Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saffeyya ta rude๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜ƒ.

Maihifinsa yarasu shekara daya data wuce hanyar sa tadawo daga Abuja. Hajiya saudat taji mutuwar mijinta uba danta domin Allah ne gatanta mijinta gata ta domin yan garin Rimin local government ita dashi tatashi A hannun kishiyar maihafiyarta domin wajen haihuwarta mahaifiyarta tarasu su ukku ita da yayyenta yaya sule, yaya mustapa sai itah kishirya maifiyarsu masiffatace Muguwa domin fuska biyu gareta in maihaifinsu nan zata nunamsu Amma da yasa kafa yabar gidan zata Fara dukansu har tagaji.Abinci ma bata basu sai in maihaifinanan. Daga baya ma saita Asirce maihaifin nasu ko gaban idonsa dukansu take.Abinci saitagama dabasu nan ta tilas tawa sai yakai yakai mustapha da Sule karatun Allo tundai mahaifin nasu ya kaucewa domin yana son yayanshi sharrin Ade ne kawai (Allah yaravamu da mugunta)

Har dai taci galaba kanshi yakaisu garin katsina Karatun Allo. Daganan fa Hajiya saudt( mahaifiyar Dr Ahmed) tazama baiwa komai na gidan itakeyinsa Har takai Kimanin shekara17 samari sukayo Mata Ricah domin kyakyawa ce ga babu wadda tafidda ciki sai Iro. (Maihaifin dr Ahmed) nan dai Akayi bikin babu abinda Aka kaimata sai tabarma da fillo da cooler kwara daya taso ayi bikinta yayayenta nan nan Amma tun lokacin da babansu yakoma malamin yace tun wanilokacin dasuka fita bara bai kara ganinsuva. Maihaifin so yadawo hankalinshi tashe. Yana fadima Ade Amma data murza kambu Asiri sai yabar maganarsu.
Ayin bikin saudat babu dangi maihaifiya. Domin tun lokacin DA. Mahaifyar su saudat tarasu sukaso su tafi dash Amma maifinsu yahana sukayi fushi suka tafiyar su basu kar waiwayensuba. Haka Akayi bikinta Bayan wata daya bikin Iro yaje cikin katsina yagamu da Abokinsa wadda sukayi karatu yasamu Aiki daganan har yayimasa hanya yasamu Aiki.daganan yakoma Alhaji ibarhim kwangila. Anabashi kwangilar makaratu masallachi, rijiyoyi. Kumabaya ha inchi cikin Aikinsa shiyasa yayi Suna . daganan sukadawo cikin katsina suka gyara gidansu na rimi saidai insu dawo su sauka ciki dawowarsu da katsina shekara daya Aka haifi Dr Ahmed.

Abin yasamo Asali dalilin dayasa Dr Ahmed yatsani mace. Wata rana yadawo daga kano wajen Amininsa Dr Hafiz yakaimasa ziyara yazo daidai welcome to katsina saiyaga mace tsaye da hijabi tana daga hannu beyi niyyar tsayawaba Amma wata zuciyar tasa yayo baya cikin sauri tazo gabanshi ta tsaya yace cikin fuskar damuwa tace ya taimaka Mata mahaifiyar tace Asibiti bata lafiya. Yamikata gashi kuma bata da kudin zuwa . nan ya tausayamata domin ko yanayi shigarta zaka San tana cikin talauchi.
[1/11, 8:29 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): ๐Ÿ’”CIWON SO๐Ÿ’”
Na
Hafsat (Hafsy baby)

09

Dr Ahmed yace shigo tanashiga sunfara tafiya yace wane hospital ne , tacemasa General hospital, yace OK, sun isa General. Yakaita har can ciki tafito tace masa nagode. Yace babu damuwa yafito yace mushiga naga marar lafiya . domin nasamu Lada ko tayi murmushi tace nagode. Sunashiga cikin haske Dr Ahmed yaga wannan budurwa kyakyawace Amma talauchi yamaidata wata kalah.

Sun isa dakin da Aka kwantar da marar lafiya Dr duk yayi ma majinyyata sannu har suka isa gadon da wannan tanufa tanazuwa tazuwa ta tambayi wani. Yaro dabazai wuce 14 years ba Khalipa yajikin Inna ne khalipa wadda ta tambaya yace gayanan tunda kikabarta tana bacci haryanxu shi take yi kinsamo Kudin maganin domin tafiyarki Doctor yashigo sai fada yake Akan rashi sayen magani Kan lokacin.

Dr Ahmed yaji tausayi yaratsa masa zuciya yayi gyaran murya yace muga takardar magani kalipa yace Yaya Basma wannann waye. Tace shine naroki Alfaarma yarageman hanya Akan dawowata daga gidan Kawu Yusuf. Dr Ahmed ya Amshi takardar daga hannun basma wadda yaji sunanta bakin Kanneta yanufi pharmacy din cikin Asibiti yasiyo magagunan duk daaka rubuta yakawomusu yace su Kira likita sai ya gwadamusu yadda zasuyi Amfani dasu yace saidayaga komai ya kammalla. Yajuya zaitafi Basma tabishi daga baya.

Tace nagode Allah saka da Alkairi bawan Allah daban samu wannnan daga gareka Daban san yadda Zanyi yau ba. Dr Ahmed yace babu damuwa har sukaxo wajen motarshi zai shiga tace kabani number ka koma ringa gaisawa ko. Gashi zakatafi bansan sunankaba. Yace sunana Ahmed
Tace wow nyc name, nan yakaaranto masa number wayansa tasa. Yajuya yanufi hanyar gidan su dake Kwado.
Basma kuma tayi murmushi tace cikin ranta burina yakusa cika Zan Auri mai mota.Kuma kyakyawa (Tofaa daganin sarkin fawa)


One week later


Dr Ahmed ne zaune yana duba wasu papers, yaji wayansa naringi yana dubawa yaga new number ne Kamar bazai dauka Amma kawai yadauka yayi shiru can Akace hello yaji murya mace hello wake magana. Akacemasa Basma ce yace Basma wace vasma dominshi har ga Allah yamanta da bayaninta cikin ranshi tace Wadda kataimakawa rannnan nan tayimasa bayani yace Ayya!! Sorry nagane ykk yamaijiki tace dasauki har An sallememuma. Yau kwana Ukku Inna natayimaka godiya nancema tayi nakiraka kayiman kwantacen gidanku zatazoyi maka godiya. Dr Ahmed yace kicemata na hutar da ita basai tazoba saidai kibani Address naku inasamu time zanshgo ganinanta wani dadi yaratsa Basma (Tofah๐Ÿ™„๐Ÿ™„)
Nan tayimasa kwantacen gidansu Unguwar Yammawa.
[1/12, 8:18 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): ๐Ÿ’”CIWON SO๐Ÿ’”
Na
Hafsat( Hafsy baby)

Wannnan page naki ne . nasadaukar dashi gareki. Aunty Saheeba Lagos.

10



Basma tana datse wayar ta waiwayen wajen wadda suke zaune tace burina yakusa. Cika munerrat wadda aka Kira da munerrat tace shakaman meyafaru Kawata Basma tace kinsa yau ko sati biyu baayi da kwanciyar umma Asibiti ba nan tafada yadda suka hadu Dr Ahmed. Kuma kinsa wani Abu Kawata wallahi yahadu daganinashi Akwai Kudi. Shiyasa Zan likemashi Har sai nasamu soyayar shi. Munerrat tace nadauka wannan burin yafita daga ranki nabaki Auren talaka sai mai Kudi Basma tace chabb!!! Inanh burina nanan na wayagayamiki Auren soyaya Zanyi Ai ingayimiki Ko yanzu nasamu wadda yafi Ahmed wallahi komin tsufanshi Zan Aureshi nataso cikin talaushi Kuma na Auri dan uwana talaka. Munerrat tace shegiya Kawata kina wuta, tace kedai bari. Dai muga zuwa Ahmed din.
****************************
****************************

Abangaren Dr Ahmed kuwa saida sukayi kwana biyu da waya da basma sannan yazo Gidansu Dayazo saiyakira wayanta wadda yayi saving da help, tafito tayimasa iso wajen innata tashiga dashi aga ibo masa ruwa. Cikin kwano duk lamba yanakaiwa yaji wani karni Amma hakanan yadaure yayi mashi kurba daya don karsu gane hakan.

Inna tayimasa Godiya kamar me nan yamike nan yana mikewa yazaro bandir yan 200 ya ajemata yace gashi nan. Inna kamar tayi Kuka taitayimasa godiya. Yafito waje Basma tabiyo bayansa Yaya Ahmed Angode Allah saka da Alkairi tana ta fari da idanuwa tasa wata Atamfa yellow da red. Wadda ta Aro wajen kawarta munerrat. Yace babu damuwa yashiga mota yabar unguwa.

Daganan tun lokacin Basma tashiga isar Dr Ahmed da waya tun bai kulata yana shareta har yana har yakai yana daga wayanta. Daganan fa soyayya tashiga tsakanin Dr Ahmed da basma. Domin basma tana da kyau ba laifi.


Daganan Dr Ahmed yaga halin dasuke cike yagyara musu gidan dasuke ciki, yashiga dinka Basma sutura Kala Kala masu tsada Daganan Basma tashiga wani girman Kai, tadinga jinta Kamar diyar shugaban Kasa, bata iyi ma yan unguwar su magana. Bata harka da sai da yayayen masu Kudi,

*********************************โ€ **************โ€ *******

Soyaya tayi Nisa tsakanin Dr Ahmed da Basma fa babu Kama Hannun yaro. Har yana niyyar fada ba. Daddy dinsa Akan Aiko Gidan su Basma domin ayi Maganar Maganar Manya kwatsam!!! Rannan Basma taje bikin wata kawarta diyar masu Hannu da shuni( domin Basma tacika shige shige inhar yayan masu shine)

KOBIYONI.ZAKUJI KOMAI
[1/13, 4:24 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): ๐Ÿ’”CIWON SO๐Ÿ’”
Na
Hafsat ( Hafsy baby)



11



Basma Anje bikin kawarta Anata yatsina saikace batasan wani Abu talauchi ba.
Anharde bisa Kujera Anata latsa wayar Tecno C8 wadda ko sati daya batayi ba Dr Ahmed yasiyamata itah. Saitaji sallama bisa Kanta tadago Kanta ta Amsa ciki ciki yace ko gimbiyar Mata zata bani damar zama. Tadago fuska tasake kalleshi taga bakalar talaka bane( kuji Basma da karfin hali๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š)

Tace babu damuwa zauna yajawo Kujera Kusa da itah yazauna yacemata Barka da dare tace yauwa yace da farko sunana Mahmoud Kabir Nakowa. Basma tadago fuskarta A razane koshi yalura dahakan yace Kina mamaki ne Ko tace wadda nakeji A gari bama A gariba duka Nigeria Kowa yasan shi yace Shikam. Basma ta jinjina Cikin Ranta ( LaiLai)

Yace tunda kikashigo wurinan naketa hangeki Kuma naga kinyi mini Inasonki Kozan samu karbuwa wajenki Kuwa??? Basma tayi Murmurshi tace Hmmm.

Mahmud bai wurinba saida suka Kulla soyaya da Basma ya Amshi phone number ta tabashi Address din gidansu Ataikacedai shiyamaidata gida. Da akatashi daga party.

**********************************************************************************


Daganan fa Komai yacanza tsaninta da Dr Ahmed ta fara canza mishi inyakirata saitaga dama tayi picking yace Mata meyasa hakanan sai tace bata Kusa da wayar(kuma kunsan wani Abu duk tarrayar da Dr Ahmed betaba fadamaata wayeshi ba).

Rannan Dr Ahmed yazo Suna tsaye Basma wayanta sai ringin yake Amma taki dauka. Dr Ahmed yace Mata waye ke kiranki ne kinki dauka tundazu. Tace wata friend dina plashing danazo Dauka zata Katse ne. OK suka cigaba da zance Amma Abu takama waige waige dahaka sukayi dai bakwana yatafi yazo fitowa yaga wata mota itama tashigo Kuma bangaren Gidan su Basma tanufa Amma bekawo ma ranshi komai ba yatafi.

************************************************************************************

Kwatsam!!!!! Rannnnan Dr Ahmed bai Sanar da Basma zai zoba kawai yazo yanazuwa. Kofar gidansu yaga motar dayagani rannnan nan yakira wayar Basma saidayayi Mata Kira 3 Kawai yaga Basma tafito daga cikin wannan motar tana dariya. Naciki Kuma yaja yabar wurin jiyowar da Basma zatayi kawai taga Dr Ahmed ta firgita dagannishi Amma kawai tabasar tanufo wurinshi tace yallabai shine ko A sanardani zakazo ne. Yace kawai wurinki naji Ina shaawar zuwa ne.Basma Ina. Wayar ki nayi miki Kira Ukku bakiyi picking ba Kuma waye yazo wajenki yanzu questions 2 yajero mata duk tare sorry my dear wayana silance take banji Kirankabane. Wannnan Kuma wadda kaganni saurayin munerrat ne yakawo kararta Akan Abinda takemasa ne. Nan dai ta Dr Ahmed yadaina Zancen. Suka cigaba da firar har lokacin tafiyarshi yayi yatafi.

Lokaci natafiya kwanaki Suna Kara Yawa.Basma ce zaune. Ita da kawarta munerrat A dakin Basma wadda yasha yagyara. Munnert kecewa basma Yanzu ki kyauta Kina tarrayya da Ahmed Kuma Bikin da Mahmoud kingi 1 weeks. Bazaki Sanardashiba Gaskiya bazaki Aureshi ba??

Basma taya tsina Fuska tace dama Ai bamuyi yarjeniyaya dashi zau Aureshi ba ga ida Zan huta. Na hau motar danake so. Saina tsaya ma mai mota daya( ๐Ÿ˜ŠRashin Sani) kyauttata da Ahmed bata wuce 10k zuwa 20k. Iyakarta takenan kiduba Mahmud Ko A sandiyar kyautar dayakkeman nabude Account yanzu Haka Ina 2 million ciki. Inbaki mantaba nafadamiki bazan taba Aure soyaya ba Aure Kudi Zanyi. Ahmed Kuma dama nafadamasa mun tafiya kauyen su Baba kawai sai dai yaji Sanarwa. Suka kwashe da dariya. Munerrat tace Amma baki kyautaba Kawata. Basma tace Kinga tashi mushiga Kasuwa Akwai Abinda nakeson siya.

*****************************************"************** Bayan Sati daya


Dr Ahmed zaune dakinsa yanajin labarai yanata trying din number Basma taki shiga domin yanason yasanar da itah cikin sati nan zai turo iyeyensa ( nufinshi inya fadamata gobe sai yasanar da daddy)

Anagama labarai kawai yaga Anhasko wani hall da Da mutane ciki anata cashewa can aka hasko fuskar Amarya DA Ango yaga kamar yasan fuskar Amarya Kamar sunsa Abinda ke ranshi Aka Kara dallaro fuskar zata ba Angonta Cake A baki. Kawai yaga fuskar Basma ya mike razane yace karya ne Ba Basma danasi bace Basma bazata yaudareniba. Kawai yaji Ana wakar Bikin Amarya Basma da Angonta Mahmud sunyi Aure. Dr Ahmed yazauna ragwab!!! Bisa Gado yace Basma nizatayi makahaka nixata yaudara Amma bata tabs nunaman ko Afuska ba .Amma babu komai Kanta ta cuta



Basai lokacin daya dauka yana tunanin ba shigowar text yaji awayashi shine yadauka yaduba yaga Basma ce. Tarutabamashi kamar haka



Aslm Ahmed dftn kana lafiya. Bawannan ba nasonka mutum ne mai Kallon labarai A kodayaushe. Kuma nasan zakaga wani Abu. Yabaka mamaki. Ba Abun mamakibane Domin ba muyi yarjejeniya dakai Zan Aureka. Inkuma Kana bukatar kudinka tundaga wadda kabiyama Inna Asibiti harzuwa yanzu zaka iya zuwa office din mijina Mahmud kabir Na kowa zaa biyaka bye bye.


Dr Ahmed yaja numfashi yagoge text din da number Basma baki daya
Daganan fa Dr Ahmed yatsani kowacce mace Aranshi Domin tunanishi duk haka suke( Anya kuwa)

Tofa shine Safeeya tafada ciwon so Dr Ahmed. Zata cimmma burinta kuwa. Kuwa .???

Wane hali take yanzu A Asibiti ???

KUBIYONI...........
[1/14, 11:33 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): ๐Ÿ’”CIWON SO๐Ÿ’”
Na

Hafsat ( Hafsy baby)

12




A bangaren Safeeya can kuwa wajen 12 Am tafarka daga Allura bacci da akayimata.

Taga babu kowa A dakin sai ita daya cikin ranta tace nasan su umma suka kawoni Asibiti to Ina sukaje.

Tanacikin wannnan tunane taji Antoro kofa ta waiwaiya taga waye.
Taga Doctor Sadeeq ne Family doctor dinsu ne.

Yazo har inda take yajawo kujerar yazauna yace Safeeya kinfarka ne,
Tace nafarka Doctor Sadeeq yace yanzu yakeke jin jikin naki ne tace naji sauki.

Yace to Alhmdlh safeeya. Yacemata safeeya meke damunki ne Har ciwon zuciya yakamaki Haka irin wannan ciwon ne.
Dayayi yawa zuciya ke bugawa. Meke damunki haka gashi kinsa damuwa cikin ranki.

saffeya tadukar dakanta kasa sai Hawaye cikin ranta tace Doctor Ciwon So mutumin dabasai inayiba sai tsanata dayakema.

Amma bazan iya fadama kowan haka tadago fuskarta tace Doctor kayi Hakuri bazaka iya jin komai bakina ba Amma Zan rage sa Abin cikin zuciyata insha Allah.


Dr Saddeq yace dayafiyi ko kima komai ga Allahh.kinji KO. Tace insha Allah. Yajuya zai fita Saffeyya tace Doctor Ina su umma ne???

Yace nace suje gidanane domin baa bukatar kowa wajenki sai gobe zasu dawo ne nima inaga jikin yayi sauki gobe Zan baki sallama.

Haryajuya zai fita saffeya tace Amma... Doctor yace yane saffeya yajuyo yadawo tace don Allah kada ka sanar da su Abba cewa ciwon zuciya ne.

Yace Mata meyasa tace masa don Allah kada kasanardasu Hakanan.
Kacemasu ulcer ne ulcer ne.

Doctor yazare Ido๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ yace meyasa saffeya tace nidai Alfarma narokeka.tana niyyar Kukaโ˜นโ˜น

Yace tonaji Amma da sharadi?? Tace wane yace komai zaki cireshi cikin ranki . kidaina damun kanki. Inko baki dainanaba zanfadama Abbanki Abinda kedamunki.

Tace insha Allah Zan cireshi doctor. Yace yauwa safeeya. Yanzu saiki kwanta kicire komai. Cikin ranki kinjiko. Ta gydamasa Kai ya juya yafita.

Saffeya ta rintse idanuwanta wasu zafafen hawaye suka zubomata.

Cikin ranta tace Ya Allah ka cireman Dr Ahmed cikin raina inba Alkairi ne ba. A tare Dani. Domin wani sonshi yaji yana Kara shiga Ranta. (Allah sarki saffeyya)


WASHE GARI



Abba da umma harda Meenat domin tace bazata school saffeyya bata lafiya. ( yar Uwa Rabin jiki)
Suna shiga suka nufi office din Doctor suka iskeshi zaune A bisa kujera yana duba wasu file. Doctor saddeq yace Ahhh,,, Alhaji sannu dazuwa nan suka gaisa Abba yace doctor yajikin safeeya ne yace Alhmdlh zaku iya zuwa kuganta taji sauki yauma dasafe mun maidota dakin dakowa zai ganta.


Abba yace Alhmdlh to Doctor yace muje nagwadamuku dakin suka rankaya suka nufi har dakin suka iske safeeya kwance Meenat ta matsa wajenta sister yajikin safeeya tace mata dasauki saikawai taga Ashe tare suke dasu Umma tana kokarin mikewa ne Abba Aaaaa Safeeya kwanciyarki. Tace Abba da umma. Ina kwanku, suka ce mata lafiya lau Safeeya yajikin tace Alhmdlh. Sukace to Allah yakara sauki. Tace Ameen.Doctor yace Alhaji inkagama inason ganinka office. Abba yace to babu damuwa, Doctor yajuya yafita. Gaban saffeya yafadi.

Amma bata nunaba Abba yace bara naje umma tacemasa to.
Umma tace saffeyya kina iyawa Meenat takaraki toilet kiyi brush ko ruwan tea ne kisha, tace Eh Meenat takama ta suka shiga toilet.
Tadawo umma tahadamata tea mai kauri tana Kurba kadan kadan
Saiga Abba ya shigo cikin Fushi Gaban safeeya yafadi
Yace Safeeya mekika rasaAmmm....


KOBIYONI๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜. For comment

08164042255
[1/15, 3:49 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): ๐Ÿ’”CIWON SO๐Ÿ’”
Na

Hafsat ( Hafsy baby)

13





Abba yashigo cikin fushi yace Safeeya meke damunki ne,haka, cikin inda zata Fara magana.

Umma tace Abba Yan biyu me Doctor Din yafadamaka ne.

Yace man Ulcer ce takamata. Saboda rashin cin Abicin datake. Mekikarasa rasa ne?? Ko meke damunki ne??

Safeeya tayi wata Ajiyar zuciya jin doctor befadi Abba Abinda kedamunta.
Tadukar dakanta.

Batace dai komaiba. Abba yace Abinci kan yakare na aje wani. A store. Amma kifadi meye damuwarki.

Dahar yahanaki cin Abinchi ne?? Safeeya ta gigirza Kai Abba babu Abinda ke damuna.

Yace Kuma Har ulcer takamaki haka. Ne. Banason haka kinji ko kidinga cin Abinci.

Tace Abba zandiga ci insha Allah yace yauwa yanzu inki gama ci farfesu Rago zakici Ko Faten doya zakici ne. Ta shagwabe fuska.

Abba sai zuwa Anjima Anjima naci yace A,a kidaure kici inki gama shan tea din

Safeeya tace Allah zanci Abba yanzu nacika cikina bakajiba.



Yace to shikennan Allah yakaimu Anjima to. Yanzu. Zan bar umma ki Zan tafi office sai nadawo. Allah sawwaka tace. ameen Abba. Sai kadawo umma da Meenat sukace Allah yakiyaye yace Ameen yajuya yafita.

Nan Safeeya tagama shan tea din suka dan tafa fira can wajen 2 hour umma tace meza Samata takaradashi .


Tace Asamata Fate doya yaji wake da Alllayahu sai tashi Kamshi yake.
Can nahango Aunty Saheeba itada Nana A Usman Suna maida yawu Amma Safeeya taki yan musu๐Ÿ˜‰๐Ÿ˜‰


Nandai Safeeya taci Harda tirsawawa umma taci da dan yawa. Ta Aje Tasha Magani da Doctor yakawomata dakanshi yace shine zata sha insha Allah zataji sauki.

SCHOOL

Abangaren Dr Ahmed kuwa yau yashiga school. Yanufi class dinsu Safeeya. Kawai sai nahango Dr Ahmed yana mika wuya yana waige waige ( Tofa meyake nema ne meya ke nema kudai muje xuwa)


Yagama Abinda yake yafita babu Abinda yanufa sai office dinshi yana zuwa ya zauna bisa kujera. Yadafe kanshi yace meke damuna kardai Ace son wannan yarinya nake. Nan yafara tunanin domin wata Rana yashigo school yaga Safeeya da Meenat tundaga rannar Meenat tafara burgeshi saboda kamun kanta Amma yadinga karya ta zuciyar sa domin yace mace ba abin yarda bace. Daganan yafara gwada Mata tsana domin karyayi wasa sonta yashiga ranshi.

To Abin yakara rikicemasa tunda ga Ranar da tazo har wurinshi.

Yau Kuma yashiga class dinsu begantaba ko tayi Fushi zata daina zuwa ne

Akan Abinda nakemata.








For comment

08164042255.
[1/16, 6:52 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): ๐Ÿ’”CIWON SO๐Ÿ’”
Na

Hafsat ( Hafsy baby)

14

Kuyi hakuri masoyan Ciwon so jiya nayi mistake wajen Rubuta sunan saffeya. Inda Dr Ahmed ketunani sai Na rubuta sunan Meenat kuyiman Afuwa๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป


Asibiti.


Doctor ne ya shigo dakin da Safeeya take yatadda ita daya su umma taje gida tadawo domin girkin Rana,

Meenat Kuma tadan fita tadawo, Doctor yace safeeya yakike jikin yanzu tace Alhmdlh yace to Zan baki wani magani sau 1 zaki dinga shan shi Kuma inkika cire damuwar ranki zakiji sauki sosai tace insha Allah,

Doctor zan kiyaye yace yauwa zuwa gobe insha Allah Zan sallameki,
Tunda naga jikin naki yayi sauki.

Yajuya yafita. Bayan fitarshi saiga Meenat tashigo tace sister Safeeya tace Naam sister kindawo Meenat Eh Aidama ba nisa na dan mika kafana ne. Nan suka cigaba da firar su har Umma tadawo tayo ma Safeeya Abinchi ta daban na marar lafiya. Nan tadaure taci domin umma tace inbataciba zata fada ma Abba,

Washe gari


Da safe Doctor yashigo yaga jikin Safeeya yaga dasauki yabata magani dasukayi Magana yace taringa shan daya Arana Abba daban kan yatafi office yabiyo nan Doctor yake fadamasa yaga jikin Alhmdlh zai bata sallama.

Abba yace babu damuwa. Doctor yashiga ya rubutu takadar sallama yabasu,

Abba yace suzo ya ajesu gida sai yawuce office suka hada yan kayansu wadda sukazo dasu. Suka tafi

Abba yanashiga gidan ko yana Ajesu yanufi office


Safeeya ko Suna shiga tazauna bisa kujera domin tace tagaji da kwanciya bari ta dan zauna ta huta. Basu jimawa da dawo wa ba,

Saiga Haidar yashigo yayi sallama ya iske umma da Meenat saffeyya, saffeyya naji sallamar shi tayi saurin rintse idanuwanta Kamar me bacci.,

Umma tace haidar Kaine shigomana ya durkusa cikin ladabi yace umma Ina kwana, tace lafiya lau, haidar, ya wurin mamyn taka dajikin yace Alhmdlh Ankwace daurin yanzuma taka kafar Amma ba sosai ba umma tace Ai sai A hankali Allah yakaro sauki. Yace Ameen umma,

Haidar yace yajikin safeeya ne naso zuwa wallahi umma Aikin office ne yayi yawa dayau zance Sai naga shigowarku Abba ya. Ajeku.
Umma tace babu komai Haidar,
Dasauki sosai tunda An sallamemu taji sauki. Umma tawaiwayen inda saffeya take Safeeya!! Safeeya!!!!
Cikin Alamun Kamar tana bacci naam umma tace Haidar ne yazo ganinki. Cikin daure fuska tace Ina kwana yaya Haidar cikin Fara' a yace lafiya Lau saffeyya yajikin tace Alhmdlh, daganan bata karacemasa komai sai da Meenat yake fira jefi jefi har yamike yatafi,

Dama umma tashiga ciki tadan gyare gyare kwana biyu baiga gyaraba.

Meenat tadawo kujerar da Safeeya take sister wai meyahadaki da yaya haidar baki sakar masa fuska ne, saffeyya tace babu komai keh tajawo wata first




School


Dr Ahmed ne zaune bisa kujera yana hada wasu file yaduba Agogon Hannusa yaga lokacin shiga lecture yayi, Kuma class dinsu Safeeya zaya, yanashiga yagama Abinda yake, Amma da kalleshi kasan yanacikin damuwa ( Abinka da miskili)

Yanufi office yazauna yace meke damun wannan yarinyar yau kwana3 batazo school ba ko yar uwata banganiba gashi yau Friday.

Gaskiya rannan Monday inbatazoba Zan tambaya wadda naga Suna zama tare naga ko lafiya duk wannnan Maganar yanayinta cikin zuciya


Domin yanzu so safeeya kawai yaji yana shigan zuciyarsa ( Tofa su Dr Ahmed Anshigo wajen)

Domin ko ga basma baijin wannnan beyi hakaba


Muje zuwa dai๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜




For comment

08164042255
[1/17, 1:24 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): ๐Ÿ’”CIWON SO๐Ÿ’”
Na

Hafsat (Hafsy baby)


15





Safeeya ce kwance bisa gado tana tunanin yadda zata fidda son Dr Ahmed cikin ranta,.

Amma me datafara tuninshi zataji Kamar Anakaramata son shi naji take Kamar tajawo Ranar Monday. Taje school don kawai taganshi, Amma tayi Mata kanta Alkwali zata ragema zuciyar ta tuninshin insha Allah,


Meenat tace shigo dakin datake sister Kizo inji Umma ga girki can Angama, safeeya ta yatsina Fuska Kai sister Abinchin nan basai Anjima zanci ma Meenat tace A,a umma tace nataso ki har muntafi tare,


Badon

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

1 Comments On CIWON SO
avatar
ammin

1 year ago

Reply

Interest

Please Login or Register in order to submit comment