Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baje a ƙasa fululu,ta shiga ɗiban Alkama tana watsa masu ,aiko kafin ai haka sun fewayeta suna tsinta da en koke koken su mai kamar waƙa

Lumshe Ido tayi tana shaƙar Ni'imtacciyar iskar dake bugawa ,kukansu na saka mata nishaɗin da sam bata samunsa a gidansu

Sadiƙu dake can gefe zaune ƙarƙashin rumfar da aka tanada don hutuwa ,sanye yike cikin gajeren wando da singlet na kakin land soldier, chat yake a kan laptop ɗinsa saidai lokaci zuwa lokaci yina ɗagowa yina kallon yarinyar ,sosai yarinyar ta tafi da Hankalinsa musamman yanda ya gane tanada tausayi da son dabbobi ,hakan yasa in tayi wani abun yikan ɗan tsura mata ido wani abun kuma sai ya mere baki ya cigaba da shafa system ɗinsa irin bai masa ba ɗin nan,amma yinajin bagaga ɗin tantabarun zai kuma ɗagowa

Daga ƙarshe dai ɗan tagumi ya rafka ya dogare hannunsa akan table ɗin gabansa ,ya ɗan karkato kaɗan yina ƙare mata kallo ,zuwa yanzu yafara gajiya da damunta ,don sosai ta fara takura masa ,amma kuma halshensa yayi mugun masa nauyi hakan yasa ya kasa magana tsabagen madarar miskilamci .
Ɗan shaking jikinta tayi ,wanda yasa tattabarun tashi firrrrr ,aiko wani ɗan murmushine ya ƙwace mata wanda yasa dimple ɗin gefen kuncinta loɓawa ,a take kuma wasu hawaye marasa dalili suka silalo a kuncinta.

Ɗan tsai da ransa yayi ,tunanin sa me yasata kuka kuma lokaci ɗaya tana dariya ?

Itakam sam batasan wajen da halittan ɗan Adam ba ,cigaba da bin duk inda wasu farare da grey ɗin tantabaru suka saka ƙafarsu take tana ɗan tafa hannu tana masu waƙa
"Tantabara woooo....Tantabara woooo"

Tana cigaba da binsu gudu gudu sauri² ,cikin rashin zato ta ƙumu da ginin daya ɗan kewaye wajen da yike zaune ,aikuwa ta faɗa rikicaaa cikin flowers ɗin dake a gefe .
Ta kuwa ƙwalla ƙaran Azaba

Dafe kai yayi cikin takaici ,a duniyarsa ya tsani ƙara
Wani ɗan siririn tsaki yaja ,kafin a kasalance ya miƙe yaje gabanta ya tsaya ƙerere ya miƙo mata hannunsa alamar ta kama hannunsa ta miƙe

Bilƙis daga inda take kwance dafe dakai ta ga an sagalo mata kyakkyawar choco hannu lulluɓe da ni'imtaccen gashi

Ɗago lulun eyes ɗin ta tayi ta kafesa da ido ,saidai tana kallonta taji cikinta ya ɗauki jiniya wui wui wui . Saboda kayan da suke jikknsa na ɗaya kenan sannan na biyu ya wani tamke fuska sai hura hanci yake .

Wani sautin marayan kuka ta saka ,zufa ta ko'ina na tsatsafo mata a duniyar ta ta tsani ko kakin ɗan sanda bare na soja

Kansa ne ya sara masa take ya fara jin kansa na masa ciwo ,rayawa yake a ransa meye hadinsa da Wagga yarinyar wacce ruwan hawaye kamar sun mata yawa,da har yike jin ƙolafucin ya taimaketa?

Duddulo mata Idanuwarsa yayi duka waje sannan ya doka mata tsawa ,wanda ya haddasa ma jijiyoyin kansa bayyana

Jikinta ne ya shiga ɓari ,take ta fara mulmule cikin ciyayin wajen ta kuwa shokaresa da takalmin ƙafarta a ƙafa

Wani malolon takaici ne ya ɗebesa baisan sanda ya miƙa hannu ya damƙota ya cikuikuyo wuyar rigarta ya tsinke lafiyayyen kuncinta da mari ba.

Wani ƙara ta saki sai ga jini na tuttulowa ta kuncinta ,take ta shiga Marisa kamar taliya ta yi luuuuu zata zube a ƙasa yayi saurin tallafota ta riɓu akan ƙafafuwan sa


Hajiya Binta da tun kukan bilki na farko ta fito harabar gidan da gudu tana ƙwalla mata kira ,har ta shigo kuma a daidai nan ,Sadiƙ ya kifeta da mari ta sulale kan ƙafarsa

Wani vibration ne ya kama jikin Hajiya Binta ƙif taja ta tsaya ta kasa ƙarasawa har saida Ladi police ta ƙaraso da sauri ,saidai ganinta a saman ƙafan Sadik ya sata tsayawa a gabansa ita bata ɗagota ba sai ma ta hau rawan baki

"My boy ya haka ? Halan ta yi rashin ji?"

Wani kunyane ya kamasa don shi kansa yasan abinda yayi sam bai kyautu ba ,amma saboda aja girma ,kawai sai ya waniyi ball da ita ya zare ƙafarsa ,ya fara taku cike da gadara da ƙasaita ,ba tare da ya tamka Hajiya Ladin ba.

Sai sannan Hajiya Binta ta ƙaraso kan Bilƙis ,ta rarumo kanta "mai gadon zinare ,me ya faru?...." Damtse bakinta tayi da sauri ganin yanda hancin erta ke bulbula da jini jajazir

Wani luuuuu ,tayi da ido kamar wacce zata sume,sannan ta miƙa hannunta tana nuna bayan sadiƙu

"Kambala'i!!" Wani zabura Hajiya Binta tayi taje ta bayansa ta damƙo wuyarsa ,batai wata ² ba ta kafe shi da wani irin gigitaccen mari ta sake ɗaga hannu ta wanke ɗayan kuncinsa


Hajiya ladi ruɗewa iya ruɗewa ko tayi Faɗi take "A'ah Binta karki kuskure ki dakata kinsan shiɗin wanene kuwa?"

Sa hannu tayi ta zungure masa goshi tamkar ta samu ƙaramin yaro

"Yaro na gani wanda aka haifa da jini tamkar yanda na haifa ɗiyata Bilkisu ,don haka ke kika san ko shi wane ne ,mumugunci kawai Azzalumi!"

Dafe kansa yayi da sauri zai iya cewa a iya tsayin rayuwarsa ba'a taɓa zaginsa ba ,kowa girmamasa yike ,sai sanadiyyar zuwan shi wannan Gidan ,dole yau ya koma gidan babansa saidai duk abinda zai faru ya faru

Da kyar ya fara jan sawunsa yina barin hanyar ,ba tare da yace kanzil ba ,itakuwa Hajiya Binta tayi kan ɗiyarta ko a gefen mayafinta ,bata damu da magiyar da Hajiya ladi take ma mumuguncin yaron da taji suna kira da Sadik ba .


Wanene Sadiƙ?
Sadiƙ Yarone na shidda ga sarki Abdul gaffar ,Yinada yayu uku maza ,Adam,sulaiman ,da Ja'afar ,sai mata biyu sadiya da A'isha sai sannan nan shi Abubakar Sadik, bayansa akwai yara Ashirin da takwas wanda suka kasance harda ɗiyoyin ƙwarƙwarorin sarki Abdulgaffar.

Kaf cikin yaran mai martaba ba wanda ya shiga zuciyar mai martaba kamar Sadik ,a yayinda ba ɗa marar ji kamar sa ,sam bai ɗakko halin babansa na dattako da girmama mutane talakawansa ba ,Girman kai da Izza tamkar shine Sarkin ,wannan dalilin yasa tun sanda ya gama secondary school ga buɗe ɗaya daga cikin guest house ɗinsa dake bayan gari ya maidashi fadarsa

Sam baya zaman fadanci tsakaninsa da gida sai in dare yayi ,yina da fadawansa ,da masu hidimta masa ,ana masa zaman fadanci ya hakimce a karaga
Kafatanin Abokan Sadik ,dole su kasance a karkashin ikon sa ,dole ya bautar dasu in ba haka ba a rabu

A gida babansa yike sarki Amma shima a fadarsa sarkine ,don haka kowa sarki yike Kiran Sadiq don kawai a zauna lafiya ,Sadik tun yina karamin sa Allah ya hore masa son Mulki hakan yasa sam baya saka ƙananun kaya sai nauyayan kaya ,kuma ko club zasu da Abokai da kayansa yike zuwa .

Tun bayan da Sadik da babban Abokinsa ,yaron fagachi wanda suke kiransa da sarautan gidansu wato Fagachi ,tun sanda suka gama makaranta fagachi yace shi soja yike son zama ,a ra'ayin Sadik yafison zama lauya amma saboda baison rabuwa da Abokinsa mai fasa masa kai a koda yaushe yina masa fadanci da banbaɗanci yasa yaje ya sama mai martaba ,akan Alankatabir sai a nema masu NDA da Yusuf Fagachi

Soyayyan da mai martaba kewa Sadik yasa shi kasa gane illan kasancewan jininsa Soja

Sun fara karatun soja cikin nasara saidai suna tama 3 A lokacin ne tsautsayi ya afkawa Sadik ,Abunda ko ya faru shine sun shirya get together da abokansa a wajen school sai dai ba daman fita ,yayi duk yanda za'a barshi ya fita amma bai yiwu ba

Ya kuwa fakaici idon kowa ya haure katanga ,dirkansa keda wuya sai a hannun wani major

Ran manjon ya ɓaci gaya ,saboda kowa yina sane da rashin ji irin na Sadik ,ƙaramun laifi ya zama Babba ƙarshe aka koresa aka dawo dashi gida

Kasantuwar hakan babbar abun kunya ne ga mamansa Hajiya mai babban ɗaki ,musamman ga tsakankanun kishiyoyinta da sukayi dace da ɗiyoyi nitsatsu ,yasa tayi shawara da jakadiyarta suka turasa gidan Commissioner of police a matsayin maɓoyan sirri har a gani in za'a iya gyara matsalar sai ya koma makarantar sa batare da kowa ya sani ba ........saidai kuma kash mai hali bayi fasa halinsa tunda Ladi polis ta ƙyalla ido akan Sadik taji tana azaban sonsa bata damu da ƙananun shekarunsa ba ,yanzu haka kuma taci alwashin sai Sadik ya sota kota halin ƙaƙa ,saidai kuma kashhhhh ,tun kafin ai nisa Hajiya Binta ta kwaɓa mata garinta ,batasan ya zata shawo kan sa ba ,duba da Yarone shi mai azaban zuciya ga baƙin hali ga riƙo da ƙulli.



©Alheri Writers Association


Mu tallata Hajarmu

Mata kuna ina???
Ehem Akace in kin ji kira samu ne
*Hajja mai gyaran aure* ta taho maku da zafafan magungunan mata ƴan gaske,tafiyayyu maras Algus,iya kuɗinki iya shagalinki ,ko mijin ki bai saba ihu ba ,Alƙawarine wannan sai yayi , Magunguna na dai ,Akwai garurruka
Gumba
Tsimi
Tabaje
Jigida me matsi da niima
Jigida mai saka farin jini awarwaron farin jini da mallaka
Zobban farin jini da mallaka
Haɗin Ƴar gata
Zuma na musamman
Cicciɓi
Kaza dahuwar uwargida da amarya .
Ƴan shila
Haɗin kifi
Ɓata jikin Kishiya
Maƙale mata
Haɗin karya gado .da sauransu.
Mu ƙa'idar maganinmu bamu badawa sai mun maki bincike in baki da infection in kuma akwai sai mun maki magani
Hajiya ,maganina nagartattune an daɗe ana yabonsu ,kar in cika ki da zance wani abu sai kin amfani dashi wallahi sai kin kawo ƴar uwarki
Domin ƙarin bayani ki tuntuɓi wannan Numbobin 09060703187
Serious masu saya don Allah🙏🏻
[5/31, 22:13] 😘😘😘: *💙🤍BARIKI💙🤍*
_(Gado nah)_
Book 1

Page 7&8

Oum Aphnan✍️


Bin bayansa Hajiya ladi tayi da sauri tana cigaba da masa magiya ,amma in ƙasa ta motsa to ya tanka ,oya oya ya shiga tattare tarkacensa ,kana ya kira wayan Yusuf fagachi ,ya gaya masa inda zaizo ya ɗaukesa.

Hajiya Binta kam sosai ta ƙullaci ƙawarta amma ta shanye bata nuna ta damu ba ,ta kai bilki inuwa ta ɗage mata kanta sama ta goge mata jinin .

Hajiya ladi kam a furgice taje bed room dinta ta ɗauki waya ta hau kiran layin Gimbiya Sauda ,saidai kira na uku kafin jakadiyarta ta ɗauka

"Hello ranku shi daɗe ,Na ɗayo aiki...." Katse ta jakadiya tayi

"Gimbiya na cikin baƙi ,bazata samu daman ɗaga waya ba"

Tsaki taja tayi cilli da wayar ,kafin ta ɗan goya hannunta a baya ta fara kewaye ɗakin
"Ina sha'awar kyakkyawar matashin nan ,idan har na bari yabar mun gidan nan ,tamkar ƙwalele yayi mun,to yanzu ya zanyi?"

Zabura tayi kawai ta nufi ɗakinsa daga ita sai ɓingilar riga mara hannu iya rabin ƙafa bai gama sauka mata ba ,ruwan silver yabi ya kwakkwanta a cuccuran tsokokin jikinta ,mirza handle din Kofar tayi tana kiran sunansa amma ba wani bayanin zai buɗe ,da sauri taje ta ɗauko master key ɗin gidan ,tana wani irin haki kamar wacce tayi gudu,saboda yanda budurwar zuciyarta take ƙara ƙawata mata kyawun sa ,da burin ta samu ya kulata a yau koda zai tafi ne ita dai.

Tana buɗe ƙofar ta maida duk ta rurrufe ta danna kanta cikin bedroom ɗinsa

A ruf da ciki ta gansa still kayan jikinsa dai sune a jikinsa

Wani killing smile ta saki ,sannan ta dunfarosa gadan gadan

Jin takunta yasa ya miƙe da sauri yayi zaman en bori akan katifan ,yana zazzaro ido cikin tsoro da furgici

Muryar ta a dishe ,cikin murya raɗa ² ta kira sunan sa

Hangame baki yayi ya kasa amsa ta, ya cigaba da zurawa sarautar Allah ido .
Zube guiwoyinta tayi akan katifan da yake kwance ta cigaba da haurowa kansa ,saida tazo dab dashi kafin ya yunƙura kamar wanda aka mintsila ya miƙe zubur jikinsa ya ɗauki ɓari

"Sadiƙu my boy ka taimaki momynka kaji ? Gani da dakon buƙatuwata don Allah karkacemun A'ah wlh in munyi babu mai ji ,sau ɗaya kawai! Wallh Allah ya jarabceni da matsananciyar sha'awarka in ka bani hadin kai zan uzzurawa Commissioner mijina sai yasa an maidaka makarantanka ...."

Miƙa mata hannu yayi alamar dakatarwa

"Dakata!!! Ni kin isheni da surutanki da bana fahimta ,Ni dan iska ne aka gaya maki? Dallah matsa Ni da jikinki zubin na Aladai"

"Kataimaka mun Sadik in baka cini ba mutuwa zanyi yau din nan"

Tazo da sauri zata cafke sa yayi saurin zillewa ya ƙumu da boglarin window a hannu ,da sauri ya saki ƙara "Ahshhhhh...ke ki mutu mana Ni ina ruwana ,wai wani masifa ne ya kawo Ni wannan gidan?"

"Masifan sona kuma sai ka soni sai ka cini dole"

"To zamu gani " ya fada yina juya baya yina cigaba da lailaya inda ya ƙume

Ba zato ta afka masa gaba-daya nan suka fara kici kici ,yina son ya kwaci kansa tana kokarin keta masa sutura ,daddagewa yayi ya kurma ihu ,don Abun yafi ƙarfinsa ta turmushesa ta haye ruwan cikinsa

"Wayyo na shiga uku ku taimakeni ku kawo mun ɗauki fyaɗe zata mun wallahi"

Gyara zamanta akansa tayi tana ƙoƙarin zuge zif ɗin rigarta "Ai baka sani ba ,duk wani wanda yake mun aiki a gidan nan tamkar mazaje nane ,damata ne ina darza ƙosashshe mu saki labule ,kaine kadai bare kuma yau zan zama influencer"

Numfashinsa dakyar yike jansa saboda nauyinta yayi tasiri akansa ko motsi bashi iyawa

"Akwai ƙawarki a gidan kuma zan cigaba da ihu har sai ta san cewa ke fasiƙa ce"

"Ahaf itama ɗin dadiro ta ce ,so menene karkasa in cika kuma in na gama in gayyato ta itama ta kwashi lagwada"

Wahalalllen Numfashi yike saki ,wani gumi na tsatsafo masa ko ta ina ,jikinsa har ya fara saki ,shi tunda yike bai taɓa sanin irin wannan wahalar ba

Shashafasa ta shiga yi tun daga dokin wuyarsa zuwa ƙasan kafaɗunsa ,zuruf ya cafki ,hannunta ya yanka mata wani irin kakkaifan cizo ya datse haƙoransa ,ihu take kurmawa na azaba jini na tsartuwa amma yaƙi saki

Dukansa take iya ƙarfi ta da hannu 1 to amma ai shifa sojane baijin bugu ,kawai yaƙi sakin hannun duk da jinin dake fita


Gwale muryarta ta yi tana ihu "Wayyo Allah zai tsinka mun jijiyoyin jini ,wayyo Azabaaaaa!"

Murginewa tayi ta sauka a kansa nanko Allah ya taimake sa ya cikata ya miƙe .
Cikin layi ta kuma biyosa luuuuu zuciyarta a ƙeƙeshe gabaɗaya zina take hangowa a ranta

Dunƙule hannunsa yayi ya shiga bata blow iya ƙarfinsa kamar ya sama wulli majiyin ƙarfi .

Warwas ta zube a wajen ya tattare kayansa ya saka sauri ² ya fice da gudu

****
Su Hajiya Binta fa ,suna ƴan wanne??

Tana nan tana jinyar erta sai ga kiran CP
Zumbur ta miƙe ta bar Bilkisu a wajen tayi saurin kanga wayar a kunne cikin muryar marasa gaskiya

"Hellooo"
Baby girl yaya ,a'ina zamu haɗu,nidai gani a guest room din gidan nan "

"Shikenan ina zuwa " ko ƙara bi ta kan Bilkisu batayi ba ta wuce hanyar shashashancin ta

Bilkisu da cikin sanɗa ta dinga bin bayan uwarta har ta ga inda ta shiga ,da sauri ta leƙa ta kafan ƙofa ,cp ta hanga tif da gajeren wando da farin singlet ya turo rusheshen ciki gaba ,uwarta na kan cinyarsa .

Rumtse ido tayi da karfi ,wasu hawaye Masu raɗaɗi suka shatato mata ,da baya da baya ta rinƙa tafiya idonta ya cika da hawaye sam bata sanin inda take jefa ƙafarta

Karo tayi da jikin mutum ,tayi luuu wannan karon da sauri ya tarota ,ya watsa mata kallon ƙiyayya akan innocent face ɗin ta

"Ƴar ƴan karuwai ,ƴan bariki ,mazinatan mata masu fasiƙanci ,maɗigo da shaye² ,ke kika ja uwarki ta mareni ko?....saina tarwatsa rayuwarki zakisan Kin shigo halarar Sadik sarki ,yanzu ki sani duk wani motsi naki ya dawo ƙarƙashin ikona sai nasa uwarki kuka akanki ,mu zuba ,wasan ba'a fara ba "

Ya hankaɗeta da sauri gefe ,taje taga² zata faɗi ta maza ta dafa wani ƙarfe shikuma yayi wucewar sa cike da isuwa.
[5/31, 22:14] 😘😘😘: *💙🤍BARIKI💙🤍*
_(Gado nah)_

Page 9&10

Oum Aphnan✍️

Daɓas tayi zaman ƴan bori a wajen ,sai sharɓe kawai takeyi ,wannan wani irin baƙar ƙaddarace? Uwata mazinaciya ,ƴar maɗigo , menene maɗigo ma tukun na? ,Kenan gorin da ƴan gidanmu ke mun da gaske ne?

Tana nan zaune taga Hajiya ladi police ta fito a hargitse tayi hanyar part ɗin ta ,wani mugun tsanarta taji ya fara shigarta ,sarai tasan collabo ɗin ta da mamanta shi ya canja Hajiya Binta a da sam ba haka take ba .

Ta kwashe kusan 1 hour kafin ta hango Hajiya Bintan ta riƙo hannun Abdul da ɗan firgice a fuskarta sai gyara zaman kallabi da mayafi take ,har ta ƙaraso inda bilki take

"Muje ko? Tsawan awa ina jiran ki falo na aza kon barci a dakin Aminiya ne ashe kina nan kina fama da ƙufulanci?"

Warrrrr ta watsa mata ƙwarar Idonta ,kafin ta raya a zuciyarta
"Bayan fasiƙanci da cin amanar ƙawance harda ƙarya?? Me ya sama mamana ne wai?"

Tsam ta miƙe ta kawo hannu zata dafa mata kafaɗa tayi saurin ƙwace kanta ,ta yi gaba da sauri ,bayan ta Turo baki gaba ,babu uhm ba um um.

******

A ɗan sahu duk yanda taso taji cikin Bilƙis ta kasa fahimtar ta ,kai daga ƙarshe ta ɗebeta tayi watsi da Al'amarin ta

"Yarinya sai baƙar rai? Allah yasa karki gaji ubanki don zaman gidan miji zaima mutum wuya,don wannan zaman gaban kana gwada wa namiji dukan tsiya zai maki yakuma haramta maki sanwa"

Ta cigaba da jera sababi har suka isa gida

Wasa wasa ,sun kwashe kwanaki bata magana da mamanta da kowa ma na gidan tsakaninta da kowa da safe tabi ɗaki ² ta gaishesu da safe ta wuce makaranta.

******

Friday 12.30
Tunda Bilkisu ta dawo daga Boko ta tarar da umman na zaune a falo tana waya ,da sallama ranganɗau a bakinta ta shigo ,saidai da sauri ta mata birki ta hanyar ɗaura mata yatsa a baki
"Shisssshhhh" Alamar tayi shiru ,sannan ta nuna mata uwar ɗakinta ,alamar ta wuce taje ta sauya kayanta

Cikin takaici Bilƙis ta girgiza kai ,kawai ta saka kanta ɗakin ,ta ajiye jakar makarantar akan keken ɗinkinsu sannan ta sauya kayan ta zuwa na gida ,A gajiye tayi sallah ta kuma fitowa falon still wayar takeyi ,fuskarta sai blushing yake alamun tana tsananin jin nishaɗin wayar da take

"Umma Abinci na"
Tsaki ta doka sannan ta janye wayar a kunnenta da sauri ta matsa dashi can nesa da hannunta ,yanda baza aji maganarsu ta cikin wayar ba

"Kedai bakida hankali wallahi kina ganin ina waya bazaki iya fita ki jirani in na gama kya dawo ba? To ki wuce wajen matar Audu abincinku nacan ,kuma kar in sake ganin ɗan ƙeyarki a ɗakina sai na gama waya "

Tana rufe baki ta soka ƴar ƙaramar Torchlight phone ɗin ta a cikin ɗankwali a saitin kunnenta ,ta cigaba da wayarta "Sorry gentle man ,kasan mata with their commitment, now I'm all for you"

Ɗan jim tayi sai kuma ta saki wani shu'umar dariya ta miƙe ta nufi firinjin ta ta ɗauko lemun ginger a Goran faro ta fara tuttula ma cikinta

Cikin sanyin jiki Bilƙis ta fice wasu ƙwallan baƙin ciki sun taru sun cika mata kwamin ido
"Wai da gaske ne mamana karuwa ce,ko kuwa kalar nata social life ɗin kenan? ...kai Innalillahi wainnailaihir rajiun"

Raɓewa a bakin ƙofa tayi sam ta nemi yunwar cikinta ta rasa ,tana kallon sa'ointa sai tsula rashin kunyarsu suke a tsakar gida ,ita dai ba um ba uhmuhm,gabadaya halin mamanta ya sa ta zama mara kwarin gwuiwa ,tana tsoron shiga sa'ointa saboda gori.

3.17pm
Hajiya Binta a hankali ta buɗe ƙofar ɗakin ,hannunta da mahucin kaba ,ta saɓe labulen akan ƙofa saboda iska ya shigo mata ,sai sannan ta gama wayarta na farali ,wanda inda sabo yaci zuwa yanzu Bilƙis ta saba dashi

Ɗago ido Bilƙis tayi ,gamida kallon mamar Tata ,itama ita ɗin take kallo

"Shegiya daddage ki zama saniyar ware ,kin zo kin rakuɓe anan,ace ɗa baida karsashi a cikin sa'oinsa ? Zaki bar wajen nan ko sai nazo na ɓarar dake "

Cikin layi ta miƙe wani irin jiri na kwasarta
Tana shiga ɗakin tayi arba da lemun ginger da uwar tasha ta aje,da sauri ta ɗauka ta kwankwaɗe ,sannan tayi baya ta faɗa kan kujera rikica ,wasu lafiyayyun hawaye suka fara mata sintiri a kunci

Tsai da ranta Hajiya Binta tayi a take kuma taji ,damuwar ƴarta na damunta ,abunka da ɗa da mahaifi

A sanyaye taje kujeran da take ta zauna ta jawo kanta ta ɗaura akan cinyarta tana goge mata ƙwallarta a hankali tana shafa mata gadon bayanta

"Me gadon zinare ,waya taɓa mun ke ? Na kwana biyu rabon da inga murmushi a fuskarki meyasa ,kinaso ki jamun asaran ranki ne ehemm?"

Shiru tayi bata tamka mata ba ,saida ta cigaba da nacuwa ,kafin ta soma magana cikin shesheƙa

"Umma wai ke ....wai ke ....wai ke karuwa ce" kawai saita tuske da wani irin firgitaccen kuka wanda yasa Hajiya Binta faɗuwar gaba ,a tsorace ta cillo mata tambaya

"Inji wani Algungumin Allahn?"

"Umma me ke kaiki gidan ladi police ? Ance da ita da mijinta basuda kamun kai ,umma nifa ƴar kice kinaso in rasa mijin aurene ace mamana fasiƙa....? Umma ya mu'allim ɗinmu yace zina bin jini take ,kullum inajin yina yiwa mazan ajinmu nasiha kar su yarda su auri ɗiyar lalataccen zuriya irin mu maaamaaa😭"

Sosai ta gama firgice mata da ihu sam ta kasa shawo kanta

"Bilkisu ki nutsu ki saurareni ,Ni ba fasiƙa bace..." Da sauri ta katse ta
"Amma kullum kina waya da maza da rana ku raba dare kuna waya da daddare da maza...a gidan mama ladi ku kulle ƙofa a bedroom ɗin ta kuna wani irin gunji ke da ita kamar muzurai ,umma me kuke yi eheee?"

"Balkisu dama samun ido kikayi haka ?"

"Umma ba samaki ido nayi ba wallahi kawai na girma ne ,shekara ta sha huɗu ,to karantar ki nayi kawai"

Wani wahalalllen Numfashi Hajiya Binta ta aje ta daɗe tana ɓoyewa yarinyar abinda ke faruwa ashe kallon kitsen akewa rogo

"Bilkisu Na yarda ki tuhumeni ,amma lokaci yayi da zan fayyace maki daga Ina matsalar take ,Ke macece babbar ɗiyata wanda watarana zaki zame mun Aminiya abokiyar kukana ....Bilkisu kome ya samu shamuwa watan bakwai yaja mata ...babanku baya bamu ci ,baya bamu sha ,baisan kuɗin makarantan ku ba....Daya bamu tiyan gero mu jiƙa muyi maku kunu ya gunmace yaje ya siyo ma dokinsa buhun dussa ,komai naku ya barmun ,gashi inaso kuyi karatu ,Inaso kusa sutura mai kyau kamar na sauran yara masu uwa da uba .....Bilkisu ga matsatsin gidan yawa, Bani da sana'a ga sharrin kishiya ,ki faɗa mun taya zan tsira dani daku in ban nemi hanyar da zan samu kuɗi koda zan yasar da mutunci na ba ne indai ku zaku rayu ba?"

"Umma ki zina saboda ki bamu abinci? Kiyi zina saboda ki bamu kayan sawa ƙawa da za'a barta anan duniya ? Wanda Allah yayi alƙawarin bawa duk wani mutum abinci da abunsha da zai yi rayuwa saidai in ya raina ne ,misali mangoron gidan nan abincine in muka tsinka mukaci zamu koshi ,ruwan rijiya birgiman kwaɗi ruwane Allah bai ƙoronsa ba ko ina akwai shi in mukasha zamu rayu....kin zaɓi muci abinci da nama da kifi muci kpomo musha ruwan leda tayaya ,Allah bazai barmu da kanmu ba ?.....Umma kin taɓa Addu'a akan matsalar ki ? Amma kinje kina turamu islamiyyar da ake biyan 5k a wata ,idan kin samu makarantar zaure ba'a karatune? Kin saka mu Makarantar boko na dubu casain a wata uku ,idan kin samu makarantun gomnati ba'a karatune? Wait mama kijini don Allah da kuɗin zina fa kike biyan kuɗin makarantar ilimin mu har kike tunanin zai mana albarka kuma ya Amfane mu dake a gaba?...kaicon wannan rayuwa tamu mara balance"

Dafe kai tayi da sauri

"Ilahu yau ake yinta ,Baƙar tukunya kenan mai fidda farar tuwo " Bata gama Ankarewa ba ,kawai saidai taga ta miƙe da sauri zata shige uwar ɗaki ,da sauri ta miƙe itama ,ta bi bayanta

"Bilkisu ina zaki ?"
"Umma bakiji an kira sallah ne? Zanje in sallah in shirin Hadda kuma"

"Yau Inaso ki fasa zuwa Haddan ki zauna muyi magana " kallonta tayi ƙur ,sai kuma tai saurin cire idonta akanta taje gaban dressing mirror ta jawo kujeransa ta zauna ,tana kallon Hajiya bintar

A hankali ta nemi gefen gado ta zauna

"Bilkisu ?"
Ɗagowa tayi ta kalleta ba tare da tace mata uffan ba

"Balkisu magana nikeso

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment