You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*
1️⃣
Baya baya ta yi ta lankwasa kamar za ta fadi sai kuma ta yi gaba tare da cira kafarta ta dama sama kafar da ta sha ado da fararen yayan wuri ta buga a kasa cikin tabon lakar ruwan saman dake sauka, ta mika hannayenta duka biyu sama ta ware karan dake hannayenta ta buga su da karfi har sai da suka yi kara, sannan ta fara juya k'ugunta yayan wurin dake daure a kwankwasonta suka fara kara, a take maza da matan dake gurin suka hau tafi, masu ganguna irin na itace suna dukawa sai ta rufe ido tana taka rawar da ta zame musu ta al'adar wanda aka saba gabatarwa sau daya a kowace shekara.
Wata siririyar busar sarewar ce ta rika tashi a tsakanin mazanjen da ke buga gangunan kidan, a take kowa ya fara rausayar da kai domin busa ce dake saukar da natsuwa da annashuwa tare da nishadin zuciyar duk wani mai saurarenta, ciki kuwa har da Sarkin Garin Garuk da yan majalisun masarautarsa da kuma fadawansa. Busar sarewa ce da babu inda zaka taba jin ta a duniya sai a garin Garuk. Ko a cikin garin babu wanda ya iya sarrafa halshe da numfashi ya busa sarewar sai Waira da dan'uwanta Eid, busar sarewa ce da Eid ya kirkireta da tsananin karfin tsafin da babu wanda zai iya busar sai shi da kanwarsa Waira, ita ma kuma saboda ya amince mata ne, busar sarewa ce da ta zama haramun ga jama'ar garen su kwatanta kwaikwayonta ma balle har su gwada yi.
Busar sarewar ce, ke kara mata kuzari da karfin taka rawar da take, yadda take lankwasa da murza kugunta sai ka rantse da Allah babu ƙashi ko daya a jikinta, ruwan saman da ke sauka yana ta wanke datti da tsananin daudar dake jikinta, domin walki ne daure a kugunta sai wani katon ganyen data daura a kirjinta ya rufe breast dinta da a yanzu suke girma, a tsakanin guiwowyinta zuwa kafafuwanta a sake yake, haka ma cibiyarta a waje take, ta saki gashin kanta dake cinkushe ya kwanta har kusan mazaunanta, kunnuwanta na sanye da yan kunnen mai karamin kokon kan karamin tsuntsu kamar yadda wuyanta ma yake sanye da sarkar kokon kan maciji.
Ranar yau rana ce ta musamman ba ga jama'ar garin kadai ba, har ga yar sarkin masafa kuma jikar sarkin masafa na garin Garuk wato Waira.
Ranar yau rana ce da suka kadaice domin yin bikin abun bautarsu, da kuma bauta masa a tsawon ranar har zuwa lokacin gudanar da wannan rawar da Waira take takawa, a al'adar mutanen garin sau daya suke bautawa abun bautarsu a shekara, a ka'idar bikin ko wace shekara da kalar yarinyar da ake zaba a bata damar taka rawa a biki, a bana ma an zabi Waira kamar yadda aka zabe ta a bara, saboda kwarewar da ta yi da kuma yadda ta iya bin salon busar tana motsa jikinta kamar wata hawainiya.
A irin wannan ranar ce kadai Waira take wanka, a irin wannan ranar ce kadai take raba jikinta da duk wani datti da kazantar da suke daukar shekara suna rayuwa a jikinta, wato sau daya tal Waira take wanka a shekara!
Waira matashiyar yarinyar ce yar kimanin shekara goma sha hudu, ya daya tilo a gurin sarkin matsafa na garin Garuk, kuma jika daya tak a gurin sarkin matsafa na garin Garuk, kuma ya daya tak mai jiran gadon sarauniyar matsafa na garin Garuk.
Waira kyakkyawa ce sosai irin kyan da karya mace take ta yi mata duba daya ta kawar da kai balle kuma namiji, fara ce fol irin farin nan mai kyau da ba kasafai kake samunsa a jikin fararen mutane ba sai zababbu, tana da yalwar gashin kai da ya cumuimuye da datti saboda rashin son wanka da tsabta, duk da yake gashi ba abun alfahari ba ne a gurin yan matan garin Garuk domin duk wanda ka duba kanta zaka ganta da gashi daga manya har yara, tun daga kan mazan ma sai wanda ya ga dama ya aske, balle kuma mata da suke ado da shi. Waira kyakkyawar matashiyar budurwa ce mai tasowa, mai tsananin farin jini a tsakanin mata sa'ainta masu tasowa, sai dai tsoron dan'uwanta wato cousin dinta Eid ya hana maza da yawa kusantar inda take. An yi ittifaki kaf a tahirin garin ba a taba yin kazamar yarinya irin Waira ba, ba kazanta ta bangarem abinci ko abin sha ba, kazanta a gurin tsabtace jiki, sam sam sam Waira bata son abun da zai hada jikinta da ruwa da sunan wanka sai a dole, kamar saukar ruwan sama ko kuma a inda ya zama dole sai an shiga ruwa sannan a wuce ta wani gurin, hakan ya saka ta shar'antawa kanta wanka sau daya a shekara, wato kamar dai yadda ake gabatar da bikin abun bautarsu a shekara bayan gama bikin take zuwa ta yi wanka, wannan ya saka ranar ta kara muhimmanci a gareta da kuma duk wani masoyinta.
Waira ita kadai ce mahaifiyarta ta haifa, wanda za ta gaji mahaifinta kamar yadda mahaifinta ya gaji kakanta, wato sarautar tsafin iya yan gidan kawai suke gadonta sai kuma jininsu, a ka'idar sarautar ba a nadawa sai saurayi ko budurwar ya kai shekaru ashiri, wannan ya saka aka ajewa Waira kujerar har sai ta kai wadannan shekarun. Sai dai haka be hana a fara koya mata tsafi da yadda ake yinsa ba da kuma saka mata shi a jikinta domin al'ada ta mutanen garin kowa da kalar na sa tsafin sai dai na wani ya dara na wani kamar yadda bahaushe ya ce ko Baba da Babansa.
Jama'ar garin Garuk wadansu irin mutane ne da ba su yarda da duk wani abu na cigaban zamani ba, tun daga kan tufafinsu har zuwa abincinsu da kuma mu'amalarsu ta yau da gobe, ba sa hawan mota sai dabbobi, makwancinsu da ginakinsu duk irin na mutanen da ne, Garin Garuk wani babban birni ne da a kimiyance za a iya kira shi da jiha, domin babban gari ne mai cike da albarkar noma da ruwa da tautsuna da itatuwa, jama'ar garin ba su yarda dan garin ya kawo musu bako ba face da sanin sarki shi ma kuma ba bakon da zai zauna zaman dindindin ba, haka ma ba su yarda jininsu ya auro ko a aura daga garesu ba sai jininsu, wato ba sa auratayya a tsakanin wata kabila sai ta su. Haramun ne dan wani garin da ba na su ba ya ji yana kaunar jininsu ma, balle kuma jininsu ya kaunace wani da ba na su ba.
Sai dai sun amincewa jama'ar garin fita waje gari domin shakatawa ko yin wani abun. Sam ba su yarda da maita ba, sai dai tsafi ya zama kamar ruwan da suke rayuwa da shi.
Ba kowa ne yake sha'awar leka wajen garin Garuk duk kuwa da kasancewar Sarkin Garin ya yarje musu, ciki kuwa har da Waira da ko bakin kofar garin bata sha'awar zuwa a yanzu, tun bayan da sarkin garin ya saka a saukar da tsafi a jikinta, sai aka iyakance mata iya inda take iya tafiya sakamakon lura da suka yi da yawan yawon da take da shi a cikin garin da kuma hawan tsaunuka da bishiyoyi kamar biranya, ko wane kalar itace da tsauni ta san yadda zata sarrafa shi ta hau, an fada mata an kuma jaddada mata idan har ta kurkura ta bar garin Garuk ba zata taba iya dawowa ba, rashin dawowar kuma yana nufin rasa rayuwarta.
Wasu daga cikin jama'ar garin suna fahimtar yaren wasu garuruwan cikin kuwa har da dan'uwanta Eid sai dai Waira bata jin wani yare sai na Gurtuk wato yaren garin Garuk, sai dai tana da karfin basirar fahimtar maganar mutane ko da kuwa bata jin yaren, kana tana da tsananin tsafin sanin abun da ya faru da mutum ko dabba a rayuwarsa ta baya, Waira yarinya ce mai tsananin shiga rai, hakan ya saka take da farin jini a gari, hakan kuma ya kara dankon zumunci da shakuwa a tsakaninta da dan'uwanta wato dan kanen mahaifiyarta Eid.
Eid handsome guy ne mai jini a jika, matashin da yalwar gashin kai ta kara masa kyau domin ya kan daure gashinsa ko ya sake shi kamar dai yadda mata suke yi, fari ne sai dai ba irin farin Waira ba domin ita ta fita dabam duk da kasancewar datti da daudar dake jikinta ya hana farin fatar nata haskawa da kyau, garuruwan da Eid be taba ziyarta ba a Nigeria kadan ne, domin ya kan fita garin Garuk yayi nisan zango ya bawa idanuwansa abinci sannan ya dawo.
Wani abu mai kama da wabi kakan Waira mahaifinta kadai ya haifa haka ita ma mahaifinta ita kadai ya haifa, dukansu sun mutu ne bayan samun magaji kamar yadda ita ma zata iya mutuwa bayan samun na ta magajin, ba al'adar tsafin ce a haka ba, al'adar zuri'ar da Waira ta fito ne a haka.
MALEEK POV.
A fusace ya nufo downstairs, kamin ya karasa saukowa Ummi dake zaune a cushion kusa da mijinta ta yi saurin sakin hannun mutumen da a kullum ita Amarya ce a gurinsa ta mike tsaye tana kallon ďanta, daman can ta san za a rina hakan ya saka take son ta tari fushinta tun kamin ya isar mata da sakon dake bakinsa.
“Ka yi hakuri ni na saka ta shiga ta share maka ďakin”
Cak ya tsaya ya jimke hannunsa da karfi yana tauna hakora.
“Amman miyasa zata shiga tana kamshin turaren mata? Not just perfume har lips stick ta shafa min a mirror, and you all know how i hate duk wani abu da ya shafi mace miyasa zata min haka?”
“Zan mata magana, amman Maleek ka rika sassautawa...”
Bata kai aya ba Abiey ya tari numfashinta yana mikewa tsaye.
“Alright Son je waje ka sha iska, zan saka a gyara maka dakin, kuma ka bar ni da kanenka nan i will deal with them”
Sai a lokacin ya sauke numfashi ya kalli mahaifinsa
“Thank You Abiey”
Ya fada sannan ya juya ya fice, Ummi ta bishi da kallo cike da damuwa ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juyo ta kalli Mijinta.
“Be kamata kana karfafa masa guiwa ba, wannan abun ya ishe ni haka I'm sick and tired of this”
Cikin kuka ta karashe maganar, Abiey ya kara masowa kusa da matarsa Zahra da bayan son damuwarta ma balle abun da zai saka ta zubar da hawaye ya rumgume ta.
“Ya isa Hayatie, kowa da yadda Allah yake halittarsa shi haka Allah yayi shi baya son mata a rayuwarsa ko wani abun da ya shafi mata”
“Ko dai asiri aka masa? Ni ban taba ganin mutum irin Maleek ba, ko kuma dai aljana ta aure shi?”
Sai kuma ta yi shiru, irin shirun dake karantar da mijinta wannan ciwon ya dade a kirjinta yana cinta.
“Ko kuma alhaki ne yake bibiyata?”
Ta yi masa tambayar da ba shi da amsarta, balle kuma ita da abun ya kullewa kai
“Ba ko daya, Zahra ya kamata ki gane kowa da yadda Allah yake halittarsa, ki daina saka komai a ranki, wata rana zai daina, kuma dai ki jawa yayanki kunne su daina taba min yaro”
Abiey ya fada yana kokarin kwantar da hankalin matarsa, dagowa ta yi daga jikinsa ta share hawayenta tana jin zafin halin da danta yake ciki.
Maleek na daya daga cikin irin mutanen da duniya take kafa tarihi da irinsu daidaiku a cikin mutane, domin ba kasafai kake jin mutumen da yake barin tahiri irin na shi ba, Maleek yana da wata bakar dabi'a da Allah ya halicce shi da ita ta tsanar mata, ko sunansu baya son ji sai dole, ya taso da wannan bakar dabi'ar ne tun yana yaro karami har zuwa girmansa, wannan ya saka ya yanke duk wata alaka da abun da zai hada shi da mace, ya'ala turaren mata ne ko wani abu na kayan kwalliyarsu, ko da hanya ce ta hada shi da mace idan akwai wata zai canja saboda kar su hadu, sai dai hakan be saka ya tsira daga gurin kanensa mata ba da suka mai da shi abun tsokana duk kuwa da tsoronsa da suke.
Sai dai ta inda abun ya zo masa da sauki be tsani mahaifiyarsa kamar yadda ya tsani kanensa ba, hakan kuma ba yana nufin ya zauna da ita su yi hira ko ya ci abinci da ita a teburi daya, idan yana neman shawara ko yana cikin wata damuwa mahaifinsa Abiey ne kadai zai iya zama da shi ya fada masa damuwarsa, sai kuma kanensa namiji.
Idan ka yi arba da Maleek yana wasa da dariya da sake fuska yana tare da abokansa ko yan'uwansa maza ne ko kuma mahaifinsa Abiey.
Yana daya daga cikin dalilin da ya saka baya son shiga yanar gizo, domin baya son cin karo da mata, wannan ya zame masa kamar wata cuta mai cutar da shi har ga Allah yana cutuwa sosai har ma ya cutar da wasu, wato mahaifiyarsa da kuma kanensa mata, wani abun da zai baka mamaki shi ne yadda mata suke rushing dinsa, domin saurayi ne da ya iya wanka da sanya turare mai jan hankali, ga kuma kyau da cikar kalama da zati irin na jaruman maza.
Babu daren da ba ya addu'ar Allah ya yaye masa wannan damuwar da mahaifiyarsa take kallonta a matsayin cuta, ya san ko ba a yanzu ba, wata kila a nan gaba abun zai fi cutar da shi fiye da yanzu, sometimes ya kan zauna yayi tunani dalilin da zai saka ya tsani mata sai ya rasa, and no matter how zai kwatanta sausauta kyamar abun a zuciyarsa da zarar yayi arba da mace ko ya ji muryarta sai tsanar ta mamaye zuciyarsa.
Kamin ya kawo yanzu ya sha wahala rayuwa sosai, domin ta ko'ina yana haduwa da makiyan nasa har zuwa lokacin da iyayensa suka fahimci damuwarsa suka fara sama masa mafita. Ko kadan hakan be taba dagawa Mahaifinsa Abiey hankali ba, domin a gurinsa ba wani abu ba ne dan ka tashi ka ji ba ka sha'awar wani abu ko kuma wani abun baya burgeka a ganinsa halittace, sai dai ta gurin Hajiya Zahra wato Ummi abun ba haka yake ba, domin ďanta baya iya zama da ita yayi hira balle ya fada mata damuwarsa, baya zauna a gurin daya da yan'uwansa mata, babu ruwansa da mace komai kyau da kwalliyarta, hakan ya saka take jin kamar ďanta ba daidai yake da sauran yaya ba, domin ta sani Maleek yana cutuwa da halin da yake ciki kamar yadda ya taba fada.
AMEER POV.
Jikinsa ne ya bashi ana kallonsa, hakan ya saka shi juyowa, sai yayi arba da Momy dake tsaye bayansa rumgume da hannayenta tana kallonsa fuskarta dauke da murmushi. Shi ma murmushi yayi ya sauke sarewar da yake busawa ya mike tsaye gaba daya.
“Momy”
“Na'am ďana tun dazun nake tsaye nan”
“Why”
“Ameer, bana son na katse maka busar sarewar da kake yi ne, domin ni ma yana min dadi”
Yayi murmushi ya shafa kansa, shi kansa da yake busar tana masa dadi balle kuma masu saurare.
“Ban san inda ka koyo wannan busar ba amman tabbas wanda ya koya maka kwararre ne sosai, domin tana shiga har cikin zuciya”
Wannan karon dariyar shakiyanci yayi wanda ta bayyana fararen hakoransa, sannan ya wuce gaba ya fara takawa, Momy ta bi bayansa tana fadin.
“Daddynka yana falo yana jiranka, na fada masa kana nan Garden kana hutawa ya bukaci a katse maka hutarwa a kiraka”
Ya juyo ya kalleta yana tafiya baya baya.
“Hmmm an kai masa karata kenan”
“Ka yi laifi ne?”
Ya juya ya cigaba da tafiyar ba tare da ya ce mata komai ba.
Ya rigata isa kofar falon hakan ya saka shi bude kofar ya jefa kafarsa a ciki yana wani lumshe ido saboda kamshi dake tashi a katon falon mai kama da wata karamar hadaddiyar daular Larabawa. A gurin da aka tanada domin aje talkami ya aje talkaminsa ya saka na shiga falon sannan ya karasa ciki. Kai tsaye Upstairs ya nufa yana wani taku kamar ba zai mutu a saka shi a ciki kasa ba, kamar an masa dole haka ya bude kofar dakinsa a hankali ya shiga, ko wace kusurwa da bango na dakin kamshi yake, kamshin turare da babu hanci da zai tantance iya kalolin da aka hada ya bada wannan kamshin mai dadin shaka, ko'ina na dakin tass yake an gogeshi sai kyalli yake irin kyalli da ko yawunka suka zuba saka iya dangwala yatsa ka laso abunka saboda yadda aka gyara gurin kai ka rantse da Allah ba a takashi ma, cikin wata tafiyar izza da girman kai ya tura kofar wani karamin dakin canja tufafi wato Closet mai yanayi da karamin Boutique.
Ya dauko wani box ya bude ya saka sarewar sannan ya cire tufafin jikinsa ya jefawa wata na'urar dake rike kaya ta saka su a gurin da aka tanada domin zuba kaya masu datti, even though daga tufafinsa har jikinsa babu inda yake da datti domin tsananin tsabtar Ameer baya yarda ko kura ta raba kusa da shi balle kuma dauda. Bedroom dinsa ya dawo ya shiga bathroom wani kalar kamshi mai dadi ne ya fara tashi a lokacin da ya soma murza shower gel din da yake wanka da shi, a tsanake ya gama ya fito ya sake komawa Boutique dinsa dake cikin dakin, ya shafa mai a jikinsa sannan turare ya raka masa baya, ya dauko kananan kaya ya saka, ya fito daga dakin yana wani irin kamshi kai ka rantse daga cikin ruwan turare ya fito.
Kofar da zata sadashi da bangaren mahaifinsa ya nufa, tun kam ya isa kamshin turarensa ya sanar da Momy da Daddynsa cewar gashi nan isowa. Dukan kanensa suna zaune a dinning din suna cin abinci tare da iyayensa, da sauri Zeezee ta rufe gashin kanta, gudun kar ganin gashinta ya hana shi cin abinci domin tsananin tsabtar da yake da ita ta saka masa kyama da tsandar abubuwa da dama ciki kuwa har da gashin mace.
Kujerarsa yaja ya zauna ya kalli mahaifinsa dake kallonsa da irin duba na mai laifi. Fadada fuskarsa da murmushi shi ne abun da ya fara yi sannan ya dauki plate ya soma zubawa kansa abinci.
“Miyasa ka kori ma'aikatanka?”
Ya dan tsaya daga zuba abincin da yake, ya kalli Daddy.
“I told them kar wanda ya sake shigo min office da kazanta, shi dayan be ji ba na lura rigarsa ta jiya ce ya maimaita kuma be wanke ta ba, dayan kuma karni yake Daddyn kasan yadda nake jin warin mutane, bana son kazanta ko kadan kuma bana son na ji mutum ba kamshi”
Daddy ya girgiza kai cikin damuwa.
“Amman Ameer wannan be kai ace ka sallame su daga aiki ba? Kuma bayan sallamar ka ce ba za a ba su salary su na wannan watan ba, secondly an fada min jiya ka kade wani mutum da mota”
“Shi ma wasa yake da brayuwarsa, overtaking yayi, ya ba ni haushi sosai shiyasa na yi masa haka next time ai zai san muhimmancin rayuwarsa”
“Wannan duk ba hujja ba ce Ameer, rayuwar mutum tana da muhimmanci”
Cewar Momy tana kallon ďa ďaya tilo Namiji kuma farincikin mijinta.
“Zan kiyaye next time, amman dai hakan ba yana nufin wani banza ya taka ni na kyale shi ba, kuna da damuwa da mutanen da be kamata mu damu da su ba”
Ya tsayar da cin abincin da yake ya sake duba mahaifinsa.
“But Daddy I'm sorry”
Da sauri Mr Bashir ya girgiza masa kai domin ko kadan baya son bacin ran ďan nasa Ameer.
“No No No don't, Daddy loves you so much”
Ameer yayi murmushi ya cigaba da cin abincinsa.
“Daman ai kai baka laifi a gurin Daddy da dai mu ne”
Cewar Teema sai duk suka saka dariya har Daddy, Ameer ya kai fork dinsa ya dauko namanta ya cinye sai ta fara kukan shagwaba, dariya yayi ya mike tsaye tare da daukar kofin lemun dake gaban Daddynsa.
“Momy thank you for the lunch yayi dadi sosai”
“Baka ci komai ba ai ka tashi, ina zaka je?”
“Abokaina ke jirana akwai inda zamu je yanzu nan”
“Take care”
Daddy ya fada masa yana kallonsa, domin ya san ba karamin aikinsa ba ne a kira shi a sanar da shi Ameer yayi wani laifin ko kuma yayi fada da wani ko ya karya wata dokar kasa.
“I will Daddy ba zan janyo maka magana ba”
Daddy yayi murmushi, sallama Ameer yayi musu sannan ya fice daga bangaren.
___________________
Ga wani sabon zubi,
Sabuwar shimfida mai zafi
A sabuwar Shekara.
ku daura Belt dinku domin wannan tafiyar ba mai sauki ba ce.
Haka kuma ba free book ba ne, paid book ne a 500.
Few pages ne muke da su na free, sauran duk na kudi ne.
One page ne kullum da yarda Allah, sai dai bana posting Monday da Friday, saboda wani uzurin, haka kuma idan ban samu yi a ranakun posting ba zan sanar kuma zan ranka page din In Shaa Allah.
Yadda na fara lafiya Allah ya amince min na karasa shi cikin aminci da farinciki, Ameen.
Ina fatar zaku karbe shi hannu hudu ba ma biyu ba. 🥰
If you want to Subscribe pay 500 to
2451879008
Hadiza Abubakar
Zenith Bank
And sent the evidence of payment to 08036126660
Yan Nijar zaku biya ta wannan line +22790165991
Za ku iya samun WANI GARI a Arewabooks @KhadeejaCandy domin pages din