Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

SADAUKI SAIFUL MAUT MAI TAKOBIN
GASKIYA: Part 1:
A wani zamani ne wanda ya shude a cikin birnin
kisra an yi wani azzalumin sarki mai suna Jawat
ibn Kafir shi dai wannan sarki Allah ya bashi
karfin damtse da karfin tsafi da mayaka na ban
tsoro dan kuwa kumin girman gari idan ya tura
mayakan sa to fa yan garin sun shiga balai da
kuma son mata ko yar wacece in dai ya hada ido
da ita to fa sai ya hada kwanciya da ita a haka
sai da ya tara mata wajen tamanin da biyar
kuma duk basu taba haihuwa ba saboda kafin ya
kwanta da mece sai yayi anfani da tsafin sa yayi
toshe mahaifarta toh a kusada garin akwai wani
karamin kauye mai suna Birnin Islama toh yan
garin kuwa musulmai ne fatake ne masu tafiye
tafiye toh su kuwa suna tafiyane da aladar
Musulunci suna da wani adalin sarki mai suna
Maut ibn Salim shi dai sarki salim Allah yayi
masa albarka da yaya biyu mace da namiji, masu
harshashe kuwa sun ce a wannan zamani ba
wanda yakai su kyau ballatana ita macen mai
suna Lasmina, shi kuwa namijin Allah ya bashi
jarumtaka da sa a don kuwa ba abin da yasa a
gaba idan yace sai yayi to kuwa ba wanda ya isa
ya tsai dashi don kuwa tun yana yaro yake yin
abubuwan alajabi don da akwai lokacin da ya tafi
dajin da akeyiwa lakabi da kauful jat a tarihin
dajin nan ba wanda yake shiga dajin nan ya fito
lafiya amma shi kadai ya shiga da zuwa kuwa sai
ya fara ganin abubuwan ban tsoro amma ko
gezau baiyi ba ya cikin dajin wajen dakika ashirin
sannan yaga wani babban zaki ya durfafo
wajensa maimakon ya gudu amma sai ya fara
shirin fada shi kanshi zakin yasan cewa ya gamu
da gomonsa ai kuwa sai zakin ya tahu a guje
kamar mayun waci yana zuwa kusa da shi sai ya
daka tsalle shi ko Saiful maut bai ko matsa ba
zakin na zuwa suka fara kokawa da yakushi har
wajen dakika talatin sai gashi saiful maut ya
kashe zakin da karfin damtse kawai sannan yakai
cikin gari totun daga ranar mutane suka fara
jinjina masa
zamu cigaba idan munga likes da comments
dinku to muna jira SADAUKI SAIFUL MAUT MAI TAKOBIN
GASKIYA PART: TWO
A kasar sarki Jawat kuwa yana zaune a dakin
tsafinsa a gaban madubin tsafinsa inda yake
binciko kyawawon mata na duniya wanda zai tura
mayakansa su dauko ta koda da karfin yaki ne ko
tsafi yana nan dai a zaune akan wani turmin
tsagi
wanda aka rufe da wani jan yadi a tarihi ance ba
wanda y taba shiga cikin dakin tsafin ya fito da
rai
saboda irin hatsatsubin da suke cikin sa shi ko
sarki jawat yana ta kallon hotunan yan matan
kawai sai ya hango wani hoton wata kyakkyawar
mace wanda tunda yake duniya bai taba ganin
kyakkyawa kamar ta ba sai yayi binciken wacece
budurwar da kuma garin da take ai kuwa yana
dubawa yaga ai yar sarkin garin Islama ne kawai
sai ya fara dariyar mugunta dan kuwa shaawarta
yake tun bai ganta ba kawai sai ya tura wani
aljanun sa ya kira wazirinsa mai suna kafaru a
lokacin da wazirin yazo sai ya rusuna ya kwashi
gaisuwa yace a mai duniya naga ka turo a kira ni
lafiya kuwa sai sarki ya numfasa yanuna masa
hoto gimbiya Lasmina aikuwa da waziri yaga hoto
gimbiya lasmina sai da ya kusa zautuwa amma
sai
kawai ya share yace ya mai duniya yanzu kana
son inje garin Islam in tambayo ma hannun
gimbiya lasmina ka aure ta sai kuwa sarki jawat
ya dinka dariya kamar bazai daina ba amma sai
kawai ya tsuke baki yace ina son yanzu ka dauki
dukiya mai yawa ka kai wa sarki maut kuma ka
gabatar da bukata ta agareshi waziri yace
angama
ya mai duniya sannan ya tashi ya tafi baitul mali
don a hada dukiyar da sarki yace.
Acan garin islama kuwa ana ta fadanci sai kawai
aka ga su waziri kafaru sun shigo da kayyayaki
akan rakuma sai suka shigo cikin fada zasu
rusuna
amma sai sarki maut ya dakatar dasu yace ai ba
wanda ake rusunawa sai Allahu wanda ya halicci
sammai da kassai shi kuwa waziri ko damuwa
baiyi ba sai yace yakai sarki maut kasani cewa
sarkin mune ya aiko mu dan mu fada maka cewa
yana son yarka gimbiya lasmina da aure tun kafin
ya gama maganarsa Sadauki Saiful ya tari
numfashi sa yace ai bazai taba yiyuwa ba dan
ruwa da wuta basa zama waje daya ku fada wa
sarkin ku haka mu bamu da lokaci da zamu bata
akan ku dan zamu je mu bautawa ubangijin mune
idan kun gadama ku tafi idan kuma kun gadama
ku
tsaya sai sarki maut yace ga sakona ga sarkin ku
kuce masa bazai yu ba GASKIYA PART: 3
Alokacin da waziri kafaru yaga irin wulakancin da
sarki maut yayi musu shi da dansa sai ya ji wani
mugun haushi sannan ya cewa dakarun da yazo
dasu cewa su tafi a lokacin da ya isa birnin kisra
sai ya huce fada wajen sarki domin ya isar da
sakon da ya karbo daga garin islama alokacin da
ya isa wajen sarki sai ya kwashi gaisuwa yace
ya mai duniya ai tun danake a duniyar nan
bantaba ganin wulakanci irin wannan ba sai ya
kwashi labarin abunda yafaru ya fada ma sarki,
kawai sai sarki ya takarkare ya ringa dariyu
wanda ya bawa waziri matukar mamaki sai kuwa
ya tsuke baki yace yanzu anan duniyar da akwai
garin da zan tura ince ina son abu amma
maimakon abani sai a wulakanta ni toh kuwa
garin islama sun shiga bala in da basu taba koda
tunanin sa ba yakai waziri yanzu ka tura a kira
min sarkin yaki don a gobe nake son in gama da
garin islama alokacin da sarkin yaki yazo sai ya
kwashi gaisuwa sarki jawat yace ina son ka tara
min dakaru kamar dubu daya gobe da safe don
ina son kashe duk wani abu mai rai kuma in baje
garin islama sai sarkin yaki yace angama ya mai
duniya sannan ya tafi ya bar sarki da waziri suka
cigaba da tattauna yanda zasu bullo wa alamarin
gobe.
Da gari ya waye sai ga dakaru nan a cikin sulken
yaki na ban tsoro don idan ka dansu kuwa to
dole ne kasan cewa wannan su ake kira da bala i
sai ga sarki nan ya fito daga cikin fadarsa da
shigar yaki wanda baitaba yi ba kai idan wani
raggon yaga wannan shiga ta sarki jawat to
gaskiya zai iya mutuwa yana zaune ne akan
tabarmar tsafi wanda yake yawo akan iska yace
yaku dakarun masifa da bala i to yau ina son ku
sani cewa wannan yakin ba zamu tausayawa
kowa ba kisa ne kawai amma ina son akama mun
gimbiya lasmina a raye don itace makasudin
wannan yaki sai dakarun su kace an gama ya
mai duniya sannan suka fuskanci kofar fita daga
birnin suka nausa hanyar birnin islama.
Acan birnin islama kuwa sadauki saiful da ya
dawo daga masallaci sai ya tafi turakar
mahaifansa yayi gaishe dasu sannan yace wa
abbansa wato sarki maut cewa shi zai tafi
farauta suka sa masa albarka da kuma adduar sa
a sannan ya tafi dakin kanwarsa wato gimbiya
lasmina suka gaisa take cewa ya samo mata
inibi nunanne yace toh sannan yafi to cikin
bargar dawakin ya hau dokinsa sannan ya nausa
cikin daji abinda bai sani ba kuwa shine bazai
kara ganin garin ba alamarin su sarki jawat kuwa
sai gudu suke har dai suka karasa garin wajen
sallar azahar suna zuwa suka afka su fara # sara
da # suka suna kona gidaje suka kashe kuwa
abirnin har cikin fadar sarki maut suka shiga
suka kama shi da matar sa da gimbiya anan take
sarki ya fille kan sarki maut sannan ya fille na
mahaifiyar su sadauki saiful aka saka gimbiya
akan doki sannan suka tafi suka bar birnin wanda
aka baje shi.
Shi kuwa saduaki saiful yana ta farauta har ya
fara shirya taho wa gida sannan yatuna da inibin
da kanwarsa wato gimbiya tace ya samo mata
yana tafiyane ya hango bishiyar aiko bai bata
lokaci ba ya tsinko mai yawa ya taho dashi gida
tundaga nesa ya fara hango wani irin hayaki ya
turnike a sararin samaniya sai ya kara gudun
dokinsa domin yaga mai ya faru.
zamu cigaba SADAUKI SAIFUL MAUT MAI TAKOBIN
GASKIYA PART: FOUR
Alokacin da sadauki saiful ya iso cikin garin su
yaga irin barnar da aka musu da kisa sai kawai
ya nufi fadar abban sa ai kuwa yana zuwa yaga
gawarwaki a ko ina burjuk yana shiga kawai sai
ya yi arba da gawar mahaifinsa da na
mahaifiyarsa amma kuma babu kawuna atare da
gangar jikin su kawai sai ya tsuguna ya fara
zubar da wasu zafafan hawaye wanda tun
lokacin da aka haife shi bai taba zubarda hawaye
ba sai yau sai ya nemu ruwa mai tsarki yayi
musu wanka yanda musulunci ya koyar damu ya
sallace su sannan ya binne su yana mai yin kuka
da bakin cikin abubuwan da suka faru alokacin
da bayanan ya dau lokuta kamar sa a daya
asannan ne kanwarsa ta fado mai a rai yayi ta
duba wa bai ganta ba yana cikin duba wa sai
yaga wani farin haske wanda tun da aka haife
shi baitaba ganin haske kamar sa ba hasken ya
tunkare shi kamar zai bankade shi sai ya sare
takobinsa daga cikin gidan ta yana dube duben
ta inda abin zai kawo masa farmaki amma
maimakon a kawo masa hari sai yaji wani murya
mai zaki tayi masa salama ya amsa sai wata
farar aljana ce ta baiyana a gaban sa tana mai
wani irin murmushi tace yakai saiful dan marigayi
maut kasani cewa ni aljana ce kuma musulma
mahaifina ya kasance sarkin garin mu mahaifina
yana da adalci amma yana da wani waziri wanda
yake zalunci don kuwa a duk cikin aljanun garin
mu suna jin tsoron sa in bada mahaifina toh shi
dai wazirin mahaifina kuwa ya kasance yana
musulunci ne a fuska amma wani gagarumin
boka ne toh wata rana muna zaune ni da
mahaifiyata sai muka ga mahaifina ya shigo a
guje yace mu hada yan kayyayakin mu mu gudu
wai wazirinsa ya hada mayaka don su karbe
sarautar sa kuma su mayar da garin mahaifina
garin bautar gumakai muna cikin hada kayan mu
ne sai muka ji an bankado kofar turakar
mahaifina in taikaice maka labari yakai saiful
maut agabana wazirin mahaifina ya kashe
mahaifana a gabana wanda har yanzu na kanji
bakin cikin rasuwar iyayena amma ba abinda zan
iya yi don sau wajen goma ina zuwa gidan
wazirin maihaifina don in dau fansa amma na
kasa daukar fansa ba dan komai ba don duk
kayan yakin da za amfani dashi bazai taba tasiri
a jikinsa ba to shi to alamarin iyayenka kuwa ba
kuwa bane ya kashe su in b sai sarki jawat na
birnin kisra don kawai ya nemi hannun kanwarka
wato gimbiya lasmina don ya aura amma kuka ki
amsa masa to shine ya taso da kansa don ya
hukunta ku toh abinda yasa na kawo maka dauki
don kuwa yanzu wazirin mahaifina da sarki jawat
sun hada karfi da karfe don su mai da kuwa da
kuwa bautar gumakai a yanzu dai acan birnin
kisra kuwa ana ta shirye shiryen bikin sarki jawat
da kanwarka lasmina
Toh acan birnin kisra kuwa sarki jawat yana isa
cikin fada yasa aka soke kawunan iyayen sadauki
saiful a kofar shiga gari ta yanda idai zaka shiga
sai ka gani sannan kuma yasa akayi shela cewa
za a daura masa aure da gimbiya lasmina a
kwanaki goma masu zuwa SADAUKI SAIFUL MAUT MAI TAKOBIN
GASKIYA PART:5
A bangaren saiful kuwa shi da bakuwar aljana
kuwa sun na ta daukar gawarwakin wadanda aka
kashe suna binnewa da suka gama ne sannan ta
gabatar da kanta cewa ya kai sadauki saiful ni
dai
sunana jazwariya yanzu ina son kayi sani cewa
akwai wani takobi wanda zai iya tasiri akan
kowani tsafi sai sadauki saiful ua dube ta yace
yake jazwariya shin kina cewa da akwai takobin
da
zai yi tarihi a jikin sarki jawat da wazirin
mahaifinki
aljana jazwariya tace kwarai kuwa don kuwa
takobin yana nan a wani tsibiri mai suna liswar
wanda daga nan zuwa can tafiyar kwana goma
ne
anan sadauki saiful yace to yanzu ya zamu yi
don
kuwa a kwana goman za a daura auren kanwata
da sarki jawat ai kuwa in dai haka ne ba mu
samu
ta zama ba don akwai babban aiki a gaba mu
yanzu kuwa zamu kama hanya ko jazwariya tace
kwarai kuma anan suka kama hanya zuwa tsibirin
liswar wanda yan tarihi sun ce ba wanda ya ke
shiga dajin da tsibirin yake ya fito lafiya ballatana
ka kai ga hawa tsibirin komin tsafin ka ko kuma
juriyarka da kuma karfin damtsenka sai ka gaji ko
aljanu ma suna shakkar wannan tsibirin don kuwa
idan sun kusanto wannan tsibirin sai kaga sun
fara
kururuwa badon komai ba sai don fatar jikinsu ne
zai dinga zangwayewa yana narkewa kamar
yanda
karfe yake narkuwa acikin gagarumin wuta ahaka
su sadauki suka kama hanya wanda shi sadauki
ya kama dokinsa ya hau ita kuwa aljana
jazwariya
ta kada fukafukanta sai kace tsuntsuwa ahaka
suka rinka tafiya hankalin su a kwance abinda
basu sani ba kuwa shi ne boka zamir yana
kollonsu ta cikin madubin tsafinsa sai ya wani
kece da wata mahaukaciyar dariya wanda yasa
duk cikin kogon tsafisa ya fara girgiza kamar zai
rugurguje sannan ya tsuke bakin sa ya daina
dariya sannan ya bace daga kogon tsafinsa
wanda
yake cikin wani tsafafen daji wanda ba kowa
yake
samun ganin wajen ba sai dai fa indai boka zamir
yace kazo to shine zaka samu damar ganin
wajen
alamarin sarki jawat kuwa birnin kisra ya fara
cika
da mutane da kuwanne bangare na duniya duk
inda
ka duba mutane ne burjik duk wani masauki ya
cika har tantuna ake kafa wa domin mutane su
samu wurin kwana mawaka da maroka kuwa ba a
bar su a baya ba kuwa don ko barci basa yi
amma
fa sun samu kyaututtuka da dama don wani sarki
ma idan wani mawaki ko maroki ya yi masa
kirari
sai kaga kawai ya bada umarni a bashi dukiya
wanda daga shi har tataba kunnansa basu isa su
karar da dukiyarnan ba shi kuwa sarki jawat gaba
dayan hankalinsa yana wajen tunanin daurin
auren
sa da za a yi nan da yan kwanaki shi dai gani
yake
kwanaki goman da yace yayi yawa yana zaune a
cikin turakarsa sai ya tuna cewa fa bai ko ga
gimbiya lasmina ba aranar ya mike ya nufi dakin
da yasa aka kulle ta aciki yana zuwa ya bude ya
shiga ya tarar da gimbiya lasmina a zaune tana
ta
faman zubarda hawayen bakin cikin rashin
iyayenta
da tayi kuma gashi bata ko kara jin duriyar
yayanta ba sarki jawat ya kusanto ta yana mai
cewa yake masoyiyata kiyi sani cewa kin riga da
kin zama tawa ba wanda ya isa ya shigo cikin
fadar nan da nufin ya kubutar dake yana cikin yin
magana yaji an kwankwasa kofar dakin sai ya
juya
ya fita yana fita kuwa ya ga boka zamir suka
gaisa anan fa boka zamir ya fada masa
abubuwan
da suka gudana tsakanin sadauki saiful maut da
kuma aljana jazwairya sai sarki jawat yace bari in
turo mayakana kamar dabu daya su kashe min
wannan yaron
Shin su sadauki saiful maut da aljana jazwariya
zasu samu damar dauko takobin gaskiya?
Sarki jawat zai samu damar kusantar gimbiya
lasmina kuwa? To domin sanin amsar tambayoyin
nan to zamu cigiba insha Allah sadauki saiful Maut mai Takobin
Gaskiya
PART: 6
Alamarin su sadauki saiful maut shida aljana
jazwariya kuwa tun lokacin da suka fara tafiya
basa ko tsayawa sai dai in lokacin sallah yayi sai
su dan tsaya su yada zango sannan su gabatar
da
sallah idan sun gama shi sadauki saiful sai ya
mike ya je ya farauto abinda zai sa a bakinsa
don
ita aljana jazwariya bata cin komai sai dai ta
rinka
salati da addu oi a haka suka rinka tafiya na
wajen
kwana biyu a cikin kwana goma kafin a daura
aure
sarki jazat da gimbiya lasmina
a bangaren su sarki jawat kuwa gashi saura
kwana
takwas washe garin ranar da sarki da boka jazwir
suka gana kuwa da dukudukun safiya sarki jawat
yasa aka kira masa sarkin yakinsa yana zuwa ya
kwashi gaisuwa yace ya mai duniya gani nan
nazo
daga jin sakon ka sarki jawat yace ina son ka
hadu rundunar mayaka guda dari wadanda suke ji
da kansu a jarumtaka ina sun kabi bayan wannan
yaron nan mai suna sadauki saiful da sarki maut
wanda kanwarsa take wajen ina ku riskesa kafin
ya
isa kan tsibirin lazmir domin yana son dauko
takobin gaskiya domin ya kawatar dani da
babban
abokina boka jazwir sarkin yaki yace toh mai
duniya ina so ka kwantar da hankalinka domin
zan
kawo maka kan sadauki saiful ibn maut sarki
yace
kwarai kuwa na gamsu da bayaninka yakai sarkin
yakina amma ina son karka kashe shi ina son ka
kamo minshi a raye domin yaga yanda za a daura
min aure da kanwarsa kwana takwas masu zuwa
da yarda ubangiji na zalzulu
ko bata lokaci baiyi ba ya fita ya fara hada
jarumai
wadanda idan suka tunkare kowanne gari toh
kuwa garin yasha bala i kai harta tsofafin harda
yara kashewa suke alokacin da sarkin yaki ya
gama tarasu sai yace sarki yace mu tunkari
tsibirin
lasmir domin mu kamo sadaki saiful maut a raye
ko a macce sai suka amsa da toh sannan kowa
ya
kama dokinsa suka fara tafiya wanda idan
kagansu
sai ka tsorata da shigarsu Alamarin su sadauki
saiful kuwa suna cigaba da tafiya basu hadu da
kowa ba har a lokacin sannan suka cigaba da
tafiya da lokacin sallah yayi sai suka yada zango
domin suyi sallah sun gama sallah kenan sai
sadauki saiful ya dan kinshigida domin yandan
huta sun da zauna bai kai ko rabin sa a ba suka
fara jin sahun dokuna masu yawa sun tunkaru
inda
suke kawai sai sadauki saiful ya mike a guje
domin ya tsaya cikin shiri bakowa bane suka
tunjaro wajen nan in banda su sarkin yaki garin
kisra ita kuwa aljana jazwariya tana zaune akan
bushiya don bata da karfin damtse ballatana ta
taimaki sadauki saiful maut suna karasowa su ka
sauko daga kan dawakansu domin su yi wa
sadauki saiful kwab daya abinda basu sani ba
cewa shi kuwa sadauki ya riga da yayi lissafin
yanda zai girbi rayukansu aikuwa ko wani bata
lokaci basu yi ba jarumai masu ji da kansu guda
goma suka zabura suka ruga a guje suka yo
kansa
SHIN SU SARKIN YAKI ZASU SAMU GALABA
AKAN
SADAUKI SAIFUL
domin sanin wannan amsa sai a biyo ni sai
anjima
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters

Please Login or Register in order to submit comment