Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba kukana zai nutsar da shi. Sai ya shiga magiya yana roko na a kan in taimaka in daina kukan nan zai fahimce ni. Ni kaina ina mamakin tashin hankalin da Haiman ke shiga idan ya ga zubar hawaye na wannan shi ne dalilin da yake sawa na yarda cewa Haiman *son gaskiya* yake yi mini. Amma fa sanin hakan bai ta6a sawa na ji tausayinsa ko da na rana ɗaya ba, wannan ne yake tabbatar min cewa bana son Haiman ba Kuna zan ta6a sonsa ba.

Na kalli yadda hankalin jarumin ɗan sarkin ya tashi saboda ganin zubar hawayena. Tabbas so na musamman ne, duk wanda kaga bai girmama so ba to bai tsinci kansa a ciki bane.

"Haiman" na kira sunansa cikin muryar kuka. Ya amsa idanunshi da nutsuwarshi duk suna gareni. "Haiman wallahi bana sonka, ba kuma na tunanin zan so ka koda a gaba ne. Ban san ya zan yiwa zuciyata ta so ka ba da nayi Haiman. Dan Allah ka taimake ni ka bar ni, ina da wanda nake so. Muhsin shi kaɗai zuciyata ta yarda da shi a matsayin masoyi ka taimaka min yarima." na tashi na tsuguna a gabanshi ina ko'karin kama kafafunshi.

Wani irin zafin kishi ne ya daki zuciyar Haiman ya mike tsaye hannunsa dafe da kirjinsa ya juya min baya. A lokaci ɗaya wani zazzafan gumi ya fara yanko masa ta ko'ina a jikinsa. "ki yi hakuri Na'eema tsakanin zuciyata da taki da akwai wata dangantaka mai karfi wadda na tabbata kema da sannu zaki santa, kuma kema zaki fara so na a lokacin da wannan dangantakar ta bayyana ga taki zuciyar. Ina son ki Na'eema ba zan iya rabuwa da ke ba. Zan iya zama dake koda bakya so na, zan jira zuciyarki har sai ta so ni koda kuwa lokacin zai kai ga lokacin tsufana ne, zan kasance mijinki har zuwa lokacin. Ni kam ba zan iya rabuwa dake ba. Zan aure ki in kuma baki dama ki ci gaba da zama a gidana har zuwa lokacin da zaki so ni. Zan zama bawa gareki Na'eema ina ji a raina saboda ke kawai aka halicce ni, na yarda da so ɗaya ne tak! Kuma shi nake miki Na'eema."

Yana kawowa nan a zancensa ya bar wurin ba tareda ya koma waiwayen inda nake ba. Wani wahaltaccen kuka ne ya su6uce mini, na shiga rera shi kamar wadda aka ce iyayenta sun cika. Ina cikin kukan ne iyayena suka bayyana a gabana cikin 6acin rai. Na kalle su sau ɗaya na sunkuyar da kaina. Malam wanda dama a cike yake da takaicina ya fara yi mini faɗa kamar zai dake ni.

"Nikam ban san yadda kike so ki maida ni ba Na'eema, da na ɗauka haukar da kike na son Bil'adama kuruciya ce sai gashi abin naki sai gaba-gaba yake, shin me kika maida kan ki ne? Ko dai bakida hankali ne Na'eema? Banda shi a ina kika ta6a ganin an haɗa auren Bil'adama da Aljan? Koko haka kike tunanin zamu zuba miki ido ki kare rayuwarki ta har abada babu aure kina bin bayan Bil'adama?."

Ummy ta kar6i maganar da cewa "Wata kila a kanta za'a fara, banza mara hankali to wallahi tun wuri ki nutsu ki dawo hayyacinki maganar aure babu fashi kuma nan kusa bada nisa ba." a tare suka 6ace rayukansu a 6ace. Hankalina ya koma tashi damuwata ta koma ninkuwa ko kaɗan bana son ran iyayena yana 6aci ta dalilina, na shiga uku ni Na'eema ya zan yi da rayuwata?.

Sai na koma fashewa da Kuka na faɗi kwance bisa shimfiɗar nan ina ayyanawa a raina cewa inama mutuwa zata zo ta ɗauke ni da na huta bakin ciki da kallon kaina a matsayin matar wanin da ba Muhsin ɗina ba.









*Nasmat* ✍
[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*MARUBUCI...*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari.


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
Yar'mutan
Arkilla✍
____________





📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com




*Page 4*




Wannan shafin ga baki ɗayansa sadaukarwa ne gareki kawar kirki. *QUEEN HAFSY* aminta ta da ke ta musamman ce, ina yi miki barka da dawowa tawan Allah ya bar zumunci da kaunar juna.







Lokaci mai tsayi na ɗauka ina wannan kukan ganin babu abinda zai kare ni da shi yasa dole na hakura na rarrashi kaina na mike na nufi ɗakina.

Duk tsananin da nake ciki sai da naji saukar ni'ima da sanyi a zuciyata, lokacin da idanuwana sukayi tozali da manya-manyan hotuna na zanen fuskar farin ganina Muhsin. Waɗanda ke makale a kowace kusarwa ta ɗakin. Duk da ba can na nufa ba amma sai naji zuciyata ta jagoranci gangar jikina ta jani zuwa gaban hoton. Na tsaya kikam ina karewa Muhsin kallo wanda yake zaune da kayan aikinsa wato littafi da Alkalami yana son fara rubutu. Nice na zana wannan da hannuna saboda babu inda Muhsin yake min kyan gani kamar in gan shi a karkashin bishiyar nan yana gwada fasaharsa ta rubutu.

Na shafi fuskarsa ta jikin hoton na fara magana cikin shaukin so dan a lokacin ji nake kamar Muhsin ɗin ne a gabana. "Muhsin kasan ina sonka ina kuma kaunarka. Amma gashi ra'ayi na yasha bam-bam dana iyayena. Muhsin bazan iya bijirewa iyayena ba, kamar yadda nake ji bazan iya rabuwa da kai ba. Ya kai masoyina hakika rayuwata tana cikin hatsari, wanda ni kaina ban san makomarta ba. Sai dai ina da buri a kan ka Muhsin. Koda ace ban aure ka ba, ban kuma kasance da kai ba, na so ace na cika maka babban burinka ta yadda har abada zan kafa hujja a zuciyata cewa na taimaki masoyina wajen zama abinda yake so ya zama. Muhsin in dai ban sami ko ɗaya daga cikin waɗannan ba zan iya mutuwa."

Na kifa kaina jikin hoton ina zubda hawaye. Can na ɗago kai na sumbace shi sannan na shiga tunaninsa shin ya tashi daga bacci ya tafi gida ko dai yana nan 'fadarsa'? Karkashin bishiyar nan nake nufi domin nan ne fadar masoyina.

Nan da nan sai naji zuciyata ta kwaɗaitu da son koma ganin fuskarsa. Juyi ɗaya nayi na 6ata sai gani na bayyana karkashin bishiyar nan Amma ban sami Muhsin ba. Wannan yana nufin ya tashi kenan. Ban jira komai ba na nufi gidansu. Kai tsaye ɗakinsa na bayyana nan ma wayam baya nan. Hakan bai sanyayar min guiwa ba na koma 6acewa sai ɗakin mahaifiyarsa gimbiya Suhaima. Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke nan da nan fuskata ta wadatu da kawataccen murmushina. Badan komai ba sai dan ganin zumar rayuwata Muhsin. Yana kwance bisa wani lallausan kilishi wanda ke shimfiɗe a faffaɗa kuma kawataccen ɗakin. Yayi matashin kai da cinyar mahaifiyar tashi tana shafa kansa. farar mace mai farar zuciya.

Can na sami wuri na zauna gefen su ina kallon su kuma ina sauraron maganarsu gwanin sha'awa. Muhsin ya kalli mahaifiyarsa yace "yake ummana shin wai ni babu wata hanya za zan bi in samo maganin wannan lalurar dake damuna?" hawaye ne suka cicciko idon Suhaima, tayi saurin share su tun kafin su fito. Sannan ta kalli ɗan nata mafi soyuwa a cikin zuciyarta tace "koda akwai ta banida sani a kan ta Muhsin, ni kaina da ace na san wata hanya ta samun warakar ka wallahi da na bita na samo maka koda ko zan rasa rayuwata ne." da sauri Muhsin ya kai hannunsa ya rufe bakin ummansa "a'a mahaifiyata, da dai ki mutu kam gwara na tabbata dakiki in yi ta zama a haka har karshen rayuwata." Suhaima ta koma share hawaye tace "kawai dai babu ne ɗana amma wlh da babu abinda zai hana ni binta, Muhsin ina son ganin cikar burin nan naka, ina son ganin ka zama cikakken *MARUBUCI* Amma ban san ta yadda hakan zai kasance ba."

Wata kasalalliyar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "inaga hakan ba zai ta6a yuwuwa bane, inaga ba zan ta6a zama bane wannan shi ne dalilin da yasa Allah ya toshe min kwakwalwa. Amma kam ina son Rubutu Ummana."

Ba umman Muhsin ba ni kaina saida hawayen tausayinsa suka zubo mini. Ta rungume shi cikeda so da tausayinsa "zaka zama ɗana, insha Allahu wata rana zaka zama." gaba ɗaya ɗa da uwar kuka suke yi wannan shine abinda ya kara zaburar da zuciyata kuka nake sosai ina tunani shin ta wace hanya zan iya taimakon Muhsin? Tabbas ya kamata ya zama amma ta yaya?.

6acewa nayi daga ɗakin gimbiya na bayyana gidanmu. A wannan lokacin na gama yanke hukunci babu tsoro ko fargaba a tattareda ni. Na tabbata wannan ita ce damata ta samun abinda nake so daga gare su. Ganin babu kowa a mazaunin mai kama da fada yasa na kutsa kaina izuwa ɗakin baba Malam na shiga da sallama.

Yana kishingiɗe bisa abin sallarsa ya amsa mini sallamar fuskarshi na kallon wani wurin daban. Hakan ya tabbatar mini cewa har yanzu mahaifina fushi yake dani. Na tsuguna ɗan nesa kaɗan da inda yake zaune. Nace "dan Allah baba kayi hakuri, ka sani sarai bana kaunar duk wani abu da zai zo ya 6ata min ranku kaida ummyna." nayi shiru ko zai ce wani abu amma baba bai ce komai ba. Hakan yasa na kara ɗorawa. "Baba dan Allah ina rokon wata alfarma daga gare ka, na yarda da za6in ku zan auri Haiman zan kuma so shi. Amma ni kuma ina bukatar ku cika mini burina kafin wannan auren." sai a lokaci baba ya ɗago ya kalle ni fuskarsa ɗauke da murmushi "dama nace ko canja min ke aka yi ne? Domin ni a nawa sanin Na'eema na bata tsallake umarnina balle ta kai ga bijire mini." "ai har abada ba zan ta6a bijirewa umarninka ba baba." na koma faɗa cike da biyayya da nuna ya isa da ni. Mahaifina ya ji daɗin wannan maganar dan sai da ya tashi daga kishingiɗen da yake ya zauna yana fuskanta ta. Na saci kallon fuskarshi sai na ganta ɗauke da murmushi nima murmushin nayi bakina ɗauke da addu'ar Allah ya taimake ni yasa yau in sami nasara kan mahaifina.

Babana ya katse mini tunani da tambaya. "Mene ne wannan burin naki da kike son cikawa kafin aurenki da Haiman Na'eema?" duk yadda naji na dake d'azu sai da nayi jim kaɗan ina tunanin makomar abinda zan faɗa. Na sake jin muryar baba yana faɗin kar kiji tsoron faɗa min ko mene ne ya' ta, tabbas zan yi miki adalci. Na lura babana ya kagu yaji mene ne burina wanda cika min shi zai sa in kar6i auren mijin da nayi ikirarin bana son sa.

Kaina na sunkuye a kasa na fara magana. "baba, nasan matsayin saninka da yawan shekarunka mawuyacin abune ace bakada masaniya a kan maganin lalurar nan ta Muhsin da na daɗe ina gaya muku. Baba ka dubi Allah da girmansa, ka dubi darajar Ma'aiki (s.a.w) sannan ka dubi daraja da karfin soyayya ka taimake ni in dai har kanada masaniya akan abinda nake tambayar ka baba ka gaya mini. Kar kaji shayin sanar min ko mene ne, idan har na samawa Muhsin waraka ya sami cikar burinsa ta dalilina to zuciyata zata sami nutsuwa zan kuma yi alfahari da soyayyata domin na taimaki wanda nake so. Sannan cikin kwanciyar hankali zan amshi auren za6in ku."

Shirun da naji babana yayi ne yasa na ɗago kaina dan ganin makomar magana ta. Ai kuwa abinda naci karo da shi ya yi matukar Razana ni ya kuma tashi hankalina...












*Nasmat* ✍
[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*MARUBUCI...*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari.

👩🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________





📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com




Dedicated to the loved Frnds 'yan uwa abokan aiki:
King Boy Isha
Kamala minna
Bamai A Dabuwa Kkm.
Zaidu Ibrahim. Mr. Zaid
Ramadan Mubarak (Mubson)

Mu gudu tare mu tsira tare. I am proud of you guys. Always 🤝



*Page 5*




* * * * *
Hawaye ne na gani fall sun ciko idon baba Malam, kasancewar kansa a sunkuye ya kara bawa hawayen damar surnanowa suka biyo kuncinsa. A take zuciyata ta harba hankalina ya kara tashi. A 6angare ɗaya kuma naji ina nadama da danasanin tunkarar mahaifina da wannan maganar. Kaico na da wannan rayuwar tawa, tunda na kasa samawa iyayena farin ciki. Gashi yau har na kai ga zama silar zubar hawayen Babana.

Sai na fashe da kuka na karasa ga mahaifina na rungume kafafunshi kasancewar yana zaune ne bisa kujera. Cikin kukan na fara magana "na shiga uku babana ka yafe min, dan Allah ka min aikin gafara. Da na san magana ta zata kona ranka da ban zo maka da ita ba baba. Wannan wace irin rayuwa ce dani? Ina son ku ina son yi muku biyayya baba dan Allah kayi hakuri wlh zan janye wannan kudurin nawa koda kuwa zai zamo sanadin fitar numfashi daga gangar jikina. Baba ka yafe min nayi alkawarin kawar da bukata ta Na rungumi taku bazaka koma zubda hawaye akai na ba, sai dai ko in na mutuwa ta ne."

Ahankali baba ya ɗago ni ya zaunar da ni bisa kujerar dake gefensa. Na lura da sauyi sosai a tattare da shi, jikinsa yayi sanyi zuciyarsa ta karaya. Tsawon dakiku babu wanda ya koma yin magana a cikin mu. "Na'eema" baba ya kira suna na cikin sanyi da alamun tausayi a fuskar shi. Ban iya ɗaga kaina ba saboda wata kunyar mahaifina da nauyin sa da nake ji. Na amsa "na'am baba." baba ya fara magana cikin jimami da mutuwar jiki yace "Na'eema kin tuna min da ɗan uwana Jamal ne ta dalilin wannan yunkurin da kike yi akan soyayya. Nasan kinada labarin inada ɗan uwa guda ɗaya jal a wannan duniyar." yaja numfashi tareda sararawa niko nayi nutso a kogin tunani tabbas inada labarin yayan babanmu mai suna Jamal wanda aka ce ya bar gida tun yana saurayi kuma har yau ba'a koma ganin sa ko jin labarin shi ba.

Tsayawar tunanina yayi dai-dai da cigaba da maganar baba. "na san baki san cikakken tarihin wannan ɗan uwan nawa ba, baki san bisa dalilin da ya bar gida ba to yau zan gaya miki. Wannan labarin da zan baki shine dalilin mu ni da mahaifiyar ki na hana ki wata masaniya akan maganin cutar wannan bil'adaman da kike so.

Na tabbatar koda ke ce a matsayin mu irin matakin da zaki ɗauka kenan." baba ya sarara kafin ya fara bani labarin yayansa wato babana Jamal wanda labarinsa kawai na sani ban san shi ba.

"Kamar yadda kika daɗe kina ji Jamal yayana ne uwa ɗaya uba ɗaya, wanda mu kaɗai ne Allah ya azurta iyayenmu da haihuwa. Ba tare aka haife mu da Jamal ba, amma muna da matukar kama. Kasancewar ba wata tsera ce tsakaninmu ba yasa nayi kusa iso shi a girma. Hakan ne yasa da yawa idan suka ganni sai su ɗauka Jamal ɗin ne, gurare da dama nakan amsa sunan shi ga duk wanda ya kira ni da shi. Saboda son da muke wa juna yasa ko kaya za'a yi mana sai iri ɗaya muke sakawa. Haka muka taso har zuwa girman mu. Inda a nan ne mummunan lamarin ya afku."

Baba yai shiru yana share hawaye cikin tsantsan kunan rai ya ci gaba... "soyayya!" ya faɗa da karfi da kuma nauyin gaske. Kafin ya ɗora "soyayya da kike gani abu ce mai matukar hatsari Na'eema, wata irin rikitacciyar soyayya ce ta 6alle tsakanin yayana Jamal da wata gimbiya 'yar sarkin birnin Durgas mai suna Sunita. Sunita ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance wadda masu ittafaki sun faɗa a wannan zamanin babu wata kyakkyawa kamarta a duk faɗin nahiyar nan. Ɗan uwana Jamal ya mace sosai akan son Sunita wadda tunda take bata ta6a jin murya ta wani ko wata ko kuma wani sauti a duniya ba.

Hakan kuwa ya samo asali ne ga kasancewarta kurma, da cutar aka haife ta. Babu wanda ya ankara da haka har saida ta girma ta kai munzalin yi da kuma jin magana. Sai a lokaci kowa ya fahimta da Sunita kurma ce bata ji daga nan mahaifinta sarki Ashwar ya shiga fafutukar nema mata magani tun yana yi da malamai har ya koma kan bokaye, na ruwa dana tudu. Amma ina biyan bukata ya gagara. A cikin haka ne ya sadu da wani hatsabibin boka wanda ya gaya masa Sunita fa bazata ta6a warkewa ba har sai an ɗiga mata sihirtaccin ruwan nan na (ma'al dawa'u) waɗanda can binne a tsibirin Darul iks a cikin kunnenta. Ruwan ko yana can bangon duniya ne a karkashin ikon shahararre kuma azzalumin sarkin nan na bakaken sheɗanu sarki Dawwaz, wanda a wannan duniyar har izuwa yanzu ba'a sami na biyunsa ba a karfin sarrafa miyagun dodanni da sheɗanu na jinni. Baya ga tsagwaron karfin tsafi dana dantsen da yake da su. Jin hakan yasa mahaifin Sunita sarki Ashwar ya saka wata doka ga manema auren tauraruwar 'yar tasa

Cewa duk mai son ya mallaki Sunita da gaske to ya je ya nemo mata waraka ta hanyar samo mata wannan sihirtaccen ruwan na ma'al dawa'u. Wannan ne yasa duk masu tururuwar neman gimbiyar suka ja da baya saboda sanin ɗinbin hatsari da masifar dake cikin tafiya nemo wannan ruwan.

Ya kasance babu kowa a manemanta sai yayana Jamal. Saboda shi tashi soyayyar ta sha bam-bam da wadda sauran suke mata. Wato shi son gaskiya yakewa Sunita."

Babana yaja numfashi yana sharar kwalla. Wannan karon hadda ni kukan nake yi domin jin inda soyayyar gaskiya take, kasancewata ma'abociyar soyayya ina son mai maida hankali gareta da kuma bata muhimmanci.

Tunanina ya yanke ne lokacin da naji baba ya numfasa zai ci gaba da bani labarin...











*Nasmat* ✍
[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*MARUBUCI...*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari.

👩🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________





📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com




Dedicated to my sweet Sister *Maryam (Ummu Hanan)* banida wata kalma da zata isa wajen yin godiya ga karamci irin naki. 'Yar uwa ta gari, ɗaya bayan ɗaya kika dinga saudaukar min pages gaskiya Nasmat bazata manta dake ba. Allah ya kara ɗaukaka min ke yasa kifi haka. Sabon littafi 👄SURAYYA👄 kuma Allah yasa an fara shi a sa'a yasa a gama shi lfy. 'Yar mutan arkilla na yin ki Maryam ki huta ta wajena. 🤝







*Page 6*




* * * * *
"To a lokacin ne Sunita ta kamu da tsananin son Jamal domin bayyanar mata da yayi a matsayin masoyinta na gaskiya. Ya zamana bata son rabuwa da shi, kullum suna tare dare ne kawai yake yi musu shamaki.

Cikin wannan hali ne ɗan'uwana ya yanke hukuncin tafiya nemo wannan ruwan domin samun Sunita ta zama mallakinshi na har abada. Fama sosai yasha da iyayenmu a kan wannan tafiyar domin su basu lamunta ya tafi ba. Har saida ya haɗa da turo musu manyan garin nan da dattijan da ya tabbatar suna jin kunyar su sannan ya samu suka amince bisa dole badan ransu ya so ba. A wunin da ya samu amincewar su a wunin ya shirya tafiyar domin dama ya daɗe da fara shiri." hmm baba ya sauke numfashi yana daɗa matso hawayen dake idon shi sannan yaci gaba "a wannan ranar nayi kuka irin wanda ban ta6a yin irinshi ba na shiga tsoro da ɗimuwa musamman da naji babanmu na bashi karin haske gameda inda zai tafin. Tunda naji jerin hatsarurrukan da babanmu ke lissafowa yaya Jamal na kan hanyar ma kafin ya kai ga isa tsibirin na darul iks wanda can kam sai abinda Allah ya yi. Sai na kankame shi ina kuka kamar zan mutu, nace babu inda zai tafi dan na tabbata yadda naji labarin wannan hanya in ya tafi ba zai dawo ba. Na tabbata mutuwa zai yi. Domin ni a gani na gwara ka kashe kanka da kanka yafi ka tunkari tsibirin darul iks.

Amma ina kukan ina karawa yaya Jamal yayi sallama da dangi da iyayenmu ya rungume ni ya sumbaci goshina yana faɗin "inda rabon ganawa wata rana Jamal zai dawo gareka Uffar" wannan ita ce kalma ta karshe d'aya furta kafin tafiyarsa. Bai koma cewa kowa komai ba ya juya yana mai karanto addu'ar nan ta neman tsari ya 6ata 6at!. Wannan shine gani na na karshe da yaya Jamal da ni da duk wani dangin mu. Iyayenmu har suka koma ga Allah maganar Jamal suke yi kullum sai sunyi maganar sa. Tun muna koke-koke muna tuna yaya Jamal har muka dangana ga Allah muka daina kukan sai dai addu'ar Allah ya dawo mana da shi. Domin har babanmu ya cika yana gaya min cewa ɗan'uwana yana nan a raye bai mutuba, amma yana cikin mawuyacin hali. Wasu lokutan har ji nake kamar nima in fita inbi bayan Jamal dan nemo shi, amma idan na tuna ni kaɗai na rage a zari'ar mu sai inji ina son zama donmi tada gidan nan.

Sunita ma tun daga lokacin ta shiga kunci da kunan zuciya na rashin dawowar masoyinta. Ta kuma yiwa kanta alkawari har ta mutu ba zata so wani namijin da ba Jamal ba. Yanzu haka ita take mulkin birnin Durgas saboda tsufa daya riski mahaifinta sarki Ashwar.

Masu ganin ta sun ce har yanzu tana nan da kyawun nan nata kamar na da, sai dai shekaru da suka ja. Ance kuma har yau tana kan bakar ta na jiran masoyinta Jamal inko ya mutu ta yi alkawari itama sai dai ta mutu a hakan nan amma itada aure har abada."

"Wannan shine cikakken labarin ɗan'uwana Jamal. Shin kin san me yasa na baki wannan labarin, har ma na ce miki yanada nasaba ga hanaki labarin maganin cutar Muhsin da muka yi?" na girgiza kai cike da jimami nace "a'a" ina sharar kwalla. Domin gaskiya labarin soyayyar baba Jamal da gimbiya Sunita ya ta6a zuciyata ba kaɗan ba.

Babana ya gyara zama ya fuskance ni da kyau yace "Na'eema maganin nan na warakar cutar Sunita shine maganin warakar Muhsin ɗinki. Babu wani magani a duniya da zai tashi kwakwalwar Muhsin tayi aiki yadda yake buri sai wannan ruwan na tsibirin darul iks wato ma'al dawa'u."

Sororo nayi ina kallon baba wanda ya dasa aya a maganarsa idonshi a kain na. Matsanancin tsoro da tashin hankali ne su yi min dirar mikiya. Zuciyata ta shiga dukan uku-uku ina kara juya maganar baba ina jinjina ta a ma'aunin tunani.

Lokaci ɗaya naji jiri na ɗiba na tunanina ya gauraya kaina yayi mini nauyi sosai har ina ji kamar zai rinjayi gangar jikina...










*Nasmat* ✍
[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*MARUBUCI...*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari.



Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment