You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
5 & 6*
Sanda MEEMA ta farka ta ganta jikin Abee ɗin ta sai ta ɗago kai tana kallon sa
Idanun su ne ya haɗu da juna, ya sakar mata murmushi yana ce mata, "You woke-up?"
Bata iya magana ba illa gyaɗa mishi kai da tayi
Still murmushin ya sake Yi Yana lumshe ido tare da buɗe wa yace da ita, "Okay, go pray and eat. I know you haven't eaten yet."
"Ok Abee". Tayi maganar tana sauka daga kan gadon, sai ta wuce ta shiga Toilet ɗin sa ta ɗauro alwala. Tana fito wa ta duba wardrobe ɗin sa ta cira Hijab, dayake akwai kayan ta a ciki tunda ko yaushe tana ɗakin sa, idan har ba karatu zata yi ba, to, bata cika zuwa ɗakin ta ba, ta fi son zama kusa dashi.
Har ta gama sallan yana kallon ta yana faman murmushi kaɗan
Bayan ta gama dawowa tayi ta zauna gefen gadon tana riƙo hannun sa, "Abee, you are doing to pray?".
Gyaɗa mata kai yayi makes her smile
"Ok let me Call Nurse". Tayi maganar tana tashi ta fice.
A Parlour ta tarar da su zaune suna hira, sai ta kalle su fuska ba fara'a tace, "Abee will pray".
"Ok". Cewar Nurse Zara tana tashi da sauri tayi ɗakin.
Direct MEEMA Kan dainning ta nufa, sosai take jin yunwa tunda rabon ta da abinci tun wanda suka ci ɗazu da Zamiya ta girka musu, shiyasa sai da ta cika cikin ta sosai kafin ta tashi tayi ɗakin Abee ɗin ta, sai da safe tayi masa sannan ta wuce nata ɗakin
Ta san ko ta kwanta baza ta iya barci ba, shiyasa ta ɗauki school bag ɗin ta ta haye hill chair ɗin da take karatu a kai me haɗe da table, ta soma duba karatun da aka yi musu tana revision, bayan ta gama sai ta ɗauko assignment ɗin da aka basu tun last week, tamkar project ne suna bincike akai, taci gaba da binciken ta cikin ɗan ƙaramin Laptop ɗin ta tana yi tana rubutu. Sai 01:30am da taji barcin yazo mata kafin ta kwanta, babu daɗe wa kuwa ya sure ta cike da mafarkai kala-kala da ta saba yi ko yaushe.
Washe gari zuwa ƙarfe 08:00am. Ta gama shirin ta, kamar yanda ta saba shigan ƙananan kaya sai ta ɗaura Abaya a kai me bottles a gaban, wannan karon Abayan brown color ne sai mayafin shi fari da Flower's kalan brown, flet shoes ta saka fari sannan ta ɗauki School bag ɗin ta ta rataya a kafaɗa ta fito, a hankali take sauka a kan Steps ɗin har ta dira ƙasa
House girl ɗin su dake gyara parlor'n, ganin ta yasa ta dakata tana gaishe ta
Kallo ɗaya tayi mata ta amsa a taƙaice tana shigewa ɗakin Abee ɗin ta
Nurse Zara da fitowar ta kenan daga Toilet ta gaishe ta cike da fara'a
Kamar kullum ta amsa mata a daƙile tana wuce wa kusa da mahaifin ta, ganin sa yana barci sai ta kalli Nurse Zaran tace, "He still hasn't woken up?"
"Yes".
Numfashi taja tana mayar da idanun ta kan shi
While Nurse Zara ita kuma tayi ficewar ta
Sai da ta shafa fuskar sa zuciyar ta na cike da damuwa, kafin kuma ta tashi ta fice, yau bata tsaya breakfast ba tayi ficewar ta, motan ta ta hau ta wuce school.
Lokacin da ta shiga class su Ummu Hani duk sun zo, yau har da Zamiya saboda jikin nata da sauƙi. Suna cikin gaisawa ne Malamin su ya shigo, sai suka nutsu suka mayar da hankalin su kan darasin da yake musu.
Sun sami break lokacin suna duba karatun su sai wayan MEEMA tayi ƙara, ɗauka tayi ta duba sai taga sunan Ishaq ne, tsaki taja ta ajiye tana ci gaba da duba book ɗin dake hannun ta
Esha Sarkin shaƙiyanci dariya ta saki tana kallon ta tare da ɗage mata gira tace, "Is that Ishaq?"
Ɗago kai MEEMA tayi tana hararan ta bata ce komi ba ta sake ɗauke kai daga kallon ta
Sai tace, "Please go if he is, don't get tired of waiting for you, you know his condition is persistent".
Sai duk suka saki dariya har Eshan da tayi maganar
While MEEMA ta sake kicin-kicin da fuska still taƙi magana
Sun san halin ta shiyasa suka yi gum da bakin su suka ci gaba da karatun su
A lokacin ne kiran nashi ya sake shigo mata, bata sake bi ta kai ba har sanda yayi mata three Miss calls, ganin ya dame ta sai ta ɗauki wayan a daƙile tana amsa mishi sallaman nashi
Sanar mata yayi, "he came outside where they used to meet".
Sai ta tashi kawai ta fice
Su kuma sai suka koma hira memakon karatun da suke yi, har wasu daga cikin mate ɗin nasu suka zauna cikin su ana yi da su.
********
MEEMA da fitar ta Direct inda zata ganshi ta nufa, tana zuwa ta hange shi a cikin rumfar da yawancin ɗalibai suke zuwa su zauna don shaƙatawa, babban rumfa ne da kujeru a wajen da aka jera su gunun sha'awa da tables ɗin su
Ƙarisawa tayi taja kujera ta zauna bayan tayi sallama a ciki-ciki
Shi kuma tuni ya mayar da idon sa kanta yana faman doka mata murmushi tare da amsa mata sallaman yana cewa, "My Baby".
Kallon sa tayi tana ɗan sakin fuska kaɗan tace, "how far?"
"I'm not Fine Baby".
Ɗan ɗage gira tayi tana kallon sa alamun tambaya
Sai yayi murmushi kana yace, "Have a drinks before we start talking". Yayi maganar yana nuna mata drinks ɗin wajen
"Laa. shukran".
"Baby you can not drink?"
Gyaɗa masa kai kawai tayi
Sai yaja numfashi yace, "We should stop talking now. I want to send to your house to have a wedding day,"
Ƙura masa ido tayi har ya dira aya, sai ta fuske tare da kini-kini da fuska tace, "Ishaq now there is no word between us, I can tell you now I will not marry".
"Why MEEMA? Why do you want to humiliate my life?"
"No. I will not humiliate your life, I will not marry if Abee is in his condition, I will never marry until he is fine".
"Ok, baby, I agree to marry you, so bring him to my home and take care of him."
"No Ishaq". Sai ta tashi tsaye tana kallon shi tace, "please don't come out to me again, i will never get married now". Ta juya tayi wuceWar ta
Yana kiran ta amma ko juyo wa bata yi ba.
Sanda ta koma class sai su Ummu Hani duk suka tambaye ta ganin ta dawo da wuri
But bata ce komi ba ta zauna taci gaba da karatun ta
Su ma ganin bata tanka su ba sai duk suka fita harkanta domin sun saba da halin ta yanzu, so hakan ba ya basu haushi tunda sun san ba haka take ba a baya.
Three O'Clock yau suka gama lectures, suka yi sallama da juna
Esha said, "MEEMA dropped her off at home because she didn't bring her own car today."
Shiyasa suka tafi tare, dayake duk wajen anguwan su ɗaya ne, sai da ta sauke ta kafin ta ƙarisa gida, tana sauka ta rufe motan ta taka tayi ciki a gajiye, tana shiga da sallama
Me aikin su ta amsa mata tana mata sannu da zuwa
Da kai ta amsa mata kafin ta wuce ɗakin Abee
Shi kaɗai ne a ɗakin idanun shi a lumshe, sallaman ta ne yasa ya buɗe idon yana kallon ta da yalwataccen murmushi a kyakykyawar fuskar sa na asalin bafulatani, wadda ta ƙara zabge wa tayi siriri da ita tsaban zaman jinya
"Abee". Tafaɗa sanda ta zauna a gefen gadon tana riƙo mishi hannu
"Ummy". Shima ya faɗa still yana mata murmushi, sai kuma yace, "uridu an ata haddas". ("ina son muyi magana ne".)
"Ok Abee, lakin jasadak sahl?" (amma jikin ka da sauƙi ko?")
"Na'am Ummy alhmadulillah. Al'aàn karajal mahaàmil kassi biî wa natahaddasa ma'ahu". ("Yanzu Lauya na ya fita mun yi magana dashi".)
"Abee maàzaà hadasa?" ("Me ya faru?")
Sai da yaja numfashi daƙyar kafin yace, "Ummy, nothing, but now I have decided to return everything to you."
"Why?" Tafaɗa da wani irin murya me kama da son kuka
Murmushi yayi yace, "nothing Daughter. I am not comfortable with the arrival of my brothers. That is why I have made this decision. I want everything to return to your name so that you can own it or after my life is yours. I own everything for you."
Kuka ta fashe da shi tana sake damƙe hannun shi, cikin kukan take cewa, "No Abee, You will be cured by God's will, nothing will happen to you ok?" Sai ta ɗaura kanta kuma a jikin shi taci gaba da kuka, domin ji take yi kamar wani abu ne zai sami Abee ɗin nata, don me zai mata irin wannan zancen? Me kuma yasa zai yanke wannan hukuncin?
Shafa kanta yake yi cike da rarrashi yana ce mata, "enough". Daƙyar ya samu tayi shiru sannan yace mata, "She went to rest".
Tashi tayi ta fita, kai tsaye ɗakin ta ta wuce ta kwanta ta hau faman tunanin da ya zame mata jiki, ga shi yanzu lokaci na ta ƙure mata karatun su ya zo ƙarshe, amma kuma ba ta iya yin karatun sosai sabida hankalin ta ba a kwance yake ba. Lumshe idanuwan ta tayi hawayen ciki na sake zubo mata a kunci, ta jima a haka kafin ta tashi ta shiga tayi wanka ta sauya kaya ta gabatar da sallah, sannan ta wuce downstairs ta zauna a kan dainning ta soma cin abinci, gaba ɗaya a tunani ta gama yi kafin ta wuce ta koma ɗakin Abee ɗin ta
Lokacin yayi barci
Sai ta haye kan gadon ta kwanta a gefen shi tana ta faman kallon shi, babu abinda ke dawo mata sai rayuwar su na baya sanda suke tsananin farin ciki, amma ƙaddara ta zo ta ɗauke musu wannan jin daɗin, sanadiyar haka Ummeen ta ta tafi ta bar su, bata san har yaushe za su kasance a haka ba, duk da ta yarda da ƙaddara kuma ta san komi zai wuce, komi zai koma musu dai-dai kamar baya, tana fatan hakan a koda yaushe, shi ne burin ta Mahaifin ta ya samu lafiya hakan ne kaɗai zai dawo da daidaiton walwala a tsakanin su
Idanun ta ta rufe da suke tsiyayar da hawaye wanda ko kaɗan ba sa gajiya, tana jin zuciyar ta na sake ƙunci a duk sakonnin da zata tuna da mahaifiyar ta.
Ta jima a haka kafin ta buɗe rinannun idanuwan ta a kan fuskar Abee ɗin ta, kallon sa kawai take yi kamar wanda bata taɓa ganin sa ba, ko kaɗan ta kasa ƙifta idanu a kan sa, Every second his sympathy deepened into her heart, numfashi taja kafin ta kai fuskar ta dai-dai nasa she kissed him on the forehead and then pressed him to his lips, sannan ta tashi ta fito. Direct waje ta nufa, a hankali take taka wa hannayen ta soke a ɗan guntun jeans trouser ɗin da ta sanya, while fuskar ta babu alamun walwala a cikin ta, gaba ɗaya damuwa ne ya sake mamaye ɗan kyakykyawar cuty face ɗin nata, duk da hakan be hana fito da zallan kyawun ta ba, domin ta kasance kyakykyawa ce MEEMA, bata da bambanci da mahaifin ta sak shi, a kallon farko idan kayi mata zaka tantance ita ɗin asalin bafulatana ce domin zaka yi tunanin ma tana jin yaren, nan kuwa bata iya komi ba a ciki, daga turanci sai larabci shi ne abinda ta iya, sai kuma kaɗan-kaɗan tana jin yaren talegu kasancewar Zamiya na koya musu, asalin ta ƴar India ce ta zo nan Riyadh karatu shi ne take zaune a Hostel.
Babu inda ta tsaya sai wajen swimming pool ɗin da ke mamaye a bayan gidan, wanda yake cikin ɗan ƙaramin garden me ban sha'awa da birge wa, Everything is green and very beautiful. Tana tsaye ta kafe idanunta waje ɗaya hannayen ta a ƙirji, sosai ta faɗa duniyar tunani, tunanin da ta saba a koda yaushe, bata san cewa hawaye na tsiyaya a kuncin ta ba har sanda taji muryan ƴar aikin su kusa da ita, sai tayi firgigit ta dawo cikin hayyacin ta tana juyo da kallon ta gare ta
"Afwan ya Sayyadaty! Anti gariîb fiî intizaàraki". "(Kiyi haƙuri Madam! Kin yi baƙo yana jiran ki)".
Gyaɗa mata kai kawai tayi
Ita kuma ta tafi
Numfashi ta ja tana saka bayan hannun ta ta share hawayen fuskar ta kafin ta taka tabi bayan ta a hankali cikin tafiyan ta na salo.
[08/10, 2:53 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
💎💎💎
*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_7&8*
Da shigan ta cikin parlour'n su ta sauke idanun ta a kan Ishaq dake zaune yana shan drink a cikin Glass Cup. Da kallon mamaki kawai take bin sa tana tako wa a hankali
Shi kuma ganin ta yasa ya ajiye Cup ɗin saman Centre table yana me miƙe wa tsaye tare da yalwata fuskar sa da murmushi, ƙyam ya ajiye idanun sa a kanta ya kasa ɗauke wa illa bin ta da yake yi da wani irin kallo me wuyan fassara
Ita kuma ganin haka yasa ta sake tamke fuskar ta bayan ta ƙariso wajen sa idanun ta a kan sa tace, "What are you going to do in our house? What brought you here? "
Sai da yayi murmushi yana shafa suman kansa kafin yace, "Oh Baby, you know there is no way I can get rid of you so easily. Please, I have come to talk to you."
Naman goshin ta ta tattare waje ɗaya tana me runtse idanu, sai kuma ta ware su a kansa murya a hassale tace, "What do you want from me?"
"I want to get married MEEMA, I love you so much I can't divorce you. Please accept my request. I may die if I don't marry you." Sai kuma ya duƙa ya saka gwiwowin sa a ƙasa tare da haɗe hannayen sa waje ɗaya yace, "please help Me MEEMA I can't live without you, I love you so much! I may lose my life for you".
Sosai a wannan karon ta fusata da kalaman sa, meyasa ba ya gane wa ne yake son takura mata a rayuwa? Lokaci ɗaya ta daka masa tsawa da faɗin, "I also do not love you Ishaq, go out in my life and leave my life alone, I will never marry you and then leave this house Now". Ta ƙare maganar da nuna masa hanya, "I say Out".
Tashi yayi tsaye yana bin ta da kallo, har gaban ta ya tako still idanun sa a kanta. Kallon kallo kawai suke yi ido cikin ido na tsawon daƙiƙu ba tare da ko wannen su ya ɗauke ba, sai ya ci je leɓe yana me ɗauke kansa a kanta ya sauke a ƙasa, hannun sa ya saka na dama ya sosa goshin sa kafin ya sake duban ta kana kuma ya taka ya bar parlour'n
Har ya fice tana tsaye a wajen ta kasa motsin kirki, zuciyar ta sosai take tafarfasa wanda ita kanta bata san dalili ba, sai kawai ta juya tayi kan Steps da gudun ta ta shige ɗakin ta tare da faɗa wa kan gadon ta, wani irin kuka me tsuma rai ta saki wanda har jijjiga gadon take yi tsaban kuka, da hannun ta take tattaro zanin gadon tana yamutsa wa still tana ci gaba da kukan ta me tsuma rai wanda ke fito wa daga can ƙasan zuciyan ta. Sai da ta ɗauki like two minutes kafin ta shanye kukan a lokaci ɗaya tana me tashi zaune, hannayen ta ta saka ta soma share hawayen duk da wasu suna sake kwaranyowa, "I will not cry again. From today on, I promise. From today on I will remove you from my life Ishaq. I will never marry." Sai kuma ta sake fashe wa da wani sabon kukan, cikin kukan take cewa, "I love You Ishaq, i really Love you, you are the only one i ever wanted you are still in my soul, i will never forget you, i love you, i hope one day we will get married, I'm sorry ok?" Sai ta lumshe idanun ta tana me jan numfarfashi, a haka har ta kafar da hawayen ta kafin ta buɗe idanun ta da suka yi jazur suka kumbura, tashi tayi ta wuce Toilet ta wanke fuskar kafin ta fito ta zauna a kan table ɗin karatun ta, School Bag ɗin ta dake saman table ɗin ta janyo tare da buɗe wa ta zaro Text book ta soma karatu, duk da zuciyar ta babu daɗi amma haka ta daure tana ta karatun domin sama ma kanta nutsuwa, ta san idan ta biye wa damuwar ta zata iya rasa chance ɗin ta, dole ne a wannan gaɓar ta mayar da hankalin ta a kan karatun ta.
Shiyasa tun daga ranan ta hana zuciyar ta sukuni bare ta bata damar yin wani tunani me zurfi, kullum tana cikin karatu ko da tana wajen Abee ɗin ta ne da books ɗin ta take zuwa, bata da lokacin kanta a yanzu saboda ganin time ɗin exams ɗin su ya gabato, idan tayi wasa zata iya Field.
Da sannu da sannu ga shi har time yayi sun soma zana jarabawan su, wanda shi ne na ƙarshe sun haɗa degree ɗin su a fannin Mascom.
Gefe ɗaya kuma bata sake ganin Ishaq ya zo wurin ta ba, ko me kama da shi bata sake gani ba, duk da a wani ɓangare na zuciyar ta tana matuƙar kewan sa amma babu yanda zata yi, hakan ma ya fi mata shi zai bata daman nutsuwa ta manta komi, duk da ta san da cewa cire soyayyar sa a zuciyarta gaba ɗaya ba ƙaramin jan aiki bane a gare ta, ada sun so juna matuƙa ita da shi wanda basu yi tunanin ƙaddara zata zo ta raba su ba, First love yana da matuƙar wahala a zuciyar ɗan Adam, haka MEEMA take ji a yanzu, sai dai ƙauna da tausayin Mahaifin ta ya sa ta jure duk wani baƙin ciki da ƙuncin dake zuciyar ta, ta rabu da shi a kan rayuwa da mahaifin ta na har abada, wannan hukuncin ta yanke shi ne ba tare da tunanin me zai je ya dawo ba.
Alhmadulillah komi aka ce yana da farko kuma yana da ƙarshe, kamar yau ne su MEEMA suka soma zana jarabawan su sai ga shi har sun kammala. Inda makarantan tasu ta shirya musu gagarumin waliman yaye ɗalibai
Sun shirya taron ne a ranan Saturday, inda aka gayyato manya-manyan ƙusoshi na ƙasar Riyadh ɗin, kama daga kan ƴan siyasa da masu kuɗi har da ƴan maƙotan ƙasan duk sun hallara, wanda dama an saba yin babban taron nan a duk shekara.
Mahaifin MEEMA na gaban talabijin kamar yanda ya buƙata a kunna masa don ganin taron waliman ɗiyar sa mafi soyuwa a birnin zuciyar sa.
Bazan iya misalta muku tsantsan kyawun da MEEMA tayi a wannan lokacin ba, duk da ko kaɗan fuskar ta babu walwala bare kwalliya, but tayi kyau sosai kasancewar ta me kwarjini ga duk wanda ya kalle ta, kyawun ta shi ke hana a gane tayi murmushi ko bata yi ba, domin ko ya tayi a hakan kyau take ma Mutane, tana zaune ne a sahun gaba-gaba kasancewar tana ɗaya daga cikin manya-manyan Ɗalibai, tayi shiga irin na larabawa babu abun da ake gani nata sai kyakykyawar fuskarta da tafukan hannayen ta. Inda a lokacin aka sanar ana buƙatar *MEEMA FAROUK* ta fito tayi jawabin buɗe taro. A cikin sanyin ta da tafiyan ta me matuƙar birge wa wanda kamar ba taka ƙasan take yi ba ta isa ga mumbarin tare da amsan speakern ta soma buɗe taro da addu'a cikin harshen larabci, wanda tsaban ƙwarewan ta da iya Yaren zaka yi tunanin ita ɗin asalin Balarabiya ce. Bayan ta ida addu'an ne ta juya harshe zuwa Turanci domin kowa ya ji, kasancewar ba kowa ne ke iya jin larabcin ba, godiya da ban girma tayi ma malaman makarantan tare da baƙin wajen, kana ta koma ta zauna
While mutanen wajen sai tafi suke mata.
Daga nan aka soma gudanar da abubuwan da ya tara su har zuwa kan kyaututtuka da ɗalibai haziƙai suka samu. MEEMA na ɗaya daga cikin waɗanda suke amsar kyaututtuka masu yawan gaske, kowa sai jinjina mata yake yi sabida yanda aka nuna hazaƙan ta
Yayinda Abee na kwance a ɗakin sa yana kallon komi yana hawaye, da ace lafiyan sa lau da ya fi kowa nuna murnan sa ga ɗiyan sa a wannan ranan, tabbas da a yanzu ya kasance a wurin tare da ɗiyar sa yana Alfaharin kasancewan sa uba a wajen ta, sai dai babu hali, but duk da haka babu wanda ya kai sa murna ɗin, tsaban murna har kuka yayi
Itama tana can tana share nata hawayen tuna mahaifin ta da tayi, tabbas da yanzu yana tare da ita suna farin ciki tare, tuna hakan ne ya saka ta zubar da hawaye, ko babu komi tana matuƙar kewan mahaifin ta a irin wannan yanayin, ta tuna sanda ta gama secondary School ɗin ta irin farin cikin da ya nuna sakamakon kasancewar ta gwarzuwa a shekaran, Allah ya yi MEEMA me ƙaunar karatu ne sosai shiyasa zai yi wuya ace ba ita ce ta wuce ko wani ɗalibi a class ɗin su ba, idan kuwa bata zo na farko ba dole a na biyu zata zo. Ta tuna sanda ta gama karatun ta before ta ɗaura Degree ɗin ta, irin Big partyn da ya shirya mata da irin celebrate ɗin da suka yi, amma kuma wannan karon babu ko ɗaya, babu damar da zai shirya mata partyn da zai kasance abinda baza ta taɓa manta wa da shi ba.
Lumshe idanuwan ta kawai tayi a sanda ta kawo nan a tunanin ta, yayinda hawayen ciki suka zubo a saman dandamalin fuskar ta
Su Esha suka rungume ta suna me taya ta kukan kasancewar sun san lokacin rabuwan su ne yayi, duk da suna gari ɗaya amma kuma rayuwan school daban ne, Zamiya ce kaɗai ta fi shiga tashin hankali tunda ita tazaran su da yawa, sake haɗuwan su zai yi wuya, shiyasa take kuka sosai
Yayinda suka haɗu suka rungume ta suna me sake fashe wa da wani sabon kukan.
Sanda za su rabu kamar kar su rabu, amma babu hali haka kowa ya wuce tare da ƴan uwan sa, while MEEMA ita kaɗai ta nufi gida, a lokacin kuka sosai take yi tunawa da Ummeen ta da kuma Abee ɗin ta dake kwance a can gida babu halin fito wa. Bata iya fitowa a motan ba sanda tayi parcking a cikin haraban gidan, sai ta kifa kanta a saman sitiyarin ɗin tana ci gaba da tsiyayar da hawaye, ta jima a haka ko motsi ta gaza yi before ta ɗago fuskar ta da yayi jawur idanun suka sake kumbura, handkerchief ta saka ta share fuskar tare da daidaita ta kafin ta buɗe motan ta fito hannun ta rike da wayan ta da keey ɗin mota kaɗai domin baza ta iya ɗauko kyaututtukan ba dole ta bar su a cikin mota tayi cikin gidan.
Babu kowa a parlour'n sai ta wuce kanta tsaye ɗakin Abee
Yana