Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

turnikesa" ya mike aguje yashiga kicin ya debo ruwan ya taho da sauri,


Faruk kuwa hakan bakaramin dadi yamasaba ,ashe haka amatullah takesona ,daman zata iya mutuwa idan namutu,masha Allah,yanzukam nayarda ni takeso,yana tsaka da wannan tunanin yaji saukar ruwan sanyi ajikinsa,saiga faruk yamike yana muzurai,shiko sudes tsaki yayi ya kama hanyar dakinsu,jiyayi amatullah tace yaya sudes,yajuyo a fusace yace menene,?ya tamke fuska,daman ciwannaka kadawo mutafi asbiti,bazan jeba,da kindamu da ciwan nawane,ya shige daki yabar su baki a sake sunabin kofar dakin da ido,mom ce ta samu guri ta zauna tana tunani,tabbas tafara gano wani abu gameda sudes da faruk,idan ko wannan zargin da takeyi ya tabbata ,bakaramin artabo za asha a gidannanba.

Abba waini sudes za su wulakanta saboda sunsamo wata kucakar yarinya ,abba har marinafa yayi ,mari fa kikace jony ke ce kamar mayya nace ki hakura da sudes dinnan ,haba saikace shine autan maza ,wallahi abba ni babu namijin da nake kallo amatsayin namiji sai shi ,abba ku taimakamin wallahi zan iya mutuwa,kuma zan iya kashe koma wane akan sudes,kisa kisafa? Ah lallai bakida hankali,ki shirya in anjima zamuje aduba kwakwalwar ki,abba ni lafiyata kalau kawaii nidai nafada muku ,Idan ba a bani sudes ba ,saina kasheshi sannan na kashe budurwar nima na kashe kaina,tana gama fadar hakan ta mike tsigi__tsigi kamar zata karye tashige daki.



Abban jony bakaramin damu yayi da furucin da jony tai akan su dudes ba , duk da shi kansa be son suwaye suba,amma insha allah duk Inda suke saiya nemosu "dole sai ya samawa jony farinciki" mamin jony ce ta karaso gurin tana cewa, alhaji!!!!!!!!!!!! Yakamata ka samarwa jony abinda take so ,don bazai yuwu ina ji inagani narasa "yata akan Wani namiji da ko kafar ajin jony bai kaiba,haba Wannan wane irin bala'ine ace yarinya tanacewa wanda baya sonta,saikace shine autan maza.



Kwantar da hankalinki uwargida na kuma sarautar mata,kamar yadda kike azaune agidannan ke kadai,haka itama jony zata zauna a gidansa ita kadai babu kari,kuma waccan yarinyar datake magana akanta ita yakeso ba jony ba,sai nasa an yi maganinta,ita da kanta jony zata yanke mata hukuncin sata kuka datai ,


"Yadai fi amma ace akan shegiyar yarinyar suka ci mata mutunci, harda Wani cewa idan ta isa ta aureshi ayko zan nuna musu nidin yar halakce, zan iya kasha mutum kawai dan farincikin jony,

A,a bance kikashe kowaba ,kibari afara Masa barazana,idan yaki sai mu hulla yarinyar Inda ba a dawowa, hhhhhhh alhaji nawa ,kasan meyasa nake dada sonka ,a,a saikin fada,kawai sabida kanason farinciki na dana jony,kuma gashi shu,umancin mu yazo daya,ni muguwa,kai mugu馃槅




________________kai sudes ba magana nake makaba nace kabude kofar nan ko,bakada hankaline kabude ka fito mutafi asbiti,mom tafada,muryar AMATULLAH ya tsinkayo tana cewa,mom dan Allah ki saka baki wallahi ciwon zubar da jini yakeyi, nan hankalin mom yakara tashi tace, sudes dan Allah kabude shiru sukaji babu alamun zai bu'de,nan danan fa tsoro yacika zuciyar amatullah,

Shiko sudes tana cikin dakin yazubar da jini sosai ,har yafara ganin uku,uku a idonsa,

Aguje suka futa harda faruk aka kirawo me gadi sukazo tare,aka hadu aka bu'de kofar,da ker,ai ana budewa AMATULLAH ce tafara watsawa aguje cikin daki,ta fada kan sides ,tana rusa kuka ,gabakidaya ta hana kowa yatabashi tabi ta kankameshi sosai,tanacewa ya sudes, ya sudes bu'de idon ka kagafa nice ,dan Allah ka kalleni katashi mutafi asbiti,yaya dan Allah 馃槶馃槶馃槶 shiko gaba daya sudes yafita a hayyacinsa,

Faruk kuwa duk da takun sakar dake tsakaninsa da sudes saida ya tausaya Masa,gaba dayafa hankalin kowa na gidan ya tashi barima amatullah da duk tabi ta rude tana sumbatu馃グ

Ana tsaka da tashin hankali nan saiga jony tashigo mamynta nabiye abayanta taci dauri ture kaga tsiya" suna shigowa falo suka nufi Inda sukaga su mom atsaye sunyi carko carko,ko salllama babu tace,kina ina shegiyar yarinya nazo na jamiki kunne akan kifita a idon jony ko wallah inamiki albishir da saina ga bayanki, afusace faruk ya kasheta dacewa,ah lallai ba abanzaba ,ashe daga uwarne,daman uwar batada hankali ina yar zatai hankali,saiyanzu nagane cewa kece kike koyamata rashin tarbiyya,idan banda hauka,kina ganin abinda ke faruwa kizo ki damemu da wata "yarki mujima da abinda ya damemu,,dakata karkafadamin maganar banza anan badakai nakeba,Wanan yakin nida waccan figaggiyar yarinyarce da take makale ajikin sudes ,ga babbar mara tarbiyya kun aje agidanku,idan banda rashin kunya ,tabari adaurama auren dashi saita rungumeshi amma bayanzuba,wacece figaggiyar,lallai bikisan wazakikira da figaggiya ba ,ke biki kalli yanayin "yarkibane an kamar na hureta tafadi,cewa faruk,mom ce tace ya isa haka,dan Allah kubarni naji da abinda ya dameni,dan Allah hajiya kiyi hakuri,indai akan sudes ne kebari muga ko zai samu lafiya ko sai ayi abinda za ai,amma kinzo kina ta hayaniya akan mutumin da ayanzu babu abinda yake bukata sai taimakon gaggawa na asbiti,ki kwantar da hankalinki,idan Allah ya bawa sudes lafiya ya furta yana son jony babu abinda zai hana ayi auren,

No wallahi ko baya sonta saiya aureta, kuma da ita kadai zai zauna!!!!!馃槨

""""""""Me" lallaima matar nan ,wato ko bayason tama sai ya aureta,to sai ingani,yanxu ko mace"andai namata auren dole ballanta na namiji mejini ajika kamar sudes, uhm ni wallahi ma mamaki kike bani,nikam dai ina tunanin kekika haifi sudes shiyasa har kike wannan zakewar,to komi danake yayarsa bazan tilassa masa akan abinda baya soba, ballan tanake da muke,haduwar hanya,rabuwar bakin titi,kinga malama oya ki ja wannan tsigigiyar "yar taki ku fucemin daga gida 馃槨

'iye ashe ke kike daurema sudes gindi yake wulakan tamin "yar,to wallahi tun wuri kifita daga idona narufe, nafadamiki" kuma inbanda ma tanace sai shi wace tsiyarce zata kawomu gidan ku,daga ke har marakunyar "danki sainayi maganinku tanuna faruk.


Afusace amatullah tace wai nikam faruk me suke cewane ,nagafa alamar kamar fada ake,faruk ne ya mayar mata da fulatanci,ya sanar da ita abinda ke faruwa,cikin tsiwa amatullah ta fara magana cikin yaran fulatanci,tana nuna mamy jony da hannu,


"Au wai dama sabida ni kukazo nan,marin da "yarki ta yimin bai ishekuba, yaushe nacemuku inason sudes da har zaku takurawa rayuwata, menayi muku,kubarni da abinda ke damuna mana,amma kunki,harda zuwa har gida,kuciwa mom mutunci ,matar danake ganinta kamar MAHAIFIYATA ,mutanen dasuka tallafi rayuwata alokacin da nake tsaka da damuwa,sukukazo kuyiwa cin mutunci sabida wannan jakar tana son ya sudes,

Al bishirinku, tafada,cikin sauri faruk ya katseta dacewa AMATULLAH bafa sajin me kike cewa,karma suji mana,ina son kafassaramusu albishir dinnan da nakeson fadamusu yaya faruk,

Tom inaji fado ina fassara musu,tana fada yana fassarawa momyn jony da HAUSA,


Inason yimuku albishir da cewa,ni AMATULLAH,zan so sudes kuma zan kaunaceshi,sannan zan zauna dashi har karshen rayuwata,babu gudu babu ja dabaya,wannan alkawari na daukarwa kaina ,zan gani dani da "yarki wacece matar sudes馃槨

Luuuuuuu yaji duk duniyar ta zamar masa kamar gaurashin wuta,nan take yafara jin zuciyarsa namasa ciwo da kuna,cikin mintuna kalilan faruk ya nemi nutsuwarsa ya rasa,saiga hawaye zuuu suna bin kuncinsa,dagudu yabar gurin ya shige daki ya fada bathroom ya saki kuka me tsuma zuciyar masu karatu,kuka yake sosai yana cewa, amatullah innalillahi wainnailaihirraju un, AMATULLAH kin cuceni "kin cuci rayuwata,meyasa"why amatullah,meyasa zakiyi alkawarin auren sudes,to ni kumafa"nashiga uku , shikenanan nadan karshen rayuwata yazo , innalillahi wainnailaihirraju un, AMATULLAH karki gujeni dan Allah,hakaya dunga kuka yana sumbatu shikadai a bathroom 馃槶.


Suko su mom basu kula da hawayen da ya zubowa faruk ba kawaidai sunzata daya shiga daki Wani abun zaiyi.


AMATULLAH kuwa tana gama fadar albishir dinta bata jira amsar momyn jony ba ta koma gurin sudes ,tana share hawaye,tana goge jinin dake zuba.


Wallahi momy bazan yardaba ,kinajin abinda waccan mutsiyaciyar ya rinyar take cewa,wallahi bata isa ta aureshiba nice matar sudes ba itaba,haba jony ki nutsu kin manta wacece ni barni da ita,ba saita rayu zatacika alkawarin nataba,to wallahi sai dai ki cika alahira dan ubanki,tai tsaki taja hannun jony suka fuce sukabar mom a tsaye baki a sake,


Sharaf tasamu gefan kujera tazauna tana tunani,da dukkan alamu ,faruk son AMATULLAH yakeyi gashi AMATULLAH kuma tayi alkawarin auren sudes innalillahi wainnailaihirraju un,oh ni Khadija naga ta kaina,wazan bawa wazan hana,sudes kanina ne,faruk kuma "dana ,tab dijan ,menene zaifaru?waye mijin AMATULLAH?to kuma waccan matarfa da taci alwashin kashemu ? Kaina ya kulle wazaibani amsar nan?no babu,ganitai surutan banza take,gonda ta tashi afara ceto sudes din tukunna kafin afara yakin ,dayake shirin tunkarokai.


bayan momy jony tagama rashin mutunci taTa ja hannun jony suka bar gidan,


Mom ce tafuta ta kirawo megadi ya taimaka masu suka saka sudes amota babu kwari ko kadan ajikinshi jini yazuba sosai,


____Abangaren faruk kuwa bayan ya ci kukanshi ya koshi ,ya yashi ya fito ,saikuma yaga babu kowa a falon ,hakanne ya tabbatar Masa suntafi asbiti ,samun guri yayi ya zauna ,yashiga tunani kala_kala ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba ,Allah sarki faruk gaba kidaya yafita a hayyacin sa yakoma kamar wani soko, yana abu kamar wani mara lafiya ,Allah sarki sharrin soyayya kenan.


Zaune suke a cikin wani falo tan kameme suna Shan shisha,da kuma giya,kowanne daga cikinsu kagani yasha ya bugu,susu ukune a falon a zaune,babban cikinsune ya fara magana yace"oga gaskiyafa kana abinda kakeso akasarnan ,Idan kaga baka kasheba saidai bakai ra,ayiba,

Hhhhhh ogan yayi dariya yace samir me katuno ne kake yimin wannan kirarin haka"

"Uhmm kawai wadannan fulanin da muka konesu da ransu natuno, ah gaskiyafa oga kashe mutum da dadi,musamman ma ace ka ketta ashana ka konasu ,馃ぃ


Shege mugu Wato kai abinne yake baka farinciki ko,"eh wallahi kai kaga wannan tsohon ,yaddanaga yana konewa yana bawa wannan "yar karamar halittar tatsunuya wai ta dau fansa 馃槨 abin saiya bani dariya,ayni naso mun kamota ,

Ah to Idan mun kamota me zakai mata???


Kawai yanayin yarinyar nagani zatai dadi,gata da kyau kamar ita tai kanta,ammadai shikkenn,komai ya wuce ,tunda nariga nasan namun daji sunyi kalace da naman jikinsmta馃ぃ


________Abangaren su AMATULLAH kuwa suna isa asbiti likitan ya amshe su aka shiga da sudes dan bashi taimakon gaggawa,sukuma su mom suna bakin dakin azaune kowa ya zabga ta gumi,saiga doctor ya fito,dasauri mom ta karasa ta ce "doctor ya jikin sides dasauki saidai ya zubar da jini sosai muna bukatar jini leda biyu,sannan likitan ya shige , amatullah ce ta karaso gurin mom tace meyasamu yaya sudes din ,babu komai amatullah kawaii dai yazubar da jini ne anabukatar jini leda biyu domin akaramasa.

Leda biyu to yanzu kenan aina za a samu jinin amatullah ta fada tana zaro ido馃槼

"""Wallahi ni kaina bansaniba, amma ina faruk yake dama batare muka ta hoba,eh "mom yana gida ay tunda yashiga daki be futoba , oky bari na kirashi sai yazo a goda dibar nashi ko zaiyi daidai.

Waya ta dakko a jakarta ta shiga neman lambar faruk,ganitai idan tatsaya duba number za su bata lokaci gorama kawai tayi searching ,nan ko tafara search din sunan faruk saiga number ta fito ansa my son,Kira ta farayi amma shiru ba a dagaba,saida taki ra sau uku tukunna faruk ya daga,ashe daman wayar tana kusa dashi bai yi niyar dauka bane kwai,yana kara wayar a kunnensa ya ce assalamualaikum mom,daga bangaran mom tace"faruk kana ina??mom ina gida Mana, okay dan Allah Kayi sauri kazo nan asbitin AMINU kano inason za a daibi jininka , kawunka sudes bashi da jini ana bukatar jini leda biyu,Kayi sauki dan Allah, Innalillahi okay mom kujirani gani nan zuwa,yauwa my son saika karaso ta katse wayar,

AMATULLAH ce tace" mom ya faruk din zaizo? Eh" gashinan zuwa yan zunnan, alhamdullah tafurta a zuciyarta.


Shiko faruk yana kashe wayar yasaki murmushin mugunta, ya ce"alhamdullah haba da inata neman mafita ,saigashi Allah ya kawo min ita cikin sauki,wallahi babu inda zanje,yamutu na auri AMATULLAH shikenanan,badai ni ake jira nazo na bada jiniba"andade ba a samasa jininba ,zanta zamuku lokaci har ya tafi inda ba a dawowa ,haka kurum ya hanani rawar gaban hantsi馃槨barima ki gani mom bacci zanje nayi ,daman rabona danayi bacci me dadi tun kafin lokacin da muka fara takun saka dani da sudes,indai kunga bayi bacci saidai bacci barawo ya daukeni,yanzukon bari naje na sha baccina,kafin su mom su dawo mutafi kai sudes makabarta,menene aciki idan harzan samu amatullah,gonda ya mutu ,kukan na dan lokacine zanyi ,daga haka ya tashi ya shiga daki ya baje a kangado ya fara sharar bacci馃ケ



Shuru_shuru su mom suna jiran zuwan faruk be karasoba ,ga doctor ya fara fada ,yana cewa idan baza su bada jininba to zai iya mutuwa sabida babu jini ajikinsa,bayadda mom ta iya da har ta yanke shawarar kawai ta siyi jini a karawa sudes sai kuka AMATULLAH tace ita a je a gwada nata ko zaiyi ,babu musu aka je a ka gwada jinin yayi daidai da na sudes mom tayi mamakin wannan al amarin,haka amatullah ta saka kayan majinyata irin wanda aka sakawa dudes ,daki daya aka ajiyesu ,ga gadonta gana sudes,haka aka debi jinin amatullah har keda biyu ,aka sakawa sudes,ita kuma amatullah ka mata allurar bacci domin ta samu ta huta,mom kuma tana waje tana ta tunanin abinda ya hana faruk zuwa ,duk da batasan wane uzirine ya hanashi zuwa ba taji haushi sosai,ko ba bu komai ran dan uwansa ayyafi kome ya tsaya yi,.


A bangaren faruk baccin sa ya ke ta famanyi harda munshari ,yana bacci yana ta zabga murmushi shikadai.


Bayan minti 10 saiga sudes ya bu'de idanuwansa tarau suka sauka akan AMATULLAH dake gefansa a kwance tana bacci cikin kwanciyar hankali,mamaki ne ya kama shi, azuciyar sa ya fara tunanin me yakawo AMATULLAH nan ,kuma waye ya kawoshi asbiti,idon sane ya kai kan karin jinin da ake masa,hakanne ya tabbatar masa jinin amatullah ne aka karamasa,har leda biyu,?mom ce ta bu'de kofa ta shigo ,taga ya farka' saitaji Wani dadi a zuciyarta, samun guritai ta zauna kusa da sides ta ce,sannu ya jikin naka?da sauki anty,

Naga AMATULLAH a kwance meyasa meta,uhm sudes meyayi zafi haka,harka bubbuga kanka a bango ,jininka ya so ya kare,gaba daya baka hayyacinka muka kawoka asbitin nan yanzu badaban amatullah"ba" nasani datu ni yanzu angama maka wankan gawa za a tafi kaika makabarta,anan mom ta kwashe labarin abin da ya faru ta fadamasa,tundaga shigarsa daki yaki bude kofa har zuwansu jony da mamarta,da kuma yadda akai sukazo asbiti,da alkairin da amatullah ta dauka na auransa,har zuwa lokacn da takira faruk bezoba da kuma yadda akai amatullah ta bashi jininta leda biyu.

Sudes tsabar farinciki besan sanda ya mike tsaye yana murmushi ,yana cewa ,anty tashi mutafi gida na warke,

"Kawarke kuma ta zaro ido 馃槼 eh anty wallahi na warke tunda nasamu abinda nakeso,bangane kasamu abinda kakeso ba fadamin mene kakeso din??? Kash anty abar maganar nan bayanzu ba tukunna dai zan fadamiki ba yauba,ki jira lokaci,ni dai ki taso mutafi,

Wai ni sai cewa kake mutafi ita kuma amatullah fa aka zamu dauketa ko,ko goyata zakai,abu me sauki goyonma ai sai namata,barima ki gani,ya saka hannu ya dakko amatullah kamar "yartsana ya sabata a kafada,

Eyyy yau naga abinda yafi karfinta馃wai nikam ba kai mukakawo rai ahannun Allah kana bukatar jiniba ,wato Ka warke sai iskanci ya karu,da allah sauke min yarinya,kato dakai kasaba min "ya akafada sai kace kasamu matarka,a hankula ya furta to da ba matar tawa bace,mekace "no ba magana naiba馃グuhm ni zaka mayar Mara wayo to tunkan a haifeka nashaki iskar duniya,Haba yaro sai iskancin tsiya ,d'azu _d'azunnan nagama kuka hankalina ya tashi saboda bakada lafiya,amma wai ni yanzu zakayiwa iskanci kanunamin kaimafa Ka girma,yayi kyau ay sai Ka taho mu tafi tunda Ka dakkota,ku jirani a mota zanje gurin doctor, okay allah ya ja da ranki my antyna馃檹馃尮


Faruk kuwa yana daki a zaune ,har yayi bacci ya farka yana ta jiran zuwan gawar sudes amma shiru, yankee shawara yayi kawai ya Kira mom ,yaji meyahansu da wowa saikuma ya fasa, sabida karta tambayeshi meyasa ya ki zuwa,saida ya gama tsara karyar da zai fadamata sanan ya danna Kira,bugu daya ta daga, asslamualaikum mom saiya saki kuka,yana cewa,wayyo Allah mom ina sudes nasani ya rasu Allah yabamu hakurin rashinsa,馃槶kiyi hakuri mom karkiyi kuka,kin kirawo su baffan katsina kuwa,kinsanar musu da mutuwar sudes, kai ubanka nace ubanka faruk mekake fada hakane ,wane shirme kake faman yi babu kangado,waye kuma ya mutu,dum gaban faruk ya fadi,a sanyaye yace mom sudes mana ,ubankane ya kasheshi to ni dan uwana yana nan araye,be mutuba, kuma bari na dawo gidan sai kafadamin ubanme ya hanaka zuwa asbitin,sanan ta katse wayar.

Faruk ne ya fashe da kukan gaske,tunda da nakarya ya farawa mom dan kartace be damuba,magana ya farayi kamar ta babbe,meyasa karayu ,wanene wanda ya bada jininsa nasan dai mom jininta ba zaiyiwa sudes ba to amma waye ya bawa sudes jini? wallahi ko ma wanene ya bawa sudes jini,sai na kasheshi amemakon ceton ran sudes da yayi,


Bayan mom ta kashe wayar futo watai tashiga mota suka dauki hanyar komawa gida.


__________________________________________________________________________________________________________________________Suna isa gida mom ta fito ta shiga cikin gidan ,tana faman kwallawa faruk Kira _tana_ cewa, faruk kai faruk!!!!! Dasauri ya fito daga daki ya karaso falon ya ce sananu da zuwa mom kindawo lafiya,ban saniba da bamu dawo lafiya ba Ka ganni haka,am sorry mom meyayi zafi haka ,naci uwar baturema wanda ya kirkiro turanci soro ba sorry ba,afuwan mom dan Allah ki yi hakuri,ki zauna,bazan zauna dinba nace bazan zauna ba ,saika zo Ka zaunar dani,to dabakaje ka ba da jini ba allah ya kawo wani yabashi koma ya samu lafiya tayi tsaki tashige daki,daidai lokacin da sudes ya shigo falon dauke da amatullah a kafadarsa ,ya yi sallama ya shige warsa dakin AMATULLAH 馃尮 shiko faruk ko sallamar ma be amsawa sudes ba sai bin su da yayi da kallo,mamakine ya cikamasa zuciya,to meyasamu amatullah,shidai yasan sudes aka tafi dashi ranga ranga Baya da lafiya,amma saiga shi kuma yanzu lafiyarsa lau,ita kuma amatullah da kafarta tatafi ,saigata andakkota,kuma ma tsabar iskanci arasa waye zai dakkomin matata sai wanan gardin sudes,to wallahi ba zata sabuba, yafada a fili.


Sudes kuwa dakin AMATULLAH kan gado ya dorata ,dake lokacin sanyine sai yaja bargo ya lullubeta,har ya juya zai tafi saikuma ya dawo ya tsaya ya zubamata ido yana kallonta cikin farinciki, ahankula ya bude dan karamin bakinsa ya furta, thank you my future wife.ilove you with all my heart beauty na.




Tashin hankali wanda ba a sa mishi rana ,faruk wazaka kashe amatullah?

Suwaye kuma baffan katsina?





Shin faruk idan yaji amatullah ce ta bawa sudes jini ,zaikasheta ko a,a?



Nace shin ya makomar daukar fansar amatullah?



Jony zata auri sudes ko a,a,?


Me mugu da muguwa iyayan jony zasu aikatawa Amatullah akan "yar su?



Wai shin amatullah tarasa gaba kidaya a halinta ko a,a,?


Shin tsakanin faruk da sudes wane mijin amatullah?


Wane dabi za a gwabza tsakanin faruk da sudes?


Kubiyoni yanzu akafara book din, Alhamdullah anan nakawo karshen book din Amatullah book 1 muhadu a book 2 idan ubangiji ya bani aron rai da lokaci 馃檹

Ina rokon Allah kamar yadda ya bani ikon farashi har na kammala book 1 lafiya Allah kabani aron ran da zan karasa book 2 lpy idan na farashi,


Kada kumanta nacemuku Littafin amatullah Short story ne,


Godiya ta musamman ga dubun dubanar masoyan Littafin AMATULLAH, 馃尮 Allah ya barmu tare馃尮



SAFHAT CE MARUBUCIYAR馃憞

BA MAHAIFIYATA BACE. PAID 500
BURINA MU,AZZAM. Free book
RAYUWAR KASKANCI.PAId 500
UMMU AMANI.PAID 500
BABA NANE SILAH.PAID 500
AMATULLAH 馃尮. Paid 500

09166764540
Story & written by hafsat Umar dangoro"yar mutan bakin rafee馃檹馃尮




An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment