Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

3 zata sake ta"

Zamewa faruq yayi ya zauna akasa tare da fasa wani gigi tatcen kuka"

Ganin faruq ya kasa tabuka komai yasa shi ya fara tunanin yadda zaiyi ya fitar da nihilah daga gidan"

Zuwa can ya dauko waya ya daddanna sannan yasata akunnen shi"

Zuwacan yace jamila inason ganin ki yanzun nan karki wuce minti 15 sannan kiyi shigar mutunci kisako babban hijjabi"

Daga can cikin wayar aka amsa mai cikin dauki"

Zama yayi kusada faruq akasa ya rafka uban tagumi tare da tunani barkatai"

Ba,awani dauki lokaci ba jamila ta iso, tashi yayi ya karasa kusa da ita sanna ya fara gaya mata yadda zatayi"

Key motar shi ya mika mata sannan ta nufi dakin baccin shi"

Zuwa can ta fito tallafe da nehila da taimakon usman suka sakata amota , yayin da faruq yake tsaye a yana lekensu"

Jamila ca ta zagaya ta zauna amazaunin drive sannan taja motar aguje tabar gidan"

Cikin sanyin jiki usman ya dawo cikin falon sannan ya kamo hannu faruq ya zaunar dashi akan kujera"

Kallonshi yayi sosai sannan yace"

Faruq nakasa yadda cewa kaida yariyar nan ciki daya kuka fito, Faruq yaya za,ayi ku fito ciki daya sannan ka dinga cewa kana bukatar ta" nidai gaskiya ina da jah"

Wani hawaye ne ya sake zobo ma faruq sannan yace"

Usman ka daina mamakin haka nida nihilah uwa daya ta haifemu"

Kai inna usman ya fadi yana girgiza kai"

Mikewa faruq yayi yana kokarin fita"

Dasauri usman ya rikeshi tare da tabambayan ina zaka"?

Gida ya fada yana share hawaye"

Karkaje gida yanzun faruq , ka bari muga dawowar jamila, yanzun kaje kayi wanka kaga lokacin sallah ya kusa"

Yana kuka kaman karamin yaro tare da jan majina yace"

Inason nasan halin da nehilah take ciki, sannan inna tunanin halin da anty zata shiga idan wannan mummunan lbrn ya same ta"

Faruq ka natsufa karka bari rudewan ka yasa agane ka kaga dai yanzun yarinyar bazata shaida ka ba......

Tsayawar motar da sukaji shiya tabbatar musu jamilah ta dawo cikin sauri usman ya mike ya fita"

Zuwa can suka shigo tare da jamila tana kwance kan kirjin usman daka kalleta zaka fahimci tana cikin damuwa"

Zama sukayi atare sannan ta fara kokarin zame hijjabin tana fadin"

Iyayen yariyar nan sunbani tausayi, gidansu babban gida ne kuma nakula akwai tarbiya sosai agidan"

Lokacin dana musu bayanin na tsinci yariyar ne abakin titi, hankalinsu ya tashi sosai, Amman da muka fito da yariyar, iyayen suka fahimci abinda aka mata take nahaifiyar yariyar ta saka hannunta duk 2 aka ta fasa uhu"

Kara kama hannun usman tayi sannan tace meyasa kukamata haka, kuma yariyar gashi tayi kankata da yawa"

Cikin sauri usman ya daga mata hannu sannan yace wannan kuma ba huruminki bane, hannun yasa a aljihu ya ciro kudin sannan ya mika mata tare da fadin tashi ke tafi zan kiraki an jima"

Bayan fitan jamila usman yaci gaba da lallashin faruq"

Amman faruq jiyake kamar anakara mai damuwar, daka kallishi zakane a rude yake"

Sai kunsan mangariba usman ya lallaba faruq yayi wanka sannan ya sauke bashin sallolin da ke kanshi tare da tunanin anya ma Allah zai karbi ibadan shi kuwa?

Bayan ya idar usman ya rakoshi har gaban motarshi sannan ya kara jajjadada mishi ya daure sosai karya nuna wata alama da saisa aganeshi"

Tafiya faruq keyi cikin motar shi hawaye nabin fuskar shi ya kusa shiga unguwar su wayar shi ta fara kara yana duba yaga anty ce"

Take yaji gabanshi ya fadi cikin sanyin jiki ya dauka"

Yaro ina kashiga tun safe baka gida?

Daji muryan anty kasan taci kuka ta koshi"

Shima muryanshi dakushe yace momy lfy naji muryan ki wani iri?

Fashewa tayi da kuka sannan tace" yaro nihilah, nihilah wani wadda bamusan kowanene ba ya lalata mata rayuwa"

Zame wayar yayi ahankali ya kashe, har yanzun kuka yakeyi dan haka gaba daya fuskarshi kunbure take gawasu ciyuyuka agoshin shi, dan haka fuskar ta hadu tayi jawur"

Cikin kankanin lokaci ya isa gida, nan take ya gane gidan acike yake"

Motocin sosai acikin habar gidan tunkafin yashiga ya gane suwaye aciki saboda motocin da yagani"

Cikin sanyin jiki ya nufi cikin gidan tura kofar yayi ahankali ya shika"

Duk suna zaune a cikin falon yayin da daddy da alhaji ibarahim suke tsaye kowannen su ya rungume hannu"

Bashir ko yana zaune aksa ya rafka uban tagumi, yayin da umma ke zaune akan kujera nihilah kwance ajikinta, anty da hajiya b tare da hajiya mariya suna zaune suma sun zuba tagume"

Shigowan faruq yasa kowa dagowa yana kallon shi"

Ahakali yake tafiya ta tsakiyan su hawaye na tsiyaya a idonshi, saida ya isa gaban umma sannan ya tsuguna"

Kallon nehilah yayi idonta rufe kamar me bacci taba fuskanta yayi tare da girgizata"

Tana bude ido hawayenta yazobo kamar daman jiranshi suke"

Hannu yasa ya fara share mata hawayen tare da fashewa da kuka"

Kuka yakeyi kaman karamin yaro, babu wadda yayi yinkurin hanashi domin gani suke kukan ma yafe rahama agurin shi"

Jin inda faruq ke kuka yasa mutane da dama kuka afalon, aciki hadda nihilah domin tunda ta dawo hankalinta takasa cewa uffan duk da cewa anyi2 tayi mgn taki, amman jin inda faruq ke kuka yasata itama ta fashe da kuka"

Sunkai kusan minti 10 ahaka sannan alhaji ibrahim yace"

Kai faruq ya isa haka, kaida zaka lallasheta kuma saika zauna kana kuka saika ce karamin yaro, ya kamata mutaru mu rugumi kaddaran da Allah ya aiko mana da ita, jarabawa ce , babu ta inda Allah beyi domin ya jaraba imanin bawan sa, dan haka kuka ko damuwa ba shine zai yaye mana tadamuwa ba, muyi hakuri mu roki Allah ya kara tsare mana yaran mu baki daya"

Umma ce ta bude baki tana share hawaye take fadin ai alhaji hakuri ya zama dole, amman zamu dosa addu,a insha Allah duk Wanda ya mata wannan aikin sai *ASIRINSA YA TONU* πŸ‘ˆπŸ»

Hajiya mariya ce tasa mayafinta ta share fuskan ta sannan tace"


Da izzinin Allah kuwa, wannan ma ai zalincin yayi yawa kowaye wannan bashi da imani da tausayi"

Faruq kara karfin kukanshi yayi, jin su umman suna addu,a Allah ya tona mishi asiri"

Cikin kuka yake bin bakin anty da kallo tare da addu,an kada Allah yasa anty tayi irin addu,an umma dan yasan nata saiya fi nakowa kamashi"

Hajiya Mariya ce ta matso kusa da faruq ta zauna agaban shi sannan ta jawo faruq ta kwantar dashi ajikinta ahankali ta fara shafah gashin kanshi tare da fadin Haba faruq kayi hakuri mana, wannan abu fah bakanta farau ba , nasan dole abin ya maka zafi, kamar yadda yamana amman inason ka daure , idan kana kuka haka kara tadawa nihilah hankali zakayi"

Ahankali faruq ya fara sauke ajiyan zuciya, tashi yayi ya zauna ya rafka uban ta gumi"

Bayan kowa ya wuce yarage daga anty sai faruq da nihilah, dan hajiya b ta wuce dakinta daddy ma tunda yafita raka alhaji ibrahim har yanzun be dawo ba"

Nihilah na kwance akan kujera yayin da faruq yake zaune agaban kujerar hannun shi sarke dana nihilah, har yanzun hawaye ne ke ziraro masa ya kasa tsaida su, yana bakincin da takaicin abinda yafaru"

Anty ko idon ta zuba musu, tana kallon su hawaye na zobo mata zuwa can tace"

Yaro?

Cikin sauri faruq ya dago ya kalleta tare da amsawa "

Cikin kuka tace "

Yaro ina cikin tashin hankali ga wani abu ya tsayamin akirji, inaji ajikina kaman wani abu mara dadi ne zai sameni"

Tasowa faruq yayi ya dawo gabanta tare da fadin anty insha Allahu bawani abu dazai faru bayan wannan Da izzin Allah"

Tana share hawaye tana fadin Allah yasa haka"

Faruq ne ya kama nihilah yakaita har kan gadon baccinta, daker take iya taka kafanta kamar me koyon tafiya"

Bayan ta kwanta ya kura mata ido, har yanzo be daina jin abin da yakeji game da itaba"

Kokarin fita yake dan yau babu bakin mgn, harya kai kofah nihila tace"

Yaya?

Da sauri ya juyo ya kalleta"

Ahankali ta bude baki tace"

Yaya dan Allah kazo ka dandanna min cinyata"

Bece komai ba ya karasa gabanta ya fara danna mata cinyar kamar yadda ta bukata"

Zuwa can ta daga rigarta tamai nuni da kwankwasonta"

Ba musu yayita dannawa har saida ya tayi bacci sannan ya rufeta ya fita"

Koda ya kwata daya rufe ido surar nihila yake gani kwata kwata ya kasa bacci dan haka ya tashi ya dauro alwala yayita sallah tare da neman gafara, zuwa can ya fara hamma, yana kwaciya bacci ya dauke shi"

Ahaka har suka kwashe tsayon sati 2 kulum faruq yana zuwa dakin nihila domin debe mata kewa, yayin da faruq ke fakewa da tausa yana lalubeta

Nihilah ta warke sarai kuma idan ka ganta babu damuwa atattare da ita"

Shiko faruq idan yana tare da nihilah mantawa yake da komai saidai idan ya kebe ya shiga damuwa gashi ya kasa gayawa kowa halin da yake ciki"

Zuwa wannan lokacin nihilah tafaraji in nama akwai aure tsaninta da yaya faruq, dan idan yana taba jikinta wani irin dadi takeji, saidai tana boyewa dan kada ya gane,

Shima faruq anashi ban garen haka yake , dan yazun ya zaman mai jiki kullum saiyaje dakin nihilah sungama matsa junan su da nufin wasa"

Faruq so yake wasan naso ya wuce haka, amman yana gudun kar nihilah ta dago manufarshi,

Dan haka yau faruq daya tashi shiga dakin nihilah ya zuba cingum guda 6 a aljihun shi"

Tura kofar yayi tare da sallama, hangota yayi kwance gefen gado hannun ta rike da novel"

Har ya zauna nihilah bata kalleshi ba, dan haka ya mika hannu ya fisge liltafin RIKICIN BABBAN GIDA yaga anrubuta ajiki, wadda Faty Afreen ke kan rubuta 2 dinsa"

Ajeyeshi yayi agefe sannan yace lallai nihilah littafin nan ya miki dadi ko kallo na ma bazakiyi ba?

Tasowa tayi ta dawo da kanta kan cinyarshi sannan ta mika hannunta ta shafa sajen sa"

Ajiyan zuciya yayi sannan shima
yasa nasa hanun cikin rigar ta da nufin wasa tun tana dariya harta fara narnarkewa"

Shima kara shige mata yake zuwa can ya dakata yasa hannun shi acikin aljihu ya dauko cingam din daya taho dashi ya bare sannan ya saka mata acikin baki

Shima saka dayan yayi abaki sannan yace"

Karfa ki tauna wani wasa zamuyi kisan menene?

Tana
dariya ta girgiza kai"

Wanan cingam din dana saka abakina zaki ciroshi da bakin ki ni kuma zan ciro na bakin ki , lokacin da kk kokarin ciro nawa,

Oyya mufara mugani waye zai fara cirowa







β„πŸ’¦Mmn Yazeedβ„πŸ’¦
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦
*ASIRINSA YA TONU*
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦


β„β„β„β„πŸ’¦
*By*
β„β„β„πŸ’¦
*Fadeela Lamido*
β„β„πŸ’¦

β„πŸ’¦



β„β„πŸ’¦
*Page 22 to 24*
β„β„πŸ’¦



*Dedication*
Hafsat Ibrahim
Ummul khairi
Hafsat Yusuf
Hausaina Faji
Hafsat Yusuf
Hauwa
Habebaty mom Nawal
Hajju
Exclusive
Maryam tata
Rabi m sulaiman





β„πŸ’¦ Dai dai lokacin da suka nufi bakin juna, sukaji muryan anty tana kiran nihilah"

Cikin sauri ya janye bakin shi tare da fadin tashi ki tafi"

Tashi tayi badan ramta yasoba taso ace suyi wannan wasan"

Jikinta asanyaye take tafiya harta isa falo, gaban anty ta tsaya sannan tace anty gani"

Jawo hannuta tayi sannan tace"

Zauna zamuyi mgn"

Bayan ta zauna anty tace"

Nihilah umma ce ta bugumin waya wai tanason ki koma can gidan su da zama"

Dasauri nihilah ta turo baki tare da fadin anty nidai gskiya bazani ba"

Sakin baki Anty tayi sannan tace"

Wanan fah shine kirikiri, ke yanzon bakiji kunya ba, wai meyasa baki da hankali ne?

Turo baki nihilah ta fara sannan tace"

Anty nifah bazan iya tafiya nabar yaya faruq ba, saidai mu tafi tare"

Caffdija abin da anty ta fada kenan, sannan ta kara cewa"

Kisan duk tsiya dai kin kusa barin gidan nan ko? yaro kuma dole ne ku raba gida, ko kina so ko baki so, dan haka maza ki fara hada kayanki tunkafin raina ya baci"


Tashi tayi cikin kuka ta nufi daki, tana tura kofar tafara cewa yaya kaga Anty.....

Sai alokacin ta lura faruq baya dakin , fitowa tayi daga dakin ta nufi nasa dakin"

Tana tura kofar ta sameshi yana zaune kan sallaya ya daga hannun shi sama yana addu,a "

Zaman yan buri tayi agaban shi tana matso hawaye"

Cikin sauri ya shafah addu,an sannan yace"

Meye ya faru kuma?

Cikin kuka ta fara fadin mai"

Bayan ya gama sauraranta sannan yace"

Kai itadai wannan umman ta cika fitina wallahi, haka fah jiya danaje gidan taita hararata, ni bansan me namata ba, wlh ta tsane ni, tashi moje gurin antyn"

Bayan sun zauna falon anty ta kallesu, sannan tace"

Ankai ma kara ta kenan?

Fuskar shi daure ya zauna sannan ya kalli anty yace"

Amman dai anty irin wannan be dace ba, haka kawai tarasa wadda zata dauka sai nihilah ta dauki khadi mana ko sadiya, nifah daman bansan me nayi ma matar nan ba ta tsaneni.......


Hannu Anty ta daga mai tare da bugamai wani gigittace tsawa ashe baka da kunya haka bansani ba?, yaushi aka haifeka dahar ka iya zazzaga wannan rashin kunyan, toh bari kuji ku baku isa ku raba mana zumunci ba, dan tunkafin nasan zan sameku muke tare, lokacin da nake da cikin ka babu irin whalar da batasha ba, sai yanzun dan tace abata nihilah saimu hanata"

Shiru faruq yayi cike da mamakin fadan Anty dan rabon da tamai irin fadan nan ya manta"

Cikin Sanyin ciki yace"

Amman dai anty irin wannan fada saikace ......

Zagi ta kunduma mishi, daga faruq har nihilah suka zaro ido "

Anty cigaba tayi da cewa wlh Yaro ka fita idona, idan ba haka ba.....kukane ya kwace mata, dan haka hanlin faruq ya kara tashi"

Saukowa yayi gabanta, hakika wannan abu na Anty yau ya bashi mamaki cikin yanayin dake nuna yana cikin damuwa yace"

Anty dan Allah kiyi hakuri basan cewa mgnta zata bata miki raiba na bari.....

Daddy ne ya katsesu da sallama, kallo yabi anty dashi tare da tambayan lfy?

Bata ce komai ba illah kukanta dayake karowa, nihilah ma dake gefe kuka takeyi, shiko faruq idon shi jawar dan yau anty ta daure mai kai"

Daddy ne ya zauna sannan ya kalli anty yace"

Menene ya faru ina mgn kinaji na"

Share hawayen ta fara sannan tace"

Alhaji ni gaskiya so nake Yaro yayi aure, alhaji wasu irin mugayen mafarkai nake akan shi"


Gaban faruq ne yayi mummunan faduwa, tare da tunanin kardai irin mafarkin dayakeyi ne itama anty tayi"

Yana cikin wannan tunanin yaji anty ta sake cewa"

Dan haka nihar nihilah ma idan aka aurar da ita hankali na saiyafi kwanciya"

Da sauri faruq yace"

Anty toh dan wannan kawai saiki zauna kina kuka, indai aure ne zanyi amman kicire mgnr nihilah abari mana yayyanta suyi, amman yanzun aitayi kankanta da yawa"

Daidai wannan alokacin daddy yace"

Ko baki matsaba daman zaiyi aure yanzun haka da mgnr da na shigo kenan, naki gaya mishi ne saboda na fahimci shiririta tamai yawa, dan bashir ya gayamin mamana ce ke zuga shi, banda kai shasha ne me zaikai ka shawara da nihilah, kanwar bayan ka, dan haka jiya mukakai sadakin ka gidan malam salihu"

Faruq da nihila hada baki sukayi wajen tambayan wannen mlm salihun?

Dakewa daddy yayi dan sunso su bashi dariya, kallo ya bisu dashi sannan yace mlm dai wanda kuka Sani, sanin kanku ne cewa duk yan gidan nan auren zumunci muke, toh kai katsaya wasa yan matan da muke dasu yanzun haka duk sun kama dahir dan haka muka yanke shawaran hada ka *Naziya* saboda mlm salihu yazama tamkar jininmu"

Hawaye ne ya fara zuba afuskar nihilah cikin kuka ta fara buga kafa kamar yadda yara kiyi tana fadin"

Haba daddy, haba daddy, dan Allah nidai gsky ban yadda ba ai garama Anty amiran, wannan *Naziyar* shegen iyayin tsiya"

Ikon Allah Anty ta fada tare da cigaba da cewa"

Shi wan da zai zauna da ita bece komaiba saike,? kinga ki kiyayi bakin ki"

Kuka nihilah tacigaba dayi sannan ta koma ta zauna da karfi tana turo baki"

Daddy hankalin shi ya mayar kan faruq bayan yagama karewa nihilah kallo, sannan yacewa faruq"

Kai kuma ka bude kunne ka dakyau kajini, wannan karon bashawara na bakaba umarni ne, dan har mun taida rana nan da 1 mouth insha Allahu, karka kawomin wani uzuri bazan dauka ba, dan ni ba mahaukaci bane irin ka bare harna zauna nihilah ta juyani"

Shi dai faruq bece komai ba, kanshi na sunkuyi akasa, acikin zuciyar shi ko cewa yake dole na hakura na aure naziya ko dan kwanciyar hankalin Anty, wata kila sanadiyar haka na daina jin abin da nakeji akan nihilah"

Nihilah ko ganin faru bece komai ba yasa ta mika kafarta ahankali ta zungure shi"

Dagowa yayi ahankali ya kalleta"

Kafada ta make mai sannan tayi kasa da murya tace"

Karka yadda wlh kazamiya ce"

Da sauri ya maida kanshi kasa, nihilah taita zungurin shi yaki dagowa"

Haushine ya kamata dan haka ta tashi aguje ta nufi daki"

Koda faruq ya mike bebi takan nihilah ba, dan yasan ta tsuniyar gizo bata wuce ta koki"

Shiko yanzun babu abinda yake so illah yaga yayi nisa da nihilah dan gudun kar abin da ya faru abaya ya sake faruwa"

Yana shiga dakinsa ya fada gado tare da tunu surar naziya yariya tana da kyau babu laifi"

Bayan sati 2 shirye shiryen biki ya kankama faruq da bashir ba zama, kwata2 baya bari su hadu da nihilah rabon shi da ita tun ranar da aka fadi mgnr saka ranan shi, sai dai ya hangeta daga nisa"

Nihilah na kwance falo idon ta rufe babu abunta ke damunta aduniya kamar auren naziya da faruq, ji take tamkar ta hadiye zuciya, gashi taga faruq har wani rawar kai yake, tana kallon shi yake lallabawa wai adole yana boye mata"

Tana cikin wannan tunanin taga ana shigowa da akwatuna, nan falon aka ajiye kara rufe ido tayi kamar me bacci"

Zuwa can taji muryan umma tare da hajiya mariya"

Hajiya b ce ta tarye su, sannan suka shiga duba akwatunan"

Dubawa suke suna yaba kyan kayan, zuwan can taji muryan khadi tana fadin kai rigar nan tayi kyau"

Nihilah jitayi kamar ta buga mata kibiya a zuciya dasauri ta bude ido ta sauke akan rigar"

Mikewa tayi cikin sauri ta koma kusa ta umma zuwa can ta mika hannu ta dauki rigar sannan tace"

Umma inason wannan rigar"

Ko kallonta umma bataiba ta mika mata rigar, sanna ta juya tace sai kuma me kk ......

Bata kai ga karasawa ba donta suka sauka akan fatan nihilah"

Gani tayi duk ta dashe tayi wani irin fari naban mamaki"

Gabanta taji yayi wani mummunan faduwa tare da fadin"

Innalilahi wa,inna ilaihir raju,un"

Nihilah *Ciki*?πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ








β„πŸ’¦Mmn Yazeedβ„πŸ’¦
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦
*ASIRINSA YA TONU*
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦


β„β„β„β„πŸ’¦
*By*
β„β„β„πŸ’¦
*Fadeela Lamido*
β„β„πŸ’¦

β„πŸ’¦



β„β„πŸ’¦
*Page 25 to 27*
β„β„πŸ’¦





β„πŸ’¦ Gaba daya falon dagowa sukayi suna kallon ta "

Daidai lokacin ant y ta fito da gudu tana fadin menaji kuna fada?

Ahankali nihilah tafara zamewa hartaje kasa, umma ce ta mika hannun ta tana bude idonta"

Wani hawaye ne ya zobo mata me zafi sannan tace"

Waiku baku da ido ne ? Yariyar nan ciki gareta "

Gaba dayan su rudewa sukayi zuwa wannan lokacin nihilah ta fara fahimtan me ake nufi dan haka tasaka wani irin marayan kuka"

Anty kuwa tunda ta zame abango bata kara mutsiba, idonta abude yake kuma tanaji tana gani amman ta kame kam"

Umma jawo nihilah tayi ta rugumeta tare da tsananin tausayinta acikin zuciyarta"

Hajiya b ce tayi karfin halin cewa kutashi kwai muje asibiti"

Cikin kuka umma ta daga nihilah dake kuka cikin wani irin sauti me ban tausayi"



Please Login or Register in order to submit comment