Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

MUMINA DA AZZALUMA
Littafi na daya 1
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- bin Hamza
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 1A


A wani zamani can baya mai tsawo daya shude an yi wani babban birni mai suna Nurul Ikhlas. Gaba 1 jama'ar wannan birni na karkashin jagorancin wani babban malami ne ma'abocin addinin musulunci mai suna Uyubul Hasanu. Sarki Uyubul Hasanu mutum ne adali, Allah ya hore masa dukiya mai yawa, kuma ga tarin ilimin addinin musulunci. Jama'ar birnin Nurul Ikhlas na matukar kaunar sarki uyubul hasanu, kuma suna matukar biyayya a gareshi, domin ko tsinke ya ajiye yace kada kowa ya ketare shi to babu wanda zai ketara. A kullum dare da rana sarki Uyubul Hasanu ba shi da wani aiki wanda yafi kai ziyara zuwa ga sauran kasashen dake makwabtaka da shi domin yada addinin Allah don kawar da kafirci a doron kasa. Birnin Nurul Ikhlas ya kasance birnin da jama'ar garin suka mai da hankalisu akan noma da ibadar Allah kurum, ko kadan basu da da wani shiri akan horar da mayaka ko dan kare birnin su daga yaki ko sumame, Ba komai ne ya haddasa hakan ba face tunda aka kafa birnin basu taba fuskantar matsalar 'yan sumame ba, kuma basu taba gwabza yaki da wata kasa ba saboda tsananin yawan du'a'insu bisa neman tsari ga Allah. Da yake jama'ra birnin Nurul Ikhlas sun rike gaskiya da amana sai Allah ya basu kariya ya amshi du'a'insu sau tari idan azzalumai ko sauran sarakunan dake mulki a makwabta suka yi yunkurin kawo farmaki izuwa ga wannan kasa sai su janye dan kansu, musamman idan suka zo kofar birnin sai suji Allah ya cusa musu kaunar birnin da jama'arsa a cikin zukatansu sai dai kawai kaga shugaban tawagar ya bada umarnin a juya da baya. Bisa wannan dalili ne zaman lafiya ya samu sosai a birnin har ma da sauran kasashen dake makwabtaka dasu ya zamana cewa ana huldar kasuwanci da juna, abinda ya rage kawai shi ne auratayya. Itama auratayyar ana yi amma sai dai su a basu 'ya' amma su baza su bayar ba saboda bin dokar musulunci. Sarki Uyubul Hasanu yana da matar aure guda 1 jal wadda ake kira da suna Hufaira. Hufaira kyakkyawar mace ce ta gaban kwatance, kuma Allah ya albarkacesu da samun 'ya mace guda 1 kyakkyawar gaske wato dai ta gaji mahaifiyarta. Asalin sunanta shine Juwairiya, amma tun tana jaririya sarki Uyubul Hasanu ke kiranta da suna 'MUMINA'. Bisa wannan dalili ne sunan ya bita har zuwa yanzu da ta cika shekara 12. A wannan lokaci ne kyawun Mumina ya kara baiyana a fili karara ninkin na mahaifiyarta har ta zamo abar kwatance a gaba 1 nahiyar. A wannan shekara da Mumina ta cika shekara 12 ne sarki Uyubul Hasanu ya fara tunanin ya fara fita yawon wa'azi don jaddada addinin Allah a doron kasa domin ya fiskanci cewa gaba 1 nahiyar babu wwani birni da ake fitowa a fili ayi addinin musulunci face birnin Nurul Ikhlas. Duk sauran kasashen ma'abota bautar gumaka ne da tsafi koda akwai musulmai sai dai suyi addinin nasu a boye ba tare da wani ya sani ba. Wani abin al'ajabi shi ne tun Mumina na da shekara 7 a duniya ta haddace Al'kur'ani mai girma kuma ta sami ilimin sauran littatafai da dama. Shi kansa sarki Uyubul Hasanu yana mamakin irin wannan baiwa da Allah yayi mata. Mumina ta taso yarinya nitsattsiya mai kaifin hankali da kaifin basira ga kuma hangen nesa. Tana da wata irin baiwa ta ban mamaki. Wannan baiwa kuwa itace duk abinda zai faru a gobe sai tayi mafarkinsa a yau da daddare kuma bata manta abinda ta gani a mafarkin. Wannan baiwa ta Mumina babu wanda yasan da ita face iyayenta, ranar da suka fara ganin wannan baiwa kuwa wata safiya ce sa'adda suka zauna su 3 cikin farfajiyar gidansu suna kalaci. Sai Mumina ta dubi mahaifiyarta Hufaira tace "ya ke ummina kiyi sani cewa jiya nayi mafarki na ganmu a zaune a nan inda muke warhaka muna wannan kalaci. An nuna min cewa wata dillaliya zata kawo kaya a cikin farin kwando lullube da jan mayafi. Zakiyi siyayya a wajenta ki biyata kudinta ta tafi, amma abin dana keso daku shi ne duk abinda ku kaga nayi mata ku zuba min ido kawai kada kuce uffan domin sai ta ha'inceki". Koda jin wannan batu sai sarki Uyubul Hasanu da Hufaira suka dubi juna suka bushe da dariya. Sarki Uyubul Hasanu yace haba 'yata shin wannan almarace ko kuwa tatsuniyace? Mu dai a sanin mu dake bamu taba jin kinyi mana surutun banza irin wannan ba. Cikin matukar damuwa Mumina ta dubi sarki Uyubul Hasanu tace ya abbana hakika babu almara ko tatsuniya a cikin wannan batun nawa ina sanar da ku hakikanin abinda na gani ne. Har Hufaira ta budi baki zata sa albarka a zancen sai sukaji muryar mace tana sallama. Lokaci guda sukayi arba da mai shigowa sai suka tsuru-tsuru suka cika da mamaki suna kurawa Mumina ido. Ba wani ne ke shigowa ba face wata dillaliya dauke da farin kwando a kanta rufe da jan mayafi. Dillaliyar ta shigo da fara'arta sannan ta durkusa har kas ta gaida sarki da Hufaira cikin biyayya, a lokacin Mumina ta zuba mata ido tana mata kallon nitsuwa. Koda dillaliya ta bude kwandonta sai ga sarkokin zinare iri-iri a ciki masu ban sha'awa. Sa'adda Hufaira ta ga sarkoki sai ta kamu da sha'warsu don haka sai aka fara ciniki, Bayan an gama ciniki Hufaira ta sayi guda 2 ta biya, sai tace $ $ MUMINA DA AZZALUMA
Littafi na daya 1
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- bin hamza
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 1A

MUMINA DA AZZALUMA Littafi na daya 1 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- bin hamza Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 1B Sai tace to itama tana da wadansu guda 2 wadanda take son ta siyar. Dillaliya tace ai se ki debosu na gani. Cikin hanzari Hufaira ta mike taje ta dauko sarkokin ta kawo. Dillaliya ta dubi sarkoki tayi musu kudi. Koda jin tayin wulakancin da tayi mata sai tace ta fasa siyarwa, dan haka ta kawo kudin wadancan data saya. Hufaira ta bata kudin ta kimanin dinare 2000 dillaliya ta karba tana gdy cikin farin ciki ta juya da nufin ta fice daga gdn. Sai Mumina ta sha gabanta tace koma da baya ki baiwa mahaifiyata ainihin sarkokinta wadanda ta kawo miki, cikin fushi dillaliya tace wace irin magana kike ni ban dauki sarkokinta ba. Hufaira ta mike ta taho garesu rike da sabbin sarkokin da tsofaffin, sannan ta dubi Mumina a fusace tace, me kike nufi da ta bani sarkokina alhalin gasu a hannuna?" Mumina tayi murmushi tace wadannan dake hannunki basu ne naki ba, ta musanya miki da wadansu wadanda basu kai naki daraja ba idan tana musu ta sauke a duba, kafinnan ya ummina sarkokinki wani iri ne kuma ya yanayin nauyinsu yake? Hufaira tace sarkokina na zinare ne kuma suna da nauyi a hanu. To kiyi nazarin na hanunki basu da nauyi kuma ki dubesu da kyau na jauhari ne. Hufaira ta daga sarkokin dake hanunta tayi nazarinsu da kyau, sai hankalinta ya tashi ta fisge kwandon ta birkitashi, Ai kuwa sai ga sarkokinta a ciki. Cikin matukar farin ciki Hufaira ta daga hannu zata sharawa dillaliya mari kawai sai sarki Uyubul Hasanu ya haneta, yace ai barawon da bai tsira da kayan da ya sata ba to baici hukunci ba, kyaleta kawai. Sarki ya dubi dillaliya yace daga wanne birni kikaxo nan? Kuma wani Addini kike yi? Ki fada mini gaskiya domin idan kika yi karya zan sa a yanke miki hannu bisa laifin satar da kika yi a gdn, Yanzu kafinnan ke kuma Mumina yaya akayi kika lokacin da ta faki idonmu ta musaya sarkokin nan? Mumina ta sake yin murmushi tace Ni ban gani da idona ba amma Ubangijina ya nunamin duk wannan abu da zai faru cikin mafarki na. Koda jin wannan batu sai jikin dillaliya yayi sanyi nan take idanunta suka ciko da kwalla ta fara kuka. Al'amarin da ya matukar baiwa su Hufaira mamaki kenan. Sarki Uyubul Hasanu ya dubi dillaliya yace ina dalilin wannan kukan naki?. Yayin da dillaliya taji wannan tambaya sai ta share hawayenta tace ya kai wannan sarki me adalci kafin na baka amsar wannan tambaya ta 2 zan baka ta 1 a gare ne, Ni dai suna na Karima, kuma na fito ne daga kasar sarki Sharudul Anzar wanda ya kasance shahararren bokan da babu kamarsa a duniya a wannan zamani. Na kasance nice jakadiyar sarki Sharudul Anzar kuma nafi shekara 30 ina masa bauta. Sarki Sharudul Anzar na da 'ya mace kyakkyawar gaske wadda kamanninta iri 1 ne sak dana wannan 'ya taku Mumina. Sunan wannan 'ya tasa "Azzaluma". Hakika farkon shigowata gdn nan na tsorata ainun saboda nayi zaton cewa sarki sharadul anzar ne yayi aikin sa na tsafi ya kawota nan. Sa'adda Dillaliya tazo nan a zancenta sai Mumina dasu sarki suka dubi junan sucikin tsananin mamaki, Mumina ta dubi karima cikin nitsuwa tace yanzu kina nufin Ni da 'yar sarki sharadul anzar kamarmu 1 ce babu bambanci?. Karima tace kwarai kuwa tamkar an tsaga kara. Karima taci gaba da cewa watarana na dauki wani tambulan na lu'u lu'u wanda sarki ke shan giya a cikinsa na taho garesu a lokacin da yake zaune da 'yarsa Azzaluma suna nishadi, sai wannan tambulan din ya fadi ya fashe daga hannuna. Koda ganin haka sai ran sarki sharudul anzar ya baci, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, tuni a wannan lokaci jikina ya kama kyarma saboda tsananin tsoron sarki bisa sanin halinsa na rashin imani. Ba'ayi masa laifi ba ma yana zaluntar mutum bare kuma anyi masa. Sa'adda sarki da'yar azzaluma sukaga na firgice na tsorata sai suka kama dariyar mugunta, sukayi ta dariyar kamar bazasu daina ba, har kwalla ta cika musu idanunsu lokaci guda kuma suka daina suka tsuke bakin su suka murtuke fuska. Sarki ya dubi 'yarsa Azzaluma yace yake 'yata yanzu wane irin hukunci ya kamata a mata bisa wannan gagarumin laifi data tafkamin kin sani cewa wannan tambulan na gaje shi ne wajen kakana na 3, kuma duk duniya babu wani makeri da zai kera irinsa ya dawo dai-dai kamar yadda yake da?. Koda jin wannan batu sai Azzaluma tace, ai hukuncin da zakayi mata 1 ne ka bata zabi 1 daga cikin 2 kodai ta kawo dinare dubu 900, 000 a mai makon wannan tambulan din ko kuma a yanke hannayeta 2, lallai kuma duk yadda za'a yi kuma ta kawo su cikin makwanni 3 kacal. Sarki yace hakika wannan hukunci yayi dai-dai tabbas ina alfahari dake, domin gajeni wajen mugunta da zalunci shi yasa na daina kiranki da sunan ki na asali sai azzaluma, ki sani cewa tun kafin ki cika shekara goma 12n nan kike cin zalin yara kanana sa'anninki, A sanina kin karya yara 340 kin kashe 550 daga tasowarki zuwa yanzu. Koda jin wannan zuga sai azzaluma ta bushe da dariyar farin ciki sannan tace, ya kai abbana ai dama ance kyan da ya gaji Ubansa, ai har yanzu banyi rabin abinda kayi ba. Ka sani sai nayi zaluncin da bb wani mahalukin daya taba yinsa MUMINA DA AZZALUMA Littafi na daya 1 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- bin hamza Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 1B .

MUMINA DA AZZALUMA Littafi na daya 1 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- bin hamza Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 1C Ai har yanzu banyi rabin abinda kayi ba na zalunci, amma ina tabbatar maka da cewa nan gaba sai nayi zaluncin da babu wani mahalukin daya taba yin kamarsa a duniya. Tabbas sai na kawar da duk wani mutum mai adalci da tausayi a doron kasa ya zamana cewa babu sauran mai tausayi. Sai na share dukkan addinai ya zamana cewa bb sauran addini face na tsafi. Sa'adda azzaluma tazo nan a zancenta sai farin ciki ya lullube sarki sharudul anzam, ya rumgumeta yana sumbatar gashinta, yace da kyau 'yata, lallai ina alfahari dake. Take sarki ya juyo ya dubeni yana murmushin keta yace, to jakadiya kinji hukuncin ki sai ki tashi da sauri ki bazama neman dinare dubu dari tara ki kawo mini cikin mako 3. Zan tsare mijinki da 'yayanki a nan cikin gidana idan kika ki kawowa ko kuma kika dawo bb wannan dinare to zan sa a fille kawunansu. Koda jin wannan batu sai na bazama neman dinare, daga wanna rana na baro birninmu na shigo wannan naku na Nurul Ikhlas saboda naji cewa birni ne mai tarin arziki na shiga dillanci, duk gdn da naje sai nayi musu satan sarkokin dinare kuma kullum sai na sauya kamannina ba don komai ba sai don kar wadanda nayiwa sata su shaidani. Yau kwana 11 kenan a cikin wannan birni naku, kullum hankorona shine na tara sarkokin da kudinsu zai kai dinare dubu dari tara domin na fanshi rayukan iyalina, amma gashi ko rabi ban tara ba kuma asirina ya tonu kun kamani lallai na rasa iyalina..." Koda karima tazo nan a zancen ta sai ta sake fashewa da kuka, al'amarin da ya baiwa su sarki matukar mamaki kenan, suka kamu da matukar tausayinta. Sarki Uyubul Hasanu ya dubi karima yace, ya ke wannan dillaliya hakika akwai ban tausayi a lbrn ki da al'ajabi, kuma tunda kin fadamin gaskiyar halin da kike ciki zan taimakeki na baki dinare dubu dari tara kije ki kaiwa sarki sharudul anzam domin ki ceci rayuwar iyalanki, amma bisa sharadi 1. Sharadin kuwa shine zaki karbi addininmu, wato addinin musulunci. Lokacin da karima taji wannan batu sai ta bushe da dariyar farin ciki, sannan tace, Ai ni koma baka taimakeni ba sai na karbi wannan addini sbd na tsumu sa'adda naji bayanin 'yarku na cewar Ubangijin ku ya nuna mata wannan al'amari duka a cikin mafarkinta, lallai duk wanda yayi wannan aiki shine Ubangijin gaskiya. Sa'adda dillaliya tazo nan a zancen ta sai sarki da hufaira da Mumina suka cika da tsananin farin ciki. Nan take sarki ya biyawa dillaliya Kalmar shahada ta maimaita. Bayan karima ta musulunta sai Hufaira shawarceta akan tayi hakuri ta zauna tsawon kwana 3 domin ta huta kuma ta koyi yadda ake bautar Ubangijin Musulunci. Bayan su Mumina sunyi sallar isha tare da karima sai Hufaira ta dauko musu abinci. Da suka kammala sai sabuwar hira ta barke tsakanin Mumina da karima. Inda mumina ta dubi karima tace, Bani labarin azzaluma. Hakika nayi mamaki da kika ce kamarmu 1 ni da ita lallai zan so nayi arba da ita. Koda jin wannan batu sai karima tace, yake mumina shawarar da zan baki itace kada ki yarda kiyi arba da azzaluma domin ganinta ba alheri bane, muddin zaku hadu sai ta zalunce ki musamman ma idan taga kamarku 1 domin tana kishi akan dukkanin wanda zai zamo kishiyarta. Tabbas sai tayi yunkurin hallakaki. Ki sani cewa azzaluma ta kasance basadaukiya ce, kuma ta kware wajen iya yaki sannan tana da dumbin sihirin tsafi, ina tsoron gamuwarki da ita. Koda jin wannan batu sai Mumina tayi murmushi har kyawawan hakoranta suka bayyana, sannan tace, 'Ya ke wannan bakuwa, ki sani cewa a ratuwata ban taba jin tsoron wani mahaluki ba face Ubangijina, idan azzaluma na takama da karfin tsafi ni kuma ina takama da karfin addu'a. Idan azzaluma na takama da sadaukantaka da iya ina tabbatar miki da cewa idan banfi ta ba to sai dai muyi kunnen doki. Caraf sai hufaira ta dubi Mumina cikin mamaki tace, yaushe kika zamo basadaukiya kuma mayakiya ban sani ba?. Maimakon Mumina tace wani abu sai kawai tayi murmushi, sannan ta mike tsaye ta nufi farfajiyar gdn inda wata katuwar bishiya take. Ita dai wannan bishiya ta kasance duguwa, kuma kaurinta ya kai kamu goma sannan tun kafin a haifi Mumina aka dasa wannan bishiya. Koda wasa sarki bai uyubul hasanu bai taba tunanin yasa a sareta ba, domin yasan sareta ma aiki ne sai an yini ana aikin. Inda bishiyar take wajen zaman sarki ne idan zaiyi lazumi, kuma tsuntsaye su kan hau kan bishiyar su dameshi da koke-koke, wani lokaci ma suna masa kashi a tufafinsa. Sai da Mumina tazo daf da bishiyar sannan tasa kafa ta naushi bishiyar, sbd da karfin dukan sai da bishiyar ta jijjigo har jijiyarta. Dai dai inda kafar Mumina ta nausa kuwa sai da ya lotsa ya burma ciki. Sbd tsananin mamakin ganin abinda ya faru kuwa Hufaira da karima basu san sa'adda suka mike tsaye ba a firgice, suka dora hannayensu akai suka wangame baki suna kallon ikon Allah. Karar tunbukowar bishiyar da faduwarta ne yasa su sarki da hadiman gdn suka rugo zuwa wajen a razane, lokacin da suka ga Mumina ce tayi wannan aiki sai kowa ya cika da mamaki.Mumina taci gaba da murmushi ba tare da tace uffan ba. Da taga ana kallonta ma sai ta shiga dakin sarki ta dauko takubba 2 ta shiga kaiwa iska sara da suka tana tsalle-tsalle har da alkafira. Wani lokacin idan tayi tsalle sama sai ka ga kamar an janyeta da qugiya, kuma sai tayi katantanwa kamar sau 7 a sararin sama cikin iska sannan ta sauko kasa ta direkafafuwanta. Sarki da sauran mutanen gd sai suka zamo tamkar yan kauye suka ci gaba da kallon sarautar Allah. Basu gushe ba suna kallon wannan bajinta da jarumtaka har sai da mumina ta tsaida kanta. Lkc guda gdn ya rude da kabbara anayi mata jinjina daga nan kowa ya fara fadin albarkacin bakinsa, wasu suce ba mumina bace, wasu kuma suce itace. Lokacin da sarki Uyubul Hasanu ya ga gdn ya rude da surutu sai ya kama hannun mumina ya ja ta zuwa cikin turakarsa ya zaunar da ita bisa shimfidarsa. Da hannunsa ya debo ruwa ya bata ta sha, sannan ya kama yi mata fifita har sai da yaga gumin jikinta ya bushe sannan ya dubeta cikin nitsuwa yace ya ke 'yata bani lbr, yaya akayi kika zamo basadaukiya kuma mayakiya amma ban sani ba. Koda jin wannan tambaya sai mumina tayi ajiyar zuciya sannan tace, ya kai Abbana ka gafarceni bisa boye wannan sirri gareku kai da mahaifiyata. Ka sani cewa hakan ta faru ne sbd kada na karya alkawari. Koda jin haka sai sarki Uyubul Hasanu ya sake dubanta cikin mamaki yace, ban gane ba, wani irin alkawari kuma? Mumina tace, fiye da shekara 6 baya wani abin al'ajabi ya faru gareni". Tayi shuru tamkar me tunani. Can ta dubi mahaifinta tayi murmushi ta fara bashi lbr kamar haka. Watarana ina wasa ni kadai a cikin farfajiyar gdn nan sai wani kyakkyawan aljani ya bayyana gareni wanda ya kasance ma'abocin addinin musulunci, yana sanye cikin shigar yaki da makamai iri-iri a jikinsa, kuma tufafinsa farare ne kal, abin sha'awa. Goshinsa nata kyalli dauke da alamar sallah. Ya kai Abbana ka sani cewa Allah ya hore min rashin tsoro don haka sa'aada naga wannan aljani ko kadan ban tsorata ba, sai ma na kama gemunsa ina ja ni a ganina na sami abin wasa. Daga wannan rana kullum sai aljani ya zo gareni muyita wasa, kuma a duk sanda yazo sai ya koya mini yadda ake sarrafa takobi. Haka kuma yana koyar dani karatun Alku'ani. Nan da nan na shaku dashi ya zamana duk ranar da bai zo ba sai naji bb dadi. A cikin shekaru 4 ne na kware ainun wajen iya yaki, har ma na kara dashi. Shi kansa yace dani ya gamsu cewa na zamo cikakkiyar mayakiya. A wannan lkc ne ya sanar dani cewa daga yau ba zan sake ganinsa ba don haka yazo ne muyi ban kwana na karshe. Lkcn dana ji wannan batu sai idanuna suka ciko da kwallah na fara zubar da hawaye, al'amarin daya dugunzuma hankalinsa kenan yace, Ina dalilin wannan kuka naki ya ke mumina? Sa'adda naji wannan tambaya sai na dago kai na dubeshi ina mai share hawaye nace, ya kai ma'abocin kwarjini kayi sani cewa yau shekarata 4 kenan ina tare da kai amma ko sunan ka ban sani ba na shaku da kai, ban san inda kake ba amma gashi ka koyar dani ilimin addini kuma ka bani horo na yaki irin wanda bb wani mahaluki da ya taba bani. Shin idan ka gujeni a yanzu baka ci amanar kauna ba?. Koda jin wannan lafazi sai zuciyar wannan aljani ta karaya, idanunsa suka ciko da kwalla, sai kawai ya rungumeni ya fashe da kuka. Nima sai na kama kukan aka rasa wanda zai rarrashi wani a cikin mu. Daga can sai janye jikinsa daga nawa muku fuskanci juna yace, Ya ke mumina kiyi sani cewa ni sunana Abtarul Hudes, yau shekarata dubu dari hudu da dari shida da sittin da 6 a duniya. Tun tasowata bani da wani aiki face yin hidima a cikin addinin Allah. Na rayu a cikin zamani kala-kala, ban taba yin aure ba, kuma ban taba haihuwa ba, don haka idan na kalleki sai naji tamkar 'Yata ce ke ta cikina. Ki sani cewa a cikin barcina Allah ya nuna mini cewa kece jarumar da zata yada addinin musulunci a wannan zamani, bisa wannan dalili ne na zo gareki don na baki gudumawata. Ina sanar dake cewa tun da na zama saurayi nake ta yake-yake a tsakanin kasashenmu na aljanu don tabbatar da gaskiya bisa karya. Har yau ban gama cin dukkan kasashen aljanu ba. A yau ne zan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment