Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fara mgn don so take Innah ta jisu tunda ta fahimci Rukayyat na tsoron Innar taji takuma gano duk tsiyar da takewa Bashir Innah bata saniba dan da ta d'au mataki cikin tsareta da ido tace.

"Rukayyat kiji tsoron Allah,
ki tuba ki komawa Allah ki sani abin da kikeyi kina sabawa dokokin Allah kisa a ranki shi aure ibadane ki d'aukeshi a matsayin bautar ubangiji ki cirewa ranki cewa shi Aure sharholi ce ki dena d'aukan gidan Aure wurin shanawa ne kisa a ranki aljannarki kike farau towa,
Rukayyat wlh ki nemi gafarar mijin ki tun kan lkcin ya k'ure miki kinfi kowa sanin kina cutar da zuciyar mijinki da mugayen kala manki ,
Shin wai Rukayyat ina ilimin ki ya tafi shin kin manta ita wannan duniyar ba komai cikin ta sai rud'u.
Shin ko
Mataa wul hayat ke rud'an ki?,
toh inma shine ki sani rayuwar k'ele-k'elen duniyar nan ba ma dauwami bane ki sani k'ele -k'elen k'alilan ne,
kin tuna cewa dama ita wuta an kewaye tane da ababen k'awa da more rayuwa da sharholiya,
ita kuma aljannah an kewaye tane da abin da rai zaike ganin takura ne,
Rukayyat shi haram sauk'in aikata wane gareshi shiko hakuri rahama ne a rayuwar duniya data k'iyama".

Hannu tasa ta dafa kafad'ar Rukayyat cikin sanyi tace.
" Rukayyat ko kin mata gidan Annabin muma Abin koyinmu akwai lkcin rayuwa tai musu tsanani har ta kai saida akayi kwana 3 basu d'aura tukunyar girkiba,
kinyi karatu kinsan yadda a wannan lkcin matan sa d'in suke hakuri da godewa Allah da wannan jarraba war,
Amman wai ke da bakiyi koda wuni d'aya bakiyi girkiba wai a hakan kike gaza hakuri da tausayawa ga mijin ki,
Shin da kike cewa batun kayan sallah da k'ele k'ele shin ki tuna matan Annabinmu abin koyinmu a lkcin da su suke ganin a matsaya yinsu na matan shugaba amman basu da kayayyakin k'awa na rayuwa har suka tinkari Annabinmu da buk'atun su a lkcin da suka buk'aci kayan duniya na jin dad'i,
suka saka shi a gaba kan dole sai ya samo musu,
da ranshi ya baci, sai yayi musu yaji na tsawon wata d'aya watau kwanaki ashirin da tara 29, Amman saboda halin mata sai a hankali yana shigowa gida sai ya fara had'uwa da Nana Aisha (A.S), tana ganin shi sai tace.
"Ba kace wata d'aya zakayi ba ai kwana 29 ne yau,
alhalin kuma a ranta tayi kewarsa fa tana Allah
Allah ya dawo, shi kuma lokacin ya k'osa ya dawo wajen matan shi shima ,
sai kuma ga abinda tayi mai welcome da shi. sai yace "mata ai kwana watan musulunci 29 ne sai tace toh.

Daga baya kuma sai Allah ya sauk'ar da Ayoyi akan cewa idon suna son jin dad'in duniya ne toh su fad'awa Annabi (S.A.W) d'in zai sake su saki kekkyawa suje su sami abinda sukeso, idon kuwa sun zabi Manson Allah (S.A.W) suyi hakurin zama a ko wanne hali da shi,
toh lallai Allah ya tanadar musu lada ninki biyu fiye da sauran matan duniya gaba d'aya, sa' sannan kuma zai basu fiyayyen al'jannah tare manzon shi.
sai sukace sun zabi Allah da manzon shi kuma kafin hakan ma Allah yace in sun zabi rabuwa da Annabin toh Allah zai musanya mishi da wasu matan da suka fisu a komai, wad'anda kuma bazasu sakashi ciwon kai ba.
a cikin suratul tahreem".

A hankali Rukayyat ta rink'a siyayar da hawaye a fuskarta cikin tsoron da nadamar abin da tayi tayiwa mijin ta sosai taji tsoro ya rufeta ya zatayi da hak'k'in mijin ta da bata mai da tayi tayi shin in tajawa kanta saki koya makomar ta zata kasan ce shi kuwa ta tabbata Allah zai musanya mai da mai rufa mai asiri ko dan hakuri da yayi tayi da ita,
Cikin kula ta rik'e hannun Aysha tare da cewa "ngd Aysha Allah ya saka da alkhairi ngd da tuna tarwa".
kai ta jinji cikin sanyi tace "ba komai Rukayyat yiwa kaine"
Cikin mmk suka d'ago Kansu suna kallon Innah da ta shigo tare da cewa..


By Garkuwar Fulani
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*A TAUSAYAWA JUNA* pg 1⃣6⃣to2⃣0⃣ Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*Ramadan kareeeeeeeeem*


Cikin sanyi Innah ta zauna gefen su tare da cewa.
"Hak'ik'a Aysha kin cika k'awa ta gari mai tunatar wa tabbas ke abin son kiyi k'awance ga duk mai hali irin na Rukayyat dan zaki tunasar da ita hak'ik'a naji dad'in kasan cewarki tare da y'ata da surkata".
Sai ta kuma juyawa gun Maryam da tayi k'asa da kanta cikin kula da k'aunar matar d'an nata tace.
" Maryama Allah ya miki albarka rabbi ya baki ladan hakurin da kikeyi,
kuma Insha Allah Umar kam zai sauya miki insha Allah zanmi shi nasiha zan kuma nusarda dashi zan fahimtar dashi illar rashin tausayawarsa gareki".
Cikin sanyi tace.
"Innah kar ayi mai fad'a zai d'auka k'ararsa na kawo".
Murmushi tayi tare da juyawa gun Rukayyat cikin had'e fuska tace.
" kinga mata nagari sune masu hakuri da mazan su a cikin ko wanne yanayin matukar bai sama addininmu ba,
kinga duk yadda yake mata tana gudun bacin ransa".

Cikin sanyi tace "Innah Insha Allah nima zan kula zan nemi gafarar Abban Salim hak'ik'a nasan yayi hakuri dani da halina".

Innah ce taci gaba da cewa .
" Hak'ik'a ya zama wajibi a garemu mata mu tausayawa mazanmu domin suna buk'atar tausayawar mu garesu sabida rayuwa ta juya komai ya canza Allah ya kawomu lkcin da tsada tai mana kaka gida sai dai muyi ta Addu'a Allah ya kawo mana d'auki dan wannan tsad'a ba mutun d'aya ta shafaba ta shafi kowa,
Kuma wannan tsada ba laifin kowa bane muk'addari ne jarrabawa ce mu dage mu samu muci wannan jarabawah,
sannan mu godewa Allah da ya bamu zaman lfy a kasar dan zama lfy yafi zama d'an sarki,
Mata musa hakuri a ranmu muke godewa mazanmu da duk abinda sukayi mana komai k'ank'antar sa,
zanin sallah ba wajibi bane sai Super was ba kuma ba sai Holland ba dan super tafi k'arfin mai k'aramin k'arfi abin dubu 25 ya koma dubu 42 yayin da duk sauran zannuwan suka ninka kud'insu,
shin maza suji da ciyar damu ko da burukan rayuwar mu abincin kanshi sai hamdala ba batun araha kam daga kan maggin da da d'ari 200 zuwa yanzu yaje har d'ari 400 sauran kayan masaru finma komai yayi wuta bare aje ga kayan yaran da sai dai hamdala babban gatan da Allah ya mana dai mun samu zaman lfy,
dako da arahar Amman baka da konciyar hankali da zaka samu nitsuwa ana rayuwa ne cikin tsoron da firgici ga dukiyar da abin more rayuwar amman ba nitsuwar da konciyar hankalin da za'a mori arahar haka ko wanne shekara da yadda zai zoma bani 'Adam mu godewa Allah mu daina jingina tsadae da muke ciki akan wani abokin halitta kamar mu wanda bai da damar sau k'ak'awa ko tsanan tawa mukoma ga Allah mu dena al'k'anta tsadar damuke ciki akan shugaban mu
Baba Buhara ba Allah bane ba kuma ba manzon Allah baneba kuma ba kumfa yakun neba shima Bawane kamar kowa baida ikon sauk'ak'awa ko tsanan tawa".

Sosai tai tamusu nasiha mai rasa jiki daga bisani tajuya gun Aysha tai ta mata Addu'a sannan ta baiwa Maryam hakuri ta kuma tasa Rukayyat a gaba tai ta mata nasiha.
sannan suka fito parlon suna fita Aysha tace ita kam zata tafi aikin yamma najiran ta suna cikin haka Bashir yazo d'au kar Rukayyat ganin Aysha zata fita sai suka tafi tare ya sauk'eta a k'ofar gidan ta sannan ya juya da Rukayyat kuma ya nufi gida da ita,
tun an cikin mota Bashir ido ya zuba mata ganin duk jikinta a mace ga fuskarta data nuna alamar tayi kuka gaba d'aya sai abin ya dameshi cikin kula yace.
"Baby meke damun ki? ko azumin ne ke wahal dake?".
jiki a mace ta tsura mai ido tana mmkin yadda Bashir ke tausaya mata Amman ita ta kasa mai uzuri a rayuwar su,
shiko ganin tayi shiru yasa d'aya sauk'eta ma bai fitaba sai bin bayan ta yayi suna shiga parlon ya kalleta cikin sanyi yace.
" Baki da lfy ko?"
kai ta girgiza alamar a,a
Ayijar zuciya ya sauk'e tare da cewa .
"OK ki konta ki huta toh bari na shiga kitchen na fara mana aikin kafin su Salima su taso islamiya na d'auko su".
yana kaiwa nan ya nufi kitchen ita kam sai binshi da ido tayi cikin mutuwar jiki tana son mishi mgn da Bashir hakuri da nemar yafiyar sa sai kunya ta hanata a haka har zuwa dare.

Bayan sun gama komai har Bashir ya konta itako tana gefen shi tana zaune mik'ewa yayi cikin sanyi yace.
" Na manta abu a moto bari na d'auko".
Har ya mik'e sai ya kuma zama jin ta rik'o hannushi cikin sanyi da kunya murya a raunane tace.
"Abban Salim ka gafar ceni kamin afuwa hak'ik'a nasan na kasance mai b'atama da kalamai na masu zafi da d'aci,
Hamma Bashir ina tsoron me zancewa maliccina in namutu da hak'k'in ka,
ka yafe min hak'ik'a na gane kuskure na na kasa tawausaya ma bare nama uzuri".

Sai ta kuma fad'a jikinshi tare da sakin kukan nadama,
cikin sanyi da jin dad'i ya tsura mata ido tare da sauk'e ajiyar zuciya yace.
" Share hawayen ki matata ni dama ban rik'eki ba na yafe miki duniya da lahira Allah ya miki albarka Baby na".

Haka suka rink'a farin ciki da samun nishad'i cikin sauri Bashir ya fice yana "bari kiga wani abu"

Bayan ya dawo ne ya dire kayan hannushi kayan yaran masu kyau da tsada kala uku-uku na mata da maza sai turame 2da leshi 1 sai shadda mai kyau kala 3 sai sauran tarka cen yara su takal ma yan kunne gyale da dai sauran su cikin mmk Rukayyat ta bishi da ido,
Shi kuma fuska a sake ganin ya samu lfy a gun matar tasa yace.
"Ga kayan yaranki Hajia kema ga naji nima ga nawa sannan naki zaki d'inka da Salima niko zan d'inka da salim kinga d'en sun samu kala shida -shida ko?".

Kai ta sunkuyar cikin jin kunya da nadama ta fad'a gareshi gashi da batayi mgn bama da ba taji kunya a banza ba.

Haka rayuwa ta koma musu cikin wadatar zuciya da tausayawa juna da yiwa juna uzuri shi kam Bashir Allah ya Bashir ladan hakurin shi.....

Maryam ce konce tana baccin ta cikin sanyi taji Umar na Jan yatsun k'afar ta a hankali ta bud'e ido tana kallonshi shiko murmushi yayi cikin sanyi yace.
" Baby tashi muyi sahur kada mu makara".
ido ta lumshe tare da cewa.
"Ni bacci nake ji Ya Umar kuma nagaji".
da sauri ya mik'e tare da cewa bari na kawo miki abin cin nasan kin gaji kina k'ok'ari ga Ramadan ga aiyuka sun k'aru".

Abin cin ya kawo har gaban ta sannan ya had'a mata tea da kanshi ya bata.
Ita kam Maryam Allah take godewa d'aya canza mata halin mijin ta.


Yusuf da Aysha ko rayuwa ta kara musu dad'i cikin fahim tar juna..


*Alhamdulillah* *Alhamdulillah*
*Alhamdulillah ala kulli halin*

~Abin da nai dai-dai Allah ya had'amu kan ladan abinda nai kuskure Allahu ya gafar tamin~

Wannan d'an guntun lbrin k'agene banyi dan wasu ba duk Wanda na batawa ta/ya gafar ceni.

Ngd wannan lbrin bawai na soyeyya bane rayuwa mu ta yau na d'an duba.

Sai mun had'e a littafi na na gaba.

*masoya na ina k'aunarku a duk inda kuke Garkuwa takuce* 😍😘


By Garkuwar Fulani

ο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»ΏCopied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)

WHATSAPP NO:
+2347039625239


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment