Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register





Asiya tayi sauri ta dauko idanuwan ta suka hada ido da wannan mata sai taga wani abu cikin idanuwan wannan mata sai ta dauko idon ta da sauri "Tace yo nagan ta ni dai ina kunu na ne?



Gashi can daki mana sannan akwai wata leda nan guri ki dauka kinji ko?.



Matar "Tace Uhm Asiya yaushe zakije gida na ne?.



To ni dai ban san ki ba kin ga ko bazanje gidan ki ba sai ta wuce daki tana mamakin irin wannan mata "Tace too wai ina Gaggo tasa mota ne?.



Gaggo ce ta shigo dakin da sallam.



Assalamu Alaikum.



Amin wa Alaikum sallam.


Haba Asiya yaushe zakiyi hankali ne? Nayi bakuwa Amman ko ki gaishe ta bakiyi ba mtsss wallahi kiyi hankali da kanki fa.



Yo wai ke Gogga shikenan sai tsaya kina yi mani fada ni fa shiyasa ban son kinayi muna jaye jaye fa.



Ba dole nayi maki fada ba eeyyye kin san Allah zan fasa zuwa gidan yaya na mai kudi ko.




Wayyo jama, a kuzo kiji wai Gaggo tana shiren yi mani bakin ciki dan kar na ci kaza Wayyo Allah na na shiga ukku na.



Cikin tsawa "Tace ke dan Allah gafara can wallahi kir ki kara ba naji muryar ki.



Turo baki tayi tana kallon Gaggo "Tace yo ni fa Yanxun ban ce ko mai ba yauwa Gaggo yaushe zamuje can ne?.



Sai kinyi rinka yin wanka da wanki tukun na.



Aradun Allah ina wanka sannan kuma ai ke kikeyi mani wanki.



To shikenan naji dai.



Ta tashi zata fita sai Gaggo "Tace ina zaki kuma?.



Zamuje gidan kwaliyar mu.



Ok babu damuwa Amman kada dade fa?.



To da gudu ta fita waje sai ta hadu da wannan mata Zaune ko kallon ta batayi ba haka tafita waje sai ga shatu.



Shatu "Tace kwaliya wai Rabi bata zo bane?.



Eh aradun Allah idan har bata zo ba to zamuyi tafiyar mu kuwa bata rufe baki sai ga Rabi ta fito cikin gida da gudu tana isowa "Tace kuyi hakuri wallahi Inna tace bazan fita ba ni kuma sai na gudo.



Asiya ta tabe baki "Tace yo dama ai innar ki yar bakin ciki ce wai dan karmuje mu ci kaza ko mtsss.



Shatu "Tace uhm muje ko?.




Haka suka wuce gidan ladidi amarya koda suka isa kofar gidan su ladidi mijin ladidi yana nan Zaune.



Asiya "Tace uhm ladidi na ciki ne?.



Washe baki yayi "yace ikon Allah *Asiya yar Gaggo* dama Ana ganin ku?.




Gashi kuwa ka gani tana cikin gida ko? .




Eh tana nan kuwa sai suka wuce cikin gida nan da gudu.



Ladidi ce ta fito daga cikin daki sai taga su Asiya sun shigo da gudu itama ta shige dakin da gudu.



Asiya ta tsaya tana kallon su sai ta bushe da dariya "Tace aradun Allah tsoro yayi maki yawa fa ladidi.



Sai ladidi ta leko tana kallon su Asiya da Shatu da Rabi "Tace shegun gari dama kune kuka bani tsoro wallahi na dauka yan fashe ne.



Asiya ta watsa mata harara "Tace su ne munafuka mtss dama zuwa mukayi ki bamu kazar amarcin ki.



Hhhh lallai kam wato dama halin ku yana nan to kushiga ciki mana.




Da gudu Asiya tashige daki ta dauko ledar nama kaza "Tace ku zauna mana Wayyo Allah na Wayyo dadi kai wannan irin dadi haka kai gaskiya ladidi naji dadin wannan kaza har da kashi take ci.



Ladidi kuwa sai dariya take "Tace uhm uhm ni dai babu ruwa na kuwa.




Oho dai ni dai sai na ci kaza haka suka zauna suka cinye naman kaza duka bayan sun gama suka cigaba da labari har dare yayi sosai sannan suka wuce gidan su.



*****************************

Washe gari


Su Ammi da daddy sun gyara sai ga humaeera tazo.



Humaeera "Tace daddy Miss you so much.



Miss you baby girl Aa Ashe tare kuke da matar kenan.


Ammi "Tace Baby jiki kira uncle dinki.



Da gudu ta wuce dakin Saheeb lokacin Saheeb ya gama gyarawa yana sanya takalmen sa sai ya ga baby ta shigo dakin da gudu.




Aa my baby har kunzo kenan.



Baby walida "Tace uhm uncle good morning Grandma tace idan ka gama gyarawa kazo muje.



Morning my baby ok muje ko sai ya rika hannun baby walida suka fito daga cikin daki suka sauko kasa yana kallon su daddy da Ammi.



Ammi "Tace kai masha Allah muje ko?.



Ok babu damuwa haka suka fita waje gurin motoci ya dauke Babbar mota d'aya suka shiga mota suka fita daga cikin gidan.



To Allah ya kaiku lafiya.



Asiya ce zaune tayi tagume tana kallon Gaggo na aiki sai "Tace uhm Gaggo.



Gaggo ta jiyo tana kallon Asiya "Tace naam Asiya lafiya dai ko?.




Lafiya Qlau wallahi dama zuwa anjima zamuje gidan kakar su Rabi.



To Allah ya kaimu lafiya dai zakuje gidan kakar su?.



Kai Gaggo wallahi kin cika tambaya da yawa sosai fa.



Da gudu Asiya ta fita daga cikin gidan.



Bayan awah biyar sai ga wata shegeyar mota ta tsaya kofar gidan su Asiya.



Mutane sai kallon ta suke Saheeb haushi duk ya kama shi daddy Yana kallon sa "yace lafiya dai ko?.



Saheeb yayi murmushi "yace babu komai fa.




Ok to ku fito muje cikin gida.



Yanxun daddy fisabillahI a wannan gidan nan zamu shiga?.




Eh mana ko bazakaje ba ne?.



Uhm daddy zan shiga cikin gidan nan.



Humaeera da baby walida da daddy da Ammi suka fito suka shiga cikin gida Amman Saheeb yana cikin mota yana kallon su da mamaki sai yada fa kansa "yace Wayyo Allah na na shiga ukku na gaskiya daddy ku takura mani fa.



Haka ya fito daga cikin mota yana kallon gidan sai ya shiga cikin gidan da sallam.



Assalamu Alaikum.



Gaggo "Tace amin wa Alaikum sallam Aa kai wana ke ganin haka kamar balarabe?.



Shine Gaggo wai ina kanwata Asiya ne cewar Humaeera.



Uhm Asiya ta fita gurin yawon ta bata rufe baki sai ga Asiya ta shigo cikin gida da gudu tana isowa "Tace washii Allah na Gaggo wai da gaske Babana yazo bata kula da su daddy ba.



Daddy "yace wai 'yata ce nake gani haka.



Da sauri ta jiyo tana kallon su daddy "Tace la Ashe da gaske ne.



Ammi "Tace 'yata zonan gurin.



Asiya tana hada ido da Saheeb ya watsa mata harara ita ta rama "Tace kan uban can kai mai kyauwo menaye maka kake harara ta ne?.



Cikin bakin ciki da takaice ya tashi tsaye "yace Ke ina wasa da ke ne?.



Yo ina ruwa na da kai ne da har zanyi wasa da kai ne?.


*Dan Allah masoyya na kuyi mani afuwa*🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻



*Hassy soja*😘🤪🤪🤪



*Comment and share*
11/25/20, 1:08 PM - Princess soja ✍🏻✍🏻: ♥️♠️♥️♣️

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏

♥️♠️♥️♣️
```Love and romantic story```


_Na_


_Hassy soja_



```Wannan labarin nawa salon sa na daban ne ban yarda wani ko wata su canza mani labari ba sai akiyaye```




*MARUBUCIYAR*


_BANI CE BA (ALJANA CE)_

_ASHE YAN UWA NA NE (MU BIYAR)_

_MUFIDA KAWAR ALJANA_

_SUMAIYYAH SUMEE BABY GIRL_

_HAKURI_

_SAI NI YAR DAJI NI KUMA YAR BIRNI CE_

_MUHSEENA DA MUHSEEN_


_AND NOW_

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏


_*BISMILLAHAR RAHAMANI RAHIM DA SUNA NA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI*_




_*SADAUKARWA GA MAHAIFIYA TA DA MAHAIFINA ALLAH YA JIKAN MAHAIFINA YAYI MASA RAHAMA MAHAIFIYA TA ALLAH YA KARA MAKI LAFIYA DA NISAN KWANA*_🤱🏻🤱🏻




PAGE... 3️⃣1️⃣&4️⃣0️⃣


*________________*📚


Yo ina ruwa na da kai ne da har zanyi wasa da kai ne?.



Ke ni kikeyiwa rashin kunya ko?.



Eh nayi rashin kunyar tana Murguda masa baki.



Cikin bakin ciki da takaice ya cika shi "yace wai ma yaushe rabun ki da wanka ne?.



Su daddy da Ammi da humaeera sai kallon ikon Allah kawai suka.



Humaeera kuwa sai dariya take cikin ran ta "Tace kai gaskiya daddy ya hada Auren su yaya Saheeb da Asiya kai Amman wallahi da naji dadin wannan hadin.



Asiya "Tace too Meye ruwan ka da ni ne tana murguda masa baki.



Saheeb "yace haba dai shiyasa nake jin warin dauda kenan.



Ammi ce da ke Zaune "Tace uhm Saheeb Asiya kuyi hakuri mana.



Humaeera "Tace Asiya na baki Auren yaya Saheeb ta kalle Saheeb ta kalle Asiya.



Asiya ta zaro ido "Tace jar uba wallahi sai dai na mutu banyi Aure ba tana harara sa.



Cikin tsawa "yace ke ina wasa da ke ne? da har zaki hada ni da wannan kucakar yarinyar.



Kan uban can ni ce kucaka? Yasin sai dai kai ne kucaki ta Murguda masa baki.



Gaggo "Tace Asiya wai baki jin magana ko? Wai ba yayan ki bane ba?.




Tabb wallahi Allah ya sauwake ni da ya zama yaya na tana hararar sa.



Nima Allah ya tsare ni da ki zama kanwata yana hararar ta.



Gaggo "Tace to shikenan ba zakije gidan kawun ki ba kenan.




Kai Gaggo ina zuwa fa gurin Ammi taje "Tace uhm uhm uhm kuna zuwa da ni ko na ci kaza ko tana kallon su.



Daddy "yace sosai ma.



Yeeee yeeee zamuje buni naci naman kaza Wayyo dadi zata fita sai taji muryar Gaggo "Tace ina zakije ne?.




Yo gidan su Shatu zanje da gudu tafi sai gurin gida su Shatu .




Girgiza kai Gaggo tayi "Tace Allah ya shirya muna ke Asiya.



Amin ya Allah cewar Ammi da humaeera da daddy.



Asiya tana shiga kwana da gudu kenan sai tayi karo da wata tsohowar mata "Tace Haba haba tsohowa dan Allah da Yanxun na buge ki fa.




Tsohowar mata "Tace 'yata dan Allah ina ne hanyar zuwa bakin titi?.



Asiya tayi tsaye tana kallon mata "Tace muje na rakaki ko?.



Matar "Tace to yar albarka ta rike hannun Asiya kenan suka bace bata.




Gaggo ce "Tace uhm Saheebu ya kuke.



Haba dan Allah Gaggo wane irin Saheebu? kuma ni fa sunana Saheeb yake ba Saheebu ba.




Yo ina ba Saheebu kake ba to menene ? ai duka sunan d'aya ne.



Daddy "Yace maryam Ashe zan kara ganin ki sai hawaye.



Da sauri ta kara so gurin sa ta rungume shi itama kuka take "Tace yaya Muhammad Abbas Ashe zan Kara ganin ka dakai da iyalinka?.



Ammi ""Tace haba maryam dan Allah kuyi hakuri mana ba gashi munzo ba.



Dagowa tayi tana kallon Ammi "Tace ai dole nayi kuka Halima saboda rabu na da ganin ku tun sanda Asiya tana jaririya.




Hakane gaskiya Amman Yanxun kiyi hakuri insha Allah tare zamuje can garin daga nan sai akai Asiya makarantar boko.



Kai gaskiya naji dadin wannan maganar taku to yaushe zamuje?.



To anan dai zamu kwana zuwa gobe insha Allah zamu Tafi.




To Allah ya kaimu lafiya dai.



Amin ya Allah suka cigaba da labari Saheeb "yace to ni dai sai zuwa gobe zan dawo.



Ina zakaje ne?.




Zan shiga cikin gari gurin abokina ne.



To shikenan babu damuwa Allah ya tsare hanya cewar Ammi.




Ya tashi ya fita sai ya shiga mota ya wuce cikin gari.



har marece yayi sosai sai Gaggo taji Gaban ta na faduwa dummm dummm dummm "Tace *innalillahi wa inna ilaihir raji un* waye meya ke faduwa ne?.




Da sauri suka ce lafiya maryam?.



Uhm wallahi Gabana yake ta faduwa tun dazu ko lafiya dai.



To Allah ya sa lafiya cewar su daddy.




Da gudu shatu da Rabi suka shigo cikin gidan babu sallama bale gaisuwa.



Kwaliya ina kika shiga ne?




Gaggo "Tace wai ku yaushe zakuyi hankali ne?



Hajiya Gaggo yo mu dama ai muna da hankali kuwa.



Su Ammi da humaeera da daddy sai kallon ikon Allah kawai suka.



To Allah ya shirye ku Amman wallahi kuyi hankali da ni kuwa.



To shikenan dai Gaggo Yanxun dai ina *Asiya yar Gaggo*?.



Tun dazu ta fita "Tace gidan ku zataje.



Rabi "Tace too ni dai ban ganta ba sai dai ko shatu.




Aa nima dai ban ganta ba da zan ce koke kika hanata zuwa.



To ina ta shiga ne?.



Bari muje mu dubo ta ko Gaggo.



To shikenan.



Da gudu suka fita sai gurin bidar Asiya Amman duk inda za, a ganta basu ganta ba har dare yayi haka suka dawo gida gurin Gaggo.




Duka hankalin su ya tashi sosai Gaggo "Tace *innalillahi wa inna ilaihir raji un* Allah kana ganin halin da muka shiga Allah ka kawo muna ita cikin aminci sai ta fashe da kuka.




Daddy "yace insha Allah ba guri mai nisa sosai ta tafi ba ki kwantar da hankalin ki kinji?.




To Yaya ko zamuje gurin mai gari mujiya.



Aa ki bari sai zuwa anjima ko.



To shikenan yaya.



Kowa yayi Zaune yayi shiru sai tunani suka gashi har tara na dare yayi to ina Asiya ta shiga ne?.



Gaggo ta ga har Yanxun shiru babu labarin Asiya "Tace yau na shiga ukku na yaya ka ganin har Yanxun Asiya shiru ko sai ta kara fashewa da kuka.



Bari na kira Saheeb na fada masa.



To Humaeera ta amsa wayar ta ga baby walida sai ta kira Saheeb lokacin Saheeb yana Zaune yana kallon TV sai yaga kiran humaeera cikin ran sa "yace ko lafiya wannan yarinyar tana kira na? Sai ya dauka "yace ya akayi ne kuma?.




Dama daddy ne "yace afada maka har Yanxun ba, aga Asiya ba.



Wace ce Asiya kuma? dan shi har ga Allah ya manta da wata Asiya.



Kamar ya Yaya Saheeb?.



Nace maki wace ce Asiya ne?.



Yar Gaggo mana.



Oho dama wannan marar kunyar yarinya ce kike tambaya ta ko?.




Uhm eh Yaya Saheeb wallahi muna cikin tashin hankali.



To ni ruwa na da ita ne kuka sani ko tana guri shegen yawon ta na tsiya mtss wallahi kada ki yin mun maganar ta kinji na fada maki ko?.



Sai ta bi wayar ta da kallo tana mamakin halin Saheeb tabe baki tayi "Tace haba Yaya Saheeb dan Allah dai kayi kokarin duba muna ita.



To naji dai zan duba aganin shikenan ko?.



Eh wallahi Ina godiya sosai my babyn Ammi.



Uhm to good bless you bye bye.



Amm daddy na fada masa "yace zai sa ayi cigeyarta.



Too shikenan babu damuwa Allah yasa aganinta.



Amin ya Allah ina godiya sosai Yaya Muhammad Abbas.



Babu komai kanwata maryam yar gata Abba da umma.



Karfe 12:00pm Dare



Gaggo ce zaune sai tunani Asiya take "Tace *innalillahi wa inna ilaihir raji un* Allah ka tsare mani Asiya duk inda tashiga.



Amin ya Allah Cewar Ammi da humaeera da daddy sai "yace to wai dama tana zuwa yawo haka?.




Aa iya karta zuwa gidan su kawayen ta Shatu da Rabi .



Yau kwan biyar kenan da batan Asiya Amman har Yanxun Babu labarin ta Gaggo duk ta rame tayi zuro zuro.



Asiya ce kwan ce saman makekin gado irin sarauta tana bacci sai ga wata yar budurwa ce ta shiga cikin dakin tana kallon Asiya tana murmushi.




Yar budurwar "Tace Uhm kawata ki tashi haka nan mana.



Zabura tayi tana kallon dakin sakin baki tayi tana kallon ikon Allah "Tace jar uban to waye ya kawo ni nan guri ko dai mafarki nakeyi ne?.



Aa ba mafarki kikeyi ba kawata cewar yar budurwar.



Cikin tashin hankali Asiya "Tace shikenan mutu nayi Wayyo Allah na Wayyo Gaggo ta.



Asiya ki kwantar da hankalin mu ba mutane bane kuma ba zamu cutar da ke ba cewar wata mata.




Asiya "Tace too dama ke ba mutum bace dama akwai aljannu tana kallon su.



Sosai ma Yanxun dai ki tashi kiyi wanka sai ki ci abinci kinji ko sannan kuje gurin gaishe da sarkin aljannu.



Wanka kuma?.



Eh kuma ki wanke bakin ki da makilin.



Too menene malukin kuma?.



Abun wanke baki mana tashi ki gyara 'yata.



Ta tashi tsaye kenan sai ga wata yarinya ta shigo dakin dauke da abinci kala kala har kala goma da sallama Ta shigo .



Assalamu Alaikum kawar gimbiya sannun ki da zuwa duniyar aljannu.




Amin wa Alaikum sallam gimbiya Jiddah ta daga kanta.




Dama nan duniyar aljannu nake shikenan na rasa Gaggo.....




*MAHAIFIYA TA ALLAH YA KARA MAKI LAFIYA DA NISAN KWANA*🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻🤱🏻




*Hassy soja*😘🤪🤪🤪



*Comment and share*
11/25/20, 1:08 PM - Princess soja ✍🏻✍🏻: ♥️♠️♥️♣️

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏

♥️♠️♥️♣️
```Love and romantic story```


_Na_


_Hassy soja_



```Wannan labarin nawa salon sa na daban ne ban yarda wani ko wata su canza mani labari ba sai akiyaye```




*MARUBUCIYAR*


_BANI CE BA (ALJANA CE)_

_ASHE YAN UWA NA NE (MU BIYAR)_

_MUFIDA KAWAR ALJANA_

_SUMAIYYAH SUMEE BABY GIRL_

_HAKURI_

_SAI NI YAR DAJI NI KUMA YAR BIRNI CE_

_MUHSEENA DA MUHSEEN_


_AND NOW_

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏


_*BISMILLAHAR RAHAMANI RAHIM DA SUNA NA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI*_




_*SADAUKARWA GA MAHAIFIYA TA DA MAHAIFINA ALLAH YA JIKAN MAHAIFINA YAYI MASA RAHAMA MAHAIFIYA TA ALLAH YA KARA MAKI LAFIYA DA NISAN KWANA*_🤱🏻🤱🏻




PAGE... 4️⃣1️⃣&5️⃣0️⃣


*________________*📚


Dama anan duniyar aljannu nake shikenan na rasa Gaggo ta fadi kasa some.



Cikin tashin hankali gimbiya jiddah tazo gurin ta "Tace haba dai kawata ki dana tsoratar mu fa mu bazamu cutar da ke ba inason ki Asiya sai ta shafa fuskar ta zubur tayi



"Tace Wayyo na shiga ukku na Wayyo Gaggo kizo ki taimake ni.



Sarauniya "Tace 'yata bakiyi wankan bane?.



Gimbiya "Tace wallahi kuwa har Yanxun tana cikin tsoro fa.



Sai ta kalle Asiya "Tace 'yata kiyi hakuri zamu ma yarda ki gida Amman sai mun gama abun da mukeyi sannan dan haka ki saki jikin ki Yanxun ki tashi kiyi wanka ki ci abinci kai har da kaza.



Da sauri Asiya "Tace gaske kike?.



Eh 'yata sai tashi sama ta wuce.



Gimbiya jiddah taja hannun Asiya suka shiga ban daki bayan sun shiga Asiya tayi tsaye tana kallon ban daki "Tace kai jama,a wai Yanxun wannan gurin wanka ne?.



Eh kiyi wanka sosai fa.



To naji dai ni fa wallahi bana son wankan nan fa mtss.



Haka Asiya ta watsa ruwan ta fito ko da ta fito sai taga wasu kayan India masu kyau sosai akwai ta dauka ta sanya.



kai masha Allah gaskiya kawata kiyi kyau sosai fa



Dan Allah fa.


Sosai ma.



Ina ma ace Gaggo zata gani haka.



Zata ganiki Amman ba Yanxun ba.



Gaggo duk ta rame ko abinci ba ta ce kowa ya shiga damuwa Amman ban da Saheeb dan shi har ya manta da ita.



Ammi "Tace maryam koda zamu koma abuja ne tare da ke?.



Muryar Gaggo bata fita sosai "Tace to idan muka fita Asiya tadawo fa.



Daddy "Yace dole tare zamu je saboda da haka kiyi hakuri insha Allah za, a ganinta cikin koshi lafiya.



Saheeb "yace wai har Yanxun bata dawo yawon ba yana kallon Gaggo..



Gaggo "Tace wallahi ni dai ina tunanin ko wani matsafi ne ya dauke ta gashi har an kusa wata d'aya.



Humaeera ta kalle Gaggo "Tace wai ko guri malam me zamuje ne?.




Gaggo "Tace kai ku tsaya ko da jiddah ce tazo ta dauke ta ne?.



Suka hada baki suka ce wace ce jiddah kuma?.



Kawarta ce sosai.



Kawarta kuma wace irin kawarta? ce wannan cewar Ammi tana kallon Gaggo.



Insha Allah ita tazo kuwa to shikenan Yaya zamuyi tafiya Yanxun dan hankali na ya kwanta.



Daddy "yace maryam wai ko akwai matsala ne?.



Aa kubari zan baku labari Amman ba Yanxun ba.



Saheeb ya tashi tsaye "yace to ni dai ina jiran ku sai kun fito ya fita waje gurin mota.


Haka suka fito suka shiga mota suka wuce gidan su Saheeb.



Gimbiya jiddah ce rike take da hannun Asiya "Tace kawata kin san ina zamuje ne Yanxun?.



Aa ina zamuje ne?.



gurin maimartaba zamuje ki gaishe shi daga nan sai muje gurin bayi na ki ganin su sai murmushi take.



Ikon Allah har da wasu bayi gare ku to menene bayi kuma?.



Zaki sanin su Yanxun kuwa haka suka wuce ko ina suka wuce sai an gaishe su har suka kawo fadar sarkin aljannu.



Suna shiga cikin fadar sarki jikin Asiya ya fara rawa saboda tashin hankali da sauri ta kalle gimbiya jiddah "Tace Wayyo Allah na Wayyo Gaggo kizo ki taimake ni sai ta fadi kasa some.



Cikin tashin hankali fadar sarki sai surutu ake Ashe sarki yana kallon ta.



"Yace kada ki tabata ki barta kawai.



Tasowa yayi yazo gurin Asiya sai ya shafe fuskar ta zubur tayi tana kallon su gimbiya jiddah tazo gurin ta "Tace sannu kawata dan Allah ki rage tunanin nan babu abun da zamuyi maki.......




*NA RAGE MAKU YAWAN TYPING SABODA RASHIN COMMENT*😞😞😞😞😞😞😞😞😞


*Hassy soja*😘🤪🤪🤪



*Comment and share*
11/25/20, 1:08 PM - Princess soja ✍🏻✍🏻: ♥️♠️♥️♣️

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏

♥️♠️♥️♣️
```Love and romantic story```


_Na_


_Hassy soja_



```Wannan labarin nawa salon sa na daban ne ban yarda wani ko wata su canza mani labari ba sai akiyaye```




*MARUBUCIYAR*


_BANI CE BA (ALJANA CE)_

_ASHE YAN UWA NA NE (MU BIYAR)_

_MUFIDA KAWAR ALJANA_

_SUMAIYYAH SUMEE BABY GIRL_

_HAKURI_

_SAI NI YAR DAJI NI KUMA YAR BIRNI CE_

_MUHSEENA DA MUHSEEN_


_AND NOW_

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏


_*BISMILLAHAR RAHAMANI RAHIM DA SUNA NA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI*_




_*SADAUKARWA GA MAHAIFIYA TA DA MAHAIFINA ALLAH YA JIKAN MAHAIFINA YAYI MASA RAHAMA MAHAIFIYA TA ALLAH YA KARA MAKI LAFIYA DA NISAN KWANA*_🤱🏻🤱🏻




PAGE... 5️⃣1️⃣&6️⃣0️⃣


*________________*📚



Tasowa yayi yazo gurin Asiya sai ya shafe fuskar ta zubur tayi tana kallon su gimbiya jiddah tazo gurin ta "Tace sannu kawata dan Allah ki rage tunanin nan babu abun da zamuyi maki.



Asiya sai kallon su take "Tace ni kam Asiya na shiga ukku na Wayyo Allah nayi gamo.



Sarkin aljannu "yace jiddah ya ankayi haka kin san tana tsoron mu meyasa kika zo da ita ne?.



Abba kayi hakuri wallahi inason tane sosai shiyasa kuma Yanxun dama gurin ka mukazo mu gaishe ka to sai ta tsoro da girman ka.



To shikenan Amman kada ki kara zuwa da ita sai tayi hankali kuma ki ma yarda da ita gida saboda hankalin su ya kwanta.



Insha Allah.



'yata tashi Zaune kinji ko?.



Tashi Zaune tayi "Tace wai da gaske duniyar aljannu nake?.



Eh mana Amman Yanxun zan ma yarda da ke gida.



Gimbiya jiddah ce ta sunkuyar da kanta kasa "Tace Abba inason ta sosai kuma inason kabani izin mu tafi tare dan Allah.




To shikenan zaku iya tafiya Amman ki dawo gida.



Ina godiya sosai Abba na sai ta kalle Asiya "Tace tashi muje kawata.



Da sauri Asiya ta kalle gimbiya jiddah "Tace too wai da gaske kike ko?.



Eh Yau gurin Gaggo zamuje.



Da sauri ta tashi tsaye tana jiran gimbiya jiddah.



Gimbiya jiddah ce ta rike hannun Asiya suka fita daga cikin fadar sarkin aljannu.



Gurin madubi suka tsaya gimbiya jiddah "Tace ya kai wannan madubi muna son fita daga cikin nan guri zamuje duniyar Dan Adam.



Da sauri madubi

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

1 Comments On ASIYA SARKIN TSIYA YAR GWAGGO
avatar
daiy

1 year ago

Reply

dddd

Please Login or Register in order to submit comment