Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ƘISSAR BILƘISU MAI GADON ZINARE

Matar Annabi Sulaimanu Alaihis salam.

Daga shafin Bashir Halilu

Acikin Alkur'ani mai girma, Allah Maɗaukakin Sarki Yana cewa:

وَتَفَقَّدَ الطَّيْرَ فَقَالَ مَالِيَ لَا أَرَى الْهُدْهُدَ أَمْ كَانَ مِنَ الْغَابِبِينَ لَأُعَذِّبَنَّهُ عَذَابًا شَدِيدًا أَوْ لَأَأَذْبَحَنَّهُ أَوْ لَيَأْتِيَنِي بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ فَمَكَثَ غَيْرَ بَعِيدٍ فَقَالَ أَحَطتُ بِمَا لَمْ تُحِطْ بِهِ، وَجِئْتُكَ مِن سَبَإٍ بِنَبَإٍ يَقِينٍ إِنِّي وَجَدتُّ امْرَأَةَ تَمْلِكُهُمْ وَأُوتِيَتْ مِن كُلِّ شَيْءٍ وَلَهَا عَرْشُ عَظِيمٌ * وَجَدتُهَا وَقَوْمَهَا يَسْجُدُونَ لِلشَّمْسِ مِن دُونِ اللَّهِ وَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ السَّبِيلِ فَهُمْ لَا يَهْتَدُونَ *

20. Kuma (Annabi Sulaiman) ya bincika tsuntsaye, sai ya ce: "Me ya sa ba na ganin Alhudahuda, ko kuwa yana cikin waɗanda ba sa nan ne?

21. "Na rantse zan yi masa azaba mai tsanani, ko kuma tabbas zan yanka shi, ko kuma lalle ya zo min da hujja bayyananniya."

22. Sai ko ba da daɗewa ba ya dawo, sannan (bayan an tambaye shi) ya ce: "Ni fa na gano abin da ba ka sani ba, na kuma zo maka da tabbataccen labari daga birnin Saba'u.

23. "(Shine) lalle na sami wata mace tana mulkar su, an kuma ba ta daga kowane abu (na mulki), tana kuma da gadon sarauta mai girma.

24. "Na same ta ita da mutanenta suna sujjada ga rana ba Allah ba. Shaidan kuma ya kawata musu ayyukansu, sai ya kange su daga bin hanya ta gaskiya, don haka su ba sa kan shiriya.

GA CIKAKKIYAR ƘISSAR NANA BILƘISU MAI GADON ZINARE.

Ibnu Kathir ya kawo a cikin littafinsa Al-Bidāyah wan-Nihāyah cewa: "Ita ce Bilkisu ‘yar As-Sayrah, Mahaifinta yana daga cikin manyan sarakuna, kuma yana kin auren ‘yan asalin Yemen. Sai ya auri wata mace daga Aljanu mai suna Rayhana bintus Sakan, wadda ta haifa masa wata diya mai suna Talqamah, wadda kuma ake kira da Bilƙisu." بلقيس

An yi wa Bilƙisu laƙabi da wannan suna ne bayan ta hau karagar mulki, ma’anarsa kuma ita ce "Alƙiyās", wato kwaikwayon mahaifinta. Ta gaji sarauta daga mahaifinta, Al-Hadhad bin Sharhabil, wanda ya fito daga zuriyar Banu Ya’fur.

Bilkisu ta kasance ‘yar sarauta mai tsatson daraja, kuma sunanta yana nufin "damuwa da bakin ciki". Mahaifinta bai samu ‘ya’ya maza ba, shi ya sa ya damƙa mata ragamar mulki, domin yana da cikakkiyar amana a gare ta.

Bayan ta zama sarauniya a masarautar Saba’u, mutanenta sun nuna rashin yarda da ita, har ma su ka raina jagorancinta. Wannan ya sa labarin rashin amincewarsu ya bazu zuwa ƙetaren iyakokin masarautar, lamarin da ya jawo hankalin wasu sarakuna makwabta da ke da burin kwace mulkinta, daga cikinsu har da sarki Zul-Adh’ar (Amr bin Abrahah).

Bilƙisu ta kasance mace mai basira, dabara, da ƙwarin gwiwa. Da ta fahimci cewa Zul-Adh’ar yana shirin yaƙar ta, sai ta ɗauki dabarar ɓuya. Ta saka kaya kamar na wani Balarabe, ta bar masarautarta ita kaɗai ba tare da an gan ta ba, har ta isa ga sarkin. Ta yaudare shi da maganganun soyayya, ta ce za ta aure shi kuma za ta ba shi mulkinta. Ta rika zuba masa giya har sai da ya bugu ƙwarai, yana tunanin tana janye shi ne da ƙauna. Da ya bugu mankas sai ta zaro wuka ta kashe shi.

Daga nan sai ta koma masarautarta da nasara, ta ƙarfafa matsayinta a idon mutanenta. Wannan lamari ya zama darasi gare su cewa babu damar tada husuma, kuma mace ma tana da cikakken ƙwazo da iya tafiyar da masarauta.
Ibnu Kathir_ Albidayah wan nihayah.

Idan mu ka koma cikin Alkur'ani kuwa, A wadannan ayoyi na suratun Namli da mu ka kawo, Allah (Mai tsarki da daukaka) Ya bayyana cewa: wata rana Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fita zuwa wata tafiya, a tare da shi akwai jama'a da yawa, sai ya zo yana bibiyar rundunoninsa na aljannu da mutane da tsuntsaye, don ganin halin da suke ciki. Lokacin da ya zo kan tsuntsaye sai bai ga tsuntsun Alhudahuda a cikinsu ba. An ce kuwa Alhud'huda yana da amfani acikin tawagar, domin shi ne ya ke nemo musu inda ruwa yake, daga nan sai a tura Aljanu su ɗebo, ko kuma su tona rijiya a ɗiba. Sai Annabi Sulaiman (AS)ya tambaya cewa, me ya sa bai ga Alhudahuda ba? Watau shi ne bai gan shi ba yana cikin ribibi ko kuma dai ba ya wurin ne? Sai aka sanar da shi cewa ba ya nan. Sai Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi barazanar cewa lallai idan ya dawo sai ya yi masa azaba mai tsanani, ko ya yanka shi sakamakon rashin ganin sa da ya yi, ko kuma ya zo masa da wata bayyananniyar hujja karba66iya wadda za ta nuna uzurinsa a fili.

Ba a jima ba kuma sai ga Alhudahuda ya dawo, ya bayyana wa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) uzurinsa na tafiya yaho, bai dawo da wuri ba, da cewa ya gano masa wani abu da shi bai san da shi ba, domin ya zo masa da wani sahihin labari wanda babu kokwanto a cikinsa daga birnin Saba'u na kasar Yaman. Watau ya samu mutanen wannan birnin wata mata ce take mulkinsu, kuma an ba ta duk wani abu da mulkinta yake bukata na karfin mayaka da tattalin arziki, sannan kuma tana da wani gadon sarauta mai girman gaske wanda takan hau shi don gudanar da sha'anin mulkinta. Alhudahuda ya ci gaba da bayyana wa Annabi Sulaimanu abin da ya gano a birnin Saba'u, da cewa ya sami wannan mata mai mulki da mutanenta suna bautar rana ne ba Allah ba, kuma Shaidan ne ya ƙawata musu ayyukan shirka da saɓon Allah da suke yi, ya kuma hana su bin hanyar gaskiya, don haka suka kasa shiryuwa su bauta Wa Allah shi kadai wanda yake fito musu da ruwan da yake ɓoye a sama, da tsirran da suke cikin kasa, kuma yake sane da ayyukansu da suke boyewa da wadanda suke bayyanawa. Shi ne Allah wanda babu abin bauta da gaskiya sai shi Ubangijin Al'arshi mai girma.

Lokacin da Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ji duk bayanan Alhudahuda, sai ya bayyana masa cewa za su duba su yi bincike don tabbatar da gaskiyar labarinsa ko karyarsa, watau kafin su san irin matakin da za su dauka a kai.

Daga nan sai Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fara ɗaukar matakin bincike, ya rubuta takaitacciyar wasika ya ba Alhudahuda don ya isar da ita ga Sarauniyar Saba'u, ya umarce shi da ya je garin ya jefa musu wannan wasikar, sai ya dan ja da baya kadan ya tsaya inda zai ji abin da Sarauniya da fadawanta za su tattauna a kansa da kuma irin martanin da za su dawo da shi.
Malaman tarihi su ka ce, sai Alhudahuda ya ɗauki wasiƙar, ya je har ɗakin daBilƙisu ta ke kwance da sassafe, daidai lokacin hudowar rana, wato lokacin da ta ke tashi ta yi wa rana sujjada, ya buɗe tagar ɗakin na ta. Kawai sai ta ga ahsken rana ya dallare ma ta ido, sai Alhudahuda ya jefa ma ta takardar, ya koma gefe, ba ta san wa ya jefo ma ta ba.
Bayan Alhudahuda ya aikata abin da aka umarce shi da shi, wasika ta je hannun Sarauniyar Saba'u, ta kuma karanta ta ga abin da yake ciki, sai ta tara manyan gari a fadarta ta fada musu cewa an fa jefo mata wasika mai girma. Abin da wasiƙar ta ƙunsa kuwa shi ne, "Wannan wasika daga Sulaimanu take" kuma an bude ta da Bismilla, watau "Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin kai". Sannan wasikar ta ce: "Lalle kada ku yi min girman kai, ku zo min kuna masu mika wuya". Watau dai yana sanar da su cewa kada su bijire masa, su zo suna masu mika wuya ga abin da yake kiran su a kai na Kaɗaita Allah da barin shirkar da suke kai ta bautar rana. Ta kuma tabbatar musu da cewa ba za ta yanke komai ba a kan wannan al'amari har sai ta saurari shawarwarinsu da ra'ayinsu.

Sai su ka mayar mata da jawabi da cewa, su mutane ne karfafa kuma jaruman mayaka, saboda haka ko da ta bijire wa Annabi Sulaimanu ta ki yarda da shi, to su a shirye suke su fafata yaki a kan haka, amma dai sai suka mayar da magana gare ta domin sun yarda da cewa ita mace ce mai zurfin hankali, don haka ba za ta yanke abin da bai dace ba, kuma a shirye suke su zartar da duk abin da ta umarce su.

Sai Sarauniya ta bayyana musu illar yaki da sarakuna masu karfi da cewa, idan har suka yi nasarar kama wata alkarya, to fa sai sun yi babbar barna a cikinta, sun yi kashe-kashe sun wawashe dukiyar al'umma, sun kama manyan garin sun mayar da su wulakantattu sun bautar da su. Ta kuma tabbatar musu cewa koyaushe haka halin sarakunan yake. A karshe dai ta zartar da na ta tunanin da cewa, za ta fito musu ta hanyar lalama, ta aika masa da kyauta ta alfarma, don ta ga ko wannan zai canza masa ra'ayinsa ko kuma a'a.

Sai ta aika wasu manyan fadawanta da kyauta zuwa ga Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Yayin da su ka isa gare shi su ka gabatar masa da kyautar Sarauniya Bilƙisu sai ya ki karbar kyautarsu, ya kuma mayar musu da martani mai zafi da cewa, suna zato za su kare shi ne da wata dukiya don su canza masa tunaninsa ya fasa aikata abin da ya yi niyya? Don haka ya tabbatar musu da cewa abin da Allah ya ba shi ya zarce abin da suke takama da shi, domin shi Allah ya ba shi kasaitaccen mulkin da bai taba ba wa wani mahaluki irinsa ba, bugu da kari kuma ga shi Annabin Allah. Sai ya soke su da cewa su ne wannan kyautar za ta burge su, har su yi ta farin ciki da ita, saboda son duniya da ke zukatansu da kuma karancin abin da suka mallaka, idan an kwatanta shi da abin da shi ya mallaka.

Daga nan ne fa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya umarci wannan ɗan aike na Sarauniya da 'yan rakiyarsa su koma su mayar ma ta da kyautarta sannan su isar ma ta da saƙonsa na cewa, tabbas ba makawa zai zo musu da rundunarsa da ba za su iya tunkarar ta ba, kuma lalle sai ya fitar da su daga garin Saba'u cikin wulakanci da kaskanci matukar ba su sallama kansu gare shi ba.

To bayan ƴan aiken Sarauniya Bilƙisu sun koma domin isar da saƙon Annabi Sulaimanu zuwa gare ta, sai Annabi Sulaiman (AS) ya tabbatar wa fadawansa cewa Sarauniya da mutanenta za su mika wuya gare shi, amma duk da haka sai ya tambayi fadawan da suke gabansa na mutane da aljannu cewa wane ne a cikinsu zai iya kawo masa gadon sarautarta tun kafin su zo su sallama kansu? Da jin wannan tambaya sai wani kakkarfan aljani ya bayyana cewa shi zai iya kawo wa Annabi Sulaimanu wannan gadon kafin ya tashi daga majalisarsa. Ya kuma tabbatar masa da cewa shi kakkarfa ne don haka daukar wannan gado ba zai gagare shi ba, sannan kuma shi mai amana ne, ba zai taba komai daga jikin wannan gado ba. To an ce sai Annabi Sulaimanu Alaihis salam ya ce wannan lokacin ya yi masa tsayi sosai. Sai kuma wani salihin malami mai ilimin littafi da ke zaune a gaban Annabi Sulaimanu ya bayyana masa cewa shi zai iya kawo masa gadon kafin ma ya kifta idonsa. Faɗar wannan ke da wuya sai kawai Annabi Sulaimanu ya ga gado gingirin a gabansa, ba tare da ma mutuin ya jira an ba shi umarni ba. Sai Annabi Sulaimanu (AS) ya ce tabbas wannan lamari ba komai ba ne sai falalar Ubangijinsa a gare shi, kuma ya yi masa haka ne don ya jarrabe shi ya ga shin zai gode wa Allah kan ɗimbin ni'imomin da ya yi masa ko zai butulce? Sannan ya bayyana cewa duk wanda ya gode wa Allah kansa ya yi wa, domin shi ne zai ga amfanin godiyar. Hakanan duk wanda ya butulce to don kansa, domin shi Allah mawadaci ne ba shi da bukatar komai a wurin kowa, kuma mai karamci ne don haka ne ma yake kara wa bayi masu yi masa godiya a kullum.

Bayan Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ga gadon Sarauniya a gabansa, sai ya umarci masu gudanar da lamarin fada da cewa su sauya kamannin gadon, ta hanyar kara masa wasu abubuwa da ba shi da shi ko rage masa wasu domin yana so ne ya auna kaifin basirarta ya ga cewa za ta gane nata ne ko ba za ta iya ganewa ba.

Ita kuwa Sarauniya Bilƙisu tun lokacinda ƴan aikenta su ka koma ma ta da saƙon Annabi Sulaimanu sai ta yanke shawara zuwa ta Musulunta, sannan ta sa aka yi ma ta rami mai zurfin gaske, ta saka gadon zinarenta aciki ta binne shi. Wanda gado ne makeken gaske mai dauƙe da ɗakuna da guraren hutawa da kayan ado aciki. Saidai duk kafin ta iso tini Annabi Sulaimanu ya sa an haƙo gadon, an kawo ma shi gabansa.
Bayan isowar Sarauniya Bilƙisu fadar Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai ta ga gadon sarauta a gabanta wanda ya yi kama da nata, to amma a iya saninta ta baro nata a kasarta, daga nan sai aka tambaye ta cewa shin gadonta kamar wannan yake? Sai ta amsa da cewa: "Kamar dai shi."

Da Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ga kaifin basirarta da zurfin hankalinta sai ya bayyana girman ni'imar da Allah ya yi masa wadda ta zarce irin abin da Allah ya ba ta na hankali da ganewa. Ya bayyana cewa Allah ya ba shi ilimi tun gabanin a ba ta wanda kuma ya fi nata, domin nasa ilimin annabta ne, sannan kuma ga shi Musulmi ne tun da farko, ita kuma kafira mai bautar rana ba Allah ba, bautar da ta hana ta ita da mutanenta su yi imani da Allah su bauta masa shi kadai.

Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi niyyar ya nuna wa Sarauniya Bilƙisu ƙasaitaccen mulkin da Allah Ya ba shi, don haka ya kirawo ta don ya nuna mata fadarsa, aka yi ma ta iso ta shigo sai ta ga ai wani wuri ne kamar ruwa mai zurfi za ta shiga, sai kawai ta yaye kwaurinta don kada tufafinta su jike da ruwa. Sai Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sanar da ita cewa wannan da take gani ba ruwa ne a kwance ba; fada ce da aka gina ta da gogaggun kasaken karau wadanda ruwa yake gudana ta karkashinsu, don haka ba sai ta yaye kwaurinta ba. Wasu Malaman tarihi su ka ce, ana yaɗa jita-jitar cewa ita Sarauniya Bilƙisu rabinta mutum ce, rabinta kuma Aljanace, saboda mahaifinta mutum ne mahaifiyarta kuma Aljana. To sai Annabi Sulaiman (AS) ya saka wani abu mai kama da ruwa a ƙasa, saboda idan ta buɗe ƙafarta zai gane ko kutum ce ko Aljana. To lokacin da ta ga abin da ta gani na mamaki da girman mulki da kasaitar iko, ta kuma fahimci cewa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba wai sarki ne ba kawai; annabin Allah ne, sai ta bayyana tubanta ga Allah ta kuma musulunta a hannun Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Kuma an ce faga baya ya aureta, ta zama matarsa.

Alhamdu lillahi.

Daga shafin Bashir Halilu.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters

Please Login or Register in order to submit comment