Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan matsafiya ki gayamin abin
da ki ke so na yi domin ki kyale mahaifina kada ki
salwantar da rayuwarsa".
Koda jin haka sai sadauki Awaisu ya yi farat ya ce,"ya ke
'yata kada kibi uamarnin wannan azzaluma domin ko
kinyi abin da take so ba zata fasa hallakamu ba.
ki sani cewa ta cika mayaudariya kuma maci amana,
kuma a halin yanzu tafi kowa karfin sihiri a duniya. sihiri
daya ne ya rage mata wato wanda ke cikin jikinki".
Alfila ta kalli Awaisu cikin mamaki ta ce, "ya kai abbana
yaya akayi wannan mata ta samu nasara a kanka alhalin
kafi karfin dantse da na sihiri?"
Awaisu ya kwada kai cikin takaici ya ce, "Ai kamar yadda
na gaya miki ta zo garinnan a siffar 'yar uwar
mahaifiyarki wacce ke zaune a birnin kisra wadda rabona
da ita tun da aka yi rashin mahaifiyarki tun da ta tafi bata
sake dawowa garin nan ba. kwatsam sai na ganta ta zo.
Bayan na sauketa a gidana sai ta gaya mini cewa anyi
yakine a birnin kisra an kashe mijinta da 'ya 'yanta biyu
don haka yanzu bata da kowa a duniya shi yasa ta dawo
garemu.
A lokacin ne ta tambayi labarinki na gaya ma ta cewa ai
boka shamzabul Azwas ya sace ki tsawan shekaru.
Koda jin haka sai ta fashe da matsanaicin kuka na bakin
ciki.
Da kyar da sidin goshi na shawo kanta ta daina kukan.
Ina mai rarrashinta ta na cewa shi ke nan yanzu babu
wanda za ta kalla ta gani a matsayi. tsatson jininta.
Daga wannan rana ta ci gaba da zama a gidana ya zamana
cewa tanayin ayyukan gida kamar yadda mahaifiyarki ke
yi mini sa'adda tana raye. Hatta abinci itace take girkawa
tana bani ina ci.
Kin sani cewa da ma ita 'yar uwar mahaifiyar taki kamrsu
daya da mahaifiyar taki don haka sai soyayya ta shiga
tsakaninmu.
Cikin kankanin lokaci magaar aure ta wakana.
A daren da na shiga dakin Amarya ne na tsinci kaina a
cikin wani irin mugun hali domin nan take na daina Jin
kwarin jikina na yan ke jiki na fado kasa daga kan gado
kuma naji ko danyatsan hannuna bazan iya dagawa ba.
Haka kuma sai na ji gaba daya sirrikan tsafina sun daina
aiki.

A wannan lokacin Amaryata tana zaune a gefan gado
kawai ta Kura mini ido tana murmushin mugunta.
Da kyar na juyar da kaina na kalleta kuma na bude baki
na ce, "ya ke matata ina dalilin faruwar wannan al'amari
a gareni?.
Koda jin wannan tambaya sai ta bushe da mahaukaciyar
dariya sannan tayi girgiza ta rikide izuwa kamannin
Shukura matar sarki Barusa.
Nan take ta gabatar da kanta a gareni sannan ta ce,"ya kai
wannan Sadauki kayi Sani cewa 'yar uwar matarka tana
can birnin kisra tare da mijinta da 'ya 'yanta lafiya kalau,
Kawai na juya izuwa kwmannin ta ne na zo nan kasar
domin na Kama garin naku Karin su sarki Sahibul Hairi su
iso tare da 'yarka Alfila".
Koda jin haka sai na cika da farin ciki duk da cewa ina
cikin wannan hali name ce yanzu kina nufin cewa su sarki
Sahibul Hairi sun sami nasarar dauko Alfila daga fadar
sarki Shamzabul Azwas?"
Shukura tayi murmushi ta ce, "kwarai kuwa kuma suna
nan akan hanyarsu ta zuwa nan domin su mika Alfila a
gareka.
