Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

still bintu na nn kullum cikin damuwa da tunani,in ta zauna d'aki bata da aiki sae dai ta shiga video a wayar ta tayi ta kallon video records d'in da sukayiwa juna ita da waheed na rayuwar su mae cike da zallar so da ban sha'awa wanda hakan kesa ta qara jin tsanar kanta suna rayuwar su mae dad'in gaske amma ta zamo silar wargaza duk wani farin cikin su da kullum in ta kwanta bacci sae tayi mafarkin waheed yazo cike da murmushi ya rungume ta yana fad'in ya yafe mata duk abinda ta mishi tazo su shinfid'a sabuwar rayuwar da tafi ta baya ma.
Ko yanzu ma kwance take tana bacci cikin mafarkin ta da yafi na kullum dad'i,dan ganin kanta tayi ta koma gidan waheed suna rayuwar su mai cike da dad'i tamkar ba wani abinda ya faru har ma tana d'auke da ciki d'an wata shida waheed sae ririta ta yake tamkar zae had'iye ta ga mami akae akai sae tazo ganin lafiyar ta snn hankalinta ke kwanci.
Firgigit taga ta tashi daga mafarkin wacce cikin rashin kuzari ta tashi zaune tare da had'e kanta da guiwa hawaye masu zafi suka shiga silalowa a hnkli kan kumatun ta dmn ko kad'an bata son tana irin wnn mafarkin ta farka amma ta rasa meyasa kullum sae tana cikin yin mafarkin ta mae dad'i ta ganta kawai ta farka ba tare da wani ya tashe ta ba,kaddai haka na nufin mafarkin ta bazai zama gaskiya ba.
Nan ta saki kuka a hankli sae ga anti Hafsa ta shigo d'akin kae tsaye ta had'iye kukan ta kuma sa tafin hannunta a 6oye tana share hawayen fuskarta.
Anti Hafsa ta qarasa gurinta ta zauna a hnkli kusa da ita tare da d'aura tafin hannun ta kan gadon bayan bintu tace"bintu sau nawa zan roqe ki kan ki rage yawan kukan nn da damuwar nn basune mafita ba addu'a ce mafita amma kinqi ki daina shin ni ban isa insa kiyi abu bane ko in baki shawara?
Bintu ta d'ago kanta a hankli tana kallon anti Hafsa snn ta girgiza kanta tace"ba haka bane anti Hafsa kiyi haquri ina cikin yanayinda bansan ta yaya zan iya fidda damuwa a raina ba ko da naso hakan kuwa dmn na kasance wacce iyayena ke fushi dani ta yaya zanga wani haske har damuwa ta cire a raina ba tare da sun daina fushi dani sun yafe min ba.
Ta qarashe mgnr ne cikin kuka, cike da tausayi Anti Hafsa ta rungume ta sae rarrashinta take tana fad'in"shiyasa nake son ki dage da yin addu'a ko Allah zae sassauto zukatan su umma su daina fushi dake"
Tace"Aunty ni kam wace irin addu'a ce banyi ba ba dare ba rana amma kmr banayi sbd na riga na aikata abinda dole sae Allah ya hukuntani.
Allah mae yafiya ne bintu dan haka kici gaba da yin addu'a ki kuma ci gaba da yawaita karatun qur'ani fiye da yanda naga kinayi da sannu zakiji qunci da damuwar dake ranki suna tafiya kinji"
Bintu ta gyad'a kanta anti Hafsa tace"to tashi muje jabir ne yake neman ki"
Ba musu ta tashi suka fito falo jabir dake zaune kan doguwar kujera sae faman danne danne yake da wayar sa har bintu taje ta zauna kusa da kujerar da ke facing d'inshi snn ta gaishe shi.
Sae a snn jabir ya d'ago ya kalle ta had'e da fad'in "iyayen bacci kin tashi duk lokacinda na shigo se ace min kina bacci ni kam wae ba kya gajiya?
Ya qarashe mgnr ne sae kallon ta yake da kulawa ita kuwa kanta qasa tayi shiru ba tare da tace mishi komai ba sbd mostly ba dan tana jin bacci take yin sa ba sae dan kawai ta ganta tanayin mafarkin sun shirya ita da waheed da sam bata son taga ta farka.
Jabir dake kallonta bae sake ce mata komai ba kasancewar sa mutum ne da baya son takura kowa wanda ko kad'an baya son ganin mutum cikin damuwa koda bai san shi ba kuwa.
Anti Hafsa wacce ta fito daga kitchen d'auke da fruits a plate an yanyankasu so cute ta kai gaban jabir ta ajiye snn ta zauna a kusa da kujerar da yake zaune tana kallon bintu tace"wae bintu ba magana naji jabir na miki ba amma kin masa shiru kmr bada ke yake magana ba"
Jabir da ya kai slice d'in kankana a bakin sa yayi murmushi yace"anti bata son damuwa ki barta kawai"
Anti Hafsa tace"hm bintu duk gabad'aya ta sauya sae kace ba kaine abokin wasan ta ba da har guje guje kukeyi a tsakanin ku"
Jabir yace"anti kinsan wancan lokacin bata cikin wata damuwa yanzu kuma akan mata uzuri"
Hakane
Cewar Anti Hafsa wacce still idonta na kan bintu tace"tashi to ki tafi dama ganin ki da ba yaya ne yace ina kike"
Bintu bata ce komai ba ta tashi ta bar gurin jabir ya bita da ido har ta shige d'aki kana ya maida duban sa gun anti Hafsa yace"anti meyasa kika ce ta tafi?
Tace"to jabir
ganin nayi ta zamar maka kmr wani foto kana mata magana ba amsa.
Duk da haka anti ae da kin barta sbd yawan zaman d'akin nn ita kad'ai na qara mata damuwa amma ko bata cewa komai in ta zauna cikin mutane yafi.
Anti Hafsa tace"wato jabir damuwa nake ji in na ganta shiru bata cewa komai shiyasa nace ta tafi d'aki amma ni kaina bana son zaman d'akin da take yi wlh.
Jabir ya numfasa yace"to me zae hana kuyi mata aure anti"
Aure kuma jabir meyasa kace haka?
Anti kinsan ni mutum ne da bana son ganin kowa a cikin damuwa tunda daidaita tsakanin su da waheed bai yiyu ba har gashi tuni ta gama idda y not idan da akwai wanda ke zowa gurinta ace kawai ya fito.
Hmm! jabir wa kake tunanin bintu zata kula a halinda take ciki snn waye zai ji dalilin rabuwar ta da mijinta da kuma matsalar mahaifar da take d'auke dashi ya aure ta.
Anti duk wani mae sonta da gaske wa en nn hujjojin ba wata matsala bace burin sa kawai ya aureta.
Hm Jabir knn da kmr wuya samun irin wnn masoyi dmn ftr kowa yayi aure ya hayayyafa dan haka kama bar wnn zancen.
Anti kuskure d'aya ne bintu ta aikata shine zubar da cikin farko da tayi sauran duk makirci ne aka shirya mata, matsalar mahaifar ta kuwa inshaa Allah matsala ce da za'a iya magance ta.
Anti Hafsa tace"akwai abinda baka sani ba jabir shine kwanakin baya na d'auki bintu mukaje asibiti dmn a bamu maganin da zae magance mata matsalar mahaifarta a nn likita ya bamu tabbacin cewa matsalar mahaifar ta babbar matsala ce da sae an fita da ita waje an mata aiki sbd wnn maganin da su zeenah sukayi sa mata ya illata mahaifar sosai ta yanda ko ta sami ciki bazai kai koina ba zae zube.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!amma anti shine ba'a sa yaran qara ba a biwa bintu haqqinta wnn cin amanar ae yayi yawa.
Wlh jabir bintu ce ta roqe ni kan kar inyi haka dmn bata son umma taji ta qara shiga wata damuwa,amma ba dan haka ba naso na sasu qara a hukunta su ta yanda ko maqiyin su suka ga zae cutar da bintu wlh baza su barshi ba.
Shiru jabir yayi can yace"Anti idan dan wnn matsalar ne ni naji na gani idan har bintu tana sona wlh zan aure ta.
Da mamaki anti Hafsa ta kalle sa tace"jabir kasan me kake fad'a kuwa kaifa saurayi ne da baka ta6a yin aure ba"
Yace"Anti nasan zakiyi mamakin abinda zae fito daga bakina shine,haqiqa na jima ina son bintu tun ba yau ba wato tun lokacin auren ku da muka fara had'uwa naji ba wata 'ya mace da nake so kmr ta, amma na kasa snr da kowa har ita kanta ba dan komai ba sae dan ganin cewa a lokacin yarinya ce sosai kuma nima ba wasu shekaru ne dani ba se na barshi akan sae ta girma dai dai nima na samu na kammala karatu na fara aiki snn ko zan bayyana sirrin da ke raina, kwatsam tana kammala secondry school naji za'a mata aure,ba yanda na iya dole na haqura dmn na riga na makara amma na shiga cikin tsananin tashin hankli da baqin cikin rashin samunta wanda dalilin haka ne ya janyo min matsaloli da dama a school har mutane suka d'auka ko rasuwar Abban mu ne ya ta6ani da yawa.
Anti Hafsa dake sauraren shi tayi shiru dmn haqiqa ta tuna lokacin da yake ta samun matsala a shchool da kowa yayi tunanin ko mutuwar mahaifin su ce ta ta6a shi da yawa dmn lokacin auren bintu yayi dai dai da mutuwar mahaifin su wanda ba dan matsalolin da yayi ta samu ba da yanzu ya kammala school har ma ya fara aiki.
Tace"haqiqa jabir na tausaya maka amma ina mai baka haquri auren ka da bintu ba zae yiyu ba"
Cikin tashin hankali jabir yace"dan Allah meyasa kika ce haka Anti?
Sbd sanin kanka ne bazai yiyu ba, da dai ace tun a wancan lokacin ne da kaji kana sonta ka fad'a da zaka same ta amma yanzu bazai yiyu ba gaskiya kayi haquri.
Yace"naji nayi kuskure da ban fad'a a wancan lokacin ba amma dan Allah tunda yanzu na fad'a kiyi haquri ki taimaka min tun kafin in rasa damata wlh still ina sonta anti ko kad'an ban ta6a jin sonta ya ragu a zuciya ta ba sae ma qaruwa da yake.
Tace"baka fahimce ni ba jabir ni matsalar da bintu take d'auke dashi yasa nace aurenku bazai yiyu ba snn kuma a matsayin ka na saurayi bai kamata ace ka auri wacce ta ta6a yin aure ba,byn kuma irin matsalar da take dashi a mahaifar ta
u have to think kayi tunani kowa ka gaya ma mgnr nn bazae barka ba.
Yace"anti koma mene ne ni nace naji na gani ina sonta a haka nidai kawai kice min kin amince"
Tace"Aa bazan ce na amince ba jabir kuma ina roqon ka dan Allah kar ka bari yayanka yaji wnn mgnr kaji"
Shiru jabir yayi yana kallon ta cikin marairaice fuska yace"anti ki gaya min dan Allah ko dai wani mugun hali nake dashi da ba kya son bintu ta aure ni"
Anti Hafsa ta girgiza kanta dan ko ta ina jabir baya da wata makusa hadadden saurayi ne mae kyaun gaske gashi fari tas tamkar zuciyar sa sam bayada wani mugun hali.
Tace"ko d'aya jabir babu wani mugun hali da kake d'auke dashi dmn duk maccen da ta same ka ta gama yin sa'a a rayuwa kawai dai auren ka da bintu ne bazae yiyu ba,ba dan naqi ba sae dan yafi dacewa da kai ka sami yarinya buduwar mae cikakkiyar lafiya.
Jabir zae yi magana knn tace"dan Allah jabir kar kace komai kaji bana son mgnr nn tayi tsawo.
Take idanuwan jabir sukayi jajur suka ciko tap da qwallah ya tashi da sauri ya bar falon.
Anti Hafsa da ta bishi da kallo ta girgiza kanta dmn ya bata tausayi amma sam ba aikin hankali bane tace ta amince son kan zae yi yawa gwara kawai ya sami budurwar yarinya dai dai shi ya aura.
Nan ta bar falon wacce bata zarce koina ba sae d'akin su ilham gun bintu ta same ta zaune kan bed ta jingina bayanta da pillow waya a hannunta ta kafe idonta akan screen d'in wayar ko kyaftawa bata yi,
anti hafsa tayi tsaye tana kallon ta had'e da girgiza kanta snn taje kusa da ita ta zauna kan bedside drawer tare da kar6ar wayar bintu ta duba abinda take tunani kuwa shine wato pics d'insu ne take ta kallo ita da waheed da gabad'aya folder d'in ba wani foto sae nasu.
Kafin anti Hafsa tace komai bintu ta kama hannuwan anti hafsa cikin yanayin begging qwalla cike a idonta tace"Anti hafsa ina son yaya waheed bazan iya ci gaba da rashin sa a kusa dani ba,dan Allah ki taimaka min in koma gareshi wlh rayuwata bazata ta6a dad'i ba sae tare dashi"
Nan kawai ta fashe da kuka anti Hafsa ta jata jikinta sae rarrashin ta take.
[12/6, 6:27 AM] Billygiro😊: *_🎱BINTUWAHEED🎱_*








*_Story n written by Billy giro😊_*






*_page 30_*
Bayan wasu en kwanaki da faruwar haka ne.
Da dare guraren qarfe tara Anti Hafsa ce ta fito daga wanka tana zaune kan dressing mirror tana shafa mai sae ga mijinta ya shigo d'akin cikin shirin sa na bacci yayi tsaye hannuwan sa cikin aljihun wandon sa sae kallon ta yake ta jikin mirror.
Murmushi ta sakar masa tare da juyowa tace"Abban ilham ya akayi wani abu kake buqata ne?
Sae da ya lumshe idanun sa a hnkli ya koma ware su a kanta snn yace"eh magana nake son zamuyi"
D'auke da murmushin da ke fuskarta ta taso suka je kan bed suka zauna tana kallon sa tace"ina jinka Abban ilham"
A hnkli ya d'an numfasa had'e da fad'in"me yake faruwa ne tsakanin ki da jabir da naga kwata kwata ya daina zowa cin abinci a nn sae dai inga kin aika masa?
Tace"ba komai nima haka kawai naga ya daina shigowa shiyasa nake aika masa qila yanzu yafi ra'ayin cin abinci shi kad'ai"
Yace"Aa akwai abinda aka masa yake fushi dmn jabir yafi ra'ayin cin abinci cikin mutane idan kuma kika ga ya d'auke qafar sa yaje yana ci shi kad'ai to lallai laifi aka masa yake yin fushi.
Anti Hafsa dake kallon sa tace"ce maka yayi na masa wani abu ne?
Aa ae bazai fad'a ba kin sani amma tabbas yana cikin damuwa duk da yace min ba abinda aka masa.
Anti Hafsa ta numfasa snn tace"hm Abban ilham jabir rigima kawae yake ji"
Wace irin rigima sae kace qaramin yaro ko wani iya shegen ne ya d'auko na son ya rainaki.
Ko d'aya ae kasan jabir baya da wnn asalima ni na masa laifi amma inshaa Allah zan same shi in bashi haquri.
Yace"wane irin laifi ne wnn da har ya iya yin fushi dake?
Tace"um um ba ruwanka nida d'an qanina ne?
Murmushi yayi tare da fad'in"au hakane ae idan tayi tsami ma ji"
Tashi tayi d'auke da murmushi a fuskarta tana fad'in"ae baza ma tayi tsamin ba bare kuji"
Murmushi kawai Abban ilham yayi ba tare da ya sake cewa komai ba ya tashi ya fita acewar idan ta kammala shirin bacci ta same shi d'aki.

Washe gari bintu ce a d'aki zaune kan darduma tana karatun qur'ani,Anti Hafsa ta shigo d'akin d'auke da sallama a bakin ta.
Sae da bintu ta kai aya snn ta amsa mata sallama had'e da gaida ta, Anti Hafsa tace"lokacin breakfast yayi fa kuma sae karatu kike tayi"
Tace"eh anti aya biyu suka rage min in qarasa surar nn in taso"
Tace"eyyah sorry na katse ki amma ina son dan Allah idan kin kammala kije BQ ki kiramin jabir acewar nace yayi haquri yazo muyi breakfast kinji.
Bintu tace"to"
snn Anti Hafsa ta fita daga d'akin.

Tana ida karatun ta rufe qur'ani ta kai shi inda ya dace snn ta fito bata zarce koina ba sae BQ sanye da qaton hijabinta har qasa.
Jabir na kwance idanuwan sa a lumshe kmr mai yin bacci ya soma jin knocking ya tashi cikin rashin kuzari kmr wani mara lafiya yazo ya bud'e qofa,ganin bintu yasa ya d'an saki fuskar sa cikin sauke ajiyar zuciya yace"bintu kece?
Tace"eh anti ce tace kayi haquri kazo muyi breakfast "
Shiru jabir yayi can yace"am sorry sauri nake in fita banida time d'inda zanyi breakfast amma kice mata koda kika zo ma baki sameni ba na fita kinji"
Bintu ta kalle sa kmr zata ce wani abu sae kuma ta gyad'a masa kae alamar taji kana ta juya ta tafi sae kallonta yake har ta 6ace ma ganin sa snn ya koma daga ciki.

Bintu ta sami Anti Hafsa da Abban ilham zaune kan dinning table suna jiran su ita da jabir.
A nn ta snr da Anti Hafsa cewa bata sami jabir ba ya fita.
Kafin anti Hafsa tace komai Abban ilham yace"ya fita? yanzun nn fa da na dawo daga kae su ilham school naga mashin d'insa a ajiye bai isa ace ya fita ba bare yau lahadi ina zai je da sassafen nn haka may be dai yana bacci bai ji lokacinda kike masa knocking ba bari inje in duba shi.

Koda yaje knocking d'aya biyu ya masa sae gashi ya bud'e qofa yace"ya akayi jabir ba kaji lokacin da bintu tazo tana maka knocking bane?
Naji har ma na fito mukayi magana.
Amma shine tace mana baka nn?
Eh nine nace tace bana nn.
Ko meyasa?
Yaya sauri nake ina so zan fita bana da time d'inda zan tsaya yin breakfast that's y nace tace haka bcos bana son kace sae na tsaya yin breakfast d'in.
Cikin rashin yarda da zancen jabir Abban ilham yace"ina zaka je da sassafen nn da har baka da lokacin tsayawa yin breakfast?
Shiru jabir yayi dan ba wani guri da zai je ya fad'a ne kawai.
Abban ilham yace"da kai nake magana ka min shiru"
Yace"yaya kayi haquri bana jin cin abinci ne"
Yaushe ka fara yin qarya jabir to ka sauya dan wlh qarya bata maka kyau,gaya min me ya had'a ka da Hafsa da har kake yin fushi da ita kuma kar ka kuskura kace min ba koma wlh"
Jabir yayi shiru dmn baya son ya fad'a kmr yanda anti Hafsa ta buqata yace"kayi haquri yaya i cnt tell u amma ka tambayi anti Hafsa zata gaya ma"
Guntun tsaki Abban ilham yayi dan ya soma kaishi maqura ya bar gurin ba tare da ya sake ce masa komai ba.
Ya dawo komai bai ce dasu Anti Hafsa ba bae kuma nuna wani 6acin rai a fuskar sa ba har suka kammala breakfast.
Bintu ce ta fara barin gurin nn itama Anti Hafsa ta tashi zata tafi sbd sauri take zata je ta kammala shirya ma Abban ilham kayan sa na tafiya.
Abban ilham yace"yi haquri hafsa zauna zamuyi magana"
Ba musu ta koma ta zauna idon sa akanta yace"mene ne wae yake faruwa tsakanin ki da jabir"
Murmushi tayi tace"wae Abban ilham meyasa kake son sae kaji, i have told u zanje in same shi in bashi haquri mu sasanta kanmu ba sae kunji ba.
D'an guntun murmushi yayi snn yace"wlh bafa zaku min yawo da hnkli ba ni sae naji me yake faruwa"
Anti Hafsa dake kallon sa a d'an shagwa6e tace"plz Abban ilham zancen nn bai shafe ka ba ka barni inje in qarasa had'a ma kayanka lokaci na tafiya.
Yace"Kar ki damu ni nama fasa tafiyar sae gobe inbi jirgin safe gaya min ina jinki me ya had'a ku".
Dariya anti Hafsa tayi had'e da jan karan hancin sa tace"ba wani nn kae dai so kawai kake in fad'a ba kuma zan fad'a ba d'in sirri ne nida d'an qanina"
Tana qarashe mgnr ta tashi da sauri zata bar gurin ya riqo hannunta ta fizge ta tafi da gudu zuwa d'akin shi tana masa dariya ya bita da kallo d'auke da murmushi kana ya tashi ya bita.
Koda ya tafi ya samu har ta d'auko jakar sa tana qarasa shirya masa kayan sa.
Ta bayanta ya rungume ta yasa hannu ya kar6e jakar ya ture ta gefe.
Cikin yanayin shagwa6a ta juyo tana kallon shi ya zauna tare da zaunar da ita kusa dashi yana kallonta yace"Allah dagaske nake miki na fasa tafiya sae gobe"
Dad'i taji har ranta ta kama hannuwan sa d'auke da murmushi tana kallon sa tace"dagaske Abban ilham meyasa?
Sbd na fahimci damuwar da ke fuskar jabir ba qaramin abu bane ya had'a ki da shi shiyasa nake son sae na sasanta tsakanin ku snn ko zan tafi dan na fahimci kmr shine mai laifin shiyasa kk 6oye min ba kya so in sani kar in masa fad'a koh?
Lumshe idanun ta tayi a hnkli had'e da koma ware su akanshi ta qara kama hannayen sa sosai a cikin nata snn tace"ba yada laifi Abban ilham kawai dai abinda yake so ne bazai yiyu ba"
Mene ne yake so?
Hm wae bintu yake son zae aura nn ta gaya masa duk yanda sukayi ba abinda ta rage.
Murmushi Abban ilham yayi had'e da girgiza kansa yace"hm in banda abinki hafsa muda ku ae mun zama d'aya kan me zaki hanashi dan yace yana son bintu bashi yace yana sonta a haka ba"
Haba Abban ilham kaddai kaima biye masa zakayi kayi tunani mana bae kamata ba wlh.
Yace"kinsan Allah Hafsa wlh tun farko ba jabir kad'ai yaso bintu ta kasance matar sa ba har dani dmn tun lokacinda na fara zuwa zance gidan ku naga bintu sak ke naji ba wanda nake son ya aureta kmr jabir amma sae na bar mgnr a raina acewar sae ta kai munzalin aure in kwad'aita masa zancen ashe shi da ya ganta yaji yana sonta ya bar abun a ransa bae ta6a gaya min ba sae yanzu da naji labari a bakin ki wanda zurfin cikin mu dani har shi yasa muna ji muna gani muka rasata, yanzu kuma da yake ganin ya sami dama kice masa a'a ae dole yayi fushi dake.
Anti Hafsa ta numfasa snn tace"Abban ilham kar ka manta matsalar bintu matsala ce da sae an fita waje da ita, fita waje kuwa ba qananun kud'i bane"
Wnn ba matsala bane hafsa kawai amincewar ki muke so idan kuma kince a'a knn kin raina da kamar mu kina ganin baza mu iya ba"
Ba haka bane Abban ilham koda ni na amince nasan bintu bazata amince ba sbd a kullum bata da burin da ya wuce ta koma gidan waheed kaga kuwa bai kamata ace naje mata da wnn zancen ba.
Shiru yayi na d'an lokaci kafin yake cewa"to ke Hafsa yanzu a ganin ki akwai yanda za'ayi bintu ta koma ga waheed?
Eh hanya d'aya ce wato yaya Abbas shine kad'ai muke tunanin idan yaje mami zata iya ta saurare shi amma shi kuma ko mgnr bintu baya son a masa ya kuma rantse kan kar Abdallah ya kuskura ya koma zuwa gun mami,to shine fa har yanzu Abdallah sae fmn lalla6ashi yake kan yayi haquri yazo suje su sami mami amma fafau yaqi yarda acewar ita bintu da ta jawa kanta taje tayiwa kanta magani ae ba uban da ya ake ta.
Abban ilham ya numfasa snn yace"hm Abbas knn soja sarkin zuciya gobe idan na koma Abuja zanje har office d'insa in same shi muyi magana inshaa Allah bazan dawo weekend d'in nn ba sae tare dashi muje a sami mami a sasanta dmn ba abinda yafi dacewa irin bintu ta koma d'akin mijinta shi kuma jabir se yayi ya haquri ya nemi wata"
Cikin nuna jin dad'i Anti Hafsa tace"nagode Abban ilham"
Yace"haba Hafsa ai kin wuce haka a gurina bari inje inga jabir in lalla6a shi ya haqura"
Tace"Aa jabir d'in ba ya fita ba"
Inafa duk fushin da yakeyi da ke ne yace ace baya nn.
Allah sarki jabir yayi haquri kar yaga laifina ba yanda zanyi ne wlh.
Yace"ae dolen shi ma ya

Please Login or Register in order to submit comment