You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ya hana su
aukuwa sai da aka daina ganinta, to balle Baba
da na san bani da wani gata sai shi, shi ne komai
dina shi kuma in na rasa shi a wane hali zan
samu kaina? wace irin rayuwa zanyi cikin
wadannan mutane?"
Tsawon sati biyu komai yiwa Baba ake yi, a
kwantar dashi a tayar dashi. Ana nan a haka sai
kuma Allah da Ikonsa ya soma samun sauki
kowa sai murna amma zan iya cewa babu wanda
ya kaini daga samun saukin nashi kuma sai ya
sallami kowa da kowa ya ce su tafi wurin
gurin iyalansu ya baiwa Alhaji damar diban
abinda yake da yake bukata.
24
kam ai ta wuce Zuwaira, sai dai mu ce Allah ya
bamu ikon cikawa da Imani." Na yi ajiyar
Zuciya na ce, amin.
Baba ya riga ya rasa karfi mai yawa don
haka ko kofar gida bai fita sai dai in yi mishi
shimfida a gindin bishiyar dake kusa da dakin
Baba Rabi ya fito ya zauna, saboda masu
shigowa gaishe shi gaba daya hirarmu kuma sai
ya maida ita yin nasiha. "Ki zama mai hakuri da
juriya Zuwaira, sannan kiyi kokari ki rinka
kawar da kai kan abin da idonki zai rinka gani,
ba komai ki ka gani ne zaki bata rai ko kiyi
magana a kanshi game da al'amarin mijinki
kuma ki rike shi da al'amarin mijinki kuwa ki
rike shi da al'amura guda biyu, hakuri da godiya
in ya yi miki laifi kiyi hakuri, in yayi miki alheri
ki gode mishi, kar ki yarda wani canjin rayuwa
ya same ki kice mishi ya kai ki kasarku kiyi
hakuri da duk abin da za ki gani watarana zaki
bada labarinshi bayan ya wuce.
A duk lokacin da Baba yake yi min
wadannan maganganun, kuka nake yi saboda
nasan duk abin da yake cewa in yin yana nufin
25
komai ba Zuwaira, addu'a kuwa kullum ina yi
miki ita. Ubangiji ya wadata zuciyarki da hakuri
ya kuma baki dauwamanmen rufin asiri in ce
mishi amin.
To a haka muka zauna babu ya rasa karfi
nima na rasa kuzari zuciyata ta karaya na zama
komai ma sa ni kuka yake yi. A haka Alhaji
yazo ya same mu yayi kwana biyu ya tafi bisa
cewar zai dawo sati mai zuwa tun daga nan ya
koma zuwa duk Alhamis suyi sallar Juma'a tare
sai ranar Asabar ya tafi.
Rannan ina tare da Baba miyar kuka nayi
mishi da naman kaza na kuma tuka mishi tuwon
Alkama nasa mishi man shanu muna zaune ina
yi mishi hira cikin natsuwa don dai in samu
yaci tuwon da dan yawa sai ga yara sun shigo
wurin nashi bayan dawowarsu daga Makarantar
allo suna fadin "Umma yau kin manta ba ki
bamu kudin Laraba ba, na ce eh ku kuma baku
tuna min ba, Baba ya zuba musu ido yana
kallonsu ni kuma na basu umarnin su bi Uwa
taje ta sa musu abinci bayan tafiyarsu sai ya ce
min yanzu da wadannan fararen kayan nasu kal-
26
kenan kike sanye da fararen kayan na suke
kallon Baba cikin tsoro na ce mishi Baba nima
ba furare kaya ne a jikina ba hankalinshi a
kwance ya ce "au Haba? to ai shi kenan
watakila idanuwan nawa sun gama aiki baba?
Na kama kuka shi kuwa ko a jikinshi sai ma ya
ce in kina yi mun haka ba zan rinka gaya miki
magana ba, to menene don na fadi haka tsofaffi
nawa ne hakan yake samunsu? Nayi shiru na bar
kuka, don Baba kar yayi fushi wurin rannan
wuni nayi ina tunanin in Baba ya daina gani irin
abubuwan da zan rinka yi mishi don in rinka
taimakonshi kan hakan.
Har akayi sallar azahar kafin na tashi na
koma wurinmu na gyaggyara ina shirin dora
miya sai ga Babangida da gudu yana fadin wai
in ji Baba wai kizo nayi maza na wanke
hannuna na bi bayanshi naje na same shi a
zaune a bakin gadonshi ya kalle ni cikin
natsuwa ya ce min, "alwala nake so kiyi min."
Na yi maza na ce mishi "Ba ka da lafiya ne?" Ya
ce min a'a kalau dina fitanne kawai bana so na
ce to na daura mishi alwala ya sauka kan
shimfidarshi ya zauna yayi sallarshi ban fita ba
sai da naga ya idar sannan na ce mishi bari in je
in dora miya zan turo maka su Junaidu su maka
hira kafin in dawo, ya ce to na dawo wurin mu
27
na samu har Uwa ta ajiye mun sanwar miyar,
mamaki ya kama ni don komai ta tsaida shi
kamar yanda taga ina yi.
Washe gari wajen azahar Alhaji ya iso tun
daga nan ya karben yiwa Baba alwala ya ma.
sani na kawo ruwa mai zafi yayi mishi wanka ya
goge shi ya shafa mishi mai ya canza mishi
kayanshi yayi tsaf sai kamshin turare yake yi da
daddare na shigo dakin bayan sallar Isha'i na
samu bai ci abincin da na kawo mishi ba, ya ce
min cikin bai mishi dadi don haka sai ya lafa,
Alhaji ya ce dan damo mishi kunu shi da yake
ruwa ruwan na ce mishi to na damo na kawo na
dawo dakina na gama abin da zanyi na hau gado
na kwanta har bacci ya dauke ni, Alhaji bai
shigo ba na farka ban ganshi ba gabana ya đan
fadi saboda tunanin ko jikin Babanne babu dadi,
na tashi na gyarawa yara kwanciya na dawo na
zauna a bakin gadona cikin tunani iri-iri naga
dai wannan ba zai min ba na fita nayi alwala na
dawo nayi sallah raka'a hudu nayi addu'a na
shafa na dawo kan gadona na kwanta sai dai
kuma bacci bai sake daukana ba zuwa can sai
gashi ya turo kofa a hankali ya shigo ina
ganinshi nayi maza na tashi na zauna a bakin
gadon nace yau kuma jikin Baba babu dadi ko?
Bai wani yi magana sosai ba sai ya zauna a
28
gefena cikin natsuwa sai ya ce min Allah ya
saka miki da alheri kan dawainiyar da kika yi da
mahaifinmu, Ubangiji ya saka miki da mafificin
sakarmako." Maganar tashi tayi min wani iri don
ban taba jin yayi min irinta ba, don haka cikin
rawar jiki da rawar murya sai na tambaye shi
"babu shi ne Baban'?" A hankali ya buda baki ya
ce min, "Babu shi Zuwaira, yau kam Baba ya
barmu sai kiyi hakuri kar kice za ki tsananta yi
mishi kuka, kiyi mishi abin da zai amfane shi
shi ne addu'a." Tsawon daren nan ba zan iya
tunawa da irin addu'o'in da na kwana ina yi
mishi ba, illa iyaka dai nasan daga mutuwar
Baba ban sake yin lattin sallah ba balle in je ina
hada azahar da La'asar ko Magariba da Isha'i.
Sai na rinka ganin tamkar lokacin sallolin nan
lokacin ne kawai nake dashi, na mika addu'ata a
gare shi bana hirar bakin cikin da nayi na rasa
don ba zan iya kwatanta komai ba iyaka dai abin
da na rike shi ne bayan rasuwar tashi ne nayi
wata irin jinya mai tsanani irin wanda ban taba
yi ba a rayuwata don sai da takai ma yayan tudu
ya dauke ni daga sasanmu ni da yara ya maida
mu sasanshi in da yaya Balki ke tafiyar mana da
mafi yawancin al'amuran sai ko Uwa.
A wannan lokacin komai ya sauya mun
duniya tayi min fadi na kara tabbatarwa kaina
29
da cewar bani da kowa in ban da yan yarannan
guda uku da suke manne dani har a halin rashin
lafiyar da nake ciki basa rabuwa dani ta sani a
gaba suke yi suyi ta kuka. Alhaji kam tun bayan
zuwan da yayi akayi arba'in din Baba ya kwashi
matanshi suka tafi ban sake sanya shi a idona
ba.
Har na soma jin sauki ina fitowa tsakar gida
ina dan taimakon yaya Balki da 'yan ayuka tun
tana hana ni har dai ta hakura ta barni.
Rannan ina kwance a daki da 'yan yara guda
uku da suke ta bacci yayin da ni kuma nake
kwance idona biyu saboda tunanin rayuwa, .
Baba nake tunawa da kalmominshi da yayi tayi
min musamman na karshen rayuwarshi wani
tunani yazo min cikin raina da wannan zaman
kadaici da nake yi ga wulakanci daga wurin
mutanen gida gore-gore da habaice-habaice
wuni nake yi a cikinsu, ga Alhajin ma yanzu
rabon da in sa shi a idona har na mance lissafi
me zan hana kawai in yazo in ce mishi ya kaini
wurin dangina sai kuma na tuna maganar Baba
nayi kuka har na gaji daga karshe dai na yanke
wa kaina hukuncin zama Jaruma da kuma bin
dukkan shawarwarin da Baba yayi ta bani. Don
haka washe gari da sassafe naje na gaida Yayan
tudu na shaida mishi cewar tunda naji sauki ina
30
so zan koma wajena, ya ce kin ji sauki tunda kin
mike daga kwanaya, amma ai ba ki warware ba
kin ganki kuwa kinga irin karewar da kika yi?
Na co ba komai ina so in koma can din ya ce to
babu laifi.
Ina gayawa yara zamu koma wurin mu suka
yi ta murna nan da nan muka gyarashi muka
koma ciki na kawar da kaina kan abin da ake yi
a gida ko ina ji ana magana ta ban nuna nasan
dani ake yi balle in tanka, na maida hankalina
wajen saye da sayarwa wanda dama na fara tun
Baba yana da rai, mutanen unguwa ma in zasu
sayar sai su kawo min in suna bukata ma su zo
wurina nema na maida dakin Baba da.dama ya
bani wajen tara kayayyakin da nake sayarwa ina
dan harkokina ga kuma 'yan dabbo bina da nake
kiwatawa wadanda suma babanne ya kafa min
tushensu sai dai kuma duk da hakan bana cikin
jin dadi zuciya ta a kuntace take kewa da
kadaici sun ishe ni.
Ana cikin haka rannan sai muka wayi gari da
safe Uwa ta dauki dusar shanu taje zata share
musu wurin ta zuba musu sai gata ta dawo da
gudu tana kuka tana fadin Umma zo ki gani, da
sauri nabi bayanta sai kawai na hango bijimina
babban a kwance an yanka shi daga nesa na kare
mishi kallo tausayinshi ya kama ni na juyo
31
kawai na dawo nazo naci gaba da aikina, ita
kuwa Uwa taje sashin yayan tudu ta fada, ya
shigo yayi min jaje ya kuma tambaye ni saidawa
za'ayi don a rage asara ko? Na ce mishi a'a a
rabar dashi kawai sadaka, su kuwa sauran
dabbobin a tasa su a gaba akai su kasuwa a
sayar, ya ce eh to kin yi dabara ba zan ce ki
barsu ba, don kar abin da ya samu sauran ma ya
same su, in banda yaya Balki ba wanda yayi min
jajen abin da ya faru, an dai basu sadakan nama
sun cinye, sai da aka fitar da dabbobin nan daga
wurin nan sai kuma na kara gane ashe suma
suna debe kewa ashe ba karamin sabo dasu nayi
ba a yanzu sai inga tamkar bani da aikin koma
ga kuma yara kullum maganar su ba ta wuce
Allah sarki shanunmu da yanzu suna nan da
munyi kaza da kaza.
Ba'a kwana talatin da faruwar wannan
al'amarin ba, rannan sai na farka cikin darea
firgice saboda ihun da nake jiwowa na gobara-
gobara, da sauri na dauki Babangida na goya nna
daure shi tamau a bayana, na dauki Junaidu na
kankame sannan na kama hannun Uwa na rike
don ban san ta inda wutar take ba, sai da muka
fito ne naga ashe dakin Baba ne yake cin wuta,
dakin da nake tara dukiyata. Muna tsaye muna
kallo dakin yayi kurmus sai dai maimakon
32
wutar ta tsaya anan abinka da jinkan ciyawa sai
da ta lamushe kusan rabin gidan, da kyar aka
samu aka tsaida ita.
Washe gari bayan an dan natsa yaya Balki
tazo min hira tana kara jajanta min abin da ya
farun, tana bani hakuri na ce mata ai ni tun
bayan mutuwar Baba ban sake ganin wani abin
da ya bata min rai ba, komai aka yi sai inga
wasa ne, wannan bai kai ayi bakin ciki dominshi
ba. Allah ya jikanshi ya saka mishi bisa rikon
amanarshi tace min amin.
Tun daga wannan lokacin na bar komai na
bar kowace irin sana'a don kuwa na gane hakan
zai iya jawo min kowane irin abu, shi kenan na
zama bana komai in na gama 'yan ayukana sai in
dauko 'yan littattafaina guda biyu da dama baba
yake koyar dani na Kawa'idi da Ahlari, inyi ta
karantawa in na kamo daga farko na kai karshe
inyi ta maimaitawa daga baya ma na shiga
koyawa yara. Wasa-wasa sai gashi mun sauke
kawa'idin da su min shiga Ahlari.
Muna nan a wurinmu rannan da daddarc sai
kawai naji muryar yayan tudu yana tashina,
jikina yana rawa na fito ya ce min taso yaran
nan ku dawo nan ku rinka kwana, na ce to na
kwaso yara nabi bayanshi zuwa dakin yaya
Balki, can ya maida mu. Washe gari da safe
kwaso
33
yayi min magana da cowar in yi hakuri in zauna
a nan don hankalinshi ya kasa kwanciya da
zaman nawa a can, na ce mish1 to.
wannan lokaci na zama wata irin abin
tausayi ban san menenc matsayina ba, babu Al
haji babu dalinshi, matanshi ma Sun daina
zuwa gida a shekara biyu da rasuwar baba ganin
da nayi mishi tunda akayi arba'in bai fi sau uku
ba, ga abubuwan da suke kewaye dani a gida
1rin mutanen da nake zaune dasu ga aiken da
yake yi min ma ya daina ga abin hannuna babu
ya kare don ma dai yayan tudu yana yi min
kokari to shima kuma ba mar shi bane ga kumna
iyali har mata uku da ya ya.
Muna wannan zama rannan kwatsam sai ga
Alhaji ya iso da yamma, cikin wata irin kwalliya
ta ban mamaki da burgewa, ana tayi mishi
oyoyo nn kuWa nayi maza na shige wani dan
daki na buya in ban da Uwa ta biyo ni ta kira ni
da ban san yanda za ayi in tito ba, na same shi a
dakin da aka sauke shi saboda umurnin da
yayan tudu yayi min 3a 1n e mu gaisa na Ce
mishi to, na tali tare da yaran dukansu ya daga
ido ya kallc ni ya rage fara'a ya ce yaya zaki zo
min da yara kuma bayan su na riga na gansu
Ban yi magana ba ya ce musu kuje gun yara
kuyi wasa, suka ce to suka fita. Na sassauta
34
murya na gaishe shi cikin ladabi ya amsa na
tambaye shi iyalinshi ban kara ba akan wannan
naja bakina nayi shiru, ya ce min yaya akwai
mas' ala ne haka naga gaba daya kin canza? Na
hadiye bacin ran da tambayar ta sanya ni na ce
mishi babu komai, ya ce to in babu komai ni
gobe zan koma dama zuwa nayi in ganku na ce
mishi to Allah ya kaimu na tashi na dawo daki
na zauna ina tunanin irin canjin da na gani a tare
da Alhaji, ya yi kyau yayi kwarjini bai bukatar
cewa ya samu daula don jikinshi ma ya riga ya
bayyana na kalli kaina naga yanda na zama na
fige nayi muzai-muzai in ba wanda yayi min
kyakkyawan sani ba sai yayi zaton shekaruna
sun zarce yanda suke bai bukatar komai a tare
dani bai sona ba ma zai lya nuna ni a yanzu ya
ce nima matarshi ce ba, to me zai hana ya kaini
wurin'yan uwana? Nayi kamar inyi mishi tuni
kan ina da 'yan uwa me zai hana ya kai musu ni
maimakon barina cikin nashi 'yan uwan da yake
yi, sai kuma na tuna kalaman na tuno shi a
hirarmu ta karshe yana cewa mahaifinki yana
sane da danginshi ya bani amanarki, don haka
ke din tawa ce kiyi hakurin zama a cikin 'yan
uwanki in hali ya samu sai kije ki gano su, don
sadar da zumunci. Hawaye suka zubo min a ido,
35
saboda tuna Baba da irin son da yake yi min da nayi.
Uwa ta shigo dakin da sauri tana murma,
"Umma wai kizo in ji Baba." Tamfar dai in ce
mata ba zani ba, sai kuma naga ba zan 1ya ba na
tashi na bi bayanta na sake shiga dakin da yake
cikin na durkusa na ce mishi, gani ya zuba min
ido yana kallona ya ce so nake in tambaye ki
Zuwaira, kin daina sona ne? Lokaci mai tsawo
baki ganni ba amma ki nuna min baki da wata
bukata game dani, na kuma tambaye ki damuwa
kin ce baki da ita, me kike nufi dani ko kuwa
kin zuba min ido ne kina jiran ganin sakamakon
da Baba ya ce miki zai same ni in har na zaluncee ki?"
Na ce mishi a'a, bana neman sakamako a
kanka ba ma kai ba da kake da matsayi mai
girma a kaina, duk wani wanda ya danganci
zuriyar baba bana neman sakamako a kanshi ko
da kuwa me yayi min, na yafe mishi zan kuma
ci gaba da yafe wa bayanin nawa yayi mishi
dadi ya ce to amma in haka ne me yasa ba ki
tambaye ni dalilin rashin zuwana ba? Na co
nasan ba zaka yi hakan da gangan ba.
Yayi murmushi ya ce na gode miki Zuwaira
da ba ki kullace ni ba, kika kuma zama ma
yafiya kan duk abin da ya same ki, bayan haka
36
ina so in tabbatar miki da cewar ban taba yin
wani abu da nufin in zalunce ki ba, ina kuma
son ki fiye da duk yanda kike zato ina son
hakurinki, ina son dabi'arki ta girmama wanda
yake gaba dake duk abin da kika ga nayi to na yi
shi ne bisa hakan ya zama min dole in har akwai
wani abin da yake bani tsoro a yanzu bai wuce
zaluntarki ba, don kullum ina tuna kalaman
Baba na įaddada min amanarki da zai bar min
wannan dadewa da kike gani ina yi bana zuwa
ba na kusa ne na tafi nema bana cikin kasa a
yanzu kuwa na gama shirya miki wurinki ke da
'ya'yanki don haka nazo ne in tafi dake.
Ban ce mishi komai ba har yayi zancen shi
ya gama na tashi na tafi nayi, kwanciyata washe
gari nazo zan gaishe sh1 sai na same su da yayan
tudu bayan na gaishe su zan tafi sai Alhaji ya ce
min ke Zuwaira! na ce mishi na'am, sai ya ce ga
dukiyarki yaya ya kawo min kudin shanunki da
ya sayar ya kuma juya miki su sun karu shi ne
na ce maimakon in karba ko zan bar mishi ne ya
ci gaba da juya miki ko? Na ce mishi to, na tashi
na tafi.
Washe gari ne kawai muka kamo hanya don
ban tsaya kintsa komai ba, Alhaji ya ce ni da
yara ne kawai zamu taho bai bukatar mu dauki
37
komai yaya Balki da wasu mata biyu cikin
matan yayan Alhaji suka yi mana rakiya.
Kai tsaye sabon gida Alhaji ya kaimu,
tabkeken gida mai manya-manyan dakuna ciki
da falo da akayi matukar kawatawa da kaya shi
ne nawa ga wani dakin a kusa da nawan shi ne
na Uwa can gefe wasu dakuna guda biyu daya
wai na Junaidu da Babangida, dayan kuwa na
yaran da zai debo mun, daya kuma wani wuri da
aka kawata da kuma biyu da falo da bayan gida
nan ne wai nashi, ni da kaina mamaki ne ya
kama ni baile kuma wadanda suka yi min
rakiya.
Kwana uku 'yan rakiyata suka yi suka tafi, da
za su tafi sai na ce wa yaya Balki in sun koma ta
bude dakina ta kwashe duk kayan da suke ciki
na bata tayi ta murna.
Bayan tafiyarsu ina zaune a falo na tasa 'yan
yara a gaba zuciyata cike da tunani iri-iri sai ga
Alhaji ya shigo, Karama da Maryam suna biye
dashi sunyi kitika-kitika sai wani juyi suke yi
suna sheki na karbe su hannu bibiyu muka gaisa
muka shiga hira sai dai da Maryam kawai don
kuwa ita Karama bata iya hadiye bacin ranta ba
nan take a gabana ta ce mishi dama ita kadaice
zata zauna anan'? Ya ce mata eh, zata ai tayi
shiru da zasu tafi na diban musu daddawa da
38
kukar da nazo da su daga gida, na basu tafiyarsu
da kwana uku sai ga Maryam tazo min wuni, ta
taya ni muka kara kintsa wuri, yayi kyau sOsai
sai da na gama abincin dare taci sannan aka zo
aka dauke ta ta tafi.
Matan abokan Alhaji suka yi ta zuwa yi min
sannu da zuwa saboda ya basu labarin
uwargidanshi tazo a wannan lokacin ne muka so
juna ni da Hajiya Hauwa, alhalin da can tana
mu'amallah da su Karama, a wannan loka cin
Karama tayi matukar tayar da hankalinta kan
dawowa na da kuma ware ni da Alhaji yayi ni
kadai ga kuma irin kawatuwan da yayi wa gidan
da ya sanya min kan wannan abin har sau biyu
tayi yaji ta tafi gida, zuwan farko yaje sai dai bai
yarda da cewar da akayi ya hadamu wuri daya
ba ya ce ai shi ba wannan lokacin ne ya fara
raba mu ba tunda ya dade da debo su mu kuma
ya bar mu a kauye me yasa tun wannan lokacin
bata yi maganar ya hadamu a wancan lokacin ba
sai yanzu? Karama bata gama wastsakewa daga
wannan lamarin ba sai labari yaje mata cewar
zan tafi aikin hajji ni da yayan tudu Alhaji ya
biya mana in na tsaya cewa Alhaji ya jiyar dani
dadi a wannan lokacin ya nuna min gata ya
karrama ni to na bata bakina ne kawai don ba
zai yiwu in fadi komai ba, abu daya dai da zan
39
gaya miki shine, nan da nan na goge nayi fes na
zama matar birni nayi kyau irin wanda ban taba
yi ba, gani dai dama mai tsabta ce kwarai to
gani kuma na shiga daula na kuma yi dace na
gamu da mata ma'abuta ado da iya kwalliya, irin
su Hauwa. Kuruciyata ta dawo danya sharaf,
fatata tayi matukar yin kyau har mutane da
yawa ke zaton wai su Karama sun gime ni.
Ina nan zaune da su Uwa da su gwanin
sha'awa babu wanda yasan bani na haife su ba,
saboda babu alamar da zata nuna hakan.
Tunda aka fadi zan tafi aikin hajji Maryam
tazo min murna, Karama kuwa sai da Alhaji ya
taso ta a dalilin kawo su dukansu da yayi shine tazo.
Nima bayan dawowana daga katagun na
shirya naje musu wuni ni da yara na taf
maimakon Karama ta sauke ni a dakinta a
matsayinta na babba sai taki ta barni a tsakar
gida sai Maryam ce ta matsa na shiga dakinta na
dawo gida ina tunanin mahakurci dai shine
mawadaci don kuwa daga kyan gida zuwa tsarin
dakunan nafi su morewa gasu kuma su su biyu a
can sun kuma kasa daidaita kansu su zauna
lafiya.
Rannan ina gida da yamma ni kadai saboda
yaran gaba daya sun tafi Islamiya sai ga Alhaji
40
ya shigo ranshi a bace. Cikin natsuwa na
tambaye shi abin da ya bata mishi rai, ya ce
haba Zuwairah, ace mutanen unguwa suna ganin
mutuncina amma kullum burinsu Maryam bai
wuce su tozarta ni ba, kowane lokaci gidana
yana cikin hayaniya wai yau har makwabta suna
shigowa rabon fada? Nayi maza na ce assha,
abu bai yi kyau ba sai kayi hakuri, ya ce a'a yau
kam na gaji na bar musu gidan suje suci kansu,
zasu dade basu sani a ido ba.
Na sake sassauta murya na ce, "kayi hakuri
kar ka yi abin da za'a zo maida magana ace
kaima ga naka laifin, tsawon lokaci ina
rarrashinshi kafin ya hakura ya tafi bayan ya ci
abincin dare.
Kwana biyu bayan naje gidan kai tsaye dakin
Maryam na shiga bayan mun gaisa da Karama a
tsakar gida na kalli Maryam na ce mata ba zan
ci komai ba yau a dakinki dama kin tattara kin
kwashe, ta ce haba-haba ai sai in yi fushi, na ce
to kiyi fushin mana Maryam sai me, tunda ke
kullum baki da aiki sai na batawa mijinki rai,
ribar me kika ci a hakan da kike yi? Ta soma
zata bani labarin Karama na ce mata kece za ki
bani labarinta ko ni ce zan baki? Ta ce min to
kiyi hakuri daga yau kuma ba zan sake kula ta
ba ko me zata yi tunda dai nasan bata isa ta rufe
41
ni da duka ba, tund atasan ba kwashewa kalau
zata yi ba in tayi hakan.
Na ce to da yafi miki mutunci a wurin
mijinki dama mutanen unguwa ga baki daya sai
ki same shi ki bashi hakuri kar kuma ki yarda ya
sake fushi dake saboda ita ta ce min to daga
wannan lokaci Maryam ta daina fadan baki da
Karama sai dai kuma zaman babu dadi.
Yarda da shawarata da Maryam tayi sai naji
dadi na dauke ta tamfar kanwa in naga tayi ba
daidai ba ko in mijinsu ya gaya min laifinsu sai
in gaya mata ta kiyaye yi mishi hakan duk abin
da na hana ta kuma tana bari in kuma tana da
damuwa zata zo ta gaya min in bata shawara
haka kawai kuma zata shirya tazo min wuni don
haka sai muka kulle sosai ni da ita tana bani
girma nima ina mata adalci ko wani abu na gani
ya bani sha'awa in zan saya tare nake saya mana
in ma tayi min kukan wani abu zan kawo kudi
in bata in ce taje tayi donni ban yarda na zauna
bana sana'a ba babu abin da bana sayarwa in ban
da tsiya na riki Maryam 'yar uwa sosai saboda
dalilai guda biyu na farko ta yarda dani tana
amfani da duk shawarar da na bata bayan haka
kuma ita ce mahaifiyar Babangida tunda kuwa
ina son Babangida babu dalilin da zai su in ki
42
Uwarshi ko da rashin kirki take min balle tana
ganin girmana.
Nayi sabo da mutane sosai saboda sana'ata
gani kuma da yara wadanda abokansu na
makaranta ke biyo su gida don wasa ni kuma
duk yaron da ya shigo ban barin shi ya fita haka
kawai sai na kawo dan abin tsarabar yara na
bashi, nan da nan sai muka yi fice gidansu
Junaidu, Junaidu da Babangida ne suka yi fice
sosai saboda ita Uwa bata fita ko ina bata kuma
dawasu kawaye kowane lokac1 muna tare a
gida.
Na dawo aikin hajji da dukiya mai yawa
saboda dalilai biyu, na farko dai nayi aikin
hajjin ne a shekarar da dala take matsayin
kwabo tamanin da biyar wato sule takwas da sisi
don haka kudaden da Alhaji ya ajiye min sai
suka yi min auki sosai, gashi kuma ya hada ni
da abokanshi guda biyu, Alhaji na maibindiga
mijinsu Hauwa ga kuma Baba Wulle wadanda
su kuma suka tafi da matansu a wannan lokacin
ne muka kulle sosai da Hauwa na