Bukatar Sarki Sahibul Hairi itace ka daukeshi ka kaishi
gurin 'yam mata uku wadanda idan ya sure su sai yafi
kowa na sarki daukaka, mulki da karfin arzuki.
Ni kuwa bazan ta6a bari ya samu wannan matsayin ba,
idan ya sameshi burina na son mulkar duniyar nan gaba
daya ba zai cika back. Lallai nice nake son na hau wannan
matsayi wanda sarki Sahibul Hairi ke bukata.
Abu na farko da zanyi shi ne, na sake rabaka da 'yarka
Alfila na tafi da ita izuwa can birninmu na cire sirrikan
tsafin jikinta wanda ka sa Mata na Mai da shi jikina domin
na samu irin karfi da boka Shamzabul Azwas ya Samu.
Kai kanka ka sani cewa Alfila ce kawai mai
irin wannan karfin.
Bayin na cire sirrin daga jikinta na sa shi a
jikina sannan sai ka rakani inda wadannan
mata uku suke domin na kamasu suma na
cire sihirin da ke jikinsu ya zamana cewa
nafi kowa arziki da daukaka a duniya tunda
na fi kowa karfin sihiri".
Koda gama wannan jawabi sai Shukura ta
bushe da dariyar mugunta.
Tana cikin dariyane ta dafani, nan take
muka 6ace tare ni da ita.
Bamu bayyana a ko ina ba sai a tsakiyar
turakar nan inda muka iske a kwance kan
gadonsa yana ta shara barci.
Nan take tayi nuni da hannunta sarkar tsafi
ta daureshi.
Nima sai ta nunoni da hannu na tsinci kaina a kan gadon
daure da sarkar sihiri kamar yadda sarki ya kasance.
Tun daga wannan rana Shukura ta rinka wanzuwa a cikin

siffar sarkinmu shi yasa kika ga kowa yana biyayya a
gareta sai abin da ta ce shi ake yi.
Yanzu ke kadai ce kika ganinta a cikin ainihin siffarta....
Hatta ni da sarki a cikin siffar sarkin muke ganinta".
Koda jin wannan batu sai Alfila ta juya ta kalli Shukura ta
ce, "yanzu me kike son na yi miki ki kyale mahaifina baza
ki kashe shi ba?".
Sa'adda gimbiya Shukura ta ji wannan batu daga bakin
Alfila sai ta tuntsure da dariyar farin ciki sannan ta
murtuke fuska tamkar wadda aka aikowa mata da sakon
mutuwa ta ce, " abu na farko da nake so ki yi shi ne, ina
so ki cire damarar da ke jikinki ki ajiyeta a gefe daya
sannan na baki wuta ki kona damarar da hannunki
Abu na biyu da za kiyi shi ne, zaki koma can kofar garin
tare da ni, kuma zan je ne a siffar mahaifinki domin
mutarbu su sarki Sahibul Hairi mu shigo da su har nan
cikin fadar domin na hallakasu cikin salim alim sannan na
dauke ki na tafi da ke".
Koda jin wannan batu sai Alfila ta mike tsaye daga kan
mahaifinta ta dubi shukura ta ce, "yanzu mene ne tabbaci
idan na aikata duk abin da ki ka umarceni baza ki ta6a
lafiyar mahaifina ba.?"
Da jin wannan tambaya sai shukura ta yi murmushi ta ce,
zaki sameni mai cika alkawari idan har ki ka aikata abin
da na umarceki".
Alfila ta ce, "ai ke ba mai cika alkawari bace. Idan da mai
cika alkawari ce baza ki ta6a cin amanar mijinki ba sarki
Barusa tunda bai rageki da komai ba a rayuwarsa, sannan
ya nuna miki tsananin kauna kamar yadda uwa ko uba
yake son dan da suka Haifa".
Kada jin wannan batu sai Shukura ta fusata ta sake nuni
da hannunta izuwa kan sadauki Awaisu kawai sai wannan
sarka ta sihiri ta kara matse sadauki Awaisu tamau fiye da
karon farko.
Awaisu ya kurma uban ihu, wannan karon har sai da
kashin kafarsa ya karye yai kara kal!
Alfila ta rusa ihu Kuma ta zare takobinta tai kan Shukura
da nufin ta sareta, sai Shikura ta daka mata tsawa ta ce,
"idan ki ka karaso inda nake zan karasa mahaifinki.
Kawai ki yi abin da na umarceki baki da wani za6i".
Cikin karfin hali Awaisu ya dubi Alfila a lokacin da gaba
dayan fuskarsa ta cika da gumin wahala ya ce, "Na gaya
miki kada ki bi umarninta.
Da dai ta umarceki ki ci amanar su sarki Sahibul Hairi
wadanda suka sha wahala suka daukoki daga cikin fadar
Shamzabul Azwas kuma suka kawoki har nan domain ki
sadu da ni ai gwara ki bari ta kasheni
Fatana shi ne burina kada ya cika tunda ta kasance
azzaluma wadda zata haddasa zalunci da bakin mulki a
doran kasa.
ya ke 'yata na gani a cikin madubin tsafina cewa kin kar6i
addinin musulinci a gurin gimbiya Humaira tun kafin

Shukura tazo garin nan, kuma ko kadan bana bakin ciki
da hakan.
Dama shirina shi ne, da zarar kin dawo gareni ni ma na
kar6i wannan addinin kuma nasa sarkin mu shi ma ya
kar6a domin gaba daya al'umar kasan nan su ma su
kar6eshi.
ya ke 'yata in kika ka bi umarnin shukura duk wannan
shirin ya wargatse ke nan. Ina tabbatar miki da cewa ni
da sarki duk mutuwa zamu yi".
Lokacin da sadauki Awaisu ya zo nan a zancensa sai
hankalin Alfila ya dugunzuma ta rasa abinda zata
yankewa kanta hukunci. kawai sai ta Kama kallon fuskar
sarki da ta sadauki Awisu a sannan kuma sai ta dubi
shikura wacceke tsaye tana ta murmushi mugunta.
Alfila ta kama duru-duru da sake-saken zuciya. Bayan ta
danyi nazari a cikin zuciyarta sai kawai ta kwance wannan
damara dake jikinta ta ajiye a gefe daya.
Koda ganin haka sai shukura ta bushe da dariyar
mugunta da farin ciki.
Nan take shukura tai tsafi sai ga wutar ice ta bayyana a
hannunta.
Kawai sai ta mikawa Alfila wutar sai ta kar6a sannan tace
da ita, "maza ki kona wannan damara".
Alfila ta nufi inda ta jefar da damarar tana waigen
shukura da su sadauki Awaisu hawaye na zuba daga cikin
idanuwanta, kai da gani kasan ba a san ranta zata kona
damarar ba sai bisa dole tunda ba yadda za ta yi.
Shi kuwa sadauki Awaisu sai takaici ya rufeshi bai san
sa'adda ya matso kwallar bakin ciki ba.
Shi kuwa sarki dama ya dade yanata kukan zuci da zahiri
bisa halin da ya tsinci kansa karkashin ikon gimbiya
shukura a matsayinsa na sarkin guda mai cikakken iko
amma sai yadda aka sarrafashi tun da gashi an kwace
masa karagasa da jama'arsa.
Tun daga ranar da ya bude ido daga bacci yaga shukura
tsaye a kansa bai kara mikewa zaune ba yana kwance kan
gado a daure, shukurace ta ci gaba da zartar da komai na
sarautar Kasar.
Haka Alfila ta dosana wannan wuta a kan wannan damara
tana ji tana gani. Nan take damarar ta kama cin wuta,
cikin dakika kadan ta kone kurmus ta zama toka.
Koda ganin haka sai gimbiya shukura ta bushe da dariyar
farin ciki, ta ce, ‘’yanzu kin bi umarnina na daya da na
biyu saura na uku kawai. Sai ki biyoni a baya muje can
kofar gari inda kika baro su sarki Sahibul Hairi.
Kafin mu tafi ina mai gargadinki da kada ki kuskura ki ce
za wani abu ba dai-dai ba a gareni domin kina yin dan
kuskureko kika ce zaki tona min asiri a wajan su gimbiya
Humaira a bakin ran mahaifinki.’’
Gama fadin haka ki da wuya sa gimbiya Shukura ta juya
ta fice daga cikin turakar, Alfila ta bita da sauri a lokacin
da sadauki Awaisu ya bisu da kallo kawai cikin tsananin

takaici da bakin ciki hawaye na kwarara bisa kumatunsa.
Gimbiya Shukura da Alfila suka jera suna tafiya a cikin
harabar gidan sarautar tamkar babu wata damuwa a
tsakaninsu.
Abin da idanun jama’ar gidan ke gani shi ne, Sarkinsu tare
da Alfila ‘yar sarkin yaki don haka duk inda suka wuce sai
ayi ta kallonsu cikin mutukar mamaki domin an san cewa
Alfila ta 6ace tsawon shekaru amma yanzu gashi ta dawo,
alhalin an ce sarkin bokayan aljanun duniya ne ya saceta
kuma babu mahalukin da zai iya shiga fadarsa ya kar6ota.
SARKIN SARAKAI
Littafi Na Biyar (5)
Part C.
.
Marubucin littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Admin
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa..
.
ALHALIN ANCE SARKIN BOKAYEN ALJANUN DUNIYA NE
YA SACETA KUMA BABU MAHALUKIN DA ZAI IYA ZUWA
FADARSA YA KARBOTA
To wai shin yanzu yaya aka yi ta dawo gida ?
Amsar da babu wanda ya san ta ke nan, sarki sahibul
hairi,
bawa haluf, da gimbiya humaira suna zaune a kofar
birnin
sun gaji ainun da jiran dawowar yarinya alfila,
sun kagu sosai, har humaira ta fara zargin anya
kuwa lafiya? Bai kamata suci gaba da jiran gawar shanu
ba
cikin matukar damuwa sarki sahibul hairi ya dubi
humaira yace yake wannan jaruma mai abin mamaki,
yanzu me ya kamata muyi?
Humaira tace ai tun da dai yarinyar nan ta dade bata
dawo ba lallai akwai abin da ya faru ba dai dai ba
saboda haka ina ganin cewa kawai mu shiga cikin
garin nan ta kowanne hali koda salama ko da tsiya tsiya
nan take humaira ta mike tsaye ta zare takobinta ta nufi
bakin kofar cikin sauri sarki sauri sarki sahibul hairi da
bawa haluf ma suka zare nasu takubban suka take mata
baya
koda masu tsaron kofar suka hangosu sai suma suka
zazzare nasu
makaman suka tsaya suna jiran isowarsu a ruguntsume
ba zato ba tsammani sai masu tsaron kofar sukaji an
daka musu tsawa daga bayansu
cikin sauri suka waiga sai suka ga ashe sarkinsu ne tare da
yarinya alfila
cikin gaggawa suka dare suka basu hanya suka

wuce ta tsakiyarsu suka nufi inda su humaira suke
humaira sarki sahibul hairi da bawa haluf sai suka
cika da tsanannin mamaki lokacin da suka hango yarinya
alfila tare da mahaifinta sadauki awaisu a tafe cikin
nishadi
awaisu rike da hannun alfila, da isowarsu sai awaisu
ya dubi sarki sahibul hairi cikin tsananin farin ciki ya
ruguntsumeshi yana mai cewa, lale marhaban da sarki
mai daraja wanda ya share mini hawayen bakin ciki na
tsawon shekaru
lallai zan kasance mai taimakonka har izuwa lokacin
da bukatarka zata biya koda kuwa zan rasa rayuwata
koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya cika da matukar
farin ciki ya janye jikinsa daga cikin nasa awaisu, sannan
ya bashi hannu suka gaisa
koda gaisuwar tasu sai jikin sarki sahibul hairi yayi
sanyi, ba komai ne ya janyo hakan ba face irin yanayin da
yaji hannun awaisu mai tsananin taushi tamkar na mata
awaisu ya dubi sarki sahibul hairi ya ce yanaga jikinka ya
yi sanyi
ne sarki sahibul hairi yayi murmushi yace, babu komai,
kawai na tuno da irin halin da kake ciki ne a yanzu na
farin ciki bisa sake saduwa da yarka alfila
tabbas na san cewa a yanzu babu wanda ya fika murna
da kwanciyar hankali a wannan birni
koda jin wannan batu sai awaisu ya bushe da
dariya yace tabbas abinda ka fadi gaskiya ne kuma babu
wanda ya fini bakin ciki a lokacin da aka rabani da alfila
inda baku je kun daukota kun dawo mini da ita ba,
tabbas zan iya kamuwa da cutar
ajali a ko yaushe
koda gama fadin haka sai awaisu ya dubi gimbiya
humaira da bawa haluf da kyau
sannan yayi murmushi yace an gaisheku manyan jarumai
hakika kun sha gwagwarmaya tsakaninku da sarki
shamzubulu azwas da sarki barusa, na gamsu cewar kun
cika manyan sadaukai a duniya
wadanda har abada ba za a manta da tarihin
sadaukantakar suba
cikin matukar mamaki humaira ta dubi awaisu tace
yaya akayi ka san irin gwagwarmayar da muka yi dasu
shamzubul azwas alhalin tsafinsu yafi naka
tasiri ba za ka iya ganin al amarinsu ba a cikin tsafinka
koda jin wannan tambaya sai sadauki awaisu ya dan
rikice ya kasa bada amsa da wuri
amma sai ya dan wayance yace ai alfila ce ta bani labarin
duk abinda ya faru a gareku
koda jin haka sai sarki sahibul hairi da bawa haluf suka yi
dan murmushi
ita kuwa sai ta tsuke fuska domin ko kadan bata ji ta
aminta da awaisu ba
awaisu ya dubesu gaba daya cikin fara a yace yanzu saiku

zo mu shiga cikin gari domin muje gidana ku zauna ku
huta kuci abinci
ba tare da gardamar komai ba kuwa su humaira suka bi
sadauki awaisu da alfila izuwa cikin garin
sai da suka yi yar tafiya mai dan tsawo sannan suka iso
gidan sadauki awaisu
da zuwa masu gadi suka bude musu kofa suka shiga ciki
shigarsu keda wuya sai ga kuyangi maza da mata sun
tarbesu da lale marhaban, sukayi musu rakiya har izuwa
babbar turakar gidan
daga nan kuma sai awaisu ya umarci wani hadimi
da yaje ya nunawa humaira nata dakin daban
sarki sahibul hairi da bawa haluf ma sai aka kaisu nasu
dakin daban kuma aka umarci kuyangi da su shirya
abinci
na musamman ga baki
lokacin da aka kai humaira dakinta aka tafi aka barta ita
kadai sai ta rufe kofar dakin sannan ta shiga kewaye
taje taayi alwala ta gabatar da sallah, a lokacinne ta tuno
da alfila da tace a ranta
'Allah ya sa dai alfila bata shagala ba ga barin yin sallah
bisa farin cikin saduwa da mahaifinta
koda aiyana hakan sai humaira taji zuciyarta ta buga da
karfi nan take hankalinta ya dugunzuma ta tuno da
tambayar da ta yiwa
awaisu dazu ya dabarbarce ya kasa bata amsa da wuri
nan take taji bata amince da awaisu ba a cikin
ranta ta fara wasi wasi a zuciyarta tana mai cewa
'Anya kuwa wannan awaisun ne ainihin mahaifin
alfila? Nikam ba zan saki jiki dashi ba har izuwa lokacin
rabuwarmu
AA Misau Nake Magana,
Gama aiyana hakan keda wuya sai humaira taji an
kwankwasa
mata kofa
Al amarin da ya fusata ta kenan tace a ranta, Me za ayi
da irin wannan al adar banza ta kafirai, sai dai a
kwankwasa
maka kofa ba za ayi maka sallama irin ta addinin
musulunci ba ?
Kawai sai ta bude baki tace shigo koda kofar ta bude tayi
arba da wani kyakkyawan saurayi mai tsananin kyau
tun da humaira tazo duniya bata taba ganin da namiji
mai
kyansa ba
saurayin yaci ado na gaban kwatance cikin sutura mai
tsadar gaske wacce tafi karfin
karamin sarki
hakika babu wata ya mace lafiyayyiya da zataga wannan
saurayi bataji sha
awarsa ba
saurayin na dauke da farantin abinci na kasaita

iri iri gami da ababan sha danginsu ruwan inibi da ruwan
hadaddan tataccen sauran yayan itatuwa
kamshinsu ya cika dakin gaba daya, koda humaira tayi
arba da wannan saurayi sai zuciyarta ta buga da karfi a
karo na biyu
nan take tayi hailala a cikin zuciyarta ta nemi tsarin Allah
daga shaidan, nan take kuwa
taji ta tsani saurayin kuma ta tsani abincin da ya kawo
yayin da saurayin ya ajiyea farantin abincin bisa wani
tebur dake daf da humaira
sai ya tsugunna ya dauki tambulan na ruwan inibi zai
zuba a kofi da nufin ya mika
mata domin ya birgeta
ko kallonsa batayi ba ta daka masa tsawa tace bana
bukatar kayi mini komai
kuma kayi sauri ka bace mini da gani, cikin rawar jiki
saurayin ya mike zumbur ya fice daga cikin dakin
bai zame ko ina ba sai wannan babbar turaka ta gidan
inda ya iske alfila da
awaisu zaune sunyi jugun jugun babu mai cewa uffan
cikin girmamawa saurayin ya durkusa a gaban awaisu sai
ya rikide ya zama wani
bakin aljani mai matukar muni da ban tsoro
awaisu ya dubi aljanin yace menene labari yakai zarmalu?
Aljani zarmulu ya dukar da kansa cikin alamun tsoro da
fargaba yace ya shugabana aiko
kadan humaira bata saurareni ba, koroni ma tayi
kuma sa adda na matsa daf da ita sai naji kamar an
tsamoni a cikin tafasashshen ruwa ba shiri na fito daga
cikin dakin
koda jin haka sai bakin ciki ya lullube awaisu ita kuwa
alfila sai ta cika da farin ciki , awaisu ya sake duban aljani
zarmalu yace ya ya batun sarki sahibul
hairi da bawansa haluf kuma?
Koda jin wannan tambaya sai zarmalu yayi murmushi
yace ai wadannan tuni mun fara samun nasara akansu
domin tuni sunci abincin da muka basu har sun bingire
da barci
awaisu yayi murmushi yace da kyau zarmalu, aikinka na
kyau
AA Misau Ke Magana, Lallai a daren yau zan hallaka
sarki sahibul hairi da bawansa haluf ita kuwa humaira
kafin daren yayi lallai zamu sake jarraba wani tuggun
akanta domin mu sami
lagonta
Ka sani cewa ita musulma ce tana da karfin tsari irin nasu
a jikinta sai munyi da gaske, zarmalu yayi ajiyar zuciya
yace ai ni dai kam tafi
karfina ya shugabana ba zan iya sake tunkararta ba sai dai
ke da kanki ki san hanyar da zaki bullo mata
Dajin haka sai awaisu ya bushe da dariya yace ai babu
mai

tarar zaki sai dan uwansa zaki ka barni da ita, lallai a
daren yau zanga karshenta kafin wayewar gari
tashi ka tafi na sallameka, koda gama fadin haka sai aljani
zarmalu ya daidaice tamkar yayan kwayar zarra sannan
ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa a wajen ba
bacewarsa keda wuya sai awaisu ya dubi alfila ya tuntsire
da dariya sannan ya
hade fuska yace na gama da abokan tafiyarki biyu
saura guda daya jal
ina mai dada yi miki tuni da cewar idan kika kuskura
kikayi
wani abu ba dai dai ba lallai zakiyi arba da gawar
mahaifinki
a ko yaushe
koda jin wannan batu sai idanun alfila suka ciko da
kwalla ta fara zubar da hawaye hawayen takaici da bakin
ciki
AL AMARIN gimbiya humaira kuwa bayan ta kori
wannan kyakkyawan saurayi daga cikin dakinta sai taki
cin
wannan abinci da ya kawo mata na alfarma
duk da cewa kuwa tana jin yunwa da kishirwa
kawai sai ta bude jakarta ta dauko ragowar wani
gasashshen
nama daga cikin guzurinta na tafiyar taci kuma ta daga
battar ruwanta ta sha sannan tayi
godiya ga Allah
kammala cin abincin keda wuya sai taji babu abin da take
so
sama da ganin abokan tafiyarta, gashi bata san dakin
da aka kaisu ba
kawai sai ta mike tsaye ta fara tafiya ba tare da fargabar
komai ba ta bude kofar dakinta ta fita ta janyo kofar
ta rufe sannan taci gaba da tafiya a cikin gidan tana shiga
wannan lungu, ta fada wancan sako tana leka kowanne
daki
bisa mamaki sai humaira taga Allah ya makantar da
dukkanin barorin gidan da hadimai sam basa ganinta
kuma gashi ta gabansu take wucewa, wani lokacin ma ta
tsakiyarsu take ratsewa har tana bangazar kafadunsu
amma ko alamun ta basa ji bare su
ganta
AA Misau Sunana haka dai humaira taci gaba da leka cikin
dakuna daban daban har ta shiga dakin dasu sarki sahibul
hairi suke
da shigarta cikin dakin sai ta iskesu a kwance tamkar
gawarwaki ko numfashin kirki basa yi
cikim rudewa da tashin hankali ta ruga kansu ta tsugunna
kawai
sai ta fara karanta addu oi na musamman tana tofa
musu, cikin dakiku kadan suka farka a tare suna masu jan
dogon numfashi a lokaci guda kuma a firgice suka mike

zaune
zumbur suna zare idanu
Al amarin da ya baiwa humaira dariya kenan
Bata san sa adda ta dan dara
Ba
cikin rudewa sarki sahibul hairi ya dubeta yace, yake ma
abociyar
kyau da jarumta menene ya faru garemu nida bawana
haluf?
Sa adda humaira taji wannan tambaya sai tayi ajiyar
zuciya sannan tace nidai ina zaune a can dakina ni
kadai sai ga wani saurayi mai tsananin kyau irin wanda
ban taba gani ba ko a mafarki da labarai ya shigo mini
dauke da abinci na alfarma
ina ganinsa sai tsigar jikina ta tashi naji ban aminta
dashi ba don haka sai na daka masa tsawa na koreshi
daga cikin dakin
yana fita sai naji bani da sauran sukuni face na ganku
domin nasan halin da kuke ciki
saboda haka sai na kama karanta wadansu adduo i a cikin
zuciyata sannan na fito daga cikin
dakina nayi ta dube dube da leke leke har na shigo nan
ubangijina bai baiwa kowa
ikon ganina ba
ina shigowa ana iskeku a kwance tamkar gawarwaki ko
numfashin kirki bakwa yi, cikin hanzari na karanta
wata addu ar daban na tofa muku, faruwar hakan keda
wuya sai naga kun farka firgigit a cikin dimauce tamkar
wadanda sukayi dogon suma, lallai abincin da aka
baku kuka ci an sa banju mai karfi, a cikinsa saboda haka
ni dai ko kadan ban aminta da wannan awaisun ba a
matsayin mahaifin alfila
AA Misau Ke Magana, Sa adda humaira tazo nan a
zancenta sai sarki sahibul hairi da bawa haluf suka yi
ajiyar
zuciya a tare suka jinjina al amarin, sannan sarki
sahibul hairi ya dubi humaira cikin alamun karayar
zuciya
yace
yake ma abociyar kyawu da jarumta hakika kin ceci
rayuwata har sau uku
kenan, lallai kina bina bashin da ba na zaton zan iya biya
amma ina fatan na samu damar biyanki wannan
bashi koda sau daya ne kafin mu rabu, yanzu dai
menene abin da ya kamacemu dayi? Humaira taja
numfashi tace ya zama dole
muyi bincike mu tabbatar da cewa wannan awaisun
shine
ainihin mahaifin Alfila? Idan kuwa muka gane cewa bashi
bane, to fa dole ne ya bamu alfila mu nemi mahaifin na
gaskiya mu dankata a hannunsa, nifa abin da ya zaunar
dani

kenan, kawai a garin nan saboda haka yanzu yanzun
nan nake son mu tura a kirawo alfila da mahaifin
nata domin mu tantance komai, kafin humaira ta
gama rufe bakinta sai sukaji an kwankwasa kofar dakin
cikin hadin baki sukace shigo, nan take aka turo kofar
saiga bakin bawa ya shigo fuskarsa cike da annuri
bawan ya risina a garesu gaba daya yace, yaku wadannan
manyan baki masu
daraja kuyi sani cewa mai girma sarkin yakine ya turoni
nayi muku jagora izuwa can filin shakatawa domin yayi
ganawa ta musamman daku
koda jin wannan batu sai humaira tayi farat ta fara
mikewa
tsaye tana mai gyara takobinta dake daure a kugunta
tace mu je zuwa ya babban hadimi, koda ganin haka sai
sarki sahibul hairi da bawa haluf
suma suka mike tsaye da hanzari nan take kuwa bakin
bawan ya juya ya fita daga cikin dakin ya nufi wani
bangare
daban na gidan su humaira na biye dashi
haka dai suka ci gaba da tafiya cikin harabar gidan su
kutsa nan su fita can kamar tafiyar ba zata kare ba
babu abin da ya daurewa su humaira kai face ganin
yadda suke ta shiga sako sako,
lungu lungu, tafiyar nata kara tsawo kamar ba zasuje inda
suka nufa ba, kwatsam ba zato ba tsammani sai suka
tsinci kansu a cikin ainihin gidan
sarautar birnin kuma a tsakiyar fada, zaune akan karagar
mulki sarkin yaki awaisu ne yayi gagarumar shigar yaki
mai matukar kwarjini da bam sha awa
da isowar su humaira cikin fadar suka ga dakarun yaki
na aljanu da na bil adama masu yawan tsiya ba adadi
sunyi musu kawanya
tun da sarki sahibul hairi yake gumurzu da gwagwarmaya
bai taba ganin dakaru
masu matukar ban tsoro ba irin wadannan, domin
girmansu ya wuce misali, makaman yakin da suke rike
dasu kuwa wani kalarma ko a tunani
kwakwalwa bazata taba kawoshi ba, koda su humaira
sukaga wadannan dakaru sunyi musu kawanya sai duk su
ukun suka zare takubbansu
suka hada bayansu a tsakiya, ma ana kowannansu ya
dubi
fuska guda ya zamana cewa sun hade jikinsu a tsakiya
suna
nazari ta bangaren da za a fara kawo musu farmaki
kawai sai humaira taji jikin sarki sahibul hairi dana bawa
haluf ya kama karkarwa kai da gani ka san cewa a tsorace
suke ainun
koda fahimtar hakan sai humaira ta daka musu tsawa
tace yaku abokan tafiya ku saki jikinku, ku daina shakkar
komai, da izinin ubangijina babu abinda zai sami dayanku

tabbas mun fado cikin tarkon abokan gaba kuma ta
kowanne hali sai mun fita
yakai sarki sahibul hairi ka mantane da duk irin
hadarurrukan da aka shiga a baya
ka sha bakar wahala tamkar ranka zai salwanta, amma sai
gashi duka ka tsira?
Ai mai rabon ganin badi ko ana dakawa a turmi sai ya
gani
kafin humaira ta gama rufe bakinta sai sukaji sarkin yaki
awaisu

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

2 years ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment