Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"tanimu be jira abinda ummuh zata fada masaba ya kama hanya ya futa daga cikin gidan baki daya,

****bayan futar tanimu zama ummuh tai tashiga rusa kuka, kamar ranta zai fita, gaba kidaya ta fita a hayyacin ta tunkafin ahe ko ina, gani tai ba tada wanda zai rarra shetane,hakan yasa ta share hawayan ta, ta sa hannu ta dakko "AMANIH, ta tsuramata ido cike da tausayin ta, harga Allah ita dai tasan tana kaunar yarin yar har cikin zuciyarta,hakanne yasa ta kiyar da tabawa umman indo I'ta, jitai ana kwalla kiran sallar la,asar, da sauri ta dauki zani ta goya AMANI,sannan tadau buta tai alwala, bayan ta idar da alwalar ne ta dakko dadduma, ta shimfita ta ,tada kabbarar sallah.

Duk da kasancewar ummuh nada karancin shekaru,amma hakan be hanata rike addinin taba, yarinyace me hankali,da tarbiya, ga sanin da rajar nagaba da I'ta , ga wayo acikin ummuh kamar me, idan ko tana magana sai ka rantse wani babban mutum dinne yakeyinta, ga kafiya acikin ummuh,idan ummuh tace zatai abu to zatayi shi dinne, dagaske, "idan kuma tayi alkawari,to tabbas zata cika alkawarin nan. Ummuh nada kyau sosai wanda idan ka kalleta sai ka kara dora idonka akanta, koda kuwa kedin macece, shiyasa dukkannun mutan kwauyansu suke kaunarta, akwaita da shiga zuciyar mutum,sai kuma kanwarta AMANIH ta zo ta take ta,dan tafita Kyau da hasken fata,duk da ita din jaririya ce,.

Bayan ummuh ta idar da sallar ne ta zauna, tashiga yin tasbihi, da salatin annabi muhammad (s,a,w)daga bisani kuma ta dakko qur,anin ta tashiga karantawa da voice dinta mai shegen dadi, bayan ta kammala karatunne,ta daga hannunta sama tashiga yin addu,o,i,tana cewa,. Ya ubangiji na ya maji 'bancin al,amarina,ka tai makeni, karda kabarni da iyawara, Allah ka min jagora akan rukon AMANIH,ya ubangijin sammai da kassai,ka tallafi rayuwar mu, bamu da kowa sai kai, kaine komai namu, mun rasa uwa,munrasa uba, bamuda wa,bamuda "yan, uwa duk sun gujemu, Allah na rokeka kada kabarmu da kanmu, kashiga lamarin rayuwar mu, ya Allah,Ameen ya Allah,sannan ta shafa addu,ar ta tashi tanade sallayar ,tashiga dakin umman ta Inda ita wasu kudade, a karkashin filon ummanta,nera dubu 5000, sosai ummuh taji dadin ganin kudinnan duk da batasan ko na wanene ba,amma tanada tabbacin na umman tane,

Wasu siraran hawaye ne yashiga zuraro mata akan kuncinta, babu abin da takeyi a lokacin sai tunanin,yadda za ai yarinya karama kamarta, ta zauna ,uwa ba kwa'ba, uba ba kwa'ba, ba wani tsayayye wanda zai jagoranci lamarinsu, amma ba komai akwai Allah shizai yauemana duk wata da muwa, ba boka, ba malam, Allah kadai ya isa.

__________yau fa ummuh tatashi ko sisi batada ita "kudin da tagani akarkashin fulon umman ta ya 'kare ,gashi AMANIH sai kuka takeyi tana jin yunwa,gaba kidaya tahana ta sakawa,tarasa inda zata saka ranta taji dadi,kawai itama sai tafashe da kuka, mara sauri, ta na rokon Allah ya kawo mata dauki.


Tana tsaka da kukan da take taji yo sallamar wata makwaf ciyarsu, inna asabe,a han zarce tashiga goge hawayen fuskarta,sabida bata son wani yasan halin da takeciki, kar makiya su samu damar yimata dariya.

Aslmualaikum amin wa alaikumussalam,
A,a inna asabe kece yau agidan namu,eh ummuh,wallahi wani gagari min abune ya kawoni, to inna asabe bisimillah,gaguri kizauna, zama inna asabe tai ,sannan ummuh ta mike ta debo mata ruwa,ta bata tasha, sannan tace ina wuni ?lpy klau ummuh yakuke, ya kan war taki,?lafiyar ta klau alhamdullah,masha Allah,daman Wana muhimmiyar magana ce ta kawoni, anan kasan kauyan nan naji ana neman "yar aiki kamarki, tunda naga ke ba aure zakiba, ko ma dai zaki aure babu me aurarki a garinnan, sabida kin huce minzalin da akewa yara aure a kauyannan,shiyasa na ce bari nazo na fada miki idan kinga zaki 'iya, wallahi zaki samu kudi me tsoka wanda zaki kula da Rayuwar kanwarki, shiru ummuh tai "tana nazarin maganar inna asabe,

Kinyi shuru bakice komiba? Inna asabe zanyi mana ayanzu babu abin da nake bukata wanda ya wuce na taimaki Rayuwar AMANIH,amma inna"" inason ki yimin wani taimako, inajinki ummuh fadamin inzan iya taimaka miki,daman AMANIH ce take jin yunwa sosai kuma kudaden hannuna sun kare, balle nasiya mata madara, ko zaki taimaka kibani aron muttala biyar5, nasiyo mata madara,........indai wannanne zan iya taimaka miki,sai dai dashara di yaushe zaki biyani?? Ina fara yin aiki zan biyaki kudinki insha Allah,

UMMUH AMANIH
By
Hafsa. Umar dangoro yarmutan
BAKIN RAFEE

漏锔� JARUMAI WRITAR's ASSOCIATION 馃摎馃摎鈿滐笍 J. W. A馃枊锔�




Pege 4

Tom shikkenan, inna asabe ta kwance bakin zaninta ,ta 'irgo mata muttala biyar ta bata, sannan ta mata sallama, daniyyar gobe zata zo sutafi gidan aikin, godiya sosai ummuh tayiwa inna asabe, bayan tafiyar tane ta durkusa kanta akasa, tai sujjada ga ubangij madaukakin sarki, wanda baya barin bawan sa da yunwa, daman akullum ummanta tana fadamata cewa, bakinda Allah ya tsaga baya hanashi abinci, tabbas babu makawa tayarda da zancen mahaifiyar ta, Allah sarki ummana Allah ya jikanku ya sa aljannace ma koma, ameeen.


______________tashi tai daga Inda take, ta dakko zani ta goya AMANI sannan,ta janyo kofar dakinsu ta fuce, daga gidan gaba kidaya, tafe take tana tafiya tana nishi ,saka makon jaririyar tayi mata nauyi, daker take iya daga kafarta, har ta karasa shagon_rabi,u me kanti,sallama tai Masa, sanan ya amsa, bayan ya amsane yace meza abiki, madara zakabani,ta muttala uku, ~~~~dakko mata yayi sannan ta mika Masa kudin ,ta juyo tacigaba da tafiya, sai da ta kusa zuwa gida, ta hadu da dan_dozon yara suna wasa, sai kallonta suke yi,suna tuntsura mata dariya kamar sunga ma haukaciya, bakaramin kuluwa ummuh tai ba, taso ace babu amani abayanta, da duk saitaci uban rayar koma yayan uban wane, bata ankaraba taji suna rera mata waka suna bin bayanta, wai tayi cikin shege ta haiwu, takiyin aure,tayi kwantai, haka suka dinga binta suna tsokanarta, duk Inda suka wuce ana bin su da kallo, ana nuna ta,da yatsa.


************gani tai bazasu daina tsokanar taba hakan yasa ta fashewa da kuka,tana tafe har ta karaso kofar gidansu inda ta tarar da wani dattijo a kofar gidan,tabbas bazata manta wanan fuskarba, domin wanan mutumin shine megidan nan, daman can su umman su haya sukeyi agidan ba gidan subane, nanfa ummuh ta hadiye kukan da take tashiga furta, innalillahi wainna ilaihirraju,un, innalillahi wainna ilaihirraju un,sai da ta maimata kalmar so uku sanan ta ta karasa Inda yake cike da fargabar abin da zai ce dasu,


Assalamualaikum,dakatar da ita yay yace, ruke sallamar ki ba ita bace ta kawoni, bani kudin haya, ko yanzu nasa afutar min daku daga gidanan, jiki a sanyaye ummuh ta sulale ta durkusa guwoyinta a kasa, tace ka taima kamama kamar da allah ya tai makeka, ka rufamana asiri kamar yadda Allah ya rufamaka, kada ka tona Mana asiri,wallahi idan kakoremu daga gidanka bamu da Inda zamuje, saidai mu ta yawo agari muna rabe_rabe, to ni ina ruwana da ko ina ma zakuje, nidai kudin hayata kawai na sani,,, ke bandama fa ba kyau tone,tone ubanki ma da ya mutu be biyani kudin hayata na wancen watanba ya mutu dan haka ko ki biyani kokuma na sa aimin waje dake, wasu hawayene masu dumi da azaba, kamar yaji, suke zubowa daga idon ummuh, wani abu take ji azuciyarta yana turiri kamar an hura wuta, ayan zu ummuh tariga ta saddakar, da zamanta a gidan, ammafa ta ci alwashin ko da ba da halak ba sai tayi yaki da talauci,


Ke uban me kike"tunani cewar wanna dattijon,kitashi ki shiga ciki kidebo tar kacenku kubarmin gidana,!!!!!! ________muryar tanimuce ta daki dodon kunnen su yana cewa, dakata baba tsoho, basai ka koresu ba ni zan biya kudin hayar, nawane, kallonsa baba tsoho yayi yace, to kaikuma a dangin wa,?? Cewar baba tsoho, adanginta kuma me sharemusu kuka aduk lokacin da suka tsin ci kansu cikin damuwa,

Tunda tanimu yafara maga ummuh batace komaiba sai yanzu,me ka ce tanimu???? Kace kaine kake sharemana hawaye aduk lokacin da muke cikin damuwa, wallahi tanimu karya kake, ni ubangiji shike futar damu daga cikin damuwa kuma shi ya ke share Mana hawaye ,ba wani Kato kamar kaba, tani mu natsane ku wallahi daga kai har iyayanka, kufita daga Rayuwar mu bamu bukatar tai makonku,,takarasa maganar tana fashewa da kukan bakin ciki, duk wanan abin da ummuh take tanimu be saurare taba, ya ciro kudi ya bawa baba tsoho kudin hayar gidan, har da nawani watanma, kana ya kama gaban sa,shiko baba tsoho ganin anbashi kudinsa ya kalli, ummuh yace Allah ya taimakeki, ki a yadda kikai kwantan nan ma, uban wa zai aureki , kinsamu yaro me hankali, yana kashemiki kudi kina Masa rashin kunya, mara kunyar yarinya kwai, mai kamada aljanu, bayan yagama karewa ummuh tas sanan ya kama hanya yabar gurin , yabar ummuh atsugune tana sharar kwalla, ahan kula ta furta, na shiga uku ni ummuh ina zan saka kaina meke faruwa da rayuwatane, daman haka duniyar nan take meyasa ban mutu nabi umman na ba, jitai an dafa kafadar ta, zumbur ta juyo indo tagani tsaye tana sharar kolla,zagayowa tai gaban ummuh ta tsuguna, tana cewa, ummuh, ummuh!!anya kece kuwa Kinga yadda kika zama meya ke faruwa ne, ummuh ce ta dubi indo ta share mata hawayen fuskarta,tace indo kidaina kuka, kinji ni ma nadaina yin kukan, meyasa bazan yi kuka ba ummuh Kinga yadda kika zama kamar ba ummuh ba, wallahi kin canza.

,uhmm indo kenan badole na canza ba"mahaifiyata ta rasu,mahaifina ma ya rasu, dan gina sun gujeni, sabida bama da komai, indo ashe daman ganin idon iyayankane, yake sawa ayimaka wani abun, dubafa ""! Indo har yara sun rainani, tsokanata fa akeyi wai nayi cikin shege, na haifi amani, naki aure, kuma wallahi indo babu wanda yayi musu magana saidai ni da ake bi da kallo, indo narasa madafa narasa gata, nazama mujiya acikin mutane, shin menaiwa duniya da mutanen cikinta, wayasan gobe, suka sanima nice zan taimakesu wataran, indo ba ayiwa bawan Allah haka, tabbas nayarda ni baiwar Allah ce kuma na yarda akwai ubangiji,yana sama yana kallon duk abinda ke faruwa da wani bawansa, kuma nasan duk daran dadewa Allah bazai barni hakaba zai taimakamin,,,,takarasa maganar tana shashshekar kuka,


Indo wadda tumtuni hawaye yaga ma wankemata fuska ne ta tsaya tana bin ummuh da kallon mamaki,yarinya karama amma jiyadda take tsara magana kamar wata meshekara,50 aduniya, tabbas tayarda ummuh"yar baiwace, tayarda itadin ayace,tabbas akwai abinda ubangiji ya boye game da rayuwar ummuh,


Hannu ummuh takai ta dan taba indo, tace, indo tuanin me kike haka,kidaina kuka nima nadaina, tashi mushiga gidan, inbawa amani madarannan yunwa takeji, kinga harta gaji da kukan tayi bacci.


____________________to bayan sun shiga gidanne ummuh tace"indo dan Allahamani bari naje nasayo gawayi, kinsan ummanku tace nadinga dumama ruwan kafin na damamata madarar,tom shikkenan ummuh sai kindawo, amma ki sauri,

Tafe take tana faman yin sauri harta isa gurin masu saida gawayin sallam tai musu sanan ta abata gawayi na muttala 'daya, karbar kundin yayi yabata gawayi, takamo hanya ta taho gida, sai sauri take a hanya kamar zata tashi sama,harta isa kofar gidansu.

Aslamualaikum, tarugo dagudu zuwa inda ummu tashigo gidan,innalillahi, ummuh kinga wani abu kefitowa abakin amani,,kallifa kamar tadaina motsi, a tsorace ummuh tasaki gawayin dake hannunta "tace indo kawota nashiga uku,kardai ta mutu, gaba kidayan su suka fuce daga gidan suna tsuga gudu, ummuh tana gaba da amani ahannunta,"indo tana binta abaya"

__________sai da sukai tafiya menisa daga kauyansu, sanan suka "isa asbitin dake gaban garinsu, wanda idan kudin adidaita zaka biya sai kabiya akkallah kamai nera100, su ummuh suna shiga harabar asbitin dasauri suka nufi inda suka hango wani likita yana tsaye,tsabar tashin hankali ummuh bamasu kula da wata mace dake gefan likitan suna maganaba, tsabar tashin hankali bata saniba tataka wanan budurwar dake gefan likitan suna magana!!!! Ta karasa gurin likitan bakinta na rawa tace,likita ,dan Allah kataima keni kanwata batada lafiya wallahi idan ba kataimakemuba mutuwa zatai, doctor mansur ne ya bude baki zaiyi magana ,amma saukar marin da fatima ta feshe ta dashi, atake agurin ummuh tagawasu taurari sun bayyana, tsabar azabar mari, kafin ta ankara fatima takaramata wani marin da harsaida ummuh ta furta karmar innalillahi wainna ilaihirraji un, mekefaruwa danine,saukar sassanyar muryar fatima taji tana ratsa dodon kunnenta, ke ni sa arkice da harzaki takani kihuce,"tsabar kin rainanima ban isa kitsaya ki bani hakuriba,da man irinku "yan kauyen nan bakuda kunya,ya isa haka fatima cewar doctor mansur,dakata ! rufe min baki anan gurin ban saka dakaiba "irin wadan nan masu abu kamar dabbobi irin mu mumike maganinsu,to wallahi tajajawa kan tama ,babu wanda zai karbi jaririyar nan ya dubata,ai ummuh da jin wannan maganar gaba ki daya kafafuwanta suka kasa daukar gan gar jikinta"ta mikawa indo amani kana ta sulale agurin,bata san lokacin da takama kafar fatima tana bata hakuri ba, dan girman Allah hajiya kiyi hakuri, kitaimakeni kamar yadda ubangijin mu ya taimakeki, kibari aduba kanwata, kada na tasata, wallahi summa tallahi ita kadai nakeda ita aduk fadin duniyar nan, dan darajar annabi muhammad (s,a,w,)ki ji tausayinmu,kada kibari "yar uwata tarasa Rayuwar ta ,takarasa maganar tana kuka kamar zata zauce,itako fatima ganin yadda ummuh take bata hakuri da rokanta hakan yasa takara samun damar cimata mutunci,daman ida arayuwarta tana kaunar taga ana durkusa mata to saikuma tasamu ummuh baiwar Allah,fatima ce tasaka kafarta dakarfi ta take yatsan ummuh guda daya,ta bangaje ta ta huce, tare da bawa duk wani likitan asbitin umarnanin ,karda asake asaurari ummuh,sann tai tafiyarta, shima doctor mansur kama hanyar sayay yajuya zai bargurin sabida bazai iya kallon irin wanan rashin imanin ba,amma kash "kafin yabar gurin ummuh ta sha gabansa ta na rokonshi kamar wadda take rokon aljanna agurinshi,?kiyi hakuri "yar nan bazan iya tai makon kiba kiyi hakuri kutafi, yana gama fadar haka yashige office ya bar ummuh atsaye tana tusa uban ihu,kar wadda za a yanka,

****************indo ce ta karaso gurin tace,ummuh kiyi hakuri kitaho mutafi,wannan kukan da kikeyi bashine mafutaba, tajanyo hannun ummuh suka futa harabar asbitin, guri ummuh tasamu ta zauna jiki a sanyaye,ta mika hannu takarbi amani ,ta kuramata ido tana kallon kekkewar fuskarta, ahankula ummuh tafurta, Allah sarki "yar uwata,Allah ya tashi kafadunki, kodan ki zama wani abu a kasarnan,harki taimaki wanima,ta karsa maganar tana sharra kuka,itako indo kallon su take cikin tausayi, hakika tana tsananin tausayawa Rayuwar su musammanma amani wadda ayanzu badu san tana rayeba ko ta mutum....
UMMUH AMANIH
By
Hafsa. Umar dangoro yarmutan
BAKIN RAFEE

漏锔� JARUMAI WRITAR's ASSOCIATION 馃摎馃摎鈿滐笍 J. W. A馃枊锔�

Pege 5

______________su ummuh suna zaune a harabar asibitin ko motsawa ummuh takasayi, sabida tsananin tashin hankalin da takeciki,gaba kidaya sun gama saddakar wa amani ta mutu,"in sukai ana doso Inda suke,indoce ta fara daga kanta tana kallonshi, da sauri ta fara jijjiga ummuh tace ,ummuh kinga likitan, kizo mukara rokonshi kozai tai maka mana yanzu tuda matarcan tatafi,ai ummuh tana jin hakan tamike suka karasa Inda yake, likita dan Allah kataima kemu , doctor mansur ne yace okay kuna son intaima ka muku,?? Eeeh munaso harsuna hada baki, okay zaku iya biyoni gidana,shuru sukai nadan wani lokacin, kowa yana tunanin anya ko suje,suna tsaka da wanan tunanin doctor ya kara cewa, okay naga alamun baku bukatar taimakon nawa,kunga tafiyata,ya kama hanya zai bar gurin,caraf indo ta ruko rigar jikinsa tana cewa,a,a doctor baza ai hakaba,ummuh taho mubishi,


****Haka su ummuh suka kama hanya sukabi doctor mansur gidansa,dake kasan garin, sun isa yabude kofa suka shiga, gidane 'dan madaidai ci me kyau na zamani, ya tsaru da kayan more rayuwa kalakala,saida suka shiga falon gidan doctor yace ina kudi aikin jaririyar, ? ummuh ce tai karfin halin cewa bamu da kudi, doctor katai makemu dan Allah,!!.

____________kunsan abin da bazai taba yuwuwaba, bazan iya wannan taimakon ba, zaku iya kama hanya kubarmin gidana,kukan suka shiga yimasa suna magiyar ya tai maka musu, amma ina ko kallo basu ishe shi ba,can kuma bayan yashiga daki yafito ,ya dubesu yace,kuna da kayan kudi ajikin ku zaku iya bani, nikuma zan taimakeku, indo tai karaf tace bangane me kake nufiba doctor,hhhhh ina nufin daya daga cikin ku tabani kanta,durum gaban ummuh da indo ya fadi,daker ummuh ta tattaro sauran jarum tarta tace, haba likita ,anya ko kana da imani,ace kagammu haka "yayan talakawa kamarmu, ko kudin daza a nemawa kanwarmu mun gaza saminshi, amma kadinga kiran mubaka kanmu, anyako kana cikin hayyacinka, okay ba kwa bukatar kanwar taku tarayu ,kutashi ku fucemin daga gida, "jiki babu kwari da indo dakuma ummuh suka mike zasu futar Masa daga gidansa,saida suka zo daidai bakin kofar da zata sadasu da harabar gidan, indo ta tunkudo ummuh waje, ta rufe kofar jikake gorof atake jamulok din kofar ya shiga,nan danan fa ummuh ta shiga bugun kofar, tana kiran sunan indo, itako indo babu abinda ke fitowa daga bakinta sai,, ummuh kiyi hakuri ,kin rasa mahaifiyarki, sannan kin rasa mahaifinki, bazan iya zuba ido na ga kin rasa "yar,uwarki daya tilo aduniyaba, dan haka na amince zan bawa doctor mansur kaina,domin samawa amani lafiya,.......


________innalillahi wainnailaihirraju un, indo kar ki haka, dan Allah kirufamin hasiri, ki hakura da aikata zina,dan Allah karki banzatar da rayuwarki akan kanwata, kibude ta kontar da amani atsakar gurin tashiga bubbuga, kofar da karfi, tana kuka tana kiran sunan indo da kalmar Innalillahi wainnailaihirraju un,jitai anyi shuru, can kuma sai taji indo ta kolla wata uban kara tareda kiran sunan ummuh,atake agurin ummuh ta sulale kasa jikake temmm,ta fadi sumammiya,...........





AMERICA

__________ Zaune yake ya harde kafa yana jijjigata ,hannunsa rike da wayarsa, sai kira ake amma yaki dauka, kekkewan saurayi mejini ajika, me kimanin shekara 23 aduniya, daga ganinsa kaga namiji me cikar kamala da zati , idanunsa a lumshe she balle na tan tance wana kalane 妫e啯顫� wow masha Allah,daga lokacin danayi arba da kekkewan bakinsa dan tsuet,jajawur kamar nalashe, tsabar kyau妫e啯瀚� hancinnan kuwa Inda kasan biro dan tsayi,masha Allah gayan ya hadu ta ko ina, ga wani faffadan kirji danai arbadashi, irin wanda idan kin konta zai miki rumfa dashi, ban kara tsorata da ken bawan allan nanba sai da nayi arba da lallausar sumar kanshi,me sulbi sai kelli takeyi, farine tass dogo bashida wani kiba sosai ammafa yanayin kirar jikinsa a kawai kyau,********kirane ya kara shigo wa wayar dake hannunsa mekyau da tsada wato Iphone 14,妫e啯鎳嶆#鍐╂噷, a han kali ya bude bakinsa ya furta kash waye wannan, wowwwww murya mai dadn gaske, ahankula ya kara wayar a kunnensa ya fursa assalamualaikum..........妫e啨浜�


________~~~~~~~~________daga can bangaren aka amsa amin wa alaikumussalam,? AMERICA ,barka da yamma,yaya AJILAN妫e啯顎� ina Fatan dai kana cikin koshin lafiya, KANO,_ ____ban sani ba da bana lafiya zakaji muryata haka,tukunnama in tambayeka EJILAN, uban me kakeyi ina takiranka baka daukaba? Am sorry my bro, ina dan wani uzurine,okay shikkenan kabiyo jirgin asba gobe kataho, lallai,lalai dady yana son ganinka,insha Allah yaya AJILAN,sanan sukai sallama ya kashe wayar,
K ANO
________________ aban garen yaya AJILAN,fito wayayi daga cikin bargon shi dake lokacin ana sanyi sosai, hakan ne yasa ya lulluba,kafarsa ya fara sakowa, sai kelli take da kyau tsabar gera da cima me kyau ,da kuma hutu,kafin daga bisani ya sa hannu ya yaye gaba kidaya bargon, wow妫e啯歇na zaro ido saka makon tsananin kamar su da nagani da wancen saurayin dake zaune a kasar AMERICA,ko mai na su "iri dayane babu banban ci ko kadan,a hankula ya ke takawa daga cikin dakin harya shiga bathroom,. Bayan minti biyu tafito fuskarsa dauke da danshin ruwa, ammafa sai dai atamke take, kamar beta ba dariyaba妫e啯袞,fito wayayi yanufi babban falon dake gidan masha Allah iya tsaruwa ya tsatu gidane na "yayan masu fada aji,dan zan iya cewa ko gidan shugaban kasa albarka, kaitsaye wani bedroom yanufa ,dauke da sallama abakin sa aslamualaikum,yatsaya afalon dake cikin dakin,daga can cikin dakin ne aka amsa masa da wa alaikumussalam,Al_hasan shigo mana, ____a hankula ya tura kofar dakin ya shiga, zaune yake a gefan gadon sa kekkewa dashi saidai kusan kamar su daya da wanan saurayin da aka kira da Al_hasan,karasawa al__hasan yayi ya zauna a gefan sa tare da furta __barka da yamma my lovely Dad 妫e啯顫抌arka dai my son , ina fatan dai ka sanarwa da Al__al hussai sakona, ?eh!!! Daya na sanarmasa, kuma insha Allah yau da asba zai biyo jirgi ya taho,masha Allah my son,damn nan dana kemaka kenan zaka iya tafiya Allah ya muku albarka 妫e啯顫� amin dady 妫e啯顎� ya tashi ya futa.



__________ a bangaren su UMMUH kuwa, indo ce dauke da amani a hanunta sai dariya takeyi irin nasu na jarirai,,fitowatai dauke da ruwa adaya hannunta, ta watsawa UMMUH a tsorace,UMMUH tai furgigita ta tashi tana. Ambaton sunan Allah da kalmar Innalillahi wainnailaihirraju un,Allah dai yasa mafarki nake ba gaskiya bane ,tare da riko indo, indo dan Allah karki cemin da gaske kinbawa wanan fasikin mutumin kanki,妫e啯肖妫e啯肖 dan Allah kifadamin ,kiyi magana mana indo dan Allah kice wani abu mana ta kara fashewa da kuka妫e啯肖妫e啯肖妫e啯肖妫e啯肖indo ce ta fara magana ,wadda daker take iya motsa bakinta tsabar tashin hankalin da take ciki,ummuh ba mafarki kike ba dagaske ne nabawa doctor mansur,kaina adomin na nemawa amanih lafiya,kuma cikin ikon Allah kinganta ta warke妫e喚妲� dago mana ki kalleta tana dariya, itadai ummuh kallon indo take cike da tsan tsar kaunarta, hakika aduniyarnan samun kawa kamar indo zaiyi wahala, gaba ki daya tarasa ma mezatace inbanda bin indo da take da kallo,idanunta tana zubar da hawaye, ita ba wanan ba me zatacewa umman indo idan sun koma gida,tabbas ta gama sadda karwa tata takare a kauyansu, kawaii ummuh datarasa me zataiyi alokacin, saita dora hannu aka ta fara rusa uban ihu, tana furta nashiga uku!ni ummuh ina zan saka rayuwata, natsani duniyar nan da duk abin da ke cikin ta妫e啯肖妫e啯顎忔#鍐╊€忔#鍐╊€忔#鍐╊€忔#鍐┬ゆ#鍐┬ゆ#鍐┬�

UMMUH AMANIH
By
Hafsa. Umar dangoro yarmutan
BAKIN RAFEE

漏锔� JARUMAI WRITAR's ASSOCIATION 馃摎馃摎鈿滐笍 J. W. A馃枊锔�

Pege 6

____________ke uban me kuke min haryanzu a cikin gidana,zaku futarmun daga gida ko saina samuku duka, UMMUH dai metake inbanda zubar hawaye,tana bara baki, tana kuka, doctor mansur dayaga alamun ummh sotake ta tara masa mutane, ai da sauri ya sa hannu ya jata feeeeee kanar wata kayan wanki ,bedire ta a ko inaba sai a waje,sannan yadawo ,ya dakawa indo tsawa ha'de da cewa ke uban me kike jira da baza ki tashiba, itadai batace ko maiba, sai yun kurin da tai zata tashi amma ta kasa tashi, sabida tsananin azabar da

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment