Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da file d'in gida yanzu fa k'arfe 7:30 Dare ya Fara Kuma Anfara Kiran magarib, sannan bakada lafiya"



.

"Nasani sagent kawai kayi Abunda nace ban motar katafi Abunka kawai kai,"



"Sanin waye ogerh d'insa yasa bai sake magana ba, Yana Kai kansa gida ya tsaya ya sauka yabashi key d'in motar Yana fad'in "Allah ya tsare ogerh" yawuce




Saida yafara shiga masallaci yayi Sallah sannan yakoma office, file ya d'auka yafara rubutu Akai,


Yajima Yana nazarin Case d'in sannan yafito sukayi sallama da masu night duty yafice. masallaci ya tsaya Dan gabatar da Sallar Isha,.






"Ke khausar kina nan kina bacci Abinki ko? Lalle yaran zamani ba'asan Ciwon kaiba Ace mijinka yafita tinsafe har dare baidawoba Amma har kikeda idanuwan bacci"





Mik'ewa tayi daga baccin da yafara d'aukar ta, bugun k'ofar da fad'an da Umma keyi yatada ta,



K'arasowa bakin k'ofar tayi tana fad'in"A'a wallahi Umma bansan baccin ya d'auke ni bane Ina k'arasa sallah ko tashi banyi ba baccin yafara fisgata,"




"Ke dalla can shasha Ai Dole kiyi bacci tinda bakisan zafinsa ba," Mtswwww dogon tsaki taja tareda barin wurin,.





Zama d'aya daga cikin kujerun palourn tayi tana zabga tagumi itadai bata san me ta tarewa uwar mijinta ba Kullum cikin masifa take koda laifin ko babu, gasu gida d'aya da babbar Aminiyarta Kuma Matar Abokinsa amma bata Bari taje can parts d'insu Humaira danyin fira, gwandama kwanakin baya Humaira d'in tana Yawan zomata Ayanzu basunan mijinta yaje k'arin karatu a Dubai Anan tahuta da mitar Umma itakam gatanan tana fama,


Duba Agogon bangon tayi ya buga k'arfe 11:00 inda sabo yaci Ace tasaba da halin Annur Amma Koda yaushe tanajin zafin jimawarsa waje,.




Umma Nata babbaka fad'a tadawo wajen Balcony d'in tazauna itak'adai sai maigadinsu datake hangowa Yana zaune danshikam badai bacci ba yanata kora shayinsu na buzaye,.





Shikuwa bayan fitowarsa daga masallacin yaji k'arar shigowar sak'o bud'ewa Yayi yaga sak'o Kamar haka......


""" *D.S.P ANNUR* Kada Kashiga hurumin da banaka ba domun rawar kanka yafara yawa kada Kashiga Abunda ba ruwanka itama haka tayi saita fuskance hukuncin mu ka kula""""




Yajima yana maimaita karanta sak'on tareda k'arfin halin Kiran layin Amma switch off

Dik k'okarinsa ganin yasami wani Abu Akai Amma baisamu ba,



Towaye wannan kuma????



Nidai Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱 banace ba ina tare dakai fa nida readers





Anan ne yak'ara b'ata Lokaci, duba wayarsa yayi ganin 11:00 Saida zuciyar sa tabuga sanin Yashiga hakken Matar sa, ga mahaifiyarsa da komai dare Bata bacci saiya dawo, Abu d'aya yatuna hankalinsa ya kwanta shine gobe Saturday Yana gida,. Da saurin Yashiga motarsa yanufe gida.,





Ranta yafara b'aci da suya Hawaye suka soma zarya Kan fuskarta ko Abinci Bata iya ciba gashi wayarta tafashe kusan kwana biyu kenan tanata binsa Amma yak'i siyo mata,.



Hong yayi Aka bud'e masa Yashiga ganin Umma waje yasa cikin sauri yak'arasa har k'asa ya tsuguna Yana gaidata




"Meya tsaidaka haka Babana bayan kasan kanada mak'iya,"?




"Wallahi Ummana wani sabon Case muka samu Wanda yake hannuna shiyasa,"





"To babana Arik'a kulawa Allah yataimaka Saida safe kaje kaci Abinci, ka kwanta dare yayi Sosai,"




"To Ummana Allah yatashemu lafiya ga Wannan" leda ya Bata ta Ansa tana masa Addu'a tawuce


Komawa mota tayi yad'auko d'ayan ledar Yashiga nasu part d'in,


Haske dik ya gauraye palourn Amma baiganta nan ba,


Rufe k'ofar yayi Yana sallama had'ida k'arasa Shiga palourn



Ansa sallamar tayi kafin tace"sannu da zuwa, ga Abincinka can Kan daning"
Tana ida maganar tawuce d'akin ta





Kasa matsawa gaba Yayi Balantana baya, saka makon ganin Hawaye Kan fuskarta muryarta ma ta tabbatar masa Tasha kuka yau d'in,


Wurin dining yaduba Abincin Yana Nan da yawansa hakan ya tabbatar masa da bataci Komai ba Kenan...........




_Kuyi hak'uri wallahi Inada matsalar idanuwa_





_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_




WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948
[2/4, 9:01 AM] My Number: *D.S.P ANNUR.πŸ’«*
_PAID BOOK #300 ONLY_



*FEBRUARY (2) 2023*



_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱..._



```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN πŸ’ž ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA (18) SAURAYINA (19 D.S.P ANNUR PAID BOOK..==..... And Other's BUT NOW (19) D.S.P ANNUR PAID BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱```




_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken *D.S.P ANNUR.* Ina fatan yabada darussuka ga kowacce macce Kai hardama mazan baki d'aya Allah ka k'ara shiryamu dukanmu_



*INAYIN LITTAFAINA BADAN NEMAN SUNA KO D'AUKABA KAWAI INAYINE DOMUN BADA DARASI DA FAD'AKAR DA AL'UMMA BAKI D'AYA....... AKODA YAUSHE ALK'ALAMIN MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱 BAYA RUBUTA SHIRME KO BATSA KO LALATA RAYUWAR AL'UMMA SAIDAI INA K'OKARIN WAYAR DA KAN AL'UMMA DAMA DAWO DAMU KAN HANYA MADAIDAICIYA ALLAH KA TSAREMU DA AIKATA AIKIN DANA SANI.. INASONKU MASOYANA ADIK INDA KUKE NID'IN CE DAI TAKU HAR KULLUM MAISON GANIN FARIN CIKINKU MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱*





*Kwanaki sai gudu suke shekaru sai shud'ewa suke inda mutuwa take riskar kowanne bawa, Rayuwa sai ficewa take inda mutuwa tana maye gurbinta, ya Allah πŸ™ kajik'anmu tinkan mukoma gareka, ya Allah kasomu kasa Asomu, ya Allah kaimuna k'arshe Mai kyau πŸ‘Œ, Allah karabamu da MAK'IYAN mu na fili dana bayyane, ya know Wad'anda suka rigamu komawa gareka Allah kajik'ansu kaimusu gafara ya Allah,. Ya Allah kaimuna maganin Wad'annan masifun da fitintinun, Allah kabamu zaman lafiya da Arziki Mai Amfani, ya Allah Kashiga tsakanin nagari da mugu, ya Allah kabamu shuwagabanni nagari masu tsoron Allah wad'an da zasu dakatar da Wannan b'arnar da Ake Aikatawa,ya Allah kaimuna maganin Wannan tsananin damuke ciki, Ya Allah kashiryemu, ka Kare Idanuwanmu daga kallon Haram, ya Allah katsare hannuwanmu daga rubuta had'ida rubuta Haram, Ya Allah katsaremu da cin Haramun.... Ya Allah Idan mutuwar mu tazo Kasa mucika da imani tareda kalmar=====LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADU RASULILLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM=== ALLAHUMMA AMEEN YA ALLAH🀲🀲*




_Yau 1/2/2023 First February nafara wannan littafin Allah ka k'addareni dagamashi lafiya AMEEN YA ALLAH_




_SECOND TO THE LAST FREE PAGE IN SHA ALLAH_




_FreeπŸ…ΏοΈ16 to 20_




.... Tabbas Yasan khausar tanada hak'uri Kuma tanada juriya kusan shekara 2 da Auren su Amma baitab'a ganin fushin taba koda Ranta yab'aci takan danne Domin kawai nemamasa nasa farinciki gashi sama da shekara d'aya da mutuwar iyayenta yakan tausaya mata Sosai, gashi wannan Aikin nasa ya Hana yabata farinciki yau harta Kai ganuna fushinta,



Cikin sanyin jiki yak'arasa bakin k'ofar d'akin ya tura Amma rufe d'akin,



Jiyo sautin kukanta yayi jikinsa yak'ara sanyi,


Cikin sigar lallashi yace"My dear Dan Allah kiyi hak'uri ki bud'e k'ofar kinji,"



Shuru batako motsaba kawai tacigaba da kukanta ne Domin shine Kawai zatayi tasami salama Aranta




"Matar *D.S.P ANNUR* kada kiyi fushi da gudan jininki mana nasani ban kyauta ba Amma Dan Allah kiyi hak'uri ki bud'e k'ofar kinji, idan baki bud'e ba, nikaina bazan samu salama ba, Kuma bazanci Komai ba,"




Cikin muryar kuka tace"katafi karabu Dani tinda Aikinka yafini mahimmanci, saboda Allah ANNUR Ace kafita tinsafe Wai har 11:30 zuwa 12:00 sannan zaka dawo bayan kasan kanada Mata fisabilillah kamun Adalci? Gashi Wannan wayar ma kak'i siyamun bayan kanada Arzikin siyenta, Kuma Koda yaushe kada kifita bawanda yake zuwa Inda nake Tinda Nima bana zuwa why Annur
Idan kadaina Sona kawai ka sallameni na k'ara gaba Wallahi Nagaji Annur," kukan da yaci k'arfinta ne yasata yin shuru.





Rawa jikinsa ya d'auka idan da Abinda yafi firgitashi baiwuce Ace yarabu da Khausar ba Yana Mata sonda shikanshi baisan Adadin shiba,



"Naji nad'auke laifuka na, kitaimaka ki bud'e kada muyi kwanan bak'in ciki kinji my wife"



Ganin batada niyar bud'ewa yasa yakoma Kan kujerar palourn ya zabga tagumi Kansa har wani ciwo ciwo yake masa,


Wata dabarar ta fad'omasa da saurin yamik'e yashige d'akinsa baijima ba saigashi Yasake fitowa d'auke da tarin makullai a hannunsa yazo yafara gwadawa cikin sa'a kuwa yasamu d'ayan yayi take d'akin ya bud'e da sauri Yashiga ciki, cikin sauri yak'arasa Kan gadon Yana janyota jikinsa,




K'okarin fisgewa take tana fad'in"karabu Dani Ni ka k'yaleni Annur"



Ganin batada niyar tsayawa yayi saurin had'e bakinsu guri d'aya,




Zazzafan kisses Yashiga aika mata tako ina hannayensa kuwa suna neman mafaka cikin rigarta inda Still bakinsu Yana had'e,.


Mutsu mutsu take tana neman k'watar kanta Amma takasa saboda ba k'aramin rik'o yamata ba,



Kuma gashi yajima Bai nemeta ba, shiyasa dik yawani haukace mata,


Still Bata daina neman k'wace kanta ba dik da itama tana buk'atarsa Amma yau saita nuna fushinta dole ya gyara,




Da k'arfi tasamu ta tureshi Takoma palourn ta zauna kan kujera tana maida numfashi,


Had'ida share hawayenta Domin yaune Karo na farko Data hanashi hakkensa.



Tana fita d'akin ya kwanta Saboda wani wahallen ciwo da mararsa tafara masa, yajima kwance kafin yasami relief, yasani yakaita mak'ura ne shiyasa


Ahankali yafito Kan kujerar ya hangota zaune tahad'a Kai da guywa tana kuka



Cikin sanyi ya matso inda take had'ida yin Neel down da guywarsa k'asa Yace cikin wani irin murya"kiyi hak'uri kidaina kukan tashi kici Abinci please banason kukan"



Batace Masa Komai ba Kuma Bata motsa ba


Mik'ewa Yayi ya d'auko Abincin yazuba dakansa yakai bakinta



Kaucewa tayi tareda cewa"nafa k'oshi Kuma ga dare yayi Ina Jin bacci,"
Mik'ewa tayi danufin barin wurin Amma saitaji yarik'o hannunta had'ida Mata nuni data zauna,



Ba musu ta zauna
Abincin yahau bata saida ya tabbatar ta k'oshi sannan ya d'auke ta cak Kamar yarinya yakaita kan gadon had'ida rufa mata barko sannan Yashiga tolet tanajinsa yayi wanka harya shirya sannan yazo ya kwanta Kan gadon, baimata Komai ba dan ya fahimce fushi take Sosai Dashi



To ASSUBAH TAGARI nidai Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱 nayi
Nan....






**************



"Ranka yadad'e Allurafa na Shirin tono garma dan wallahi shegen yaron Nan yanason ganin bayanmu"




"Habadai Alhaji Musa kada k'aramin k'waro ya d'aga maka hankali mana, mema zaiyi wai,"




"A'a fa tanimu wallahi nikaina gani nake da matsala, yaron Nan baida tsoro gashi da yawan ibada ga matar Nan tasa itama Kullum cikin ibada Tayama zamu kaishi k'asa,''




"Yarda muka Kai mahaifinsa da y'ar uwarsa Haka shima zamu kaishi" cewar Alhaji sani



"Amma kuwa idan har munason yin wannan nasarar to Dole mufara rabashi da matarsa," cewar Alhaji tanimu




"Hakane maganar ka Domin kuwa itace lagonsa, Dan Haka zamusaka A satota kuma muyi tsafi da ita," cewar Alhaji musa



Dariya Suka saka gabaki d'ayan su had'ida watse zaman..




Tawagar matsafa kenan, Alhaji musa, sani, tanimu sune babbar tawagar sai Sauran Abokan San duniyarsu,


Sunriga sunb'ace da neman duniya cikinsu wasu sunbada y'ay'ansu wasu sunbada iyayensu wasu matansu dadai sauransu,



Mutuwar Humaira ma kusan sune silar kwashe jininta wanda da taimakon k'awarta Hajara, Wanda ba Wanda yasan Hajara tana cultism koda kuwa y'an gidansu....



Hajara tinda ta bud'e Ido taga Annur taji mugun sonsa Aranta shikenan tafara neman tsafaceshi Saidai tarasa damar hakan saboda baya wasa da ibada, Amma tayi nasarar wargaza bincikensa kansu Wanda dik tamantar da kowa Kan Case d'in...........





_kuyi manage banada chagy Wallahi_







_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_



WhatsApp group 07064904617 or call 07031012948

*D.S.P ANNUR.πŸ’«*
_PAID BOOK #300 ONLY_



*FEBRUARY (2) 2023*



_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱..._



```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN πŸ’ž ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA (18) SAURAYINA (19 D.S.P ANNUR PAID BOOK..==..... And Other's BUT NOW (19) D.S.P ANNUR PAID BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱```




_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken *D.S.P ANNUR.* Ina fatan yabada darussuka ga kowacce macce Kai hardama mazan baki d'aya Allah ka k'ara shiryamu dukanmu_



*INAYIN LITTAFAINA BADAN NEMAN SUNA KO D'AUKABA KAWAI INAYINE DOMUN BADA DARASI DA FAD'AKAR DA AL'UMMA BAKI D'AYA....... AKODA YAUSHE ALK'ALAMIN MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱 BAYA RUBUTA SHIRME KO BATSA KO LALATA RAYUWAR AL'UMMA SAIDAI INA K'OKARIN WAYAR DA KAN AL'UMMA DAMA DAWO DAMU KAN HANYA MADAIDAICIYA ALLAH KA TSAREMU DA AIKATA AIKIN DANA SANI.. INASONKU MASOYANA ADIK INDA KUKE NID'IN CE DAI TAKU HAR KULLUM MAISON GANIN FARIN CIKINKU MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱*





*Kwanaki sai gudu suke shekaru sai shud'ewa suke inda mutuwa take riskar kowanne bawa, Rayuwa sai ficewa take inda mutuwa tana maye gurbinta, ya Allah πŸ™ kajik'anmu tinkan mukoma gareka, ya Allah kasomu kasa Asomu, ya Allah kaimuna k'arshe Mai kyau πŸ‘Œ, Allah karabamu da MAK'IYAN mu na fili dana bayyane, ya know Wad'anda suka rigamu komawa gareka Allah kajik'ansu kaimusu gafara ya Allah,. Ya Allah kaimuna maganin Wad'annan masifun da fitintinun, Allah kabamu zaman lafiya da Arziki Mai Amfani, ya Allah Kashiga tsakanin nagari da mugu, ya Allah kabamu shuwagabanni nagari masu tsoron Allah wad'an da zasu dakatar da Wannan b'arnar da Ake Aikatawa,ya Allah kaimuna maganin Wannan tsananin damuke ciki, Ya Allah kashiryemu, ka Kare Idanuwanmu daga kallon Haram, ya Allah katsare hannuwanmu daga rubuta had'ida rubuta Haram, Ya Allah katsaremu da cin Haramun.... Ya Allah Idan mutuwar mu tazo Kasa mucika da imani tareda kalmar=====LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADU RASULILLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM=== ALLAHUMMA AMEEN YA ALLAH🀲🀲*




_Yau 1/2/2023 First February nafara wannan littafin Allah ka k'addareni dagamashi lafiya AMEEN YA ALLAH_



_LAST FREE PAGE 21 TO 30 IN SHA ALLAH SATURDAY 4/2/2023 FEBRUARY_




_PAGE πŸ…ΏοΈ 21 to 30_


D.S.P ANNUR
Complete Hausa Novel

......"Sanin kinason Anwar shiyasa mukeson kimana Wannan Aikin," cewar Alhaji tanimu




"Taya kake tinanin nida kaina zanbada gudun muwar cutarda Abunda nakeso,"? Cewar Hajara




"Maganar banza kike wane irin jind'ad'i ne bamu bakiba, ke yanzu Dan munzo neman buk'ata gareki saiki k'i? Wallahi Baki isaba Hajara kokibi umarnin mu komu kasara hadda Taki rayuwar Domin a tsarin k'ungiya ba Wanda ya isa yamuna taurin kai,"




"Wallahi Koda zaku kasheni bazan Bari wani Abu yasami Annur ba Amma zanbada gudun muwa wurin ganin Anhallaka matarsa Amma bandashi,"




"Kunga enough eh munason kishiga aikin wurin samun dam shiga cikin jikin matarsa harta yarda dake daga saiki Sato Mana ita zamu hallakata inda ke Kuma saiki Samu Annur d'in," Cewar Alhaji musa



"Amma Alhaji musa Bai,"..............




D'aga masa hannu yayi Alamar dakatarwa kafin yace" nine shugaban nagama magana Hajara zaki iya tafiya,"



"To Shugaba Nagode Kuma Nanda kwana biyu Aiki zaiyu" ficewa d'akin taron tayi




"Sainake ganin Kamar kayi kuskure idan kaduba *D.S.P ANNUR* mukeson kaiwa bawai matarsa ba Amma meyasa zaka yanke hukuncin barin shi bayan kasan muddin Yana raye burinmu bazai tab'a cikaba,"




"Matsala tadakai k'wak'walwar ka bataja, shin Taya mukaga bayan mahaifinsa Bata hanyar yudara ba? Taya muke neman zautashi da mugayen mafalkai? Babbar matsalarmu matarsa Domin Koda yaushe itace ke d'aurashi kan hanyar Ubangiji, yayinda zamucigaba da sakawa mahaifiyarsa nauyin Baki kada tafad'a Masa komai, itakuwa Hajara muda kanmu zamuga bayanta Domin dodo zamuba jininta data Gama muna Amfani,"



Shek'ewa da dariya sukayi suna Amanna da shawarar shugaban nasu,"...

KU DANNA HOTON DAKE NAN KASA DON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN

https://t.co/1snEFZGmFU




********************





Sam baisamu bacci Daren jiya ba Domin damuwa tarufesa nafarko fushi da matarsa take dashi na biyu dik yamanta komai case d'in Yana k'ok'arin Tina wani Amma yakasa Tina Komai, Yana Haka har Akakira Sallar Assubah yamik'e Yana watsar da tinanin Dan kansa yafara Ciwo



Bayan yagama shirin zuwa masallaci ya tadata tayi Sallah shikuwa yafice masallaci,.





Saida haske yafara bayyana sannan yadawo gurin mahaifiyarsa Yashiga Suka gaisa


Kallansa tayi Tace"Wai meke damunka Babana cikin kwanakin Nan dik kabi ka rame musamman daga jiya zuwa yau,"




Gyara Zama yayi Yace"Amma Umma nakai mizanin da zansan gaskiyar labarin Abunda yasami babana da k'anwata,"



Shuru tayi kafin tace"sanin komai baida mahimmanci gareka Domin Wanda ya mutu bazai dawoba babanka yariga ya mutu,"




"To waya kashe su Wai? Meyasa nake ganinsu A mafalkaina? Wai Kodai inada tab'in k'wak'walwa ne,"?



"A'a babana bako d'aya Amma nikaina narasa dalilin kasa fad'a maka Amma dai kacigaba da Addu'a sannan Nan kusa gaskiya zata bayyana,"



"To Ummana Allah yasa," barin part d'in yayi yanufo nasa




Tagama shirya daning tana kitchen tana wanke-wanken kayanda ta tab'a tajiyo shigowar sa har kitchen d'in da sallama

Ansawa tayi batareda tajuyo ba Tace "sannu da dawowa"



Baiyi magana ba yak'arasa inda take had'ida rungumarta ya d'aura kansa Abayan ta,



"I'm really sorry my love, kidaina ignoring d'ina nakasa jurewa,"



Ita kanta tana Azabtar da kanta ne gashi tanajin wani iri Ajikinta


D'aura hannayenta tayi Kan nasa tace,"shikenan yawuce mijina na hak'ura kaima kayi hak'uri kaji," tak'arasa maganar tana shigewa jikinsa



Murmushi Maisauti yasaki had'ida sunbatar goshinta sannan Yace" bakimin komai ba my dear nine da laifin Kuma Ina dad'a bada hak'uri,"





"To na hak'uri yanzu sakeni nakaiwa Umma Abinci nadawo muci namu ko,"?




"Bani kawai Zan kaimta kishiyar namu,"



"To ai bangaisa da Umma d'in ba kabari naje,"



"Zakije ne ai yanzu dai Ayi Abunda nace kawai,"




"To yallab'ai,"




"Hahhhhhhhh yallab'ai nadawo Kuma" ya Anshe Abincin ya kaimata



"Au babana Kaine kadawo mai yawon kawomin Abincin,"?



Yana Sosa Kai yace,"a'a Ummuna kawai ganin Aikin dayawa ne shiyasa nace tabari nakawo Amma zata zo ai,"





"Allah ya kyauta, nidai nafara Gajiya yarinya batako Haihuwa nagaji da zama da ita wallahi,"



Shuru yayi baice Komai ba Saida tagama fad'an sannan yamik'e yafice





Wannan shine mak'asudin tsanar Khausar da Umma tayi ganin shekara 2 Bata Haihuba,.




Bai nunamata Komai ba tareda ita sukaci Abincin suna gamawa yace"jeki shirya kid'an rakani wani gun,"


Cikin Murna Tace,"dagaske mijina yau Dani zaka fita,"



Yana murmushi ganin Murna kan fuskarta Yace"Sosai kedai Yi sauri Kona tafi na barki,"




"Ah Yanzu zanzo my dear"




Cikin k'ank'anen lokaci harta tashirya saidama tajirashi



Kalan dressing d'in ta yayi shima farin yadi yasaka sunyi kyau


Tare suka fito suka biya Inda Umma



"Ina kwana Umma" Cewar khausar




"Da bankwana ba ai bazaki ganni ba, Wai ma dan walak'anci tin sanda safiyar ta waye sai Yanzu zakizo gaidani, da uwarki ce ai bazakiyi jinkiri ba,"




Kanta nak'asa tace"Dan Allah Umma kiyi hak'uri wallahi nad'an makara ne,"



"Eh lalle ai dole ki makara dama can ke sakarya ce baki Aje Komai ba sai bacci"



Cikin k'osawa da kalaman Annur yace,"Umma Ayi hak'uri baza'a K'ara ba in Sha Allah Yanzu zamu fita ne,"





"Shasha sakarai dik tabi ta dabaibayeka yarinya gata juya ba haihuwa Amma ka kasa rabuwa da ita Nidai nafara gajiya, gangalin ba Ainatafi k'wari , saikun dawo,"



Saurin mik'ewa tayi tafice hawaye na biyo fuskarta



Cikin Azama yabiyota hak'uri ya Fara bata yana lallashinta


Daurewa kawai tayi Amma Abun yamata zafi



Babban mall ya kaisu inda yazab gamata siyayya harda waya


Murna takeyi tana Masa godiya



Daidai hanyar fitowarsu Suka had'u da Hajara,


Ganinsu cikin farinciki hakan ba k'aramin haushi yabata ba, cikin sauri tasaka hannunta jaka tashafo wani magani cikin dabara tayi baya Kamar zata fad'a Kan Khausar cikin saurin itakuma tad'an rik'eta take tasamu damar shafamata wannan maganar ga hannunta



"Ah subhanallah ke lafiya,"? Cewar Anwar Yana rik'o Khausar datayi wani baya Haka Kawai bayan had'uwar jikinsu




"Bakomai yallab'ai kawai fa taimakona tayi, gaskiya kinada kirik'i sister Nagode in badamuwa kiban number ki,"





Wani irin haushi taba Annur taya haka kawai zata buk'aci number ta daga taimako?




"Ah bakomai saidai kiban Taki domun Yanzu muka siye Wayar,"



"To gashi sister Dan Allah kimin magana kinji,"



"In Sha Allah zanmiki nagode"




Wucewa sukayi Annur Yana fad'a kanme zata Bata number ta...............................





```HUNMMMMMM YANZU WASAN YAFARA SAIDAI KASH ANAN KUMA FREE PAGE YAK'ARE IDAN KINA KANA BUK'ATAR KASANCEWA DA WANNAN LITTAFIN TO KA HANZARTA BIYAN 300 D'INKA KAWAI DAN SANIN WAD'ANNAN CHAKWAKIYAR................


Shin khausar zata Sami cikin kuwa ta fita hantarar uwar mijinta?



Shin D.S.P ANNUR zaisamu damar Sanin gaskiyar?



Shin su Alhaji tanimu zasuyi nasara?


Hajara zata samu cikan burinta na Auran Annur kuwa?


Shin Annur zaisan gaskiyar?



Mezai Aikata idan yasan gaskiyar?



Shin zasu sami nasarar sace matarsa kuwa? Idan sun d'auketa zasu kasheta? Ko zata sira ne?

Wanne Hali Annur zaishiga bayan idan Aka d'auke matarsa?



Shin mesukama mahaifinsa?



K'anwarsa da gaske tananan raye kuwa??


To Nimadai Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱 banace ba Domin sani kawai muhad'e a NEXT PAGE da 300 Amma...........




_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_




WhatsApp number 07064904617 call 07031012948

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment