Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sawun dakin
nasa ma ya bace bat.
Bisa dole suka hakura suka koma can masaukinsu..
Da isarsu sai Husam ya duni zaunal da lasmir yace
Sarauniyar kasuwa ta ci amana ta tabbas wadannan
dakarun da suka zo mana aiken makiyanmu ne baskar.
Dole ne mu kwashe kayanmu daga nan mu tafi izuwa
birnin daban.
Domin neman dakaru dubu dazasu taimaka mana wajen
shiga birnin azzalumai kamar dole nemuyi taka tsatsan
akan komai da kowa.
Tabbas yanzu sarki baskar da bokan zarmus sun san cewa
mun fito shirin zuwa birnin azzalumai .
Batarre dawata gardamaba sai zaunal da lasmir suka
shiga hada kayayyakinsu..
Page 9
zidane kd.
Nan da nan kuwa suka gama kintsawa suka nufi wani
bangare daban a cikin daji..
Suna cikin tafiyar ne zaunal ya waigo bayansu sai yaga
wani abu daya bashi mamaki ba wani abu yagani ba face
yadda sawayen dakarunsu ke bacewa bat nan take amma
da yake ya san cewa akan shirin Husam sai kawai yayi
murmushi ya juyar da kansa suka ci gaba da tafiya..
Sai da suka kwana uku cur suna tafiya kuma ba sa yada
zango face dare yayi sosai kuma sai da duhu sannan su
kwana , kashe gari kuwa sai su tashi da sassafe su cigaba
da tafiya a kwana na uku ne da farkon yammaci suka
hangi wani dan bban gari a gabansu.
Da yake Husam ne akan gaba sai ya ja linzamin dokin ya
tsaya cak ya kurawa garin idanuwa da ganin haka sai
summa zaunal suka yo koyi dashi..
Tsawon kusan dakika dari shida Husam na kallon garin
idanunsu a kafe ko sau daya bai kifta ba alamar cewa
nazari yake yi acikin halwar tsafi..
Daga can sai yai doguwar ajiye zuciya gami da motsa
idaninsa ya dubi zaunal da lasmir yayi murmushi yace ba
mu da wata matsala acikin wannan gari sai guda daya..
Caraf sai zaunal yace wace irin matsalar mutanen
wannan garin ita ce tsananin son kudi, mazansu da
matansu.
Akan kudi babu abinda ba zasu iya yi ba. Koda jin haka sai
lasmir tayi murmushi tace aikuwa indai suna da son kudi
za muyi saurin samun abinda muke bukata.......
ANAN ZANDAKATA SAI KUMA IN ALLAH YAKAIMU GOBE
DA SAFE ZAKU JINI DA CIGABAN WANNA LABARIN .
NAKU HARKULLUM SULEIMAN ZIDANE KD..
KUYI COMMENT.. DA share :...... IZUWA WANI GROUP..
ANA TARE....
BIRNIN AZZALUMAI 4
Littafe na hudu
Part B.
Typing.. Suleiman zidane kd..
09064179602:
KODA JIN HAKA SAI LASMIR TAYI MURMUSHI TACE
AIKUWA INDAI SUNA DA SON KUDI ZAMUYI SAURIN
SAMUN ABIN DA MUKE BUKATA..
Page 11
Tana gama fadar hakan sai ta kada linzamin dokinta tayi
gabata na mai tunkarar kofar birnin...
Batare da barta lokaci ba kuwa sai Husam ya bi bayanra
sannan zaunal...
Da isowarsu kofar garin sai suka iske kofar a rufe dakaru
biyu na tsaye daga waje a wajen shigar yabi daga ciki
kuma akwai kimanin dakaru guda dari a tsaitsaye cikin
sharin ta kwana ...
Daya daga cikin masu gadin biyu ya dubi su lasmir da
kyau ya kare musu kallo yace kusu wannenne?
Kuma menene ya kawo ku nan sarlak?
Har lasmir ta bude baki zata bashi amsa sai Husam ya tari
numfashinta yace mu mutanen birnin hal ne sannan
kuma fatauci ya kawo mu nan.
Page 12
zidaen kd..
Koda jin haka sai badakaren nan yayi murmushi yace
barkanku da zuwa sarlak..
Batare da wani bata lokaci ba sai badakaren ya bude
musu kofa ya ceku zo ku shige..
Husam ya bude su cikin mamaki yace ai baku cake
kayanmu ba..
Badakaren yayi murmushi yace kar kadamu ai mun
sauya tsari..
Gimbiya na ciki ita ce za ta caje ku..
Koda jin haka sai hankalin su Husam ya tashi jikinsu ya
basu cewa ruwa ba ya tsami banza lalle akwai wani abin
da yafaru wanda ya sa aka sauya tsarinan wannan garin....
Kai tsaye suka kada dawakansu izuwa cikin gari na Sarlak
amma wannan karo husa, ne akan gaba zaunal na biye da
shi lasmir .
Suna shiga akan mai da kofa aka rufe ..
Take suka ga wadansu dakaru guda dari cikin gagarumar
shigar yaki..
Page 13
zidane kd..
Hamsin na tsaye a dama Hamsin na tsaye a hagu..
A tsakiyarsuu akwai wani karamin gado na katako mai
dauke lema samansa.
Kwance akan gadon wata jarumar ce cikin shigar kayan
yaki na karfe.,
kanta mana cikin hular karfe tana shara barci abinta ..
Koda su hasam suka zo zasu gifta ta gaban wannan
mayakiya da ke barci sai kawai suka gata daga hannunta
guda nan take dakaru suka sha gabansu husam kana
tsayar dasu..
Mayakiyar ta mike zaune daga kwance sannan tasa
hannayenta biyu ta cire hular karfen dake kanta...
Nan take kyakkyawar fuskarta ta bayyana a lokaci da
dogon gashin kanta ya tarwatse a sama cikin iska kuma
ya zubo a bayan gadonta..
Koda ta bude kyawawan fararen idanunwata ta dubi su
Husam sai nan take zaunal yaki zuciyarsa ta buga d karfin
tsiya fiye da lokacin da yayi wa lasmir ganin farko..
Page 14
zidane kd..
Koda mayakiuar tayi arba da zaunal sai ta kura masa
idanu ko kifatawa bata yi kuma ta kasa mikewa tsaye har
sai da daua daga cikin dakarunta yayi mata magana yace
ranki ya dade ba duba su zaki yi bane..
A kasannan ne mayakiyar ta mike tsaye zumbur tamkar
wacce ta farka daga mafarki ta karaso wajensu ,..
.
A wannan lokacine lasmir ta murtuke fuskarta nayiwa
mayakiyar wani irin kallo na rashin yarda...
Nan dai mayakiyar ta sa aka caje kayansu Husam koda
taga suna dauke da dinare mai yawa sai fuskarta ta
fadada da Murmushi ta dubi Husam cikin risinawa da
biyayya tace lalle marhaban da sarkin jiya na birnin
azzalumai ..
Page 15
Koda jin wannna batu sai zukatan su Husam suka buga da
karfi sbda tsananin mamaki har firgicinsuu ya bayyana
karara akan fuskokinsu...
Daga nan haka sai mayakiyar ta tuntsure da dariya
sannan ta dubi husam cikin nutsuwa tace kwantar da
hankalinka yakai ma abocib adalci wannan dakeson
daukar fansa akan mace amanarsa..
Ka yi sani cewa har abada bazan taba zama mai cutar
dakai ba saidai na taimake ka akan kokarin cika burinka..
Yau shekara goma kenan nae jiran zuwan wannan rana
da zakazo wannan birnin namu domin a dalilin nima zan
sami damar cika nawa burin. Sannan gimbiya risha ya ga
sarki marzak na wannan birnin namu.
A dalilin wanna zuwa nakane muka sauya tsarin tsaro a
garinmu ba don komai ba sai don mu hana makiyan ka
samun damar shigowa birninmu.
Page16
Lallai ku manyan baki ne masu daraja a wannan gari
kuma mahaifina zai yi matukar farin cikin zuwanki..
Ku zo mu karasa fada..
Zarisha na gama fadin hakan sai ta nufi inda aka daure
dokinta..
Nan fa husam lasmir da zaunal suka kama kallon juna ba
tare da daynsu ya iya cewa koamai ba...
Husam ne ya fara kada dokinsa ya bi bayan gimbiya
zarisha ....
Koda ganin haka sai zaunal da lasmir suka bisu ..
Zarisha ta ci gaba da yiwa su zaunal jagora izuwa cikin
gari amma sai tarinka yawan waiwayowa baya tanba
kalon zauunal, hakan ne yasa lasmir taji ranta ya baci, ta
cigaba hararrarta...
Page 17.
Duk da zarisha ta lura da yadda lasmir ke hararrata ko
kadan bata dam ba shi kuwa zaunal da yaga kallon da
zarisha ke yi masa yayi yawa sai ya sunkuyar da kansa
kasa ya daina yarda suna hada idanu..
Shi kuwa Husamm wani abu ne ya sameshi wanda yayi
matukar daure masa kai yajefa shi cikin wasi wasi da
fargaba..
Ba kamai ne ba wannan al amarinba face jiyayi a karon
farko yayi arba da zarish ya kamu da tsananin sonta
ku,ma so ron wanda namiji ke yi wa matar da yake son
mallaka a matsayin abokiyar rayuwarsa...
Akan wane dalili zanso wannan budurwar sa ar yar cikina
alhalin tsawon shekaru goma ina begen matata zamirat
mace dana so fiye da dukkan matan duniya kuma akan
tana fara soyayya kuma ban kara jin ina son wata ba sai
yanzu...
Page 18
zidane kd..
Amma dai idan haka so yake to tabbas so mahaukaci ne
kuma kuruciyarsa tafi ta yaro dan shekara uku tun da
gashi yana neman jefa ni cikin ramin karya..
A bangaren jarumar las,mir kuwa itama zuciyarta cika
makil da wasi wasi tarinka yiwa kanta tambayar barkatai
mnarasa cikakkiyar amsa ...
Tambayar farko da ina kishin kallon da zarish ke yiwa
zaunal?
Shin hakan na nufin na kamu da sonsa kena?
Kyau ko jarumtaka?
Bai fini kyau ba.
Jarumtaka kuwa in yafini ai da kadan ne.
Babu wata hukka da zata sa na kamu da sonsa..
Kamar yadda lasmir ta kance a cikkin wanna hali na
zance zuci haka shi ma zaunal ya kasance..
Abin da zuciyarsa ta fara raya masa shine ina ma ace
allah zai mallaka masa wadannan matan
Page 19
Biyu a matsayin matansa na auew ai da shikenan ya rufe
kofar karin aure,,.
Wata zuciyar kuma sai tace dashi kai wawa ai da baka
taba zaton zaka ga wata mace mai kyan lasmir ba sai
gashi kuma kaga wacce mata fitta zarisha?
Sa adda zaunal yazo daidai nan a zance zucinsa yaga sun
iso fadar sarki marzuk mahaifin gimbiya zarisha..
Nan take suka sauka daga kan dawakansu su hudu
hadinai suka kama dawakan su tafi su.
Page 20
Zarisha ta wucce gaba suna biye da ita suka kunna kai
cikin fadarr ba tare da wani shamaki ba...
Marubuci yace ABIYO MU A LITTAFE NA GABA DON JIN
MAI ZASU TARAS A FADAR...
NAKU HARKULLUM SULEIMAN ZIDAN KD.....
PAGE...
Aslm yan uwa ga page dinnmu sai kayi kokari shiga
domin samun Littafe Kala Kala cikin blue dinnan Na kasa..
Duniyar Masoya Litattafan yaki only
Home of Littafan Yaki And Hausa Novels
Hausa Novels And Yaki by Zidane
Matan Arewa Special Group
Zauren Muslims
BIRNIN AZZALUMAI
Littafi na Biyar 5
Na Abdulaziz Sani M Gini
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
BIRNIN AZZALUMAI 5
Littafe na Biyar .
Complete book 5
Typing.. Suleiman zidane kd...
Shekaran bugan littafe 2018:
Page 3
Fadace Babban kuma kasaitacciya.
A kwalla sai da suka ratsa ta cikin kofofi bakwai sannan
suka iso inda sarkin Zaruk yake.
Bisa wata katuwar karaga suka hango shi azaune fadawa
da dakaru da mutane gari sun yi masa kawanya ana ta
tafiyar da harkokin mulki cikin nishadi da farinciki .
Koda sarki zarmuk ya hango Gimbiya zarishi tare da su
Husam sai ya mike tsaye cikin matukar farinciki ya sauko
daga kan matattakala karaga ya taresu .
Nan take ya rungume Husam yananuna tamkar wanda
yaga dan uwansa najini..
Cikin Girmamawa da karramawa ya kama hannun Husam
yajashi Har zuwa kan karagarsa ta mulki suka zauna tare..
Ita kuwa mulki suka zauna tare .
Ita kuwa zarisha sai ta mikawa zaunal Hannunwanta da
nufin ta kamanashi ta jashi izuwa mazauninta sai yazuke
hannun nasa ta kamo Lasmir..
Koda suka hada idanu sai zarish ta yiwa lasmir
murmushin dole tta jata suka nufi wajen zaman nata
suka zauna..
Page 4
Zidane kd..
Shi kuwa zaunal wani ba fade ya kai shi wani wurin
dabam ya zauna....
Nan take aka kawo wasu Husa, abinci da abin sha na
alfarma suka ci suka sha a lokacin da wadansu mawaka
da yan rawa ke dauke musu kewa a tsakiyar fadar...
Ana cikin wannan sha ani sai marzuk ya dubi Husam a
cikin fara a yace har abada sark sarki ne ko da baya kan
karaga ballantana sarkin dake daf da komawa kan karaga
tasa .
Sa adda Husam yaji wannan bati sai yayi dan guntun
murmushi yace mecece Hujjarka har da zaka ce ina daf
da komawa kan karagarta?
Page 5.
Zidane kd.
Marzuk yayi murmushi yace ai zuwan wannan jarumin
da kuke tare dashi ya tabbatar da hakan gareni da kuma
zuwanku birnina..
Tsawoon Shekaru da kayi akan karagar Har ka sauka baka
taba kawi min ziyara ba ni ma ban taba kawo maka ba
alhalin muna makotaka da juna sai yanzu...
To nima bincike nane ya nuna min cewar duk ranar da ka
kawo kanka kasata a wannan lokacin zan cika babban
burina da ya gagare ni tsawon shekaru cikin mamaki
Husam ya dubi Barzuk yace menene Wannan burin naka?
Buri na da naka kusan iri daya ne.
Yar uwata wadda muke uwa daya uba daua kuma wacce
ita kadai ta rage mini daga cikin zuri ata tana hannun
boka zarmus bokan dake taimakon babban makiyinmu
baskar..
Page 6.
Zidane kd.
Yau shekara goma sha daya kenan rabona da ita.
Kuma duk yadda zanyi na yi domin na karbota na kasa...
Bincike ya nunamin cewa dole kun hada karfi da karfe
daku da yata Gimbiya Zarisha sannan zaku iya kawar da
sarki baskar da boka zarmus sannan zan sake ganin yar
uwata jalila kai kuma kaga matarka zaminat....
Sa adda sarki marzuk yazo nan a jawabinsa sai Husam
yasake kamuwa da tsananin mamaki yace yanzu kana
nufin kace zarisha jarumace?.
Zarmus ya gyada kai cikin murmushi yace kwarai kuwa
yata gagarumar jaruma ce kuma gawurtacciyarr
matsafiya ba na zaton cewa akwai abinda za ku fita kai da
yarka da bakon jarumi Zaunal sai dai akwai wani abu da
Daya shigemini duhu akan zaunal.
Page 7.
Zidane kd.
Husam ya gyara zama yace mene ne ya shige maka duhu
akan jarumi zaunal?
Zarmus yace bisa binciken danayi duk irin masifar da
zaunal zai shiga da kuma tsananin walahar da zai sha
babu wani mahaluki da zai sami nasarar hallaka shi walau
mutum ko aljani kwaro ko wata dabba.
Kaga kenan yana da wata baiwa ta musamman wacce
mukakaso gano kota mecece nida zarisha..
Ka sani cewa nan da kwanaki biyu kacal za a kammala
shirin wanna tafiyar izuwa Birnin Azzalumai ni ma dani za
ayi wannan tafiya amma ina mai baka shawara da hakura
dayin wannan tapiyarr ka barawa lasmir wannan sandar
taka ta tsafi ta tafi kuma ka zauna anan ka jira mu muje
mu dawo..
Cikin matukar mammaki akaro na biyu Husam ya sake
duban sarki marzuk yace sbda me kabani wannan
shawarar?
Marzuk yayi shiru kamar ba zai bashi amsa ba yayi ajiyar
numfashi sannan yace sbda idan kaje birnin azzalumai
mutuwa za kayi...
Sa adda Husam yaji wannan batu sai hankalinsa ya
dugunzuma yayi shiru baice komai ba,..
Bayan an gama zaman fada sai aka kai su Husam
masaukinsu..
Wani kayatacce gida mai dauke da komai na jin dadi.
Kuyangin dake hidima a gidan sun kai su ashirin da biyar
kuma dukkansu kyawawa ne yan mata.
Nan take aka rabawa su Husa dakuna wato kowannen su
aka bashi dakinsa daban..
Page 9.
Zidane kd..
Bayan Jarumi Zaunal yashiga cikin dakinsa ya ajiye
kayansa sai dawo falo ya zauna domin ya dan huta kafin
lokavin barci yayi..
Zamansa keda wuya sai yaji an kawankwasa masa kofa..
Batare da yasan ko waye ba sai ya bada izinin shigowa...
Sbda shi azatonsa Husam da Lasmir ne sukazo domin su
tattauna akan gagarumar tafiyan dake gabansu...
Kwatsam sai yaga ashe gaba dayan kuyagin gidan ne su
ashirin da biyar suka shigo dukkaninsu sai suka jeru a
gabansa..
Babbar a cikinsu ta dube shi tace ya shugabana gamu
gareka ka zabi wadda kake bukatar data debe maka
kewa...
Kodajin wannnan batu sai mamaki ya kama jarumi
zaunal kuma ransa ya baci ya dubeta a fusace ya ce bana
bukatar dayanku ku fice mini daga dakii batare da wata
gardama ba sai kunyangi suka fice gaba dayansu....
Page 10
DALILIN YASA NIMA NABI BAYANSU KENAN DAN KAR
LAIFIN WANI YA SHAFE NI .........
SAI KUMA IN ALLAH YAKAIMU GOBE ...
NAKU HAR KULLLUM ZIDANE KD..
BIRNIN AZZALUMAI 5.
Littafe na biyar.
.
.
PART B.
Typing Suleiman zidane kd.
Page 10
Kodajin wannnan batu sai mamaki ya kama jarumi
zaunal kuma ransa ya baci ya dubeta a fusace ya ce bana
bukatar dayanku ku fice mini daga dakii batare da wata
gardama ba sai kunyangi suka fice gaba dayansu....
A dai dai wannan lokacin ne gimbiya Zarisha ta nufo
dakin kwatsam sai ga Lasmir mata taho.
Suna hada idanu sai lasmir ta murtuke fuska ita kuwa
Zarisha sai ta kama yin murmushi.
Kusan tare suka shiga cikin dakin suka iske jarumi zaunal
a zaune yayi tagumi.
Koda yaji motsin shigiwarsu ya dago kansa sai yayi arba
da yanmatan biyu tsaye a gabansa.
Cikin kaduwa da mamaki ya mike tsaye ya dube su yace
lapiya?
Me kuka zo yidakina yanzu?
Lasmir tace inason nagana da kai ne ya kai dan uwana.
Kodajin haka sai zarisha ta kyalkyale da dariya tace ta
yaya zaunal ya zamo dan uwanki alhalin baki da wata
nasaba ta jini dashi?
Idan baki sani ba ki sani nafiki sanin komai a kansa kuma
kai mana nasan komai akanki.
Shi din nan da kike gani ba ya tsafi kuma tsafi baya tasiri a
kansa kuma ya kasance ma abocin addinin musulunci.
Koda jin haka sai idanun zaunal da na lasmir suka zazzari
suka kamu da tsananin mamaki...
Zarisha ta kyalkyale da dariya sannan tace ni da kuke duk
min kamu da sonsa domin zukatanmun suna ta tunanin
kuma suna tayi mana wasi wasi akansa.
Soyayyar mu a gare shi ta banza ce domin dayarmu ba
zamalleki shi ba..
Wadda zata mallakeshi zata bayyana a can birnin
azzalumai kuma mace ce wacce duk tafi mu kyau ta fi mu
matsayi ta fimu shekaru.,
tunda nidake duk baza mu mallakeshi ba ina rokonki da
ki ara mini wannan rana ta yau da shi muyi soyayya ta
dare daya...
Kafin Zarisha ta gama rufe bakinta tuni jarumi zaunal ya
daka mata tsawa yace da bakinki kinceni ma abocin
addinin musulunci bane to mu a dokarmu ba ma kadaita
da wata mace face muhararrama ko matar aure don
haka ba na bukatar zaman wani lokacin ku alfarma guda
daya ke da ita ku rufa mini asiri kada ku gayawa kowa
cewa ni musulmi ne don fadin hakan zai iya janyo
mattsala a cikin gagarumin aikin dake gabanmu..
Da jin haka sai jaruma zarisha tayi murmushi tace kada
ka damu ba zan kara gayawa kowa ba,
amma dai mahaifina ya san ko kai waye..
Page 13.
Zidane kd
Na yarda yanzu zan tafi na barka amma na tabbatar
dacewa dole mu kasance tare ko da kuwa a mafarki ne..
Tana gama fadin hakan sai ta juya ta fice daga cikin dakin.
Fitar ta ke da wuya sai zaunal ya dubi lasmir yace ku
kuma me kike jira baki tafi ba??
Lasmir tace ina da tambaya guda daya a gare ka kafin
kafin ka amince akan zaka taimake mu mu yaki Sarki
baskar domin karbo Mahaifiyata daga Hannunsa Abbana
yace ka fadi ladan da kake son mu biya ka?
In dai ka ba ni amsar wannan tambayar ba zan sake
kusantarka ba...
Lokacin da jarumi zaunal ya ki wannan tambayar sai ya yi
ajiyar zuciya sannan yace har yau har gobe na kasa yanke
hukunci akan ladanDa zab nema a wajenku..
Page 14.
Zidane kd..
Abin da zuciyata ta rayamini shi ne bazan iya gani abinda
ya dace na nema ba face bayan burinki yacika.
Sa adda lasmir ta ji haka sai hankalinta ya dugunzuma ta
juya da nufun fita daga cikin dakin har tasa kafarta a
wajen sai ta sake waigowa ta dubi zauna tace shi kayi
tunanin ko wacecce zata mallake ka nan gaba?
Shin ka amince da duk abubuwan da ta fada?.
Zaunal ya numfasa yace a matsayina na musulmi bai
kamata na yarda da duk wata magana ta matsafi ba..
Ina fatan baki da sauran wata tambaya a gare ni sai da
safe..
Idan kin fita ki jamin kofa...
Zaunal na gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya shige
can cikin dakin barci cikin sanyi jiki da matukar
damuwa..
Page 15.
Zidane kd.
Lasmir ta juya da sauri ta fice daga cikin dakin kuma taja
kofa da karfi ta rufe..
Kai da jin karar rufe kofar kasan cewa a fusace take...
Kashe gari bayan su zaunal sun gama kalaci a babbar
turakar sarki Marzuk sai ya gayyacesu izuwa wani babban
filin dake tsakiyar gidan sarautar..
Shi dai wannnan fili ba a yin komai a cikinsa ba face gasar
jarumtaka.
Ga isarsu filin sai suka iske gaba dayan jama ar garin sun
taru mazansu da matansu manya da yara sun yiuwa
tsakiyar filin kawanya suna ta shewa da jinjina..
Koda ganin wannan al amarin sai mamaki ya kama
Husam lasmir Da zaunal.
Husam ya dubi sarki Marzuk cikin rashin fahimta yace me
kuma za a yi anan har ka gayyace mu?
Koda jin wannan tambayar sai sarki marzuk yayi
murmushi yace ina son na gwada jarumtakarka da ta
yarka a kaina da yata...
Nida kai zamu fafata yanzunan yata zarisha zata fafata da
yarka 'lasmir.
Idan mune muka yi nasara a kanku to tafiyar da za ayi
mune shugabanni.
Idan kuma kuka yi nasara to kune shugabanin tafiyar
caraf sai jarumi zaunal yace to idan kuma kuka yi ragas
fa?
Kuma yaya yanayin nasarar wannan gasar zata kasance?
Sarki marzuk ya dubi Husam cikin murmushi sannan ya
dubi husam cikin murmushi sannan ya dubi zaunal yace
idan mukayi ragas kaine zaka zamo shugabanmu a cikin
tafiyar...
Yanayin nasarar wannan gasa shine ne duk wanda gadon
bayansa ya taba kasa ya fadi gasar..
Gashi fadin hakan ke da wuya sai zarisha ta kurawa lasmir
idanu tana yi mata murmushin mugunta..
Page 17.
Zidane kd.
Nan take sarki marzuk ya cire alkyabbar jikinsa sai gashi
cikin gagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini da ban
tsoro..
Ita ma zarisha ta cire doguwar rigar dake jikinta sai gata a
cikin shigar yaki da takubba guda biyu dauke akan
cinyoyinra..
Sarki marzuk ya dubi husam yace maza ko koma
masaukanku kuyi irin shigar yaki wacce kuka saba kuma
ko debo makamanku ku dawo muna nan muna jiranku..
Koda jin wannan batu sai husam ya dubi yarsa lasmira
suka yiwa junansu murmushi kawai sai suka juya da baya
suka ruga da gudu izuwa can masaukansu.
A wannan lokacin zarisha ta matso daf fa jarumi zaunal ta
dube shi tace wai meke damunka ne gana baka cikin
sukuni sosai?
Zaunal yayi ajiyar numfashi yace ai babu yada za a yi na
mai wwani sukuni sbda al amura gaba daya sai sauyawa
suke.
Da farko dai ni abin da yasa na baro kasa ta har yanzu
ban sa ...
Kafin ya karasa maganar sai zarisha ta tari numfashinsa
tace shin kammanta ne da abin da na fada maka jiya
daddare?
Matar da zaka aura tana can a birnin azzalumai amma ba
zaka ganta ba sai alokacin da muka fafata yaki.
Koda jin wanna batu sai zaunal ya murtuke fuska yace
nifa na gaya miki cewa duk abin da zaki fada daidai yakke
da tsatsuniyar yara domin har abada bazan taba yarda da
maganar tsafi ba..
Page 19.
Zidane kd
zarisha tayi murmushi tace amma dai ai kayi imani cewa
akwai aljanu ko?.
Duk ma abocin addininka yaya yarda cewa ubanjiku ne
ya halarci mutum da aljan da sammai da kassai yarda
cewa ubangijinku yana sanar da mutane ilmi iri iri a cikin
har da ilmin taurari...
Don haka kada kayi mamaki bisa du irin abin da zan fada
maka..
Lallai zaka gaskata zancen idan lokacin yayi..
Tana gama fadin hakan sai ta tafi ta bar shi ta wuce izuwa
cikin tsakiyar filin gasar..
A lokacin ne shi ma sarki marzuk ya bi ta a baya izuwa
cikin filin..
Wohoho! Idan mutum ya ga lokacin da wadannan jarumi
biyu ya da uba suka jera tare a cikin irin kirar da allah
yayi musu ta kwarjini da jarumtaka da kyan siffa dole
nesu burge shi..
Shigar su zarisha cikin filin gasar ke da wuya sai ga Husam
da yarsa Lasmir sun shigo a cikin gagarumarr shigar yaki
mai matukar kyau kwarjini da ban tsoro..
Nan fa kallo ya dawo kansu ai kuwa jama ar birnin ba su
san sa adda suka fara yi musu jinjina da tafi ba..
Al amarin da ya karawa Husam da lasmir kwarin gwiyawa
kenan suka nufin cikin filin gasar kai tsaye zuciyoyinsu
dauke da sa ran samun nasara....
KUBIYO MU LITTAFE NA GAVA DON JIN YADDA ZATA
KARKE....
SULEIMAN ZIDANE KD..
Mu HADU LITTAFE NA SHIDDA.
WHATSAPP 08161272634:::::
BIRNIN AZZALUMAI
Littafi na shida 6
Na Abdulaziz Sani M Gini
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com

BIRNIN AZZALUMAI 6
Littafe na Shida
Part A
Typing.. Suleiman zidane kd..
08164272634
:.........
Da Shigowarsu cikin tsakiyar filin inda sarki zarmu da
zarisha ke tsaye sai suka tsaya suka fuskanci juna.
A sannan alkalin gasar ya shigo ya tsaya a tsakiyarsu ya
dadda tuna musu yanayin gasar da kuma dokokinsa..
Daga cikin dokar gasar shi ne in dai mutum ya fadi kasa
da bayansa babu damar a sake kai masa wani hari ko a
cutar dashi sannan kuma a cikin jaruman hudu duk irib
yanayin daza su shiga wani bazai taimaki wani ba kuma
duk wanda ya mutu a wannan gasa babu batun daukarr
fansa sbda dama gasa ce mai hadari ta sai da rai.
Alkalin yana gama yin wannan jawabin sai ya fice daga
cikin filin ya koma cikin yan kallo yana zauna daf da
jarumi zaunal.
Faruwar hakan ke wuya aka buga gangar fara gasa.
Nan take sai jaruman hudu suka ja baya kuma kowannen
su ya murtuke fuskasa alamar cewa ba sani ba sabo
kuma ba ragayya..
Kamar hadin baki sai dukkaninsu suka zare makamansu..
Husam da lasmir suna rike da takubbansu da
garkuwoyinsu, sarki zarmus da gimbiya zarisha kuwa
suna rike da takubba guda bibiyu.
Bayan jaruman hudu sun ja baya ga juna sai suka fara
kallon kalo kowannen su na nazarin abokin gwaminsa har
izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai suka rugo da
gudu izuwa kan juna.
Zarisha ta afkawa lasmir shi kuma sarki zarmus ya
afakawa Husam aka ruguntsume da azabbben fada ya
zamana cewa suna kai wa junansu sara da suka cikin
tsananin zafin nama tunga da jarumtaka.
Page 5.
Zidane kd.
Duk sa adda makamansu suka hadu sai dai kaji kara da
tartsatsin wuta na tashi.
Nan fa filin ya rude da shewar jama a .
Sai da jaruman hudu suka shafe kusan dakika dubu daya
da dari uku suna fafata azababben yaki batare da
dayansu ya sami nasarar koda kwarzana a jikin daya ba.
Babban abin da ya fi daurewa mutane kai shine duk salon
da sarki zarmus suka zo shi sai a gasu zarisha ma sun iya
hakama lasmir duk salon dasuka zo shi sai aga cewa sun
hasam sun iya..
Koda jaruman hudu suka ga sun shafe wannan tsawon
lokaci suna gurmurzu ba tare da sun sami wata nasara ba
sai duk suka ja da baya.
Page 6.
Zidane kd.
Kowannensu ya mayar da takobinsa cikin kube.
Husam da lasmir suka yi jifa da garkuwowinsu izuwa can
gefe daya suka gyara tsayuwarsu sina ganin haka sai sarki
Zarmus da xarish suka dubi junansu suka yi murmushi
alamar cewa suna murna da fidda raini da karfin damtse.
Koda ganin abina dake shirin faruwa sai jarumi zaunal ya
gyara zama cikin murna domin yana son yaga iyakar
jarumtakar Husam kuma sai yaji a zuciyarsa yafi son su
zarisha su sami nasara,,.
Batare da bata wani lokaci ba sai jaruman hudu suka sake
rugawa ga junansu suka kacame da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment