Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

buɗe shagonta tana shiga jazz da shi da pretty suka shigo kallon su tayi tace


'' Allah ya rufa muku asiri baku daki gurbi ba ban dade da zama ba..,

zama sukai jazz tace

'' lallai kam jiya nai ta kiran wayar ki switch up me ya faru bayan mu gama tsara guri har 2:49 ina club...,

BAƘIN SHAFI

oum yasmeen

EPISODE 3

Previous to the last page

'' lallai kam jiya nai ta kiran wayar ki switch up me ya faru bayan mu gama tsara guri har 2:49 ina club...,

Continue

ajiyar zuciya ta sauke tace '' wayata ce ta lallace..,

fito da syrup pretty tayi ta buɗe tace '' Allah ya kiyaye gaba..,

amin ya Allah amma dan Allah kar ki sha ba zai yiwu ba customer's su zo min ba ana kallon ki ki ta tun ɓele..
haba nasreen ya kike mana yawa ne yanzu ni nake tunɓelen yawa wata akuya ko tinkiya

Pretty ta faɗa tana kai Syrup bakin ta tunda ta saka shi tas sai da ta shaye shi ta wurlar da kwalbar fashewa tayi da sauri nasreen tace

'' wallahi sai kin share min anya kuwa ina cikin nutsuwar ki..?,

ina fa take cikin nutsuwar ta sunyi faɗa da bash

Jazz ya fada yana dariya

tashi nasreeen tayi ta cire mayafinta tace '' ya kake mata dariya..yau dara fa ba dad'i wallahi tama yi kokari da ba faɗi ba an kwashe ta..,

Nasreen kenan ya ali yaga ali fa akai ya fito daga dakin hotel ta fito ina abatun damuwa shine fa har da marin budurwar indai takaice miki labari kaca kaca akai har sai da yan sanda suka shiga cikin lamarin yanzu bashi ba ita shine fa ta shiga cikin wani hali

to mene abin damuwa tunda ke kin aikata shima ya aikata ga ani na gaskiya ba abin daga hankali ko ki damu

baza ki gane ba wai mutumin nan fa yan sanda ya faɗa suyi mana tsakani da shi kin ji fa wani rainin hankali

tashi tayi ta zauna kusa da jazz ta kwashe da dariya shima dariyar yake yace

'' wallahi ban taɓa ganin original yan iska ba irin bash da pretty yau ya saba kai ta gurin yan sanda nifa gani nake kamar fa ya raina su wallahi..,

buɗe fridge tayi ta ɗauko lemoka ta miƙa musu itama ta buɗe tana cewa gaskiya nima ban taɓa ganin haka ba kar kai mamaki dan da wani watan su koma su jone

wallahi kin kai da nisa ki basu nan da zuwa sati ki gani duk yadda kike tunanin su to wallahi sun wuce gurin cewar jazz yana shan lemo

ita dai pretty tayi shiru domin ba a cikin hayyacinta take ba dan ma dai Allah ya rufa asiri bata surutai beb yau fa naga tsohon dan iskan nan sabeer ke kinga kallon da ya jefe ni da shi...kin fa cool esay ce take faɗamin ya fasa auren ki yanzu maganar ake tayi a media

da sauri ta ɗago lemon da ta kurɓa kasa haɗewa tayi ta furzar dauko wayar sa yayi yace '' kalli..,

da sauri ta karɓa idan wata futsararriyar yar tiktok sanye da towel ta riƙe brush take cewa

Update update jama'a har zan shiga wanka naji wannan labari nace ba zan bari ta wuce ba tare da na faɗa muku ba asirin dai NASREEN MAI TANGARAN ya tonu ana ƙoƙarin daura auren ta miji yace ya fasa saboda yar iska ce akwai video ta duk me so ya je internet yayi searching wannan account din saboda gudun yi min blocking account Dina Zan dora muku anan

idanuwanta ne suka ƙada sukai ja sabeer ya gama cutar ta tsakanin ta dashi saidai Allah ya saka mata wayar ta ce tayi ringing da sauri ta dauki jaka ta buɗe ta dauko ganin sunan baffa rado rado gaban ta ne ya waɗi hannun ta na rawa ta dauka muryar ta na rawa tayi sallama a wannan karon ba be amsa ba daga jin muryar sa yana cikin tsananin baƙin ciki yace

''Duk inda kike ki zo parlour ina son ganin ki..,

jin sauti kamar ya kashe ta kalle wayar kallon jazz tayi tace

'' su mary za su zo yau naga ba su zo da wuri ba zan je gida ana son gani na..,

Okay ba damuwa sai kin dawo ɗaukan jakarta tayi da key ta fita cikin sauri ta buɗe motar ta ta shiga gudu ta dinga sharadawa har ta isa gida fitowa tayi ta fara knocking gate din

tana maida hannunta za ta ƙara bugawa me gadi ya buɗe shiga tayi yana mata magana ma da yake hankalinta ba akan sa yake ba har ta isa part din baffa tana tunani bata san me ya saka sa kiranta ba shiga tayi bakinta dauke da sallama

gabanta ne ya waɗi ganin daddy abbey abban yaya uncle Yusuf jikinta ne ya ƙara sanyi ta ƙarasa zama tayi wani kallo baffa ya watsa mata tare da miƙa mata waya bata san me yake nufi da haka ba hannunta na rawa ta amsa ɗagowa tayi suka hada ido da Altab sai a lokacin ta fahimci wa ya wura wutar kallar wayar tayi gaban tane ya waɗi ganin akan a ke maganar amma duk wanda ya tsaya yayiwa...

Video kyakkyawar fahimta ba ita bace ba ɗagowa tayi tace

'' yarfen yan media ne wallahi bani bace ko daban ba kunyar mutane ko dan kunyar Ubangiji na bazan so na aikata abin da zan zo nayi dana sani ba wallahi masu editing ne suka haɗa wannan baƙin shafi suka so su yi min amma kai wa vedio kallo na tsanaki bazan so na zubar da mutuncin gidan nan...,

Rufe min baki daman ke baƙin ki baya mutuwa to daga yau kune yayana ku sheda shima zan kirawo mahaifinta na sheda mai na cire hannuna akan ta ke Khadijah kema ban yarda ko kwayar shinkafa ki bata ba tun da bin da take kenan ta ci da kanta...

tana so ta ƙara maimaita mana abin da ya faru shekarun baya idan shekarun baya na iya ɗaukan tension din abin da ya faru to a wannan karon ba zan iya dauka ba kamar yadda na zare hannu akan ta kuma ku zare rayuwar duniya darasi ce wata ran zata koya mata darasi wanda zai zauna a kanta har abada tunda yanzu darasin da Ubangiji ya nuna mata be mata ba har taje ta ƙara wani abun

Baffa kai hakuri idan hankali ya gushe tunani ke dawo da shi be kamata mu zuba mata ido mudai ci gaba da yi da baki da kuma addu'a har Allah ya dawo da ita kan tafarki

Cewar dada

Wani kallo yayi mata ya ɗauke kai ya Khalil ne yace

"Baffa wallahi nasreen baza ta taɓa aikata haka ba kawai dai abin da nasani tana tare da mutane nan banza..ni zan aure ta..,

wallahi ban yarda ba ai daman idan ka ga kare na shinshina takalmi ɗauka zai yi to wallahi ban yarda ba wata kila ma yanzu haka ma wata kila tana ɗauke da cutar kanjamau..

Cewar mamy tana wura hanci shaf idanuwanta sun rufe ashe harda man tan gidan aka haɗa taron

ƙasa tayi da kai tace

'' ko baki faɗi haka ba zan taɓa auran sa ba ya khalil na gode da irin karamcin ka a gare ni...,

Cikin baƙin abba yace '' futsararriya ana magana kina mai da wa karya tayi ba ta hanyar ake samun cutar ba wallahi kin zame mana baƙar kadara...,

ko ganin gaban ta bata yi fita tayi bata tsaya ko ina ba sai a wajejen motar ta bude wa tayi ta shiga ashe ya khalil ya biyo ta ganin yana ƙoƙarin tsai da ita ta fisgeta yau zata aikata abin da kowa yake fatan aikatawa yau zata sama duk abin da suke cewa tana yi

basu da fahimta ne taya zasu ga wannan video suce ita ce a gaban wani joint ta faka ta fito shiga tayi wajensa ta zauna a gaban me sai da wine tana zuwa ya jera mata kwalba biyar ya buɗe wata ya zuba mata a glass cup ɗauka tayi har ta kai baƙin ta sai kuma tunanin ta da ya gushe ya dawo a hankali ta furta

Ya ayyuhalladhina amanu innal khamra wal maysira wal ansaba wal azlamu rijsun min 'amali shaytani..,

sauke wa tayi ta miƙa mai ATM ya cire kuɗin wacce ya fasa mata ta fito daga gurin jikin'ta na rawa cin karo tayi da ya khalil cikin rawar baki yace

'' nasreen daman kina shan giya...? Ina ilimin ki da tunanin ki yake me zata amfanar da ke abin da Ubangiji ya hana shi kike yi wallahi a yanzu kin fara saka min shakku akan ki..,

kai ta girgiza tace

'' I went because I drank, but one time God brought back my thoughts that I didn't drink..,

wani kallon rainin hankali yayi mata sannan ya juya batare da yace komai ba ya shiga motar sa cikin sauri ta ƙarasa amma tuni ya ja ya tafi shiga tayi cikin motar ta ko gabanta bata iya gani

a da tayi niyar daukan mataki akan wa'yanda sukai mata wannan abu a yanzu kowa da kowa ya zare hannunsa a kanta komai ta fice mata a rai tana fatan Allah ya ɗauki ranta ta huta daman maganar uwa da uba ba a maganar su suna can wata duniya ma banbanta suna can suna rayuwa successful ba wata damuwa ita dai sun ruga sun cutar da ita sun haifeta ta hanyar da bata kamata ba gashi nan rayuwa sai watan gaririya take da ita..

a hankali ta fara tafiya cikin gushewar hankali ji tayi ta ci karo da wani abu ɗaga nan bata ƙara sanin inda take ba

gashi titin nasrawa JRA ne ba mutane sosai mota ma zuwa take fit ta wuce tamkar walkiya raka raka gaban motar yayi kanta ya bugu da glass din taka ya fashe

BOMFAI JAR....

Sosai suka shiga harkar idimar abinci saboda masu kawo amarya suna kan hanya adda asma ce ta ajiye flask din hannunta tace

''maman iffa dan Allah kinga dawowar nasreen wallahi tun dazu zuciya ta ƙasa nutsuwa da fitar da tayi bata cikin hayyacin ta be kamata a barta ta fita a wannan lokacin ba duk kuwa irin laifin da ta aikata a wannan karon baffa ya nuna tsani da yawa wallahi ban taɓa zaton zai yi haka ba...,

to ke mece damuwar ki ina cewa iyayenta ma sun watsar da ita kina ga dan tashin nuna mahimmancin auren yar su ba wanda ya zo a cikin su gwara shi abban sufwan ma ya turo da kuɗi mahaifiyarta fa wa yasan inda take tunda iyayenta suka kawo ta suka wuce Cameroon sun ƙara waiwayar ta dan haka ba ruwanki da duk wata sabgarta ai daman buri yayi kama da mutum ke kinga uban shagon da ta bude a zooroad ta fake da bashin baki taci ubanta ne ya bata kudin da ta bude idan ba karuwanci take ba

innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un kinga zato zunubi ne wallahi ta nuna min komai yanzu ma ta kusan biyan su

dariya dukkan su sukai maman iffa tace

'' lallai ta mai da ke wata bita can yanzu mene ba ayi fake domin ta rufe mutane abokin dan iska Dan iska ne wallahi ga mutanen da take yawo da su baki ga uban birthday din da tayi ba ko ina shi kaɗai wallahi ya ci a zarge ta nifa mamy tayi min dai-dai da tace danta bazai aur ta ba ko nice abin da zanyi kenan yar iska kawai sai aikin girman kai..,

Maman arfa tace

'' ai wallahi gwara da suka budewa shegiya aiki yau ma naji ance za aje a kwaso kayan da aka jera a gidan da za akaita sun dauki kayan lefen su ma...,

kai adda asma ta girgiza ta fita yan kawi amarya ne suka zo da uwar gararsu bayan an Kaita gurin su Dada suka bada amanarta sannan suka kaita gidan ta gaba da su sosai..

sai satin gidan nata suka ahaka taro ya watsai sai rufaida da ƙawayenta sai washe baki take amma ƙasan ranta , ta kasa nutsuwa da kwanciyar hankali zare jikinta tayi daga na cikin kawayenta ta shiga wani daki ta murza key dauko wayar ta tayi bugu ɗaya aka ɗaga ƙasa ƙasa tayi da muryar ta, tace

'' wallahi anty tsoro nake karfa ya gane..,

saurarwa tayi domin jin me aunty nata zata ce ajiyar zuciya ta sauke tace

'' duk abin da kika ce insha Allahu zan kiyaye amma wallahi duk randa ya gane a kwai matsala aunty..,
da hallacan rufewa mutane baki ke da kanki kikewa kanki mugun fata kinga sai an jima sauran kuma ki ƙiyin abinda na saka ki wallahi ke ta dama ba ni ba kinsan irin kudin da na ɓatar akan auren nan ita kanta babar tasa, zata shiga uku mudai gama da shi ita duk me sauki ce

Insha Allahu aunty zan kiyaye

karma ki kiyaye tana gama faɗar haka ta kashe wayar ta mai da wayar ta tayi inda ta ciro ta ta gyara kanta ta fito yauwa tun ɗazu nake neman ki sara ta faɗa tana kunna turaren wuta a bonner

dafa kanta tayi tace '' na dan shiga can daƙin..nayi waya hayaniyar ku ba zata bari naji komai..ba,

dariya suka saka sara tace

'' amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida kedai faɗi gaskiya ko kin matsu muyi gaba ango ya shigo..?,

tura ɗauro gaban goshi tayi tace

'' ku kwana mana ni me ce damuwata...,

wallahi karya kike kina da damuwa ke ɗin ni wallahi nayi mamaki ma da har aka fara bakin nan cikin sauri rufaida ta tari numfashin Maryam tace

'' haba dan Allah ku dinga sanin zancen da zaku yi yanzu me ne abin yin maganar nan anan salon wani yaji kamar baki san komai ba..,

dariya sarah tayi tace

'' kura da fatar akuya wahainiya me canza siffa an zaton wuta a maƙera sai a ka ganta a masaƙa...,

ke yi shiru kamar knocking naji ana yi ko

gaskiya kamar shi ake yi koma ɗaki wata kila yan uwansa ne mu zamu tare su da sauri ta koma har tana tuntuɓe buɗe kofa sara tayi aunty lubna da aunty Aisha su suka shigo suna ɗaga kai sama..

kusan halin su ɗaya da umman yaya wato mahaifiyar altab a kwai jin kai da isa da sauri Sara tace

'' bayin Allah ku suwa ye kun shigo mana kai tsaye kamar baku ga mutane a parlour ba ba gaisuwa balle sallama...?,

wani kallo aunty lubna tayi wa sara na sama da ƙasa sannan ta ja ɗan ƙaramin tsaki tace

'' da hallacan matsai ko na bige ki ke kinsan mu suwa ye to Kannan ango ne..,

Maryam ce ta, ta tashi tace

'' Allah ya saka uwar sa ce taya za ku shigo mana ba sallama ko wayanne irin gidadawa ne..?,

chingum ɗin bakin ta , A'isha ta tofar tace

'' ke har awa kike wannan maganar to wallahi idan yau muka ga dama sai kun yi kwanan cell kinga ko abin da nake umma ta fahimta ta toshe kunnen ta dangin matsiyata ga kayan ɗakin nata zo mu tafi..,

ta ina zata gane aminci ya rufe mata ido cewar aunty lubna

jan hannunta A'isha tayi suka fita sai jin karar tashin motar su sukai fitowa rufaida tayi tace

'' gwara da kukai musu haka yan iskan karya wallahi sai na gyarawa kowa zaman ta..,

dariya suka saka da shewa


POV ALTAB....


Dan rainin hankali ko ka gama zumu ɗin ne kamar baka son barin gidan nan tun ɗazu nake ce maka an kawo ta ka haɗa kayan ka zuwa sallar isha sai mu kai ka amma kayi buruss

Cewar RUFA'I

dan murmushi yayi shi kaɗai yasan me yake ji a jikin sa ba daban biyayyar mahaifiya ba da son kaucewa zaɓen tumin daren da yake neman ya yiwa kansa ba zai iya auren rufaida ba duk da ba abin da ta rasa ilimin addini aiki da shi tsoron Allah ya khalil ne ya shigo a birkice zama yayi ya na sauke gauran numfashi..

Zuciyar ta kasa aminta da abin da idanuwansa suka gani zancen ta yake so ya gaskata amma me ya ga fa takai bakin ta innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Allah ya yaye mai wannan baƙin shafin da ya lulluɓe kwakwalwar sa wannan wacce irin ƙaddara ce

kallon sa altab yayi ya taɓe baki wani irin haushi sa yake ji tashi yayi yace

'' malam lafiya ka shigo min ba ko sallama..?,

idanuwansa ne suka ƙada sukai ja haka idanuwan altab akwai abin da yake hangowa a idanuwan altab amma tunanin da hangen nesan sa sun kasa hasaso mai mene wanne abu ne kamar yadda idon altab yayi ja haka na Khalil kallon ido cikin ido sukewa junan su cikin jin zafin abin da altab ya aikata khalil yace


'' Wallahi Allah altab ka bani mamaki yan zu da ka nuna musu wacce riba ka samu ni nasan wace ce nasreen na Fika sanin ta..,

Cikin ƙaraji altab yace '' wallahi karya kake yarinyar da na raina da hannuna yarinyar da tun tana cikin jini aka danƙa min ita a hannu na..,

tashi khalil yayi tamkar zai shiga jikin altab yace

'' wannan duk abanza tunda baƙa kokarin sakata farin ciki baka kokarin gushe mata damuwa ni nayi rawar gani akan nasreen dan nayi mata maganin damuwar ta na haɗa wata mata da Allah akan ta zama mahaifiyar nasreen ta nuna mata so tamkar mahaifiyar ta ta jawota a jiki sai dai kash tun kafin a je ko ina matar ta gajiya...nasreen bata cancanci tsana daga gurin ka ba har da zaka tun zura baffa yanzu dan an hanani aurenta sai me idan har nasreen mata ta ce zan aure ta...,

Karya kake idan har ina numfashi a doron duniya baza ka taɓa auren ta ba

da sauri RUFA'I ya shiga tsakaninsu yace

'' haba khalil me kuke yi haka kun tashi tare komai naku tare kuna yara ba kuyi faɗa ba sai yanzu yau fa ranar farin ciki ce a gare ku..,

Ni wallahi ba ranar farin ciki bace rana mafi muni a guri na kasan irin halin da ya jefa baiwar Allah nan kasan a halin da na barta shi ya zo yana rayuwa kamar ba shi ya saka ta ba bara kaji RUFA'I idan aka bawa ALTAB bindiga ya harbe nasreen tsab zai iya harɓe ta domin baya kaunar ganin ta a doron duniya

A'uzubilla me kake faɗa ne haka..?,

Cewar rufa'i yana riƙe altab da yake kokarin kai wa khalil duka
Ja da baya khalil yayi yace

''sake shi RUFA'I ce mai akai shi ka dai ne me zuciya...,

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wai me ya shiga kan ku ne ina raba ku , kuna ƙoƙarin yin faɗa da hankalin ku da tunanin ku me maƙon ku kuyi wa wani faɗa kune yau da kan ku kuke yi kar ku manta fa lokacin muna makaranta mahaifiyata Allah ya jikanta da rahama har kwatance take mun da ku amma yanzu kune kuke neman illata junan ku

Rufa'i ya faɗa ya share hawaye jikin su ne yayi sanyi musamman Khalil juyawa yayi zai fita sai kuma wayar sa tayi ringing ashe akan kujera ya ajiye ta komawa yayi ya ɗauka ganin baƙuwar number ya ɗaga tare da akarawa a kunne sallama yayi ba tare da wanda ya bugo ba ya amsa sallamar sa ya zarce da cewa kai ne khalil...?,

Cikin sauri yace '' eh nine me ta faru..,

zan turo maka address kazo asibiti yar uwarka tayi hatsari ana buƙatar ku

ehyi me kace kit ya kashe wayar kallon sa rufa'i yayi yace

'' me ya faru..?,

nima wallahi na rasa gane wa me ke faruwa wai zai turo min address yar uwata tayi hatsari

ko nasreen ce

nima haka nake tunani domin na barta a wani hali sai da na tawo nayi dana sanin tawowa amma bara na ƙara kiran shi danna kira yayi message ya shigo wayar sa da sauri ya bude a fili ya shiga karanta wa yace

Unique Care Al-Haramain Hospital
Plot 297 Jido Layout, Danladi Nasidi Housing Estate Mariri

da sauri rufa'i ya karɓi wayar karantawa yayi ka be ƙarasa ba ya karɓi wayarsa ya daka a aljihu ya fita cikin sauri ya ke komai mantawa da yayi mukulli baya jikinsa tsaki ya ja ya koma part dinsa ya dauko key ya fito bude mota yayi ya shiga

yayi mata key ya kusan buge me bawa shukoki ruwa sai kaucewa yayi ganin a yadda yake Sahara gudu a cikin gidan ya bawa ma'aikatan gidan tsoro sudai sunsan baya shaye shaye buɗe mai get me gadi yayi dai-dai sako hancin motar su lubna sai dai sune suka kauce mai amma shi kamar ma be gansu ba

ko da ya hau titi sharara gudi ya dinga yi har ya isa asbitin parking yayi a waje domin ba zai tsaya jira ba har a ba shi katin shiga da mita ayi checking ta ƙaramar kofa ya shiga wayar sa ya fito da ita daga aljihu kiran mutumin ya shiga yi amma ba ɗauka ƙara kira yayi sai a na biyar sannan ya ɗaga kai tsaye yace mai kana kina gani nan a cikin asibitin...?,

Faɗama masa yayi nan da nan ya mai da wayar aljihu ko tsayawa kashe wayar be ba ya shiga reception hannun sa na dama ya shiga akwai hanya miƙe hanyar yayi har emergency room wuru wuru ya fara can ya hango mutumin yana zurga zurga cikin sauri ya ƙarasa yace

'' tana wanne daki ne..?,

kai hakuri yanzu likitoci na kanta ta bugo ne akai nima wucewa na zo yi na ganta na kaita wasu asiti saboda rashin dan sanda ba a karɓeta ba shi ne na kawo ta nan da ita saboda abin yayi yawa zato suke ba hatsari bane

jingina da bango khalil yayi ko me ya faru da nasreen da sa hannun altab shi ne sanadin komai da ya faru da ita kasa cewa yayi sallar magariba aka kirawo dole ta saka ya tafi yayi salla bayan ya idar ya tsaya yayi mata addu'a sannan ya dawo lokacin wani likita ya fito yana share zufa da sauri khalil ya ƙarasa gunsa yace

'' yaya take kun shawo kan matsalar...?,

dafa shi baturen yayi yace

''don't worry everything will be fine..,

kai khalil ya gyaɗa yace

''I can go in and see her..,

yanzu za a fito da ita a Kaita wani dakin zaka iya shiga amma kafin nan ina son ganin wanda ya kawo ta

sai a lokacin khalil ya lura da mutumin nan baya nan yace

'' kawo ta yayi nine dan uwanta shi temaka mata yayi..,

Okay biyo ni office binsa yayi har office dinsa zama yayi sannan yace

'' a'a ga guri ka zauna mana...,

zama yayi zuciyarsa na tsananin bugu buɗe laptop likitan yayi sannan yace

'' yar uwar ka ta kamu da cutar ciwon zuciya me tsanani i am sorry to say

da sauri khalil ya ɗago yana hango baƙar fuskar altab duk shi ya sakata a cikin wannan hali ci gaba da cewa likitan yayi idan ba ayi taka tsantsan ba ko wanne lokacin zuciyar ta zata iya bugawa sannan ta kamu da cutar mental processing disorder amma wannan ba wata matsala bace hankali ana tafiyar fa ita yadda take so zata war ware
idan har kun lura za ku ga akwai abubuwan da take selecting idan kunyi kokarin da raba da shi ciwon zai ci gaba har ya girma ya zame mata matsala

Rubutu yayi a takarda ya miƙo amsa yayi yayi mai godiya magani zai siyo sannan ya biya duk wani kuɗi da aka ka she mata wayar sa ce ta fara ringing cirowa yayi sunan mamy ya gani raɗa raɗa akan screen din wayar sa yasan yanzu za su iya samin labari wata kila saboda haka ta kirawo shi ɗan haka be ɗauka ba...

A yanzu nasreen bata da wani gata da ya wuce nasa insha Allahu ba zai taɓa barin ta tayi kuka ba fita yayi yaci ka ciɓis da mutumin da

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment