Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce ya tashi ya nufi wata ƙofa inda ta nan ne zai isa shashin sa yana shiga bedroom ya nufa ya cire kayan sa ya shiga toilet wanka yayi ya fito ya shirya cikin jallabiya brown colour ya feshe jikin sa da tsadaddun turarurruka masu kyau da tsada tuni yake fidda ƙamshi me dadi counter din sa ya ɗauka ya fito a hankali yake motsa baƙin sa yana tasbiyi sai ka kula sosai sannan zaka gane baƙin sa na motsi central mosque ya nufa

masallacin fadar shugaban ƙasa da yake an kusa kiran sallah da yake ba jami'yar su bace ke mulki sun gaisa da abokan hamayya sun gaisa cikin mutunta juna

(Wani abun sai mu talakawa in mutum baya jam'iyyar da kake ka dau gaba da shi kenan har abada wani har jafa'i kake jamai mu dena yarda masu mulki suna gwara kanmu alhalin su nasu a haɗe yake siyasa daman ita mugun wasa ne)

Sai bayan sallar Isha'i ya dawo gida kai tsaye dining room ya nufa abinci ne sunfi kala goma ajere da sauri yusrah ta taso ta cire rigar dake jikin ta yan zu doguwar riga ce me roba duk ta bi jikin ta ga uban farce da tasa yawa me shirin shan jini tace

"Bara inyi zuba maka ,

Da sauri ya ɗaga mata hannu ya nuna mata hanya

Wasu kwallace ne suka toro a idon ta ga yahun bakin ta da ya ƙafe jiki a sanyaye ta juya tana juya ɗuwawu

taɓe baki yayi domin ko a jikin sa shi yana mamakin yan matan yaxu su dinga yiwa maza tallan kan su lemon kwakwa ya zuba ƙadan sai farfesun hanta wanda yaji albasa da kayan ƙamshi ya zuba kanda ya fara ci


bayan ya gama ya ɗauki tissue ya goge bakin sa ya nufi bedroom ɗin Hajiya Turai domin yi mata sallama akan daduma ya yatarar da ita tana addu'a zama yayi a ƙasa suka shafa tare yace

"Hajiya sai dai safe,

Cire hijab ɗin ta tayi tace

"Har ka gama ?"

Eh zan je in ƙwanta gobe zan je store ne saboda a ƙwai sababbin kayan da nayi order to sun zo tun waccan satin ina so in rabawa yan kasuwa ne be dace in roƙe Kaya ba bacin ana nema


Hakane Allah yayi albarka ka

Ameen baffa yace ki fito da kuɗi kimanin biliyan hudu

"To, kawe tace mai

Tashi yayi ya nufi shashin sa shirin kwanciya yayi kasan bacci yasan ya kashe lamp ya mai da dum light yayi addu'a ya kwanta ya ja blanket ɗin sa ɗaya wayar shi ya ɗauko ya buɗe tiktok ya nemo sunan ta duk wani video nata iya fusƙarta kawe take nunawa tsaki yayi yace

Allah ka rabamu da fitinar zamani ka mar a mafarki yaga yusrah ita da wani namiji suna kiss ɗin juna sosai hankalin sa ya tashi

Wannan kenan. 10:30 pm

Zabga ƙamahi take kai kace ɓarin turare tayi a kayanta abaya ce baƙa yar Turkiyya sai taunar chengum ta ke ba kwalliya a fuskar ta amma tayi kyau mayafin a bayar ta sashi a kanta kashin kanta ya sha gyara kowa sabgar gaban sa yake a gun masu shaye shaye nayi masu soyayyar shan minti nayi masu rawa nayi masu shan shisha hayaƙi ta ja ta fisar tace


"Wallahi Binta kina ban mamaki ya kamata ki amince da muƙatar Alhaji kin san kuɗi ba matsalal shi bace ,

Dena danna wayar ta tayi tayiwa ƙawarta ta banzan kallo tace

"Rufy bani da wata daraja da ƙima sai wannan mutuncin nawa ba zan rabawa kadangarun bariki ba insha'Allahu sai na kai shi gidan mijina yar da zai kalleni da mutunci sannin kanki ne kinsan mumsa kanmu a wahala duk wani mutumin arziki baya kallon yar tiktok a matsayin me mutunci wasu ma kallon mushurukai suke mana dan haka

Wallahi ƙar ki ƙara yimin wannan zanca balle ni da duniya ke kallo na karuwa ga shi wannan najadun tsohon ya ƙara zubar min da mutunci yau Wallahi su nusi sun shiga ukku we harni zasu yiwa kahu video yana Bara sun sa yace ni yar sa ce bana bashi komai shi yasa yake bara shi yasa yau ko Kabo na ban bayar ba sun bashi kuɗi dan su cimin mutunci,



Gaskiya basu kyauta ba

Hango su tayi da sauri ta tashi ta nufi tabirin giya ta fasa ɗaya ta nufi kansu tuni komai ya tsaya aka kashe kiɗan saboda ƙar fasa ƙwalba da a kaji wayan da suka dade basu zo club ɗin ba yau sun zo domin sun san a kwai drama tun har neman magana yasa su nusi suka taɓo yar gaban goshin gwamna.........

*


Bourn page


Cikin sauri rufy ta kamo ta cikin Muryar wanda ta sha tayi manƙas tace


"Haba sister wannan ba girman ki bane kina da yara kisa suci uban su me akai akayi su nusi ko followers 1k basu da shi sun taɓo kine dan ki kula su suyi suna ,

A jiyar zuciya ta sauke ta yar da ƙwalbar a ƙasa ta ɗauki jaƙar ta rataya ta dubi nusi tace


"Za mu haɗu ko ba a nan ba kin san bana barin bashi ƙaramar arniya ki bari sai kin kai sannan sai ki taɓo ni ƙanne mata ido ɗaya tayi ƙas da hannu,

Wani irin ihu gun ya ɗauka suka ci gaba da rawar su

Ita kuwa fita tayi ranta a ɓaci jin horn tayi da sauri ta juyo

Wani matashi ne ya ci asƙin nan na yan isa ya leƙo da kansa yace

"Hey Beb how you doing ?,


Cikin ɓacin rai ta buɗe gidan gaba ta shi ga ta saki a jiyar zuciya ta biyu tace

Jazzz kai ni gida raina a ɓace yake


Wata ƙwalba ya ɗauko yace

Kullum ina faɗa miki in kina shan wannan ba ke ba ɓacin rai

Cikin I don't care manner tace

"Jazzzzzzz Please ai sai ɗauƙar hakki yayi yawa ƙarshe in shaye shaye yayi min yawa in hauka ce ko ? to ba haka nake ba nasan mutuncin kai na ,

Murmushi yayi yasa

waƙar simi me taken love don't care ya saki ya fara tafiya a hankali yana bin waƙar juyowa yayi yace

Okay Alhaji datti yace min
yau 12:00 ki same shi a government house

Ɗa gowa tayi tace

"I don't have any time,

Da katawa yayi da bin waƙar yace

"Why not?,

Banyi niya ba kasan we yana so in ƙarɓi ƙwangilal ɓata wannan pro 'azzam Bilal mu'azzam kura

Kina tsoron sa ne

Dariya tayi tace

"Ko ɗaya sai de ina tsoron Allah kasan fa sharri zan mai ,

Dariya yayi har da ruƙe ciki sai da ya gama sannan yace

"Beb tsoron Allah fa kika ce ai Wallahi da gani har ke ba batun tsoron Allah a rayuwar mu kin san kafin izo nan daga ina nake hmm Allah ya kyauta na birni ya cuci na ƙauye ,

ai kasan duk iskancin mutum akwai wan da ya fi shi wata ƙila kai kafi ni

Hmmmm kee uhmm ai Wallahi ko bokan daji haka ya ganki ya ƙƴale

Wani kallo ta yi mai tace


Uhmm haka kake gani ni Yanzu so nake in zub da makaman yaƙi na gaji Wallahi


"Ya kamata in karatu ne in roƙe kalaman ki sau nawa kike faɗar haka,


Rufe sexy eyes ɗinta tayi tace

"A kwana kin nan Wallahi ina yawan yan mafarkai ko da na tashi bana gane komai ina tsoron wani abu ya faru fa bana ganina a wannan duniya a wata daban nake gani na fa ga wani mutum bana iya ganin fusƙar sa sai de bayan sa ,


"Hhhhhhhhh ko suruki na ne?,

Hmmmm ka dena daukan magana ta wasa jazz

"To Allah ya kawo mafita,

"Ameen,


zo muyi video yau in rikita fans ɗina kin san wasu cewa suke we bakƴa video da namiji

Hmmmm kawe ta ce

Iphone 15 ya ɗauko ya shiga tiktok yace

Hey fans gani ga Princess bintu

Murmushi tayi tace

Hey fans yau gani ga jazzzzzzz nan yasa musu waƙar salim smart me taken labarina baya zama nawa inhar bake tariyi na sukai bi waƙar dai dai gidan su ya tsaya yace

''beb gobe in dawo ?'

Ba zan fita gobe ba

Okay bye

Bye fito wa tayi tsaki ta ja ganin yan zaman sha isaka da yake zafi ake suna zaune suna hira da munafurci canza taku tayi tafiyar ta tayi sai ƙas ƙas taƙalmin ta keyi

Wani daga ciki ne yace


Allah ka shirya mana zuri'a


Juyowa tayi ta ɗage glass ɗin ta sama tace

"Amin dan karuwa uban ka yasa kwabashu me huta ,

Tuni sauran sukai shiru domin sun san tsaf zata zage su

shiga soron gidan su ta shi ga ta ƙunna fitilar wayar ta da yake ba huta da sauri ta tsaya ganin meragaje da saurayinta ɗantala suna manne da juna cikin ƙunar rai tace

Dan uwar ka a she baka da hankali tunda har ka iya zuwa gidan mu kana nema ka lallata meragaje rayuwa

Jikinsa rawa ya fara yace

Dan girman Allah ki haƙuri

Uhmmm ke kuma shiga gida ko inyi kasa kasa dake kai kuma zamu haɗu a way zanyi maganin ka

Ki yi hakuri

Baza tayi mai

Meragaje ta shiga gida da gudo tana kuka

Cikin sauri uwani ta fito tace

Meragaje lafiya kike kuka

Koroni tayi muna tare da ɗantala we zai lallatani

Kan uban can ita daga ina take ke gwara kina gida ita fa

"Daga gidan uban ki ,

Hantar cikin uwani ce ta kaɗa batayi zatan zata jiba ta zata ta tsaya suyi tujara da ta saba ashe ta shigo

cikin sauri ta kama hannun Meragaje suka shiga ɗaki


Kama ƙugu tayi jin alamar ringing a jaƙar ta da sauri ta ɗauka ganin sunan yasa ta ja ƙaramin tsaki ta ɗaga tayi shiru

"Haba Binta kin sa fa dake muka do gara na tabbata in ki kayi wannan aikin Wallahi za mu sami kujera kin san fa ni zan fito ta karar gwamna nayi miki alkawarin biliyan shidda har da mota wacce ba kowa ke hawan ta ba,

Shiru tayi ta shiga tunani anya kuwa za ta bar kuɗin nan tana da buƙatar nemo mahaifin ta saboda rashin kuɗi

bata sami zuwa Saudiyya ba domin mamanta har address ɗin sa ta bata kawar da wannan tunanin tayi tace

Amma Alhaji datti baka ganin duniya zata zage ni sannan taya zan kulla mai sharri har a yarda

Wata irin shu'umar dariya yayi yace


Wannan ba matsala bane domin kinsan na iya kulla sharri da maƙirci zamu kulla mai gadar zare kuma keee zaki je zan baki karamar camera ki sa a jikin ki tunda Allah yayi miki halitta da zaki ɗauki hankalin duk wani ɗana miji in de me lafiya ne


Samin gu tayi ta zauna tace


"Alhaji tsiraici na zaku nuna wa duniya akan mulki tab Wallahi da na san Wannan banzar maganar zaku zomin da ita Wallahi da tuni na daɗe da dena harka da ku kai hmmmm,

Kin daka ta kiji mana ko fusƙarki ba wanda za a nuna sannan kuma za'a rufe jikin ki kawe hugging ɗin sa zaki yi kin fahimta sannan sai kinyi taka tsantsan muna sakin video nan zaki dawo gidan gwamnati da zama


Okay na yar da


Yauwa ko ke fa kashe wayar tayi ruwa ta ɗiba ta zuba a buta ta nufi bayi bayan ta fito ta tora ƙofar ɗakin ta da sauri ta kunna fitilar wayar ta wa zata gani cikin baƙin ciki tace


"Kut melesi jajar uban can Wallahi yau kowa ba zai bacci ba jajar uban can lalle ,

Iya da take sharar bacci bata san wacce wainar Binta ke toyawa ba

A fusace ta fito ta fara dukan ƙofar ɗakin kahu labahani

Cikin magagin bacci yace

Wane mara neman albarka ne yake tashi na tun asuba da na fita nema ban dawo ba sai hudu

Wata da bara ce ta haɗo mata ta maƙe murya tace

"Fatalwa ce ,

Cikin ɗaki kuwa tuni wani irin tashin hankali ya ruske shi Oni labahani a haka mutuwa ta zo ban cika burina ko ɗaya ba a duniya ashe a fili yake


Gyara tsayuwa tayi tace


"Ai kuwa yau zaka baƙunci lahira domin mun gani ana ta'asa a gidan ,


Dan girman Allah fatalwa kiyi min rai Wallahi ban sani ba cikin yar da bara ya sa ƙafa ya doka a wa uwani domin Wallahi ba zai fuskanci tashin hankalil nan shi ka ɗe ba yace

"Uwani tashi daman ance in da rai zaka sha kallo yau ga fatalwar gimbiya nan ta dawo kan mu,

Aikuwa cikin masifa ta ɗauko tasar da taci abinci ɗazu ta buga mai tace


"Zan fasa maka kai kafin ni ka fasamin fatsarmama in ban da ka mai dani mara hankali fatalwar gimbiya ce za tazo gidan nan?"


*Ya ku yan adam har kuna da lokacin yin faɗa alhalin yau zaku mutu*


Innalilahi dan girman Allah ai bansan gaskiya yake faɗa ba kaimin rai Wallahi bacci nake ya ta sheni

Ai kuwa yau zaku yi kwanan barzahu

Tuni uwani ta saki gudawa a zaune yayin da numfashin labahani da ƙƴar yake fita saboda ta shin hankalin da yake ciki ko mutsi ba yaso yayi ƙoƙari yake ya tuno addu'a amma ina ya kasa sai mun jaye nu'ara kulya li'ilafi yake mai mai tawa tun yanayi ahankali har ya dawo da ƙarfi.........…..✍🏼


*BINTA YAR JA GALIYA*




free page



Dariya ce ta kusan kuɓucce mata ta danne tace

"zan baku zaɓi ku zaɓa in kuna so in barku da ranku sai kun hana saurayin meragaje zuwa gidan nan in da gaske yake ya fito ya aure ta

ko in hana ku ba haya na tsawan shekara ɗari ko in saƙar maka gudawa ta tsawan shekara tamanin ,



zaro ido yayi tuni wata gudawa ta kuɓucce mai ji kake tsuuuuuu yawa an saki fanfo taɓa ƙasan shi yayi ga wani irin wari da ya game ɗakin a zuciyar shi yace


"anxu gun har an fara saƙar min tawa yasan wataran ba gudawa zaiyi ba sai de ya kashayar da ƴa'yan hanjin sa ,



duban uwani yake amma a baɗini wasu taurari yake gani sun za gaye shi yau yasan ƙar shan sa ya zo shekara ɗari ba kashi ko ƙwana ɗaya mutum beba yake ji balle mutum yayi shekara ɗari

futsari ne ya biyo baya jin har da gudawa yo rana daya mutum yayi gudawa yake fita hayyacin sa balle shekara tamanin ai kawe mutuwar tsaye zaiyi da kƴar ya iya buɗe baki yace



Innalillahi fatalwar gimbiya ku yimin min rai dan allah wallahi ba laifina bane laifin uwani ne na matsani yaron nan ita ta dage sai ya zo gun mairo

Zuface ta ƙaryowa uwani tace

Wallahi sharri yake mun kullum sai ya bashi kuɗi ko mero


MERO da ta fita hayyacin ta tayi dana sanin shigowar ta ɗakin nan tace

"Eyyy eh wayyo allah,

banzan kallo labahani yayi mata yace

"tsakani na da gimbiya a ƙwai ƙauna ta gaskiya da amana kowa na garin nan ya sheda,

FATALWAR GIMBIYA ni na zaɓi na farko zan hana shi zuwa

a'a ke naki da banne waccan tsohowar da ta kwanta a ɗakin binta zaki taso ta sannan ƙarta ƙara ƙwana in ba haka ba mu shanye muku ƙafafuwa ke da ita

"To, zan taso ta insha allah haka baxata faruba ,

Duk da halin da yake ciki be hanashi zabgawa uwani wata uwar harara yace

"hmmmm ai duk ke kika jamini saboda san ƙuɗin ki shegiya me subfar ƙaguwa ,

"kun ceci kan ku ni zan tafi chaina ,

Ɗif suka ji da sauri uwani ta tashi ta fito domin tada iya mahaifiyar ta da tazo daga ƙauye


da gudu binta ta waɗa ban ɗaki cikin ta har murɗewa yake saboda dariyar da ke cin ta in bahaka tayi ba iya ba zata fitar mata daga daki ba in tujara dake ji da ita to iya tafita

Jin alamar gudu yasa uwani ta dafe kanta domin a tunaninta fatalwar gimbiya ce ta tashi sama domin ƙarta warce mata kanta yasa ta dafe shi


"IYA IYA IYA ,

sosai tsohowar ke sharar munshari har da yahun bacci

Hannu uwani tasa ta buga matashin iya a fusace iya ta sa hannu ta buge hannun uwani tace

Dan allah ku barin na huta tun ɗazu kuke ta shina yawa wanda na ciwa wani bashi


"hmmmm iya yau fatalwar gimbiya ta zo gidan nan ɗazu ta tafi wallahi tace ƙar ki ƙara ƙwanciya a ɗaƙin ƴar ta in ba haka ba sai ta shanye mana kafafu,

cikin sauri IYA ta tashi ta zabgawa yar tata harara tace

Owani lami me yashin madina ƴar da na haifa da cikina ita ke sharara min ƙarya uwani bura'uban ki uwani na yi miki kama da wacce fatalwa zata ambaci sunan ta to yasin har in bar gidan nan a ɗakin nan zan ƙwana


Wasu hawayene masu yaji suka zubu a idon uwani tace dan girman allah iya ki zo mu tafi ƙar suji ja'in jar da muke da ke

zani ta gyara ta fyace majina ta sai ta matashin ta ƙwanta tace

Alƙur'an uwani ki fita adona in rufe wallahi uwani ina raga miki da iliyane da tuni na zubar mai da haƙura ai ɗazu itama shegiyar ina jinta nayi mata shiru domin ban zo gidan nan in ƙwanta a tabarma ba nazo inji laushin katifa ai gashi ta haƙura ta fuce tasan duk tujararta na fita hhhhhhh gaba da gaban ta aljani ya taka huta




majina uwani ta face ta haɗa hannuwanta biyu tace

"IYA dan girman Allah ki haƙuri ki taso mu tafi ,

wata uwar ɗirga sukaji a lamun abu buwa sun sauka tuni hanjin cikin uwani ya cure gu ɗaya ta fara zare idanuwa domin ba baƙin magana IYA ta ja musu da ta taso da duk haka bata faru ba

"wani irin ƙugi su kaji guggugug wata ku bil adama kuna da taurin kai na baku dama ku fita ƙunƙi gashi ni har naje chaina na dawo kuna zaune ,


zaro ido IYA tayi ya dafe ƙirji daman tun zuwan uwani da ta bita Allah sarki ashe sona uwani ke yi oni lami na shiga ukku yau sai ta Allah tace


*"UWANI* in kin sami kuɓuta ina bin matar me gari naira hamsim kuɗin daddawa ki amso kiyi min sadaƙar ashirin da biyar sannan ki gina min masallaci da raguwar kuɗin tun huri na keso in iya sa'alun amma sakalci na ya hanani

yanzu da tayi min rana ina zuwa ƙabari ana tambayata in amsa kuka tasa domin ba haka ta so ba taso abar mata jiran duniya ,

zuba mata ido uwani tayi da alama IYA ta fita hayyacinta bata san me take faɗa ba yanzu har yaje chaina ya dawo ji tayi fa a radio ance ba ƙasar da takai chaina nisa

"ɗazu na ƙafa muku sharaɗi kun bujere min to zaku rufe idanuwan ku har sai wani daran yayi sannan ku buɗe in kuka ƙus kura kuka buɗe to fa rundunar aljani gushshu zatayi sama daku sannan ki faɗawa labahani ƙar ya sake ya ƙara fita waje da sunan bara sai de yaji anyi sama dashi bashi ba dawowa,

"To mun gode ,


tuni suka rufe idon su suka fara laluban ƙofa ruge ruge suka shi ga yi ganin uwani ta bangaje IYA ba ta luraba yasa IYA ta fusgota ta dawo da ita baya tayi wuf ta futa gani take in ta ƙara second ɗaya rundunar aljani gushshu zata yi sama da su


Ganin iya ta futa yasa itama ta fita a guje har ta buge da garo ɗakin uwani suka shiga suka cure gu ɗaya hakama malam ya zuba ta gumi dan ko shakka babu yasan fatalwar gimbiya ce ta zo musu ba mala'ika ba duk abin da ake yana ji har da hana shi bara

duban mero yayi duk ta fita hayyacin ta sai surutai take allah ya rufawa saminu asiri da yau be ƙwana a idan nan ba

da ya ƙwana da dashi wannan rundunar gushshu zata haɗa domin ai ba zasu bar shi ba saboda kajin mutane da yana sakat a garin nan kullum cikin cin kaji yake suma harya sammu su




*WANNAN KENAN*



"wallahi momcy duk abin da zan ja hankalin sa ina yi amma wallahi a banza anya kuwa yana da lafiya?,


YUSRAH ki nutsu ki gano abin da baya so da wanda yake so shine fa amfanin zaman ki kenan a gidan wallahi na ƙwaɗayin dukiyar gidan alhaji ƙura kin san kaf ƙasar nan ba na biyun su a ƙuɗi da mulki ke ce wacce zata zamo silal dawamar mu a daula kinsan a kullum sai naji ɓakin cikin hajiya turai saboda mahaifin mu ya fi son ta shiyasa har ya bawa bilal auran ta lokacin da na gane haka wallahi har ƙwanciya nayi a asibiti ƙarshe sai ya haɗani aure da mahaifin ki wanda bashi da wata shahararriyar dukiya dan haka wallahi ko zan yawo tsirara sai na rusa hajiyan turai akomai


MOMCY yanzu wanne mataki zamu ɗauka naji hajiyan turai tana cewa we waccan shegiyar yarinyar zata dawo gidan nan


ƙwafa tayi tace


"Uhmm zanyi maganin ta ,



MOMCY ya zanyi ya so ni duk abin da nake kamar baya gani fa


Dariya tayi tace


"YUSRAH yana kula da komai halin su ɗaya da mahaifinsa zai nuna miki kamar besan komai ba to kisam mummuƙe yake yana lura da komai sannan duk kan wani taƙun kowa yana sa mai ido amma zanje gun bokana Jibi,


"TO bye,

"Bye,


washe gari 🌅


cikin sauri yake komai saboda yau suna da taron jam'iya gashi sauran ƙwana sittin zaɓe wani satin za ai primary election za su yi tsare tsaran abubuwa geznar yasa blue black tayi mai kyau abinka da farar fata yasa black shoe ga rolex black a hannusa hula ya sa me tangaran gyara babbar rigar sa yayi ya sai ƙamshi yake zab gawa

ɗauki brief case ya ɗanna remote ya kashe komai na ɓangaran sa cikin nutsuwa yake taka stairs case wayar shi ce tayi ƙara alamun shigowar message be biya ta ƙai ba ya nufi shashin hajiyan turai duk inda yabi sai sojojin nan sun gaishe da shi amsa musu yake cikin sakin fuska

a bakin ƙofar hajiyan turai ya tarar da sam driver sa sam yace


"good morning sir ,


morning sam

ɗur ƙusawa yayi ya amshi brie case ɗin sa

miƙa mai yayi

Cikin hausar sa mara fita yace

"sir ga sabuwar jaridar c.n trues ,

cak ya tsaya be juyo ba yace


innaje office zan duba ta

"sir is very important ,

juyowa yayi ya amsa shafin farko yaga picture ɗin shi anyi rubutu da manyan baƙi

*SHIN KO KUN SAN DALILIN DA YANA ƊAN TAKARAR SHUGABAN ƘASA AZZAM BILAL ƘURA YIN AURE* ✍🏻



*Binta yar jagaliya*


*Oum yasmeen yar mutan yakasai*



Zubawa rubutun ido yayi yawa me shirin gano wani abu wato in kana so ka san asalinka shiga siyasa rintsai don sa yayi a hankali bakin sa ke furta

*HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL*

ba abin da ya ɗaga mai hankali sai we ana zargin sa da yana hurɗa da karuwa shi yasa yaƙi aure ringing ɗin wayar shine ya dawo da shi hayyacin sa da sauri ya ɗauka ganin mahimmancin kira yasa dole ya ɗaga yayi shiru


AZZAM kana dawo wa daga taron jam'iya ka biyo jirgi ka tawo akwai matsala duk da alhmdllh nayi maganin matsalal


to kawe yace mai sukai sallama kai tsaye shiga ciki yayi domin gaishe da hajiya turai sai wanda ya karan ce shi zai gane cewa yana cikin fushi sosai fuskar sa har ja tayi abinka da farin mutum cije leɓansa na ƙasa yayi a rasa da me za ahaɗa shi sai da zina rumtsai ido yayi tambas siyasa mugun wasa ne in baka da juriya ka shigeta sai a haukata ka ba abin da ya tsana ya ƙƴamace shi irin zina dai dai ta kansa yayi yayi sallama


cikin fara'a ta am samai yace

"lafiya azzam naga yanayin ka ya sauya wannan fa jaridar da ka duƙunƙune ta me ke faruwa?,

risina wa yayi ya ƙaƙalu murmushin dole yace


"hajiya bakomai barka da safiya kin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment