Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

RUWAN ƊUFANA

ƘISSAR ANNABI NUHU ALAIHIS SALAM

Daga shafin Bashir Halilu.

Allah Maɗaukakin Sarki Yana cewa

وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَى قَوْمِهِ فَلَبِثَ فِيهِمْ أَلْفَ سَنَةٍ إِلَّا خَمْسِينَ عَامًا فَأَخَذَهُمُ الطُّوفَانُ وَهُمْ ظَالِمُونَ فَأَنجَيْنَهُ وَأَصْحَابَ السَّفِينَةِ وَجَعَلْنَهَا ءَايَةً لِلْعَالَمِينَ .

【Ma'ana】

14. Kuma haƙiƙa Mun aiko Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya zauna cikinsu shekara dubu ba hamsin (950), sai (ruwan) Ɗufana ya ci su, alhalin suna azzalumai.

15. Sai Mu ka tserar da shi tare da mutanen jirgin ruwa, Mu ka kuma sanya shi (jirgin) aya ga talikai.

Annabi Nuhu (AS) yana daga cikin manyan Annabawan da Allah Ya aiko domin shiryar da mutane zuwa ga tauhidi. Ya kasance cikin jerin Annabawan da ake kira "Ulul Azmi", wato manyan Annabawa guda biyar mafiya daraja a gurin Allah.

Ibn Kathir ya kawo a cikin littafinsa Al-Bidāya wan-Nihāya cewa, Annabi Nuhu (AS) shi ne Nuhu ɗan Lamik ɗan Matushalakh ɗan Annabi Idris (AS) ɗan Yarid ɗan Mahla'il ɗan Qainan ɗan Anush ɗan Shith (AS) ɗan Annabi Adam (AS). Wato, Annabi Nuhu (AS) yana cikin zuriyar Annabi Idris (AS) kuma yana da nisa da Annabi Adam (AS) da kakanni tara kawai.
Annabi Nuhu (AS) ya rayu a wani yanki da ake kira "Al-Kūfa" a kasar Iraƙi, kusa da kogin Furat, ko kuma a wasu ruwayoyi, ana cewa yana kusa da yankin Armeniya da ƙauyukan da ke kusa da Dutsen Judi.

Ibn Kathir ya ambata cewa Annabi Nuhu (AS) yana da ‘ya’ya uku, waɗanda daga su ne aka samu rarrabuwar jinsin ƴan Adam da ƙabilu daban-daban. Daga cikin ƴaƴan na sa da akwai Samu, wanda shi ne Kakan Larabawa, Yahudawa, da Nasara. Sai Hamu, shi kuma shi ne Kakan mutane baƙar fata, musamman yankin Afrika. Sai na ukunsu Yafisu, shi kuma shi ne ya haifi Turkawa, mutanen Mongoliya, da sauran ƙabilun Asiya. Sannan yana da wani ɗa mai suna Kan'ana da kuma matarsa mai suna Waliya amma su ba su yi imani ba, don haka aka hallakar da su a ruwan Ɗufana.
Annabi Nuhu (AS) ya tashi cikin mutanensa lokacin an yi wasu mutane masu ƙima a idon al'umar zananin, kamar wasu shugabanni da malamai da sauran mutanen da ake girmamawa. Irin waɗannan mutane sun haɗa da wanda ake kira Wudda da Suwa'a da Yagusa da Ya'uwƙa da kuma Nasra. Mutanen zamanin sun kasance idan wani babban mutum ya mutu a cikinsu sai su sassaƙa gunki mai kama da shi su ajjiye don tunawa da wannan mutum da kuma koyawa ƴan baya halayensa na kirki da sanar da su tarihin manyan cikinsu. To lokacinda waɗannan mutane biyar su ka mutu su ma sai aka sassaƙa gumakansu aka ajjiye don tunawa da su. Bayan shuɗewar shekaru masu yawa sai shaiɗan ya dinga raya musu cewa ya kamata su dinga bautawa irin waɗannan mutane masu daraja, sai su ka koma bautawa waɗan nan gumaka a maimakon bautar Allah, sai Allah Maɗaukakin Sarki Ya aiko Annabi Nuhu (AS) don ya kira su izuwa kaɗaita Allah da bauta da kuma barin bautar gumaka.

Sai su ka fara yi masa izigili, su na yi masa dariya, suna ce masa ya samu matsala ne, har ya fara tatsuniya yana cewa wahayi ake masa. Suna cewa ai ba zai yiwu Allah Ya aiko mutum ba saidai Mala'ika. Da su ga ka Annabi Nuhu (AS) lallai da gaske ya ke yi sai su ka fara yi masa barazana da kisa da azabtarwa kuma su ka hana mutane sauraronsa.

Annabi Nuhu (AS) ya dinga zuwa duk inda ya san mutane suna taruwa kamar kasuwanni da sauran gurare, yana yi musu wa'azi. Yana wa'azi a kowane lokaci, dare da rana, har ta kai Annabi Nuhu (AS) yana zuwa har gida yai sallama da mutum yai masa wa'azi. Duk inda ya ga taron mutane ko masu yawa ko kaɗan yana tsayawa ya isar musu da saƙon Allah amma mutanen sai ƙara kangarewa suke yi. Ta kai idan Annabi Nuhu (AS) yana magana sai mutanen su dinga saka hannu suna toshe kunnuwansu ko su rufe fuskarsu don kar ma su ganshi. Hatta cikin gidan Annabi Nuhu (AS) da akwai ɗansa wanda bai imani ba da kuma matarsa wacce itama ba ta imani da shi ba kuma ta yi yunkurin kashe shi a lokuta da dama amma ba ta samu nasara ba. Ita ce Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi alƙarin sai ya ƙonata ranar Alƙiyama, cikin suratut tahriym, ayah ta goma, Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce

ضَرَبَ اللَّهُ مَثَلًا لِلَّذِينَ كَفَرُوا امْرَأَتَ نُوحٍ وَامْرَأَتَ لُوطٍ كَانَتَا تَحْتَ عَبْدَيْنِ مِنْ عِبَادِنَا صَلِحَيْنِ فَخَانَتَاهُمَا فَلَمْ يُغْنِيَا عَنْهُمَا مِنَ اللَّهِ شَيْئًا وَقِيلَ ادْخُلَا النَّارَ مَعَ الدَّاخِلِينَ.

Ma'ana:

10. Allah Ya ba da wani misali ga wadanda suka kafirta da matar Nuhu da matar Luɗu; sun kasance karkashin (igiyar auren) wasu bayi su biyu salihai daga bayinmu, sai suka ha'ince su, saboda haka ba su wadatar musu komai ba (daga azabar) Allah, (ranar alƙiyama) kuma aka ce (da waɗannan mata guda biyu): "Ku shiga wuta tare da masu shiga."

Allah Maɗaukakin Sarki Ya bayyana cewa kasancewarta matar Annabi Nuhu ba zai hana Allah Ya ƙonata a wuta ba, za a kaisu wuta ita da matar Annabi Luɗu (AS) saboda sun kasance suna ha'intar mazajensu.

Cutarwar mutane ga Annabi Nuhu (AS) kuwa sai ƙara tsananta ta ke yi, ga shi tsawon shekaru masu yawa amma sun ƙi yin imani. Sai da Annabi Nuhu (AS) yai shekara ɗari tara da hamsin yana wa'azi alhali an aiko shi yana ɗan shekara ɗari biyu da hamsin. Kenan sai da ya cika shekara dubu ɗaya da ɗari biyu a duniya amma kullum sai arna sun yi masa duka, wani sa'in ma suna zato sun kashe shi, sai daga baya kuma Allah Ya dawo masa da ransa, ya koma ya cigaba da wa'azi.

Sai bayan cikar waɗannan shekaru ne sai Allah Maɗaukakin Sarki ya yi wa Annabi Nuhu wahayi cewa "Babu wanda zai kuma yin imani daga cikin mutanenka, saidai wanda dama tini ya yi imani, don haka kada ka damu da abinda suke aikatawa".

Jin haka sai Annabi Nuhu (AS) ya yi addu'a kamar yadda ya zo a cikin Alƙur'ani. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

قَالَ نُوحٌ رَّبِّ إِنَّهُمْ عَصَوْنِي وَاتَّبَعُوا مَن لَّمْ يَزِدْهُ مَالُهُ وَوَلَدُهُ إِلَّا خَسَارًا * وَمَكَرُوا مَكْرًا كُبَّارًا * وَقَالُوا لَا تَذَرُنَّ وَالِهَتَكُمْ وَلَا تَذَرُنَّ وَدًّا وَلَا سُوَاعًا وَلَا يَغُوثَ وَيَعُوقَ وَنَسْرًا * وَقَدْ أَضَلُّوا كَثِيرًا وَلَا تَزِدِ الظَّالِمِينَ إِلَّا ضَلَالًا مِمَّا خَطِيئَتِهِمْ أُغْرِقُوا فَأُدْخِلُوا نَارًا فَلَمْ يَجِدُوا لَهُم مِّن دُونِ اللَّهِ أَنصَارًا * وَقَالَ نُوحٌ رَّبِّ لَا تَذَرْ عَلَى الْأَرْضِ مِنَ الْكَافِرِينَ دَيَّارًا ) إِنَّكَ إِن تَذَرْهُمْ يُضِلُّوا عِبَادَكَ وَلَا يَلِدُوا إِلَّا فَاجِرًا كَفَّارًا ) رَّبِّ اغْفِرْ لِي وَلِوَالِدَيَّ وَلِمَن دَخَلَ بَيْتِيَ مُؤْمِنًا وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ وَلَا تَزِدِ الظَّالِمِينَ إِلَّا تَبَارًا )

Ma'ana:

21. Nuhu ya ce, "Ya Ubangijina, lalle su sun saɓa mini, sun kuma bi duk wanda dukiyarsa da 'ya'yansa ba su kara masa komai ba sai asara.

22. "Suka kuma shirya makirci babba.

23. "Suka kuma ce: 'Kada ku bar abubuwan bautarku, kuma lalle kada ku bar Waddu da Suwa'u da Yagusu da Ya'uƙu da Nasaru."

24. "Hakika kuwa sun batar da adadi mai yawa; kar kuma Ka kari kafirai da komai sai bata."

25. Saboda saɓonsu ne aka nutsar da su, sai aka shigar da su wuta, don haka, ba su sami wasu mataimaka ba Allah ba.

26. Nuhu ya ce: "Ya Ubangijina, kada Ka bar wani mutum daya daga kafirai a bayan kasa.

27. "Lalle idan har Ka bar su, to za su batar da bayinka, kuma ba za su haifi kowa ba sai fajiri mai tsananin kafirci.

28. "Ya Ubangijina, Ka gafarta min ni da mahaifana da kuma wadanda suka shiga gidana suna muminai, da kuma (sauran) muminai maza da mata, kada kuma Ka kari kafirai da komai sai hallaka."

To bayan da Allah Ya amsawa Annabi Nuhu (AS) roƙonsa na cewa zai halakar da waɗanda ba su yi imani ba, sai Ya umarce shi da ya fara ginin jirgin ruwa. Ibn Kathir ya ce Allah Ya umurce shi da yanke wasu itatuwa, ya haɗa su da tarin laka ko taɓo sannan ya gina jirgin ruwa mai girma. Lokacin da Annabi Nuhu (AS) ya fara aikin gina jirgin ruwan sai Mutanen gari su ka fara yi masa dariya suna tambayarsa, “Kana gina jirgi a cikin hamada, cikin rairayin sahara? Ina ruwan da jirgin zai hau?” Amma shi bai kula su ba, domin ya san cewa umarnin Allah ne.

A duk sanda su ka zo wucewa sai sun masa izgili da rashin kunya, an ce har shara su ka dinga zuba masa acikin jirgin ko kuma idan ya fara aikin sai su lalata masa.
Shi kuwa Annabi Nuhu (AS) Allah Ne ke sanar da shi yadda tsarin jirgin zai kasance da girmansa da faɗinsa da inda za a yi masa gurin zama da tagogi da dai sauransu. Kuma Allah Ne ya sanar da shi yadda ake sa jirgin yay gudu ko ya tafi a hankali.

Allah Ya yi wa Annabi Nuhu (AS) wahayi cewa, da zarar ya ga ruwa yana ɓulɓulowa daga ƙasan tanderu to lokacin halakar da mutanensa ya yi. Don haka cikin kowacce halitta daga halittun duniya ya ɗauki guda biyu, namiji da mace, ya saka acikin jirginsa da sauran mutanen da su ka yi imani da shi kowa ya shiga, domin kuwa za a sake sabuwar duniya ne, za a halakar da kowa sai waɗanda su ka hau jirgi kawai.

Ana nan kuwa sai mutane su ka ga ruwa ya fara ɓulɓulowa ta ƙasa, an ce duk inda aka kunna wuta sai kawai a ga ruwa yana ɓulɓulowa, kamar murhun abinci da tanderun gurasa da dai sauransu, ga ruwan sama kuma mai ƙarfin gaske yana sauka. Idan mutum ya shiga ɗaki ya ɓoyewa ruwan sama sai kawai ya ga ruwa yana ɓulɓulowa ta ƙasan ɗakin. Ruwa ya dinga fitowa daga cikin ƙasa ga kuma ruwan sama yana sauka ba kakkautawa. Ruwa ya cika ko ina, fili, koguna, tafkuna, da duwatsu har duniya baki ɗayanta.

Shi kuwa Annabi Nuhu (AS) sai Allah Ya aiki dabbobi da kansu su ka dinga shiga cikin jirginsa suna ɓuya, kowacce dabba namiji da mace. Tun daga manyan dabbobi da kanana da kwari da tsuntsaye da dabbobin ruwa da sauran mutane masu imani, kowa ya shiga. Ana cikin haka ne Annabi Nuhu (AS) ya hango ɗan nan na sa wanda bai yi imani ba, mai suna Kan'ana, yana duru-duru, ya rasa yadda zai yi acikin ambaliya, sai ya kira shi ya ce masa "Ya ɗa na, zo ka hau jirgi tare da mu, kar ka zama cikin kafurai" Sai ɗan ya ce masa "Zan je in samu dutse na hau, zai kare ni daga ruwa"
Annabi Nuhu yai-yai da shi ya hau amma ya ƙi, ƙarshe dai igiyar ruwa ta murɗa da shi, ta je fa shi can, Annabi Nuhu (AS) ya dena hango shi. Sai Annabi Nuhu (AS) ya fara yi masa addu'a, yana neman Allah Ya kuɓutar da shi amma Allah Ya sanar da shi cewa wannan ɗan na sa bai yi imani ba, don haka ya dena yi masa addu'a ko neman gafara. Shi kenan dukka sauran mutane da dabbobi da tsuntsaye su ka nutse, sai dai wadanda Annabi Nuhu (AS) ya tara a cikin jirginsa. Duhu da hadari ya mamaye duniya. Ruwa ya tashi har ya shanye dutsen da yake mafi tsayi a duniya, sannan ya rufe komai.

Bayan kwanaki da watanni, Allah Ya umurci ruwan ya tsagaita: "An ce: Ya ƙasa! Ki shanye ruwanki, kuma ya sama! Ki tsaya! Sai ruwa ya ragu, kuma al’amarin ya ƙare, sai aka tsayar da jirgin ruwan a kan Dutsen Judi, kuma aka ce: " Halaka ta tabbata ga mutane azzalumai!"

Daga nan, Annabi Nuhu (AS) da mabiyansa su ka sauka daga cikin jirgin, su ka sake farawa da sabuwar rayuwa.

Ana kiran Annabi Nuhu (AS) Kakan mutane na biyu, bayan Annabi Adam, saboda kowa ya mutu sai zuriyarsa ne su ka yi saura a duniya, daga su aka sake tara mutanen duniya.

An karɓo daga hadisin Anas (RA), ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lokacin da Allah Ya aiko Annabi Nuhu (AS) zuwa ga mutanensa, yana da shekaru ɗari biyu da hamsin (250). Sai ya zauna a cikinsu tsawon shekaru dubu, ba hamsin (950). Bayan ambaliya kuma, ya ci gaba da rayuwa har tsawon shekaru ɗari biyu da hamsin (250). Lokacin da Mala'ikan mutuwa ya zo gare shi, sai ya ce masa: ‘Ya Nuhu, babban Annabawa kuma mai tsahon rai, wanda ake amsa addu'arsa, yaya ka ga duniya?’

Sai Nuhu (AS) ya ce: ‘Kamar mutum ne da aka gina masa gida mai ƙofofi biyu; sai ya shiga ta ɗaya, ya fita ta ɗaya ko kuma ya shiga ta ɗaya, ya zauna na ɗan lokaci kaɗan, sannan ya fita ta ɗaya ƙofar.’

Daga shafin Bashir Halilu.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters

Please Login or Register in order to submit comment