Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa ya k'yaleta....✍️✍️✍️.


Mom Islam ce

*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 31_32



_____Suna sauka cikin ikon Allah saiga wani bature yazo yake cemusu ance yanuna musu masaukin su Humaid saboda rashin yarda yace "saiya kira dady aikuwa yana kira dady 'yace”nine na turoshi dafatan kun sauka lafiya ?lafiya Lou Humaid yace”daganan suka shige motar wanan bature ,itadai Khadija gajiyace ta buwaye ta dan burin ta bai wuce taganta tana hutawa ba ,wani katafaren hotel suka sauka Khadija ce tazaro ido tace"nifa tsoron jajayen fata nakeyi wallahi kar azo angama cinikinmu, Humaid ne ya gimtse dariyar sa shikuwa wanan Bature babu abinda baijiba wanada Khadija tafad'a kasancewar yana mu a mula musulmai sosai amma shi Christen ne saboda baya sallah ,door bell baturen ya danna k'ofar ta bud'e da kanta zaro ido Khadija tayi tace”to Allah gamu gareka tana tafiya tana sambatu shikuwa Humaid ko kallonta baiyi ba ,direct wani rantsatsen step naga sun hau d'aki mai number goma suka shiga ,Humaid ganin ba'ayi maganar komai ga shuwagabanin hotel d'inba yasashi cewa to sukuma masu hotel d'in anbiya sune?eh baturen yace”tun jiya dadynku yayi komai ,godiya Humaid yayimai mutumin 'ne yace”sunanan Joseph barin baka number ta musayar lamba sukayi daganan Joseph yace”suyi wanka su huta za'a kawo musu abinci .


Tana shiga d'akin Humaid ma yashigo tunda tashigo take kallon d'akin kyau tsari gakuma nerorin da 'aka kashemai tabb tace ”lallai wasu basusan zafin kud'i ba ,Humaid da gajiya ta tarumai yace”to sannu 'uwarsu zaki 'iya fita ki sanar musu ,ko kallon inda yake batayi ba tashige bathroom wanka tafarayi kasancewar akwai sabon sabulun wanka da sabbin brush da man goge baki saida tayi wanka sanan ta d'auro alwalah tafito ganin har bacci yafara d'aukar Humaid yasata kurma uban ihu tace”wayoo nashiga uku ,a firgice Humaid ya farka yana salati ganin Khadija tayi shuru yasashi cewa komai aka had'a da jaki saiyyaci kara ,zaro ido tayi tace”waye jakin nikake kira da jaki, murmushin takaici tayi tace ”d'an adam mai mance hallacci babu komai kasan ba'acin bashina ,mamakinta yakeyi dahar take gayamai maganganu san ranta saboda taganshi a kwance bazai 'iya 'aikin k'arfi ba yasa takeyimai wulak'anci ,dariya yasa lokaci d'aya kuma yace”yaro baisan wutaba saiya taka."




K'yaleshi tayi tafara sallah tana idarwa ta dubo al qur'anin data taho dashi tafara rera karatu , idon Humaid a lumshe kamar mai bacci ya bud'e ido yana saurarrar karatun Khadija jiyakeyi kamar karta dena ,bayan takammala karatunne ta mik'e tayi gurin kayansu bud'e jakarta tayi ta dubo atamfa rigada skirt mai adon flowers green zatasa kayan ta tuna 'aifa Humaid na d'akin juyawa tayi tace ”malam zaka iya juyawa saboda zansa kaya karkuma 'a kalleni ehe, juyowa Humaid yayi yace”wanan banzan jikin'naki mezan kallah jikinda kowa yagama ganinsa ,tanajin takaicin wanan kalmar amma 'akwai lokacin ramako, d'ibar kayan tayi takoma bathroom ta sanya sanan tazo tana shafa mai kasancewar garin da zafi kuma dukda sanyin AC mutum gumi yakeyi ,kwaliyarta tayi a nitse sanan wuce dining table d'inda 'aka kawomusu abinci ganin cimar kamar ba irin tata ba yasa ta had'e fuska tana rik'e ciki ,hango wayar tafida gidanka tayi ganin 'number su a calendar yasata d'auka cewa tayi nifa bazan iyacin wanan jagwal gwalon ba 'akawomin tuwo kokuma indomie mutumin da baigane maitake cewa ba yace ” give me one minute please am coming zaro ido tayi tace ”tabb 'banza shima turancin bai gama bakinsa bba."


Humaid daketa dariya yana k'arawa yace”LADIDIN KAUYE y'an mata had'e rai tayi tace”wallahi kabari dan banhuce na d'azu ba, shiru yayi dan yasan komaiye ma zata rina 'aikatawa ,nocking aka farayi Humaid ne ya lala6a ya mik'e saikuma ya tsaya yace ”saikije kiyimai bayani,Khadija ce tace”bagane nawa turancin zaiyi ba dan 'naga shima koyo yakeyi yanzu hakama brain d'ina tafi tashi ,wucewa kawai Humaid yayi ya bud'e k'ofar mutumin 'ne d'auke da farantin abinci bud'ewa yayi yaga indomie ne aciki godiya yayiwa mutumin daganan yasauka k'asa da tiren abincin samun guri yayi yafara loda indomie saida ya cinye duka sanan ya tashi yabar plet d'in agurin yakoma sama.



Samunta yayi ta rafka uban tagumi tana kuka ko kallon gunda take baiyi ba bare tasanma yaganta taji dad'in 'narkewa bathroom ya wuce yayi alwala yazo ya gabatar da sallah tunda yayi sallama yaketa jero adu'a 'akan Allah yabashi lafiya ,itadai Khadija tarasa meke yimata dad'i a duniya kasancewar bata ragawa ciki ko kad'an mik'ewa tayi taduba maid'an dama dama tafara tuturawa badan yayi mata ba tana gamaci ta d'auki waya takirawo momy cikin farinciki momy tace” daughter dafatan kuna lafiya dai ko?eh muna lafiya Lou "amma momy 'yaushe zakuzo?momy tana murmushi tace”gobe ne insha Allah muna zuwa zamu wuce hospital amma zaku rigamu wucewa,to kawai tace shikuwa Humaid dama can magana ba damunshi tayiba, daganan sukayi sallama da momy.


Dare nayi basuci wani abinci mai nauyi ba ,Humaid na k'ok'arin hayewa gadon tarigashi ,hak'ura yayi ya koma k'asa ya shinfid'a bargo ya kwanta .



Washe gari bayan sunyi sallahr ashba babu wanda ya koma shirin tafiya 'asibiti sukeyi bayan Humaid ya fito daga wanka yaduba jakarda Khadija, ta lodamai kaya 'acikin ganin gajerun wanduna yasashi salati yace”wato kinmaidani d'an iska kenan ko ?cigaba tayi da kwaliyarta daganan ta mik'e tana cewa to inka shirya nizan wuce ,Humaid ne yace”kin dad'e baki wuce ba banza kawai jibeta 'ahaka kamar saliha ,shiru tayi saboda batason wanan kalmomin da yake jifanta dashi amma burinta lokacin yazo .


Yana gama shirin ya fice ko magana baiyi mataba jitayi yana kiran Joseph a waya dagudu ta fito tana tsaki ,ganin Humaid yashige mota yasata bud'ewa tashige da sauri wani katafaren hospital suka nufa suna sauka koshi Humaid ' d'in saida ya jinjina kyau irinna asibitin suna zuwa 'aka tarbesu office suka wuce domin ganin babban likitan suna shiga sukaci karo da wani mutumin farine dogo yanada jiki amma ba sosai ba yanada bak'in gashi dakuma gashin baki wanda yafito da tsananin kyawunshi ,kallon Humaid yakeyi kallon a ina nata6a ganinka Humaid ne yace ”aslamu alaikum mutuminne ya mik'awa Humaid hannu cankuma mutumin yace”naso nasanka koba kaine Humaid Abdullahi ba ?gingina kai Humaid yayi yace ”nine nima kamar nata6a ganinka 'a lokacin da zamu bud'e hospital d'inmu ,tunani mutumin yayi cankuma yace”ai dadynka abokina ne sosai kuma yayimin bayanin komai toya jikinnaka dasauk'i Humaid yace ”daganan yafara yimai tambayoyi."


Doctor d'inne yakai dubanshi ga Khadija yace” wanan iyalinka ce? a'a Humaid yace”.
K'anwata ce OK doctor yace ” please zaki iya bamu guri akwai wata magana danakeso muyi maganar ta doki Khadija to kwai tace tafice daga office d'in ,tasami guri ta zauna tana zuba uban tagumi ✍️✍️✍️.






Mom Islam ce



*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 33_34




_____Zuciyarta na k'una tarasa maike yimata dad'i amma babu komai ,doctor ne yakai dubanshi ga Humaid yace” yakamata kasani akwai aikin dazamuyi maka kuma yana buk'atar nutsuwarka gaskiya ko kanada mata saidai tayi hak'uri har na tsawo one month kasancewar aikin 'na buk'atar kulawa ,cikin farinciki Humaid yace” doctor ashe zan warke daganan suka fito doctor yanunamai d'akin dazai shiga ,batare da yayiwa Khadija magana ba yashige d'akin yana murmushi 'itako Khadija dataga batada muhimmanci yasata komawa masaukin su zama tayi tadinga rusa kuka kamar wace akayiwa mutuwa ,had'a kayanta tashiga yi tana surutai da alamu ranta ya 6aci sosai ATM d'inshi ta d'auka ta d'auki jakarta tayi waje ,rasa ina zatayi tayi zuciyarta ce take cemata ki koma Nigeria kawai ,hakan ko akayi ta d'auki shawarar zuciyar ta ,mutumin dake jigila dasu wato Joseph shi ta kirawo a waya tacemai dan Allah yazo ya kaita airport ,cemata yayi aisu alhaji suna hanya mezatai a Nigeria ,cikin zak'uwa tace ” fils na maganin Humaid aka manta kuma dole saidasu za'ayimai aikin , cemata yayi to bari yakirawo y'an airport d'in yaji ko jirgin 'Nigeria ya tashi, to tacemai dan burinta taganta 'a k'asarta yana kira yacemata nanda 30 minutes sasu tashi ,cikin hanzari taje ta tarkato kayaanta tafito ta kullo d'akin ,barin keys d'in tayi a hotel d'in suka wuce filin jirgi 'itada Joseph ,lokacin da suka isa 'ana kiran Nigeria dagudu tashige kasancewar yanzu harkar Bank akeyi tabiya kud'in komai .



Duba lokaci tayi a ’agogon dake d'aure a hannunta k'arfe 10:23am jin jirgin zai tashi yasata yin adu'a can kuma taji hawaye tafara cewa kuyi hak'uri momy ba'asan raina nadawo ba 'amma babu inda na iya saboda bak'incikin da Humaid ke k'unsamin bayan wasu mintuna ta jirgi ya sauka murna dakuma danasani fall cikin Khadija saboda tana ganin kamar batayiwa su momy adalci ba ,tana sauka tacire sim card d'inta tasai wani wanan kuma tasa 'a jakarta direct gidansu ta wuce wato gidan Humaid ganin mai gadi nanan yasata farinciki nocking tayi had'e da sallama cikin gaggawa mai gadin ya bud'e mata yana cewa hajiya sannunku da dawowa ywwa tace”tashige ciki mai gadin mamaki yafara to ina Humaid d'in??tabb 'bashida mai bashi amsa yasa shi yin shiru, da k'atuwar jaka tafito saboda ta d'ibo kayan abinci su katan d'in indomie dakuma su Maggi star da mangyad'a duka ta loda 'a jakar ,mai gadi naganinta da d'irmemiyar jaka yasashi zaro ido amma babu batun magana ,ficewa tayi batare datace ga inada zataje ba , bank taje taciro kud'i masu ywwa daganan ta dawo gida ,maida jakar tayi tana haki .



*ACAN INDIA*?


Tunda momy suka sauka take gwada number Khadija shiru a kashe ,dady ne yakira Joseph yace”yakaisu hotel d'in da Khadija suka kama d'aki acan ,Joseph da jikinshi yafara sanyi yacewa su dady wanan madam d'in yau tatafi Nigeria, what!!! Dady 'yace”cikin kid'ima ya 'akayi hakan tafaru maikuma yafaru momy da batada wuyar kuka tace”wallahi Humaid ne sanadi dama ba sonta yakeyi ba shine ko rayuwarta ta salwanta bashida matsala ko tana kuka tana magana ,dady ne yace” Joseph muwuce hospital d'in kawai ,mota suka shige suka nufi asibitin da isarsu sunyi sa'a wanan doctorn yanan office d'inshi suka wuce bayan sun gaisa ne sukace ya mara lafiyar yake dasauk'i doctor yabasu amma tare da shada musu d'azu akayi aikin kuma 'akwai alamun nasara masha Allah sukace yanzu ina yake?doctor ne yace” yana room 3 , amma naga bank'ara ganin sister nashi dasukazo d'azu ba ,lokacinne momy tace”matarshi ce doctor ne yace”amma shine yacemin ba iyalinshi ba ,dadyne ya mik'e suka fito dasu momy dakuma doctor room d'in aka nuna musu suka shige."





Ganinshi kwance yana bacci yasa dady dka mai tsawa yace ”ina kakai Khadija?? "arazane ya tashi yace”dady 'yaushe kuka iso ?babu wanda ya kulashi dan haka yayi shiru ,can kuma yace”ai takoma hotel ,dady dayaga Humaid nason raina masa hankali yace ”hotel d'in ubanka !!!...



Momy ce tace ”nidai yanzu damuwata number Khadija kuma gashi a kashe kiran number Jalal sukayi yana gurin aiki yace”bai gantaba rasa yazasuyi sukayi saboda halin marainiyar Allah, ...




Haka sukayi kwana uku a daddafe duk a tunaninsu Khadija tana gidanta ,a kwana na biyar ne aka sallame su kasancewar Humaid yaji sauk'i sosai gobe zasu dawo Nigeria tunda suka koma hotel d'in Humaid yashiga damuwa dan yasan indai ba'aga Khadija ba to shima ya 6ata dan wallahi saisu momy suncimai mutunci fiyeda tunani, washe sukayi shrin zuwa Nigeria ,jirgin safe sukabi .


*NIGERIA*
Sun sauka lafiya daga saukarsu gidan Humaid suka wuce maigadi ne yace”hajiya fa jiya tabar gidannan saboda naga ta loda kaya 'a wata k'atuwar jaka tashiga motar ta ko magana batayiba ta shige ,momy ce tazaro ido tace”yanzu fargabar da Khadija take jefamu yayi kenan ?" Dady cikin k'unar 'rai yace”kai kuzo muwuce duk inda zataje taje zamatadawo da k'afarta momy na kuka tana kiran sunan Khadija gashi wayarta bata shiga ,Humaid kam yakasa magana dan yasan kad'an suke jira sufara balbaleshi da masifa 'a motar Humaid suka wuce can anguwarsu momy suna sauka Jalal na shigowa yana ganinsu yace”ina Khadija fa momy ce tashige ciki da 'alamu kukanne zai ku6ce mata shikuwa dady cewa yayi ta 6ata ,Jalal daya tsaya kamar gunki yarasa takamai man amsa yace ”to nikam yaya Humaid ina Khadija? "wani mugun kallo Humaid yayiwa Jalal daganan yashige ciki.





Damuwa iya damuwa sun shiga sosai amma shi Humaid bai damu sosai ba kasancewar ba damuwarshi bace ,dady dayaga abin babba ne dan yau da dawowarsu kwana uku yacewa su momy su shirya suje k'auye ko tana can ,momy batayi wata kwaliya sosai ba ta fito suka wuce itada dady ...



Da isarsu malam Adamu yafara yimusu lale marhabun shigewa gidan sukayi suka sami 'inna tana zaune tayi k'wad'on rama ,zubo musu tayi aka kawo musu ruwa mai sanyi na randar k'asa ,malam Adamu ne yace”ina zuwa can anjima saigashi yadawo da k'waryar fura da nono dakuma ludaya ,zuzubawa su momy akayi bayan sunci sun k'oshi sukace dama 'abinda yakawomu shine mund'auka Khadija tazo nanne?"inna dake cin rama tace”walhi rabona da ita tunda 'akayi bikinsu nikam mukuma bamu k'ara wai wayarku ba malam Adamu ne yace”to yar marainiyar Allah ina tashiga momy ce tace”har wayarta sun gwada amma 'a kashe ,shirin komawa sukayi dady 'yabawa malam Adamu dubu hamsin sukayi gaba,godiya su inna suka dinga jerowa suka yimusu rakiya,har zuwa gurinda sukayi parking d'in motarsu.



Dady 'yana tuk'i yana tunani anya ba wani abin Humaid yayiwa Khadija ba dan sunsan halinta batada son zuciya ,momy ma 'a tata zuciyar tunani takeyi kodai Humaid ya cusa mata wani mugun abunne yasata guduwa ,har suka bar garin babu maiyiwa wani magana,da isarsu jos suka wuce gidan TV da gidan redio domin bada sanarwa ko 6ata tayi ...✍️✍️✍️.




Mom Islam ce

*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 35_36




_____Daganan sukayi gida jiki babu k'wari kowa ya sauka 6atan Khadija yazame musu tamakar mutuwa tayi ,dady ne yakira Humaid a waya yake cemai maza _maza yazo yanason ganinshi ,gaban Humaid na fad'uwa ya shigo gidan bayan yayi parking d'in motarshi ne ya shiga parlor ganin babu kowa yasashi wucewa d'akin dady ,samun dady 'yayi a kishingid'e kamar mai bacci, da sallama ya shiga yanemi guri ya zauna zaice ina wuni dady, _dady 'yace”bana buk'atar gaisuwar ka saboda yanzu batada 'amfani kuma wallahi kaje ka nemomin Khadija duk inda tashiga kokuwa kayi danasani a rayuwarka ,gumi ne yafar a keto mai tako ina yace”dady nimafa wallahi...wani azabbaben mari dayaji saida ya mik'e yana shirin bigewa da bango ,ficewa yayi daga gidan yana gunguni ,shima Humaid d'in gidan TV da gidan redio ya nufa yabada cigiya daganan yakoma gida yana 'adu'oi akan Allah ya baiyyana ta yafita daga masifar da iyayenshi suka kirari ,yaukam hankalinshi ya tashi sosai ganin fushin dady ba k'aramin tsorata yayi ba .


Washe gari ko gigin zuwa gidansu baiyi ba kasancewar bayason jin kalmomin da zasu hargitsamai k'wak'walwa , gashi yau saura sati d'aya ciwon jikinshi ta warke ,kuma yanada burin yin aure domin 6arje sabon shafi ,amma baisan wazai tunkara da maganar ba tunda wanan muguwar ta gudu ai ta jazamai fitina ,kwata_kwata bashida kwanciyar hankali kamar shine marar gata 'a duniya 'amma yasan mafita k'auye ya nufa gidansu malam Adamu yana shiga yasamesu suna ,zaune shida inna bayan ya gaishesu ne yake yimusu jajen 6atan Khadija ,malam Adamu ne yace”yau kimanin sati uku kenan Allah yasa tana raye ,amen yace ”can kuma yace”dan Allah baba inaneman wata 'alfarma ne ,babane ya maida hankalinsa ga Humaid yace” inajinka yaron kirki maiya faru ?"sunkuyar da kai Humaid yayi yace” baba sonakeyi nayi aure kafin Allah ya baiyyana Khadija muci gaba dayi mata 'adu'a."




Jinjina kai malam Adamu yayi saboda lamarin babu dad'i wato shi ta 'aure ma yakeyi ,cankuma yace” karka damu yarona yaushe iyayen ita yarinyar sukace ka turo ?"cikin rawar jiki Humaid yace” ranar juma'a ne ,malam Adamu ne yayi lissafi yace” saura kwana hud'u kenan to insha Allah zanzo kuma kafin inzo zankira mahaifinnaka muyi magana ta waya ,inna ko sai jinjina kai takeyi tana tuno Khadija, godiya Humaid yayi tsabar farinciki bandir d'in y'an dubu ya 'ajiye masa yana komawa mota ,yakira budurwar tashi saida sukayi hira sosai sanan sukayi sallama , ya mik'i hanya tafiya yakeyi cikin farinciki da nishad'i saboda yakusa zama 'ango hhhh...



Tunda yakoma gida ya kirawo masu decorection d'in gida gyra 'aka yiwa gidan kasancewar yarinyar y'ar manya ce shiyasa yakeson shima 'asan d'an manya ne ,part d'inta na can gefe gaban d'akin Khadija kayan Khadija kuma 'yadawo dasu k'asa 'amarya takoma sama ,kwana uku da magana ,dama Humaid ko k'ok'arin dosar gidan baiyi ba ,momy dajin zancen auran Humaid batace uffan ba haka shima dady 'yace” babu hannunshi ,malam adamu ne sukaje gidan surukan shida Humaid shikuma Humaid ya wuce gurin budurwar sa mai suna khairat ,hira sukeyi cikin so da k'auna dama irinta ya dad'e yana nema wato mai budadd'en ido ,ruk'omai hannu tayi tace”zomuje zagayeshi tadingayi da girma dakuma shuke shuken gidan suna rik'e da hannun juna....


Malam Adamu na fitowa ya koma can gidansu dady baisami dady a d'akinshiba yasa ya danna number Humaid, yana d'agawa malam Adamu yace” to kazo anyanke magana ,cikin azama Humaid yabaro gidan yayo gidan su ,samun malam Adamu dayayi shi kad'ai yaji dad'i sosai ,malam adamu ne yace” sun yake dukiyar aure nabada cikin kud'in da kabani d'azu to ansa biki sati uku masu zuwa ,godiya Humaid yaketa yimai daganan malam Adamu yace” zai koma, wasu mahaukatan kud'i Humaid ya d'ibo yabawa baba ragewa yayi kana yace” Allah yasa 'albarka saganan sukafice ,Humaid da sauri yafice daga gidan kamar marar gaskiya hmm..


Da kanshi yaje ya had'o kayan akwati daganan ya zarce gidan mahaifiyar momy yabata labarin abinda yafaru da Khadija amma yad'an had'a da k'arya ,su hajiya lefinsu dady suka dinga gani kuma sukace insha Allah zasu tsayamai kan maganar auran ,godiya yayi musu yabar kayan a gidan yadawo gidanshi ...



Yau saura sati biyu biki shirye²akeyi ta kowane 6angare amarya kuwa gyara takesha kamar ba gobe ,batun soyayya kuma sai abinda yayi gaba dan babu baya, ana biki saura 1 week ne dangin momy suka kai kayan akwati ,da shigarsu dangin maman khairat suka hau gulma suna cewa ji wanan banzan akwatin kamar na y'ar talaka ko besan wa ya 'aura bane?,sudai dangin momy haka suka kai kaya suka dawo jiki a sanyaye, dady ne yakira Humaid a waya yake cemai duk wasu takkaddu dayasani na hospital d'inshi to ya tarkato ya kawomai dan haka shima tuna 'aure zaiyi yafara neman 'nakanshi tashin hankali gamida rikicewa Humaid yashiga ko 6atan Khadija baisashi shiga damuwa irinta yauba ,hak'uri yake bawa dady amma ina dady 'yace” aina rantse ,daganan dady 'ya katse wayar ....


Yau saura kwana biyu d'aurin aure Humaid yayi d'inkuna sunkai kalla goma saboda murnar khairat ,a yaune dady 'yabada saukar alkur'ani mai girma masallatai akan 6atan Khadija , Humaid ne ya tattarawa dady kayanshi ya kaimai ,dady ko kallonshi baiyiba shikuwa Humaid mamakin abinda dady 'yayimai yakeyi ,kiran Jalal yayi a waya yake fad'amai halinda yake ciki ,Jalal cikin k'unar'rai yace ”to Allah ya kayauta nikam ina goyon bayan dady kasancewar baka damu da Khadija ba,Humaid ne yaja waya ya kashe saboda 6acinran yafara isarsa."



Washe gari akayi dinner anzubar da kud'i a bikinnan ,Humaid ko tunaninshi in kud'inshi suka k'are ina zaisami wasu ?amma bashida 'amsa gashi yarinyar sai k'irk'iro hidimomi takeyi kuma bayason yin harkar k'aranta hmm ,momy kam tamik'wa 'Allah komai ganin Khadija batada niyar dawowa gashi yau watanta biyu bata gida 'Allah yasa dai tanacikin k'oshin lafiya .



*WEEDING💖💫*

Yaune dubban jama'a suka shaida d'aurin auran Humaid ADAM da 'amaryarsa KHAIRAT USMAN DOLLARS akan sadaki dubu d'ari biyar hmm tofa riders kunjifa 😉,kowa mamakin kud'in auranan yakeyi amma babu mai bakin mgna kasancewar gaba da baya securitys ne kewaye da gurin ,y'ar manya kenan,misalin k'arfe 9pm aka wuce da ita gidanta ,duk iskancin su saida suka yaba da gidan saboda ba k'aramin kyau yayi ba misalin k'arfe 10pm kowa ya watse daga 'amarya sai ango ,bayan sunyi sallah ne ya dafa anta yayi mata 'adu'a daganan aka faracin kaji ,bayan sun kammalah ne Humaid yashige wanka 'a can toilet d'in shi itama 'amaryar wanka tashiga ta sanya sleeping dress.....✍️✍️✍️.




Mom Islam ce

*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 37_38




_____Da sallama yashigo yana sanye da gajeren wando ,ganinta 'a kwance kan gadon yasashi rungumo ta ,itako amarya jin haka yasata fara kissing Humaid cikin zumud'i humaid dai rasa kuzarinshi yayi saboda Khairat na neman sauya salon izuwa cire kayanta ,humaid ko mamakin inda khairat bata tsoron wanan dare yakeyi saboda yaji ance duk mace na tsoronsa, mirginawa gefe yayi yana maida nunfashi khairat kuwa haushi yabata dan ita bataso hakan ba ,Humaid zai mik'e takuma taroshi tace ”wallahi baka isaba kamance da hakk'ina daya rataya a wuyanka?"shiru Humaid yayi can kuma yakoma gurinta ,kasancewar itace jigon abin yasa baisha wuyar samun hanya ba ,ko jigata sosai batayi ba ,lokacinne Humaid yafara sambatu yana shimata 'albarka kasancewar tana tareda budurcin ta ,bayan yasami nutsuwane ya sauka 'aikuwa yana sauka ta matsoshi ,cewa yayi wanka zanyi na kwanta lokaci yayi nisa, zaro ido Humaid yayi yace”to ai saimu kwanta amma yanzu tashi muje muyi wanka ,mak'e kafad'a tayi tace ”wallahi ni bai 'isheni ba 😒garama kadawo ,ficewa yayi ko kallinta baiyi ba itako Khairat kuka tafara tanacewa namiji kamar mace babu kuzari wallahi saina gyaraka.




Tunda Humaid yakoma d'aki yafara tunanin ko.Khairat na daga cikin wa inda' ake cemusu harijai ne shifa bazai 'iya yin abu kullum ba kamar abincin gida ,ya shige wanka ,6angaren Khairat kuwa lokacinne takumajin wata sabuwar sha'awa na tasomata zabura tayi ta mik'e tafito part d'in Humaid ,ganin k'ofar a bud'e yasata shigewa batare datayi sallama ba ,cire kayan jikinta tayi ta kwnta d'ai d'ai tana jiran shigowar Humaid ,Humaid yaga lokacin datashigo yasashi k'in fitowa daga bayi ,yanemi guri ya zauna kamar zaiyi kuka, itako gajiya datayi da jiranshi yasata batasan lokacinda bacci mai nauyi yayi gaba da itaba ,yana ganin tayi bacci ya fice kamar munafiki cikin sand'a ,parlour yakoma ya kwanta.




*WASHE GARI*🤙
Washe gari kowannen su yatashi yayi sallah shiko humaid masallaci ya wuce saida gari yayi haske sanan yadawo gida, yana shigowa ya tarar da khairat da fara'arta tazo dagudu ta rungume shi ,shima fara'a yayi mata daganan tajashi zuwa dining, k'arewa kwaliyarta kallo yakeyi dan ba k'aramin kyau tayiba ,sanye take cikin riga doguwa ta shadda mai ruwan pink 'suna isa dining ta bud'e wani food flaks mai shegen kyau ,humaid ne yace ”wanan kuma daga Ina "tana murmishi tace ”daga gidan momy na ,masha 'Allah yace Allah yabasu lada 'amen khairat 'tace ”daganan tafara saving d'inshi tana bashi a baki ,farinciki fall zuciyar humaid yana cewa yanzufa nayi aure ,aini 6atan khadija yayimin rana tabb da tanan babu maibarina inyi aure ,shima bata'a baki yashiga yi saida suka k'oshi tukun khairat ta taso daga chair d'in datake zaune ta haye jikin humaid ,wasu abubuwa takeyi mai masu wuyar fasarawa abinka da farin shiga dan danan yafara sauya sallo ,kinkimarta yayi sukayi bedroom d'inshi ,ya shafe minti hamsin suna 'abu d'aya."



Dazai tashi saitace ita bata gaji ba ,fuska kamar ta mai kuka🤣 yace ” please Khairat live me tofa hmm cikin kasalaliyar murya tace ” yanzu wasan yafara dan wlh nikam ban gaji ba ,jiki a sanyaye ya zame yaje yai wanka ya dawo ,ganin zata kamoshi

Please Login or Register in order to submit comment