You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
tace amma Nusaiba ta bata wayonta ka samu miji haka irin mijin Novel zukeke ga kudi amma ta dinga irin wannan rayuwar gaskiya na tausaya Masa shike nan zauna mu koma siyar da alalar mu inda Muka fi wayo amma Nusaiba ta bani mamaki samun miji haka,Dauda yace to anji kin damu mutane da miji kyakyawa ne ni bani da kyan ne?kina ta wani yabon mijin wata ga naki amma baza ki yabe shi ba,Siyama tace to ai Kaine Kawu lebe Kamar sakatar kofa,zanci Ubanki Dan ubanki lebena ne kamar sakatar kofa? Siyama ta sake cewa ba lebeba hakora kamar goslow a hanyar Lagos wasu sun taho ta nan wasu ta can,Dauda yace Zaki ci ubanki ni ba ubanki bane Zaki dinga maida Ni kakanki ki kiyayeni wlh,Aunty tayi dariya tace gwara da yarka ce ta fada da nice cewa zaka Yi sai kaci mutunci na
Mama ce a zaune tana waya da Nusaiba tace me nake ji Haka gida daki daya chab dama karyar tasa ta Kai haka,Bari dai sai nazo ta furta lokacin Shehu Yana gida kusa da Mama a zaune,yace Wai ke me kike nufi ne? Nusaiba kin hanata sakewa naji labari jiya Ameer ya fada min komai yanzu tsakani da Allah ki kalli gidan nan da a kuntace muke amma yazo ya Kara Mana dakuna ya Bude Miki shago bafa ni ba ke ya budewa shago ya bani jari Kuma na koma kasuwa sosai ya auri yarki yanzu tsakani da Allah dan karya zai iya yin wannan taimakon,a tunanina ke me yiwa Nusaiba fada ce ashe ke kike zugata, Babu abinda zaka fadamin Shehu dakata kana ciyar damu?, Tunda na taso a gidanka wahala nake Sha Ni da yarana,Sanda Ina da hali ba kece kika cinye kudin ba suka Kare Kika tsaneni komai nayi Miki ban birge ba ya Zan Miki face na zura Miki Ido ke da yaranki tunda kince ba abinda nake tsinana muku,Hakkin Yara a kanka yake kwarai kuwa na sani amma idan na baki kudin cefane kina bari ki basu abincin ba kadan kike dafa musu ba ki siyar da sauran komai na baki siyarwa kike yi,Mama tace to ka kyale min yata ba ruwanka yace Ina da hakki na fada Mata gaskiya,yanzu bazan magana ba tunda bai kawo kararta ba amma duk Sanda ya kawo Kara Nusaiba zata Gane kurenta auren me kudi hauka ne da arziki da talauci duk na Allah ne Kuma wlh kuji tsoron Allah ya mike tare da sa takalminsa ya fice.
Mama Kuwa Ameer ta samu ta balbale shi da fada akan me zai fadawa Shehu.
Charity Alalarta taci gaba da yi amma yanzu tallan ma bata fita ake zuwa a siye a gida,Nusaiba tunda Suka koma gidan haya bata girki ficewarta takeyi su hadu da Sufyan saurayinta a restaurant in taci ta koshi ta dawo gida,Aslam da Kansa yake dafa ma Kansa abinci bai iya ba amma haka zaiyi jagwalgwalonsa ya ci,yau da Yamma Siyama sai gata a gidan sanye da hijab har kasa da Leda a hannunta tayi sallama ta shigo Murmushi ya saki shi ta iske a palo yace manyan kasa ne yau a gidan, Charity dariya tayi ta rusuna tare da gaida shi ya amsa,Ina matar fa? Ta fita ta tafi gidansu yace,Siyama tace okay dama abinci na kawo maka ban sani ba ko tana girkin,yace wow na gode Kamar kin San yunwa nake ji,ledar ta Bude ta dakko abinci a robobin take away har kala biyu tace kaga wannan Fried rice ce dazu Muka Yi da Aunty wannan Kuma tuwon shinkafa ne miyar Egusi,Kawuna nane ya samu kudi shine yau Muka ce bari muji Dadi kaci kaji da Dadi harda nama,mikewa tayi ta dakko spoon a kitchen tace gashi ya karba Yana kallonta cike da mamakinta tafi matarsa sau dubu,Fara cin abincin yayi gaskiya yayi Dadi ya furta Yana ci Siyama tana Kare Masa kallo,kallon fuskarsa takeyi Yana ci har ya cinye daya ya Sha ruwa pure water yace dayan sai dare tace to,Charity ta tura dayan kasan kujera tace gashi a nan na boye maka Kar marar Imani tazo ta dauke,dariya yayi yace na gode ta hada ledarta da roba tace tafiya zanyi tunda bata nan, yace da wuri haka kiyi zamanki ki tayani hira dama na gaji da kallon film,tace to ta zauna tare da tambayarsa har yanzu baka samu aiki ba ka fara?
Ae yace Mata amma Ni da abokina Sabeer Muna ta fafutukar nema ko za a dace, Charity tace to Allah ya kawo tana Jin kunya tana satar kallon Aslam ba karya ya hadu gashi Kamar balarabe fari tas ita Kuwa ja ja ce, gidan ta kalla kaca kaca tace gidan naku yayi dirty yace a haka ma Ni nake sharewa,mikewa tayi ta hau shara ta gama tayi mopping ko Ina ta gyara kitchen,toilet din ma ita ta wanke musu ita kal kal ta dawo Palo ta zauna suna kallon film game yakeyi a wayarsa ps tace game kake Yi? Yace kin iya ne? Tace ae na iya wani abokina ne Hunaif yake bani wayarsa Ina Yi,yace ko dai saurayinki ne? Dariya tayi ya kalli kyawawan hakoranta reras gata kyakyawa sosai tace ya taba cewa Yana so na danginsa suka hanashi sabo da Ina saka riga da wando Wai Yar Lesbian ce ni,Dariya Aslam yayi Yana latsa waya yace ai maganinki kenan da kike saka riga da wando ke ba a kudu ba kin San wani Yana kallonki shedar da zai Miki ta banza shi yasa ake so a dinga kiyaye shiga,da shiga ake Fara gane mutumin kwarai ga sunanki Charity kowa Charity,Siyama tace ai Riga da wandon ne yasa a unguwa aka saka min suna Charity idan na nuna bana son sunan anfi kirana da shi that's why na karbi sunan Hannu bibiyu,Riga da wandon ma kana ganinsu manya manya nake sawa bana saka damammu Kuma yanzu na rage sakawa tunda nake Yana damaging Image dina,yace yawwa ko ke fa ai yafi amma dole ace Yar lesbian ce tunda barma barma kike sawa Kalar na maza,dariya ta sake Yi akwaita da fara'a,tace Allah ya tsine musu wlh masu lesbian ga maza can suna nema Mata suna musu mugunta,dariya Aslam yayi ba shiri yace Charity kenan ke kam ba ruwanki da boye boye kamar Yar kudu haka kike Charity tace idona ne ya Fara tsikewa da duniya mu fa Yan talla ne iya shege ba Wanda bama ji,sai da na Fara talla na gano illar barin ya mace tayi talla
Kaga idan mace tana talla ko wanne gara Wanda ko a Hanya Bai Isa ya Miki magana ba idan kina talla kowa zai kulaki ko wanne gaja ne Kuwa,sannan akwai Wanda a hanya bai Isa ya iya ko magana ba Amma sabo da talla zai fada maka Maganar da yaga dama,sannan me talla kowa Yana da lasisin da zai Mata magana ko a dinga tsokanarta ko wani ma yaci Mata mutunci,mace me talla Namiji zai iya janta da zancen banza ya ja mayafinta ya daketa wani ya mareta wasu Kuma duk Magana ta banza yarinya tun tana karama Matukar tana talla za a dinga Yi a gabanta,tunda waje ne na maza idan Suka taru akwai kalaman banza da bai dace taji ba amma za a dinga Yi a gabanta wasu ma su dinga janta da Harkar banza irin wannan ke sawa Yan talla suke lalacewa yau da gobe zata Saba har ta daina kunya,sannan ga gogayya da maza mutane manya daban daban zai sa idonta ya bushe ta dawo Bata da kunya Kuma bata tsoron kowa kadan daga illar talla ga ya mace,Aslam yace hakane Nima sai yanzu naga hakan, Uhm ta furta tana kallon Wayar hannunsa me tsada
Sabeer ne yayi sallama tare da shigowa shima,Sai yau Siyama taga Sabeer,gaida shi tayi Yana binta da kallo ya mikawa Aslam Hannu suka gaisa ya zauna yace ko kece Siyaman? Charity tace ae yace Sannu mun gode fa,Sabeer ya dameta da kallo,Aslam Yana kallonsa,Siyama mikewa tayi tace zata tafi,sai yaushe? Aslam ya tambaya tace sai an ganni Kawai yace muje na rakaki Suka fito tare suna tafiya a hankali suna hira tana ta bashi dariya.
Nusaiba aka sauke a taxi ta tsaya tace Charity sai da Kika sake biyo mu Nan dan masifa yanzu ba kudin da za a baki to,Tsaki Siyama ta ja tare da furta banda lokacinki Nusaiba,Nusaiba ce tace zo wahalalliya Ina son magana dake,Charity ta ja gefe Nusaiba tace tunda taku tazo Daya da Aslam dan Allah kisa ya sakeni,ki fada Masa Ni takarda ta nake so ya sawwake min na gaji bazan iya rayuwa da shi ba,Siyama ta kalleta tace ki kalli Namiji irin Aslam hadadden mutum Kamar shi yayi kansa kice Wai kin gaji da shi,ae dan Allah ni na gaji bana son auren ya sakeni,kinfi so ki Zama bazawara ae gwara haka ke karuwai ma suna nan su da karuwanci suke Yi suna zaman su a duniya Lafiya bare ni Dan an sakeni na Zama bazawara,wlh idan Bai sakeni ba Kara Zan kaishi wajen Yan Hisba,Siyama juyawa tayi tare da komawa wajen Aslam ta fada Masa abinda Nusaiba ke so saki,yaji Matukar ciwo ya danne,Yana komawa gida tace wallahi yau ba zaman lafiya sai ka sakeni,Aslam yaki kulata rigarsa ta rike ya samu ya kwashe ta da Mari ya sake zabga Mata Mari Wanda ba shiri ta sake shi tana kuka wallahi sai ka sakeni,yace baki ji kunya ba mahaukaciya aure wata hudu na sakeki Baki da hankali,kuka Nusaiba takeyi sosai yaki sakinta haka Suka kwashe satikai kullum da masifar da zata fito da ita a saketa sabo da bai da kudin da zata karba yanzu Kuma sai takalo rashin mutunci iri iri shi Kuma yaki sakinta,harda daina kwana a dakinsa ta dawo palo a nan take kwana kullum.
Yau Mama ce tazo gidan tana zuwa ta saki ihu a palon tace a Nan yata take Zama daki nawa ne? Nusaiba dake zaune tace daya,Daya tal yanzu idan da kwana zanyi bani da wajen bacci kenan tab amma Aslam ba karamin azzalumi bane ka ajiye bawa me rai a nan, Nusaiba tace zauna Mama bari na Miki girki dama bana dafa Masa abinci,Mama tace kinyi dai dai tana zaune Nusaiba ta dafa Mata shinkafa da Miya harda kazar da ya siyo jiya Mama taci ta tauna Kashi ta sha ruwa me sanyi ta sake zuga yarta tace Kai Kai kamarki a wannan gidan daki Daya sai Palo kujerun ma ba na kasar waje bane ba Yan Dubai ba Yan nan Kano ne,Nusaiba tace kalleni Mama yanda na girma nayi kiba nayi wani fresh kowa ya ganni yaga kalar hutu amma matsiyacin ya makale yaki sakina,gida ko filin tsakar gida babu kalli tv din ma karama sai kace ta Office din principal din makarantar sikandire cewar Mama,wani takaicin Aslam ya sake rufe Nusaiba,Mama Kuwa sai sake zugata takeyi,tashi tayi ta leka kitchen ai wani ihu ta saki tace hodijam inji Dan fillo wannan kina samun balance kuwa? Sai dai manage Mama shi yasa bana shiga
Suna haka Aslam ya shigo sanye cikin wata shadda Yar ubansu grey color cikin kayansa na baya masu tsada ya saka ya shigo da takardun makarantarsa,Mama ta Bata rai tare da kallonsa shekeke ta tabe baki tace kamar gaske akwai kudin Kai karya bata Yi ba,Aslam ko kulata baiyi ba ya wuce bedroom dinsa,Mama tsabar rashin son zaman lafiya tace sai na dawo kwana zanzo na kwana biyu haka,Nusaiba tace Allah ya nuna mana Mama sannan ta fita ta tafi gida,Aslam ya fita bai dade ba ya dawo da Leda a hannu yayo cefane harda Naman rago da yawa,tun kafin yayi magana Nusaiba tace wlh sai dai ka dafa da kanka Kuma abinci daga ni sai uwata na dafawa mun cinye,bata ko rage Masa ba gashi Yana Jin yunwa Charity bata da waya bare ya Kira ta, tashi yayi ya fita bai ko saurari Nusaiba ba ya shiga Napep zuwa gidan su Charity
Yana Fitowa daga Napep Suka hadu da Shehu Baban Nusaiba,Shehu da fara'a da murna yace surukina gobe nake so nazo gidan naka jaje wlh ashe haka Abu ya faru marar Dadi,Aslam ya duka zai gaida shi yace tashi tashi Aslam ubangiji ya maida alkhairi,yace ameen,Shehu yace ya Nusaiban iceko lafiya kuke? Aslam baiyi kasa a gwiwa ba ya zayyanewa Shehu komai,Shehu Baki ya rike yace wallahi ban San me ake ciki ba abin wato har ya Kai haka,duk uba bazai so a saki yarsa ba amma tunda Nusaiba take maka haka na baka dama ko nine iyaka abinda Zan iya kenan na saketa,Dan Allah kayi hakuri Kai mutumin kirki ne,har gobe Ina ganin mutuncinka Kuma bazan fasa zumunci da Kai ba ko da ace baka tare da yata,Aslam yaji dadi da farin ciki,Shehu yace ka kyale Maman Yarinyar tunaninsu daya taho muje gidan Yar uwata ka huta a can,Shehu yaja Aslam zuwa gidan Yar uwarsa Alawiyya ba nisa da gidansa ita me rufin asiri take aure komai nasu me kyau ne,kana ganin Aslam zaka Yi tunanin da kudinsa tunda Yana da sutura,palon Alawiyya Suka shiga babbar dattijuwa yace mijin Nusaiba ne,Alawiyya tace Shehu ai na gane shi,Aslam ya gaishe da ita ta fita ta kawo musu lafiyayyen girki Aslam dama yunwa kamar zai mutu baiyi Kara ba ya zage yaci ya koshi shi da Shehu Kamar ba surukai ba suna yin Sallar la'asar Aslam yace zai tafi Shehu ya rakoshi har kofar gida Suka Yi sallama shi ya koma cikin gidan wajen Yar uwarsa,Aslam Kuma ya karasa kofar gidan su Charity,Yana tura yaro ciki sai gata ta fito zata siyo manja,taga Aslam ba zato,Murmushi ta saki kayatacce tace Ina yini ya amsa da fara'a tace Ina kaje haka? Yace cefane nayi tace baza ta dafa ba nama ne zai lalace shi yasa nace Bari na kiraki ko ki dafa min ko kizo ki dauka ki kawo gidanku kuci Kar ya lalace,Charity tace nama guda wa yaki dadi har kasa yawuna ya tsinke,ya saki Murmushi ba shiri,ciki ta koma tace Aunty ga kudin ki aiki yaro Aslam yazo nema na,Aunty tace Kuma dan Iskanci sai ki dawo da kudin,Bata tsaya ji ba tace ki fadawa Kawu matsala ce a gidan zanje wajen Nusaiba,Aunty tace to a kula dai tace to,ta fito tare da cewa muje Suka fito tare Suka Mike suna tafiya suna Hira har yaji sanyi a ransa
Titin kwalta zasu tsallaka Yana ta tunani ya tafi bai kula da mota ta kusa zuwa inda yake ba Siyama ce ta taho da gudu ta fisgi hannunsa tace mota da sauri suka tsallaka suna tsallakawa motar ta wuce da mugun gudu,ta kalleshi tace tunanin me kake Yi haka ta furta tana kokarin zare hannunta a nasa Wanda ya damke hannun nata cikin nasa Yana Jin wani shock da bai taba jinsa a jikin wata ya mace ba,Napep Suka shiga zuwa gidansa Siyama ce ta biya kudin ta hanashi ya biya kudin,suna zuwa Nusaiba chatting take abinta ga ledar kayan nan a gefe,Siyama tana zuwa tace ke ballagazar matar aure shashashar matar Aslam, kallon Charity Nusaiba tayi Kawai ta ja tsaki,Siyama ta zari ledar Aslam ya zauna tace Ogana me za a dafa Murmushi ya saki yace kiyi farfesu Kawai sai Dan abincin dare,an gama ta furta tana kallon Nusaiba tayi fatali da kafar Nusaiba dake mike a hanya tace matsa can Yar banza Yar wofi,wawiyar banza,Dariya Aslam ya shiga yi Nusaiba ta galla Masa harara tace dan uwarki ba Charity kike ba ko Ngozi kike nafi karfinki wahalalliya me bauta a banza, Siyama ta yiwa Nusaiba dakuwa ta shiga kitchen tare da kunna gas ta Fara aikin girkin sai wurin magriba ta gama farfesun ta ebi dan kadan a roba me murfi ta rufe,Ta fuskanci yana son tuwon danyar shinkafa shi tayi Masa da miyar danyar kubewa ta Gama komai yayi Alwala zai fita masallaci tace na gama, yace Banga kinci ba tace gashi na eba ta nuna Masa robar, tare Suka fita ta shiga napep shi Kuma ya wuce masallaci.
Nusaiba tunda tana zuwa restaurant bata damu da abincin Aslam ba Sufyan Yana mugun kashe Mata kudi yanzu burinta Aslam ya sake ta,washe gari Mama Shehu ta tambaya tace zata je kauyensu ya barta tana tafiya sai gidan Nusaiba da Yar Jakarta wai tazo zata kwana biyu a gidan yarta,Nusaiba ta dauki Jakarta ta Kai bedroom ta hau girke girke Aslam Yana zuwa yaji kamshin girki na tashi yasan da dalili shigarsa bedroom kenan ya iske Mama a ciki yaga Kuma jakar tata tabbas kwana zata yi, mamakin suke mugun bashi,Mama ganin ya shiga ta fito,a gabansa a palo Suka zubo abincinsu Suka ci Suka koshi ko tayi basu Masa ba Yana Jin yunwa sai fita yayi yaci a resturant bai dawo ba sai 10pm lokacin Mama da Nusaiba sunyi Shirin bacci sun kwanta a saman gadon me gidan sun shige bargo tare,Aslam ya dan leka ya girgiza Kai yace idan baki da kunya Mama kin hadu da Dan zamani,bedroom din ya Shiga Mama ta bude baki,toilet ya Shiga suna ji Yana wanka Mama tace yau na shiga Uku da fitsararre,sai da yayi wanka ya fito daure da guntun towel,Mama Hannu ta dora a Kai tare rufe Ido tana yau na shiga Uku yau Naga jaraba,cikin bargon ta Danna kanta,turaruka ya fesa ya zura Jallabiya arsh,Kawai Saman bed din ya nufa yace Mama Dan matsa gefe kadan gadon zai iya daukar mu mu uku ba damuwa,Mama taga da gaske hawa zaiyi ya kwanta ta dirga kasa harda faduwa tace amma Kai ba dan arziki bane ban taba ganin suruki marar tarbiyya ba sai kai ta fice Palo tana cewa Nusaiba Miko min jakata a Daren nan Zan koma gida,Nusaiba ta mike tana hararar Aslam ta dauki jakar Mama da tarkacenta ta fito,Aslam ya kwanta a saman bed dinsa tare da Jan tsaki yace iskancin banza tunaninku ku kadai ne Yan iska uwar banza ya lulluba da bargonsa,Ita Kuwa Nusaiba a daren ta fita ta samawa Mama Napep ta koma gida,Shehu sai ganinta yayi ta dawo,yace ya na ganki ke da Kika ce Zaki kwana a kauye,Mama tace Wlh mutan gidan da naje domin su sunyi tafiya basa gida shi yasa na dawo,Shehu yace ke Kika sani kuma.
Washe gari da wuri Nusaiba ta Kai karara Aslam Office din Yan Hisba tace so take a fadawa mijinta ya saketa bashi da lafiya baya iya biya Mata bukatar Aure sannan ma ita ta daina sonsa ya Fadi abinda ya kashe zata biya shi ya saketa,Aslam yana gida ya fito zai fita Kawai yayi arba da jamian hisba mutum biyu suka Mika Masa takarda ana nemansa a Office din Hisba yasan Nusaiba ce kawai Sabo da haka Kawai sai ya nufi can a Napep.
Wacece Raudat
Raudat Ibrahim Waku 'yace ga Ibrahim Waku hamshakin me kudi ne dan asalin jahar Gombe Wanda ke zaune a Oyo state,tunda kasuwanci ya kaishi can ya shahara ya Zama hamshakin me kudi na gaske ya tattara da yaransa su Raudat gaba daya ya koma Oyo da Zama,matarsa daya tal Hajiya Rahmatu itama Yar Gombe ce, yaransu biyar Raudat ce babba sai kannenta biyu maza biyu mata,Raudat tana gama secondary ta samu Saurayinta Hussain dan Kaduna state,Hussain talakawa ne a zahiri ba son Raudat yake ba irin masu auren Mata ne dan kudinsu dan ace Kawai ya auri Yar me kudi,Baban Raudat tunda yaga Hussain da Kuma cewar baya sana'a ko kadan yace ta hakura amma taki ji Sam dole aka Yi Mata auren wuri
Bayan anyi auren Raudat da Hussain Baban Raudat shine ya Kama musu gida haya a Kaduna sannan gara ma kayan abinci mota guda aka ajiye da komai sannan baya Bari yarsa Raudat da talauci,Raudat komai ita ke Yi a gidan ta koma itace mijin ba karya akwaita da hankali ga hakuri duk wani kyan haki Raudat tana da shi dai dai gwargwado,Hussain Kawai sai dai ya kwanta an bashi jari ya cinye an sake bashi har Karo na uku amma sai ya kashe,tunda Raudat ta aure shi bai taba kwanciyar aure da ita ba Basu taba sex ba sabo da bashi da lafiya amma yaki yarda fada bashi da lafiya,abinka da yarinya itama sai ta kasa fadawa kowa suna zaune haka har kusan shekara Hussain ga mugun son Mata bai da aiki sai kula Mata duk kudinsa Yan Mata ke cinyewa shi Kuma dayar ma da ya aura ya kasa biya Mata bukata amma Yana hangen na waje,a Haka ko Raudat bata bashi kudi ba sai wulakanci da cin mutunci iri iri Indai tana son zaman lafiya to ta bashi kudi,abinda yake batawa Raudat rai Shan giyarsa sai ya Sha giya yazo ya Mata dukan taiya,duk ta rame sam bata San mene dadin miji ba,ana haka ya fara Mata sharri sai ya shirya zance na karya ya fadawa dan ginsa da abokansa,akwai Sanda ma yace bata bashi abinci Kuma har zaginsa takeyi,Watarana ma ya dinga fadawa abokansa ai maza take bi da Aurenta har kunnen Danginsa zance.
Su Kuma dangi ba bincike ba komai suka saka Raudat a gaba Babar Hussain da kanta ta sa Hussain ya saki Raudat dama bai damu da ita ba itace take sonsa kawai a hakan ma da ya saketa sai da ta Sha kuka auren shekararsa Daya da Dan watanni ta koma gidansu,tayi jinyar zuciyarta sosai kafin ta hakura da son Hussain shi kuwa Hussain baya ta tata Sam,Babanta ne ya maida ta school tayi degree tana gamawa ya samo Mata aiki Babba da NGO su Kuma duk inda aka turaka aiki dole sai ka je,Kano Suka kawota supervisor ce sune suka rabawa irinsu sababbin motoci masu tsada,dama Kuma a can Oyo tana da tata motar da Babanta ya siya Mata,shi yasa tazo kano ta Kama gidan haya har Suka hadu da Affan suke fada Kuma kusan a tare Suka zo Kama gidan ta Sha Matukar wahala a hannun Hussain kafin Allah ya yanke mata.
Affan
Affan Kuwa asalin Fulanin Zamfara state ne, sunansa Aliyu A. Aliyu,mahaifinsu su biyu Maza ya Haifa Yusuf shine Babba an haife shi da shekaru hudu aka samu cikin Affan,da cikin Affan Allah yayiwa babansu Aliyu rasuwa,Babar su tana haihuwa aka sakawa Affan sunan Mahaifinsa wato Aliyu shine aka boye sunan ake kiransa da Affan, su biyu Suka taso a hannun mamansu a Zamfara duk da cewar babansu bai mutu ya bar wata kadara ba face wata gona layi biyu,bayan Yusuf da Affan sun gama secondary School babu kudin ci gaba da karatu,sai Mamansu ta siyar da gonakin nasu ta hada kudin kaf ta Kira Yusuf da Affan tace kunga kudin nan nasan bazai isheku kuyi karatu ba ku biyu Kuma ina so a cikinku wani yaje yayi degree a rayuwa ya kuke gani Kai Yusuf gadon ku ne idan Kuma kowa bazai iya barwa kowa ba to sai dai mu Kama sana'a da kudin,Yusuf ya kalli Affan yace gaskiya ni bazan iya barwa Affan kudina ba,Affan Kuwa Nan take yace Yaya Yusuf ni na hakura da karatun dama kaga nine karami na bar maka kudin gado na halak malak kaje kayi karatu idan ka samu aiki daga baya ka biya min ni nayi karatun daga baya ai ba'a girma da karatu,Yusuf yayi farin ciki sosai karshe aka Nemo admission lokacin baya wahala a ABU Zaria Yusuf ya shiga ya gama degree dinsa gashi Allah ya hadashi da Abokinsa Dan gidan me kudi ya ja shi cikin Harkar kasuwancinsu na siyar da gwala gwalai har aka zo ma ana tura Yusuf kasar waje yana siyo kayan, a hankali a hankali Yusuf ya Zama me kudin gaske ya kera katafaren gida a Kaduna gida na gani na fada,ko aikin gomnati ma bai nema ba,ya manta da halaccin da Affan ya Masa ya kasa tunawa ya sashi a university,karshe da yazo zamfara da galleliyar motarsa Wai yazo