Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida da kyar take tafiya, kallo adda Binta ta bita dashi ta ankara da jinin daya bushe a kafarta, ga kuma wani na gangarowa, dariya ta sheƙe da ita tace "innai yarinyar nan ta girma ba mashin shine...,?
kamar ta yanzu wasu ana shirin aurar dasu wasu kuma har da ya'ya
ita dai batace ƙala ba tacigaba da tafiya har ta isa bukkarta, ta kwanta jikinta na mata matsanancin ciwo musamman ma kirjinta da gabanta, a haka har baccin wahala ya ɗauke ta, jin maganar baffa suna hira dasu adda Binta tasan karfe uku tayi, dakyar ta tashi farin ciki ya kamata jin sallamar faɗima, baffa ya amsa tace "innai shatu na nan...,
Eh kawai tace mata, wucewa tayi ta shiga bukkarta da sauri taso tace "faɗima a galabaice
Cikin mamaki fadima take kallonta tace "shatu me ke damun ki? baki da lafiya ne? wannan jinin fa daya ɓata miki kaya da kafa...?,
da kyar ta tashi ta zauna tace eh wallahi bani da lafiya fadima, bakona ne yazo kuma ba ruwan da zan wanke jikina
cikin tausayawa tace "to Bara na ɗauki tulu na ɗebo miki ruwa...,
kamo hannunta tayi tace harda abinci fadima ina buƙata dan Allah, banci komai ba tun jiya
riƙe hannunta tayi gam tace" karki damu kawata, zan damo miki kindirmo amma bamu da siga,

HALEEMATOU YAR LAGOS
EPISODE 17-18

Eh zan iya sha haka ta fada a galabaice kamar kuma zatayi kuka, fatima ta fita cike da tausaya mata tunda dama tasan irin zaman datake a gidan, bata dade ba ta dawo da ruwa da kwaryar nono, lokacin ya Usman ne kaɗai a tsakar gidan, ta ajiye kayan gefe sannan ta zuba ruwa a cikin kwarya ta kai bayi, shiga ta taso ta shatu ta kaita bayi ta fito, ya Usman kuwa fita yayi ya zauna ya zuba tagumi yana danasanin abinda yayiwa shatu, musamman ma daya ga yadda ta koma, to wai ma meya sa ya aikata haka?
bayan wannan abun daya faru kwanan sa ɗaya ya koma makaranta, haka ta dinga rayuwa ba dadi, kwatsam rana ɗaya ciki ya fito ba ƙaramin tozarci taci ba, a gaban ya Usman innai ta watso mata kayanta tabar gidan,
abin ka da ruga tuni kowa ya fito ana kallona, yara suka rakota har tasha suna yi mata ihu, haka ta hau mota bata da kuɗi, da kyar aka samu wanda ya biya mata kuɗin mota zuwa lagos, haka ta dinga fadi tashi a Lagos har ta samu wajen zama, Allah ya taimaketa ta samu aiki a shagon linda tana biyanta duk wata,
shine fa har ta haifi haleemo, taci gaba da rainonta da dadi ba dadi, wannan dalilin ne yasa bata son komawa garinsu, amma sau tari ta kanyi tunani musamman da Haleemo tayi wayo take yawan tambayar mahaifinta, komai na ya Usman haleemo bata bari ba, abu kaɗan ne ta dauko nata, dan haka tafi kama dashi sosai tamkar an tsaga kara,
ɗa sauri haleema ta ɗago jikinta na ɓari, kenan ta wannan hanyar aka sameta innalillahi wa'inana'ilaihir raji'un, ta fara kuka kamar ranta zai fita daman ita ba kowan kowa bace? ga wannan mummunan tabon da har abada ba zai gogu ba, cikin rawar baki tace umma... maganar dataso tayi ta kakare sai kawai ta kifa Kanta a cinyar mahaifiyarta ta tana kuka, bata hana ta ba domin tasan wannan kukan shine samun sa'ida a ranta,
Wannan kenan Kano
Daddy daddy tun daga kan bene take magana, cikin tsawa ammee tace "amra anya kuwa kina da hankali? me makon ki sauko ki sameshi ki mishi magana sai kace wanda zai gudu,
ƙarasa saukowa tayi tace "daddy Dan Allah yau tun da kana gida zaka kai mu shopping, idan kace yaya ya kai mu ba kai mu zai ba....,
ɗagowa yayi ya goge bakinsa da tissue yace 'amra kiyi hakuri yanzu zan tafi office...,
zunɓuru baki tayi ta kalli ammee tace "dan Allah to ki kai mu gidan aunty Farida....,
ammee ta harareta tace ba inda zani, ke kin fiye son yawo habaa, ta sa kuka ta hau sama daddy yayi dariya yace "amrah a kwai rigima....ba kamar momyna ba da ba runwanta....,
briefcase ɗinsa ya ɗauka yace Allah ya shirya mana su, ammee tace ameen amma amra sai addu'a lokaci daya ta birkice, Allah ya shirya mana baki daya
Amin ya Allah ya faɗa yana rataya briefcase dinsa, ya fita tayi mai Allah ya tsare ya buɗe motarsa ya shiga, tare da yiwa mai gadi horn ya buɗe mai ya fita, kiran mansur ne ya soma shigo mai a waya, amma sanin dokar tuki ya faka gefe ya ɗaga wayar, tare da karawa a kunne ya amsa sallamar'sa, gaisawa sukai mansur yace " yau naga ikon Allah daddy Faisal....,
takaici ne ya kama daddy yace"kai daman ba wata magana ce me mahimmanci ba ka kirani....?,
wallahi abokina ina cikin al'ajabi yanzu nan ina wani shago naga wata yarinya wallahi kamar ku ai kafin ya karasa ya kashe wayar ci gaba yayi da tukinsa wajan wasu masu sai da nono ya je ya tsaya siyan fura yayi zai buɗe motar sa yaji ance ya Usman da sauri ya jiyo ƙarasuwa faɗima tayi tace "ya Usman ina huni ko kun kara jin labarin shatu kuwa.....?,
lafiya qalau ya iyalin naki
Alhamdullahi kasan yanzu a kano nake aure unguwar daɓai
to Allah ya bada zaman lafiya
amin ya Allah dan Allah ko kaji labarin'ta
dan jim yayi yace "a'a bamu ji ba...,
gefen mayafin'ta ta saka ta share hawaye tace"Allah ya bayyana'ta in a raye take in kuma ta mutu ya jikan'ta....,
amin ya Allah miƙo mata kuɗi tayi tace baza ta amsa ba sai da ya matsa ta amsa shiga mota yayi zuciyarsa ba dadi tunani ya ishe shi har ya isa office be de tunani ba
shima yanzu ya fara zargin anya kuwa tana darai har ta kai wannan shekarun ba ta waiwayo gida ba parking yayi ya fito ma'aikatan Company ne suka shiga girmama shi cikin mutuntawa yake gaishe shi har ya buɗe office ɗin'sa be dade da zama ba Faisal ya shigo gaishe shi yayi yace "daddy ina huni....,
lafiya qalau Faisal daman baka gida
zama yayi yace"eh ina nan...,
to Allah yayi albarka
amin ya Allah
shirune ya biyo baya file ɗin da aka tara mai tun safe ya shiga dubawa Faisal na taya shi Faisal dole kai zan tura Lagos ka tawo da wannan order da mukai in jinan sun zo
To Allah ya kai mu ya faɗa yana ci gaba da duba file ɗin
Wannan kenan Lagos

Haka rayuwa ta ci gaba da gudana yayin da haleema ta zama cikin damuwa saidai kullum umma na yi mata na siha da wa'azi amma kam zuciyar ta ta bushe idan ta tuna rashin imanin da mahaifin nata yayi mata har ya zaɓi ta zo ta wannan kazamar hanyar da take tsanar zina ashe zina ce tayi ta jin sallamar aunty zulfa'u da sauri ta ɗago tace
"Aunty zulfa'u sai yanzu kika dawo...,
zama tayi ta cire mayafin da ta rayata tace "wallahi kuwa kin ganni nan shegen mutumin nan ya ɓata min rai wallahi har na gama zamana wai be zo ba wani meeting ya tsare shi....,
dariya halee tayi tace"wallahi ki gane ba wani meeting matar'sa dai ta riƙe shi...,
pillow ta hulla mata dariya tayi tace "wallahi gaskiya nake faɗa miki...,
wallahi halee kin raina ni ina umma
yau ta tafi aiki
ke me ya hanaki zuwa...?,
hmmm bakomai
tabe baki zulfa'u tayi tace "ta nuna miki halinta ko..?,
au kin san halin nata
wallahi na sani yar iska ce neman mata take ni kuwa me zanyi da yar uwata mace ga namiji hajiyata
to Allah ya shirye ki kema daman zaki aure wallahi
halee kenan ta faɗa tana tashi tsaye cire kayan'ta tayi,
ta ɗauki
towel ta daura ta fita suka gaisawa da iya aliya, shiga bayi za tayi taga da mutum ciki, taja wani dogon tsaki tana cewa kai Allah ya yaye mana zama a wannan gidan, wannan wacce irin jaraba ce haka? ace mutum ya rasa inda zai yi iskancinsa sai a bayi, kai dan kuttumar ubanka ka fito,
dayake kusan rabin yan gidan suna jin hausa, gida ne me face me face you, ɗakuna goma sha biyar ne ban daki ɗaya, kuma kullum baki zuwa suke suna fita, ko da sunday yaji zagin da zulfa'u tayi masa shima sai ya rama, yace "kai ma kuttumur uban ka shege....,
dai dai lokacin haleema ta fito taji yana zagin zulfa'u, tace lallai ta samu damar da za tayi maganin dan iskan mutumin nan, cikin ɗaga murya tace "Wallahi ka fito kona janyo ka ɗan wahala kawai..,
buɗe kofar bayin yayi yace shigo idan kin isa, da sauri haleema ta dauke ido gabanta na faɗuwa, domin haka ya fito baya kaya jikinsa haihuwar uwarsa ko kunya, ita kuwa zulfa'u ko a jikinta tace "wallahi kasan halina sarai, saina shigo wallahi na kuma ci mutuncin ka....,
fitowa yayi gaba daya ashe bashi kaɗai bane shida kartuwarsa ne
salati halee tayi tace "tab amma wannan anyi dan iska wallahi...,
yace ko kema kina ciki ne
tace Allah ya kiyaye
shigewa daki sukai zulfa'u tace "kinga sunday yadda kika san gindin ayu ne dashi, kullum kana nan kana can shege a haka zai kare
kinga aunty zulfau shiga bayi dai kafin wani ya fito, kafin haleematu ta rufe bakinta tuni maman tobi ta shiga, da sauri halee ta tashi taje ta fusgota, kifa mata mari mamman tobi tayi kafin ta sauke hannunta itama ta rama tace "ke wacce irin jaka ce kina jin abin da ake, amma saboda dudewar basira kika banza kamar baki ji ba zaki shiga...,
maman tobi tace ni kika mara?
ko zaki rama ne?
zulfa'u ta fito ta shiga ta barsu nan suna fada, matan gidan ne suka taru aka bawa maman tobi rashin gaskiya...
ganin kowa ya bata rashin gaskiya ta ja matattun ƙafafuwanta ta shiga daki, zalfau ta fito haleematu ta shiga wankan itama tayi ta fito, shiga daki tayi ta ɗauki wayarta tana game batare data saka kaya ba, dama daurin gaba ne jikinta, ajiye wayar tayi ta fara wani tunani dole fa ta zama fitsararriya idan tana so mahaifiyarta da ita su zauna lafiya a gidan nan..
ba wanda ya isa ya taka su, zalfau ce ta shigo ta zauna take cewa halee tunanin me kike...?,
tace na samun mafitar zama a gidan nan ne
ta faɗa kanta tsaye batare da shakka ba ko shayi,
good girl abin da tun farko ya kamata kiyi kenan, kin ga ana yi min abin da ake yi muku....?,
ta kalleta tace a'a
to saboda an san ni ga abin da nake kuma bani da kunya, tunda har na iya baro garin mu na taho nan karuwanci, bance ki zubar da mutuncin ki ba amma ki tashi tsaye ba dan iska ko shegiyar da zaya kawo miki wargi,
halimatu kam ta dauki hudubar nan, ta kwanta rub da ciki tace "Insha Allahu daga yau sai na gyarawa ko wanne shege zama a gidan nan,
Well-done yarinya haka nakeso
sallamar ra'isa ce ta tayar da halee da take kwance, da bacci har ya dan fara dibarta, tace" ra'isa ke nake gani haka ko me?
dariya ra'isa tayi ta cire katon glass din dake fuskarta daya kusa cinye rabin fuskar, sai zabga kamshi take kamar an yi ɓarin turare, zama tayi tace sannun ku ina umma....?,
amsa wa zulfau tayi ta fita halee tace tana wajan aiki...,
to Allah ya temaka
amin ya allah ya akai ki ka gane gidan mu?
dariya tayi sosai tace " ke ma dai tun ina primary school nake biyowa ta nan fa kafin mu tashi....,
Allah sarki to ya karatu halee ta tambaye tana tana ƙoƙarin tashi
rike ta tayi tace " ina zaki kuma...,
tace zan samo miki ruwa da biscuit ne,
wallahi karki damu kafin na fito sai da naci abinci
halimatu ta koma ta zauna, daman biscuits din bashi zata karbo, Ra'isa ta kalli haleematu sosai tace kin yi kyau abinki haly, komai naki ya ƙara fitowa,
ta faɗa tana kallon shatin kan nonuwanta daya fito
dan murmushi halee tayi tace hmmm ina wani kyau, duk rayuwa ta tasa mu a gaba, ke dai Allah ya kyauta,
ayya Allah ya kawo muku mafita kawata
amin ya Allah nagode ra'isa, da kika ziyarar ce ni ma nagode wallahi,
lah bakomai Jin hayaniyar kawata, jin hayaniyar yarabawa tayi tace Bara na fita na gani meke faruwa...,
halimatu ta dauki mayafinta ta fita, turusss tayi ganin an kawo umma ko cikakken numfashi bata yi, da sauri ta karasa inda take tasa kuka ta shiga girgiza ta, ajiye mata ita sukai suka tafi, ra'isa ce ta temaka mata suka fitar da ita suka sata a mota, zulfa'u da ita suka zauna a baya tare da umma, kuka haleematu take batasan inda zata sa kanta ba taji dadi har suka isa asibiti, cikin sauri haleema tace ra'isa meya kika kai mu privete asibiti? kinsan fa bamu da halin biyan kudin da zasu cajemu,
juyowa tayi tace yanzu umma temakon gaggawa take bugata, tana buƙatar inda za a kula da ita, idan kuma muka kai ta asibitin gwamnati gaskiya sai an dade kafin su fara bata wani temako, wannan asibitin na bahaushe ne kuma be sa kudi dayawa ba.. sannan sai ya gama maka komai zai maka bill ka biya shi...,
kai kurum ta gyada alamar ta gamsu, harabar asibitin suka shiga aka fito da ita, da sauri nurse suka kamata suka sata a wani gado suna tura ta zuwa dakin bada taimakon gaggawa, inda su kuma suka tsaya daga baya, ra'isa tayi musu sallah ita zata wuce, godiya sukai mata ta tafi, wata nurse ta fito tana waya tana cewa tana bukatar taimakon likita cikin gaggawa, saboda har yanzu bata farfado ba ta fada cikin harshen turanci,
saurarawa tayi jin abin da zai ce sannan ta kashe wayar, kallon bangaren dasu haleema suke da zulfau suke tayi cikin kwantar da hankali tace, ku kwantar da hankalinku likitan yana nan zuwa nan bada jimawa ba,
kai kurum halee ta ɗaga mata cike da damuwa, shiga nurse din tayi zuwa lokacin har sun sakawa umma oxygen,
Cikin nutsuwa yake taku har ya iso kofar emergency room din, zulfa'u ce ta ɗago kanta ta dunguri haleematu dake ta faman kuka, dagowa tayi da sauri suka matsa, dogo dashi ingarman namiji ne fari tas, hutu da jindadi ya zauna mai, ko kallon inda suke beyi ba ya shiga dakin..
Zulfa'u ce tace "jar uban.. yau ake yin ta, halee kinga abin da na gani kuwa? irin wannan mijin nake fatan samu....,
wani kallo halee tayi mata lokacin ta sausauta kukan da take, kallonta tayi ta lumshe ido,
ba'a ɗauki wani lokaci ba aka fito da umma, da sauri suka bisu har dakin da suka shiga suka kwantar da ita, ɗaya daga cikin nurse din ta dubi zulfa'u tace, likita yace daya daga cikinku wata ta sameshi office,
da sauri halee tace muje, nurse na gaba tana binta abaya har office dinsa, wani irin faɗuwa gabanta yake, baƙinta dauke da sallama ta shiga, fita nurse din data rakota tayi, har ta shiga bata ga alamun ya amsa mata sallama ba sannan be dago ba, sai danna laptop yake cikin kwanciyar hankali tamkar besan da zuwan mutum a office din ba, cikin fargaba tace " doctor.....,
ɗagowa yayi ya jefeta da wani kallon tsana, domin ya gane zulfa'u budurwar sa'id ce abokinsa, da alama su suka jefa mahaifiyarsu cikin wannan halin, glass dinsa ya zare sannan yace" ke ba'a koya miki tarbiya bane ko kuwa tarbiyyar ce bakya dauka? kin wani tsaya mun akai...koda yake mutanan da suka jefa mahaifiyar su cikin mugun hali menene ma baza su iya aikatawa ba....,
sosai tayi mamakin jin hausar sa tar, ga kuma gasa mata magana da yake, cikin tashin hankali tace dan Allah doctor meke damun ummana....?,
taɓe baki yayi ya miko mata takarda yace " mace me daraja suturta jikinta take, ba ta rika rabawa gadangarun bariki jikinta ba, halinda kuka jefa rayuwar ku ya janyowa mahaifiyar ku ciwon zuciya, har yana barazana ga rayuwarta, saboda ya isa haka a dena karuwanci haka nan,
toshe kunnewanta tayi hawaye na zubowa a idanuwanta, bakinta na rawa sai dai ta kasa karyata maganarsa, amsar takardar tayi ta fita ta shiga dakin ta zauna, amsar takardar zulfa'u tayi tace " wannan fa....,
ba tare da ta kalleta ba tace maganin da za'a siyo ne.
zulfa'u tace tab ni wallahi bani da ko sisi.
haleematu tace balle kuma ni,
shiru sukai dukkan su suna tunanin mafita sai sukaji an turo kofar, da sauri suka kalli kofar shine ya shigo, yayi sallama zulfa'u ce ta amsa, kallon su yayi tare da watsa musu harara yace kun bata maganin ta sha?
da sauri suka kalli juna, da kyar halee ta iya cewa yanzu nake shirin tafiya na siyo,
kunsan irin amfanin da magungunan nan suke dashi ga rayuwarta kuwa? na lura baku damu da lafiyar baiwar Allah nan ba, da alama so kuke ku karasa ta
tashi haleematu tayi ta ratsa ta bayansa ta fita, zulfa'u ce tace kai hakuri doctor, wallahi yanzu muke shirin tafiya siyowa, amma ga halee nan zata siyo...,
fita yayi bece mata komai ba, tunda haleematou ta fita bata san inda take jefe kafarta ba, iya nema tayi neman kudin ta rasa, kantin sunday da taje sai washe baki yake, guri ta samu ta zauna ta karanto mai matsalarta, murmushi yayi yana lashe baki kamar wani maye, yace badamuwa bani kayan kudi na baki....,
tashi tayi tana kuka tace " wallahi dana kwanta da arne gwara na kwanta da musulmi, idan ma bada kan nawa zanyi...,
banza yayi mata yaci gaba da shan lemonsa da biredi, tun ƙarfe 2 ta fita ba ita ta dawo asibiti ba sai shida, karo suka ci yana ƙoƙarin fita ita kuma ta shigo, da sauri ta matsa hawaye duk ya bushe a fuskarta bakinta ma ya bushe, ƙasa tayi da idonta kwalla ta cika shi, wucewa tayi tana shiga taga aunty zulfau na zaune ta zuba uban ta gumi, dagowa tayi tace halee kin samo?
tayi shuru sai hawaye, tace Wallahi duk inda kike tunani naje ban samo ba
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un gashi yanzu ya ƙara gwada ta tare da yi mata scanning sai an mata aiki miliyan ɗaya
zaro ido tayi tace " wayyo Allah Allah ka zama gatan mu...,
tashi zulfau tayi tace" halee ba mu ga ta zama ba muje gun doctor din gobe ake so ayi aikin...,
binta tayi a baya har office dinsa saidai baya nan jiransa sukai yi halee ta jingina da bango turus yayi ganin su cikin hade rai yace " ku matsa mini zan buɗe office ...Dina,
ba musu zulfa'u ta matsa mai shiga yayi bin yasan sa sukai suka zauna akan kujera zulfau tace "

doctor neman alfarma muka zo yi, wallahi mun buga mun buga ko rabin kuɗin nan bamu samu ba, DAN Allah ko zaka iyayi mata bashi, ko share share ne haleema tayi maka a asibitin nan har ta gama biyan kuɗin umma...,
Shiru yayi yana tunani can yace bani da bukatar ɗaukan ma'aikata, amma zan taimakeku saidai akwai sharadi, sharadin kuma contract ne na aure, za muyi aure saboda mahaifina, wacce nake so tana karatu a UK kuma sai ta gama za muyi aure, zaki dinga kula da mahaifiyata da duk wasu aikace-aikace na gidan, wannan aikin kaɗai zaki yi mun zuwa nan da wata 12, shekara daya kenan kafin jalila ta dawo muyi aure,
amma bayan shi ba komai, kar kiyi tunanin kuma ke din matatace a a zaki zauna ne a matsayin baiwa, saboda bazan iya ma'amalla da mazinaciya ba fasika....,
da sauri zulfa'u ta kalli haleema domin jin me zata ce, tashi tayi jikinta na rawa ta bar office din, bin bayanta zulfa'u tayi har suka koma dakin da ummah ke kwance, kuka Haleema ta sa ta kifa kanta a ƙarfe gadon da umma ke kwance, ji tayi an shafa kanta da sauri ta dago, cikin murya irin ta marasa lafiya umma tace haleema me yace muku.?,
kafin tayi magana xulfau ta riga ta faɗa mata komai, sai dai ta boye mata auran contract ne,
zulfa'u idan ita bata da hankali kema baki dashi? haleema ina zaki samo wannan kuɗin? bana fatan ki faɗa mummunar hanya dan haka zulfa'u kar ya fasa, maza kuje ku ce kun amince,
ko dan umma ta rayu ta yadda zata sa daukar da rayuwarta, tunda ta taso take dawainiya da ita bata san kowa ba bata san dadin uba ba, ita kaɗai ta sani to ta zaɓi ta rayu ita ta mutu, tashi tayi xulfa'u ta rike hannun ta suka koma office din daktan, a wannan karon sun tarar da abokin sa sai hira suke, gaisawa sukayi Faisal yace Bara na dan baku waje ko,
ba tare daya kalli su ba yace" noo zauna ba private issue bane...,
zama yayi yayinda su zulfa'u duk sun muzanta, cikin rawar murya tace mun amince....,
takarda ya dauko yayi rubutu ya miƙawa Faisal shima ya saka hannu, sannan Faisal ya dawo mai da ita, wani kallo yayiwa Faisal din batare da yayi magana ba, miko musu yayi ba tare da sun karanta ba suka saka hannu, yace baku karanta ba ko baku iya karatu bane?,
Cikin tsoransa haleema ta kalli zulfa'u, domin iya karta primary, taso ta cigaba karatun ya ki yiwuwa umma takwanta rashin lafiya, shine dalilin fara aikinta, to gara ita ma akan zulfa'u da batayi ko primary din ba, ido ta kurawa rubutun cikin sanyin murya kamar koda yaushe tace" ni Sufyan Yusuf matawalle zan yiwa A'isha aiki akan naira miliyan daya bashi, da zumar yarta zata biyani ta hanyar yimin aiki na tsawon shekara ɗaya, ba tare da hutawa ba ko zuwa ganin gida,
yace madallah kuna iya tafiya, bayan sun fitane faisal ya kalle shi yace haba Sufyan, tunda har kasan basu dashi me zai sa kayi haka? kalli yarinyar nan daga gani basu dashi, gwara ma dayar ba alamun babu a tare da ita jibi kayan jikinta, tunda har kasan ba sonta kake ba be kamata ka aure ta ba....,
daktan ya dan hassala da maganganun faisal yace, waccan da ka gani karuwar sa'id ce, da alama ya da kanwa ne, kar kai mamakin itama kanwar haka take, da ace mutanan kirkine baza su yadda da wannan contract din ba, duk hanyar da zasu subi zasu bi suga sun samo kudin, idan ka lura basu da dangi ne yanzu haka an gaji da halinsu, shiyasa ka aka sakar musu ragamar komai
faisal yace kada kace haka sufyan, mu dinga kyautatawa dan adam zato, idan kasan waccan karuwa ce ita wannan da baka santa ba kuma baka taɓa ganinta ba fa? Ubangiji yana saɓa halaye, dan wannan bayaji suna tare ba hakan yana nufin shima bayaji bane, yace amma kasan abokin barawo barawone ko? ya faɗa yana rubuce-rubucen sa.

koda suka koma wajen ummah duniyar tunani ta lula, da alama dai yasan zulfa'u kam, ta kalli zulfau tace anti zulfa'u kinsan shi ne?
ajiyar zuciya ta sauke tace" sai yanzu na gane shi abokin Sa'id ne saurayina, amma wallahi yanzu ma mun rabu, da ace muna tare da tuni kudin nan shi zan tambaya...bamu taba haduwa dashi ba sai dai kamar ina ganin hoton daktan a wayarsa,
dan motsi umma tayi da sauri haleema ta taso tare da mata sannu,
dakyar ummah ta amsa da yauwwa,

washe gari suna zaune sukaji an turo kofa, bata ɗago ba jin kamshin turaran sa tasan shine, shida wata nurse suka shigo ta takure jikin bango tayi kasa da kanta, kallon ta zulfau tayi tace " halee zan fita zuwa gobe zan dawo..,
cikin sanyin murya da tafi ta ko yaushe sanyi tace" to nagode Allah ya saka da alkairi...,
ta fita taja musu kofa a kuma daidai lokacin ne wani nurse namiji ya shigo ya fara tambayar umma ya jikin nata, ta amsa masa da sauki, duk abin daya tambayeta tana bashi amsa gameda da yanda takeji, fita yayi nurse din tare da mata fatan samun sauki nan kurkusa.
UNITED KINGDOM
Ƙwance take a kan wani makeken gado, wata baturiya ce ta fito daga toilet ba kaya a jikinta, hawa gadon tayi ta kwanta tana shafa jikin jalila, itama ta fara mayar mata da martani, data farajin ta hau kan network gaba daya ta birkice, babban burin ta taji sun manne da juna, ware kafarta tayi tana sarrafa mata na'urarta, ai kuwa sakonni ta ko ina suka fara

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment