fuskarta ta ce" lpy lao Sheikh ya ayyuka?" "Alhamdulillah" ya furta sannan ya koma gaban Dad, a hankali ya zame hular kansa ya ɗora kansa kan ƙafafun Dad ɗinsa yana sakin ajiyar zuciya

"Muntashi lpy?"

Shafa kansa Dad ya yi sannan ya ce" lpy lao Heesham ka tashi lpy?"

"Alhamdulillah" ya bashi amsa sannan ya miƙe yana kallon wrist watch ɗin hannunsa ya ce" sai na dawo"

"Allah ubangiji ya tsare" suka bashi amsa, gaba ya yi har sannan ta na tsaye bata motsa ba

"Hauwa'u tashi ki bisa"

Tom ta ce sannan tabi bayansa kamar yanda Dad ya ce mata.


Tsaye ta samesa suna magana da wani managern company ɗinsa bayan sun gama ya kalleta ganin yanda ta haɗe rai ya kama hannunta bai ce komai ba suka shiga mota

"Heeshama!"
Sunan da ya furta kenan yana matse hannunta dake cikin nasa, shuru ta masa kamar ba da ita yake ba ya tallafi haɓarta yana ƙarewa cute face ɗinta kallo ya ce "ke dawa?, rigimar me ce?" ya yi baya yana jingina da kujerar motar.


Kallonsa ta yi sai kuma ta fashe da kuka, shuru ya yi mata yana sauraren kukan nata wanda yake jinsa har ƙasan zuciyarsa saida tayi mai isarta sannan ta fara sauke ajiyar zuciya, sai da yaga ta yi shuru duka sannan ya ce

"Now tell me ke dawa?"

Kallonsa ta yi da kwaɓaɓiyar fuskarta ta ce" ko bakai bane ba"
Wara idanunsa ya yi yana nuna kansa da yatsa ya ce "ni kuma menayi Heeshama?" tana wasa da gemunsa ta ce

"Shine ka mai dani ɗakin Shareefat bayan nace maka a ɗakinka zan kwana" tana kaiwa nan ta sake fashewa da wani sabon kukan, ɗauke kansa ya yi yana murmushi dan ya gama gano zallar rigima ce take ɗawainiya da ita ɗan bubbaga bayanta ya yi ya ce

"Sorry Abba bai ƙarawa"

"Promise?" ta tambaya cikeda shagwaɓa, shuru ya yi mata da farko ai kuwa ta sake buɗe bakinta akaro na uku zata zumduma ihu, tattausan hannunsa yasa ya rufe mata bakinta yana kallonta ya langwabar da kai ya ce

"Ki yiwa Allah karki fasamin kai Heeshama" haɗiye kukan ta yi tana kallonsa ita kaɗai tana tura baki har suka isa makarantar tasu

"Abbana ka kaini har cikin makarantar" ta faɗa tana wasada fingers ɗinta, girgiza kai ya yi ya ce" ki bari sai an tashi yanzu zan makara" zatayi magana ya nuna mata hanyar waje batayi musu ba ta sauka sannan ta shige makarantar, saida ya daina ganota sannan ya saki ajiyar zuciya

"Ya Allahu"

Shine abunda yake furtawa har suka bar makarantar.


Kallonsa yake har ya ƙaraso ƙofar office ɗin yana murmushi ya ce

"Dr Khalil daman ana ganinka?"

Harararsa Khalil ya yi ya ce" dani dakai aga wanda ba'a ganinsa" shafa kansa Bilal ya yi sannan ya ce" toh ya kake ya gida ya bayan rabuwa, ina Nabeela?" murmushi Khalil ya yi ya ce" wlh komai lpy dole ka tambayeni Nabeela tunda bakazo aurenmu ba" da mamaki Bilal ya ce" daman kunyi aure?wlh ban saniba"

"Eh daman ya za'ayi ka sani tunda baka damu ka sani ba baka neman mutane, ina ɗan namu?" dariya Bilal ya yi ya ce " daman kasan inada ɗa?" tsaki Khalil ya yi ya ce" tunda baka damu kaji na mutane ba ka ɗauka mu bamu jin naka wlh ina sane na ƙi zuwa saboda bakada mutunci sai kace ba'a rayu tare ba" girgiza kai Bilal ya yi ya ce

"Sorry friend wlh ba haka bane amma in sha Allah yanzu zamu dinga zumunci"

"Allah yasa har zuciyarka"
Dariya ya yi ya ce" Ameen na Nabeela" harararsa ya yi ya ce " naji kuma gashi na auri Nabeela"

"Allah ya bada zaman lpy Friend"

Murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce "Ameen Bilal daman nan asibitinka ne?"

Gyaɗa masa kai Bilal ya yi ya ce

"Ai ban saniba nima asibiti kusada nan yake tom wani friend ɗina nazo dubawa"

Kama hannunsa Bilal ya yi yana cewa
"Muje ciki sai mu ƙarasa hirar".



Shuru Dad ya yi ta ce" Alhaji kayi shuru?" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce" kinsan banason azo ayi abunda za'aji kunya nan gaba amma zanga yanda za'ayi idan Heesham ya yarda dan bazan masa auren doleba yana namiji kuma kinsan Sameer ma bazai bari ba"

Numfasawa ta yi ta ce" ni dai dan Allah kasan abun yi dan wlh nagaji da kallon Heesham babu aure yaro kamar ba namiji ba sa'anninsa daga mai ƴaƴa biyu sai mai uku haba"


"Na tabbata Heesham bai yi haka da ganganba dole there must be a reason da yasa bai yi aureba coz yanada ilimi shiba jahili bane kinga kuwa dole something fishy"


Ruwan hannunta ta ɓalle ta sha sannan ta ce

"Wlh Nihal batada matsala she is fine gurl batada flaws ko kaɗan"

"Allah yasa hakane"

"Ameen".
[3/6, 14:03] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4


*I Dedicated this book to yhu Aunty Sarauta my nimcyluv, much luv*



*Paid Book*
*Free page 9-10*

*Last Free Page*



Da sauri ta kalli Mommy sai kuma ta ce "haba Mommy dan Allah ki mata magana wlh da gaske ina son Sheikh wlh" sakar baki ta yi ta na kallonta ta ce" toh ta ce min sunyi magana da babansa sai ki bari sai sun yanke hukunci tukun na " zumɓura baki ta yi sai kuma ta tashi ta shige ɗakinta, girgiza kai Mommy ta yi ta ce" Allah ubangiji ya shirya".




Rungumeta Shareefat ta yi ta ce" oyoyo Sister sannu da zuwa" zama Nihal ta yi sannan ta ce" thank you sis ina Mami?" "ba tanan taje unguwa" gyaɗa kai Nihal ta yi sai kuma ta ce" ina Sheikh" riƙe haɓa Shareefat ta yi ta ce" har anfara tambayarsa toh baya nan" murmushi kawai ta yi sannan suka cigaba da hira.




"Wai ke bazaki faɗamin ina ne gidanku ba?" dariya Jiddah ta yi ta ce" wlh nima bansani ba kuma na manta ban tambayi Abba ba" harararta Hajar ta yi ta ce" ay shikenan tunda bakiso nazo gidanku" murmushi Jiddah tayi ta ce" haba friend wlh zan tambayo" okay ta ce sannan suka cigaba da karatunsu.




A gajiye ta dawo gidan dan ba ƙaramin yawo ta sha ba, zama ta yi kan kujera

"Wash" ta furta daidai lokacin suka fito daga kitchen ɗin, zama suka yi gefenta suna mata sannu da zuwa amsawa ta yi sannan ta ce

"Bari naje nayi wanka wlh na gaji sosai"


"Ayyyah Mami sannu, kin kuwa siyo?" gyaɗa mata kai tayi sannan ta haye sama.


Kallon Nihal ta yi ta ce" wai ke me kike nufi?" ƙasa ta yi da murya ta ce" ina nufin ta bar gidan nan yanda Sheikh bazai sake ganinta ba saboda nifa ina tsoron watarana yace zai aureta wlh" ajiyar zuciya Shareefat ta sauke sannan ta ce" haba wlh bai kamata ba nifa babu ruwana idan kika aikata abinda zai zo ya dameki kinsan babu yanda za'ayi Mami ta bari ya auri wannan yarinyar kuma ma tayi masa ƙanƙanta kwata-kwata bazata shige 15-16yrs ba kinga kuwa da'ace yaya yayi aure da wuri to da tabbas ya haifi kamarta saboda haka ki daina wani damun kanki ki saka aranki kin auri Sheikh an wuce wajen" shuru ta yi batace komai ba kuma badan ta yarda da duk abinda Shareefat ta faɗa ba.




Murmushi ɗauke a fuskarta ta buɗe motar tana kallonsa ta ce" Abbana kazo ɗaukana?" gyaɗa mata kai ya yi dan baya son surutu sannan suka cigaba da tafiya. Suna shiga gida bayan anyi parking ta fito bata tsaya shiba dan ita haushin bai kulata ba ne ya dameta, girgiza kansa kawai ya yi yana kallonta har ta shiga gidan sannan ya sauke ajiyar zuciya


Da sallama ta shiga ɗakin, zaune ta tarar dasu suna hira ta ce" sannunku" fuska a sake suka amsa mata Shareefa ta ce" sai yanzu kika dawo?" gyaɗa mata kai ta yi ta ce" na tsaya jiran Abba ne shiyasa" ji tayi gabanta ya wani yanke ya faɗi duk zuciyarta ta dagule amma ta yi ƙarfin halin cewa" ina Sheikh ɗin?" tura baki Jiddah ta yi ta ce" nima ban saniba ai bana kula shi" dariya shareefa ta yi dan yadda Jiddah ta yi dole abin ya baka dariya wai sunyi faɗa Sheikh. Bata kuma cewa komai ba ta shige toilet dan yin wanka dan zafi take ji.




"Amma yaya mai zaka zo yi a kano?"

Daga ɗaya ɓangaren ya ce" zanzo na tafi dakai ne saboda Mimi ta matsa" haɗe rai ya yi kamar yana gabansa ya ce" nifa bazan koma gidan nan ba daga nan ma US zan wuce baza su sake ganina ba" kwantar da murya ya yi ya ce" haba Ajmal wannan fa ba daidai bane abunda kake abunda ya faru ya riga ya faru kuma ya wuce dan Allah ka shirya gobe zanzo ɗaukarka" tsaki Ajmal ya yi sannan ya ce" Allah ya kawo ka" "Ameen " ya amsa sannan ya kashe wayar, daidai nan Khalil ya shigo yana kallonsa ya ce" kai da wa naga kana mafan masifa?" cilli ya yi da wayar hannunsa sannan ya ce" wlh Sultan ne zai dameni" murmushi Khalil ya yi dan yasan halin Ajmal da saurin fusata ya ce" dan Allah to kayi haƙuri kazo zamu ci abinci"

"I'm full"

Ya furta sannan ya yi kwanciyarsa kan royal bed ɗin yana kallon sama, girgiza kai ya yi dan yasan tunda ya ce bazai ci ba to ko za'a kasheshi bazai cinba.





"Kaiii wlh Mami ya yi kyau sosai gold ɗin, nima ki siyamin irinsa"

Shareefa ta yi maganar tana shagwaɓe fuska, dariya Nihal ta yi ta ce" baza'a siya ba ɗin?" harararta ta yi ta ce" dalla babu ruwanki dani tom!" murmushi Mami ta yi tana kallonsu duka ta ce "shikenan duka zansa akawo muku" rungumeta sukai atare suna faɗin

"Thank you Mami"

Goge hawayen idanunta ta yi tana sake kallonsu cikeda sha'awa, ji take inama ace ita ce mai mahaifiya, wataƙila bata rabon samun farinciki daga uwa mace yasa duk inda taje bata samun wacce zata riƙeta matsayin ƴa, kallonta Shareefa ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta dan sosai Jiddah take bata tausayi inama Mami ta ɗauketa matsayin ƴa, kama hannunta taji anyi batareda ya yi magana ba ya jata har cikin ɗakinsa. Zaunawa ya yi ya zaunar da'ita kan cinyarsa yana kallon fuskarta, fashewa ta yi da kuka tana rungumeshi ƙam-ƙam, sosai take kuka kamar ranta zai fita kuma bai yi ƙoƙarin hanata ba dan tabbas tana buƙatar tayi kukan ko tasamu sauƙi a zuciyarta. Sai da tayi mai isarta sannan a hankali ta fara sauke ajiyar zuciya kuma taji sanyi a ranta

"A daina kuka komai zai shige kinji Heeshama"

Kallonsa ta yi tana shashsheƙar kuka ta ce " Abbana meyasa ni bazan taɓa farin ciki ba?, meyasa bana samun wacce zata ɗaukeni matsayin ƴa?, meyasa Ammina ta mutu ta barni?, meyasa nima ban mutu ba sanda ta haifeni?, banida gata Abba, banida uwa Abba, bansan mene ne farincikin da ɗa yake ji ba idan yana tareda uwarsa wlh Abba ji nake kamar...... Saurin rufe mata baki ya yi yana girgiza mata kai ya ce


"Ba'a cewa haka Heeshama, a rayuwa duk abinda kaga ya sameka to damaan haka Allah ya rubuta maka, ƙaddararka ce a haka, kuma sannan kinada kowa Heeshama, ki ɗauka ni ne Abbanki, Amminki, kuma yayanki duk abinda kike so a rayuwa ki sanar dani Heeshama na miki alƙawarin tsaya miki akan komai saboda haka banson kina furta irin waɗannan kalaman isn't good Heeshama" ya faɗa ya sauke numfashi dan rabonda ya yi magana mai tsayin haka har ya manta.


Shuru ta yi ahankali kuma ta ɗora kanta akan ƙirjinsa not too long bacci ya yi awon gaba da'ita, kallon kyakkyawar fuskarta ya yi yana sake rungumeta dan yana matuƙar jin yarimyar har cikin ransa.






Shuru ya yi har Dad ya gama faɗa sannan ya ce "amma Dad.. Dakatarda shi ya yi ta hanyar yi masa alama da hannunsa sannan ya ce " Heesham dolene kayi aure kuma not too long saboda zamanka a haka ba abu bane mai yiwuwa kuma kamar yanda mahaifiyarka ta zaɓa maka mata idan ta hali kana iya aurenta amma ni bazan maka dole ba abinda kake so shi zakayi kana iya zuwa kayi tunani ka yankewa kanka shawara amma tabbas inason kafin nan kafin 2months kayi aure idan kuma baka fito da mata ba kuma baka ɗauke wacce aka zaɓama ba to zaka wayi gari ka tarar an kai maka mata gidanka kuma babu saki, ɗazu munyi waya da Sameer kuma shima abinda ya ce kenan karma kayi tunanin guduwa duk inda kaje zansa a nemoka understood?" gyaɗa masa kai kawai Sheikh ya yi dan ji yake kamar kansa zai rabe biyu saboda tsananin ciwon da yake masa, a daddafe ya haura saman yana shiga ɗakinsa ya shige banɗaki, ruwa ya sakarwa kansa saida yaji hankalinsa ya fara dawowa jikinsa sannan ya yi wanka ya fito. Wata armless ɗin riga ya saka da wadonta ya kwanta nan da nan bacci ya ɗaukesa.




Murmushi ya yi ya ce" wato dai kana jin maganar yaya Sultan ko?" harararsa Ajmal ya yi ya ce" wlh kawai saboda shi zan koma, amma yanzu yaushe zaka zo?" "sai da bikin ka" wani shegen kallo ya yi masa yana rufe trolley ɗin ya ce"kada Allah yasa kazo" murmushi kawai ya yi yazo ya rungumeshi ta baya ya ce" in sha Allah friend nan bada jimawa ba zanzo harda Nabeela" murmushin shima ya yi ya ce" Allah ya sa" dariya sukayi duka sannan ya ce" amma dai please ka ci abinci yau kafin ka tafi" "idan naƙi fa?"

"Sai nasa ayi maka duka dan ni bazan iya dukanka ba" fashewa ya yi da dariya sannan ya yi waje.





Throughout ranar haka ta yini a makaranta tana jinta wani iri bata ce ga exactly abinda yake damunta ba amma jinta take duk wani lonely hatta Hajar basuyi wata hirar arziƙi ba har aka tashi, sosai tayi mamaki ganin yazo ɗaukanta yauma, bayan sun ɗanyi nisa ya kama hannunta batareda ya yi magana ba ya zaro wani diamond ring mai kyau kuma mai matuƙar tsada sai sheƙi yake yi ya zura mata a ɗan yatsanta na tsakiya sosai ring ɗin ya yiwa farar fatarta kyau kamar an dasashi, murmushi tayi ta ce" Abbana ya yi kyau sosai nawane?" gyaɗa mata kai ya yi ya ce" na kine Heeshama promise me bazaki manta dani ba" da sauri ta kalleshi ta ce" Abba meyasa zaka ce haka?" numfasawa ya yi amma bai ce komai ba, ta riƙe gemunsa ta ce " Abbana!" juyowa ya yi taga yanda idanunsa suka rini kamar gauta da sauri kuma cikin tashin hankali ta ce" Abbana bakada lpy?" girgiza mata kai ya yi dan ya gagara yin magana haka kawai taji gabanta yanata faɗuwa har suka isa gidan




Kallonta ya yi ya ce" ki shiga Heeshama zani unguwa?" kallonsa ta yi sai kuma ta kwaɓe fuska ta ce" Abba zan bika" girgiza mata kai ya yi ya ce" kije gida kinji Allah ya Albarkaci rayuwarki" murmushi ta yi ta ce" Ameen Abba na, Allah ya dawo dakai lafiya" "Ameen" ya furta da kyar, a hankali ta sauka tana tafe tana waigowa taga shima kallonta yake har ta shige parlon.



"Ina zamuje Sir?"

"Airport" Sheikh ya furta yana lumshe idanunsa shi kaɗai yake furta

"Ya Allahu Ya Rahmanu, Ya Zul-Jalalu wal ikhram".




"Mami banfa gansa ba" harararta Mami ta yi ta ce "wlh idan naje na ɗaukoshi sai ranki ya ɓaci" gyaɗa mata kai Shareefa ta yi sannan ta zauna suna hira da Nihal.



Duba sosai Mami ta yi amma bataga gold ɗin ba, sosai kuma abun ya ɗaure mata kai dan tasan babu kowa a gidan idan ba itaba, Shareefa, Nihal a parlon. Sakkowa ta yi tana kallonsu ta ce" bakuga inda na ajiyesa ba jiya ko na canza masa waje ne?" da mamaki suka ce "wai kema baki ganshiba Mami?" gyaɗa musu kai tayi Shareefa ta ce

"Kuma naga babu wanda ya shigo gidan nan jiya"


"Nima abunda yake bani mamaki kenan" Mami ta faɗa. Shuru suka yi sai kuma Nihal ta ce

"To ko za'a tambayi Jiddah ne ko ta gansa?" da sauri Shareefa ta ce" a ina Jiddah ta ganshi batama san mene gold ba bare ta ɗauka".


"Nifa cewa nayi a tambayeta ko ta ganshi, ko ya kika ce Mami?"


Da sauri Mami ta yi hanyar ɗakin Jiddah ba tareda ta sake yiwa koma magana ba.



"Mu koma gida i forget something"

Sheikh ya faɗa lokacin sun kusa kaiwa Airport ɗin, okay kawai drivern ya ce sannaa ya yiwa sauran motocin umarnin dasu koma suka kama hanyar gida.



Bata cikin ɗakin amma ruwa na zuba a banɗaki alamar wanka take, dube-dube Mami ta hau yi a ɗakin, time ɗin Shareefa suka shigo da Nihal da sauri Nihal ta ce" lemme help you Mami" daga nan ta fara bincike duka cikin ɗakin ita kuwa Shareefa sai binsu da kallo take.



"Mami i got it"

Nihal ta faɗa da ƙarfi, da sauri duka suka juyo suka kallonta tana riƙeda sarƙar gold ɗin a hannunta, tsabar shock sun kasa rufe bakinsu hatta Shareefa kallon sarƙar take da sauri Mami ta karɓa tana cewa


"Ina kika ganta Nihal?"

Daidai nan Jiddah ta fito daga banɗakin tana kallonsu da mamaki

"A cikin wasu kayanta ta ɓoye Mami"

Iyaka ɓacin rai ran Mami ya ɓaci ita kuwa Jiddah kallonsu take da rashin fahimta da sauri Shareefa ta shaƙe mata wuya ta figeta har parlon tana mata wani shegen kallo ta ce

"Ɓarauniya kawai, kin bani mamaki Jiddah ki rasa me zaki sata sai gold wlh kinyi asara daman ance tsintacciyar mage bata mage, no wonder Mami ta tsaneki ashe ɓarauniya ce bamu sani ba wlh kin yi asara banza kawai ƴar matsiyata"



Allah sarki Jiddah kallonta kawai take tama kasa magana ko kuka dan batasan akanme take mata magana ba, Mami ce ta fito tana kallonsu ta ce

"Shiyasa tun zuwanta nace bana sonta daman wlh ni nasan tabbas tanada wani mugun hali da take aikatawa yasa naji na tsaneta Heesham ya kawo mana masifa"


Da mamaki ya ce"what's wrong Mami?" kallonsa ta yi sai kawai ta fashe da kuka ta ce" Heesham sanda nake faɗa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

2 Comments On SHEIKH HEESHAM
avatar
ayshertul-humaira

5 months ago

Reply

Is not complete

avatar
naja-atu-8

4 months ago

Reply

Allah yaqara basira

Please Login or Register in order to submit comment